UMM ADIYYAH CHAPTER 74 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 74 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Amb. Aliyu, abokin Baffa mai dattako da sanin

ya kamata.

“Allah ya ja girma, ya kara daukaka, mun

gode Yallabai. Allah Ya saka da alkhairi.”

“Ba komai, ku kuma sai ku kula, ku kiyaye

sharuddan zaman aure, ku dubi yadda

Annabi (S.A.W) da magabatansa suka gudanar

da nasu al’amuran, ku yi koyi da su.

Bare ma yanzu abu ya zo da sauki, ka na zaune

za ka samu ilimi kan komai na

rayuwa. Ku rinka kwaikwayon abinda musu-

lunci ya zo da shi, to ku na cikin rabo,

amma da zarar kun saki layi, to alkawarin Al-

lah ne sai kun ga ba daidai ba. Allah Ya

kara hada kanku, ya ba ku zuri’a dayyaba.”

“Ameen Ya Rabbi, mun gode sosai. Baffa Al-

lah ya saka da alheri.” Zaid ya karasa

yana kallon bangaren da Baffa yake zaune.

Har yanzu dai a dan tsume yake tam! Da

alama albarkacin Amb. Aliyu suka ci har

ma ya amsa. “Shi kenan ai tunda ka kawo Ba-

banka ya kwatar maka ‘yanci.”

Dariya Zaid ya yi yana dan sunne kai, ba Www.bankinhausanovels.com.ng 

wanda ya kai shi farin-ciki yadda yake jin
kansa a lokacin, tabbas rabuwarsa da Umm
Adiyya wata jarrabawa ce ta afka masu,
kuma sun koyi darussa sosai daga hakan, baya
fatan ko a mummunar mafarki ya
sake ganin abinda suka fuskanta.
Hajja Ku kuwa sai da ta sa Umm Adiyya a
gaba can kuryar daki, “Ke ban son kukan
munafurci, ki fada mana kina son komawa gi
dan mijinki ne, ko kuma a’a? Mutum ya
dage yana nema miki ‘yanci, kin zo ki na ta
koke-koken gulma.”
“Eh Hajja.”
“Eh meye?” Hajja ta fada tana kallon token na
ta.
Ina son na koma.”
Baki ta rike da hannunta, tana jinjina kai, “TTo
ka ji tsiya, shi ne za ki zauna ki na ta
kuka a boye a daki, kin bar mu sai kumfar
baki muna tada jijiyoyin wuya, a dole a bar
ki ki sakata ki yi son ranki. To tunda abin naku
haka ne, kun hade min kai, sai na ce
Allah ya kare gaba, ya sanya alkhairi. Ku dai
san da cewa jin kanku kuma ya kau,
babu zancen maganarku ta sake barin dakinku,
ku san girma ya kama ku, ku koyi
sasanta kanku, idan kun samu sabani.”
“Na ji Hajja, mun gode.”
“Shi kenan ai, bari na fadawa su Baban naku,
ayi abinda za ayi kafin wannan mara
hakurin ya tare min a gida.”
Umm Adiyya kam fara’arta ya ki buya.
Makale wuyan Hajja ta yi, tana gode mata.
“Za ki karya min sauran kasusuwan, a tattara a
kaini, dama wannan mijin naki na jin
haushin na wana shi. To ta Allah ba taku ba,
sai na ga rabon da ya jona wannan
abin kan na karasa Inshaa Allahu.” Umm
Adiyya ta rufe idanu cikin jin kunya sannan
ta fice a dakin.
***********x **
Kafin dare dai labari ya karade ko ina. Hajja Ku
da Modibbo duka sun amince a
mayar da auren Zaid da Umm Adiyya.
Koda Zaid ya kirata a waya, sun gaza cewa ko-
mai don farin-ciki. “Alhamdulillah.”
Daga Karshe ya furta.
“Noorie, da saura dai.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Da sauran me?”
“Na ji ka na ta washe baki ne, kamar wanda
aka ce ma an daura auren.”
“An isa wajen ai, abin da ya saura kalilan ne.
Saboda haka kafarki daya na gidana
Twinkle.”
“A’a duka ne.” Ta fada tana dariyar zu-
“A’a
mudinsa.
“Ki na wasa ko?”
“Na isa na yi wasa da Mr. Zaid Abdur-Rahman
Sarkin yakin Umm Adiyya?”
“Ki saurareni gobe Inshaa Allah.”
“Gidan Hajja Ku dai ba nisa yake da ba, bare
ka ce..”
“Naki din, don’t tempt me (kar ki kwadaita
min). Zan yi hakuri sai da safe, ina zuwa
Hajja za ta fara fade-fade, daman ta sani a
gaba.”
“Uhm! Ba ni da labari, akwai abinda yake
katse ka ai, idan ka ga damar yin abu.”
“Me, A kanki? Babu abinda ba zan fuskanta
ba, ke ma kin san wannan. Amma akwai
abinda ake kira kawaici ai.”
“Na ji duka wannan. Yaushe za ka koma?”
Kada harshe ya yi daga daya bangaren, “Wai
ki na tsammanin zan bar garin nan ni
kadai ne?”
“Da sai da wa? Ka yi sati ba ka zuwa wurin
aiki.”
“You’re talking to the boss. (Kina magana ne
da oga kwata-kwata.)”
“To shi kenan, The boss’s boss (ogiyar oga) ke
fada maka ka bi a hankali kar a
koreka dai.”
Dariya ya yi mai sauti, dirin muryarsa na sauka
har cikin kirjinta, “Yaya Zaid. Sai da
safe.”
“Allah tashe mu lafiya. Ina da sako wurin Ha-
Jja Ku.”
“Menene?”
“Idan kin tashi da safe ki ce ta ba ki ajiyata.”
“Na zaci ai za ka zo.”
“Ke dai ki fada mata.” Kanta ya kulle, amma
duk da haka ta amsa masa da to. Ranar
tsabar murna ma bai bar su sun yi barcin ba.
Wajajen karfe biyun dare. Umm Adiyya ta
mike za ta shiga alwala, ta ga wayarta na
haske.
Nan da nan ta daga. “Me ki ke yi ba ki yi barci
ba?”
“Me ka ke yi kai ma?”
“Na tashe ki ne, mu godewa Allah.”
Murmushi ta yi na jin dadi, “Na gode da
tashina. Sai da safe?”
Tsaya, tsaya. Da gaske na gaza barci ne, ki na
jin abinda na ke ji kuwa?”
Dariya ta yi cikin zazzakar muryarta ta ce,
“Yaya Zaid, ni dai ba abinda na ke ji.”
“Mood spoiler kawai. (Sarkin sace gwiwa
kawai)” Ya fada har da tsumewarsa.
“Je ka yi alwala.”
“Da alwalata. Bye, love you.”
Murmushi ta yi ta girgiza kanta, sannan ta ce
“Me more.”
“Ki gama zagayenki dai, zai ma fito idan na
ritsa ki.”
‘Good night.” Tana fada ta kashe wayar. Don
ta san halinsa sarai, yanzu zai rikito
mata zance.
*****k *****k ***
Lokacin da Umm Adiyya ta fadi sakon Zaid wa
Hajja Ku. Wani murmushi ta yi ta ce,
“Allah hoinu.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Hajja wani abu na ce?”
“Ki yi shiru, ki yi abinda ke gabanki, kin faye
yawan tambaya.”
Umm Adiyya dai tana zaune ta ga an je ka-
suwa an sayo sako wa Hajjan, Nan da
nan ta ga an fara dafe-dafe da kirbe-kirbe, ba
ta kai ga tambayar me za ayi ba, ta
samu wayar Adda Asma’ .
“Mashaa Allah, Injiniya mata a gidan Injiniya.
Kuna sha’aninku, wato duka sai da ku
ka ci fadan za end din.”
“Adda Asma!”
Okay, da gaske, na maku murna sosai, Allah
ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya
mai daurewa.”
“Ameen, na gode, ina uwata Maamata ta
kaina?”
“Za ta zo miki ai hutun amarci.”
“Kin ji wani hadi a wurin,
ko me za ki fada ki
fada. Maama a kodayaushe ana
maraba da ita, matukar banda uwar Maaman.”
“Ba ki da kunya yarinyar nan. Ina angon
naki?”
Oho, ba mu yi magana ba.”
“Iye, irin jan class din nan ba? Ga Abban
Maama, wai zai miki magana.”
Tsaya-tsaya kar ki ba shi, na san zai min tsiya
ne.
“Hi! Ummu A.” Ta ji muryarsa a kunnenta,
datse hakora ta yi ta runtse idanu, ba mai
rabata da Adda Asma, wato a sakel hannu
(handsfree) ma ta saka ta.
“Haba kanwata, kuma yau ni din ake gudun
magana da ni?”
“Ba haka bane fa. Abban Maama, kawai dai…
Ina kwana?”
“Lafiya kalau, yaya hidima da zirga-zirga? Na
so zuwa mu yi kamfen ai, ayyuka suka
sa ni a gaba, da fatan an warware komai
lafiya?
“Lah, ba komai Abban Maama. Alhamdulil-
lah.”
“To ya yi kyau hakan ake so ai, sai ayi ta
hakuri ko? Da hankali ake girman, shi aure
dama sai ana yi ana duban bakin gatari, saboda
abu ne da ba na mutum guda ba,
abinda za ka yi zai shafi duk kowa na kusa da
kai ne, don haka kauda kai a wasu
lokutan, yana da amfani.
Amma abu muhimmi shi ne samun fahimtar
juna, kar ku yarda da batun kuma masuu
tsoma kai cikin lamura (third parties), ina so ki
dauka yanzu zaman da za ku je ku yi
tamkar sabon zama ne, ki shafe duk wani
abinda ki ka sani da, ku shimfida sabuwar
rayuwa yanzu, wanda take cike da yarda da
aminci da fahimtar juna. Allah ya hada
kanku ya azurtaku da zuri’a dayyaba.”
“Ameen Abban Maama na gode sosai. Inshaa
Allah za mu kula.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Sai mun zo cin girkin amarya.”
“Aw! Haba dai har dadewa za ku yi ba za ku
zo ayi shirin hidimar da ku ba? Ni da na
ke son a kawo min Maama tun wuri?”
“Za a kokarta a zo kam ayi shirin hidima,
dama kin san Addarki ai da bala’in son
gida, motsi kadan jira take yi ta ji abu ya faru,
ta samu dalilin zuwa.”
“Ai to ba inda ya kai gida dadi.”
To ni dai ban ce haka ba, kar Yaya Zaid ya ji
ni ya ce ni na zuga ki, ki ka fadi
hakan.”
Suna dariya suka yi sallama. Asma’ ta karbi
wayar “Okay, ma’assalam sis ki kula da
kanki.”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *