DAWUUD
CHAPTER 3
‘daure fuska siyama tayi sosai tana kallon aleeya tace, 1
Wat do you think you’re doing aleeya?
Abinda Yakamata nayi tun ranar farko banyi shi zanyi yanxu.
‘dari biyu siyama ta Ciro cikin school bag dinta ta jefawasu Layla tareda Jan hannun aleeya tace,
Let’s go zuciyana tafara tashi da warin dau’darsu. 1
Fizgewa tayi cikin ‘daga murya tace,
Dasu zan tafi so gwara ki dauki ‘dari biyunki zatai Miki amfani gurin Hawa taxi kar kafin mukai warin dau’darsu yasaki amaye kayan cikinki..
Wat?,,,,siyamar ta fada tareda matsowa gabanta tana rage murya tace,
Karma kifara tunanin ‘daukar wainnan sadaka yallah din Dan haka salin alin kibasu sadakar dazaki Basu mutafi coz wannan abin dakikeyima you’re disgracing your self. 1
Hannu ta qara miqawa Layla akaro na biyu laylar taqara qanqame Bilal har lokacin kuka sukeyi.
Tsaki siyama taji cikin tsawa tace,
Kubar Nan shegu matsiyata. 2
Miqewa sukayi aleeya ta damqo hannun Layla tareda kallonta Ido cikin Ido tace,
Zan taimakeku zaku bini?
Qura Mata ido Layla tayi akaro na farko,
Sake tambayarta aleeya tayi tana kallonta tace eh zasu bita.
Murmushin farin ciki tasaki tareda qara riqe hannun laylar suka nufi mota batareda taqara waiwayar siyama ba ta sakasu mota tacewa driver sutafi. 1
Wani mugun huci siyama ta furzar tana cewa,
Allah yasa wannan taimakon yazamo muguwar qaddarar rayuwarku ta har abada,
Ina muku baqin bakin Allah yasa wannan shegiyar sadaka yallar tazamo babban bala’in dazai wargaza rayuwarku gabaki ‘daya atare… 5
Idan ita Bata zamo muguwar qaddararki ba Toni zanzamo muku muguwar gobarar dazata qone farin cikinku da rayuwarku duka. 5
Tunda suka shiga motar tayi shiru tana kallon Layla itakuwa Bilal daketa farin ciki ta qurawa ido yaune karo na farko dasuka ta6a shiga mota arayuwarsu.
Babban gidan dasuka shiga yasa ta qanqame hannun Bilal harsuka fito motar.
Kallonta aleeya tasakeyi tareda qara riqo hannunta suka nufi cikin palon gidan.
Ammy da abbanta na zaune apalon suna magana tashigo da sallama hannunta na riqe qam da hannun Layla dake biyeda ita kamar raqumi da akala. 1
Tsaye ammy ta miqe tana kallonsu Layla dasukafi Mata Kama da mahaukata arikice tace,
Aleeya suwaye wainnan?
Ahankali tasaki hannun Layla ta matso gaban abbanta ta durqusa murya a sanyaye tace,
Abba ina qaunarta tun ranar farko Dana ganta ranar da mahaifinsu ya rasu mukaje Dan Allah Abba ka taimakesu., 1
Kallonta yayi cikin kulawa ya tayarda ita ya jawota kusadashi yace,
Aleeya ai nabasu taimako tun…..
Girgixa Kai tayi tace,
Abba sonake kazama uba agaresu inason sudawo Nan taredamu ingantacciyar rayuwar dakake bani nakeso kabasu. 1
Kallonsu Laylar ammy tayi taga yanda sukayi wani iri kalar tausayi saitaji jikinta yayi sanyi Nan take wata zuciyar ta ingizata data kar6esu matsayin ‘yaya kodan ‘yarsu qwaya ‘daya tal data nuna son hakan. 1
Shiru Abba yayi ganin tafara hawaye yace,
Shikenan yanxu dai zasu zauna kafin gaba zansan abinyi.Rungumesa tayi tareda cewa, +
Thank you Abba.
Ammy miqewa tayi ta miqawa Bilal hannu tace,
Zoka fadamin sunanka.
Ahankali yakalli Layla kafin ya matsa kadan yace,
Bilal.
Jin tsami da warin dasuke tashi ajikinsu yasa tayi saurin Kiran shafa’atu Mai aiki tace taje dasu tayi musu wanka.
Harsunbi bayanta aleeya tayi saurin riqo hannun Layla tareda sakar Mata murmushi tace,
You’re my responsibility from now on so I will be the one to clean you up.. 1
Sunkuyar dakai layla tayi sbd batasan abinda aleeyar tafada ba saidai binta datayi har cikin qaton lafiyayyan room dinta dayaji adon komai blue and white Bilal kuwa shafa tatafi dashi danyi Masa wanka.
Kallon Abba ammy tayi bayan tafiyarsu tace,
Allah zai biyaka for this kaida ‘yarka sbd tun farko haka Yakamata kayi kodan ita babbar dake mace.
Sauke numfashi yayi ahankali yace,
Tunda aleeya na qaunarsu I have no other option but to Join the Q,
Insha Allah zan kwatanta Basu kyakkyawar rayuwa.
Allah yatamu riqo tace tana kallon qofar dasukabi.
Kayan jikinta tasata cirewa tareda miqa Mata blue towel ‘dinta daqyar ta tube ta ‘daura tana cewa,
Ina Bilal.
Murmushi aleeya tasake tana tattara tsumman kayanta data cire tana cewa,
Anje yimasa wanka ki kwantarda hankalinki kinji.
Toilet suka shiga tsoro da mamakin gurin Yakamata Amma miskilancinta yasa hakan Bai fitoba
Aleeya tajata bakin shower tun ba’afara wanke kaiba ruwan datti suka Fara zuba Nan take towel ya canxa kala sbd dama qin cirewa tayi.
Mamaki da tsoro dau’dar dake fita ta Bata Amma hakanan takejin Bata qyamarta tasa shampoo tayita wanke Mata Kai harsaida ta qararda kusan robar shampoo ‘din.
Sabulu da soso ta damqa Mata a hannu tareda juya tafice daga toilet din.
Jiki asanyaye tayi wankan tafito daure da sabon babban towel ‘dinda aleeyar ta nuna mata arataye.
Tasowa tayi tajawota ta zaunar gaban mirror tana goge Mata jiqaqqen gashinta tana kallonta ta cikin mirror fuskarta ‘daukeda murmushi tace,
Haryanxu Baki fadamin sunanki ba nadaiji na qaninki ‘dazu saura naki.
Kallonta Layla tayi kafin ta sauke Kai ahankali tace,
LAYLA Amma baabana nakirana da NUR.
Murmushi aleeya tasaki tareda dawowa gabanta ta riqo hannunta tace,
Ni Baki tambayi sunanaba.
Ahankali tace,
Naji dazu anfada.
Ok kifada naji da bakinki.
Ahankali ta “dago takalli aleeyar tace,
Aleeya.
Miqewa tayi tana Jin farin cikin daga yanzu tasamu ‘yar uwa Kuma qawa bazata qara komai ita kadaiba.
Kayanta ta ‘dauko gown black da sabon pant da vest tabata tana cewa saka Bari nakawo Mana abinci.
Ficewa tayi taje kicin da kanta ta ‘debo musu abinci a plate ‘daya takawo tareda robar coke biyu.
Kallon abincin Layla tayi ta ha’diye wani tsinkakken yawu kafin ta ‘dauke Kai tana wasa da sarqar hannunta.
Aje abincin tayi tana kallon sarqar da Laylar ke wasa da ita tace,
Sauko ga abinci.
Kallon abincin tasakeyi kafin asanyaye tace,
Tareda Bilal zanci.
Karki damu Shima gashican za’a saka Masa nasa.
Miqewa tsaye tayi tana qara sanyaya muryarta tace,
Dan Allah inaso naci taredashi munsaba bamaci dabam.
Okay okay Bari nakirashi sai yazo kuci wannan Ni naci nawa dabam.
Da sauri taje takirawosa suna shigowa da gudu yayo gurin layla Yana cewa,
Layla dubi kayan da’aka sakamin Masu kyau Kinga harda takalmi aka bani kumafa harda wanka akamin kema ji anbaki Kaya Masu kyau Dan Allah Layla karmu tafi muyita zama anan harmu gir……
Rufe Masa Baki tayi tana murmushin farin cikin ganin yanda yayi fes farin ciki da murna fal ataredashi.
Abincin gabansu aleeya ta nuna Masa cikin dariyarsa tace,
Ga Kuma abinci Yana jiranka kaci saika ture.
Zaro Ido yayi yawunsa na katsewa ganin taliya da miyar kwai da namomi.,
Tunda suke Basu ta6acin taliya ba har gwara nama idan sallar layya tayi idan yaje yawon bara ko aikin yakan samo tsokoki suci.
Zama yayi da sauri Yana jawo hannun layla Yana cewa,
Zo muci layla Kinga harda namafa.
Zama tayi ganin ganin aleeya ta fita Nan suka Fara cin abincin jikinsu har rawa yakeyi dukkaninsu
Kallonta yayi cikin dariyar Jin Dadi yace,
Layla wlh abincin Nan Dadi Allah yasa su riqemu suce suna sonmu wlh idan suka koremu ba inda zamu kuka zamuyatayi muqi tafiya..
Dariya tayi ahankali tana Kai lomar taliya bakinta tace,
Da ganifa sunada kirki bazasu koremu ba kumama aleeya nada kirki tana sonmu…..
Dariyar datake riqewace tun dazu data samesu sunata faman cin abincin ta kubce Mata ta qaraso tana cewa,
Bilal layla tafadi gskia ko kowa baya sonku ni ina sonku daga yanxu nima nazama yayarka.
Cikin Jin Dadi jikinsa haryana rawa yace,
Da gaske zamuyita zama anan bazamu qara kwana bola ko titi ba.
Hawayen tausayinsu suka ciko idanuwanta ta jawosa jikinta tace,
Name alqawari insha Allah bazaku qara rayuwa ako inaba sai taredamu.
Ahankali Layla ta ‘dago murya a sanyaye tace,
Mungode.
Zaunawa tayi tareda saka hannunta a abincinsu tana cewa,
To nima aci Dani tunda daga yanxu nima Dani za’ariqa cin abincin.
Suna gamacin abincin ta sake jawosu suka nufi palon Abba suka qara gaishesa ahankali ya riqa yimusu tambayoyi akan rayuwarsu Nan Bilal yayita fada Masa komai tin talauci da wahalar dasukasha tun baabansu nada rai har zuwa yanxu itadai tana rakube gefe.
Cikeda tausayawa ammy tajawota tana cewa,
Sannu kinji Layla.
Kai ta ‘daga ahankali tana wasada sarqar hannunta Wanda yake ‘dabiarta.
Janta aleeya tayi suka koma ‘dakinta shikuwa Bilal zagewa yayi yanata bawa Abba labari abban na sauraronsa qaunar yaron nashigarsa sbd kewar yara qanana data shigesa gashi ba ranar samunsu sbd bazai qara ta6a haihuwa ba.
Ammy kuwa dariya da tausayin labarin da Bilal din ke bayarwa kawai take sbd duk yakai qarshen kalma saiyace Dan Allah su riqesu karsu koresu.
Mamaki da tausayine yakama aleeya lokacinda sukazo sallah taga yanda laylar keyi Sam ba ilimi aciki suna gamawa ta juyo ta kalleta tareda gyara zama tanayi Mata gyara. 3
Ita kuwa sunkuyar dakai kawai tayi tana sauraronta.Lokaci yaja Ahankali tafara sabo da kowa na gidan Bilal kuwa ba ruwansa tuni yayi sabo da kowa musamman Abba kamar dama Nan aka haifesa ammy kuwa Layla takeji matuqar ji da it’s duk da har lokacin takasa sakewa gabaki ‘daya aleeya ce madai ta sake da ita sbd yanda take matuqar ji da ita Wanda Dan Dole kowa keji da Layla agidan sbd aleeya. +
Wata ‘daya sukayi agidan suka tattara suka koma Lagos sbd can dama suke da zama hutu da aiki sukazo yi duk da dai su Yan asalin Nan ‘dinne.
Sosai su Layla sukayi mamakin ganin girma da kyawun gidansu nanan din Dan duk kyawun na adamawa wannan yafi.
Decorations din dakin aleeya aka canxa musu komai bibbiyu aleeya blue Layla pink Amma gadonsu ‘daya.
Kaya sosai ammy ta ‘dinka musu kusan komai iri daya sbd gabaki ‘daya aleeya cewa tayi batason komai nata asiya musu sababbi iri daya da Layla.
Ba iyayenta da Masu aikin gidan kadaiba hatta ita kanta layla mamakin tsananin qaunarda aleeya ke Mata takeyi sbd kaf rayuwarta ba’a ta6a nuna Mata qauna irin wannanba saidai iyayenta.
Bilal kuwa ‘dakinsa dabam da Mai kula dashi Shima komai ansaka Masa tundaga kan wardrobe kayan wasa dana karatu sbd suna dawowa Basu wani jimaba aka sakashi makaranta primary 1 Amma ana hada Masa da lesson sbd yayi saurin fahimta Dan na class na Masa wuyar ganewa tunda ba ta6a shiga aji yayiba.
Layla kuwa Mai lesson guda aka dauko Mata sunayi ba qaqqautawa ga malamin arabic dake zuwa har gida Yana musu su duka uku Dan dama aleeya Bata zuwa islamiya saidai malam yazo gida ya karantar da ita.
Kullum dare kafin su kwanta sai aleeya tayita nanata Mata karantunta na lesson na addini kuwa sai sunyi sallar asuba. 1
Ada aleeya Batada wata walwa ko sakewa kullum tana daki kwance Wanda hakan ke matuqar ta6a zuciyar iyayenta harsuka dauko siyama ‘yar yayar ammy riqo Amma rawar kanta da rashin nutsuwarta yasa suka mayar da ita gashi Sam basa shiri sosai da aleeya kullum cikin fada suke da kokawa da komai sai anrabasu Amma yanxu zuwansu Layla yasa hankalinsu kwanciya matuqa sbd ganin farin ciki a rayuwar ‘yarsu su kansu yanxu hankalinsu yaqara kwantawa ganin gidan yasake kammala da yara Dan kuwa dukkaninsu jinsu sukeyi kamar yayan dasuka haifa uwa uba yanda Bilal yasake musu Yana yanda yakeso kamar sune suka haifesa ba ruwansa.
Lokacinda su aleeya zasu rubuta junior waec aka kutsa layla cikinsu ta zana duk da batai wani kyauba Amma ba laifi tasamu 4 credit shima sbd antaimaka matane sosai gurin rubutawar hutun shiga senior class suka fara cikin farin ciki sbd next hutu tare zasu koma and this time around boarding school zasu duk da ammy bataso sune sukeso Abba yace kuma tunda sunaso sai ankaisu.
Kwance suke a ‘daki suna kallon hotunan dasukai a wayar ammy Bilal yashigo hannunsa riqeda wayar ammy ‘daya Yana game yace,
Ammy tace kubata wayanta.
Ba Wanda ya kallesa cikinsu aleeya tace,
Ka Kai Mata na hannunka wannan muna hotuna ne.
Juyawa yayi da gudu saidai suka jiyo ihunsa da qarfi Yana Kiran Layla.Azabure suka fito suna kaiwa Palo suka tsaya kallon wadda ke tsaye da babban akwatinta da alama shigowarta kenan sukaci karo tayi wani mugun ball dashi.
Da sauri aleeya ta qarasa ta riqosa daidai fitowar ammy tana cewa,
Lafiya waye ya ta6asa aleeya kune ko….
Ganin siyama tsaye yasa sake fara’a tana cewa,
Siyama kece daga zuwanki Kika ta6amin ‘da.
Wani ‘dacin baqin ciki ta ha’diye daqyar ta qaqalo murmushi tace,
Wlh karo mukayi bamu luraba.
Nasan arina dama bayason tafiya kullum saidai gudu,
Sannunki da hanya tafiyar bazata Kuma fa ko ‘dazu nakira antin mun gaisa Amma Bata fadaminba.
Eh wlh ammy ninace Dan Allah karta fada muku nafiso ku ganni.
To ai kin kyauta saiku wuce ciki ki huta kici abinci.
Dakinsu ta nufa da akwatinta batareda ta kalli ko gefenda Layla takeba sbd zata iya ha’diyar zuciya sbd baqin cikin ganin yanda harta zarta aleeya kyan gani duk da aleeya ma ba bayaba gurin kyau.
Ammy Jan Bilal tayi suka wuce dakinta layla kuwa na ganin haka tayi kicin gurin shafa’atu tana tayata aikin abincin dare.
Aleeya ma kicin din tazo bayan taje sun ‘dan ta6a fira da siyamar ta zauna kan freezer tana kallonsu suna aiki sai surutu take musu na wani labari suna dariya hankalinsu kwance.
Da daddare ma kafinsu kwanta Saida siyama taso cin zarafin layla kamar ammy tasani ta Aiko Bilal yakira layla tace tayi kwanciyarta a ‘dakinta itakuma ta wuce dakin Abba.
Tunda siyama tazo gidan yazamewa layla wani iri sbd tsangwama duk da alamu dayawa sun nuna su Layla sun fita matsayi agidan yanxu hakan ke qara Mata wata irin tsanar Layla har cikin jininta takejinta duk da layla da ammy sunqi Bata fuskar wulaqantasu laylar duk saitaji zama gidan yafita ranta daqyar tayi sati biyu ta tattara takomawarta gida ta shiryawa uwarta qarya da gaskiya akansu laylar Nan itama umman ta qullaci ammy akan wulaqanta siyamar da’akayi kan sadaka yallah ‘yayan tsintuwa.
Siyama na tafiya gidansu yadawo yanda yake hankalinsu Layla ya kwanta gashi lokacin tafiyarsu makaranta yayi tuni akayi musu komai aka kaisu Bilal harda kukansa shima akaisa bording school akasamu aka lalla6asa bayan kwana biyu tuni ya manta da maganar bording yafara sabawa da kadaicinsu danma shafa’atu ta iya debe Masa kewa sosai idan Abba na gari kuwa shekanan yafi kowa farin ciki.Ranar dasuka Fara kwana a hostel aleeya na ganin dare yayi tsoro Yakamata tafara kukan neman gida murmushi Layla tayi cikeda tausayin aleeyarta tadawo kusada ita ta kwanta tana rarrashinta itakam data Sha kwana bola da titi sam bataji tsoron kwana anan dinba kawai dai sai kewar gida dasu Bilal da ammy. +
Kuka sosai aleeya tayi duk sai laylar hankalinta yatashi itama saidatayi kukan.
Tun ranar kullum tare suke kwana a gado ‘daya sbd kullum sai aleeya tayi kukan dare Kuma idan ba Layla kusada ita Bata iya bacci ahaka harsuka Fara sabawa da yanayin rayuwar makaranta sukadai,
Sam basuyi wasu qawaye ba sbd basason wani yashiga tsakaninsu Wanda ammy tayi musu fada sosai akan duk sukayi qawaye to saisun shiga tsakaninsu shiyasa Sam sinqi yarda suyi qawa ko ‘daya Dan kar a rabasu sbd zuwa lokacin jisuke bazasu iya rayuwa ba junaba..(ha’di daga Allah). 1
Sosai aleeya ke dagewa tana fahimtarda Layla duk karantunda ake musu itama Kuma Layla itake dagewa kulada komai nasu gurin zamansu na hostel sbd duk wata wahala aleeyar Bata Saba da itaba.
Ahaka harsukai exams sukayi hutu
Ranar dasuka dawo Bilal da ammy murna kamar me Amma su ammy sunsha dariyarsu ganin yanda suka rame sukai duhu musamman ma aleeya da Bata Saba da wahala ba ko kadan.
Sukuwa mamakin ganin girman bilal sukayi Dan dama shi jikinsa irin Mai girman Nan ne.
Tunda suka dawo hutun gaske sukeyi Dan koina basa fita so biyu kawai suka fita ‘daya tareda ammy ‘daya Kuma sukadai direba yakaisu gidan qawar ammy gurin birthday party din ‘yar qaramar ‘yarta.
Kamar qyatawar Ido hutunsu ya qare suka koma school.
Sannu ahankali harsukai ss3 lokacin tuni ‘yan matanci ya bayyana Dan kuwa kowaccensu tazama budurwa kuma ba laifi kowace nada sama da qasa daidai jikinta duk da dai dukkaninsu baza’a kirasu da sirara ba ko Masu qiba jikinsu saidai aleeya tafi Layla jiki kadan ita Kuma layla tafi aleeya tsawo kadan ta 6angaren kyawu kuwa saidai ace Masha Allah Dan kuwa ‘yan matan na ammy sunadashi Layla kyawunta na buzayen asali yafito aleeya kuwa kyawun asalin fulanin adamawa.
Ranar dasuka gama makaranta ranar abbansu yayi musu kyautar manyan wayoyin da kyautar zuwa umrah gabaki ‘dayansu gidan Nan suka hau murna da tsalle tsalle.
Bilal zuwa lokacin Yana js3 ne Amma girman jikinsa harya kusa kamosu Kuma lokacin tuni yarinta ta tafara tafiya yafara sanin kansa Dan har musabaqar qur’ani yashiga sabuwar islamiyar da aka kaisa bayan tafiyarsu makaranta Kuma yazo da uku kuma hakan ba qaramin alfahari yasa su Abba ba sbd zuwa lokacin kowa tunanin yake dukkaninsu ‘yayansa ne.
Satinsu biyu suka wuce umrah dukkaninsu.
Lokacinda layla taganta gaban ‘dakin Allah tayi kuka sosai sbd ko acikin mafarki Bata ta6a gangancin tunanin samun irin wannan rayuwarba saidai batasan Mai Allah yatanadar wa rayuwarsu agaba ba Ashe,.
Tayiwa mahaifanta dasu Abba addua ba iyaka kafin musamman ta roqi Allah karya kawo komai na duniya dazai shiga tsakanin qaunar dasukewa juna itada aleeyarta sbd aleeya wani 6angarene na rayuwarta dasai mutuwace zata rabata dashi duk da tasan qaunar da aleeya ke Mata bazama ta kwatanta da wadda ita take mataba.Tana gamawa ta juyo ahankali ta nufi gurinda su aleeya da Bilal ke jiranta sbd ammy da Abba suna tareda baqi a masaukinsu yau Basu fitoba.
Fitowa sukayi daga masallacin suka tsaya wani tsadadden gurin Shan coffee da cake sbd shine yawanci Layla fitiso takasa iya cin abincin garin aleeya da Bilal kuwa komai rashin da’din abinci sai sun gwada cinsa.
Su aleeya ne agaba tana bayansu wayarta take dubawa kanta na qasa.
Karo tayi da mutum gabanta yayi mummunan fa’duwa saita kasa ‘dagowa ta durqusa qasa ta ‘dauki wayarta ta ta6a da sauri zata wuce……
I think you’re taking what’s mine miss…
Cak ta tsaya jikinta ya ‘dauki rawa Nan take Sam hakanan takejin batason ha’da Ido da koma waye
Saurin kallon hannunta tayi taga ba wayarta bace ta ‘dauka da sauri ta miqa Masa batareda ta juyoba..
Hannu yakai zai kar6a….
Dawood…aka kira sunansa daga bayansa kar6ar wayar yayi batareda ya sake kallon gefentaba ya juya Yana kallon maska daya kirasa..
Come on man the coffee will get cold.
Qarasowa yayi ya zauna suka Fara Shan coffee ‘dinsu suna tsokanar sufyaan dayayi wani iri waishi missing Mariam ‘dinsa yake amatse yake dasu koma gobe.
Murmushi dawood yayi yace,
You know you’re unbelievable sufyaan Sam idiot baka gajiya da sex.
Dariya maska yasaki Yana sipping coffee ‘dinsa yace,
Oh my see who’s talking..I think gwara sufyaan sbd ko yaushe yaso zai daina idan yaso Amma kana tunanin that crazy girlfriend of yours zata barka gaba…
Tayani fada Masa maska and the idiot keep saying she’s not my type I’m just managing Amma he’s always inside her legs… 1
Murmushi yasaki Jin wulaqancin dasuke Masa yace,
Two idiots.
Amma deep inside sun tado Masa da kewar saraah dinsa taso biyosu yaqi yarda sbd matuqar tana kusa dashi bazai iya haquraba saidai har abada baya fatar aikata makamancin hakan gari Mai tsarki suda sukazo ibada.
Kallonsa maska yayi Yana cewa,
Ji Wanda kewa wani fada he’s missing his chewing gum already.
Qyalesu yayi tareda lumshe fararen oily eyes dinsa yanajin yanayi na farin ciki na shigarsa.
Zama sukayi aleeya ta kar6o musu coffee da cake Fara Sha sukayi suna fira Wanda duk yawanci surutun aleeya da Bilal ne ita kuwa lumshe idanuwa tayi ahankali tana Shan coffee ‘din tana sauke ajiyar zuciya ahankali sbd har lokacin jikinta sanyaye yake da kukan datayi gaban kaaba.
Ta cikin qatuwar mirror glass din dake cikin gurin ta hangosu zaune a table ‘din bayansu,
Su ukune kowannensu na dukan kyau da hutu daya bayyana jikinsu qarara.
Ido ta qura Masa zuciyarta ta buga da qarfi tayi saurin sunkuyar dakai tareda aje cup din hannunta ta miqe tace,
Ta gama su tafi Dan dama Suma sun gama.
Tunda suka dawo masauki ta kwanta shiru tanajin numfashinta na fita da sauri daqyar tasamu bacci ya ‘dauketa tattareda sabon alamari atareda ita.