TSANANI
CHAPTER 15
Mijin Adda na shigowa aka nuna masa kayan da doctor ya bani, cikin farin ciki ya hau d’aga kayan ya fara gode masa da wannan ƙoƙarin da yayi min, kallona yayi ya miko min kuɗaɗen da ya bani.
“Karbi Sa’adatu kiyi abinda kike ganin ya dace da su” cikin girmamawa na dube shi.
“Ku bar shi Abba na bar muku duniya da lahira”
Yaji dadin abinda nayi masa sai ya karbi kuɗin yace Adda taje ta kaiwa Innah su yi shawarar a kan abinda ya kamata a siya min da su wanda xai amfane ne ko zuwa gaba.
Washe gari bayan nayi shirin makarantar islamiyya, misalin ƙarfe biyu na rana naji kiran wayar doctor cike da nutsuwa nasa hannu na ɗauka tare da kara wayar a kunnena, ban ce komai ba sai da ya fara magana.
cikin siririyar muryar shi yace
“Salamu alaikum amaryar doctor” ya faɗa tare da rausayar da kanshi
Amsa masa nayi da “wa alaikumussalam” ina ɗan sakin murmushin farin cikin sake haduwa da doctorna.
Wani ɗan murmushi ya saki, har cikin xuciyar shi yana jin daɗin muryar Sa’adatu, yana mantawa da komai idan yana sauraren ta.
Shafa sumarsa yayi tare da cewa
“Da fatan dai kin kula min da kanki, shi ne kuma jiya nayi ta kira da daddare baki ɗauka ba ko har an fara ja min aji ne”
Xaro ido nayi kamar yana kallona
“Aji kuma?? Ni ai ba ni da ajin da xan ja maka doctorna”
Murmushi yayi wanda ya sanya dimple din da ke fuskarsa lotsawa.
“Kina da shi mana gimbiyata ke dai Allah ya bani ke ki gane matsayin ki a wannan zuciyar”
A hankali na amsa masa da “Ameen”
Barka da safiya yayi min sannan ya faɗa min yana kofar gida yana jirana, dakin Adda na shiga na faɗa mata sannan na fita wajen shi.
Yau ma jingine yake jikin motar shi cikin shigarsa ta kayan likitoci yayi matuƙar kyau kayan sun kara zayyana masa kyansa, tare yake da yaransa guda biyu yan kyawawa kamar su ɗaya da baban su kamar an tsaga kara, babbar baxa ta wuce shekara uku ba sai karamar mai shekara biyu kana ganinsu xaka ga kamar yan biyu ne sbd tazarar su ba yawa, rike yake da hannun babbar karamar kuma yana rataye da ita a kafadarsa har suka shigo cikin soron, yana tafe yana min wani kallo wanda ke ƙara narkar da xuciyata.
Cikin ladabi na gaishe shi tare da kamo hannun yara nashi.
“Ku zo nan yarana”
A hankali babbar ta miko hannunta ita kuma ƙaramar ta makale a kafadarsa a lamar baxata xo ba, cikin gwaranci ta gaishe ni.
Da sakin fuska na amsa mata tare da mannata a kirjina.
Tambayar sunayen yaran nayi inda ya faɗa min babbar sunanta fateema amma ana kiranta da Hanan sai ƙaramar ita ce Raihana.
Yar siririyar ajiyar xuciya ya sauke
“Ga yaran ki nan na kawo miki su fara sabawa da ke kafin ki dawo gidansu da rayuwa, xan dawo anjima na dauke su idan na dawo daga aiki”
Ya ƙarasa maganar yana mikewa tsaye.
Cikin sigar shagwaba nace “Har xaka tafi doctor na ban gaji da kallon kyakkyawar fuskarka ba”
Sunkuyo wa yayi dai-dai fuskata numfashinsa na sauka a saitin wuyana.
“Zan dawo na ganki Babyna nima dole ce xata sa na tafi na bar ki, gashi naga kema kin yi shirin makaranta, ban so na makarar da ke malam ya dakar min matata”
Cikin sigar shagwaba na dube shi
“Tunda ina da kai babu wanda ya isa ya taɓa ni, idan kuma baka kishina ne to?”
Dan siririn murmushi yayi
“Ni kuwa nake kishin ki da ina da hali ko namijin kuda baxan bari ya taba min jikin matata mai tsada ba”
Murmushin farin ciki nayi ina jin daɗin wadannan maganganun nasa, hannu yasa a aljihu ya miko min kudi.
“Karbi kiyi kudin motar zuwa makaranta”
Saurin makale kafada nayi
“Ka bar shi baxan karba ba kuɗin da ka bani jiya ma ban kashe su ba ballantana ka karo min wasu”
Tsare ni yayi da Manyan idanuwansa
“Ki karba idan ba haka kuma za mu yi faɗa da ke”
Da sauri na tashi na ja hannun Hanan muka shiga gida kasancewar Raihana taki yarda da ni, sai da na tabbatar ya tafi sannan na fito don tafiya makaranta.Tare da Hanan muka je makaranta, duk wanda yaga yarinyar sai ya yaba kyanta, gaba ɗaya mutane basu bari ta xauna a wajena ba, kowa rububin daukanta yake yi.
Bayan mun fito sallar la’asar mu’allim ya aiko yaro ya kira ni, da har xan bar Hanan a hannun khadeejah sai kuma na tafi da ita office din.
Kaina a sunkuye nake tafiya har na iso gare shi, fuskata dauke da murmushi cikin sansanyar murya nayi masa sallama amma bai amsa ba, sai leken fuskata da yake yi yana murmushi.
Ina jin saukar numfashin sa a kumatunta, cikin sigar shagwaba nake turo baki tare da kawar da kaina gefe guda ina cewa.
“Mutum yana ji ana yi masa sallama amma baxai amsa ba”
Salon da nayi amfani da shi wajen yin maganar ne ya sanya shi sakin siririyar dariya yana cewa.
“Idan ma ban amsa ba ai laifinki ne Sa’adatu”
Da sauri na xare idanuwana ina tambayar shi, tare sauke shi a kan kyakkyawar fuskar shi
“Laifina kuma?”
Lumshe kyawawan idanuwansa yayi yana fadin
“Masha Allah tabarakallah kina da kyau Sa’adatu”
Juyar da ido nayi gefe guda yayin da kaunarka shi ke ratsa dukkan wani sashi da bargo na jikina, ina ji a raina baxan iya rayuwa da wani da namiji ba bayan mu’allim.
“Ina wuni na faɗa” tare da riƙe hannun Hanan.
Tsura min idanunshi yayi sai can ya amsa da Lafiya lau.
Tsuke siririn bakin shi yayi.
“Me yasa jiya nace zan zo kika hana ni? kuma nayi ta kiran wayarki a dai-dai lokacin da xan zo ɗin baki ɗauka ba kuma baki biyo kirana ba”
Ya ƙarasa maganar yana taɓa kwantaccen sajen shi gami da ɗan yamutsa fuska.
Cikin marairaicewa nace
“Jiya ban jin dadi ne tun rana nake ta aikin bacci har dare ban farka ba, sai yau da safe shi yasa ban kiraka ba amma kayi min afuwa dearna”
na ƙarasa maganar ina tsugunnawa alamar ina neman afuwa.
Kafin na kai ga tsugunnawa ya kai hannu xai dago ni da sauri na kauce tare da buge hannun shi, komawa gefe yayi yana yar dariya tare da rungume hannuwan shi a kirjin shi.
Juyawa nayi na fara tafiya ina hararar shii ƙasa-ƙasa yayinda shi kuma ya bi bayana yana dariya, da sauri ya sha gabana yana cigaba da dariya, cikin marairaicewar murya yace.
“Haba Sa’adatu ya xaki tafi ki kyale mu’allim dinki, bayan horon da kika min jiya kika ƙi ɗaukar min waya sannan kika hana ni xuwa wajen ki yanzu kuma xaki tafi ki bar ni, na san nayi laifi kuma xan gyara laifina ba komai ne ya janyo min ba illa soyayyarki”
Ya ƙarasa maganar yana leken fuskata
Dawowa nayi na xauna ina cigaba da kallon shi, har yanzu kyakkyawan murmushin sa yake sakar min, ni kuwa sai harar shi nake yi.
Sake kallona yayi “mijinki kike harara ko Sa’adatu? ba kyau dai abinda kike yi”
Ban bashi amsa ba ya cigaba da magana.
“Abinda yasa na kira ki yanxu ina so idan kin koma gida ki faɗawa Adda gobe magabatana xasu zo a yi maganar auren mu, idan na samu dama kuma yau ɗin xan shigo, don haka kiyi min tanadin soyayya mai yawa”
Da sauri na xaro ido kamar xan yi hawaye.
“Gaskiya yayi wuri mu’allim ka bari mu kara sabawa da juna”
Nan da nan fuskarsa ta canja ɓacin ransa ya bayyana a sarari.
“Banda wannan sabon wane irin sabo kike so mu yi Sa’adatu? Ko dai kin samu wanda yake hure miki kunne ne shi yasa kike fada min haka, ke fa kike fada min a baya bakya so auren mu ya dade me yasa kuma yanxu xaki canja min magana”
Ya ƙarasa maganar tare da xuba mun manyan idanuwansa wanda suka yi ja sbd ɓacin rai.
Muryata na rawa nace
“Ba haka bane mu’allim, kawai dai ina so na gama makaranta ne”
Sake tsuke fuska yayi “idan kina hannuna xaki cigaba da karatun ki don haka kada ki sake yi min magana irin wannan”
Girgiza kaina nayi alamar to
Ringing din da wayata tayi ne yasa ni saurin sa hannu a jaka na kashe ta, sbd na san babu mai kirana a dai-dai wannan lokacin idan ba doctor ba, tunda sim card din nawa sabo ne babu Wanda na bawa number ta.
Kallon tuhuma ya bi ni da shi
“Dama da waya kike xuwa makaranta Sa’adatu? Kuma wannan ma ai ba ringing din wayar da na baki bane a ina kika same ta”
Rawa muryata ta fara yi gaba ɗaya na dabarbarce sbd yadda ya tsare ni da tambaya tambaya ga shi ya haɗe rai babu alamar wasa a tattare da shi, cike da tsoro nace +
“Wayar Adda ce na aro ba tawa bace”
Hannu ya miko min “bani wayar na gani ta haka ne xan tabbatar da abinda kike faɗa”
Cikin rawar hannu na miƙa masa. Da
hotona ya ci karo a kan screen ɗin wayar ina jingine da motar doctor, cikin messages ya shiga ya fara bincike, cin karo yayi da irin sakonnin soyayyar da doctor ke turo min.
Damuwarsa ce ta kara tsananta.
“Haba gaskiya mana naga kin fara canja min, abubuwan da baki min su a baya yanxu kin tsuri yin su, idan nayi magana sai ki kawo min wani dalili mara asali, me yasa xaki yaudare ni Sa’adatu, me nayi miki da xaki yi min wannan sakayyar, idan bakya sona tun farko me yasa xaki koyawa xuciyata kaunar ki, kin riga kin san kece mace ta farko da na taɓa furtawa kalmar ina sonta, yanxu kuma kawai sai ki canja ra’ayi, ba tare da kin fada min ba?”
Ya karasa maganar tare da fashewa da matsanancin kuka, nima sosai nake yin kukan, na rasa ta ina xan shawo kan mu’allim ya fahimci har yanxu ina sonsa, idanunsa a rufe ya fice ya bar office din ya bar ni tare da Hanan ina cigaba da rusa kuka mai ban tausayi.Na ɗauki lokaci mai tsawo ina ta faman rusa kuka ina tausayin kaina ina tausayin mu’allim da halin da na jefa shi, gaba ɗaya kaina ya kulle na rasa me ke min dadi a duniya, Hanan da ke gefena sai bi na take da kallon tausayawa, gami da share min hawayen da ya bata min ilahirin fuskata, na dade ina jiransa amma bai dawo gare ni ba, Hakan yasa na dai-daita nutsuwata na share hayawena tare da ɗan wanke fuskanta, don kada yan uwana dalibai su gane wani abu ya faru tsakanina da mu’allim.
Ina fito wa na shiga duba ilahirin makarantar ko zan ganshi, amma babu mu’allim babu dalilin sa, hakan ya sanya ni komawa gida don ko na zauna a makarantar ma baxan samu nutsuwar yin karatu ba.
**********
A ɓangaren mu’allim kuwa gida ya wuce don baxai iya cigaba da zama a makarantar ba sbd mawuyacin halin da ya tsinci kansa, bai taɓa tsammanin Sa’adatunsa xata yi masa haka ba, yana zuwa ya faɗa dakinsa, kwanciya yayi rigingine yana xubar da hawaye masu zafi, bai taɓa tsanar soyayya ba irin yau, a zahiri yake Magana.
“Kin cuce ni Sa’adatu dama haka xaki yi min, sai da kika bari marainiyar zuciyata ta saba da ke, wacce bata san komai ba sai soyayyarki yanxu kuma xaki juya mata baya ki yaudare ta, baki kyauta min ba Sa’adatu wlh, kin xalunce ni”
Yana cikin maganar kuka mai ƙarfi ya sarke muryar sa sai a kasan xuciyarsa ya cigaba da maganar. a dai-dai lokacin ne yaji messages suna ta shigowa wayar sa, da sauri ya kai hannu ya ɗauka yana dubawa, sunan Sa’adatu ya gani, wannan dalilin ya sanya shi wurgi wayar gefe guda.
“Ba ki da wata kalma da xaki faɗa min a yanxu na yarda da ke amma kin ha’ince ni, kin riga kin san halina Sa’adatu bana iya hada soyayya da kowane da namiji, ina da tsananin kishin abinda nake so, wannan dalilin yasa bana kula yan mata, yanzu kuma ke da na yarda da ke, shi ne xaki ɓullo min ta wannan hanyar me nayi miki?me nayi miji kika azabtar da ni haka?”
Ya ƙarasa maganar yana cigaba da kuka mai ban tausayi.
Messages din ne dai suka riƙa shigowa ba kakkautawa, a hankali ya kai hannu ya fara buɗewa don ganin abinda ta aiko masa da shi.
*_ka saurare ni mu’allim ka yayyafawa xuciyarka ruwan sanyi ka nutsu kaji abinda xan faɗa maka, kada kaje ka yanke hukunci cikin fushi daga ƙarshe mu zo mu yi nadama, kaima ka san ina sonka baxan taɓa yaudarar ka ba, ka san halina ka san yadda nake sonka, don an bani waya ba shi ne yake nuna aurena mutumin nan xai yi ba, da ka kwantar da hankalin ka a lokacin nake da niyyar maka bayani, amma kuma sai kayi gaggawa, dan Allah ka taimaki zuciyata ka tsaya kayi bincike kada sanadin hakan ya sa mu rasa junanmu_*
Yana gama karantawa ya sauke wata gauruwar ajiyar zuciya sannan ya buɗe sako na biyu
*_Wata rana zaka fahimci irin yadda nake ji a kan ka, zaka fahimci gaskiyar mafarkin da nake yi a kowane dare, sannan kuma zaka gane muhimmancin irin matsanancin son da nake nuna maka a zahiri, amma a lokacin da zai zamo, babu wata sauran dama a tsakanina da kai ina mai baka hakuri a bisa abinda ya faru tsakanina da kai, na gode ina sonka har abada_* +
Sake jefar da wayar yayi tare da ‘kan’kama hannun shi a kirjin shi yana maimaita.
“Hakuri a kan me? A kan kin cuce ni, kin yaudare ni, kin nuna ni kadai ne a ranki ashe irina muna da yawa a gurinki, hakuri a kan marin xuciyata da kika yi, kika jefata a mawuyacin hali, ko wane irin hakuri kike magana nayi a halin yanxu?
Ya faɗa tare da mi’kewa zaune yana furzar da numfashi mai tsanani zafi, juyawa yayi ya kwanta tare da rungume pillown shi a kirjin shi yana jin wani radadi mai matuƙar xafi a xuciyar shi.
*********
Rusa ihun da nayi shi ya jawo hankalin Adda wajena da sauri ta shigo dakina tana tambayar ko lafiya nake kuka.
Cike da rudani na rungumeta ina faɗin
“Mu’allim ne Adda ki taimake ni ya daina sona, dan Allah ki taimaka ki taya ni bashi hakuri”
Cike da firgici ta dube ni
“Me kuma ya faru tsakanin ku Sa’adatu yi min bayani dan Allah, me kika yi masa?”
Labarin abinda ya faru tsakanin mu na bata.
Cike da tausayawa ta dube ni.
“Ki kwantar da hankalin ki indai wannan ne yana faruwa tsakanin masoya, kuma ana dai-daita wa ke dai kiyi addu’a Allah ya warware miki matsalar ki, Allah kuma ya zaba mafi alheri don ni kaina al’amarin ki yana kwance min tunani, na rasa wanda kike so a cikin masu neman ki da aure, ya kamata dai ki nutsu kiyi addu’a Allah ya fitar miki da na gari wanda xai rike ki tsakani da Allah”
Fita tayi ta bar ni kwance ina ta aikin kuka, shi kuwa mu’allim na aika masa da messages sun kai biyar babu wanda ya bani amsa, hakan ya ƙara saka min damuwa, ga shi idan na kira shi sai dai tayi ta ringing ta gama baxai dauka ba.
Ina a wannan halin Adda ta sake shigowa ta sanar min da zuwan doctor, turo baki nayi cike da shagwaba.
“Ni gaskiya Adda baxan fita ba duk shi ne ya janyo min wannan matsalar tsakanina da mu’allim”
Riƙe baki tayi
“Laifi ne don yaxo yace yana sonki, Allah ne yayi miki baiwa ya kawo miki masu sonki ta ko’ina har sai kin xaba kin darje, Banda abin mu’allim tunda ba aure aka daura muku ba, kuma ba kudin aure ya kawo ba, menene na damuwa, da ya kawo kayansa ne shi ne xai ce baxa ki kula kowa ba, ita fa budurwa haja ce masu tayawa da yawa amma mai siyen daya ne, kuma wani baya auren matar wani to, menene na d’aga hankalinsa, kinga bana don shashashanci tashi ki gyara fuskarki, ki fita soro yana jiranki don har shimfida nasa an yi masa, ki tashi nace ki wanke fuskarki kada ki fita fuskarki duk jirwayen hawaye”
A sanyaye na tashi na fita na wanke fuskata na dan shafa powder sannan na fita hannuna janye da hanan.
Ina isowa muka yi ido biyu da shi yana sakar min rikitaccen murmushinsa mai narkar min da xuciyata, saurin kawar da kaina nayi tare da cewa.
“Assalamu alaikum sannu da xuwa”
Ban tsaya na saurari abinda xai ce ba na samu guri na xauna.
Ƙasa nayi da kaina sosai ina wasa da yatsuna, hankalina gaba ɗaya baya wajensa ya tafi wajen mu’allim, hannun shi yasa ya d’ago ha’bata yana kallona ido cikin ido tare da jan hancina.
“Nayi miki laifi ko Sa’adatu, naga sai ci min magani ake yi?”
Kamar xan ce “eh” sai kuma na fasa nayi saurin girgixa kaina alamar ba komai.
Sake matsowa yayi daf da ni tare da riƙe hannuna yana murxawa a hankali, cikin kasalalliyar murya yace. Kiyi hakuri ba a son raina na tafi na dade ban dawo gare ki ba, na san dai wannan shi ne laifin da yasa sa’ar mata ke ci min magani” ya karasa maganar yana murmushi. +
Nayi niyyar faɗa masa abinda ke raina da ramin da ya afka ni a ciki, sai kuma na juyar da xancen nace.
“me yasa baka faɗa min ba cewa baxa ka dawo da wuri ba, shi ne ka ajiye ni ina ta jiranka har sai da kwalliyata ta goge, cewa fa kayi yau da wuri xaka dawo na ganka ka san dole na shiga damuwa tunda xuciyata ta riga ta saba da kai”
Hawayen da nake ƙoƙarin boyewa ne suka fito nan da nan na fara rusa kuka, duk a tunanin sa kukan rashinsa nake yi, nan kuwa bai san kukan gwaramar da na haɗawa kaina nake yi ba.
A razane ya dube ni tare da kai hannu ya rungumo ni jikinsa yana bubbuga bayana a hankali cikin sigar rarrashi, bai iya cewa komai ba sai jujjuya ni yake yi a kirjinsa, duk yadda naso na kwace sai na samu kaina da gazawa, sai ma ƙara narkewa nayi a jikinsa ina shaƙar daddadan kamshin turarensa.
Mun ɗauki mintuna masu yawa a haka, sannan ya d’ago fuskata, yana bi na da wani rikitaccen kallonsa wanda ke sanya duk wata gaba ta jikina sanyi, a hankali yasa hannu shi yasa share min hawayen da ya bata min fuskata, hakan yasa na ƙara rikicewa da soyayyar shi lokaci guda na shiga wani irin yanayi wanda ni kaina baxan iya fadin irin halin da na shiga ba.
Na tabbatar da cewa ya gane halin da na shiga, wannan yasa shi kiran sunana, cikin wata irin rikitacciyar murya.
“Sa’ar mata”
A hankali na d’ago idanuna ina kallon shi cike da soyayya, Kafin nace wani abu yace
“Kiyi hakuri ba a son raina na tafi ba kyale ki ba, aikin jama’a na tsaya yi na samo mana lada, ko baki son mijinki ya samo miki ladan da xamu wuce aljannar Allah kai tsaye”
A shagwaba na amsa da “ina so”
“Ina sonki Sa’ar mata tunda nake ban taɓa son wani abu kamar ki ba Sa’adatu, ki so ni ki tarairayi jaririyar xuciyata da ta dade da narkewa a soyayyarki”
Yana gama faɗa ya lumshe idanu ina jin yadda xuciyar sa ke ta faman bugawa.
Wata soyayyar shi da kaunar shi ce ta kama ni, tabbas ina son doctor amma son da nake masa bai kai wanda nake yiwa mu’allim ba, yanayin yadda yake tarairaiyata da yadda yake gudun bacin raina ne, yasa naji a yanzu xai iya kwacewa mu’allim fadarsa, katse min tunanin da nake yi yayi da cewa.
“Kin san me nafi tsana a duniyar nan Sa’adatu”
A hankali na girgixa kaina alamar “a’a”
Shafa gefen fuskata yayi
“Bana son ganin hawayen ki kuma ina jin tsanar duk wanda xai yi sanadiyyar zubar hawayenki, kiyi hakuri ki yafe min, da na zama sanadin fitar hawayen matata mai tsada, wanda ba a yau ya kamata ya xuba ba sai lokacin da aka kawo min ke dakina”
Da sauri na kai hannu na toshe mishi baki
“Kayi shiru ka daina faɗa kada naje kuma ban zama matar taka ba”
Yanayin fuskarsa ne ya canja,
“Kada ki sake yi mana wannan fatan ni naki ne har abada”
A hankali na amsa da “Insha Allah”
don ni a yanzu shi ne xabina indai izuddeen bai dawo gare ni ba
sakin junanmu muka yi na samu na xauna yana cigaba da bi na da mayataccen kallo.
Mun dade muna hira sannan muka yi sallama, yayi ƙoƙarin tafiya da Hanan Amma taki yarda ta bi shi, don har mun fara sabawa da juna nima yarinyar ta fara shiga raina sosai, ledar ice cream din da ya siyo mana ya miko min sannan muka tafi gida.Ina shiga ciki na ajiye kayan a gaban Adda, fito da su tayi ta bai wa kowa nasa, ko da aka bani rabona ban iya ci ba sbd damuwar mu’allim ta cika zuciyata, Adda ta lura da damuwar da na shiga kallona kawai tayi ba tare da tace min wani abu ba, wayar da ke hannuna ce tayi ringing, Ina dubawa naga sunan doctor ya fito a hankali na tashi na shiga dakina gami da faɗawa kan gado. +
Cikin kasalalliyar muryata da damuwa ta cika ta nayi masa sallama, sai da ya ɗan ja lokaci sannan ya amsa da cewa.
“Wa alaikumussalam amaryata, duk kin sanyaya min jikina ji nake kamar na dawo na cigaba da kasancewa da ke, kinga ko driving din na kasa, kin xama komai nawa Sa’adatu kece wacce nafi buƙata a cikin rayuwata yanzu”
Ya ƙarasa maganar yana kanne idonsa kamar tana ganinsa.
Ɗan gajeran murmushi na saki gami da mi’kewa zaune
“Nima kaine mutumin da nafi bukatar kasancewa da shi a rayuwata, sbd a duk lokacin da na kalle ka xuciyata na min haske naji kamar na bika ka cigaba da kulawa da ni” 1
Gyara xama yayi tare da ƙara saita wayar a kunnen shi
“Da gaske kike sa’ar mata ko dai na dawo??””
Rufe idona nayi da tafukan hannuna, a shagwabe nace
“A’a kada ka dawo so kake a ce ka xama mijin tace”
Dariya ya fara yi sosai.
“To ai ba laifi bane don na zama tace ni kan tace ne ma, indai a kanki ne a faɗa min komai ma na yarda”
Dan murmushi nayi gami da shafa fuskata.
“To shikenan naji amma dai kada ka dawo ka bari gobe kazo na ganka kuma kafin ka tafi office nake son ganinka”
“Shikenan da girman kujerar ki zan zo ranki ya dade”
Sallama muka yi na kashe wayar.
********
Yau mun kwashe sama da kwana ki uku bama waya da mu’allim, ko na kira shi baya ɗauka makarantar ma ya daina xuwa gaba ɗaya, ga shi ban san inda xanje naji labarinsa ba, tunda babu wanda na sani a unguwar su, a cikin kwana ki ukun nan har na rame na canja sbd nasa damuwar sa a raina, duk da cewa doctor yana kulawa da ni yana bani farin ciki amma hakan bai sa na manta da tunanin mu’allim ba.
A safiyar yau Alhamis na shirya kenan xan tafi gidan su Rukayya na faɗa mata halin da nake ciki naji ƙarar shigowar message ina dubawa naga sunan shi, da har nayi tunanin kada na buɗe na duba sai kuma na danne xuciyata na buɗe.
*_”Da fatan kin wuni lafiya, idan kin bani dama ina so naxo yau za mu yi wata magana, da fatan baza ki juyar da bukatar talakan masoyin ki ba don naga yanxu masu kuɗi ke buɗe miki ido”_*
Mamaki ne ya cika xuciyata da jin wannan kalaman nasa to “me yake nufi da masu kuɗi sun bude min ido?”
Komawa nayi na xame na rungume wayar a kirjina Ina jin radadi da zafin da zuciyata ke min.
Ƙara naji wayar nayi, da sauri na miƙa hannu na ɗauka, number doctor na gani a jiki, gefe na ajiyeta sbd yanzu bana buƙatar jin wata magana nafi so na xauna ni kaɗai nayi nazarin wannan bakar maganar da aka fada min.
A dai-dai wannan lokacin na sake jin ƙarar shigowar message din mu’allim.
“Ki fito ina jiranki idan kuma kika ɗauki lokaci mai tsawo xaki iya nemana ki rasa”A sanyaye na tashi na shiga wajen Adda na faɗa mata sannan na ɗauki kujera biyu na tafi wajensa.
A soron na tarar da shi ya harde hannun shi a kirjin shi, kallo ɗaya nayi masa na san yana cikin matsanancin tashin hankali, duk yayi baƙi ya rame, abinka da mai manyan maganai idanun shi duk sun faɗa rami, har naxo kusa da shi bai san naxo ba ya tafi duniyar tunani.
A hankali nayi masa sallama, kamar wanda ya farka daga mafarki ya juyo ya kalle ni ba tare da ya amsa sallamar ba sai ma juyar da kan shi yayi gefe ba tare da ya sake kallona ba.
Komawa nayi kusa da shi na sha gaban shi, cikin rawar murya nake cewa.
“Me nayi maka haka mu’allim da kayi min wannan tsanar har baka son ganina, me yasa xaka hukunta ni a kan dalilin da baka tsaya kayi bincike a kansa ba?”
Abin ka da me xuciya a kusa kafin yace wani abu, har hawaye ya cika fuskata ko ta ina.
A gigice ya dube ni
“Kiyi hakuri ki share hawayen ki ba kuka nace kiyi min ba, naxo ne mu fahimci juna wannan kukan da kike yi, shi ya ƙara tabbatar min da kina sona Sa’adatu kiyi hakuri na yafe miki komai ya wuce”
Wani sanyi da farin ciki naji a raina.
Xaunawa yayi a kujerar da na kawo masa yana kallona.
“Bana son xubar hawayen ki, tunda ni kika yiwa laifi na yafe miki, mu kulle wannan maganar mu shiga wani sabon babin”
Murmushi nayi tare da harar shi ƙasa ƙasa
“Sai da ka wahalar min da zuciya sannan xaka ce wani ka yafe”
A hankali ya shafi fuskar shi.
“Nima ai kin wahalar min da tawa xuciyar baki ga yadda na koma bane nayi baki duk na rame”
Murmushi muka yi gaba ɗaya muka shiga hirar yaushe gamo yana bani labarin halin da ya shiga bayan mun yi faɗa, nima labarin na riƙa bashi wani mu yiwa junanmu dariya wani kuma mu zaulayi junanmu.
Muna cikin hirar muka ji tsayuwar wata hadaddiyar mota a kofar gida, tsayawa fadar irin kyan motar ma xai iya zama kauyanci, gaba ɗaya muka bayar da hankalin mu ga masu fitowa daga cikinta.
Me xan gani?? Rukayya ce ke fitowa daga cikinta da gudu ta karaso wajena muka rungume juna muna murna, cikin farin ciki na dubeta.
“Daxu fa har na shirya xan xo gidan ku sai kuma wannan ogan ya tsare ni”
Sai a lokacin ta lura da mu’allim cikin girmamawa suka gaisa.
Sake jefa mata tambaya nayi
“Ke da wa kika zo kuma? kice masa ya shigo mana kin bar shi a mota shi kaɗai ko ba a so mu ganshi ne??”
Murmushin tayi
“Kin san ko ina boyewa kowa kayana ke baxan boye miki ba, da ni da ke abu daya ne”
Dafata nayi tare da cewa “Haka ne kam kawata”
Kafin mu ƙarasa maganar da muke yi, tuni na cikin motar ya bayyana, sanye yake cikin wata tsadaddiyar shadda milk colour wacce aka yi mata aiki da brown din xare, takalminsa da hularsa duk kalar aikin da ke jikin kayansa ne, kana ganin kalarsa kasan hutu ya bi jikinsa.
Tun daga nesa yake sakar min kyakkyawan murmushinsa wanda ke sanya ni farin ciki a duk lokacin da nayi tozali da kyawawan hakoransa, ban san lokacin da na tafi da gudu ba ina kiran sunansa…………….
Ko wane ne Wannan saurayi da Sa’adatu ke muradin gani a rayuwarta yau kuma Allah ya haɗa su??
Sai ku biyo ni don jin kowa wane ne shi