DEEMAH CHAPTER 4 BY ZAHRATEEY
Nayi mamaki sosai da masu gidan basu dawo nan kusa ba, kwanaki sun ja watanni sun shud’e ni dai har yanzu ban saki jiki da zaman gidan ba, domin nasan bada jimawa ba komai zai zama mafarki, yan gidan ku sunfi bani tausayi sosai, yanda suka bararraje suka shantake kamar babu mutuwa, ina jiye musu ranar da zasuyi kwanan titi ko kwanan gidan _Inna Abu_ ko kuma wani gida wanda ko rabin kyaun gidan mu na da bai kai ba.
A yau muka cika wata shida a cikin gidan, ina fitowa daga kitchen naji _Baba K_ yana ta faman “to, to Allah ya kawo ku lafiya alaji” yana ajiye wayan ya tashi ya fara taka rawa yana wakar miliyan goma suna tafe, sai a lokacin ba fahimci cewa ta faru ta kare dan da alama dan k’arya ne ya kira kuma hakan na nuna cewa me gidan na hanyar dawowa, d’akin _Mama Qudi_ na shiga na sameta tana kwance a kan royal kujerun dake cikin d’akinta sai faman danna remote takeyi tana canja tasha ” su _Mama Qudi_ an samu duniya” na fad’a a cikin raina, dama duk kayan gado da kujeru gidan _Inna Abu_ aka kai aka zuba a d’akunan da babu komai, ita kuwa sai murna take ta faso gari, dan kujeru biyu ne yanzu a falonta saboda girman falon, ko wani d’aki kuma an zuba gadon matan gidan mu, dama d’akuna biyar da hud’u gadajen matan gidan mu, d’aya kuma dama kayan _inna Abu_ ke ciki, sai boys quarter kuma d’aya kayan d’akin _Baba K_ d’aya kayan d’akina, sauran kuma sayarwa akayi _Baba K_ ya zuba kud’i a aljuhu.
Ina zuwa nace mata ta had’a kayanta duka ta ajiye a guri d’aya, domin _Baba K_ ya sayi sabon gida can za’a koma, dan naji yana waya d’azu, da sauri _Mama Qudi_ ta sauka daga kan kujera ta h’au tattare tattare, haka suma sauran matan gidan mu na bisu d’aya bayan d’aya, hatta sauran k’annena hud’u da suka rage a gidan duk sai da nasa kowa ya had’a kaya cike da zumud’in zuwa sabon gida.
Karfe hud’u dai-dai aka fara shigowa da motoci cikin gidan, ta window na l’eka na ga motoci uku ne na alfarma, kuma _Khalil_ ne ya bud’e gate din, a hankali duk suka fito daga motar fuskarsu d’auke da mamaki, sai bin ko ina sukeyi da kallo, _Khalil_ dama yana bud’e musu gate ya koma can 6angarensu ya barsu da rufewa, tsaye sukayi a waje na kusan second talatin sannan suka fara takowa zuwa cikin gidan, Babban mutum ne a gaba sai wata mata a bayansa sai yara shida yan mata uku maza uku, ina jin suna knocking na koma d’akina, sai naji _Baba K_ yana saukowa tare da cewa ” maraba da bak’in karamci gani nan zuwa ashe dai har kun gane gidan” ya fad’a yana murd’a k’ofar cikin falon.
“Bismillah shigo shigo” ya fad’a yana wage hakora, _Ya Kolo_ da suke saukowa saboda jin hayaniya tace “Hajiya kece yauba gidan namu?” Kallo ne ya koma kansu, bayan an gaigaisa shine _Ya Kolo_ ke bayanin cewa ai itace ta bugeni da mota kwanaki, kuma sau biyu tana zuwa dubani amma ina barci, godiya sosai _Baba K_ ya shiga mata na d’aukan nauyin kud’in asibitin da tayi, shine take cewa ai asibitin mahaifinta ne wato me _A&S Company_ sosai yan gidan mu sukayi mamakin rashin girman kanta, ashe y’ar masu kud’i ne har hakan amma bata nuna alamar komai ba, bayan shurun da sukayi na d’an lokaci _Baba K_ ya aika aka kira mu duka wai muzo mu kwashi gaisuwa, bayan mun fito sun gaigaisa dan ni a al’adata babu gaisuwa sai sannu, sai matar take cewa “Bake bace kwanaki kuka kai mana aike a gurin biki, daga shagon _Iya Loja_?” Sai a lokacin na kalle ta, kuma na ganeta kenan ma gurin da mukaje d’in dama na mahaifinta ne, sai yanzu naji matar ta burgeni, gaskiya tayi ne a rayuwa haka nake son in ga mutum me kudi ko talaka yana abu cikin tsari da sanin yakamata. “Eh nice Hajiya, dama ke kika bugeni da mota ashe? Kiyi hakuri laifi nane saboda ina cikin damuwa ne a ranar” murmushi tayi tace min ” babu komai ni zan baki hakuri ai tunda nice nake tuk’i cikin gaggawa dan akwai inda zanje, kuma muna shirin komawa UK ne amma saboda abin da ya faru yasa muka d’an jinkirta da naga yanayin jikin naji sai muka tafi” murmushi na mayar mata ina jinjina karamci da mutunci irin nata.
Alajin ne ya katse shurun da cewa “ya akayi kuka saya gida me kyau irin haka?” Nan fa _Baba K_ ya fara bada labarin yadda akayi ya saya da kuma kud’in da yanzu yake jira a gurin alajin sai gida kuma da zasuje su gani. Kowa a gurin mamakin rashin wayon _Baba K_ yakeyi da kuma takaicin halayyarsa na son kud’in daya kai shi ya boro shi, “dama wanda yaki sharar massalaci zai yi na kasuwa ai” na fad’a a cikin raina, bayan ya gama bayyana komai sai Alaji yayi gyaran murya ya fara bayanin cewa shi bai saida gidansa ba, hasali ma gidan ya saya ne ya bari a gyara mishi kuma bayan an gama ya sa aka zuba furnitures saboda zasu dawo Nigeria baki d’aya, kuma kamfaninsa d’aya bud’e a Nigeria yana buk’atan kulawar yaransa, shiyasa suka dawo baki d’aya, duk yaran business admin suka karanta, shiyasa abin yazo mishi da sauki ya d’aura su a matsayin shugabannin 6angarori daban daban a cikin kamfanin, sannan wata d’aya ya rage bikin yaransa duka both mata da mazan. Kuma ba dan baya son gini bane yasa ya sayi gidan, kawai yana son ya zauna cikin anguwan marasa k’arfi ne domin ya rinka taimaka musu. A yanzu _Baba K_ ya dai fahimci cewa damfaransa akayi aka kwace mishi gidanshi sannan aka bashi wannan gidan da takardun bogi, kuka ya saka yana tsinewa _Atika_
Bayan ya gama kukan ya juyo ya kalleni, ganin ko kad’an babu damuwa a tare dani yasa yace “kin san dama abin da suka zo suyi kenan amma kikayi shuru kika barni na afkawa tarkonsu ko?” ko d’agowa banyi ba, yadda nake zaune ina kad’a kai babu alamun zan tanka mishi ma, sake maimaita tambayar yayi, ganin haka yasa Hajiya tace mishi meyasa yayi tunanin hakan, shine yake bata labarina da abin da yasa yayi tunanin ina sane, mamaki ne duk ya kamasu, taya za’ayi ace mutum na irin hakan, anya babu aljanu a cikin lamarina, haka kuma na koma topic of discussion, harda cewa za’a samo malami ya dubani, daganan alaji yace “Khadeemah da gaske kinsan hakan zai faru?” Kwarjinin mutumin yasa na kasa sharesa, “eh hakane” na fad’a ina basu labarin duk abin da nasani game da _Atika_ sosai sukayi mamakin halayyarta kuma suka bawa _Baba K_ laifi tare dayi mishi nasiha, wanda ni nasan ya shiga ya fita ne kawai.
Bayan an gama jajanta lamarin aka tambaye shi ina yake ganin zamu koma, shine yace gidan _Inna Abu_ Alaji yace ba damuwa zuwa gobe sai mu koma su zasu wuce gidan iyayensa dake GRA, a chan zasu kwana, dama a chan suke sauka duk sanda suka zo cikin kasar, dawowar da zasuyi ne yasa suka sayi gida suma dan su zauna a ciki, duk da cewa ya sayi wani fili ana mishi gini tare da yaransa maza dan yafi son su zauna kusa dashi idan sunyi aure, amma kila sune zasu zauna a chan shi da matarsa zasu zauna a nan d’in.
Haka kuwa akayi suka tafi suka bar yan gidan mu da jimami, duk da cewa sunji haushin abin da nayi amma kuma basu ga laifi na na son ganin _Baba K_ ya shiryu ba, haka kowa ya kwana da damuwa a ransa, washe gari Alaji ya bada mota mubi tare da direba muka kwashe komai ba mu muka koma gidan _Inna Abu_, ko ya rayuwa zata kasance a gidan, Allah masani.
ifinmu ya gaji arziki balle har ya samu tarbar arziki? Yanda dai nayi tsammani hakan ne ya faru, duk yadda takeji da _Baba K_ sai ga shi tace ba zai zauna mata a gida ba, salon wai itama ya sayar da gidanta.
dake kokarin zubowa daga idanuna nayi, ina karawa kaina karfin gwiwa, rai na fansa ga ahalina, ruhina zai samu salama idan na d’auki fansar mutuwar yan uwana yayata da kannena, wannan shine kawai maslaha ga duk wani masifar da suke kokarin sake tunkaro mu ta wannan fannin. Abin da nake kokarin yi shine dai-dai, zan iya kuma komai zai zama tarihi da yardan Allah.Mun isa _Abuja_ lafiya lau, duk da cewa munyi dare amma tunda dai mun isa lafiya ai sai godiya, dama munyi akan shi kad’ai zai tafi ni zan jirashi a wani gurin, idan sun amince da abin da muka shirya sai ya taho ya kaini, idan kuma aka samu ak’asi sai muyi wani dabaran daban. Saboda tsaro na saka nikab tunda sun riga da sun sanni.
, masu hira sunayi haka masu hutawa sunayi, Kamar da wasa muka fara ganin mutane suna durowa, cikin k’ank’anin lokaci suka zagaye mu, tashin hankali da ba’a sa masa rana, yanda duk aka seta bindiga daga ko wani 6angare yasa mukayi saranda. Babban abin tashin hankalin shine babu damar 6acewa dan yau ba’a yi amfani da jajayen kaya ba, kowa da kayansa yazo shiyasa ba’a tafi inda aka saba ba dan hasali daga gurin murnan zagayowar shekara na d’iyar sarauniya muke baki d’aya. Cikin kankanin lokaci akayi gaba damu baki d’aya, daga chan kuma ni da _Baba K_ aka sama mana gurin kwana, washe gari bayan na tattara duk bayanan dake hannu na, na damka musu muka musu sallama muka tafi bayan sun had’a mu da goma ta arziki muka kama hanyar _Bauchi_.