DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 1 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE

DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 1 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE

 

 

Cikin sa’a fati ta samu makaranta,

Haka abinda take nema ta samu wato

•Phamacy; sai dai zai kai Karshen wata kafin ta

tafi. Haka nan yayi daidai da bikin Habit da

Abida, don haka ya zama dole ta jira sai anyi

bikinta ta tafi Faruk kam baya nunawa Maryam Kiyayya, sai dai ko kadan bai taba jin son ta a ransa a maisayin mata ba.

Don haka ko shimfida basu taba hadawa

ba. Maryam tun tana dauka ya kyale ta ne har

abun ya soma damunta, don ko sha’awarta bai

taba nunawa ba bare taja aji.

To wai meke faruwa? Nan dai ta yi shiru

bata kula shiba ta ga iya gudun ruwan sa, haka

ba ta yi yunkurin gayawa kowa ba. Biki kam ya

yi biki, Fati gidan su Abida ta koma gaba daya,

haka nan su Umma da zuriyar su Fati duk sun yi

kokari tamkar bikin yar gidan, gudunmawa kam

ba iyaka. Bayan an gama komaì Kano aka kai

amarya, haka nan Fati ita ce kan gaba, don kuwa

ta dade tana son zuwa garin ta dan yawata ta ga

gari ba wai taje fisha ba. Faruk babban abokin

ango hakiKa ba karamin dadi yaji ba, don ya san

dole Fati tazo in ya so su yi wacce za su yi, don

kuwa auren Maryam ba zai sa ya fasa niyyarsa

na auren taba.

Abin da ya bawa Faruk mamaki shi ne,

duk programs din da aka yi sun hadu da Fati,

amma yana mata magana tamkar ba ta san shi

Ba.Fat! Fati!!” Yana kiran ta amma ko tsayawa ma ba tayi ba bare ta muna alamun amsawa, kuma tabbas ta ji shi. Da sauri ya sha gabanta,

“Wai Fati me kike nufi ne?”Tsayawa ta yi tana kallon sa tamkar ba ta sanshi ba.Fati wannan wane irin abu ne? Ko baki gane ni bane?’

Dogon tsaki ta ja ta wuce, fisgota ya yi da

karfin gaske wanda yasa har taji wani

azababben ciwon kai, ya daka mata tsawa,

“Kina da hankali kuwa? Ina miki magana za ki ja min tsaki? An ja din kayi abin da za ka yi, Umar

Faruk bari in gaya maka, lokaci ya wuce da

tsawarka zata tsorata ni, tunda ka min magana

na Kyale kaima sai ka kyale ko ana dole ne? In

soyayya ce nace bana yi ana so dole? To bari ka

ji, daga yau kar ka sake takurani ka matsa min,

Faruk bana sonka, bana son.Saukar mari

ta ji a fuskarsa, ba tayi mamaki ba, don ta zaci fiye da haka daga gare shi, don gaskiya ta san ta cusa masa bacin rai. To amma sai ta juya ta kalle shi ta yi murmushi taCe,Na gode”Ta juya tayi cikin gida.Sauri yayi ya bita fuskarsa cike da

tsantsar damuwa da nadamar marin da ya yi

mata.Fatima!” Ya sha gabanta yana shirin

fadar wani abu.Ta tare shi,Don’t ever Said

something to me, okey

Da gudu ta karasa cikin gidan ta barshi tsaye a wajen tamkar yasa hannu aka ya yi ihu.

Ba wanda yaga abinda ya faru tsakaninsu.

daga ita sai shi sai Allah. Hakika

Hmm an fara muje zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *