DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 12 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 12 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

zage ki. Sai daga baya aka gano kin zama kurma, kina iya magana amma ba kya ji, amma a duk sanda jirgi zai shige za kiji rugugin jirgi
Kin rayu a hannun kaka ta, ta rike ki ke da Izaddeen dan wan Inna ta, wanda kun shaku da shi sosai. Kin san abinda ya hana auren ku da shi? Mahaifiyar sa ta ce ba zai auri kurma ba”.
Izzatu ta mike, “Umma na gano ko ni din ‘yar
waye, ni ‘ya ce ga Musbahu Kaltingo. Zan nemi uba
na, ba zan yarda a sake kirana da shegiya ba”. Ta mike, “Naji abinda nake son ji”. Surayya ta biyo bayan ta, ta ce. “Ni kin katse min labarin da nake so inji”. “To ai an gama, me yai saura da ba ki saniba?”
Ta janyo wayar ta don ta turawa masoyants (text), sai ko taga sako, ta soma karantawa.

Izzatu, inada damuwa, ina bukalar tattali da addu’a, na rasa inda zan sanya raina, don na rasa ni din DAN WAYE?
Izzat,  ba ki damu da damuwa ta ba. Ko ba uba aka haife ki zan aure ki, bana so ki sa damuwa a ranki.
Izzat, kina fushi dani saboda na fada miki abinda dan uwanku ya fada akan ki, shi kenan, ni dai na san ina son ki, in kinyi fushi dani wa zai kula da damuwa ta?
Cikin zafin nama ta soma mai da (text) din tamkar yana kallon ta. Ba na kusa, ina dakin Umma ta, yanzu na
taho na gani. Ina so ka kwantar da hankalin ka, ka
nutsu, saboda bana so lafiyar ka ta samu matsala. Ka
sani ina son ka”.
Ta tura, bai fi minti biyar ba taji shigowar wani.
Uhm.Ta ji Uhm din nan har cikin ranta, ta mayar masa.
Uhm ba amsa bace, kana nufin ba ka yarda da so da kauna ta bane? Wallahi ina son ka, ko baka da iyaye ni na ishe ka rayuwa, zan zamar maka bango abin jingina.


Www.bankinhausanovels.com.ng Ta tura masa, yana karantawa murmushi yayi, ya rubuto mata.Mu hadu a Facebook.
Sun hadu a facebook suna ta hirar su cikin jin dadi da sanar da kowa halin da kowannen su yake ciki
Yau ashirin da uku ga watan shida, yau ce kotu ta zauna don ci gaba da sauraren shari’ar Mah da Haj. Saratu, to ko DAN WAYE?
Yau ma kotu ta cika, don mutane suna mamakin wannan al’amari. Yau shari’ar su ce ta farko, kowanne fangare akwai lauyan sa.
Weediyan da Weesal suna zaune, sai ga Mustapha ya shigo, duk ya rame.
Ran Weediyan ya kara baci, taji uwa ta kashe Momyn musty, duk da cewa uwa daya uba daya suke da momin su.
Haka bangaren Mubarak, ransa ya baci, baya son rama alheri da sharri, amma ai ba laifin sa bane. Bayan shigowar alkali aka soma gabatar da shari’a, wannan karon akwai manyan lauyoyi wadanda suke kare hakkin talaka, haka akwai masu yin abu don Allah, irin kungiyoyin matasa, duk sun halarci shari’ar. Don da yawa sun dauki aniyar kwatarwa Umma Halima danta.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kam Mubarak so yake ya samu damar da za su kadaice da abokin sa, dukkanin abokan sa sun halacci gurin, su Alpha da su Faisal.
Lauyan Haj. Saratu, wato Barrister Sunusi shi ya fara mikewa yayi gaisuwa, bayan magatakarda ya gabatar da kara, ya ce yana son yin magana da Alhaji Abdulmajid.
Barrister Alpha Jazi ya mike, ya ce shi ne
lauyan sa, kuma duk tambayar da za a yi masa a
shirye yake da amsar ta.
“Ina bukatar takardar haihuwar Mustapha”.
Barr. Alpha ya mikawa Barrister Sunusi, ya duba yayi dam, ya mikawa Alkali, ya ce. “Iyakar tambaya ta kenan”.
Barrsiter Lu’ulu’a Ahmad Tijjani ta mike,
“Suna na Barr. Fatima Ahmad Tijjani, amma ana kira na Barrister Lu’ulu’a, ina aikin kare hakkin talakawa da mata da marasa galihu. Ina tare da abokan aikina Ahmad Yahaya, da kuma Umar Ibrahim. Ina so zan yi magana da Haj. Saratu”. Lauyan ta ya mike, “Ayi min tambayar da za
a yi mata”. Ya dubi alkali, “Zai iya jin tambayar da zan
yi mata, amma amsar sai ita. Ta fito tana taku irin na isassun mata, ta ce.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“kin ce Mustapha ba danki bane, kin zauna da sbi tun yana yaro, amma ba ki fada ba shin meye dalilin ki na haka?”
Ta ce, “Na jima da sanin Mustapha ba dana bane, don lokacin da na haife shi a asibtii da aka tambaye ni me na haifa naga namiji ne da wani katon digon baki a tsakiyar cikin sa, zai yi fadin kobo, to daga nan ban san yadda aka yi ba, lokacin da na farfado aka bani dana da na duba babu wannan
tabo. Na sanar da mahaifiya ta, sai ta ki amincewa”. “Saboda me ta ki amincewa”.
“Saboda yawancin lokaci ba ta yarda da magana ta .
“Saboda me?”
“Dama haka take, ba ta fiya yarda da maganganu na ba”. Ta ce, “Ina son ganin mahaifiyar taki idan tana gurin nan”.
Haj. Lami ta fito, Barriter Lu’ulu’a ta kalle ta.
“Meye sunan ki?” “Suna na Haj. Lami Saminu”.
Ta ce, “Ke ce mahaifiyar Saratu?”
Ta ce, “Eh, ni ce”.
“Ke ma kin yarda Mustapha ba danta bane?” “Ban yarda ba, saboda tunda ta haife shi take sanar dani ba danta bane, wani lokacin sai ta fadi
Www.bankinhausanovels.com.ng
kamar mai iskokai. Kuma sannan tunda ta haife shi ta tsane shi”.
“Dama can tana irin haka ko sai da ta haife
“Eh ta dade tana yi tun tana yarinya, amma kuma bayan haihuwar sa abin ya fi damunta. Kuma Mustapha ya fi kowa damuwa da ita, in ciwon ya tashi duk inda ya ji mai magani yana hanya. Ni dai ina ganin aljanun kanta basu yi dai dai da na danta ba”.Ta ce, “Na gode”.
Ta juya ga mai shari’a, ta ce.
“Ya mai girma mai shari’a, Haj. Saratu ba mai cikakken hankali báce, tana da tabi a kwakwalwa, ina so kotu ta sa a binciki kwakwalwar ta, amma ba ta sahun masu hankali”.
Kotu tayi tsit, alkali ya ci gaba da rubuce
rubucen sa, ya ce ya daga shari’ar zuwa sati hudu
Masu zuwa, don tantance hankalin Haj. Saratu.
A farfajiyar kotu Mubarak ya tari Mustapha,ya ce
“Sannu Yallabai”.Ya kalle shi, ya ce, “Ya gari?”
“Lafiya”.
Ya ce, “Na ji ance ka ajiye aiki, saboda me? Ko ka samu wani?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya cc, “A’a, bana son rama alheri da sharri”. “Kada ka damu, kaddara ce daga ni har kai
mun hadu da kaddara”. “To Mustapha in haka ne me zai sa ka share min?”
Ya ce, “Bana son ganin ka, a duk sanda na kalle ka ba zan ɓoye maka ba ina damuwa, nafi so
ka rabu dani rabuwa ta har abada”. Hawaye ya biyo fuskar Mubarak, sai ya juya.
A lokacin Weediyan ta karaso tana murmushi, tana tsintar kanta cikin farin ciki.
Ta ce, “Musty”.Ya ce, “Sai matar manya”.
Sai tayi fuska, ganin ta sha kunui sai shima bai
ce komai ba.Yaushe ka zo?”
Ya ce, “Yau din nan?”.
Ya ce, “Bari in shiga motar ki”. Tayi murmushi ta ce, “Mota ko gwangwani?”
Ya ce, “Haba Weediyan, kin fi karfin hawa
gwangwani”.
Ya shiga motar ta, Alpha ya leko.
“Ina za ki kai min amini?”
Ta harare shi, “Wai aminin ka, to aminina ne”
Duk suka yi dariya, ta ja motar tayi slow a
Www.bankinhausanovels.com.ng
inda Mah take, Mustapha ya fito ya ce..Mah”.
Ta kalle shi fuska a sake, ta ce.
“Wai ko kana gari?”
Ya ce, “Yau na shigo”. Ya ce, “Shigo mu kai ku gida”.
Suka shiga, Mubarak bai tanka ba, suka tsaya, ta bude ta shiga, suka tarar da har sun riga Baba
dawowa, ya ce.
“Mah, ya kwana biyu?”
Ta ce, “Ina son ganin ka”. Ya ce, “Zan dawo Mah”.
Weediyan ta ce, “Zan kawo miki shi Mah dinmu”.
A mota ma hirar Mah din suke, Weesal ta ce. “Musty, Mubarak yana son ka, yana damuwa da kai, ya kamata ku yiwa juna afuwa, duk kuna jin haushin sanin juna, Allah Shi Yasan dalilin hada ku”.
“To naji, ashe kin koma wa’azi’. Weesal ta ce, “Ba haka bane”. Ya kalli Weediyan, ya ce, “Za kuyi min
rakiya”.Suka ce, “Ina?”Ya ce, “Sai mun je”.
Sun isa gidan su Izzatu, ba su dade da
Www.bankinhausanovels.com.ng
tsayawa ba suka fito, tana ganin sa da mata ta ja kafafunta ta kasa karasawa, shi ya karasa. Ta ce, “Su waye wadannan?”
Ya ce, “Kanne na ne”. “Ai nasan baka da kanne”.
“Ya’yan kanwar babata ne”.
Ta ce, “Bana son kana kula mata, don ina da zafin kishi, bana son kowa ya kula min kai”. Lokacin da ya ce, “Mu karasa, Weediyan ta kunsa, ji tayi tamkar ta mutu. Ta Karaso, Weesal tace.
“Sannu”.
Ta gai da su, suka kasa lura, ta ce su Shiga, Weediyan ta shiga mota, don bata bisu ba, itama Izzat ganin ta shige mota sai ta ki tafiya, tayi ta jansa da hira don ta gano lallai akwai magana.
Ta tsare shi da ido, “Wace ce wannan?” Ya ce, “Weediyan ce”.
Ta ce, “Ni da ita wa za ka aura?” Ya yi murmushi ya ce, “Saboda me kika tambaye ni?”Ta ce, “Amsa nake so”.
Ya yi murmushi, “Ke mana tawan”.
“Good, kada ka sake zuwar min da ‘yar fashin miji, na gano so take ta kwace min kai”.
Ya yi dariya, ya ce, “Kishi, kishi kumallon
Www.bankinhausanovels.com.ng
A lokacin ta shige, su kuma su Weesal suka fito suka shiga mota. Musty shi ya ja su zuwa gidan su, ya shiga ya fito ya leko ya ce.
“Matar manya, me nayi miki?”
Tana dago ido yaga yayi jawur alamar anci
kuka an koshi, ya ce.”Lafiya?”
Ba ta tanka ba illa ta juyo ta ce.Zo ki ja motar mu tafi gida”.
Weesal ta ja mota suka hau iti, ta ce.
“Ya aka yi matar manya?” Ta ce, “Ni na rasa kanki, ki fito fili kiyi abu kin kasa”.
Ta ce, “Ai na fada miki ina son Musty ko? Ina da burin babban mutum mai Naira, ba zan kara haduwa dashi ba, saboda ko na soshi shi kuma yana son kurma, ni inyi kishi da kurma? Ina! Na rabu da shi.
Tabbas ina son Mustapha, sai dai nafi son kudi da shi, nafi son hutu da shi, kuma na fi son in taimaki al’umma”, Weesal ta ce, “Ke kam kin shiga uku, da
gidan talauci kika fito kila kiyi sata ko kiyi kwace”. Ta ce, “Ni fa son kudi na ba irin na ‘yan matan yanzu bane, ni ina son in taimaki al’umma, in
Www.bankinhausanovels.com.ng
taimati mabukata”.
haka ne, amma ai ko kinyi babu lada, domin don ace kinyi kike yi ba don Allah ba”.
Ta zaro waje, ta ce, “Allah Ya sani don Shi nake. Ni fa Allah Ya sani bani da burin kaina, ma’ana ban taba aje kudi don in amfana ba, kuma na san ina da kyau, su kuma maza sun fi son mai kyau, shi yasa na ce sai manya zan aura”.
Weesal ta juyo ta ce, “To yanzu in kin juyo
irin auren da kike so kuma ya kulle bakin aljihun sa
ya za kiyi?” Ta ce, “To ba zan auri Bahaushe ba, zan auri
yaren baban mu”.
Ta ces, “Ashe Turkey za kije?” Ta ce, “Haka nake tunani”.
“Uh matar manya, amma fa ban yarda dakeba”.
Ta ce, “Kamar ya?”
Ta ce, “Kina son Mustapha kuma na dade da sanin ko kinyi aure ba zaki iya zama da wanda kika aura ba, saboda inda’ duk kake zaton zaman aure ya
shige nan”. Ta zumburi baki, ta ce, “To auren kika yi bare
ki san kansa?” Ta ce, “No, duk ‘yan group dinmu matan aure
ne, kuma wallahi ba abinda suke Boyewa duk na san

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *