YANAYIN RAYUWA CHAPTER14

😞YANAYIN RAYUWA😰😭🌷🌷🌷🌸🌸💐💐. CHAPTER 14 

 By halimatusadiya ( saliha)🥰 Rubber chair,yaja ya zauna akai, nurse ce tashigo,tace ma mom zata ma zali aluran barci. Tanaji ance alura,ta tashi da karfin ta,sauri yayi ya kamata,se ido take ta zura wa😳. Duk ta surata,cikin cool voice ya cema ta ” I hakuri,bazeyi zafi ba.” Yafada cikin rarrashi,kallon su kawai mom takeyi. Bayanda bayiba amma taki yarda, nurse din taga haka,se tace ” Bari inyi,a cikin drip din kawai,tun da taki.” Mom tace ” ok,ba damuwa,kiyi kawai.” Acikin drip din, tayi mata,tana fita,ya Umar ya dauki waya dun kiran ya Usman. Dun lukacin daya fita,baya nan,nan ya zayyana mishi halin da zali ke ciki, Amma Kuma yace mai jikin da sauki. Zama yayi shiru,daga shi har mom kuwa da sake saken dayake ya zuciyan shi. 💞💞💞💞💞💞💞 SCHOOL Yau tunda yazu school,yarasa meke mai dadi,gashi kuma tunda safe bega zali ba. Yayi ta tunani,haka har time nashi yayi. A tunanin shi inyaje class ze ganta amma ba tanan,a daddafe yayi lesson nashi yafita. Halima kuwa,bata san meya hana zali zuwa ba,kuma taga yau fiskan Uncle ba fara’a yayi lesson. Break time,zaune take a inda suka saba zama,ji tayi school din ba ma dadi da zali ba tanan. Khalil dake kufan, class nasu ya hangi halima,yasa ya issu gunta dun sanar da itta zali ba lafiya. Sallama yamata,ta amsa cikin sakin fuska,dun ta sanshi. Kallon halima yayi yace ” Emm, halima daman zali ce ba lafiya,shiyasa bata zo school ba.” ” Subhanallah,meke damunta haka?” Tafada cikin damuwa,yace ” Ciwon kaine.” Tace ” ayya,kagaishe ta,insha Allah,zanzo ingaishe ta,inna kuma gida.” Ya amsa da to,kafun ya mata sallama,ya wuce class. Uncle kyari,kuma yana kumawa class,ya shiga kiran wayan zali amma ba’ayi picking ba,hankalin shi ba karamin tashi yayi ba. Tunani,iri iri yakeyi,chan kuma kume ya tuna ohho,yatashi yayi waje. Wani student yakira yace yaje ya kira mai,halima dun class nasu daya da yaron ya santa. Ba musu ya tafi,be same ta a class ba,yasa shiga duba inda suke zama da zali. Yayi sa’a yasame ta a gun,ya gaya mata aiken,bata kawu kumai aranta ba,ta tashi ta bi yaron zuwa office da Uncle kyari. Da sallama tashiga office din,shiko yaron ya kuma. Amsa wa yayi hade da nuna mata gun zama,ba musu ta zauna akan kujeran da ya nuna mata. Gaishe shi tayi,ya amsa. Gyran murya yayi,kafun yace ” Halima,ya zulaihat bata zo school ba.” Kanta akasa tace ” Bata da lafiya ne.” Cikin ta damuwa yace ” Meke damunta.” Tace ” ciwon kai.” Duk sunyi magana cikin harshen turanci,shiru yayi na dan lukaci,kafun yace zata iyya tafiya. Ba musu ta tashi ta tafi class,da tunanin ,meyasa Uncle ke tambayan ta zali,kude ya santa ne,kaiya ma ai student nashi ne dole ya tambaya. Haka take ta tunawa har takuma class. Hospital🏥 Tunda aka mata alura bata jimaba,tayi barci. Kye na gidan mom ta bama driver ya kuma dashi gida,kar yaran su dawo,ba kuwa kuma ba kye. Ba musu ya karba cikin girma mawa,ya wuce gida. Yana issa ya sami,aunty hapsat a veranda, bata kye din yayi,ya gaya mata halin da ake ciki. Har to 6 aka sallame su,dun ruwan yakare. After two days jikin zali yayi sauki,Alhamdulillah,amma har week din yakare bataje school ba,halima kuma tazo ta duba ta da jiki. Yau yaka Sunday,ranan da za’a kawu zo neman auren aunty hapsat. Gidan kuwa Yana busy,su mama sunzo da yaranta. Bayan sallah la’asar aka kawu,buhun gishiri biyar,goro fufu biyar,se katun na sweet da chewing gum,bansan nawa bama. Alhamdulillah,dun ansa ranan aure,nan da 5 months masu zuwa. Ranan har dare,su mama suka kuma,tayi tayi su sake suyi hira da zali,amma zali taki sake mata. Duk sawon kwana kinnan wayan zali akashe. After sunyi sallah isha,suna zaune a falo suna hira,maryam ce ta kalli zali tace ” Sis,dauko mana wayanki man muyi snapping,na kayan.” Shiru tayi dun,ta manta inda ta jiye wayanta,chan kuma ta tashi tace ” Bari in duba.” Dakin su tashiga,ta fara duba wayan,acikin lukan takardu ta samo. Zama tayi a bedside din,ta kunna wayan,yana bude wa,ta se message ba adadi,na shiga,bata bi ta kansu ba. Dun itta duk sammanin ta MTN ne,fita tayi ta nufi falo,tana issa ta mika ma Maryam wayan. Nan tafara snapping din kayan,mom ce ta kalli maryam tace ” Ohh Maryam kekam dasun waya,inna ga inan saya miki,waya kam,ba aiki.” Dariya sukayi zali tace ” Waya ga masu Kuna towo.” Ta fada cikin suka na tana ma Maryam gullo, Maryam na ganin haka tabi kan zali. Kafun ta issu gun da zali take tuni,zali ta tashi ta arche a dari. Binta tayi,harda ki. By halimatusadiya saleh( saliha)🥰 😞 YANAYIN RAYUWA😰😭🌷🌷💐💐🌸🌸🌸. By halimatusadiya ( saliha) saleh🥰 Har daki tabita,zali ko tana shig tayi toilet ta rufe da key,sayawa wa Maryam tayi tace ” Ai ba’a bayan gidan zaki kwana ba,zaki fito kisame ni.” Zali ta kelkely da dariya tayi tace ” agun zan kwana.” ” Ba kinre naniba,za ki fito ai.” Inji maryam Zali tace ” anki afito in.” Daga nan zali bata sake magana ba,maryam kuma guri ta samo ta zauna,tana jiran fitowan zali. Wasa wasa,zali bata fito ba,maryam data gaji da zama,tayi waje abunta. Zali koh data gaji da jiran fitan maryam,se ta fara wanka. Jin shiru tade na jin musin Maryam yasa tafita. Daure take da towel,ta rike tana rike da kayanta ahannu. Ajiyewa tayi ta wuce dress mirror ta zauna, lotion ta fara shafawa,tana gamawa ta fisa turare. Gun worldrop ta wuce dun dauko sleeping dress nata. Taji ana faman bude kofa,amma bata juya ba,dun itta ta’aza su Maryam ne. ” Ki gama muyi magana” Muryan ya Umar taji,kaman daga sama dun batayi sammanin shi bane. Juyawa tayi zuciyan ta na duka uku2,shi ko yana magana yaganta,haka,bushe wa yayi yana kallon. Itta koh,ganin kallon yayi yawa,yasa ta tayi saurin daukan hijab nata a hangar. Da sauri tasa,duk abunda take be cire idon shi akanta ba. Zama tayi a bedside din tace ” inna jinka.” Tayi magana cikin inina. Dakyr ya iyya takawa har inda take ya zauna,akusa da itta,jin yana faman zama gun da take yasa ta dan masa mai. Sun dauki sawun mintuna suna zaune,bawan da yache ma dan uwansa Kala. Ganin shirun yayi yawane, yasa ya sa hannun shi ya rike nata. Wani irin shock sukaji a tare,yasa yayi saurin sakin hannun ta. Sun kuyar da kanta tayi,ta kasa magana,dun yanda zuciyan ta ke bugu uku2,ta rasa meyasa kullum in suna tare se zuciyan ta ya sinke,kuma inya taba ta seta ji shocking. Sintan muryan shi tayi yana chewa, ” zalleee.” Wani irin sanyi ne taji a zuciyan ta yasa, bata san lukacin da tace ” Na’amm” Gyara murya yayi yace ” plxx inna so kigaya min me yasame ki ranan,kar ki manta nagaya miki,kuda yaushe zan iyya tambayan ki,kuma i na so kigaya min yanzu.” Bata samman yana rike da maganan haryan zuba,duk samanin ta,ya manta. Jin bata ce kumai ba,ya sa yace ” Look zali,kinsan cewa nifa mijin kine,kuma bakida wanda zaki fadawa sirrin ki seni,kuma abunda ya dame ki yadame ni, kuda ba dukaba try to tell me,plxx🙏🏻” Dagowa tayi ta kalle,ido su ya hado yasa tayi saurin sauke nata idon kasa. A take taji wani tausayin shi,yanda yayi maganan,why not ta ga yamai,wata killa ze famince ta. Sintan kanta tayi tace ” yayah wani ne yace yana sona,plxx yayah ka taimaka ka sak…..” Wani wawan mari yadauke ta dashi,dun saba ragen yanda yaji zuciyan na duka uku2,wani bakin kishi ne ya takure mai a wuya,baisan lukacin da ya gakara wanke ta da mari ba. Sabara gen marin da tunda take bata taba jiba,dun ko mama bata taba mata irin marin nan ba. Fado tayi daga kan gadon,dafe da kuncin ta,wasu zafa fan hawaye ne ya zubu mata kaman anbude tab. Nuna ta dayasa yayi cikin rawar murya,yace ” Ase bakida hankali,da aure na akanki kice wani na sonki,uban wama yace yana sonki, ehh” Ya fada cikin daga murya,itta kam se aikin kuka take takasa musa wa daga inda take. Nufuta yayi,wani damka yamata,yace ” Zaki gayamin wa ya yace yana sonki ko sena dake ki.” Jikin ta ne ya hau rawa saba ragen yanda yarike ta. Mom da take dakin ta taji kaman hayaniya a dakin su hapsat yasa ta fita dun jiyo lafiya. Tana fita suka ci karo dasu hapsat zasu je dakin dun suma hayaniya suka ji,a dakin su. Basu saya bata lukaci ba suka nufi dakin,ban kade kufan mom tayi suka shiga. Suka tarar da ya Umar ya na rike da zali itta koh se kuka take,yace ” Baza kiyi magana ba.” Yada ga hannu ze wanke ta da mari,yaji anrike hannun shi. Yana juyawa yaji,an wanke shi da wani wawan mari,wanda yasa ya rike kuncinshi,yana duba wa ya ga waye ne,mom ya gani,suna hada ido tasake wanke shi da mari. Zali koh yana sakinta tayi bayan mom tabuya,tana shishshekan kuka,kan kame mom tayi dun gani take kaman ze sake kama ta. Cikin bacin rai mom tace ” uban wa yasa ka kayi mata duka, ehh!,me ta ma.” Ku magana ya kasa,dun zuciyan shi duk adagule yake,ga laifin zali,ga marin da mom tamai akai,wani bakin ciki ne yaji. Saba ragen ransa yabace,har jijiyan kansa suka tashi,se kumi yake hadawa. Ganin mom ta sare shi da tambayoyi ne yasa ya tashi ze fita. Da karfi ya bangade kufan,ya fita,binsa da ido kawai su mom suke yi. Yana fita mom ta ja zali zuwa dakin ta,suna fita se ga dad yana faman fitowa daga dakin shi,ganin su yace ” Lfy nake jin hayaniya?” Mom tace ” lfy, babban yayah ne ya daki maryam,dun ta taba masa laptop.” Yace” Allah ya shirye su,itta ma Maryam tana da nata. ” Mom tace ” Ameen.” Zali dake rakube a jikin mom yasa dad be lura da itta ba,nan sukayi sallama dad ya kuma dakin shi,mom kuma ta shiga dakin ta da zali. 💞💞💞💞💞💞💞 Umar koh,yana shigan daki, toilet ya wuce,ya Usman na ganin yanda Umar ya shigo dakin yasan akwai abuda ke damunshi. Be mai magana ba,ya bishi da ido kawai har ya shiga toilet, ” Allah ya sauwake.” Yace a fili. Umar kuwa ya dauki sawun 30 minutes a toilet,kafun ya fito. Kumai be shafaba ya nufi bed din ya kwanta,ya Usman yace mai ” Lafiya kuwa,me kedamun ka.” Bece mai kumai ba ya juya,yayi kwanciyan shi,ganin baida niyan amsa mai yasa,ya shigaba da lasa wayanshi. Ranan Umar baiyi barci da wuri ba kusan 12 kafun barawun barci ya saceshi. Suna shigan daki,mom tace ” Cire hijabin ki ki kwanta da safe muyi magana.” Cire hijabin tayi,dun ta ma manta towel ne ajikin ta,wani kallo mom ta mata wanda yasa ta jin kunya. Sunkuyar da kanta tayi tace ” mom bari indauko kayana.” Mom tace ” ba inda zakije.” Waya ta dauka takira aunty hapsat,ta nadauka call din tace ” Bama maryam kayan zali ta kawumin.” Bata jira me hapsat zata ceba ta kashe wayan. Plxx comments, more love Fan’s ,Allah bar zumunci, special thanks to banking hausa novels.🥰🙏🏻 By halimatusadiya ( saliha) saleh🥰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *