DAN ADAM CHAPTER 26
Idan kana bani hakuri bana jin dadi wallahi Baba, ni na hakura komai ya wuce awajena. Abinda ya faru kaddara ce, kuma Allah Ya yi ba makawa sai ya faru. Ka daina damuwa kada wani ciwon ya kamaka.” Ya jinjina kai yana murmushi can kasan ransa kuwa, yabawa ya ke da kaifin basira irin na ‘yartasa. Damuwa dole ce a wajensa, ko don ma rashin sanin irin kallon da danginnasu zasu yi gareshi. A fili kuwa ya nunamata komai ya wuce. Wayarta da ke(ringing) ne ya katsesu, ta sa hannu ta janyo jakarta ta ciro don ita ta mance da ita ma, ganin mai kiran yasa ta ajiye wayar don kunyar dauka ta ke ji gaban Babannata, lura da hakan yasa shi yin murmushi sannan ya mike. “Bari dai na lek’a wajen abokan hirata yau sun ji shiru, daga nan na saka kati na kira su Yalla6ai na ji yanda suka isa. Wannan ki kaita ga daki nan akwai katifa ku kwanta anan.” Ya karashe yana nuni da Mariya. Ta amsa da to, bayan fitarsa ta janyo wayar da sauri saidai kafin ta kai ga amsawa har ta yanke, ta bi wayar da kallo cike da shauki anan take ta kira ya kuma shigowa. Ta d’aga da sallama. Faruk da ke kwance saman gadonsa rungume da filo ya lumshe ido jin muryarta ya amsa sallamar ciki-ciki. Jin yanayin muryarsa ne yasa ta fadin. “Kun isa lafiya? Ya mura?” “Alhamdulillah, kin samu Baba kin mance da mijinki ko?” Ta ji kunyar maganar, har lokacin bata gamsu da yanayinsa ba, kamar dai akwai damuwar da ya ke 6oyemata. “Ummina.” Ta kasa amsawa sakamakon jin kiran sunannata da ya yi yana zaga dukkan ga66an jikinta, ta lumshe ido gami da jingina kai da bango tana kallon sararin samaniya wanda ke cike da taurari. “Ba za ki amsa ba?” Ta daure ta amsa. “Um.” Murmushi ya yi mai sauti kafin ya ce. “Ina kewarki. Ina matukar kewarki Ummina, ban gane hakan ba saida muka dawo gida, duk sai ya yimin fad’i.” Murmushi ta ke yi saidai ta kasa cewa komai don ita kunya ma ya bata, ga kaunarsa da ke k’aruwa sosai a ranta. Ita kanta ta yi kewarsa fiye da tsammaninta. “Ba magana ko? Wannan kunyar fa ta gulma ce akwai ranar da zan kaudata don na gaji da ita tana cutata.” Ta rufe idanunta da hannu tamkar yana ganinta, banda “Um” ba abinda ta ce. “Banso aka k’i tsayar da maganarmu ba yanzu ba, saidai Baba yana da gaskiya, ni kaina zanfi so kiga danginki ko burinki zai cika tukunna. Ina kara tayaki murnar sasantawa da mahaifinki, Allah Ya k’ara kauna tsakaninku.” “Amin Yaya Faruk, nagode.” “Na gaji fa da Yaya yayannan, ki chanjamin suna.” Ta danyi dariya kawai. “Dagaske nake, ana muku ruwa?” Ta girgiza kai. “A’a.” “Ayya, mukam ruwa sosai ake yi.” Murmushi ta yi. “Alhamdulillah, kun ji dadi.” “Ina wani dadi, babu Ummina a gida?” Kamar ta nutse don kunya ta kasa magana can kuma ta ce. “Saida safe.” Ga mamakinta ta ji ya saka dariya sosai, sai itama yasa ta murmushi. Bayan ya tsagaita ya ce. “Allah Sarki Ummina, ina son wannan kunyartaki saidai please ta kasance iyakar yanzu kafin mu kai ga aure kin ji ko?” Murmushin dai ta ke yi ba ta ce komai ba. Atishawa ya saki har uku a jere, ya karashe da fadin Alhamdulillah, ta amsa da YarhamukAllah sannan ya amsa mata da “Yahdikumullahuwa wa yuslihu balakum.” Shiru ya biyo baya kafin kuma ta daure ta ce. “Don Allah ka sha maganin mura.” Ya ji dadi ainun na kulawar da ta nuna gareshi. “Banason magani, sau daya na sha ya sanyani bacci ban k’ara sha ba.” “Haka za ka daure ka…” Sai kuma ta ji nauyi ta yi shiru. “Kin damu da ni har haka Ummina?” Wasa ta hau yi kawai da jelar dankwalinta batare da ta ce uffan ba. Ya sauke ajiyar zuciya. “Zan sha tunda ba kya sona da mura.” Ta murmusa. “Ka turomin lambar Hajiya don Allah.” “Me za ki ce mata?” “Gaisawa za mu yi.” “Shikenan zan aikomiki.” Daga haka suka yi sallama, ta mike ta shiga dakin da Baba ya yi mata nuni da makwancinsu, ta gyara shimfidar, dakin katifa ce kawai sai shirgin kaya a gefe. Da taimakon wayarta ta haska ta dauko Mariya bayan ta kai ta ta yi fitsari ta shimfideta. Ita kuwa kayan jikinta ta rage ta d’ebi ruwa ta zagaya kewaye don garin akwai zafi, bayan ta yi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga na bacci cikin wadanda Faruk ya siyamata. Ta feshe jikinta da turare mai sanyin kamshi sannan ta zauna gefen katifar tana tunanin ko ina mahaifinta ya wuce? Sallamar Saude ta ji wanda ya sanyata jin wani mugun faduwar gaba, kafin ta amsa, ta tsinci muryar Babanta wanda daman ba nisa ya yi ba yana zaune kofa. “Me ki ka zo yi a gidana?” Saude ta dubeshi, daman a k’ule ta ke don acan Kawunta Isah ci mata mutunci ya yi ya nuna babu inda zaije daman tuni ta bar ganinsa da daraja. Da ta gaji da zama ta ga dai babu wanda ya kulata an barta a tsakar gida yashe yasa ta taho ko tayin abincin da akayimata bata ci ba don ta rantse gidanta za ta kwan. “Ka manta inada ‘ya? To babu inda zanje sai na yi idda.” “Idda a gidan wa? Wallahi ba ki isa ba Saude, ke ba irin matar da zan yi marmarin na komawa aurenta bace, tun muna mu kadai ki tattara ki barmin gida kafin na jibgeki na tara miki jama’a!” Ummi dai tana daga daki tana lek’ensu don tsakani da Allah har yanzu tana jin tsoronta sosai. Saude ta yi shewa. “Ahayye! Lallai Abdullahi wuyanka ya isa yanka! Har ni Saude ka ke gayawa haka? To ni kuwa yau babu inda zanje, anan gidan zan kwana don uban mutum!” Tana maganar kamar ta6a66iya, daidai da su Habiba da sauran makwafta mafi kusa suna ji, ko daga majalisar su Malam Balarabe suma suna jiyo ihunta da maganarta. Zagin da ta yi ya firgita dukkan masu sauraro, ai Malam Balarabe baisan lokacin da ya janyo igiyarsu ta shanya ba nan take ta tsinke, ya soma tsulamata yana fadin. “Kinyi kadan, karyarki ta yi karya ki zagi ubana! Kin yi kadan Saude.” Ihunta yasa mutane suka shigo, itama Ummi fitowa ta yi tana rokon mahaifinta da ya kyaleta. “Haba Malam Balarabe da girmanka? Wannan ba girma bane, dukan mace don Allah ka yi hakuri.” Cewar Malam Yahuza kenan, Saude wacce ta ci duka ta hayayyako mishi. “Kai dalla can rufewa mutane baki, solo6iyon banza da wofi, duka-duka yaushe ka samu kwato kanka a hannun Habiba?” Hakan ya harzuka Malam Balarabe ganin bakar maganar da ta ke fadawa abokinsa, ya k’ara tunzura zai kai mata duka, gam! Ummi ta rike igiyar gami da durkusawa tana fadin. “Don Allah Baba ka yi hakuri, ka kyaleta.” Saude ta mike tana gyara zaninta tana ihun kuka, Malam Yahuza da sauran mazan suka rasa bakin magana, suna shirin fita ai kuwa ta cakumo wuyan Ummi ta baya tana fadin. “Kema sai kin bar duniya yadda Hasiya ta barshi, sai na kasheki!” Ummi da ta ji shak’a ta soma kwatar kanta saidai ta kasa, cikin zafin nama mutanen suka yo kanta, dakyar aka yi nasarar kwatar Ummi daga hannunta, kuka sosai Ummi ke yi tana shafa wuya tana tari don ba kadan ba, ta ji shak’ar. Mari lafiyayye Malam Balarabe ya wanke fuskar Saude da shi, ai kuwa ta hau tsalle tana zage-zage, ya finciki hannunta tana tsalle tana ihu tana zagin iyayensa da Ummi har tana fadin “Da nasan haka za ki zama da tun kina jaririyar kema mun kasheki!!” Haka har ya watsar da ita a kofar gidan ya kulle ta waje. Mutane sai hakuri suke bata daidai da mata fitowa sukayi kallon wannan abin al’ajabin. Bata jira komai ba ta nufi kofar gidan Malam Yahuza. Hannuwanta a k’ugu tana karkad’a jiki. “Ina ki ke shegiya bak’ar munafuka? Ki fito! Ki fito nace!!!” Tana shirin shiga gidan Malam Yahuza ya tureta daman cike ya ke da haushinta. “Karki sake ki shiga gidana, kada na k’ara ganin kafarki wallahi.” Dariya ta shiga kyakyatawa ga hawaye jage-jage saman fuskarta kamar mahaukaciya sabuwar kamu tana nunashi daga sama har k’asa kafin ta rangad’a bud’a. “Ayyiririii! Eh babu shakka akuyar daure ta samu sake! Yahuza kai ne ka samu iko haka? To wallahil azim yanda aurena ya mutu kema Habiba yau naki zai mutu!” “Idan ke ce da shikan a hannu sai ki zo ki rabamu!” Cewar Habiba sa’ilin da ta leko kanta, Malam Yahuza na kokarin tsawatarmata akan ta koma ciki saidai maganar Saude ya dakatar da shi, duk jama’a na kallo, Malam Balarabe kuwa jira ya ke yi ta gama haukanta ta bar wajen ba zata shigar mishi gida ba. “Keda ki ka kashe rai! Wallahi jama’ar gari ku shaida Habiba da hannunta ta kashe Hasiya!!!” Can na hango Bokanya tana faman kyakyata dariya tana kara jijjiga abin tsafinta a hannu, cikin ihu da kururuwa ta dauki wata kwarya ta fasa tana fadin. “Kadan ku ka gani shegu! Kadan ku ka gani!! Na soma karya dukkan mugun aikin da na k’ullamuku! Daman kwa yarda da wani bayan Allah? Hahaha! Mu daman ta6a66u ne mun yarda!!! Hahahaha!!!” Wannan furucin Bokanya kenan sa’ilin da ta ke kallon dukkan abinda ke faruwa ta cikin wata k’atuwar kwaryar sihiri. (Wa’iyazubillah).1 Mutanen wajen suka yi sak, Ummi a guje ta fito daga gidansu kanta babu ko kallabi ta zubawa Saude ido jin abinda ta fad’a. Habiba fitsari ta soma saki a wando don kuwa bata ta6a tsammanin akwai ranar da Saude za ta yi mata haka ba! Gaba daya waje ya dauki salati. Wuf Habiba ta fito bayan ta ture hannun Malam Yahuza wanda ya tokare kada Saude ta shigar mishi gida. “K’arya ta ke yi! Ta haukace! Kada ku yarda karya ta ke min!!” Saude wacce bata bar kyakyata dariya ba ta ce. “Ina rantsuwa da Allah ita ta kasheta amman da sa hannuna!” Ta karashe tana soshe-soshen jiki don haka kawai ta soma jin wani k’aik’ayi a fatar jikinta. Kafin wani ya yi yunkurin karasawa gareta Ummi cikin zafin nama ta k’arasa, ta rik’e kafadunta tana kuka cikin daga murya ta ce. “Ki gayamin, dagaske kune ku ka kashe Ummana?” Dariyar dai ta ke yi itama cikin kwaikwayon daga murya ta Ummi ta amsa. “Eh! Ni da Habiba muka kasheta! Kema na so a kasheki saidai Habiba ta bada shawara a kyaleki nan gaba jari za ki zamarmana! Kuma kin zama.” Ta karashe cikin dariya. Sai kuma tiryan-tiryan ta shiga bada labarin yanda komai ya faru. Ummi batasan sadda ta fidda hannu a zafafe ta dauketa da mari hagu da dama ba, tana yi tana kuka da fadin. “Ban yafemiki ba Saude(ta fada gatsal don girman ya fadi)! Ban yafemiki ba!!” Sai kuma ta durkushe tana kuka sosai, nan aka ankara Habiba ta gudu. Ai kuwa wasu matasa suka rufamata baya. Ita kuwa Saude wacce bata ji marin Ummi ba asalima dariya kawai ta ke yi, ta karasa ga Malam Balarabe wanda ke kuka har da sheshsheka saidai ya kasa samun karfin zuwa ya rarrashi Ummi sai wasu matan makwafta ne suka zo suka dagata. “Abdullahi kai mutumin kirki ne, ka so ni sosai, saidai ni tun daga ranar da ka yimin kishiya na tsaneka.” Ta cigaba da dariya sannan ta dora. “Habiba kawata ta ban shawarar 6oye kishina kuma na bi, babu irin maganin da ban barbada muku ba a abinci kai da ita, sai kuma duk da haka ka fifita ta a kaina!” Ta karashe ciki daga murya a fusace sannan ta dara. “Kuma ta zo ta samu ciki.” Fadin haka yasa Saude soma kuka duk mutane na kallonta cike da takaici har lokacin wadanda suka bi bayan Habiba basu dawo ba, Malam Balarabe da ya rasa ta cewa tagumi kawai ya yi yana hawaye yana dubanta, can kuma ta dora tana soshe-soshenta. “Na sha gwada kashe Hasiya da dan cikinta ta hanyar duramata magunguna ina fakewa da fadin na gargajiya ne na kara lafiya, saidai banga wata illa da ya yi mata ba har zuwa sadda cikinta ya shiga wata tara ta soma nakuda muka kasheta muka bar jaririyar. A karshe na asirceka ka daina kaunarta, na saka dangin uwarta da danginka suka daina zuwa inda ku ke, amma Abdullahi duk wannan kaunar da na nunamaka bai hana ka sakeni ba?!!!” Ta karashe tana mai dibar k’asa ta watsamishi ya rufe fuskarsa. Nan kuma ta hau tsalle da soshe-soshe, baiyi wata-wata ba ya soma yunkurin dukanta dattijan suka hana. Malam Sule makwafcinsa ya ce. “Ai dukanta yanzu kuma 6ata lokaci ne Malam Balarabe, ba ka ganin ma bata cikin hayyacinta?” Malam Balarabe kawai sai ya juya ya shiga gidansa yana kuka, Ummi ta bi bayansa da sauri itama. Habiba cikin sa’a aka cafkota, ana zuwa Malam Yahuza ya tsinke igiyar aurensa da ita, nan ta hau kuka da neman gafara, Malam Balarabe ya fito aka hada kansu sai ofishin yan sanda. Habiba da kanta ta yi bayani don Saude hauka ta ke yi tuburan tana faman kyakyata dariya. Aka gark’amesu da zummar sai washegari a k’arasa maganar. Ummi da mahaifinta wannan ranar kasa bacci suka yi ga ciwon kai mai tsanani da Malam Balarabe ya kwana da shi, ita kanta Ummin da shi ta kwana sakamakon kuka da ta sha. Nafila kuwa a wannan daren ta yi shi hakanan addu’o’i. Babu wanda cikinsu ya ta6a kawo hakan, kowannensu tunaninsa bai wuce mutuwa Hasiya ta yi ba kawai ashe azzaluman ne suka kasheta. Malam Balarabe da Ummi saida suka yi kwanaki uku kafin su bar Ringim zuwa Gombe don kuwa saida aka yi shari’a a babban kotun jaha dake birnin Jigawa a karshe aka yankewa Habiba hukuncin daurin rai da rai. Ita kuwa Saude bayan an tabbatar dagaske ta haukace kai tsaye aka mik’ata asibiti, cikin danginsu babu daya da ya zo banda Malam Yahuza. A motar suna tafe har Mariya saidai ran kowannensu babu dadi suna cike da tunani, shi Malam Balarabe tunaninsa bai wuce na irin kar6ar da danginsa za su yi gareshi ba sakamakon watsi da su da ya yi, yayinda a 6angaren Ummi ta ke tunanin rayuwa ta DAN ADAM mai cike da kalabule, ga jarabta kala-kala. Shi dan Adam kwata-kwata a rayuwa ba shi da wani jin dadi da hutu face na idan ya kyautata mu’amalarsa da Mahaliccinsa, wannan kadai zai tsira da shi har mutuwarsa. Abin sai godiyar Allah, kaga dai duk mutum mutum ne amman a halayya da dabi’u an bambanta, wani sai ka rikeshi da gaskiya ya ci amanarka, wani sai ka dunga yi mishi kallon mak’iyinka, batare da sanin shi din mai sonka domin Allah bane, DAN ADAM ne zai fidda makudan kudade, ya aikata dukkan wani nau’i na sa6on Allah don kawai ya k’untatawa dan uwansa DAN ADAM rayuwa, haka kawai sai ya tsaneshi, ya hana kansa sukuni idan ya ganshi cikin jin dadin rayuwa batare da shi din ya yi mishi laifin komai ba, dan uwa sai ya cuci dan uwansa, ya kasheshi. Ta sanya hannu ta share hawayen da suka zubomata tana mai k’ara rungume Mariya wacce ta yi filo da cinyarta tana bacci. ‘Ya Allah, mu bayinKa ne masu yawan zunubai, Ya Allah ka gafartamana, Ka barmu kan tafarki na gaskiya. Ya Allah ka sa mufi karfin zuk’atanmu. Mun shaida babu abinda bautawa sai Kai, mun yi imani Annabi Muhammad(s.a.w) ManzonKa ne. Allah Ka jik’an wadanda suka rigamu gidan gaskiya.’ Tana maganar a zuciyarta, sannan ta k’ara goge hawayenta, kwantar da kanta ta yi saman kujera ta lumshe idanu tana tunanin rayuwarta har zuwa yau, tamkar rana makamanciyar yau ba zata zo ba, ranar da komai zai zo karshe. Haka ta yi ta tunane-tunane har suka iso cikin Gombe bayan sun ci awa kusan biyar akan hanya. Kai tsaye Gombe Motor Park suka shiga sannan kowa ya soma saukowa. Malam Balarabe ya tarar musu taxi. “Tudun Wada zaka kaimu.” Ina a Tudun Wada?” Cewar matuk’in. “Bayan gidan Sarki.” Suna tafe Malam Balarabe na nunawa Ummi wurare gaba daya ya kasa ma rufe bakinsa, itama saita tsinci kanta da farinciki, Mariya ma kalle-kallen ta ke yi bakinta washe har suka iso unguwar. Wayar Ummi ta yi k’ara ta amsa. Hajiya Babba ce don kuwa ta yi kiranta kwanakin, suka gaisa kafin ta tambayi ko sun isa, ta amsa mata da eh. Ta ce ta gaishe da mutanen gidan. Daga haka suka yi sallama alokacin da kuma ta ga sun tsaya daidai wani gida karami ya sha fenti ruwan madara, wanda a kusa da shi wani gidan ne shima shigensa don hatta da fentin iri guda ne. Zaune a kofar gidan, wani dattijo ne kishingide saman tabarma, a gefensa kuwa wani ne da bai wuce shekaru hamsin ba suna hira da dariya saidai tsayuwar tasi din a kofar gidannasu yasa hankalinsu ya dan koma gareta. Jikin Malam Balarabe har rawa ya ke don ko shekaru nawa ya yi ba fa zai mance wadannan fuskokin ba, Haruna yayansa ne sai kuwa Mahaifinsa. Shima Harunan mik’ewa ya yi da sauri. “Abdullah!” Jin sunan da ya ambata yasa Dattijo Malam Buba mikewa zaune daga kishingidar da ya yi yana mai gyara zaman gilas dinsa na masu ciwon ido gami da k’urawa wanda aka kira da sunan Abdullah dansa idanu. Tuni Malam Balarabe ya karaso da sauri suka rungume juna shi da yayannasa. Kawai sai suka fashe da kuka, Ummi ganin haka itama ta soma hawayen tausayamusu. Duk a silar kaddara sun rabu da juna. Ganin mai tasi ya gama sauko kayansu daga boot, ta tambayeshi ko nawa ne kudin sannan ta zaro a jakarta ta biyashi ya wuce. “Abdullah ashe za mu k’ara sanyaka a idanunmu?” Cewar Harunan kenan cikin zubar hawaye. Malam Balarabe ya na sharar hawaye ya karasa ga mahaifinsa wanda ya yi shiru yana ta faman jera hamdala a zuciyarsa ganin addu’arsa ta shekara da shekaru ta kar6u a yau. Ya riko hannuwan mahaifinsa shi kuwa Haruna ya nufi wajen su Ummi wadanda ke gaisheshi. “Malam gani gabanka, ka yankemin dukkan hukuncin da kaga ya dace, na yi babban laifi, na manta da dukkan hakkinku da ya wajaba a kaina na kula da shi, ka gafartamin Malam, na tabbatar har da k’in jin maganarku da na yi na auri son raina.” Malam ya damk’i hannunsa cikin rawar murya ya ke fadin. “Ba ka da laifi Abdullah, na jima da fahimtar hakan, shiyasa ban ta6a rik’eka ba a raina. Gareni, na yafemaka, tashi mu shiga ciki Abdullah mahaifiyarka ta sanyaka a ido ka nemi gafararta.” Da taimakon Malam Balaraben Mahaifinnasa ya mike, suka yi ciki, yana dogara sandarsa. Ummi wacce Haruna ya gama ja da hira yana fadamata irin matukar kamar da sukayi da mahaifiyarta, itama tasan hakan sakamakon hotonta da mahaifinnata ya bata. Suka mara musu baya suna mai daukar jakankunan wadanda uku ne kacal. Saida suka shiga ta fahimci ashe dai ginin nada dan girma, irin ginin nan na gidan yawa, yara suka yita binsu da kallo, Abida mata ga Usman wato Baffa ta dubi Haruna bayan shigewar su Malam Balarabe da Malam. “Waye wannan?” Yana murmushi mai bayyana hakora ya amsa. “Har kin mance da Balarabe? Ai shine da iyalinsa.” Ta zaro ido tana mai dafe kirji, yayinda ta ke bin su Ummi da kallo, Ummi ta gaisheta sannan itama Mariya ganin haka ta gaidata. Dada na zaune a rumfarta tana gyaran wake, tsohuwa mai ran karfe, idan ka ganta ba ka ce yara bakwai sun fito daga jikinta ba don kuwa da kuzarinta. Ta ajiye waken gefe ta yi sakato tana duban wanda ke rike da mijinta. Ko shekara nawa Malam Balarabe zai yi ita din mahaifiyarsa ce da ba zata ta6a mance fuskarsa ba. Kafin su kai ga karasawa gareta ta mike da sauri ta shige dakinta. Suka karasa suka isketa zaune saman gadonta na karfe tana faman sauke ajiyar zuciya. . Bayan zamansu ne ta dubeshi kamar ta tashi ta makureshi. “Me ka zo yi mana?! Ka zo ka ga ko mutuwa muka yi ka ci gado ne?!!!” Tana maganar a zuciye, hakan ya karyawa Malam Balarabe zuciya ya hau zubda ruwan hawaye. “Haba Fatima, ban sanki da zuciya ba, kada fushi yasa ki aikata abinda za ki nadamarsa nan gaba.” Cewar Malam cikin harshen fulatanci. “Nadamar…” Sai kuma ta kasa magana sai kawai ta fashe da kuka sosai don kuwa ita bata ta6a takawa ta je inda suke ba, hakazalika tun zuwan da ya yi sau daya bayan aurensa ya wuce da Hasiya bai k’ara takowa garesu ba don ko mutuwar Hasiya sai Jar Kwami ta je musu gaisuwa. Har da wannan zafin ta ke ji na dumbin shekaru har goma sha takwas da aka kwashe ba tare da ta sanya dannata a ido ba. Duk iyakar lalla6awa da ban hakuri da Malam da Malam Balarabe suka bata, babu alamar saukowarta haka suka tattara suka fita inda Malam ya ba wa dansa shawara akan ya yi hakuri har ta huce don a yanzun tana cikin zafi ne. Ko bayan fitarsu, dakin Malam din suka nufa har Haruna don Baffa yaba can kasuwa har lokacin bai dawo ba, nan Malam Balarabe ya yi sallar la’asar sannan ya yi zaman hira da mahaifinsa. Acan suma su Ummi sun samu tarba kwarai daga matan gidan da yan uwansu, daidai da Dada ta ja su jiki musamman Ummi wacce ke tunano mata Hasiya yarinya mai shiga rai da sanin ya kamata don shekaru biyun da ta yi a nan wajensu kafin zuwan mijinta sun saba kwarai da ita. Haruna ya hau ba shi labarin bayan rabuwa, Malam na sauraronsu, anan ne Malam Balarabe ya dubeshi. “Ni kuwa Malam ya labarin Kanwata Aisha? Har yanzu suna can Adamawan? Yaranta nawa da Yakubun?” Shiru ya biyo baya kafin Malam ya yi dauriyar ba shi amsa. “Sai hakuri Abdullah, Allahn da Ya fimu son Aisha ya kar6i abarsa, yanzun ta shekara da rasuwa.” “Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun!” Cewar Malam Balarabe kafin ya soma kuka har da sheshsheka, kanwarsa ma ciki daya ta rasu ba tare da ya sanyata a idanu ba? Rabonsa da ita tun kafin tafiyarsa Ringim. “Addu’a za mu yi mata, ciwon koda ta ke fama da shi har da abin ya gagara Yakubun suka dawo nan tare da ita don ta yi jinya, saidai takan yawaita tambayarka, har Yakubun yaso zuwa wajenka ya kira mata kai amman Allah baiyi ba, har ta rasu. Yaransu uku, babbar wacce ta ci sunan Hasiya, shekarunta sha shida, tana can Jar Kwami hannun Lamido kakanta, Yusuf da Aminatu kuwa suna can Adamawa hannun mahaifiyar ubannasu. Malam Balarabe ya jima kwarai cikin jimami don kuwa bayan mutuwar Hasiya, wannan ce mutuwa ta biyu da ta girgizashi. Rayuwa kenan. “Allah Ya ji kan Aishatu, Yasa ta huta. Zuwa jibi sai naje Jar Kwami mu gaisa da su.” “Ku tafi gobe, Manu ya jima yana son ganin jikarsa.” Cewar Malam kenan, ya amsa da toh. Garin ya yiwa Ummi dadi matuka, har hawaye ta yi ganin irin gatanta, ashe daman tana da gata har haka? Kwanon abinci kuwa sai wanda ta za6a ta ke ci, don daga matar Baffa har Halima matar Haruna kowacce saida ta aiko, aka yanka kaji aka soyamusu. Dada sai nan nan take yi da su, acewarta su basu da laifin komai awajenta…….