DIYAM CHAPTER 15

DIYAM CHAPTER 15

Nabi bayansa da kallo ina jin kamar ya ciro tawa zuciyar ne ya tafi da ita. My chest felt empty kamar babu komai a cikinsa, ji nake kamar in bishi a baya da gudu in rungume shi kamar yadda naje yi sanda ina karama, ina son ya rungume ni nima kamar yadda ya taba yi min a gidan Alhaji Babba, but I couldn’t saboda akwai wata igiya data ke rataye a wuya na, igiyar auren Saghir.+ Bazan iya komawa palon ba saboda duk bana son kallon fuskokin su. Yes, Alhaji Babba ya cuce ni iyakacin karshen cuta amma kuma still yayan Baffa na ne, kuma va’a taba chanjawa tuwo suna, komai suka yi bazan taba cewa su ba iyayena bane ba. And there is wani satisfaction da ake samu a cikin forgiveness, wannan satisfaction din shi nake yi wa Sadauki kwadayin samu.3 Sai na juya na tafi gurin Maman Iman duk da dai ita kuma surutu ne da ita ni kuma a lokacin bana son magana. So nake inyi shiru inyi jinyar zuciya ta. Dan haka ina zuwa sai nace mata bana jin dadi ne ina so zan kwanta, sai kuwa ta bude min dakin yaranta, dakin mu ni da Asma’u a da. Na shiga na kwanta, but sai dakin ya cigaba da dawo min da memories din da. Sadauki’s memories, na sake gwada kiran wayarsa still bata shiga. Dai na kifa kaina a pillow na fara kuka. It really hurt to love someone so deep while you are married to another, another din kuma wanda ba ka so.2 Sai da akayi magrib Maman Iman ta shigo ta tashe ni in yi sallah. Ayi alwala nayi sallah sannan na koma part din Inna, ina shiga na tarar sun tafi, Inna ta bini da kallo tace “kuka kikayi ko?” Na girgiza mata kai amma sai hawaye suka fito. Tace “me yasa kika masa magana dazu? Ba nace miki ki fita daga maganar ba? Tunda ke kince kin yafe shi ki barsa ya karbi abinsa. Na gaya musu nace Asma’u ma tace bata bari ba”. Ranar sunday, da safe muna shirye shiryen komawa gida ni da Subay’a kamar daga sama sai jin sallamar Sadauki nayi a tsakar gida. Na dakata da folding kayan da nake yi naji Inna tana amsa masa da yake tana tsakar gida ni ina palo, naji ya gaishe ta ta amsa tana tayi masa sannu da zuwa tace ya shigo palo, yana daga labule muka hada ido sai yayi sauri ya saki labulen ya koma yana cewa “basai na shiga ba Inna, dama zan dan shiga dakin Ummah ne” sai Inna ta kira saka mayafinta da kanta ta shiga gurin Maman iman ta gaya mata za’a wuce, saboda sai an bi ta nan za’a karasa dakin Ummah. Subay’a dake kusa dani ta tashi ta leka tsakar gida, sai naji yace mata “Subis, come here” sai ta makale a bayan kofa taki fita, yace “ba zaki zo ba? Dan kin ganni baki babanki kuma fari ko?” Sai inna ta dawo ta tarar dasu tayi dariya tace “Subay’a kizo ki gaishe da babanki mana?” Subay’a ta tura baki tace “ba baba na bane ba” inna tace “ji fitsararriya?” Yayi dariya yace “gado tayi ai” sai Asma’u ta shigo, tana ganinsa ta kama murna tana gaishe shi, yace “yar asama yammata” a raina nace “wato yana iya yiwa kowa magana faran faran, ni ce dai na koma aljana a gurin sa”. Asma’u ce ta raka shi ya bude dakin Ummah ya shiga, sannan ta dawo. Inna ta shigo tana kallona tace “kina jin Sadauki ba zaki fita ki gaishe shi ba?” Nace “baya son ganina inna. ganina a dakin ne fa yasa ya fasa shigowa”. Inna tayi shiru kawai bata ce min komai ba ni kuwa zafin da nake ji a raina yasa na dauki kayan na koma cikin daki, amma sai na kasa cigaba da gyarawa na kwanta kawai. Ina kwancen ya dawo, ya leko yayi wa Inna sallama sai ta ce yazo tana son magana dashi. Ya shigo palon ya zauna tace “Sadauki. Ni dai kam bansan wanne kalamai wanda yayi laifi irin wanda nayi maka zai yi amfani dashi gurin rokon gafarar wanda yayi wa lafin ba. Na cutar da kai Sadauki iyakacin cutarwa kuma duk a bisa son zuciyata ba wai dan kayi min wani laifi ba. Amma a karshe sai ya kasance ni din dai nice a wahale. In kace ma ba zaka yafe min ba Sadauki bazan ji haushi ba saboda na cancanci koma menene zakayi min. Amma abinda na sani shine nayi nadama, Sadauki dan Allah….” Sai ya dakatar da ita yace “Inna na yafe miki ai, da ban yafe miki ba Inna ba zaki ganni a dakin nan ba. Maganar ta wuce tsakanin mu har abada” sai Inna ta kama yi masa godiya, har ya sake mikewa zai fita sai ta kira Asma’u, sai kawai zuciyata ta raya min in leka su, naje ta jikin labule ina lekawa sai naga ta kamo hannun Asma’u ta saka a cikin na Sadauki tace “na hana ka auren Diyam a lokacin da kiyayyar ka ta rufe min ido, amma yanzu ga Asma’u na baka, duk abinda yayi Diyam shi yayi Asma’u har kamanninsu iri daya ne, ina fatan zaka karba kuma wannan zai wanke maka zuciyarka”9 Na juya ina dafe kirjina kamar mai kokarin gana zuciyata fadowa kasa. Idanuwana kamar zasu baro mazauninsu ina girgiza kaina a hankali ina cewa “no, no, no” amma sai naga Sadauki yayi murmushi, sai ya cire hannun Asma’u daga nasa ya mayar wa da inna yace “Inna na gode da wannan babbar kyauta da kika yi min, kuma da gaske wannan kyautar ta wanke min zuciyata sosai amma kiyi hakuri bazan iya karba ba. Zuciyata Diyam take so ba kamannin Diyam ko asalinta ba, in na karbi Asma’u banyi mata adalci ba saboda zan tilasta mata zama dani alhalin zuciyata bata tare da ita. Kiyi hakuri idan ban kyauta miki ba amma hakan shine zaifi mana alkhairi a gani na”.1 Na saki labulen na zauna a gurin ina juya lamarin a kaina. He refused Asma’u, sweet teenage Asma’u, yana claiming that his heart belongs to me, how can that be? Bayan ni kuma I belong to someone else? Sai yamma muka koma gida, daga nan kuma muka cigaba da lonely rayuwar mu nida Subay’a. Duk da ina kokarin ganin na rage tunanin Sadauki amma kullum tamkar kara min shi akeyi. Two weeks after that akazo aka raba gidan Alhaji Babba. Aka ja katanga tun daga part dinsa har zuwa bakin gate, sai ya kasance part din nasa da filin compound din dayake gaban part din har zuwa dakin maigadi da gate din gidan duk na sadauki ne. Main house din kuma da sauran abinda ya rage na compound shi kuma na Alhaji Babba, amma ko gate basu dashi dan haka sai katanga suka fasa ake shiga gidan, ko kudin da za’a sayi kofa a saka babu.2 Ba’ayi sati dayin haka ba dakunan Alhaji Babba suka zama dakunan kaji, Sadauki ya cika katon palon Alhaji da kuma two bedrooms dinsa da kajin gidan gona, broilers da layers. Compound din kuma akayi katuwar rumfa aka zuba raguna da tinkiyoyi, dakin maigadi kuma ya saka masu kular masa dasu.6 Alhaji Babba kuma ya koma cikin gida, dakin da Inna ta zauna nan ya dawo da zama. Washegarin da aka zuba dabbobin da sassafe murja ta kira ni “Diyam wallahi yau bamuyi bacci ba a gidan nan. Yadda muka ga rana haka muka ga dare wallahi, ragunan nan tun magrib suka fara koke koke har garin Allah ya waye sannan kuma kaji suka dauki nasu suma. Ni dai gidan ki zan taho in taya ki zama kafin hamma ya dawo ya kore ni” nace ta taho babu komai. Sai kuma naji babu dadi a raina. Murya, Hajiya Yalwati da sauran yayan Alhaji Babba basuyi wa Sadauki komai ba amma har dasu ake paying. Isn’t Sadauki taking this too far? Bayan gudun daukan alhakin wanda baiji ba bai kuma gani ba? Da dare Sadauki yaje gidan mu. Ya gaishe da Inna sai yace da Asma’u. “Yar Asama kina son gidan gona?” Tace “gidan gona kuma hamma?” Sai ya ajiye mata takardu yace “gashi nan na baki kyauta. Duk karshen wata za’ake kayo miki kudin da aka samu a ciki” Asma’u sai murna da tsalle, yayinda Inna ta saki baki ta kasa magana.2 Yana tafiya Asma’u ta kira ni tana son bani labari amma maganar ta kasa fitowa dan murna. Nace “kinga ki nutsu ki fada min, me ya faru?” Tace “hamma Sadauki ya bani kyautar gidan gonar sa da yayi a gidan Alhaji Babba” cikin mamaki nace “what?” Sai ta mikawa Inna tayi min confirming maganar. Har da sunan ta da komai a jikin takardun. Na kira shi da niyyar yi masa godiya amma shiru wayar bata shiga kamar kullum. Nayi tsaki na yar da wayar feeling very frustrated sai kuma na dawo na sake dauka na tura masa message “ina yiwa Asma’u godiyar kyautar da aka yi mata. Allah ya kara arziki mai albarka” na tura sannan na zauna rike da wayar a hannu ina jiran reply. Can sai gashi ya shigo. Three words “You are welcome”. Nayi tsaki ina jin haushin sa, amma bansan dalilin da yasa nake jin haushin nasa ba.Murja tazo gidan muka zauna tare da ita, da yake ta gama makaranta kuma tun tuni ana ta zaune gida ba’a cigaba da karatu ba, ita tafi son tayi aure ma. Tace “wallahi Diyam na gaji, na gaji da zaman gidan nan wallahi. Gafa samarin nan ina dasu, kuma duk wanda nacewa ya turo a cikin su wallahi fitowa zaiyi amma Alhaji shiru har yanzu yaki yace wani abu, kuma maganar sa daya wai wasu kudi yake jira su zo kuma duk munsan babu wasu kudin da zasu zo fa. Ni so nake in bawa umman mu shawara duk ace da samarin mu su fito, in yaso kowa kudin auren ta da kuma kudin sadakin ta sai a hada ayi mata kayan daki yadda ya sawwaka kawai. Ai ba sai an kashe mana kudi ba mu auren mu ke so kawai” na jinjina maganar nace “amma biki fa? Gara fa?” Tace “wannan kuma mijin ki zaki yiwa magana dan Allah ya rage matsolancin sa yayi mana. Kudin yadin da yake sawa a jikin sa kadai ya isa ayi abincin biki da shi” nayi dariya nace “kai murja, hadda sharri kuma?” Tace “wallahi ba sharri bane ba kayan da yake sakawa ko sanda Alhaji yana da kudi baya saka irin su. Amma ya bar alhajin da yar shara”.+ Sanda Saghir yaji labarin abinda Sadauki yayi a gidan su ya kira ni ya zazzage min bala’i. Bance masa komai ba har ya gama sannan nace “ni dai bani na kar zomon ba, ni ratayar ma ba’a bani ba, ka bari in ka dawo sai kaje ka neme shi kayi masa masifar, but I doubt in zaka samu ganin sa dan kasan manyan mutane ba kowa suke bari ya gansu ba” ina fadar haka na kashe, yayi ta kira naki dauka dan nasan cigaba zamuyi daga inda muka tsaya. Tun ana gobe zai dawo yakira yagaya min “ke yanzu ko dan I miss You din nan ma baki iya gayawa mijin ki ba. Kinga ni kuma har da tsaraba na siyo miki. Ina fatan dai kin tana de ni saboda da kishin ruwan ki zan dawo” sai naji ma abin ya bani dariya nace “duk wanda ka gama samu anan bai ishe ka ba? Mai zakayi da yar mitsitsiyar Diyam?” Bai musa ba yace “naki special ne. Da gaske nayi missing dinki fa” sai na kashe kawai. A raina ina jin inama yayi zamansa a can kar ya dawo? Banyi niyyar yi masa komai na dawowa ba amma dai sai na daure nayi masa girki, wainar shinkafa na miyar taushe da taji tantakwashi. Na hada masa lemom kankana. Sanda zasu taso ya kira wai zai turo friend dinsa ya kaimu airport ni da Subay’a mu taro shi, nace ni aiki nake yi sai dai suje da Subay’a. Na shirya ta kuwa suka tafi, nima nayi wanka na shafa mai kamar kullum na saka normal kayana na gida nayi kwanciya ta a kan gado. Ina jinsu suka zo, kawai naji wani bacin rai ya sauko min nayi tsaki na gyara kwanciya ta. An jima kadan Subay’a ta shigo tana ta tsalle. Mommy ki zo Daddy ya dawo, ya siyo min kaya da jirgi da mota” nace “kice kin gode, sannan kice masa ga abinci nan a dining” ta fita na koma nayi kwanciya ta. Sai gasu nan sun dawo tare, na tashi zaune ina kallonsa shima yana kallona, ya kara fari har da kumatu yayi alamar ya huta sosai, yace “shikenan? Babu oyoyo mijin ki yayi tafiya for two months amma ko dan welcome back hug ba zai samu ba?” Nace “na dafa maka abinci, nace maka sannu da zuwa sai menene kuma?” Ya saki hannun Subay’a ya hawo kan gadon sai nayi sauyi na sauka na fita na bar musu dakin. Na tarar da lodin kayansa a palo, na dauka na kai masa dakinsa na tarar yana shirin wanka, na dauko abincin da nayi masa na kawo palon sama na ajiye sannan na koma kasa muka zuba ni da murja muna ci tace “ke ba zaki tafi gurin mijin ki ba ya dawo daga tafiya? Ke ana neman mijin ke kina wulakanta naki?” “Humm” kawai nace mata sai ga kira kuwa Subay’a tana yi min inzo inji Daddy. Yana zaune a kujera ya hade rai “ki zo ki zuba min abincin tunda ba zakiyi min wankan ba” bance komai ba na zuba masa na kawo table gabansa na ajiye masa. Yace “wai ke ciwon rashin magana ne ya same ki? Na fi so ina fada kina mayar min yafi dadi” nace “ba ciwon rashin magana bane ba, ƴata ce ta girma shi yasa nake shiru a gaban ta” yayi dariya yana kallon Subay’a data zauna ta zuba mana ido. Na juya zan koma kasa sai ji nayi yace “kai! Matar nan wani duwawu naga kina yi fa” nayi saurin kallon Subay’a naga tana dariya sai kawai na girgiza kai na tafi.1 Muna kasan Subay’a ta jawo wani karamin akwati da kyar, murja ta tashi ta taimaka mata suka sauko dashi tana cewa “Mommy kinga kayan da Daddy ya siyo min” tana ta bubbuda wa, kayan sawa ne masu kyau da takalma, sai toys, murja tana ta yabawa, sai kuma Subay’a ta koma sama da gudu sai gata da karamar travelling bag mai kyau ta kawo min. “Inji Daddy, wai irin kayan da turawa suke sakawa ne ya siyo miki kema kike sakawa. Ki koma irin su” na bata rai nace “to sarkin surutu” na karba na ajiye, murja ta dan dake ni tace “tashi zaki yi kije kiyi godiya sosai” na mike na tafi amma sai nayi kwana na shiga dakina nayi kwanciya ta. STORY CONTINUES BELOW Sai bayan magrib ya shigo dakin yana kallona ina ninke sallaya yace “zan fita, zan tafi zance” na dauke kaina nace “ba gidan Alhaji ya kamata kaje ba? Ka gaishe su kuma kaga abinda aka yiwa gidan?” Sai kawai naga yayi murmushi yace “au kishi kike dan zanje zance ko?” Na zauna a bakin gado nace “Saghir, na riga na gaya maka tun kafin kayi tafiyar nan ni ko mata goma zaka aura ba zanyi kishin ka ba. Ni da son samu nane ma hudu nake so kayi, yadda zaka bani takarda ta in kara gaba” ya karasa shigowa yana cewa “wato kin ganshi ko? Alhaji ya tura ki kin ganshi ko? To bara kiji, in shi yake zuga kima ki gaya masa, auren ki yanzu na fara. In kinga na rabu dake to mutuwa nayi” ya juya ya fita. Ranar da wuri na yiwa murja sallama na hau sama tana tsokana ta “wato miji yazo shine zaki tafi turaka ko?” Nayi dariya kawai na tafi, na shirya Subay’a na kwantar da ita sannan nima na shirya na rufe kofa ta nasa key nayi kwanciya ta. Cikin bacci naji karar wayata, na dauka na ga Saghir ne sai na saka ta a silent na juya na cigaba da bacci na, sai kuma naji shi yazo yana knocking, ko kallon kofar banyi ba har ya gaji yayi tafiyar sa. Da sassafe ya bar gidan, a raina nace “Allah ya raka taki gona”. Da yamma sai ga Mama tazo, ni na dauka zuwa tayi gani na sai da naji ta kama yi min fada sannan na fahimci Saghir ne ya kai kara ta. “Diyam me kike nema wa kanki? Kin manta abinda annabi ya fada cewa mata sunfi yawa a wuta? Kuma mafi yawansu sun shige ta ne sakamakon rashin bin aure? Abinda kike so kenan? Wuta kike so ki kai kanki? To wallahi ki nutsu kiyi wa kanki fada. Ganin Sadauki ya dawo ne zaki kuma dorawa kanki kulafucinsa ko? So kike a lahira shi Sadaukin da kike yi saboda shi idan ya aikata aiyukan alkhairi ya kasance a aljanna ke kuma kina wuta saboda shi?” Nace “Mama ni ba dan Sadauki bane ba, Sadaukin da ko kula ni baya yi?” Tace “to ya zaiyi ya kula ki? Matar aure ce fa ke. Ke ai har yanzu ba hankali ne ya ishe ki ba shi kuwa da hankalinsa. Saghir yace shi yana sonki, yana son zama dake, me yasa ke ba zaki so shi ba? Shima Sadaukin nan fa dole watarana aure zaiyi, yadda yake da kudin nan ma sai ki ga ya auri hudu a rana daya. In haka ta faru kuma ya zakiyi?. Sai dare Saghir ya dawo gida. Yana shigowa palo murja ta gaishe shi ya hade rai yace “ki shirya gobe ki koma gida” tace to sai ya wuce sama. Murja ta kalleni pleadingly, ni kuma na daga mata kafada. Kamar bazan tashi ba musamman ganin ko kallon inda nake baiyi ba kuma dai sai na tashi na bi bayansa. Ina shiga dakinsa naga yana kokarin cire kaya sai na kama masa ya cire nayi hanging rigar sai yace “Mama tazo gidan nan kenan” na rike kugu nace “tunda ka kai kara ta ba dole tazo ba?” Ya zagayo hannayensa a waist dina yace “naga kina neman ki kaini lahira ne shi yasa na nemo taimakon gaggawa” ya shafa fuskata yace “you really are beautiful” na ture hannunsa nace “bararojin kuma?” Sai yayi dariya yace “wai baki manta ba, ai bararoji suna da kyau so it was a compliment” ya saka fuskarsa a cikin gashina yana shakar kamshinsa yace “tell me duk abinda kike so inyi miki” nace “ka bar murja ta cigaba da zama a gidan nan” yace “done. Sai kuma me?” Nayi shiru, yace yana zuge zip din rigata “ba zaki ce in fasa aure ba? Say it and it will be done” na sake shiru na rufe idona ina jin daci a bakina yace “kice ‘hamma Saghir Please kar kayi min kishiya” bance komai ba ya daga ni ya dora akan gado, hawaye ya fara bin fuskata yace “kice hamma Saghir ina sonka” nayi shiru sai yayi ajjiyar zuciya yana hawowa gadon yace “watarana zaki fada, ina nan ina jira”. Ina kallon sa yana ta shirye shiryen sa, ni ko su inna ban gayawa zancen auren sa ba sai da suka ji daga gidan Alhaji Babba, Hajiya ta kira ni a waya “yanzu Diyam da gaske Saghir auren nan zaiyi? Shi yanzu kudin da zai kashe gurin auren ya bawa Alhaji su mana ko shago ya bude ya fara dan kasuwanci. Yanzu kina ganin kofar gidan nan ma da kyar Saghir ya saka ta shi ko a jikinsa ma wannan cin mutuncin da akayi wa gidan nan” “sai hakuri Hajiya” shine kawai abinda nace mata.2 Har dani akaje aka kai lefe, aka saka rana akayi komai aka fara hidimar biki. Kowa sai mamaki na yake yi wai ni ko a jikina mijina zaiyi aure. Shi kuma Saghir kullum sai ya ce ince masa ya fasa aure ni kuma naki fada. Sai yayi fushi ya daina yi min magana sai kuma dan kansa ya sauko. Sadauki kuma bai kuma bi ta kaina ba, sai dai yakanje ya gaida Inna, kudin gidan gona kuwa account ya bude wa Asma’u ake zuba mata a ciki sai dai kawai su dauko suyi amfani da abinsu”. Satin bikin Saghir yana kamawa Hajiya ta kirani tace ita fa babu wani taro da zata yi, ni kuma sai nace zanyi walima ranar kawo amarya anan gidan Saghir, yadda kowa yazo in an kawo amarya sai ya ganta. Saghir yana ji ya fara fadan wai za’a bata masa gida. Ranar kafi suka zo suna ta daddaga hanci, na saka murja ta nuna musu spare dakin da yake sama suka ce “dama yace ba sai anyi mata komai ba ya saka komai a gidan, gadon ma da cewa yayi kar ayi mune muka ce sai anyi saboda kar a mata gori”. Ina jinsu suna gulmar “wannan yar karamar yarinyar ce uwargida?”. Aka daura aure Saturday, Sunday kuma aka kawo amarya. Duk yan uwa sunzo walimar dana shirya, anci ansha sai kuma aka karbi amarya. Ni dai ina dakina basu kawo ta ba nima banje ba har aka gama kowa ya watse. Na shirya Subay’a nima na shirya muka yi kwanciyar mu sai na jiyo hayaniyar maza a waje, ni na manta ma ashe ana siyan baki. Sukayi ta hayaniyar su suka gama suka tafi ninina ta karanta novel din da Rumaisa ta turo min kafin ta tafi, sai ga Saghir ya shigo dakin. Ya hawo kan gadon ya karbi wayar daga hannuna yace “uwargida ran gida” sai abin ya bani dariya ma, yace “ki fito kiga amaryar ki. In ba kyason ta kuma kinyi alkawarin kula dani yadda ya kamata a yau zata koma gidan su” na mike ina saka hijab nace “ta sha zamanta. Tunda ba’a kaina zata zauna ba ni kuwa ina ruwana da ita?” Sai na wuce na barshi a nan. Ina shiga palo na ganta a xaune tana kallon kofar dakina. But unlike abinda Saghir yace na cewa nafita komai ni sai naga kamar ta fini komai except kyawun fuska. Ta fini shekaru, daga gani ta fini ilimin boko, ta fini girman jiki dan duk abubuwan da Saghir yake yawan complain cewa bani dasu ita tana dasu sosai. Tasha heavy make up da wani uban attach har gadon baya. Rigarta kusan rabin kirjinta a waje, na tambayi kaina “a haka akayi siyan bakin?” Na zauna nace “sannu amarya” ta kalleni tana yamutsa fuska tace “yauwa, sannu” Saghir ya shigo ya zauna a kusa da ita, kamar jira take yi sai ta dora kanta a kafadarsa hannunta kuma a kirjinsa. Nayi murmushi ina kallonsu, yace “Halima ga Fauziyya, Fauziyya ga Halima” ya kama jawabin zaman lafiya, baya son hayaniya waye da waye ya gama sai yace “to yanzu amarya zata gama kwana bakwai dinta da musulunci ya bata a matsayin ta na budurwa, daga nan sai kuma ayi maganar rabon kwana. Sai dariya taso kubce min na rufe baki na juya fuska, yace “kina da magana ne, Diyam?” Na girgiza kai, yace “no ki fadi abinda yake ranki, naga kamar kina dariya” nace “kawai dai naji kace budurwa ne, ni kuma da na ganta na dauka bazawara ce” sai tayi sauri ta mike zaune sosai tace “excuse me? Shi da zai aure ni bai gaya miki budurwa zai aura ko bazawara ba?” Nace “ba muyi wannan maganar dashi ba kuma to be frank bani da problem da koma wacece, Allah ya bada zaman lafiya, aci sati daya lafiya, sannan akan sati dayan na kara muku shekara daya kyauta from me to you” sai na mike nace “Allah ya bamu alkhairi”.1 Ina shiga daki yana shigowa shima, ya jawo ni tace “what? What was that? Wacce maganar banza naji kinyi a gurin can?” Nace “kyauta nayi maka ko ba ka so? Ji nake mai kula da kai a gado kake nema kuma gashi ka samu, ko shekarar tayi kadan ne in kara muku wata?” Sai na kwace jikina nace “and don’t touch me kasan ba kwana na bane yau” na haye gado naja bargo. Ya tsaya yana kallona sai yace “yanzu har tsanar da kika yi min ta kai haka? To shikenan, saki kike nema na sani kuma ba zaki samu ba. Naji, Fauziyya zata kula da gado na amma duk abinda ya danganci aikin gida ke zaki ke yi, wanke wanke, shara, girki da komai” na gyara kwanciya nace “done. Shekara ta nawa ina wanke wanke da shara da girkin? Dan dai karin kwano daya ai ba zai gagare ni ba”. Na rufe ido nace “in zaka fita dan kashe mana fitila Please”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *