UMMI CHAPTER 8
A yau sati biyu kenan da MK ya sa a nemo mishi Ummi. Tun dawowar shi daga Lagos bai qara zuwa ofis ba… Asali ma tunda Ummi ta tafi MK ya kasa yin wani abun arziki a rayuwar shi. Gaba daya ma ya rame don baya cikin kwanciyar hankali sannan baya wani cin abinci kamar yadda ya kamata. Burin shi a kullum shine a kira shi a sanar da shi an ga Ummi.+ A dalilin babu qwaqwarar details din Ummi ne Fahad ya samu hoton ta a CCTV camera na gidan MK Wanda aka yi making copies aka fitar. A yanzu haka an baza mutane accross the states in the country don neman ta wanda kuwa har yau shiru babu wani bayani. Dukda dai search din ya fi qarfi a north, a north din ma fulani states saboda ba sai an fada ba sun sani cewar Ummi tana da jinin fulani.. Kudin da ake kashewa kuwa tun Fahad yana lissafawa har ya bata wurin lissafi. Millions of naira aka kashe wanda ake kan kashewa don gano Ummi amma shiru. where could she be???13 ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO ABUJA Kwance take a kan gadon dakinta yayinda take fama da zazzabi. Maleeka dai kusan kwana biyu kenan tana jin jikinta wani iri. Ga kasala da amai da yake yawan taso mata. A yau dai zazzabin ya fi na kullum domin kuwa tun safe da ta farka bata sauka daga kan gadon ba.2 Rabon ta da MK har ta manta domin kuwa har yau fushi take yi da shi sossai. Har yau jira take yi ya zo ya bata haquri sannan su koma normal.3 Su girman kai manya. Tana lullube a cikin duvet ne wayarta tayi ringing. Da qyar ta miqar da hannu ta janyo wayar ta duba. Sunan Jameela ta gani. Ko da tayi answering muryarta qasa-qasa tace “Jay..” A dayan bangaren ne Jameela tace “Leek ya na ji muryar ki down? ba dai zazzabin bane??” Maleeka wadda idanuwan ta suke a rufe tace “wallahi Jay na yau ma abin babu kyau… gaba daya na kasa sauka daga kan gadon ma” Jameela tace “subhanalillah.. ina Ya MK fa?” Ran Maleeka a bace tace “manta da shi jor.. ni rabona da shi ma har na manta.. idan bai zo ya bani haquri ba I swear sai dai mu cigaba da zama a haka..”4 Jameela cike da mamaki tace “wai wane irin tunani ne da ke Leek??? dont you think this is the time da yakamata ki nemi sulhu da Ya MK?? dont you think it’s time da yakamata ki zauna kuyi settling differences dinku?? ki tuna fa ke ce mai laifi.. atleast tunda kin yi nasarar korar yarinyar tun kafin labari ya canza ai sai ki matsa kusa da shi don ki..”2 Maleeka wadda ta tashi zaune ce tace “please Jay just stop..” Jameela tace “toh shikenan Leek… yanzu me ke yi miki ciwo?? yakamata ki je asibiti” Tace “wallahi Jay jiri ne yake yawan diba na sannan ina yawan ji kamar zan yi amai.. ga mugun zazzabi da yake takura ni..” Kai tsaye Jameela tace “are you pregnant??” Zaro idanuwa Maleeka tayi tace “what??? me?? it’s not possible ai…” Sai kuma tayi shiru tana tunani sannan kuma ta dafe kai yayinda ta shiga tashin hankali lokaci guda..6 Maleeka dai ta tuno ranar da suka yi rigima da MK a dalilin kwashe mata pills da yayi wanda hakan ya sanya tayi fushi ta bar gidan ta tafi England. A dalilin tashin hankalin da take ciki ta manta bata yi tunanin siyo wasu pills din ba ta sha dukda kuwa ko tayi hakan tendency na pills din suyi aikin su is so minimal tunda it wasn’t immediately after they had sex… wani al’amarin kuma shine yadda tayi missing period dinta… STORY CONTINUES BELOW Ji nayi tace “na shiga uku Jay… it’s possible I am..” Daga nan kuma sai ta fashe da kuka yayinda tace “wallahi ya cuce ni… I really cant be pregnant”4 Jameela ce tayi saurin cewa “Hey qawata… meyasa kike fadin haka??? it’s the best thing that could happen to you right now.. dama abinda Ya MK yake so ne… idan har kina da ciki ai shikenan duk wata rigima a tsakanin ku zata kau…”1 Maleeka wadda take cikin tsananin damuwa tace “hell no my friend.. idan ma har akwai cikin nan wallahi zubar da shi zanyi..”1 Da sauri Jameela tace “subhanalillah Leek..” Maleeka ta dakatar da ita tace “Please Jay… I will call you back, akwai important abu da yakamata inyi yanzu” Ko kafin Jameela tayi magana kuwa sai Maleeka ta kashe wayar ta jefar da ita gefe ta yaye duvet din da ta rufa da shi ta sauka daga kan gadon yayinda na ji tana fadin “ai wallahi idan ma akwai shi zubarwa zanyi.. ba dai abinda yake so bane?? toh bazai samu ba tunda dai ni zai wulaqanta a dalilin ‘yar aiki..”3 Da qyar ta shiga closet don shirin yin wanka yayinda take ta masifa har tana zubar da hawaye. Har ta fito daga bathroom masifa take yi. Wayarta kuwa sai ringing take yi yayinda tayi watsi da ita.. Jameela ce take ta kiran ta amma ta qi picking. Ko da ta shirya cikin wata doguwar free gown na material marar nauyi gani nayi ta koma kan gado ta kwanta yayinda ta dauki wayar intercom ta kira kitchen. Ji nayi tace “make some tea and bring it to my room please..” *************** Maleeka dai bayan ta shanye tea din da aka kawo mata ne na ga ta shiga closet dinta ta fito riqe da gyale a hannunta. Gani nayi ta yafa shi a kanta sannan ta tsaya gaban madubi tana qare ma kanta kallo. Fuskarta fayau babu make up sannan da alama yau babu lokacin yin shi.. Tabbas Maleeka looks very sick… ta sani lallai banda damuwar da take ciki akwai wani abu. Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “I swear I am not keeping it…” Har a wannan lokacin amai yana taso mata yayinda ta ji jikinta babu dadi amma fa dukda haka ta wuce ta fita. Wurin ajiye makullan mota ta nufa ta janyo key daya sannan ta sa kai ta fice daga gidan cike da tsananin tashin hankali. Ni kuwa nace ina zata je????1 ♧♧♧♧♧♧♧ ASOKORO DISTRICT HOSPITAL Zaune take a ofis din likitar yayinda take sauraron bayanin ta. Ji nayi likitar tace “congratulation Maam, you are 6 weeks pregnant…” Ban ankara ba na ga Maleeka ta dafe kanta yayinda ta fashe da kuka tana fadin “no no no… please no…” Da sauri likitar tace “Ma’am what is it?? aren’t you supposed to be happy???” Cikin kuka Maleeka ta kalli likitar tace “hey I dont want it… kawai ki cire mun shi” Cike da mamaki Likitar take kallon Maleeka. A yadda ta ganta dai ta tabbatar Maleeka ba irin ‘yan iskan matan nan bane da suke yin ciki suke zubarwa, daga ganinta ta tabbatar she comes from a good family sannan ai ko da take cike from ta cike a matsayin she is married don haka ne ta tashi ta koma kusa da ita ta zauna tana kallonta. Maleeka wadda take kuka sossai ta shiga tashin hankali. Likitar ce ta dafa ta sannan tace “‘yar uwa me yayi zafi haka??? a matsayin ki ta musluma Allah zai baki babbar kyauta ki ce baki so??? baki sani ba ko wannan din da kike qoqarin zubarwa shine kadai qwan ki a duniyan nan?? baki sani cewar akwai matsaloli masu tarin yawa ba a fanin zubar da ciki??? Nasani sarai qila kun samu sabani ne da baban babyn amma hakan bai zamo reason da zai sa ki yanke irin wannan hukuncin ba so please I am speaking to you as a mother, as a Muslim, and as a doctor please I beg you think through what you are about to do… it’s very risky and….” STORY CONTINUES BELOW Maleeka wadda take ta sauraronta ce na ga ta share hawayen ta sannan ta miqe tare da fadin “thank you doctor” Bata saurari komai ba ta wuce ta bar ofis din da sauri. Haka ta bar likitar cike da tsananin damuwa yayinda take ta addu’a akan Allah yasa ta karbi shawarar ta. *********** Maleeka dai ko da ta fito daga asibitin gaba daya ta kasa tada motar. kanta ta kifa kan steering tana kuka yayinda na ji tana fadin “na shiga uku yanzu ya zanyi??? what was I even thinking??? aborting it in this hospital.. it can be traced easily ai”3 Gani nayi ta dago kanta yayinda ta share hawayenta sannan ta cigaba da fadin “….the only way to do this is outside the country… Zasu bani pills that will do it without complications and they will watch over me closely to ensure that babu matsala tunda su qwararru ne… again, doing it there will be better tunda babu wanda zai sani..”2 Kalaman likitar ne suka fado mata a rai wanda kuma na ga jikinta yayi sanyi. Daga baya kuma ta ja tsaki tare da tada mota tace “I have to go to America the soonest” ta ja motar ta bar asibitin.2 Toh fa… Maleeka fa tayi nisa bata jin Kira…8 ♧♧♧♧♧♧♧♧ Yinin ranar kuwa tana dakinta, tuni ta hada kayanta sannan har tayi booking flight dinta ta gama shirinta tsab. Haka Jameela ta dinga kiran wayar ta yinin ranar amma sam ta qi picking. Ta sani sarai Jameela tana so ta hana ta aikata abinda tayi niyya ne wanda ta sani sarai idan ta saurare ta tabbas zata yi laushi don haka ne ta dinga ignoring calls dinta. Haka ta tura Mata messages dayawa amma still babu reply. da wannan ne Jameela ta haqura ta qyale ta.6 Ni kuwa nace na she sabi… atoh!! ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO A yau kwana biyar kenan da Maleeka tayi tafiya. MK dai dayake ko haduwa basu yi bai ma san tayi tafiya ba sai a bakin Hafsah ya ji. Ko kadan bai damu da tafiyarta ba because bata gaban shi a yanzu. Burin shi a rayuwar nan bai wuce ya ji ance mishi an ga Ummi ba. Kwance yake a falon shi yayinda idanuwan shi suke a rufe. Sossai yayi zurfi a cikin tunanin Ummi. Gani nayi ya bude idanuwan shi yayinda ya miqe ya nufi study dinshi. Zama yayi a kan kujera ya fara kallon videos na CCTV cameras din gidan tun lokacin da Ummi take nan yayinda ya dinga kallonta. Yawanci cameran kicin ta fi hasko ta idan tana aikace aikace ko kuma tana dafa abinci. Sossai yarinyar take birge shi.. very young and beautiful girl wadda take cike da natsuwa, ga addini… Ji nayi yace “Oh my Ummi kina ina ne??…” Wayar shi ce tayi ringing yayinda ya duba. Sunan Fahad ya gani. Da sauri yayi answering yayinda na ji yace “abokina ya ake ciki ne??” Shiru ya dan yi sannan yace “toh gani nan..” Gani nayi ya miqe sannan ya wuce ya fita. MK ya shigo falonshi ya tarar da Fahad zaune yana jiran shi yayinda yake latsa wayar shi. Fahad ya dago kanshi ya kalli MK cike tausayawa yace “abokina kana cin abinci kuwa??” MK ya zauna a kan kujera kusa da Fahad sannan yace “manta da abinci abokina… ya labarin Ummi har yanzu shiru??” Fahad yace “well I think an gano wata da tayi matching description din Ummi dukda dai…” MK ne ya miqe da sauri yace “hey dagaske??” Fuskarshi ce tayi displaying tsananin farin ciki yayinda ya cigaba da fadin “…a ina?… abokina please tell me… I really need to..” Fahad ne ya dakatar da shi yayinda yace “MK relax… ba’a tabbatar ba. we are trying to confirm if it’s actually her” MK ya shafa kanshi da hannuwan shi biyu sannan yayi rubbing dinsu together yace “I can’t wait for that… just tell me inda aka ganta ni zan je inyi confirming da kaina..” Fahad yace “its ADAMAWA…” Kai tsaye MK yace “get my jet ready… I will be leaving for ADAMAWA today…”2 Da sauri Fahad yace “hey today???… ka bari mu tabbatar da ita din ce mana.. besides na ji sun ce sunan wannan UMM AIMAAN…” Fahad dai bai rufe bakin shi ba ne ya ji MK yace “it’s her abokina… it’s my Ummi. Please just get my jet ready now…”6 Ghen ghen ghen…YOLA AIRPORT, JIMETA ADAMAWA STATE. Wuraren qarfe goma saura na dare jet din MK ya diro garin Adamawa.5 Ina tsaye na hango shi ya fito daga arrivals din tare da su yayinda suke ta magana. Bashir da Usman dai suna cikin secret service agents din da aka yi hiring don neman Ummi. Sune wadanda suka samu major lead wanda har ya sanya MK zuwa garin Adamwa. Sanye yake cikin wandon three quarter sweat black colour da farar polo T-shirt. Dukda ramewar da yayi da kuma tsananin damuwar da yake ciki yayi kyau sossai tunda dai dama kyakyawa ne. Gani nayi sun qarasa wurin wata Mercedes Benz qirar AMG GLE-580 baqa wuluk sannan sabuwa gal…. sai sheqi take yi. Usman ne ya sanya trolley din MK a boot din motar yayinda suka shiga. Suna tafe a kan hanya ne na ji MK yace “toh yanzu yaron da yace ya santa din yana ina ne??” Bashir yayi gyaran murya yace “dan qauyen su ne…” Usman ne ya cigaba da fadin “so far shine ya bamu tabbacin cewa lallai ita ce… sai dai mun ganta din zamu tabbatar” MK ya saki ajiyar zuciya a ranshi yace “insha Allah ita ce” Haka dai suka cigaba da tattaunawa har suka kai shi Hotel din da aka yi mishi booking for the rest of his stay a garin Adamawa. ♧♧♧♧♧♧♧♧ MADUGU ROCKVIEW HOTELS JIMETA Tsaye yake a wurin window na dakin yayinda yake magana da Fahad a waya. Ji nayi yace “yeah abokina… munyi da su gobe da safe zamu je. I swear I am so eager to see her” A dayan bangaren ne Fahad yace “MK please dont get your hopes high on this.. idan ba ita bace fa??” MK yayi murmushi yace “see, kana gani coincidence ne a gano Ummi a Adamawa??? garin fulani… sannan ace sunan ta UMM AIMAAN and hakan ya zama ba ita bace?? we both know cewar Ummi fulani ce kuma duk mai suna UMM AIMAAN can take a short form UMMI.. na ji a jikina its her”6 Fahad ya girgiza kai yace “Allah yasa ita ce abokina, just keep me posted” Yace “i will.. please kar ka manta I am on a business trip incase an tambaye ka ni… that’s it” Fahad yana dariya yace “kar ka damu my friend.. your secret is safe with me. hope dai duk abinda kake buqata is to your taste?? the hotel… is it a good one??” MK wanda ya dan kalli executive dakin da yake yace “not bad abokina… ni kam a yau ko qarqashin gada aka ce in kwana gobe za’a kaini in ga Ummi wallahi zan kwana…”8 Cike da mamaki Fahad yace “kai abokina… wannan soyayyar fa tana bani tsoro”2 MK wanda yake dariya yace “soyayya fa kace… not again abokina”3 Fahad dai cike da tsokana yace “I am sorry angon Leek” Tsaki MK yayi sannan yace “don Allah kar ka bata mun rai..” Fahad yana dariya yace “ban gane kar in bata maka rai ba… ka daina sonta ne ko me??” Ya girgiza kai yace “hey.. let me find my Ummi first..”7 STORY CONTINUES BELOW A haka dai suka cigaba da hira wadda duk yawanci ta Ummi ce. ♧♧♧♧♧♧♧♧ Washegari!!!2 A yau juma’a tafe suke a cikin motar wadda Bashir ne yake tuqawa sai Usman a gefen shi. MK yana zaune a owner’s corner yayinda ya qagara su kai shi wurinta. MK wanda yake ta kalle-kalle ne ya ga sun saki hanya yayinda suka shiga wani qauye. Babu kwalta a qauyen sannan dukda wutan lantarki ta ratsa ba kowanne gida zaka ga pole ba. da alama ba kowa yake iya affording ba. Gidajen qauyen dai are dispersed sannan yawanci duk bukka ne. Kadan daga ciki ne akayi ginin siminti wadanda su din ma idan ka kalle su zaga gane da qyar aka yi su. Yara ne birjik a qauyen suna ta wasannin su. Ga ‘yan mata masu tallan nono suna ta kai da komowa.. haka makiyaya masu kiwon Shanu suna ta kora shanun su zuwa inda zasu samu abinci. Duk inda motar su MK ta gifta kuwa sai an bi su da kallo. Yara kuwa sai bin motar suke yi yayinda mata suka dinga leqowa ta katanga da qofofin gidajen su. MK wanda yake ta kallon wadannan mutane yana ta mamakin yadda suke rayuwa a irin wannan wurin.2 Gani nayi ya runtse idanuwa ya bude sannan yace “ya salaam… yanzu a nan qauyen Ummi take??”2 Bai ankara ba ya ga sun tsaya a kusa da wata tsohuwar makarantar LGEA yayinda Bashir yayi parking. Gani nayi Usman ya bude qofar shi ya sauka yayinda na hango wani dan matashi wanda bazai wuce shekara Goma sha biyar ba ya nufi wurin shi. Bayan sun gaisa ne na ga Usman ya zagayo tare da yaron ya bude mishi qofar baya. Daidai yaron zai shiga ne na ji wata yarinya tace “Atiku ina zaka je??” Atiku wanda yake ta washe baki yace “Zan kai su gidan turawa ne” Ya shiga ya zauna a gefen MK yayinda Usman ya rufe qofar ya zagayo shima ya shiga. Gaba daya hankalin yaron yayi nisa a kalle-kallen tsarin motar. Shi kam a rayuwar shi bai taba shiga mota ba sai yau. Tunda aka haife shi ma bai taba fita daga qauyen nasu ba balle har ya shiga mota. Muryar MK ya ji daga gefen shi yace “dan samari muna lafiya??” Da sauri ya juyo ya kalle shi yace “ina wuni Hamma” MK yace “lafiya, ya sunan ka” Yace “Atiku” MK ya girgiza kai yace “Atiku Wazirin Adamawa kenan” yayinda yaron yayi murmushi. MK ne yace “kace ka san Ummi???” Atiku yace “na san ta Hamma… kwanaki ma ta je birni amma kwanan nan ta dawo.. yanzu haka ma yau dinnan za’a daura mata aure da Alhaji Buba….”4 Zuciyar MK ce ta buga a dalilin jin kalaman yaron… Cike da tsananin tashi hankali yace “what??? aure???”2 Gani nayi ya buga seat da qarfi yace “hey stop the car” Bashir ya tsayar da mota yayinda na ga MK ya bude qofa ya fita. Gaba daya hankalin shi ne a tashe yayinda na ga yana ta shafa kan shi da hannuwa biyu yayinda yake ta kai da komowa. Gaba dayan su suka fito yayinda Bashir yace “Sir.. it’s possible ba ita bace”3 Usman ne ya fiddo hoton Ummi ya nuna ma Atiku yace “ka tabbatar wannan ce??” Atiku wanda yake kallon hoton Ummi ne yace “aradu Ummu Aimaana ce… yau auren..” Bai qarasa magana ba ne MK ya juyo tare da pointing at yaron alamar yana warning dinshi yace “hey just shut up… it’s not possible…” STORY CONTINUES BELOW Tuni idanuwan shi sunyi ja yayinda su Bashir suka hango tsananin damuwa da rudewa a tare da shi. A yanzu dai sun qarasa tabbatar da how important yarinyar take a wurin shi- even from the huge amount of money he has spent on the search they could tell that she is precious to him. Shi dai Atiku bai ma gane abinda MK ya fadi ba amma dai tabbas ya san baya son jin zancen auren Ummi ne. Bashir ne yace “Sir yanzu meye abun yi??” MK wanda yake ta kai da komowa sossai zuciyar shi take tafasa.. gani nayi ya dawo kusa da Atiku ya dafa shi yace “a ina ne za’a daura auren??” Atiku yace “A masallacin Malam Modibbo ne.. bayan sallan juma’a” Gani nayi MK ya kalli agogon hannun shi yayinda na ji yace “mu je ka kai mu masallacin” Usman ne yace “Sir me zaka yi??” MK wanda ya bude qofar mota zai shiga ne yace “i am stopping the wedding ofcourse… I am taking her back with me”2 Da kyau Hamma..7 ♧♧♧♧♧♧♧♧ A lokacin da suka iso masallacin Malam Modibbo kuwa sun tarar ana ta huduba yayinda mutane suke ta yin alwala suna haramar shiga masallacin. A dalilin daurin auren da za’ayi ne yasa masallacin ya cika fiye da kowacce juma’a. Tunda suka iso kuwa jikin MK yayi mugun sanyi. Zuciyar shi kuwa kamar zata faso qirjinshi. Qafafuwan shi ma kamar bazasu dauke shi ba. A yanzu dai da za’a auna jinin shi toh fa tabbas ya hau. Da qyar yayi composing kanshi sannan ya janyo Atiku yace “mu je ka nuna mun mahaifin Ummi..” Atiku ne yace “Hamma ba fa mahaifinta bane.. Baffanta ne.. asali ai iyayenta sun rasu” Nan take na ga MK ya runtse idanuwa ya bude yayinda ya qara tausaya mata… wato ma marainiya ce kenan… A haka suka shiga harabar masallacin yayinda aka dinga bin MK da kallo. Wasu ma har nuna shi suke yi. Daga ganin yanayin shi sun tabbatar dan birni ne.. MK dai sanye yake cikin wani tsadadden farin yadi wanda ya sha dinkin zamani. Kayan sun bala’in yi mishi kyau.. Dukda kuwa a hargitse yake yayi masifar kyau. Hular tashi ma can ya baro ta cikin mota. A lokacin da suka qaraso wurin Baffa ne Atiku ya nuna ma MK shi sannan ya matsa gefe. Baffa yana tsaye tare da wadansu mutane wadanda da alama suna cikin masu arzikin qauyen domin kuwa daga yanayin shigar da suka yi zaka tabbatar da hakan. MK wanda ya qarasa wurin su ne yayi sallama sannan ya duqa har qasa ya gaishe su. Ko da suka amsa gaisuwar Baffa yace “yaro daga ina kuma???” Kai tsaye MK yace “daga Abuja… Sunana Muhammad Kabir Sodangi. Dama na zo ne akan maganar Ummi..” Cike da mamaki Baffa ya kalli dattijon da yake gefen shi sannan yace “ka zo daurin aurenta kenan??” Zuciyar MK ce ta buga yayinda yace “a’a Baffa.. na zo ne in hana auren..”6 Gaba dayan su suka cika da mamaki yayinda na ji wasu suna ta salati.2 Dattijon da yake gefen Baffa ne yace “kana da hankali kuwa??? ya za’ayi kazo ka ce zaka hana aure….” Yayi wani murmushin takaici sannan ya cigaba da fadin “….idan ka ga ba’a yi aure na da Ummi ba toh mutuwa ce ta shiga tsakani..”3 A razane MK ya kalli dattijon wanda a shekaru zai kai saba’in.. wai shine zai auri Ummi.. the girl that is barely seventeen years.. shi kanshi da yake just thirty yana gani tayi mishi qanqanta idan ma ace shine zai aurenta sai wannan?? STORY CONTINUES BELOW Cikin sanyin murya ya kalli Baffa yace “don Allah Baffa kar kayi ma yarinyar nan aure.. kar ka aura mata dattijo mai shekaru kamar wannan.. a gani na ai Ummi bata isa aure ba…” Baffa ne yace “haba yaro.. ai mu anan ‘yar shekara goma sha hudu ma munyi mata aure balle Ummi wadda take goma sha bakwai a yanzu..” Dattijon ne yayi saurin fadin “idan banda zancen banza irin naka ma kana nufin duk kudade na da na kashe zasu tashi a banza?? ai auren nan kamar anyi shi an gama don haka kawai ka koma inda ka fito”3 Basu ankara ba suka ji MK yace “idan aka biya ka kudaden da ka kashe zaka haqura ka qyale ta??” Gaba dayan su suka sa mishi idanuwa cike da mamaki. A yanzu kuwa an zagaye su yayinda ake ta sauraron badaqalar da ake yi. Gaba daya qauyen babu mai arzikin Alhaji Buba. A yanzu haka matan shi uku ne.. yana so ya cike da Ummi. Alhaji Buba dai yaran shi ashirin da uku a yanzu haka. Yana da gonaki dayawa sannan yana da shanu tuli.. Har motoci yake da su wadanda ake haya da su a garuruwa. Babu Wanda bai San cewar Alhaji Buba babban Dan iska bane a qauyen amma saboda arziki da Allah yayi mishi babu mai iya aibanta halinshi a gaban shi saidai a bayan idon shi. Alhaji Buba babban mashayin giya ne.. baya kyautata ma matan shi da yaran shi. Arziki gareshi amma kuma Iyalin shi basu morar arzikin. kullum suna cikin tsiya. Tun dawowar Ummi da ya ji labari ne ya nace ma Baffa akan ya bashi auren ta. Daada ce ta ziga shi ya amince ya bashi Ummi… A yanzu haka duk qauyen babu yarinyar da aka yi ma gata wurin aure irin Ummi.. Qatuwar gona da shanu dayawa Alhaji Buba ya ba Baffa a dalilin Ummi…3 Alhaji Buba wanda yake kallon MK ne yace “toh wai kai a tunanin ka don ka fito daga garin Abuja kai wani mai arziki ne??? a tunanin ka zaka iya biyan dukiyar da na kashe akan Umm Aimaan??” MK ya matsa kusa da Alhaji Buba yace “ka fadi mun kudin da ka kashe… ni nayi maka alqawarin zan biya ka”3 Shi dai Alhaji Buba ya sani sarai duka abinda ya kashe basu wuce miliyan daya da dubu dari biyu ba amma ganin cewar MK yayi challenging dinshi ne yace “na kashe sama da miliyan biyu…” Tun kafin ya rufe baki MK yace “zan tura maka miliyan uku…” Aikuwa daga nan mutane suka dinga mamaki yayinda suka yi ta maimaita zancen. wasu ma fadi suke yi qarya ne.. MK bazai iya biya ba. Shi dai Alhaji Buba hakan yayi mishi daidai.. rashin auren yarinyar ma yayi mishi amfani tunda gashi har riba ya samu. Kai tsaye ya kalli Baffa yace “toh Malam.. ni ina gani na haqura da ‘yar ka.. ” Ji nayi ya juya yana neman limamin masallacin yayinda na ji yace “ina Malam Modibbo sai a shaida mishi an fasa daurin auren” Gani nayi MK ya sauke ajiyar zuciya yayinda ya dinga hamdala. Alhaji Buba kuwa ya kalli MK yace “toh yanzu yaro ta ina za’a turo mun kudin nawa??” MK yace “kana da account na banki?? idan kana da shi ka bani lambobin yanzu zan kira accountant dina sai ya tura maka” Aikuwa nan da nan ya fiddo wayar shi ya bude sannan ya miqa ma MK. Suna kallon MK ya fiddo wayar shi ya kira accountant dinshi sannan yayi mishi bayanin komai. Dayake cikin harshen turanci yayi maganar basu gane me ya fada ba har ya gama. Bayan ya kashe wayar ne ya kalli Alhaji Buba yace “yanzu zaka ga kudin ka Alhaji” yayinda Alhaji Buba ya dinga washe baki. Shi dai Baffa yana nan tsaye yayi shiru yana ta sauraron abinda yake wakana yayinda ya cika da tsananin mamaki. Yau Ummi ce ake kashe miliyoyin kudi akanta??? Bai ankara ba ya ji MK yace “Baffa akwai alfarmar da nake nema a wurinka akan Ummi..” Daga nan kuwa kowa yayi shiru suna sauraron abinda zai fadi. Ji suka yi yace “ina so ka bani Ummi in tafi da ita..” Gaba daya suka zaro idanuwa yayinda Baffa yace “yaro ka tafi da ita na baka…”5 Malam Lawali wanda ya kasance makwabcin Baffa ne yace “haba dai.. ya zaka fadi irin wannan maganar?? dayake Ummi ba ‘yar ka bace shiyasa zaka ce ka bada ita? haka kawai bamu san komai akan wannan yaro ba.. babu dangin iya balle na uba sai ka fadi haka?? da ‘yar ka ce Binto ai bazaka fadi hakan ba…”3 Malam Lawali ya cigaba da fadin “….a wannan zamanin bazamu dauki ‘yarmu mu baka ita ba haka nan.. tunda dama auren ta za’a yi da Alhaji Buba kuma an fasa zaka iya maye gurbin shi…”8 Ya kalli sauran mutanen da suke wurin yace “ko ba haka ba ne??” Gaba daya aka dinga girgiza kai yayinda suke fadin haka ne. Ya kalli MK wanda ya zama so confused yace “Kai yaro idan dai dagaske kana so ka tafi da ita gaskiya saidai a matsayin matar ka yadda mun san cewar aurar da ita akayi sannan sai mun tabbatar da kai din waye ne… don haka a yanzu shawara ya rage naka. Zaka aure ta???”2 Zuciyar MK ce ta buga yayinda ya shiga tsananin tashin hankali.. Ya auri Ummi??? how?? idan ya tafi da ita ya ce ma su Abba me?? Idan kuma ya tafi ya barta anan din ya rayuwar shi zata kasance babu ita??? aure zasu yi mata kamar yadda suka yi niyyar aurar da ita a yanzu.. shin ya rayuwarta zata kasance??? Kiran sallah suka ji wanda hakan ya sa aka fara shigewa masallaci yayinda suka bar MK nan tsaye cikin tsananin tashin hankali. Shi kuwa Alhaji Buba tunda ya ji alert ya juya ya fita daga masallacin cike da murna. Sallar ma fasa yin ta yayi.6 Ka ji mutumin banza🤣MADUGU ROCKVIEW HOTELS JIMETA Kwance yake ruf da ciki a kan gadon dakinshi yayinda yayi zurfi a tunani. MK dai kusan awa biyu kenan da ya dawo daga qauyen su Ummi. A yadda yake kwance zaka yi tunanin bacci yake yi amma sam ba haka bane… asali dai tunani ne mai yawa ya cika mishi qwalwa. A hankali na ga ya tashi zaune yayinda ya dafa kanshi. Idanuwan shi sun yi jajawur yayinda yayi looking so confused and disorganized. Ji nayi yace “MK what have you done???”2 ●●●●● MK dai bayan an idar da sallan Juma’a ne ya samu Baffa ya sanar da shi ya amince zai auri Ummi. MK dai ya yanke wannan shawara ba tare da yayi tunani mai zurfi ba domin kuwa ya sani sarai idan yayi tunani mai zurfi he might end up losing her which is not an option… losing Ummi will be like losing his life!!3 A nan kuwa aka nemi sanin ko shi din waye.. Ko da MK ya sanar da su waye mahaifin shi wadanda suke yawan shiga birni sun gane domin kuwa babu garin da babu gidajen man Alhaji Muhammad Sodangi. A wannan lokacin kuwa jikin Baffa yayi mugun sanyi… ya fahimci cewar lallai yarinyar ta fita daga sahun talakawa har duniya ta nade, ya tabbatar yau idan ya kai zancen wurin Daada toh fa lallai babu sauran kwanciyar hankali… toh meyasa???4 A haka dai aka daura auren Muhammad Kabir Sodangi da Ummu Aimaan akan sadaki naira dubu dari wanda Bashir da Usman suka zama shaida a bangaren MK din.11 Sossai mutane wadanda suka San halin da Ummi take ciki a gidan Baffanta suka yi mata murnar samun sassauci. A haka kuwa aka dinga bin su da addu’o’i na fatan alkhairi. STORY CONTINUES BELOW Har aka gama wannan daurin auren kuwa hankalin MK a tashe yake domin kuwa ya san he has gotten himself into serious trouble..3 ●●●●● Gani nayi ya koma ya kwanta yayinda na ji yace “me zan ce ma su Abba??? and Maleeka?? Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un…”11 Wayar shi ce tayi ringing wadda tun dazu take ringing din amma ya kasa dagawa. Miqar da hannu yayi ya janyo ta sannan ya duba. Sunan abokin shi ya gani. Ko da yayi answering ya kai kunnen shi ji yayi Fahad yace “haba ango.. ina ta kiranka inyi maka congrats kayi banza da ni…” Muryar MK qasa-qasa yace “abokina I am in a serious trouble… na tafka babban kuskure a rayuwa ta, wallahi ban san abinda nayi ba… I just.. I didn’t know what I was thinking da har nace a daura mun aure da UMMI, for crying out loud I already have a wife, ya zanyi da mata har biyu?? again me zan ce ma Abba?? nayi aure without their permission???…”7 Fahad wanda yake sauraron abokin shi ya sani sarai akwai matsala but then he needs to calm him down don haka ne yayi gyaran murya yace “Hey abokina listen to me.. what you did was not at all a mistake, we both know cewar you have a thing for this girl. Kai da kanka ka sani cewar bazaka taba iya barin UMMI a wannan qauyen ka dawo ba, ka sani cewar yarinyar tana affecting rayuwarka, ka sani cewar you cant do anything without her… and you know why??? because a rayuwar nan UMMI itace SOULMATE dinka. Na sani cewar there will be problem with your family and Maleeka but trust me, rashin UMMI a kusa da kai is a more serious problem for you kuma ka sani… you made the right choice and I assure you komai will fall into place with time..”11 MK wanda yake sauraron abokin nashi ne ya saki ajiyar zuciya sannan yace “but abokina…” Fahad ya dakatar da shi yace “but what MK?? I have a question for you” Yace “go ahead..” Fahad yace “deep down within you kayi regretting abinda kayi yau??” MK ya dan yi shiru sannan yace “No my friend but UMMI is just a small girl.. she is just seventeen.. ta ya zan yi zaman aure da…” Ji yayi Fahad ya fashe da dariya yayinda yace “bar wannan zancen abokina… kai ne kake gani kamar qaramar yarinya ce but trust me UMMI is old enough to do duk wani abinda matar aure zata yi a dakin mijinta.. itace perfect for you kuma na tabbatar maka zata kula da kai fiye da yadda kake tunani… just bring her home my friend”13 Ajiyar zuciya MK ya saki yayinda ya girgiza kai yace “toh abokina.. thanks alot for this, what would I have done without you a rayuwar nan…” Fahad wanda yayi dariya yace “wallahi da nasan za’a yi daurin auren ka da na biyo ka… my only best friend got married and I wasn’t in attendance?? damn!!!” MK yayi murmushi yace “ai abokina I swear har aka gama daurin auren ban san me ke faruwa ba…” Fahad yana ta kwasar dariya yace “ai su Bashir sun bani labarin yadda aka yi… but hey, ka dai ga amaryar taka ko??” Shafa kanshi yayi yace “wallahi ban gan ta ba..” Gani nayi ya kalli agogo ya ga qarfe biyar da rabi na yamma yayinda ya cigaba da fadin “….duk a rude nake abokina.. but anjima zan je in gan ta. I think ma gobe zan dauko ta because bana son zaman ta a qauyen nan…” Daga nan dai suka cigaba da hirar su yayinda Fahad ya cigaba da qarfafa mishi qwarin gwiwa akan auren Ummi da yayi. ♧♧♧♧♧♧♧♧ RUGANGE VILLAGE ADAMAWA Tsaye take a tsakar gida riqe da dorina yayinda take ta zane yarinyar tana masifa. Ita kuwa tana qunshe cikin hijabinta yayinda take ta kuka. STORY CONTINUES BELOW Tunda Baffa ya dawo ya sanar da Daada abinda ya faru a masallaci ne ta dinga zabga masifa da bala’i iri-iri. Gaba daya baqin da suka zo yinin biki ta kore su. Qawar Ummi mai suna Murjanatu da ta zo mata haka itama aka kore ta. Hatta qatuwar tukunyar da aka dora bisa wuta an sauke ta. Baffa ne zaune a bisa tabarma yayinda ran shi yake a bace. Ji nayi Daada tana fadin “shegiya mayya.. ya za’ayi ina ji ina gani ki tafi birni a matsayin matar wani hamshaqin mai arzikin sannan Binto tana nan… Ai wallahi dole ne za’a warware wannan auren..”5 ●●●●● Ummi dai tun satin da ya gabata da aka sanar da ita zancen aurenta da Alhaji Buba ne ta shiga tsananin tashin hankali… gashi dama tunda ta dawo qauyen su take fama da wani mugun zazzabi.. dayake wurin Goggonta ta zauna a lokacin sai ta kai ta chemist. da su Baffa suka dauko ta daga wurin Goggonta kuwa a dalilin azaba da take sha a wurin su ne zazzabin ya qara rufe ta gashi ko kula ta ba’a yi ba balle a bata magani… Sai kwana uku da suka wuce ne da goggonta ta zo gidan da qarfi da yaji ta fitar da ita ta mayar da ita chemist din qauyen aka yi mata allurai wadanda har yau ma bata gama karbar su ba. A yau dinnan kuwa bata san hawa ba bata san sauka ba sai ji tayi Daada ta fiddo ta daga daki tana ta dukanta.. Ga baqin cikin an aurar da ita zuwa ga mutumin da yayi qaurin suna wurin iskanci a qauyen sannan kuma ga zafin duka da na zazzabin da yake jikinta. Daga maganganun da Daada take yi ta fahimci lallai an daura mata aure amma fa ba da Alhaji Buba ba… toh da waye aka hada ta wanda take ta jin haushi haka??? abinda basu gane ba shine gaba daya auren ne bata so.. da sun sani sun qyale ta a haka.. ●●●●● Cikin kuka Ummi tace “don Allah Daada kiyi haquri.. ki taimaka mun a warware auren don wallahi ni auren ne ma bana so…”2 Kafin ta rufe bakinta kuwa Daada ta qara zabga mata wani dukan yayinda tace “qarya kike yi munafuka.. dama kin sani sarai cewar zai zo ya aure ki din.. shima din don dai bai san ko ke wacece bace shiyasa… da ya san cewar uwarki mayya ce ai da bazai yarda ya hada zuri’a da ke ba…” Ta juya ta kalli Baffa tace “duk laifin ka ne wallahi… akan wanne dalili zaka bari ayi wannan mummunar aika-aikar??” Baffa wanda yake zaune with no expression a fuskar shi ne yace “toh ya zanyi Saratu?? abu ne da aka yi shi a bainar jama’a.. Ga Malam Lawali da yayi tsaye..”1 Tsaki ta ja sannan ta juyo ta qara zabga ma Ummi dorina yayinda tace “aikuwa zan ga yadda za’a yi ya tafi da ita…” Sallamar Goggo suka ji wadda ta shigo gidan a fusace. tun tana qofar gida take ta jin hayaniyar Daada. Aikuwa Ummi tana jin muryarta ta miqe a guje ta nufi wurinta tana kuka yayinda ta rungume ta. Ran Goggo a bace ganin yadda jini ke zuba a goshin Ummi ta kalli Baffa wanda yake zaune a bisa tabarma sannan tace “duk wanda ya ci amanar maraya wallahi Allah bazai bar shi ba… abinda kayi ma yarinyar nan tun rasuwar iyayenta sai Allah ya saka mata. A yau Ummi ta tashi daga qarqashin ikon ku tunda har kun aurar da ita don haka tafiya zanyi da ita… idan mijin nata ya zo zai je wurina in bashi ita…” Gani nayi ta ja Ummi wadda take ta kuka zata fita da ita yayinda Daada tayi saurin tare su tace “ai wallahi babu inda zaki je da ita..” Ta juyo ta kalli Baffa tace “kai kuma bazaka sa baki ba??” Baffa wanda ya taso jiki a sanyaye yace “Aminatu ba tun yau ba nayi miki iyaka da wannan yarinyar.. yarinyar nan dai diyar qani na ce uwa daya uba daya don haka babu ruwan ki da duk wani abinda ya shafe ta” STORY CONTINUES BELOW Goggo tayi murmushin takaici tace “haka ne Bello.. dukda ba uwa daya muke da ku ba ai uban mu daya don haka Ummi diya ta ce.. a da kuna da iko da ita amma a yanzu baku da shi tunda kuka sallamar da ita don haka ku bani wuri in tafi da ita tun kafin rayukan ku su baci”2 Daada kuwa tana ta cika tana batsewa ne tace “aikuwa sai dai su baci…”2 Bata kammala maganarta ba ne suka ji Goggo tace “Lado!! kuna ina??” Aikuwa gani nayi wasu majiya qarfi sun shigo suna fadin “gamu nan Goggo” Lado dai tare da abokin shi Bilya suka shigo. Daada dai ganin su Lado sai ta ja baya domin kuwa ta sani sarai Lado yana da mugun qarfi… shi ba dan rigima bane amma irin yaran nan ne masu kare duk wani mai gaskiya a qauyen… idan dai kai marar gaskiya ne yanzu sai su ci uban ka. Lado kuwa a gidan Goggo ya tashi don haka tamkar uwa take a wurin shi.3 A haka kuwa suna ji suna gani Goggo ta janye Ummi suka bar gidan yayinda su Lado suka rufa musu baya. Bayan sun fita kuwa Daada ta fashe da kuka tana ta masifa yayinda take ta zagin Baffa akan shi ya janyo musu abinda yake faruwa.2 Goggo kuwa suna fita daga gidan tace ma su Lado su zauna a nan qofar gidan su jira lokacin da angon Ummi zai zo don su kawo shi gida.2 A haka ta wuce da Ummi Chemist don a duba lafiyarta. Haka kuwa aka dinga kallon su ana mamakin yarinyar da aka daura ma aure yau itace har an fito da ita. wasu kuma ganin halin da take ciki ne suka dinga tausaya mata yayinda aka dinga zagin su Baffa domin kuwa yawanci an san irin zaman wahala da take yi a gidan. Ayyah…2 ♧♧♧♧♧♧♧♧ Da daddare wuraren qarfe takwas tana kwance a kan katifar dakin Goggo tana bacci. Goggo tana zaune a gefenta tana ta kallon ta yayinda take ta tausaya ma yarinyar. Lado ne yayi sallama ya shigo dakin yace “Goggo ga angon Ummi nan mun qaraso da shi..” Tace “toh madallah. Yana ina??” Yace “yana cikin mota a waje” Ta miqe yayinda suka fito tare tace “kace da shi ya shigo” Goggo tana nan tsaye ne ta jiyo sallamar MK wanda ya shigo gidan. Dayake dai gidan Goggo akwai wutar lantarki, tsakar gidan akwai haske. Ko da ta amsa sallamar qarasowa yayi kusa da ita ya duqa har qasa ya gaishe ta. Cike da fara’a ta amsa. Ji nayi tace “au.. ashe ma angon namu yaro ne.. toh ai ni nayi zaton dattijo ne.. ya sunan ka??” MK yana murmushi yace “Muhammad Kabir” Goggo tace “toh masha Allah Kabiru… bisimillah shigo ciki. Amaryar taka ma bacci take yi.. bata dade da ta samu baccin ba” Shi kam MK tunda ya ji ance ‘amaryar shi’ duk sai ya ji wani iri. wai yau shine harda mata biyu.2 hahahahaha… Ji yayi Goggo tana fadin “shigo” Ajiyar zuciya ya saki sannan ya miqe ya shiga. Gani nayi ya tsaya cak yayinda zuciyar shi ta buga a dalilin hango fuskarta da yayi. Fuskar yarinyar da ta rikita mishi qwalwa a cikin ‘yan kwanakin da bai ganta ba, yarinyar da ta sanya dukkanin harkokin shi suka tsaya cak a dalilin rashin ganinta, yarinyar da ta fi mishi ko wacce halitta kyau a fadin duniyan nan, yarinyar da take da muryar da ta fi mishi ta kowa dadi a duk fadin duniyan nan, yarinyar da ya tabbatar idan babu ita a kusa da shi toh fa rayuwar shi tana cikin garari… Yarinyar da yake ji zai iya yin fada da kowa akan ta… ya tabbatar bazai iya rayuwa babu ita ba… his SOULMATE, his WIFE.. his UMMI!!12 STORY CONTINUES BELOW Qunshe take a cikin hijabinta tana ta bacci yayinda fuskarta tayi ja alamar ta ci kuka sannan ga plaster din da aka sa mata a goshi inda Daada ta ji mata ciwo. Goggo wadda take ta faman gyara mishi wurin zama gani tayi ya nufi wurin Ummi da sauri ya tsugunna a gabanta cike da tsananin damuwa yayinda ya dan dafa goshinta.. Da sauri ya juyo yace “me ya same ta?? a ina ta ji wannan ciwon?? faduwa tayi??” Goggo dai sossai ta ji dadin ganin yadda MK ya damu matuqa da halin da Ummi take ciki. ita kam ta tabbatar zai kula da ita fiye da yadda suke tsammani. Gyaran murya tayi sannan tace “kar ka damu ba wani ciwo bane babba…” Muryar Ummi suka jiyo cikin bacci tana fadin “Hamma… Hamma… Hamma don Allah kace musu bana son auren nan.. su qyale ni…” tana maganar yayinda hawaye ke bin fuskarta. Da sauri MK ya riqe hannun ta tare da bubbugawa alamar lallashi yace “hey relax…” A gigice ta bude idanuwanta ta sauke su akan MK wanda shima kallonta yake yi. Gani nayi ta qyafta idanuwan ta alamar tana so ta tabbatar da wanda ta gani a gaban ta.1 Hamma??!!! Da sauri ta tashi zaune yayinda zuciyarta take ta bugawa. Basu ankara ba sai suka ji ta fashe da kuka. Har yanzu yana nan riqe da hannun ta yayinda na ji tana fadin “Hamma ashe dama zan sake ganinka a rayuwa ta?? ya akayi ka zo?? don Allah Hamma ka fadi musu bana son auren da suka yi mun, sun hada ni aure da wani wanda ban san shi ba.. mutuwa zanyi a gidan..” Ji tayi yace “Ssssshhhh… Ummi stop. Ni ne mijin da suka aura miki…”1 A firgice ta zaro idanuwanta tare da qwace hannunta daga nashi tace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un… Hamma me kace??” MK dai wani tsananin tashin hankali ya gani a fuskar yarinyar wanda kuwa ya san dalili. tsoron Maleeka!!1 Kamo hannunta ya sake yi sannan yace “Ni ne mijin ki Ummi..” Aikuwa ji suka yi ta fashe da sabon kuka yayinda suka ji tana fadin “na shiga uku ni Umm Aimana.. Hamma meyasa ka bari suka daura mana aure?? wallahi Adda zata kashe ni…” Da sauri ta qwace hannunta ta koma wurin Goggo ta rungume ta tana kuka yayinda tace “Goggo don Allah ki ce ya sake ni.. bazan bi shi ba don wallahi matar shi zata kashe ni..” MK dai dafe kai yayi cike da tsananin damuwa. Bai yi mamakin reaction din Ummi ba domin kuwa ya ga irin dukan da ta sha a wurin Maleeka. Shi kanshi ya sani sarai akwai case babba yana jiran su a Abuja… Maleeka and his parents!! Muryar Goggo ya ji tace “kamar ya zata kashe ki??” Anan kuwa ya ji muryar Ummi cikin kuka tana ba Goggo labarin abubuwan da suka faru da yadda Maleeka tayi mata duka ta dawo. Goggo wadda jikinta yayi sanyi ce tace “subhanalillah.. dama lokacin da kika dawo jikin ki duk ciwo ashe Mace ce tayi miki duka?? ashe dama qarya kika yi mun kika ce ‘yan fashi ne???” Dago kai tayi tana kallon MK wanda ya cika da tsananin damuwa tace “kai Kabiru ka san da hakan shine ka auri yarinyar nan?? a gaskiya…” Da sauri MK ya dakatar da Goggo tare da fadin “don Allah Goggo kiyi haquri… wallahi da ina nan duk hakan bazata faru ba.. A yanzu haka nayi miki alqawari zan kula da Ummi fiye da yadda zan kula da kai na, Bazan taba bari mummunan abu ya same ta ba Insha Allah… don Allah Goggo…” Ummi dai tana kwance a kan cinyar Goggo tana ta kuka. Kukan nata kuwa sossai yake qona ran MK. Ji nayi yace “Ummi don Allah ki daina kuka.. Insha Allah babu abinda zai faru.. Hamman ki zai kula da ke kin ji???” Ummi dai gaba daya ta ma daina sauraron MK.. kuka kawai take yi. Kusan tsawon awa daya MK da Goggo suna ta aikin lallashi wanda da qyar tayi shiru har bacci ya kwashe ta.. dayake dama a cikin alluran da akayi mata akwai ta bacci wadda Goggo ta sa akayi mata saboda ta sani cewar yarinyar zata iya samun matsala da bacci. Bayan Ummi tayi bacci ne Goggo ta kalli MK tace “Kabiru” MK wanda yake cikin damuwa yace “na’am Goggo” Tace “na sani cewar baka san ko wacece Ummi ba.. baka san komai akan Ummi ba. Zan baka labarin Ummi a yanzu sannan ina roqon ka alfarma akan ka dinga tuna wannan labarin da zan baka a koda yaushe ko Allah zai sa ka qwatar mata ‘yancin ta a duk lokacin da ka ga za’a cutar da ita…” ♧♧♧♧♧♧♧♧