ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 32 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 32 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

da shi, amma ita za ta warware wa kanta, ba za ta sanya ni in ji kunya a garin nan ba Ita kuma Inna tace Ai yanzu idan su Aliyun

sun aiko daga gidansu tunda ta ce shi take so, sai a daura musu aure, albasshi sai ta wuce makarantar da take kwakwa, idan ma tana aiki ne ayi biki” Shi’kuma Baba ya ce,

“Haka din za a yi Aisha, amma dani niyyata sai ta gama jami’a, amma yanzu aiba ta yiwuwa, gara mu kau da ita kada ta hada mu da jama’ar gari. Allah ya sauwake” Inna ta ce,Amin Suka ci gaba da maganar azumi. Baba ya ce,Kin san mun yi uku cikin kwana goman da suka

Wuce, yaushe za mu fara ukun wannan goman?”

Ta ce,Malam ai sai mu bari sai ran Litinin mu

tashi da shi”Ya ce,Allah ya nuna mana

Da wannan shawarar hirar ta tashi suka kwanta.

Ni kuwa a wannan rana na nemi barci na rasa sai

tunanin abubuwan da suke afkuwa a gare ni nake haka cikin dán Kananin lokaci nake yi, na ga ranar da na dawo Inna ke gaya mini cewar Kabir na Kaduna ya z0, kuma mahaifina ya yi masa kalami masu kwantar da hankali,an samu maganarsa ta lafa, saboda mahaifina ya nuna masa na kawo masa wanda nake so saboda haka ya

hakura. Ya ce,To, ya amince amma shi ba zai taba

fidda rai a kaina ba sai nayi aure”Mahaifina ya shiga gida ya fiddo masa kudin da ya taba ba ni a Kaduna ya mika masa, ya ce shi kuma atabau ba zai taba amsar abin da ya ba ni ba, nafi karfin wannan a gare shi. Haka nan mahaifina ya

hakura ya kyale.To an lafa wannan kurar, yanzu kuma ga wani wanda ya fi maza da yawa wayo yace, duk abin da na fada masa ya yarda, amma kuma shi a nasa bangen kamar ma munyi aure mun gama. Kuma ga mahaifina ya ce, nice mai warware wanna rigima,wanda ban san yadda zan nuna wa Ibrahim ba. Sai dai in daina fita idan yazo. Na kunna fitila na duba agogo na ga karfe uku na dare, sai na fita  na yi alwala na zo na fara nafila har yayin da na yi sahur da shayi da biredi, na kara bude Alkur’ani mai girma na fara karantawa, sai da na yi sallar asuba sannan na kwanta.Ranar ban fito ba sai da misalin sha daya da rabi na safe, shi ma sai da Hadiza tazo ta tada ni ta ce,Ke yar banza tashi ga iyayen Mukhtar can sun cika mana gida” Na ce,Haba Hadiza

wallahi azumin tsofaffi nake yi shine za ki maka mini duka haka?” Tace Lalle Asia kin nuna kin isa, yanzu yau da azumi kika tashi amma shine ba ki sanar dani ba ni ma in dauka?” Na yi mata bayanin yadda a kai har na dauki azumi, sal tace

“Ke bari in je kicin Inna Aisha ta bar mini aiki, tana can gidanmu wajen tarar baki, wallahi

Asiya ba kigà akwatin da na hango ba, gaskiya

Mukhtar ya kashe kudi” Na ji dadì na yunkuro daga kwance na zauna, na ce, Ashe yau za mu sha kallo, bari dai in je in yi wanka ko na ji karfin jikina Da azuhur muna zaune a falo da ni da Hadiza,sai ga Zainab ta rugo aguje ta ce,

“Yaya Hadiza ga bakin Katsina nan sun z0 ganin ki”Muka yi sauri muka shiga dakina muka kulle kofa, sukazo suka yi, suka yi amma muka ki bude musu kofar har suka gaji suka tafi

Bayan sun tafi muka fito muna ta dariya, daga

nan sai Yusuf ya shigo ya ce,Yaya Asiya ana nemanki a kofar gida”Na yi sauri na dauki bakin gyalena na rufe kaina muka fita tare da ‘Zainab da Madiza.Mutumin da yake nema na direban Ibrahim ne, bayan mun gaisa ya miko mini wasika, ya ce,Ga kaya can cikin mota, kuma an ce ya koma da amsa Na ce, To”

Su Yusuf da Zainab suka shigo da kayan, ni

kuma na shiga na ba da amsa. Kayan da Ibrahim ya aiko mini kiret din Kwai uku da katon din kafirison, sai dankali a cikin buhu da kayan shayi cikin kwali, sai gyararrun kaji shida. Ga abin da ya rubuto a wasikarsa.

Ranki ya dade,

Ya ya mutan gida? Ina fatan suna lafiya, kuma

ana azumin dai ko? Ina fatan an daure an dauka, idan haka ta samu a yi buda baki faliya. Asiya jiya gaskiya ba ki barni na sami barci ba kamar yadda na saba, kinsan dalili? Wallahi kyawon idanuwanki, wadanda suka yita walainiya da taimakon hasken farin wata shi ya fi

tsaya mini a rai. Yadda nake jinki a yanzu a jikina

kamar mun shekara da haduwa ba kwana daya ba. Ina gai da ‘yata Hadiza.

Naki, Ibrahim Tsiga.

Mun karanta wannan wasika kamar sau uku ni

da Madiza muna kallon yadda Ibrahim ke son kutso kansa da dabara.

Lokacin da Inna ta komo gida mu kuma muka

nufi gidan su Hadiza don mu ga kayan zancen da aka kawo mata.

Akwatuna guda biyu babbai da karami

masu suna Delsy. Kaya kam sun hadu babu ce kawai babu, duk abin da muke sO

na tsarawa Mukhtar ya Juba wa Hadiza.

Inna Hafsatu taCe,Ni yanzu motar da zan

samu ta kai ni Danja wajen dangin mahaifin su Hadiza su ga wadannan kayan nake tunani

Sai na ce.Inna ki yi wa Baba magana mana

Zai samo motar ofis dinsu ba sai a kai ki ba, don dai yini guda Ta ce,

“Wallahi Asiya wani lokaci har kunya nakeji

duk yadda wani nauyinmu yake shi ke dauke

mana shi, yanzu idan bai sami motar ofis din su ba, karshe ya dauko mana ta haya, kin ga irin haka ai da matsi NaCe, Inna to mene ne,

lokacin da Yaya Aminu na nan duk hidimar makaranta ba shine ke yi mana ba, hatta kudin tara shi ke bamu, Kuma kin san dai Baba ba zai so ba a ce kin shiga motar haya da wadannan akwatunan haka ba. Yanzu idan na je gida

Zan gaya masa in ya so ko ranar litinin ne sai a kai ki Tace To shi ke nan Asiya”. NaCe,

“‘Bari in je gida in fara shirye-shiryen

buda haki Na mike muka nufi gida da ni da Zainab. Na sami Inna ta idar da sallar la ‘asar ta zauna na sari wuri kusa da ita na zauna muka fara maganar kayan sannan muka gangaro kan kayan da ibrahim ya kawo mani

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *