DIYAM CHAPTER 13

DIYAM CHAPTER 13

Na rike baki ina dariya, ko ba dan Saghir ba ko dan ni kaina da abinda yake cikina nayi murnar wannan aikin. Nace “Masha Allah. Alhamdulillah. Amma fa kayi sa’a, abinda mutane sai su dade suna neman aiki basu samu ba amma kai kaga lokaci daya ka samu” yayi dariya yana zama akan kujera yace “maybe mutanen da kike magana akan su basu san inda ya kamata su nemi aikin ba ko kuma basu dace da aikin ba. Kinsan appearance matters alot a gurin neman aiki, yanzu misali ni, kowa ya ganni yasan na chanchanta da post din dana samu” na zauna ina mamakin bragging irin na Saghir, nace “komai fa a rayuwa yana da lokaci, wadanda basu samu aiki ba lokacin samun su ne baiyi ba, kai kuma daka samu lokacin kane yayi, ita rayuwa…..” Ya daga min hannu “don’t spoil my mood please. Je ki kawo min ruwa” nayi ajjiyar zuciya na tashi.2 Ranar daya fara zuwa office ne bayan ya dawo na tambaye shi “to an baka office? Da fatan sun fara baka aiki kanayi” yace “wanne irin aiki kuma?” Nace “rubuce rubuce mana, ba shine aikin secretaries ba?” Yayi tsaki yace “fin sec fa aka ce miki, ni harkar shiga da fitar kudi a companyn ne kawai part dina, besides, ina da mataimaki so shi zaike handling duk aiyuka” nace “so? Kai menene naka aikin?” Yace “who cares about aiki ne wai, what I care about is the salary kuma zasu ke bani mai kyau shikenan”.3 Tunda aiki ya samu kuma shikenan Saghir ya koma tsohuwar rayuwar sa, inya fita tun sassafe baya dawowa gida wani lokacin ma har sai nayi bacci. Baya zuwa gida a bige, amma hakan bawai yana nufin ya daina bane ba dan sau da yawa in ina gyaran kayansa nakan ji wannan warin a jiki, sai dai bani da wani kwakwkwaran hujja. Yana ciyar damu, duk da dai considering yadda yake kashewa jikinsa kudi baya yi mana yadda ya kamata amma dai muna cin abinci. Shi kuwa kullum cikin sababbin dinkuna yake yakance “gwara mutum yayi dressing sosai kar a raina masa hankali”. Cikina yana ta girma abinsa, ni kuwa babu komai a raina sai fargaba dan kuwa har yau ban manta da wahalar da nasha a waccan haihuwar ba, gashi wannan cikin duk da cewa daya ne a ciki amma tafi wancan cikin girma, wannan yasa tun cikin yana waya bakwai na tattaro kayana na dawo kasa kusa da uwani kuma kullum ways ta tana kusa dani dan am not looking forward to haihuwa ni kadai irin waccan. Amma lokacin da muka je scanning tare da Saghir, bayan an gama mun zauna sai doctor yace “am afraid ba zaki haihu da kanki ba, dole za’a yi miki cs ne” duk muka bude baki da mamaki, Saghir yace “ta taba haihuwa fa doctor, twins ma” doctor ya dauko takardar scan din yace “tana da abinda a likitance muke kira da placenta previa. A ka’ida in aka tashi haihuwa ɗa ne a farko sai an haife shi sannan sai mabiyya ta biyo baya. But in her case mabiyyar ce a farko sannan dan, meaning ko da ace ta fara labour to placenta ce zata yi blocking babyn yadda ba zai fito ba so babu yadda za’ayi sai dai ayi delivering through cs” na fara kuka, ni takaicina shine yanzu wai yanka cikina za’ayi a fito da babyn ni Diyam, kai mata munga ta kan mu. Saghir yayi tsaki yace “kuma menene abin kuka a ciki? Ke da ya kamata kiyi murna ma babu ke babu wahalar haihuwa. Sai ni aka bari da wahalar kudi”.4 Alayi fixing date, a week to my edd sai dai da sharadin in naji nakuda kafin lokacin muyi sauri mu tafi. Na dage kullum da addu’a, na kuma gayawa su inna suma suka tayani da addu’a har Allah ya nuna mana lokacin. Mama ce tazo gidan muka tafi tare, dama Inna tunda nayi aure bata taba zuwa gida na ba. Tun a day to aikin mukaje suka bamu gado muka kwana a can, sukayi duk gwaje gwajen da zasuyi sannan washegari sai ga Hajiya Yalwati tazo daga gidan Alhaji Babba, har aka zo aka gama shirya ni babu Saghir babu labarin sa. Naji duk jikina yayi sanyi. Anzo ance lokaci yayi na dauko waya ta and I found myself dialing number din Sadauki, hoping to hear his voice just once more amma naji a kashe na kashe wayar na ajiye feeling so lonely kanar ni kadai ce a duniyar. Mama da Hajiya Yalwati suna ta lallashina suna min addu’a a haka aka shiga dani. Aikin mai bacci akayi min saboda jini na yaki karbar na ido biyun. Dan haka duk abinda akayi ban sani ba har aka gama aka fito dani dakin hutawa. Anan ne na dan farka kadan naga Inna a zaune kusa dani ta rike hannuna, gefe kuma Mama da baby a hannun ta “Sadauki” na fada cikin bacci, “inna ki kira Sadauki kice yazo ya duba ni” sai na kuma komawa bacci. Sanda na sake farkawa doctor na gani da nurse a kaina, suka yi min sannu daga nan na sake komawa. STORY CONTINUES BELOW Sanda nayi final farkawa kuma babu kowa a dakin sai ni kadai, na bude idona ina ta kalle kalle ina jin kaina yana ciwo sai na hango Saghir a can kusa da window da alama waya yakeyi. Irin yadda naga yana bada respect ga wanda suke wayar yasa ni son sanin ko wanene saboda ban taba ganin yana magana irin haka ba. Sai daya gama sannan ya juyo, muka hada ido yayi murmushi ya nuna wayar yace “my boss. Ya kira yaji ya jikin ki saboda na fada masa za’ayi miki aiki. Yana da kirki sosai. Can you believe he paid for everything hadda karin kudin ragon suna?” Na rufe idona na dauke kai ina jin haushinsa har cikin raina, wato abinda zai fara fadamin kenan bayan an yanka ni an fito da jaririn daya saka a ciki?3 Sai yazo ya dafa kafada ta “am sorry banzo ba tun jiya, I am not good at all this emotional stuff ne shi yasa nayi zamana a gida kawai” sai kuma ya juya ya tafi gurin crib din baby ya dauko yana murmushi, na yi kokarin tashi amma na kasa nace “kawo min, menene?” Yayi dariya “au baki ganta ba? Baby girl ce, so beautiful like her mother” this is the first time daya kirani beautiful. Ya karaso ya sunkuyo yana nuna min ita, and he was right, she is so beautiful but tafi kama dashi because she looked just like twins dina, just ta fisu girma sosai. Nayi murmushi ina jin attraction so much like wanda naji akan twins. Na daga hannu na shafa kanta ina murmushi, yace “inye, Diyam an zama uwa, sai ki daina yi min rashin kunya in ba haka ba zan saka take rama min” ya jima yana ta surutun sa shi kadai sannan ya mayar da babyn cikin crib dinta ya dauko waya yayi ta daukan ta pictures sannan yazo yayi kissing dina a goshi ya fita. Four days nayi a asibitin. I was so in love with my daughter naji tamkar na samu another reason to live. Sau daya Saghir ya dawo ya tambayi Inna ko akwai abinda muke bukata, ya dauki daughter dinsa sannan yayi min sannu ya fita, and that was all, ko abinci ba’a taba kawo mana daga gidan Alhaji Babba ba. Wannan yasa ranar da aka sallame mu muka wuce gidan Inna, shi ogan ma baisan an sallame mu ba sai daya kira ni naki dauka sannan ya kira uwani tace ai an sallame mu sai kuma gashi a gidan Inna, wai ai ba’a gaya masa zan zo gida ba, ya gama rashin kunyar sa ya fita. Inna tana ta mitar abin, a raina nace “zabin ki ne dai”. Tunda Hajiya Babba taje ta dubani a asibiti bata kuma zuwa ba, shima Alhaji Babba ko leke sai yace ace min baya jin dadi ni kuwa nasan dan mace na haifa ne da namiji ne da ko da rarrafe sai yazo.1 Kullum in ana kallon yarinyar nan sai na tuno Sadauki, lissafin mu ni da shi shine mu haifi girl mu saka mata Subay’a, to ga girl din kuma na samu amma bata Sadauki ba, gashi ko sunanta ban sani ba duk da nasan yayi mata huduba gaya min ne kawai baiyi ba. Sai ranar suna da safe ya kirani “anyi radin suna a gidan Alhaji. An saka mata Saratu” sunan Hajiya Babba. Na runtse idona ina jin haushin sunan, nace “Allah ya raya, zamu sami wani sunan da zamu ke gaya mata” yace “already na riga na samu, Subay’a” na maimaita cikin mamaki “Subay’a?” Yace “yes, ko ba kya so?” Nace “no, ina so, a ina ka sami sunan?” Yace “my boss called, ya nemi alfarmar duk sunan da aka sawa baby a ce mata Subay’a, and I see no harm in honouring his wish. Besides, shi ya sayi ragon suna” ya karashe maganar yana dariya. Na kashe wayar ina mamakin me yasa boss dinsa zai ce a gaya wa babyn mu Subay’a? Inna ta tambayeni suna nace mata sunan Hajiya Babba ne za’a ke ce mata Subay’a, ta maimaita sunan tana kallona.11 An dan taru a gidan sunan babu laifi, duk da cewa yan’uwa ne kadai kuma yanuwana da nasa duk daya ne, sannan ni ba kawaye ba ba makota ba, sai makotan mu na nan gidan da suka shishshigo mana. Abincin suna ma Saghir baiyi ba, cewa yayi ai ba shi yace in taho gida ba dan haka wanda ya kawo ni gidan sai yayi abincin sunan. Ragon sunan ma a gidan Alhaji Babba aka yanka aka soya aka kuma raba sai namu rabon aka kawo mana a kwano. Bayan suna Mama tazo ta dauke ni muka je asibiti, ni na dauka wani check up za’ayi min sai naga an saka min wani abu mai kamar allura a dantsen hannuna ashe abin family planning ne aka saka min na shekara biyar. Satina biyu a gida Saghir yazo yace ai na warke haka, in shirya in koma. Haka ina kuka ina komai na hada kayana dana Subay’a, Allah ma yaso Asma’u tana hutu nace tazo mu tafi, itama kuma tana shiga mota yace da iznin wa zan tafi da ita? And that kept me wondering if I don’t have a say in my own marriage. Shin miji shi kadai ne mai making every decision, ita mace bata da nata ra’ayin? Ko kuma ita mace bata da zuciya ne a kirjinta? Bayan komawar mu gida ne nayi realizing something, Saghir’s weakness lies in his daughter. Yana son Subay’a sosai da sosai dan zan iya cewa yana sonta fiye da komai a duniya. Kullum tana hannunsa sai dai in baya gida ko kuma in zanyi feeding dinta. A lokacin ne kuma aka fara daukan sabon session na makaranta, a lokacin yan set din mu zasu shiga ss3. Nayi wa Saghir maganar komawa ta school sai cewa yayi “ita kuma Subay’a fa? Yaya kike so ayi da ita? Sai dai ki bari sai wani session din kafin nan tayi kwari” sai ya kara da cewa “in kuma kafin nan kin kuma samun wani cikin shikenan” ban mayar masa da magana ba saboda bai san zancen implant dina ba, haka na hakura da zancen makaranta dan babu yadda zanyi, in nace zan kai kara ma bayan sa za’a bi ace in bari yarinya ta tayi kwari. A lokacin ne kuma yake sanar dani cewa ogansa zai tafi kasar waje karatu “he will be managing the company from there, kin san komai yanzu an mayar dashi computerized ballantana manyan harkoki irin na wadannan mutanen” nayi kamar ban ji shi ba dan ni har na gaji da maganar ogan nan, kullum oga this oga that, oga yace kaza oga yayi kaza, I wonder me suke yi a office din bayan zaman hira.Bayan Shekara Biyar1 Shekaru biyar suka zo suka wuce. A cikin su abubuwa da dama sun faru, na farko Hardo da Uwani duk sun rasu sati daya a tsakaninsu, Hardo ne ya fara rasuwa munje Kollere zaman makoki itama uwani ta kama jinya sannan ta rasu ranar sadakar bakwai dinsa. Naji mutuwar Uwani sosai kusan fiye da yadda naji ta Hardo.1 Rayuwata a gidan Saghir babu abinda ya chanza sai abinda ya kara gaba, ya dawo da shaye shayensa, ya kuma mayar da neman matansa openly wanda da yana dan boyewa amma yanzu kiri kiri yake yi musamman tunda kudade suna shigo masa, har gida mata suke zuwa neman Saghir, tun yana yi min karyar cewa abokan aikin sa ne har ya daina. Lokuta da dama kuma yana dora min laifin neman matansa, yace nice na gaza sauke masa hakkin sa shi yasa yake zuwa yake nema a waje wanda ni kaina nasan ina da laifi ta wannan bangaren, nayi nayi in tursasa zuciyata ko yayane in saka Saghir a cikinta amma taki yarda, Sadauki ya riga ya chika duk wani lungu da sako na zuciyata yadda babu wani bugawar da zata yi wanda babu tunanin sa a ciki. It was so hard living with a man while my heart belongs to another. Another din da ban ma san inda yake ba, babu amo babu labarin sa daga shi har yaya ladi. Sometimes sai in samu kaina da tambayar ko wanne hali yake ciki? Ko ya samu admission din yayi karatun? Ko rayuwa tana tafiyar masa dai dai ko kuma akasin haka?1 Amma kuma hausawa sunce idan bera da sata daddawa ma da warinta. Ina da laifi a zaman mu da Saghir na sani amma shima ai da laifinsa, at least da ace yana treating dina well da ko ban so shi ba bazan ki shi ba, da zan iya managing in faranta masa as long as nima yana faranta min amma Saghir was doing total opposite of faranta min. Tsawa, hantara, bakar magana and occational duka duk ina samu daga gurin Saghir. Yana ciyar dani, barely, dan duk ranar dana ganshi da leda a hannu ko kuma naga yana yi min murmushi to nasan wani abun yake nema a gurina ni kuma a lokacin zan tayar da tawa tsiyar har sai mun rabu baran baran.2 Na koma makaranta bayan na yaye Subay’a, shima da kyar Saghir ya bari har saida na hada shi ta Hardo lokacin yana da rai sannan ya saka ni a wata government school anan bayan layin mu. Na fuskanci challenges da yawa a lokacin musamman saboda kasancewa ta matar aure a makarantar yan mata, kuma duk yan class din na girme musu dan ma bani da girman jiki dan haka da wahala ma ka gane shekaru ma, babu kuma wanda yake yarda nina haifi subay’a musamman saboda tana da girma sosai ita. Har nuna ni ake yi, ni kuwa sai naja kaina gefe nayi facing karatuna kadai wannan yasa har na kammala banyi wadansu kawaye ba sai dai gaisawa kadai. Inna tana ci gaba da kasuwancin ta, dashi suke ci, sha da sutura ita da Asma’u kuma dashi take biya wa Asma’u kudin makaranta, ta gaya min cewa tunda ta bar gidan Alhaji Babba, kaf yanuwan Baffa babu wanda ya taba daukar kwandala ya bata yace ki siyawa Asma’u ruwa, komai ita take yi musu wani lokacin ma harni take dan dinkawa kaya ta aiko min dashi tunda nawa mijin ba mai yi bane ba. Zai dai dinkawa kansa suttura kamar banza, yayi ta shiga yana fita, mayukan shafawarsa da turarukansa ma kadai abin jinjinawa ne amma ni kayan kyalliya tun na lefe na, da suka kare da wahala yake siyamin wani abu dana yi maganar kayan lefe na ma sai cewa tayi “da uban waye ya siya miki kayan?”.1 A lokacin da nayi candy a lokacin nake da shekara ashirin da daya, Subay’a tana da shekaru biyar. Har lokacin kuma ina nan jiya iyau, babu abinda na kara a girman jiki sai ma kara motsewa da nayi wadda rannan da Inna take mita naji Mama tace yana da dangantaka da planning din da nake yi, maybe in ya barni zan yi kibar. Sometimes Saghir ma da kansa yana complain “Diyam kina da kyau sosai a fuska, mu maza kuma ba wannan kadai muke bukata ba muna son mace mai lady body parts” yana magana yana nuna irin parts din da yake nufi, nakan bashi amsa da “ai bani na halicci kaina ba, dan haka bani zakayi wa complain ba”.1 Ranar nan nayi bakuwa, Maman Iman, tazo ta wunar min ita da yaranta da Asma’u na wadda ta shiga ss2 yanzu. Sai Maman Iman ta dauko wasu kulle kulle a leda ta jani bedroom dina ta fara tsaramin STORY CONTINUES BELOW “kinga wannan garin da nono zaki ke sha ko da madara, kamar bayan la’asar haka yadda kafin dare ya fara aiki. Shi kuma wannan gumba ce ki adaba kina cin kayar ki a hankali tana da amfani sosai, wannan kuma na tsuguno ne, ki barbada shi a garwashin wuta sai ki tsugunna a kai ya shiga jikin ki sosai” Nasan magungunan menene dan kusan duk sanda naje gida sai ta bani irinsu, wani lokacin ina fitowa nake zubawa a kwatar kofar gida inyi tafiya ta. Amma sai nace “maganin menene wannan maman iman? Maganin tajika ne ko kuma na mayu” ta harare ne “a’a maganin sihiri ne. Kar ki raina min hankali mana Diyam, kinsan nawa na saka na sayi maganin nan kuwa? Wannan na tsugunnon da kyar ma na same shi shine na raba biyu na kawo miki rabi amma zaki raina min hankali” nayi dariya nace “maida wukar yayata ta kaina. Amma ki tafi da kayanki kar inyi miki asarar kudi dan wallahi ba amfani zanyi dasu ba” na fada ina dora mata akan cinyarta, ta dawo min dasu kan tawa cinyar tace “wallahi ki gwada ki gani, matar data bani ta tabbatar min da cewa indai kika yi amfani da wannan yadda kika san cingam haka mijin ki zai manne miki” nayi dariya na sake mayar mata nace “bana son ya manne min kamar cingam, ki kara akan naki sai abban iman ya kara manne miki kamar superglue” kafin ta bani amsa aka budo kofar dakin da kallo, Saghir ya tsaya yana kallon mu sannan yace “dan wulakanci kinsan ma dawo amma kika yi zaman ki ba zaki zo ki bani abinci ba” Maman Iman ta gaishe shi, yayi mata kallo daya ya dauke kai fice. Na mike nabi bayansa idona blurry with tears, yaushe wannan zubar hawayen nawa zai kare? Indai har nayi baki, ko kuma shi yayi baki, to kuwa tabbas sai ya wulakanta ni a gabansu, shi yasa har banaso inyi baki indai tana gida.1 Washegari muna kasa ina taya Subay’a yin homework dinta sai gashi ya dawo daga office. Ta tashi da gudu ta tafi gurinsa shi kuma ya daga ta sama yana juyata suna dariya. Na gaishe shi ya amsa ciki ciki sannan direct ya wuce dining ya zauna ya zaunar da Subay’a a kan table din ya fara zuba abinci suna hira. Na taso na karba ina zuba masa nace “Subay’a sauka ki zauna akan kujera, na hana ki zama akan table ko?” Ta kwabe fuska tana kallonsa yace “ita da gidan ubanta, table din ubanta kuma abincin ubanta” yana fada yana yi mata chakulkuli tana babbaka dariya, garin dariyar har ta zubar da abincin dana fara zuba masa. Nayi ajjiyar zuciya na zagaye su na wuce kitchen na dauko duster nayi clearing gurin, sannan na sake zuba masa wani. Ban mayi mata fada ba dan nasan indai yana gurin to ban isa ba, maybe a karshe ya kare da zagina a gabanta. Sai daya gama sannan ya kama hannunta suka yi sama sannan suka sake saukowa tare, ya chanza kaya, yace min “zan koma office, muna ta shirye shirye oga zai dawo office ranar monday” na gyada kai nace “a dawo lafiya” a raina ina cewa “gyara ya dawo din ai ko ka mayar da hankali gurin aikin” ni nayi mamaki ma da har yau basu kore shi ba saboda sai yayi sati baije ba, na kuma ji labarin cewa company basa yadda da irin wannan kailular.1 Ranar Monday din da yamma, ina daki ina karatun novels a waya ina ta murmushi ni kadai ganin yadda mata suke soyewa a gidan mazajen su, sai naji shigowar sa, nayi sauri na boye wayar dan ya hana ni yace anan nake kara koyon rashin kunya. Ya shigo dakin babu sallama kamar kullum, ya karaso ya tsaya a gaban gado da leda a hannunsa yace “ga wannan ki tashi kiyi wanka ki saka, and please kiyi kwalliya mai kyau, in an jima da dare zamuje party” na zauna ina fito da kayan nace “party? Biki ake yi?” Ya zauna a kusa dani yana cire takalmi yace “no, wani surprise party ne muka shirya wa ogan mu a office, manyan ma’aikata duk kowa zai zo da familyn sa shi kuma za’a kira shi as far ana nemansa dinnan da gaggawa sai yazo zai gan mu” yayi tsaki “ni idea din sam bata yi min ba, tunda akace zai dawo kowa sai wani rawar kai yakeyi kowa yana neman gindin zama”. Nayi murmushi kawai ina duba kayan. Doguwar riga ce mai dan karen kyau daga gani nasan an saka kudi masu yawa gurin siyan ta kuma ba dan ni aka siya ba sai dan a burge mutane. Nayi wani tunani, I had never been to a party before, what if naje na kwabsa mishi? What if yaje ya dizga ni a cikin mutane? Kamar yasan tunanin da nake yi sai cewa yayi “but please Diyam, please don’t embarrass me a cikin mutanen nan, my entire reputation depends on this, please don’t do anything stupid” na mayar da rigar cikin ledarta nace “if it will make you feel better, ka tafi kai kadai kawai. Ni ba saba shiga cikin irin wadannan mutanen nayi ba” ya bude baki yace “salon a raina ni? Ace bani da iyali? Ki shirya kawai muje Allah dai ya kiyaye ni da jin kunya”.1 STORY CONTINUES BELOW Shi ya dauko Subay’a daga islamiyya ya kaita makotan mu inda naje ajiyeta sanda ina school. Sannan ya dawo yace min in nayi sallar magrib in shirya shima zaije ya shirya. Na tashi na shiga wanka kawai naji jikina yayi wani irin sanyi zuciyata tana ta bugawa, ni duk ji nake yi bana son zuwa gurin taron nan nasu gani nake yi kamar wani abu ne zai faru idan naje amma babu yadda zanyi haka nayi wanka na fito, na shafa mai na saka rigar daya kawo min. Golden color ce da akayi mata agon stones na silver, sai veil silver da stones golden. Ina sakawa Saghir ya shigo yana fadan har yanzu ban gama shiryawa ba, sai kuma yayi shiru yana kare min kallo da sakakken baki. “You look really beautiful” na dauke kai ina kallon kaina a mirror, babu abinda na sakawa fuskata in banda kwalli amma ta fito fes tana kyalli, kayan jikina sun kara haskaka fatata, sai naga ya saka hannunsa a aljihu ya dauko wata sarkar gold ya karaso ya saka min a wuyana, sai kuma yayi kissing wuyan, nayi saurin matsawa ina wayencewa da saka yan kunnayen daya ajiye. Ya sake biyo ni ya dauki comb yana taje min gashin kaina zuwa baya sannan ya saka ribbon ya daure min shi a keya side din hagu ya zubo dashi ta kafada ta yana cewa “let’s show them abinda matan su basu dashi” Na cire ribbon din ina girgiza kaina nace “babu kyau fito da gashi ga wadanda ba muharramai ba” yayi tsaki, “ke chafsi ne dake wallahi” a raina nace ‘naji din’ na daure gashina a tsakiya kamar kullum sannan na nannade shi sai nayi rolling veil din irin yadda naga su Rumaisa yammata suna yi. Sai kawai na tsaya ina kallon kaina a madubi, ban taba ganin nayi kyau irin na ranar nan ba. I looked like baby doll din da kullum ake kwatanta ni da ita. Na rike clutch silver sannan na saka silver hills masu tsinin da suka kara min tsaho. Ya tsaya a bayana yana kallona ta cikin mirror yace “perfect, ina ma kin fi haka girma but hakan ma is okay. Am sure babu wanda zaizo da mata irin tawa”.1 A hankali muke tafiya, kowa da abinda yake zuciyarsa. Ni tawa zuciyar wani irin bugawa take yi wanka har daci naje ji a bakina, a tsorace nake sosai kamar in bude motar in fita a guje. Har muka je gurin, wannan shine karo na na farko da naje companyn Abatcha Motors. Dare ne kuma kusan duk fitulun gurin a kashe suke saboda basa son idan ogan yazo yayi tunanin wani abu, dan haka a lokacin bazan iya adar da komai dangane da yanayin gurin ba, baya muka zagaya mukayi packing, nan naga duk kowa yana packing ana ta fitowa kowa da matarsa ko budurwar sa. Saghir ya juyo ya kalle ni yaga yadda nake a tsorace yace “bafa cinye ki za’ayi ba, just do as i do. Duk wanda kika ga nayi wa magana sai ki gaishe shi, ba kuma cewa nayi ki durkusa har kasa kina gaishe da mutane ba” na gyada masa kai muka fita a tare, ya zagayo ya zura hannunsa cikin nawa muka shiga cikin mutane. Faran faran muke gaisawa da mutane kowa yana introducing matarsa, Saghir proudly yake nuna ni a matsayin matarsa, ina kuma lura da yadda idanuwa suke bina da kallon yabawa. Sai da aka gama gaggaisawa sannan muka zagaya muka shiga cikin building din gaba ki daya, nan ma babu fitulu sai guda daya dan haka dimly kowa ya samu guri ya zauna ana jiran wanda ya tafi tahowa da oga su dawo.una nan zaune ana dan hira kadan kadan suka shigo, sai aka yi saurin kashe fitila dayar da aka kunna gurin yayi duhu daga ki daya. Muna jinsu suka karaso suna yan maganganu. And my heart stopped at the sound of the voice I heard.3 Sukayi unlocking kofar suka shigo cikin inda muke, and I heard one of them said “Mubarak let’s hurry up and do this. I am kind of tired” clearly in Sadauki’s voice. Na zare hannuna daga cikin na Saghir na mike tsaye da sauri “Sadauki!” Na fada under my breath. Sai kuma lokaci daya fitulun gurin suka kama gaba-daya yan gurin kuma suka hada baki wajan ambaton “surprise!!” Then I saw Sadauki a tsaye a gaba na, idanunsa cikin nawa. Komai ya tsaya min. Numfashi na ya dauke, na saki jakar dana ke rike da ita a hannuna and ikon Allah ne kadai yasa nima ban bi jakar na fadi ba. Sadaukin ne dai a tsaye yana kallona, my Sadauki. But he has changed alot, he has grown more bigger and more muscular, his dark skin shining as brightly as his bright eyes. He looked more matured, more handsome, more confident and he looked rich. Very rich.2 In a flash of second aka zagaye shi, kowa yana kokarin yi masa magana hakan yayi blocking view tsakanin mu, “what is Sadauki doing here?” Shine tambayar dana fara yiwa kaina a lokacin da numfashi na ya dawo jikina. Maganar Saghir da naji a kusa dani ita ta dawo dani hayyacina har na tuna me ya kawo mu gurin, but banji mai yaxe ba saboda voice dinsa sound so faraway kamar daga miles yake yi min maganar, the only sound da yayi filling kunnena shine na Sadauki yana gaisawa da mutane. Na girgiza kaina, trying to clear my head nace “me kace?” Tsaki kawai yayi, ya kama hannuna muma muka shiga mutanen da suka zagaye Sadauki suna gaishe shi tare dayi masa congratulations na kammala karatu. “karatu?” Na tambayi kaina. Menene hadin Sadauki da gurin nan wai? Mu ba zuwa mukayi mu taya ogan su Saghir murnar dawowa daga karatun sa ba? Ya naga kuma anayi wa Sadauki murna? Ban samu amsar tambaya ta ba na ganmu tsaye a gaban Sadauki ni da Saghir, Saghir ya mika masa hannu yace “congratulations Mr Abatcha, and welcome back to Kano” sukayi shaking hands, nabi hannayen nasu da kallo sannan na sauke ido na akan Sadauki, trying to digest what I was beginning to understand.1 Mintsini Saghir ya sakar min a hannu sannan cikin whisper yace min “for God’s sake stop staring at him and greet him” sai kawai nabi Saghir din da kallo ba tare da nace komai ba, kamar daga sama naji muryar Sadauki yace “Hello Madam” na juya ina kallonsa, sai naga kamar ya saka wani mask ne yayi hiding Sadauki na, kamar this man is not the Sadauki I knew, this man is Mr Abatcha.1 Madam?” Na maimaita cikin kokonton abinda kunnena yaji min. Sai ya dauke idonsa daga cikin nawa ya wuce mu ya tafi gaban taron ya daga murya yace “Thank you, all of you. I really appreciate this surprise party and I am really surprised” ya danyi dariya, “but I am sorry I can not stay, I have something really emergency that I need to do. You guys should go ahead and enjoy yourselves. Thank you ones again” sai na juya da sauri yayi hanyar waje, abd without even a second glance at me ya fice daga building din. Da sauri organizers din partyn suka bishi a baya, ciki har da Saghir, nima sai na samu kaina da binsu a baya, hoping to see him again, to talk to him even dan in tabbatar cewa da gaske shi dinne kuma da gaske bai gane ni ba. “Can it be? Ace Sadauki bai gane ni ba ni Diyam?”1 Ina fita kofa yana tayar da mota, yaci taya ya bar gurin a guje ba tare da ko ya tsaya ya saurari ma’aikatan sa da suka biyo shi a baya ba. Nabi motar da kallo har ya fita daga gate, sai kuma na zame na durkusa a gaban wata flower bed na jingina kaina a jiki ba tare da ko damuwa da menene zai iya fitowa daga ciki ya cutar dani ba. I only wanted to wake up, wake up from this nightmare where Sadauki doesn’t know me. Ina jin su Saghir suka wuce suka koma ciki suna ta maganganu babu wanda ya lura dani, bayan mintina kadan kuma sai aka fara watsewa kowa yana fitowa yana neman shiga motarsa. A lokacin ne kuma naji muryar Saghir ya na nemana “Diyam! Diyam!” Amma na gaza bude baki ballantana in amsa masa har yazo inda nake sannan cikin whisper yace “what the hell are you doing here?” Maimakon in bashi amsa sai hawaye ya fara kwarara daga idona kamar an bude pampo, ya fincike ni ya tayar dani tsaye yana grinning at mutanen da suke wucewa sannan ya kaini mota ya cusa ni ya rufe kofar muma muka fita. Ba wanda yayi magana har muka je gida, yana packing ya zagayo ya bude inda nake ya fige ni zuwa cikin gida ya jefa ni a kan kujera yace “me kike tunanin zakiyi archiving ne by embarrassing me a cikin mutane? By trying to destroy my carrier? Oga na yana miki magana ki wani tsaya kina kallonsa kamar statue? Sannan kuma ki fito ki zauna a cikin flowers are you nuts?” Na dafe kaina da hannuna, ni ihun da yake min ji nake kamar zai tsaga min kaina gida biyu. Har yanzu kaina yaki budewa balle in yi tunani. Farkon abinda nake so in fahimta shine me Sadauki yake yi a gurin aikin su Saghir? Kuma har nani suna addressing dinsa as if shine manager dinsu daya dawo daga karatu suka shirya masa party. Can it really be? In kuma har ya kasance haka ne to how comes? Ni dai Sadaukin dana sani sanda muka rabu seven years ago bashi da komai, kuma shekaru biyu bayan rabuwar mu Saghir ya samu wannan aikin then how comes Sadauki yayi kudin da har zai bude companyn motoci a cikin shekara biyu? Bayan wannan kuma shin sun gane juna ni suke playing ko kuma suma kansu basu gane ba? Anya kuwa Saghir zai karbi aiki a gurin Sadauki in har yasan shine? Sai wani tunani yazo min, as we were growing up ni da Sadauki, bazan iya tuna ranar da Saghir yaje gidan mu ba, lokacin ma shi kusan kullum baya kasar. And Sadauki was never allowed to enter gidan Alhaji Babba tun yana dan karamin sa har sai sanda naje nake shigo dashi a boye and even then basu taba haduwa ba. So what I was sure of shine basu san faces din juna ba. But, me yasa Sadauki zai yi acting kamar bai sanni ba? He did looked surprised akan party din but he did not act surprised to see me there, meaning yasan dangantaka ta da Saghir. And then many things started to become clear to me, sunan subay’a, aikin Saghir. Tabbas Sadauki ya gane Saghir bayan yayi masa tambayoyi a gurin interview wannan shi yasa ya dauke shi aiki even with his pass certificate and lack of experience, kuma shi yasa har yanzu ba’a kori Saghir ba daga aiki duk da negligence dinsa. But why? Ina son insan me yasa Sadauki yayi haka? Is my Sadauki still behind the mask of Mr Abatcha? Sai bayan na dawo daga tunani na nayi realizing har lokacin Saghir fada yake yi. Na tsaya ina kallon sa ina realizing cewa he had no idea mai ya faru a gurin nan. Shi kawai fada yake na wulakanta ogansa. Nayi gyaran murya nace “Allah ya baka hakuri. Ni ba’a saba cemin Madam bane ba shi yasa na kasa amsa masa. Amma kayi hakuri, nan gaba in ance min madam zan amsa” na mike zan hau sama yace “ina jakarki?” Sai lokacin na lura bata hannuna nace “ta fadi a gurin” nan kuma sai ya koma fadan yar da jaka “tunda bake kika siya da kudin ki ba ai dole ki yar” ni dai nayi wucewa ta sama na barshi a nan.1 STORY CONTINUES BELOW Ranar yadda naga rana haka naga dare. All I wanted to do is to see Sadauki again and ask him tons of questions da suke zuciyata. Exactly a week after that. Muna palo ni da Subay’a ina kokawar yi mata kitso tana ta zillo tana kuka Saghir ya sauko daga sama. Ya saka hannu ya dauke ta daga cinyata ya suka hau kujera yana warware mata kitso dayan da da kyar na samu nayi mata shi. “Tunda bata so sai a rabu da ita, ke waye yake takura miki yanayi miki kitso in bakya so?” Ban ce komai ba danni yanzu bana cikin mood na musu da Saghir. Yace “wato idan Allah ya yi mutum shi mai sa’a ne a duniya to bashi da wani sauran stress kuma a duniya. Kinga a office dinmu tun daga dawowar oga yadda ake ta rububi ana shishshige masa kowa yana so ya kafa kansa, ni kuwa babu abinda ya dame ni dasu aikin gaba na kawai nake yi. Amma kinsan ina daki kawai yayi kirana a waya, wai dan Allah in an jima inje airport in dauko shi zai dawo daga Maiduguri, kinsan dan can ne ai, babarbare ne” na cigaba da harkokin gabana looking uninterested, Amma kirjina lugude kawai yake yi nace “hmmm, Allah ya taimaka” ya danyi shiru sai kuma yace “I have an idea, tunda kowa neman shiga yake a gurin oga why not me? Nima ai ina son promotion din. Idan na dauko shi daga airport nan gidan zan kawo shi, you prepare dinner for him tunda dama bashi da aure kuma bashi da gida a hotel yake zama, nasan zaiji dadi, in ya ci abinci anan sai in kaishi hotel din da take zama” na yi saurin juyo wa ina kallon sa, sai na samu kaina da girgiza kaina nace “no” no matter how much zuciyata take son ganin Sadauki nasan ba dai dai bane ba, shigowar sa cikin gidan aure na ba abu ne mai alfanu ba “Please ka zarce dashi inda zai sauka kar ka kawo shi nan” ya mike tsaye yana kwantar da Subay’a da tayi bacci a hannunsa yace “yes, nan zan kawo shi first. Zan fita in yo miki cefane and you cook something nice for him, abincin da kika san mutane irin sa zasu ci” kafin in sake retaliating ya fita. Na zauna a gurin na dafe kaina kirjina yana bugawa da karfi, wata zuciyar tana gaya min cewa in gaya wa Saghir waye ogan sa wata kuma tana hanani har sai na samu Sadauki munyi magana na fahimci inda yasa gaba tukunna. But yaushe zan same shi? Ni a matsayina na matar ma’aikacin sa? Ni a matsayina na wadda yayi addressing as Madam? Ina nan zaune har Saghir ya dawo da ledoji niki niki ya shiga kitchen ya ajiye, ya fito yace “ga nama can da kayan miya da fruits, akwai wani abu da kike bukata kuma?” Na langwabar da kai “ni yanzu mai zan dafa masa?” Yace “think of something, nima ban sani ba”. Daga haka ya fita ya barni. Sai dana kai Subay’a islamiyya sannan na dawo na shiga kitchen, na saka ledojin a gaba ina kallo, me zan dafa? Kuma wai Sadauki zan dafa wa abinci a matsayin sa na ogan mijina. Lallai life is full of twists and turns. Sai na tuno da tuwon Ummah da take yi mana muna yara ni da Sadauki. Tuwon laushi miyar yauki sai ta dagargaza kaza a ciki ta cire kashin gaba daya. Sadauki yana so sosai dan har cewa yake yi ayi dan haka na nutsu na fara shirya masa. Na gyara fruit din nayi smoothie na saka a fridge. Zuwa magrib na gama na shirya komai a dining table sannan na fita na dauko Subay’a sai kuma na sake gyara gidan na saka turaren wuta naja subay’a muka hau sama. A sama nayi wanka nayi mata wanka itama muka yi sallah tare sannan ta kwanta ina yi mata kitson da taki tsayawa ayi dazu, a haka har tayi bacci sannan naji shigowar mota, gabana ya yanke ya fadi na kalli window amma wani barin na zuciyata yace “kul kika leka kallon haramun” sai na kwanta na dunkule a guri daya kamar mai zazzaɓi, naji an tsayar da motar an kuma bude an fito sai dai ba’a rufe ba, naji ina son in san me yasa ba’a rufe din ba. Na jawo pillow na dora a kaina na danne da hannayena amma the next second sai gani na nayi a bakin window a bayan labule ina leka waje. Saghir na hango a tsaye a bakin mota yana magana dana cikin motar wanda shi bai fito ba, sun jima suna magana a haka, kamar na cikin baya son fito wa yayin da Saghir yake ta insisting akan sai ya fito. Sai kuma naga ya zuro kafafuwansa ya fito Saghir ya rufe masa kofar sai suka jero a tare suka doso cikin gida, yayinda fitilar gaban gidan ta haske min su.2 Two men; one fair and the other one dark, fair one din shine mijina amma ni zuciyata dark one din take so; one taller than the other ni kuma tall one din nake so, one younger than the other ni kuma younger one din nake so, one frowning the other one smiling ni kuma me frowning din nake so, one employer the other one employee ni kuma employer din nake so. But the other one is my husband. That was how cruel my was. For a split second, Sadauki smiled, a smile that went straight to my heart, nayi saurin sakin labulen naja da baya kamar wadda ta taba wuta. Ji nayi kamar an debo wani tarin sonsa cikin trailer an zuba min a zuciyata sai naji tayi min nauyi dan haka na ruke kirjina na zauna akan gado ina ambaton sunan Allah da niyyar ya kawo min dauki a cikin lamari na tun kafin inyi tabewar da zata kaini ga halaka. Waya ta ta fara ringing, da kyar nayi karfin halin dauka na kara a kunnena Saghir yace ina whisper “mun shigo. Ki zo ki kawo masa abinci” nace “dan Allah Saghir ka bashi kawai, bana jin dadi wallahi” nasan banyi rantsuwa akan karya ba saboda yadda nake jin jikina tabbas nasan akwai zazzaɓi a tare dani, yayi tsaki ya katse wayar. Na koma na kwanta na jawo Subay’a jikina na lullube mu, amma muna fikin kunnena sai yake kokarin zuko min maganganun da ake a palo, wishing to hear muryar Sadauki. Ina nan kwance kawai naji an hawo saman sai aka bude dakin, Saghir ya shigo fuskarsa kamar zaiyi kuka “Diyam? Me yasa ne wai ke kullum burinki kiga na tozarta a duniya, why?” Na tashi zaune ina girgiza kaina nace “me nayi kuma?” Yace “tuwo. For God’s sake tuwo Diyam zaki yi wa wannan mutumin da bana jin ya taba cin sa? Ko ni ba cin tuwo nake yi ba kuma kin sani” nace “cewa yayi ba zai ci ba?” Yace “to ni ina zan iya bashi? Kin san da yadda nayi convincing dinsa ya shigo kuwa kuma kawai sai inkai masa tuwo?” Na tashi na zura jihab dina na fita ya biyo ni a baya. Yana facing stairs, wannan yasa ina fara sauka na ganshi amma shi kansa yana kasa yana daddanna wayar hannunsa. Na dauke ido na daga fuskarta ina kallon gefe nace cikin wata muryar da naji kamar ba tawa ba “Barka da zuwa” ya dago kai, kallo daya sannan ya mayar da ganinsa kan wayarsa yace “Barka kadai Madam. Ya gida?” Still with the Madam, na fada a raina and my heart hurts. Ban amsa ba na mike naje dining na duba na tabbatar komai yana nan yadda ya kamata sannan na dawo na tsaya ina kallon Saghir da yake ta kokarin yi masa hira nace “ga abinci a table Ko nan za’a kawo muku?” Sadauki ya mike da sauri yace “thank you, zamu ci a can din. Ni am fine ma really, maigidan ki yace sai nazo naci, so I guess I will just have a taste and go” sai kuma ya tafi dining area da sauri Saghir ya bishi a baya, yana zuwa ya dauki plate zaiyi serving kansa sai plate din ya zame daga hannunsa ya fado ya tarwatse, and I noticed that his hand was shaking. Saghir ya kwalla min kira “zo da sauri ki gyara gurin nan” amma kafin in karasa Sadauki ya bar gurin da sauri yayi hanyar waje, Saghir ya kalleni da alamar tambaya na daga masa kafada, sai kuma ya bishi wajen.2 Na tsaya da tarin abinci a gaba na ina kallon kofa, so the mask has fallen, my Sadauki is still in there kawai duk pretence ne.9 Ina tsaye Saghir ya dawo yace “get a basket ki zuva warmers din a ciki, he is taking it away” naje na dauko na hada masa komai har drink din na rufe, Saghir ya karba yana cewa “Allah yasa ma yaci, wannan mutumi kamar aljanu ne dashi”.12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *