UMMI CHAPTER 10
MK ne yayi parking a gaban Boutique din yayinda ya fita ya zagaya ya bude mata qofa.+ Sai a wannan lokacin ne Ummi ta dago kanta ta kalli inda suke. Tunda suka baro qauyen su take ta buga game a wayar shi… ita dai sossai take son game. Gani nayi ta fito daga motar ta tsaya. Bayan ya rufe ne ya janyo hannunta suka shiga boutique din. Boutique din dai ba wani babba bane amma babu laifi akwai kaya masu kyan gaske.. Ummi dai tunda suka shiga take ta kalle-kalle. Daya daga cikin sales reps din shagon ce ta qaraso wurin su tace “you are welcome sir..” Yace “thanks… beautiful stuff for my beautiful queen please”6 Matar tayi murmushi sannan tace “this way sir.. what would you like…” Yana riqe da hannun Ummi suka fara zagaye yayinda yake fadi ma matar abinda suke so. Da farko dai layin dogayen riguna suka je… Jallabiyoyi, maxi long dresses, material gowns masu kyan gaske da sauran su.. Matar ta dinga ciro kaya masu kyau yayinda MK ya dinga zabar ma Ummi. Duk wanda ya tambayeta ko yayi sai tace ‘yayi’ Da alama dai zabin MK shine zabinta.2 Bangaren takalma ma haka matar ta dinga ciro mata kala-kala amma fa duk flats domin kuwa Ummi bata son takalmi mai tsawo tunda dai bata taba sakawa ba. Da aka koma bangaren kayan bacci kuwa Ummi dai gani tayi ana ta ciro mata wasu sexy ones.. wasu ma kasa gane fasalin su tayi… A nan suka samu bambancin ra’ayi da MK domin kuwa duk wadda ya nuna sai tace bata so. MK kuwa ya gane dalilinta na rashin son su.. bai bi ta kanta ba ya cigaba da nuna sexy and beautiful ones yayinda matar ta dinga cirowa.. Ganin haka ne Ummi ta matsa kusa da shi tace “Hamma wadannan fa bana son su” Yana murmushi yace “toh Baby bari a hada miki da wadannan…” ya nuna wasu kayan bacci masu wando da top. Da suka koma wurin inner wears kuwa gani nayi Ummi ta dan bata rai yayinda ta tsaya daga nesa kadan. MK cike da tsokana yace “Baby zo ki zaba mana.. ko in zabo miki ne??” Ummi dai yi tayi kamar ma bata ji yana magana ba yayinda ta kauda kanta gefe daban. Matar ce ta fara fitar da wasu sexy bras da panties. MK yana kallon Ummi wadda take ta turo baki yayinda take wasu maganganu wanda bai gane ba domin kuwa cikin yaren fulani ne. Dariya yake son yi amma kuma ya matse. Gyaran murya yayi yace “Baby wadannan na hannunta sunyi kyau amma kuma kamar sunyi miki yawa ko??” Ummi ta dan dago kai ta ga wasu qananan bras da panties a hannun matan yayinda take mamaki wai yace sunyi mata yawa bayan kadan zasu yi mata. Yana kallon matar yace “smaller sizes madam..” yayinda ya kalli Ummi yace “bari ta dauko miki wanda basu kai wannan ba…” Da sauri tace “a’a Hamma… wannan din fa sunyi kadan” STORY CONTINUES BELOW Zaro idanuwa yayi yace “kadan fa kika ce… ki kalla da kyau fa..” Gani yayi ta nufi wurin different sizes din ta dauki wasu wadanda suka fi na hannun matar girma tace “wannan zasu yi mun..” Gani nayi MK yayi shiru yana kallonta a ranshi yana fadin “is she bigger than I thought???.”10 Nikuwa nace toh wa ya sani?? kullum tana qunshe cikin hijabi…🤣🤣 Bayan an hada musu kayan ya biya ne aka zuba musu a mota. Ko da ya zagayo zai bude mata qofar motar sai gani yayi ta qura ma wani wuri ido. Da ya kalla sai gani yayi shagon sayar da kayan wasan yara take kallo. Ji nayi yace “Baby yaya??” Murmushi tayi sannan ta dan matsa kusa da shi tare da pointing at glass din shagon tace “Hamma ka ga irin Babyn da nake wasa da shi a waya dinnan can… ashe dama akwai shi dagaske??” Yana dariya yace “teddy bear?? kina so ne??” Tace “eh Hamma..” Yace “mu je mu siya toh” A lokacin da suka shiga shagon kuma ko me ta gani sai tayi saurin riqe hannun shi tace “Hamma mu tafi kawai na fasa” Cike da mamaki yace “meyasa??” Ta dan turo baki tace “kamar fa na yara ne… ka ga shagon ma fa duk kayan wasan yara ne” MK dai dariya ta bashi sossai. Kafin yayi magana kuwa wata mata tace “welcome Sir…” Yana murmushi yace “thank you… a cute Teddy bear for my wife please..” Matar tana murmushi tace “this way sir…” Suna biye da matar ta kai su wurin teddy bears kala-kala. Ummi dai a guje ta nufi wurin wani qaton teddy bear ta dauka sannan ta juyo ta kalli MK tace “Hamma ina son wannan.. yayi kyau??” Yana murmushi yace “yayi kyau sossai Baby.. da wane kuma??” Tace “shi kadai nake so..” Yace “kin tabbata??” tace “eh Hamma” Daga nan suka dawo counter ya biya suka tafi. Ummi dai ko da suka shiga mota tana nan riqe da teddy din tana ta wasa da shi yayinda MK yake ta kallonta yana murmushi. One thing is for sure.. Ummi is so special to him!! As long as she is close to him toh fa he is very much okay!!3 Sai da ya biya Cherry-Blossom ice cream spot ya siyo mata ice cream sannan suka wuce hotel din da ya sauka ♧♧♧♧♧♧♧♧ MADUGU ROCKVIEW HOTELS JIMETA A lokacin da suka iso masu aikin hotel din ne suka kwaso kayan Ummi suka kai musu har dakin MK. Ita dai Ummi tana riqe da teddy bear dinta har suka iso dakin. Ko da suka shiga gani yayi ta tsaya a bakin qofa yayinda take kallon shi. In a confused state tace “Hamma ni ina daki na?” Yana murmushi yace “a wannan dakin zamu kwana Baby.. Gobe kuma sai mu tafi gida” Gani yayi ta bata rai kamar zata yi kuka yayinda ya girgiza kai ya nufi wurinta. Kan ta a duqe ta ji ya dafa kafadunta, hakan kuwa sai da ya haddasa mata faduwar gaba. Tuni jikinta ya fara rawa. Duqo da fuskar shi yayi saitin fuskar ta yace “Baby kwantar da hankalin ki… ni babu abinda zanyi miki kin ji??” Har yanzu ranta a bace ne yayinda ta ji ya cigaba da fadin “… ko bata yarda da Hamma bane??” STORY CONTINUES BELOW Da sauri ta dago idanuwan ta tana kallon shi. A yadda fuskar shi take daf da nata kuwa sai da ta ji tsikar jikinta sun tashi. Bata taba kallon fuskar shi this close ba sai yau. Sossai MK yake da kyau.. a yanzu ma gani tayi ya qara kyau sossai da sossai saidai ‘yar rama da ya dan yi. Shi kam ganin yadda ta sa mishi ido sai ya sa hannu ya ja kumatunta tare da fadin “wannan kallon fa?? ko so ake a gano muni na??” Murmushi tayi sannan tace “ai wallahi Hamma kai kyakyawa ne sossai… ni fa ban taba ganin mai kyan ka ba”3 Yana murmushi yace “hmmm…nagode Baby” Tana kallon shi tace “Hamma in tambaye ka??” Yace “go ahead..” Tace “na ga ka rame.. kayi ciwo ne bayan na tafi???” Kai tsaye yace “eh” Cike da damuwa tace “me ya faru?? kan ka ne yayi ciwo ko?? kayi aiki dayawa kenan Hamma… na gaya maka ka rage yin aiki dayawa..” MK dai sa mata idanuwa yayi yana ta kallonta yayinda take ta yi mishi masifa.. Yana murmushi ya kamo hannunta suka qarasa shiga dakin yayinda yace “kiyi haquri Babyn Hamma… zanyi qoqari in rage yin aiki dayawa” A ranshi kuwa yace “if only she knew I was down because of her…” Ya zaunar da ita a kan kujera ya dauko ice-cream ya miqa mata tare da fadin “ga mutumin ki nan..” Cike da murna ta karba tace “nagode Hamma…” Wayar shi ce tayi ringing ya duba ya ga sunan abokinshi Fahad. Yana murmushi yayi answering yayinda na ji yace “yes my friend… gata nan na dauko ta” Ya dan yi shiru sannan yace “I swear my mind is at ease.. having her close to me is just the only thing I want…” Yana kallon Ummi wadda take ta shan ice cream dinta ya cigaba da fadin “….thank you my friend” Yana dariya yace “toh bari in sa speakerphone… tana jin ka” Ummi wadda ta dago tana kallon MK ji tayi Fahad yace “Babyn Hamma shine kika gudu kika bar mu ko??” Tana murmushi tace “Hamma wallahi ba guduwa nayi ba… Adda ce ta kore ni” Yana dariya yace “toh aikuwa gashinan mun dawo da ke a matsayin amarya… ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya”3 Shiru tayi bata ce komai ba. MK yana kallonta yace “bazaki amsa ba?? bata son zama da Hamma kenan..” Da sauri tace “Ina so Hamma..” Fahad kuwa dariya ya dinga yi yayinda yace “my friend I am sure she loves you too…” Da sauri yace “hey shut up..” ya cire speakerphone din yayinda ya matsa nesa kadan da Ummi yace “how far.. su Abba sun kira ka?” Fahad yace “surprisingly no my friend..” MK ya saki ajiyar zuciya sannan yace “nima basu kira ni ba.. Chubby dai ta kira ni jiya” ya dan yi shiru sannan yace “hey do you think they found out??” A dayan bangaren ne Fahad yace “I dont think so abokina.. ai da sun gano da Hafsah ta fadi maka”1 Gani nayi MK ya shafa kanshi sannan yace “well, we are coming back tomorrow…” A haka dai suka cigaba da hirar su a waya yayinda Ummi take ta shan ice cream dinta. Bayan yayi sallama da abokin shi ne ya kashe wayar. STORY CONTINUES BELOW Gani yayi an kusa fara kiran sallan magrib don haka ne ya wuce dressing room don shirin shiga wanka. Ummi dai bayan ta gama shan ice cream dinta sai gani nayi ta miqe ta fara gyara dakin.1 Dakin ba wani kaca-kaca yayi ba sai wasu ‘yan abubuwa da basu ajiye a rightful place dinsu. A lokacin da ta dauki Brush din MK da yake kan gado ta juyo zata dora a kan Vanity mirror ne na ga ta sake shi a qasa yayinda tace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un…” MK wanda yake tsaye daure da towel a qugun shi cike da tsananin mamaki yace “Baby lafiya??” Da sauri ta juya yayinda zuciyarta take ta bugawa. Ummi dai gaba daya jikinta rawa yake yi. Bata taba ganin babban mutum half naked ba.10 🤣🤣🤣 Bata ankara ba ta ji ya dafa kafadun ta yace “hey.. lafiya?? me ya faru??” Idanuwanta a rufe yayinda muryarta take rawa tace “Hamma me yasa kake yawo babu riga a jikin ka??” Kallon jikin shi yayi sannan yayi murmushi tare da girgiza kai yace “toh Baby wanka nayi ai.. ba sai na shafa mai bane zan sa riga??” Kafin tayi magana ne ya ja ta ya zaunar da ita sannan yace “yi haquri toh… yanzu zan sa” Tana nan zaune yayinda idanuwan ta suke a rufe har ya gama shafa man sannan ya fesa sprays wanda nan da nan dakin ya fara qamshi… qamshin da take bala’in so. Dressing room ya shiga ya shirya cikin qananan kaya sannan ya fito. Ji tayi yace “Baby bude idanuwan ki na sa riga..” A hankali ta bude yayinda ta dan juyo ta kalle shi… Sossai yayi mata kyau, bata san lokacin da ta sa mishi idanuwa babu qyaftawa ba. Brush dinshi da ta yar ne ya duqa ya dauka yayinda ya tsaya gaban madubi yana brushing gashin shi. Har a wannan lokacin kallon shi take yi. Sossai MK yake birge ta.. kayan da ya sanya a yanzu kuwa tana bala’in son su domin kuwa kyau suke yi mishi.. Shi kam har ga Allah bai san ta sa mishi ido ba sai da ya juyo sannan ya ganta.. murmushi yayi yace “Baby kallon fa yayi yawa.. ko dai ban yi kyau bane??” Tana murmushi tace “Kayi kyau sossai Hamma.. ina son wannan kayan da ka sa” Yana murmushi ya nufi gefen gadon inda take zaune ya zauna kusa da ita. One thing he likes about the girl is tana fadin magana straight from her heart… daga dan zaman da yayi da ita ya fahimci cewar she is an open and direct person and he likes that personality.7 Tana wasa da yatsun hannuwanta ne ta ji yace “nagode Babyn Hamma.. tunda kina so zan dinga sa irin su don ki dinga gani kin ji??” Tana murmushi tace “toh Hamma nagode” Tashi yayi yace “bari in je Masallaci in dawo.. an kusa fara kiran sallah” Tana kallon shi ya fita yayinda ta sa hannuwan ta biyu ta rufe fuskarta tace “wallahi ina bala’in sonka Hamma..” Can kuma ta bata rai yayinda tace “yanzu idan muka koma Adda ta gan ni fa?”5 Shiru tayi ta koma tunani mai zurfi yayinda duk ta bi ta bani tausayi.1 Kiran sallah ne ya sa ta zabura ta miqe yayinda ta shiga bathroom don yin alwala.. ************** Bayan ta idar da sallah zama tayi ta cigaba da karanto haddan Qur’ani har aka kira Isha’I tayi. Tana idar da sallan Isha’i ne ta ji an qwanqwaso qofar dakin. Da sauri ta miqe ta nufi wurin qofar sannan tace “waye?” STORY CONTINUES BELOW A can bangaren dai ji tayi ance “room service ma’am..” Dan shiru tayi tana tunanin ta bude ko kar ta bude tunda dai bata san me mutumin yace ba.3 Tunani tayi qila wani saqo ne aka kawo ma MK don haka ne ta dan bude kadan ta leqo. Trolley ta gani dauke da kayan abinci a bisa. Mutumin ne yayi mata murmushi yayinda ta jiyo muryar MK a bayan shi yana fadin “Hey Joe.. is it what I ordered?” Yana murmushi yace “yes sir” Ummi dai komawa tayi yayinda mutumin ya tura trolley din ya jera kayan abincin a kan qaramin dinning table din da yake cikin dakin sannan yace “excuse me” MK yace “go ahead” Bayan Joe ya fita ne yace “Baby zo mu ci abinci..” Ummi ta taso ta qaraso wurin table din yayinda ta fara budewa zata zuba mishi. Ya zauna a kujera kenan wayar shi tayi ringing. Ko da ya duba sunan Usman ya gani.. bayan ya amsa ne na ji yace “kuna reception??” Ya dan yi shiru sannan yace “okay gani nan zuwa” Ummi wadda take qoqarin zuba mishi pounded yam ce tace “Hamma ina zaka je?? ga fa abincinka nan…” Murmushi yayi yace “zan ga su Bashir ne Baby.. yanzu zan dawo.. ki tabbatar kin fara ci kafin in zo kin ji??” Tace “toh Hamma” Bayan ya fita ne ta mayar ta rufe yayinda ta koma kan kujera ta dauki teddy dinta ta rungume. Wasa-wasa har qarfe goma saura bai dawo ba. Gani nayi ta tashi nufi wurin trolley din sabbin kayanta da suka siyo ta bude yayinda ta dan birkita ta dauki abubuwan da zata buqata sannan ta wuce bathroom. ************** Wuraren qarfe goma sha daya saura ne MK ya shigo dakin. A lokacin kuwa Ummi tana kwance bisa doguwar kujerar da take dakin rungume da teddy bear dinta tana bacci. Bayan ya ajiye ledar hannun shi ne na ga ya nufi wurinta ya tsugunna a gaban ta yana kallon fuskarta. Dukda ramewar da yarinyar tayi sossai tayi kyau.. A yanzu da take bacci sai tayi kama da barbie doll.. very young, innocent and beautiful. Gani nayi yana murmushi yayinda ya fiddo wayar shi yayi snapping dinta hotuna. kyakyawar fuskarta ya dan shafa wanda ya sanya ta bude idanuwanta a hankali ta gan shi. Murmushi tayi sannan tace “Hamma ka dawo?? ina ta jiranka har bacci ya kwashe ni..” Yana ta kallonta yayinda yake murmushi. Allah ma ya sani yana jin yarinyar nan a ran shi.. da bai gano ta ba ya tabbatar rayuwar shi bazata yi amfani ba. Ummi wadda ta kula kamar bai ji ta bane ta tashi zaune tare da fadin “Hamma kana ji na kuwa??” Ya dan sosa kan shi sannan yace “Yes Baby.. uhmm.. kiyi haquri na dade ban dawo ba.. kin dai ci abinci ko??” Girgiza kai tayi alamar a’a yayinda tace “Hamma ya za’a yi in ci bayan kai baka ci ba..” Murmushi yayi yace “toh ba nace miki ki fara ci ba kafin in dawo?? anyways tashi mu je mu ci..” Ya kamo hannunta suka koma wurin table din yayinda ta zuba musu a plate daya kamar yadda ya umurce ta. Haka ya sa ta dinga bashi a baki sannan itama tana ci. Sossai ta saki jiki wurin cin abincin… da alama ta fara sabawa kenan!! Pepper soup na cat fish din ma haka ta dinga cire mishi qaya tana bashi.. haka dai har suka cinye yayinda ya kira room service ya zo ya kwashe kayan abincin. MK dai hana ta kwanciya yayi na dan lokaci saboda abincin da suka ci ya sauka. After a while ne ya miqe yace “toh Babyn Hamma tashi mu kwanta” Gani yayi ta miqe ta nufi kujera zata kwanta yayinda ya cafko hannunta yace “a kan gado zamu kwanta..” Zaro idanuwa tayi wanda kafin tayi magana yace “babu abinda zanyi miki… kwantar da hankalin ki” yayinda yayi mata murmushi. Jikinta a sanyaye ta nufi gefen gadon ta dan zauna yayinda shi kuma ya haye kan gadon ya kwanta… Zuciyarta ce take ta bugawa yayinda ta dan juyo ta kalle shi.. Ganin ita yake kallo ne tayi saurin kawar da kanta. Fashewa yayi da dariya cike da tsokana yace “Baby kwanta mana.. wannan Hijab din ma ai da kin cire shi!! wai ba kya jin zafi ne?” Da sauri tace “a’a Hamma…” MK dai juyawa yayi yana murmushi ya kashe wuta yayinda yace “toh sai da safe..” Ummi dai ta dade a zaune bisa gadon sannan ya ji ta qarasa hawa ta kwanta. Ya tabbatar she is not comfortable amma gwara hakan domin kuwa bazai bari ta kwana a kan kujera ba haka shima lafiyar shi qalau bazai kwana a bisa kujera ba..4 ************** Da asuba kiran sallan farko ne MK ya farka ya ji ta maqale a jikin shi kamar mage. Gashi ta shaqe mishi wuya.. Da sauri ya kunna bedside lamp… MK dai yayi mamaki sossai ganin yadda ta maqale mishi.. Kamar ba ita bace take ta tunanin yadda zata kwanta a kan gado daya tare da shi sai ga ta maqale da shi. Ya sani sarai Ummi bata san ta maqale a jikin shi haka ba. it looks as if she is scared of something… Murmushi kawai yayi yayinda ya dan ja kumatun ta yace “Baby me kike yi a nan??” A gigice ta bude idanuwan ta yayinda tayi qoqarin barin jikin shi amma yayi hugging dinta very tight. Zuciyarta ce take ta bugawa yayinda jikinta ke ta rawa.. the first time da ta zama so very close to namiji a rayuwarta. Gani nayi tana ta qoqarin qwacewa amma ta kasa. Muryar ta tana rawa tace “don Allah Hamma kayi haquri..” Yana kallon kyakyawar fuskar ta yayinda yake ta murmushi yace “idan kin fadi mun abinda kike yi a jikina zan qyale ki..” Tace “Hamma wallahi nima ban sani ba… kayi haquri bazan qara ba” Girgiza kai yayi sannan yace “toh shikenan Baby..” Ya sake ta yayinda ya tashi zaune yace “bari inyi shirin zuwa masallaci” Ya sauka daga kan gadon yayinda ya barta zaune tana ta kallon shi. Bayan ya shige bathroom ne ta saki ajiyar zuciya sannan tace “toh wai ni meyasa na maqale a jikin shi haka?? na shiga uku.. Yanzu shikenan zai dinga yi mun kallon ‘yar iska”7 kuma dai??🤣 ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Wuraren qarfe takwas da rabi na safe MK yana kwance a kan gado yana bacci.+ Ummi ce ta fito daga bathroom sanye cikin hijabi.. da alama dai wanka tayi amma fa ta sanya kayanta tun a cikin bathroom din. Zama tayi a kan kujerar Vanity mirror yayinda ta fara shafa mai. Hankalinta yayi nisa wurin duba turarukan da suke kan vanity table din da har bata san MK ya farka daga bacci ba.. Gani nayi ya natsu yana kallonta yayinda ya ga ta bude daya ta dan daga hijabinta ta fesa… Sossai take bashi dariya.. Ya sani sarai ta qi cire hijabi ne saboda kar ya ga jikinta. Ummi tana fesa wani turaren ne ta gan shi tsaye a bayanta… Zuciyarta ce ta buga yayinda ta zabura ta tashi tsaye. Da qyar ta ajiye kwalbar turaren a kan Vanity table din. Ba tare da yayi mata magana ba ya kamo hannuwanta ya hada ya riqe gam sannan ya sa dayan hannun shi zai cire hijabin da ke jikinta. Muryarta tana rawa tace “don Allah Hamma ka bari..” Aikuwa bata qarasa magana ba ya cire Hijabin.. Gani nayi MK ya zaro idanuwa yayinda ya dan matsa baya yana kallonta.. Ji nayi yace “Hasbunallahu wani’imal wakeel…”3 Ummi dai tunda ya zare hijabin ta runtse idanuwan ta yayinda jikinta yake ta rawa. MK dai wata kyakyawar hourglass shaped lady (ko kuma ince girl), fara sol ya gani a gaban shi.. Gashinta da ya warware kuwa ya sauka bayan ta sossai saboda bala’in tsawo… Is she this beautiful??? dama haka take??? Sanye take cikin wata doguwar riga wadda ta bi jikinta har qasa. Wannan rigar dai tana cikin rigunan da suka siya jiya… Rigar dai very simple amma kuma sossai take da kyau.. Babu tantama kuma jikin yarinyar ya qara ma rigar kyau. MK dai kasa dauke idanuwan shi yayi daga kanta.. Gaba daya ta tafi da hankalin shi. Bai taba ganin kyakyawan abu a duniyar nan ba kamar yarinyar da take tsaye a gaban shi. Ummi is just seventeen amma kuma take da beautiful body kamar wannan?? shi kam ko da wasa bai taba kawowa a ranshi cewar yarinyar ta cika haka ba.2 Ummi dai har yanzu idanuwanta a rufe yayinda duk ta bi ta takure. Ji take yi kamar tayi tsuntsuwa ta gudu daga dakin. Bata ankara bane ta ji ya janyo ta jikinshi ya rungume ta very tight yayinda suke jin bugun zuciyar juna.. A wannan lokacin kuwa daga ita har shi sossai suka shiga wani yanayi na daban… zuqatan su sun motsa sossai. Wani irin sanyi ne yake ratsa jikinsu musamman Ummi wadda hakan ya zama mata baqon al’amari. A yadda babu hijabi a jikinta ji tayi kamar tsirara take. Kwantar da kanshi yayi a kafadarta yayinda hannun shi ke cikin gashinta yana wasa da shi.. numfashi kawai yake ta saki. Gaba daya Ummi ta kasa motsi yayinda ta ji wasu abubuwa suna ta yawo a jikinta. Wannan shocking din da take ji a duk lokacin da ya taba ta kuwa ta ji shi babu iyaka… sai sakin numfashi takeyi itama. Bakinshi ya kai saitin kunnen ta yace “Baby you are extremely beautiful.. kina da kyau sossai..” Ummi dai bata ma san yana magana ba domin kuwa ta riga tayi nisa.. STORY CONTINUES BELOW Bata ankara ba ta ji ya fara tura ta baya wanda har ta jingina da bango. Ya duqo da fuskar shi saitin nata yayinda yayi tucking gashinta wanda yake neman rufe mata fuska a bayan kunnen ta. Idanuwanta a rufe yayinda jikinta ke ta rawa. Ji tayi yace “kiyi mun alqawari…” Muryarta tana rawa tace “wanne alqawari Hamma..” “cewar zaki daina sa mun Hijab a cikin gida..” Da sauri ta bude idanuwan ta tana kallon shi yayinda ta bata rai tace “toh ni fa bazan iya ba..” Kumatunta ya ja sannan yace “zaki iya baby… please” Gani nayi tayi shiru tana kallon shi yayinda shima yake kallon ta. Ita dai Ummi a duniyan nan babu abinda MK zai nema tayi mishi wanda bazata iya yi mishi ba.. dukda wannan din abu ne mai matuqar wahala a wurinta amma haka kawai ta ji dole ta daure ta yi mishi. Ji tayi yace “please Baby… please…”6 Murmushi ta dan yi tace “toh shikenan Hamma.. zan daina sakawa” Yayi murmushi yace “thats like a good girl.. thank you” Gani nayi ya dauko ledar da ya shigo da ita jiya ya miqa mata yace “ga sabuwar wayar ki…” Cike da murna ta karba sannan tace “Hamma nagode sossai” Gani nayi ta bude yayinda na hango kwalin iPhone 11 pro Nace da kyau MK1 Gashin da ya kwanta a gaban goshinta ne yake ta kallo wanda ya bashi sha’awa sossai. Gani nayi ya matsa yana shafa gashin yayinda yace “ina son wannan…” Tana murmushi tace “nagode Hamma…” Daga nan ya juya ya nufi hanyar bathroom yayinda ya barta tana ta murmushi. Ummi dai bala’in jin dadi take yi idan ta ji MK yace yana son wani abu nata.1 hmmmm… ************** Wuraren qarfe goma sha daya yana zaune a kan kujera yana duba wasu reports a Macbook dinshi yayinda Ummi take zaune a kan gado tana buga game a wayarta. MK dai motsi kadan sai ya dago kai ya kalle ta. wasu lokutta ma tare suke dagowa suna kallon juna wanda kuma sai suyi ma juna murmushi.3 Ummi dai ta kula kallon da yake yi mata har yayi yawa don haka ne tace “Hamma meyasa kake ta kallo na??” Yana murmushi yace “saboda kinyi kyau sossai Baby.. don Allah ki daina sa Hijab dinnan.. ina so in dinga kallon ki a haka..” Tana murmushi tace “dagaske bazan sa ba Hamma tunda baka so..” Ji nayi yace “zo ki zauna kusa da ni” Babu musu ta tashi ta fara dosowa wurinshi yayinda ya zuba mata idanuwa babu ko qyaftawa. Shi fa har yanzu mamaki yake yi wai Ummi ce haka… the girl he saw as a little girl.. the seventeen year old Ummi!! da alama dai Ummi ta ruda MK…3 The truth is Ummi tana da kyau… ta fi Maleeka kyau, Ummi fara ce… ta fi Maleeka haske, Ummi tana da dogon gashi… ta fi Maleeka dogon gashi, Ummi tana da qira mai kyau (the figure 8 kinda shape)… idan har Ummi bata fi Maleeka ba toh saidai su zo daya.6 Abinda Maleeka zata nuna ma Ummi bai wuce fannin wayewa ba, aji, ilimi (ilimin ma na zamani) da ‘yan abubuwan da baza’a rasa ba..5 the question is, are all of these significant to MK??1 STORY CONTINUES BELOW Kyautatawa tana daya daga cikin abubuwan da suka sanya Ummi ta shiga ran MK.. Ummi ta damu da MK sossai sabanin Maleeka wadda take nuna halin ko in kula da al’amuran shi.. Duk abinda MK yake so toh fa Ummi ma tana so… Sossai yake jin yarinyar a zuciyar shi. Farin cikin ta shine nashi, zaman ta kusa da shi shine kwanciyar hankalin shi. Bai taba kawowa ba a ranshi cewar abinda yake ji game da yarinyar a zuciyar shi SOYAYYA ce, A tunanin shi SO daya ne kuma ya riga ya ba Maleeka.3 Shin haka ne??3 Toh gashi kuma bazai taba iya rayuwa babu Ummi ba… Tabbas the girl sitting few inches away from him is his LIFE PARTNER, his SOULMATE.. idan ya rasa ta a rayuwar shi toh tabbas zai shiga uku. and you say it’s not love?? Wayar ta ce tayi ringing yayinda tayi saurin kallon shi tace “Hamma waye ke kirana??” Yana murmushi yace “Oho Baby.. ansa ki ji…” Tana answering kuwa ta jiyo muryar Goggonta. Cikin ihu tace “laaaa… Goggo ina kika samu waya??” Shiru ta dan yi yayinda take sauraron Goggo daga nan kuma ta juyo ta kalli MK tana murmushi tace “na ji dadi sossai Goggo.. Allah ya saka mishi da alkhairi” Kallonta kawai yake yi yayinda ta cika da murna.. Ya kula Ummi tends to appreciate every little thing no matter how small.. another one thing he likes about her amongst so many others!! Wayar shi ce tayi ringing shima, Ganin sunan Bashir ne ya tashi yayinda yayi answering. Ji nayi yace “ina zuwa” sannan ya kashe. Kallon Ummi yayi yace “bari in ga su Bashir in dawo” tace “toh Hamma” yayinda ta cigaba da hira da Goggo. **************** Da Yamma ne suka fara shirin komawa Abuja. Sosai hankalin Ummi yake a tashe domin kuwa idan ta tuno Maleeka sossai take shiga damuwa. Gaba daya jikinta yayi mugun sanyi. MK ya kula da hakan amma bai ce komai ba tunda shima hankalin nashi ba a kwance yake ba. hahahaha.. Abinda dai ya sani shine bazai qara bari a raba shi da yarinyar ba… yayi alqawari he is going to do everything possible to protect her. Zai yi qoqarin convincing iyayen shi akan suyi approving auren shi da yarinyar. Maleeka??5 Ya sani zai samu matsala da ita amma he will try his best to ensure cewar yayi settling differences din da ke tsakanin su. is it possible??? *********** Ummi tana tsaye a gaban Vanity mirror sanye cikin wata Jallabiya mai kyan gaske. Kusan minti Goma kenan tana qoqarin dunqule gashinta wanda ta kama da hair band ta kitsa jelar. Da ta dunqule shi kuwa sai ya kwance. ita dai Ummi ta saba idan ta daure gashinta bata wani dunqule shi tunda dama cikin hijabi ne. Gani nayi ta bata rai yayinda take wasu maganganu cikin yaren fulani. MK wanda ya fito daga dressing room ne ya tsaya yana kallonta tana ta masifa…. da alama wani abun ne ya bata mata rai. Da sauri ya nufi wurinta ya tsaya ta bayanta tare da dafa shoulder dinta yace “Baby ya kike magana ke kadai? me ya faru?” Cikin shagwaba tace “ni wallahi ban san ya zanyi ba.. ka ga idan na dunqule gashina sai ya kwance.. Da ace Hijab zan sa ba sai..” STORY CONTINUES BELOW Da sauri ta juyo ta fuskance shi tace “Don Allah Hamma ka bari in sa Hijabi tunda fita zamu yi” MK dai shiru yayi yayinda ya sa mata idanuwa yana ta kallonta.. Allah ya sani Ummi ta fi mishi komai kyau a duniyan nan. Ya shagala a kallonta ne ya ji tace “Hamma don Allah ka ji??” Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “juya” Cikin rashin fahimta ta juya yayinda take kallon fuskar shi ta mirror. Gani tayi ya kama gashin nata ya fara nadewa a tsakiyar kanta yayi shi in form of dough sannan yayi tucking edge din in such a way da bazai kwance ba. Bayan ya gama ne yana kallonta ta mirror yace “shikenan??” Tana murmushi tace “shikenan Hamma.. Nagode” Kumatun ta ya ja sannan yace “kinyi kyau sossai” Cike da jin dadi tace “nagode Hamma” Bayan sun gama shirin su tsab ne suka yi checking out of the hotel suka kama hanyar Airport. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧ YOLA AIRPORT JIMETA Bashir da Usman ne suka kawo su Airport din. Ko da suka iso da sauri Ummi ta kalli MK yayinda ta dan matsa kusa da shi cikin rada tace “Hamma jirgi zamu hau??” da alama dai bata so su Bashir su ji ne. Shima cikin rada yace mata “eh Baby..” Kai tsaye tace “ni fa ina tsoro… don Allah mu tafi a mota”1 Zaro idanuwa yayi yace “A mota??? Kai na fa zai yi ciwo..” Tun kafin ya qarasa maganar shi tace “shikenan Hamma mu je a jirgin” Murmushi yayi yace “kar ki damu wannan jirgin wanda zamu hau ba babba bane… kar ki ji tsoro” A sanyaye tace “toh Hamma” Bayan an zuba kayan su a Jet din MK ne ya shigar da Ummi har ciki sannan ya fito suna wani magana da su Bashir. Gani nayi ya miqa musu hannu sukayi musabaha yayinda suke murmushi. Daga nan kuma ya wuce ya shiga Jet din. A lokacin da MK ya shigo ya nemi Ummi bai ganta ba don haka ya shiga daya daga cikin rooms na jet din sai ganinta yayi tana ta bin abubuwa da kallo har tana taba wasu.. fuskarta kuwa yayi displaying tsananin mamaki hade da excitement.. Da alama dai interior na jet din ne ke bata mamaki at thesame time kuma ya birge ta.. Gyaran murya yayi wanda ya sanya ta juyo da sauri. Yana murmushi yace “Baby ya akayi… ko jirgin baya da kyau ne Hamma ya canza wani??” Cike da mamaki ta matso wurin shi tace “Hamma ka canza wani?? naka ne??” Girgiza kai kawai yayi alamar ‘eh’ Gani yayi ta bude baki cike da mamaki yayinda ta sa hannu ta rufe bakinta.. Yana dariya ya riqo hannunta suka fito yayinda na ji yace “zo mu zauna kafin jirgin ya tashi” Ganin su kadai ne tace “toh Hamma mu kadai zamu je?? ina sauran mutane?? ba ance mutane dayawa ne suke shiga jirgi ba??” Zaunar da ita yayi yayinda ya sa mata belt yace “wannan private jet sunan shi… ba na kasuwa bane. Daga ni sai ke sai kuma ma’aikatan jirgin…” Kafin ya rufe bakin shi ne tace “toh Hamma motar ka kuma anan zaka barta ko mutanen da suka kawo mu sune zasu kai maka Abuja??” STORY CONTINUES BELOW MK wanda ya zauna a gefen ta ne yace “nan za’a barta Baby.. na gama amfani da ita” Haka ta dinga yi mishi tambayoyi kala-kala yayinda yake ta bata amsa. Ya kula cewar Ummi is very Inquisitive.. she wants to know everything. if only she went to school she will no doubt be a very bright student. A lokacin da akayi notifying din shi cewar za’ayi take-off kuwa gani nayi ya kamo hannunta ya riqe gam don ya sani sarai zata iya rikicewa. Aikuwa abin mamaki bata wani rude ba… kawai dai ta yi shiru ne yayinda ta runtse idanuwan ta. Lokacin da jet din yayi settling a sama kuwa sai ta bude. Shi kam murmushi kawai yayi. Ya balle belt din seat din yayinda ya ja ta suka dinga zagaye jet din yana nuna mata interior din. Tambayoyi kuwa ya sha su… They had a good time a wannan lokacin.. sossai Ummi ta dinga bashi dariya da tambayoyin ta. Sossai MK yayi enjoying company din yarinyar. ♧♧♧♧♧♧♧♧ NNAMDI AZIKWE INTERNATIONAL AIRPORT ABUJA Fahad yana zaune a arrivals yana jiran su ne ya hango su sun shigo. Yana riqe da hannun ta yayinda suke magana da alama dai tambaya take yi mishi yayinda yake ta bata amsa. Wasu ma’aikata ne biye da su janye da akwatunan su. Fahad yana murmushi ya miqe ya qaraso wurin su yana fadin “Abokina sannun ku da zuwa…” Sukayi musabaha yayinda MK yace “my friend how are you??” Fahad yana murmushi yace “I am good..” Ya kalli Ummi wadda kanta yake a duqe tana murmushi yace “amarya babu gaisuwa?? ko ta manta Hamma Fahad ne??” Cikin ‘yar qaramar muryarta tace “ina wuni” Ya girgiza kai yana murmushi sannan ya kalli MK yace “lafiya lau… hope dai kina kula mun da abokina??” Ta dago kai ta kalli MK wanda shima ita yake kallo. Har yanzu yana nan riqe da hannunta. Murmushi tayi yayinda Fahad yace “abokina you look good.. kamar ba kai ba 3 days ago. I am glad you found her..” MK yana murmushi yace “and I am glad I brought her back… but I am scared!! Abba ain’t gonna take this lightly” Fahad yace “dont worry my friend everything will be okay insha Allah” Ya dan saci kallon Ummi yace “I see you have started to transform her already..” MK ya bugi kafadar shi yace “Fatima will do the rest abokina…” Yana murmushi yace “it will be an honour for us oga Sir..” Haka suka jera har wurin motar Fahad. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Suna kan hanya yayinda Ummi tayi shiru tana tunani.. jikinta ne yayi sanyi da ta tuno lokacin da Maleeka tayi mata duka ta kore ta. Yanzu gata nan ta dawo a matsayin kishiyarta…3 Ita dai ta tabbatar qarshen ta ne ya zo domin kuwa bazata taba manta munanan kalaman Maleeka ba.. dukda kuwa ba komai ta gane ba tunda akwai turanci a maganganun.. Gani nayi ta dago kai ta kalli side view din MK wanda yake zaune a gaba tare da abokinshi suna ta hira. Lumshe idanuwa tayi yayinda ta saki ajiyar zuciya… STORY CONTINUES BELOW Ita dai Allah ya sani tana bala’in son shi. a dalilin shi zata iya jure duk wani wulaqanci da zata fuskanta a rayuwarta… Unconditional love I suppose??!!2 Fahad ne yace “abokina where to?? Gidan ka na Maitama or Asokoro???” Kai tsaye MK yace “Asokoro my friend” Da sauri Fahad ya kalle shi yace “what?? your Babe’s house?? why???” Ya girgiza kai yana murmushi yayinda yace “haka kawai..” Fahad yace “but you know how dangerous this could be ko???” Yace “I know but the faster she accepts reality the better… kar ka damu I have everything under control”5 really???? ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Security ne ya bude gate din gidan, ya duqa har qasa yana miqa gaisuwa. As usual dai horn kawai Fahad yayi mishi yayinda ya qarasa har gaban porch din gidan yayi parking. Kamar ance ma MK ya juyo ya kalleta sai kawai gani yayi tana ta rusa kuka. Hankalin shi a tashe yace “subhanalillah” yayinda Fahad ya juyo da sauri ya ga Ummi tana kuka. Da sauri ya fito daga motar ya bude qofar baya ya shiga. Janyo ta yayi jikinshi ya rungume ta yana bubbuga bayanta yace “Meyasa Baby take kuka?” Cikin kukan tace “Hamma ni wallahi tsoro nake ji… Adda fa zata kashe ni idan” Da sauri ya rufe bakinta yayinda yace “Adda bazata kashe ki ba Babyna… kin ga ki daina jin tsoron kowa, tunda ina nan tare da ke babu abinda zai faru…” Fahad yana zaune yana ta kallon drama din su yana murmushi. Shi kam to him sai yanzu ne abokin shi yayi aure.. perfect match!! yanzu haka idan ka gan su yadda take kukan shagwaba yana lallashinta abun gwanin ban sha’awa. nikuwa nace ai dama kai dan adawar Leek ne!! A haka dai ya lallaba ta suka fito. Masu aikin gidan ne duk suka rufe motar suna ta kawo gaisuwa yayinda MK yake amsawa. Su dai sun ga Ummi amma sam basu gane ta ba.. basu gane ita ce mai aikin da Maleeka ta kora ba. Ya akayi basu gane ta ba??4 MK ne ya kalli abokinshi ta window yace “abokina thanks… zamuyi waya anjima” Fahad yace “okay” Ya kalli Ummi yace “toh amarya a huta lafiya..” Ummi dai bata ma ji me yake fadi ba domin kuwa hankalinta a tashe yake matuqa. *********** MK yana riqe da Ummi suka shiga gidan. As usual dai gidan shiru.. Zuciyar Ummi sai bugawa takeyi yayinda qafafuwanta suka yi mugun nauyi… ta tabbatar banda don MK da ya riqe ta da bazata iya yin tafiya ba. Matsoraciya🤣🤣5 Ganin ya ja ta hanyar wani sashe a kusa da na Maleeka ne tace “Hamma ina zamu je??” Kai tsaye yace “sashen da zaki zauna Baby..” Tsayawa tayi tace “don Allah ka bari in zauna a dakin da Adda ta bani lokacin…”4 Katse ta yayi tare da fadin “ssssshhhhhh… kin fi qarfin wannan dakin Baby… kin zama matar Hamma wanda yake ji da ke sossai don haka you deserve one of the best sections a gidan nan” Ita dai Allah ya sani a tsorace take.. sossai take jin tsoron Maleeka don kuwa bazata taba manta dukan da ta sha a wurinta ba. A haka dai MK ya ja Ummi zuwa sashen. Wannan sashen dai sossai ya hadu.. Yana dauke da falo daya da dakuna har uku don haka bai kai na Maleeka girma ba amma kuma komai is on point. Dakin da ya bata kuwa sossai ya tsaru.. babu abinda babu na jin dadi a cikin shi sannan ga girma da yake da shi. Da qyar MK ya lallabata ta amince zata zauna a sashen. Komawa yayi ya dauko trolley dinta wanda ke main falon qasa inda masu aiki suka ajiye. A lokacin da ya shigo mata da akwatin kuwa tana nan tsaye inda ya barta. Ko da ya ajiye qarasowa yayi wurin ta ya janyo ta jikin shi ya rungume yayinda ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “ko kin fi son dakin Hamma ne??? sai mu dinga kwana tare??” Da sauri ta girgiza kai tace “a’a wallahi Hamma… idan Adda ta kamani…” Fashewa yayi da dariya sannan ya sake ta yace “wasa nake baby.. huta abinki.. bari in je dakina inyi wanka in zo” Tace “toh Hamma” Aikuwa yana fita ta bi bayan shi ta sa key a qofar yayinda ta saki ajiyar zuciya. habawa🤣5 ♧♧♧♧♧♧♧♧ MK ne ya fito daga bathroom dinshi daure da towel a qugun shi yayinda yake goge kan shi da wani towel din. Wayar shi ce take ta ringing. Ko da ya duba sunan Hafsah ya gani. Jefar da towel din hannun shi yayi sannan yayi answering. Tun kafin yayi magana ne ya ji tace “Ya MK me ke faruwa ne na ji su Abba suna ta fada wai kayi aure???..” Zuciyar shi ce ta buga yayinda hankalin shi yayi mugun tashi… “…. tun dazu nake ta trying wayar ka bana samu… Ya Maleeka ma fa har suma tayi da ta ji zancen, yanzu haka tana gida.. wai dagaske ne kayi aure??? how?? as in why didn’t you tell us?? is it the girl???…”4 Hankalin MK a tashe yace “Hafsy it’s a long story.. I am on my way..” Bai jira tayi magana ba ya kashe wayar ya jefar da ita yayinda ya dafe kanshi wanda yayi mishi nauyi. Ji nayi yace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un… yanzu me zan ce ma su Abba??? how did they find out??”Baby open the door mana.. Hamma ne”+ Ummi wadda take zaune a gefen gadon dakin ce ta tashi ta nufi qofar ta bude. MK dai dukda tsananin tashin hankalin da yake ciki sai da ya tabbatar yayi composing kanshi kafin ya zo wurinta. Murmushi yayi yace “ke dama matsoraciya ce ashe?? meye na rufe qofa ki sa key??” Ummi wadda take tsaye a bakin qofar ce ta turo baki tace “toh Hamma ni fa dagaske bana so Adda ta gan ni..” Hannunta ya kamo ya janyo ta suka fito daga dakin tare yayinda yace “ki daina tsoro Baby.. babu abinda zata yi miki” Ya sagala hannun shi a kafadarta yayinda ya cigaba da fadin “ki ma kwantar da hankalinki.. Adda bata nan” Ajiyar zuciya ta saki yayinda tace “toh yaushe zata dawo??” Yace “nan da kwana biyu don haka ki cire damuwa a ranki kin ji??” Tace “toh Hamma” Yace “ni zan fita.. zan je gidan Abba in dawo” Zaro idanuwa tayi tace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. Hamma???”2 Cike da mamaki yace “Baby what??” Tace “sun sani cewar kayi aure?? Hamma ka tabbatar zasu bar ni in zauna a gidan nan?? ka ga fa Adda ‘yar uwarka ce kuma….” Bai ankara ba kawai sai ya ji ta shige jikin shi ta rungume shi very tight for the first time yayinda ta fashe da kuka. MK ma kasa magana yayi… gaba daya jikin shi yayi sanyi yayinda yake sauraron sautin kukan ta. Ji yayi tace “Hamma don Allah kar ka bari a qara raba mu… wallahi Hamma idan aka raba mu mutuwa zan yi…” Da sauri yace “Ssssshhhhh… Baby daina fadin wannan maganar… insha Allah babu wanda zai raba mu, bazan bari a raba mu ba saboda kina da muhimmanci sossai a rayuwa ta” Da qyar ya banbare ta daga jikin shi yayinda ya sa hannu ya share mata hawayen fuskarta yace “please ki daina kuka… bana so” Ya zaunar da ita yayinda yace “kiyi mun alqawari idan na fita bazaki yi kuka ba..” Tana kallon shi cikin ido tace “Hamma kai ma ka san zanyi… amma nayi maka alqawari bazan yi dayawa ba kuma zanyi addu’a akan Allah yasa su yarda… ka ga idan ma basu yarda ba kace musu zan zauna a matsayin ‘yar aiki, kawai dai su taimaka mun kar su raba mu..” MK dai dukda damuwar da take tattare da shi bai san lokacin da ya fashe da dariya ba. Gashin gaban goshinta da ya kwanta ne ya shafa yayinda yace “Ke Mata ta ce Ummi.. ni kuma mijin ki kuma Insha Allah haka zamu zauna har abada” Ya miqe tare da fadin “zan sa a kawo miki abinci.. wanne kike so?” Da sauri tace “a’a Hamma… abincin sayarwa babu dadi.. zan dafa da kaina, kai ma zaka ci??” Shi dai MK ya sani sarai cakwakiyar da ke gaban shi bazata bar shi yayi sha’awar cin wani abinci ba amma dukda haka sai yace “zan ci Baby” Tayi murmushi sannan tace “sai ka dawo Hamma.. Allah ya bamu sa’a”3 Cike da tausayin yarinyar yace “Ameen Babyn Hamma..” Tana ta kallon shi har ya fita. Sossai hankalin Ummi yake a tashe.. addu’a kawai take yi akan Allah yasa kar su Abba su kore ta. Ita dai ta tabbatar idan aka raba ta da MK sai ta mutu.3 STORY CONTINUES BELOW Ayyah… ♧♧♧♧♧♧♧♧ MUHAMMAD SODANGI RESIDENCE MAITAMA Sai bayan sallar Magrib ne MK ya shigo gidan.. Ko da ya faka motar shi ya fito gaba daya ma’aikatan gidan da suke harabar gidan suka nufi wurinshi yayinda suke ta gaishe shi kamar kullum. Sama-sama ya amsa gaisuwar sannan ya sa kai ya shige cikin gidan. Mamy ce zaune a falonta tana kallon TV. MK ya shigo falon cikin sallama.. Mamy dai ba tare da ta dago kai ta kalle shi ba ta amsa sallamar. A sanyaye ya gaishe ta amma sam bata amsa ba. Hankalin shi yayi masifar tashi domin kuwa ba qaramin abu bane ba zai sanya Mamy ta qi amsa gaisuwar shi sannan ta qi kallon shi…. asali ma hakan bai taba faruwa ba. Qarasowa yayi ya zauna a gefen ta yayinda yace “Mamy don Allah ki…” Hannu ta daga mishi tare da fadin “yana sashen shi idan wurin shi ka zo..”2 Daga nan ta miqe ta bar falon yayinda ya bi ta da ido. Gani nayi ya dafe kai cike da tsananin tashin hankali yayinda na ji yace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. what is happening to me??” Yayi kusan minti biyar a nan zaune ne na ga ya miqe jiki a sanyaye ya nufi sashen Abba. A lokacin da ya shiga Babban falon shi kuwa ya tarar da shi yana magana a waya don haka ne ya qarasa ya zauna a qasa yayinda ya cika da fargaban abinda zai wakana a tsakanin shi da mahaifin nashi. Yana nan zaune har Abba ya gama wayar shi. Bayan ya kashe ne MK ya dan russuna yace “ina wuni Abba” Ba tare da Abba ya kalle shi ba yace “tashi ka fita ka bani wuri…”4 A rude MK yace “Abba please I am sorry… I…” Cikin fada Abba yace “Kabir I said get out!!” Ba tare da MK ya qara fadin komai ba ya tashi ya fita daga falon… A yanzu kuwa kan shi ne ya fara yi mishi mugun ciwo yayinda qafafuwan shi suka yi sanyi. Tabbas Abba yayi fushi.. dama dai he is not the type that takes shit.. Abba yana da zafi sossai domin kuwa idan ya kafe akan abu toh fa sai kayi dagaske sannan zai sauko. He is very strict compared to his brother, Daddy. MK dai tafiya kawai yake yi amma bai san abinda ke gaban shi ba. Yana daf da fita daga gidan ne ya ji an riqo hannun shi. Da sauri ya juyo ya ga Hafsah tsaye tana kallon shi cike da damuwa. Ji nayi tace “hey come here..” yayinda ta ware hannuwan ta. A comforter is definately what he needs right now!!2 Ba tare da bata lokaci ba yayi hugging dinta. Ji nayi yana fadin “Hafsy trust me… I didn’t have a choice but to marry her.. I just.. I am..” Muryar Hafsah na ji tace “Its okay bro..”1 Tayi breaking hug din sannan ta riqo hannun shi tace “come..” MK dai babu musu ya bi Hafsah har sashen ta. Zaunar da shi tayi a daya daga cikin kujerun lafiyayyen falonta yayinda ta zauna a gefen shi tana fuskantar shi tace “Bro nasani cewar ba haka nan kayi abinda kayi ba.. na sani cewar something is not okay between you and Ya Maleeka. Na girma na gan ka tare da Ya Maleeka, I have seen how much you love and adore eachother, na ga yadda kake sacrificing duk wani abu just to make her happy, na san yadda baka taba kula ko wacce mace ba a dalilin Ya Maleeka… na tabbatar akwai abinda Ya Maleeka tayi maka wanda har ya sanya wata ta samu shiga rayuwarka.. now please can you just tell me everything already???” STORY CONTINUES BELOW MK wanda yake dafe da kan shi yace “Hafsy I dont…” Dakatar da shi tayi tace “I promise you bazan fadi ma kowa ba idan ka gaya mun.. please tell me” A nan dai MK ya ba Hafsah labarin abinda ya faru tsakanin shi da Maleeka tun farkon auren su har zuwa abinda ya faru da har ta kai shi ga auren Ummi. Tunda MK ya fara bata labarin kuwa ta cika da tsananin mamaki. Har ya gama bata labari kuwa she was in shock.. she never thought Maleeka would do something like that. Hafsah tana kallon MK cike da mamaki tace “But bro I thought she loves you… I mean, duk sacrifices din da kayi ma Ya Maleeka tun tana qarama amma ace bazata yi maka this one thing ba?? toh wai tsaya.. ya akayi baka taba reporting issue dinnan ba?? it’s a serious case fa..” Shi dai MK shiru yayi yayinda ya ji Hafsah ta cigaba da fadin “…Na san halinka na rashin son tona asirin mutane ko tozarta su musamman wannan din da ya kasance YA MALEEKA ce but gaskiya bro you need to report this because it’s the only way da su Abba zasu sauko su fahimce ka eventhough ina suspecting ko da hakan bata faru ba you will still have a thing for that girl..”5 MK wanda ya kalli Hafsah yace “No Hafsy, I will convince them somehow amma bazan fadi wannan maganar ba… As for Ummi I see her as a sister that I feel obliged to protect..”3 Cike da tsokana Hafsah tace “haba dai yayana.. ka manta cewar da ni kake magana??? wallahi I know you well.. nasani cewar yarinyar nan ta sace maka zuciya ne, idan ba haka ba wacce mace ce zata sa jinin ka ya hau har ka kwanta jinya sannan ka kashe kudade masu yawan gaske don neman ta?? again you took the trouble of marrying her dukda ka san implication din… idan baka sani ba yau zan fadi maka..” Ta nuna shi da yatsar ta tace “You, Muhammad Kabir have fallen deeply in love with Ummi”6 Runtse idanuwa yayi sannan ya bude yace “oh no Hafsy… I told you I..” Snapping fingers dinta tayi sannan tace “trust me bro.. da kanka zaka zo ka fadi..” Kafin yayi magana tace “wallahi da fa har ta bani haushi ashe ma taimakon ka tayi.. aikuwa Allah yasa ta haifo maka yara kyawawa.. ita kuma Ya Maleeka sai ta je ta cigaba da yin business dinta..”3 Girgiza kai yayi kawai sannan ya miqe yace “thanks alot Hafsy.. talking to you really helped” Itama miqewa tayi tace “nima na ji dadin conversation dinmu Bro… atleast my doubts have been cleared.. mu je in raka ka” Tana riqe da hannun shi suka fita yayinda na ji tana fadin “ka cigaba da lallaba su Abba, na tabbatar zasu sauko… afterall kai fave dinsu ne” Murmushi yayi yace “Insha Allah my Chubby.. thanks alot” ♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Ko da MK ya dawo gida main falon gidan na qasa ya zauna. Kwanciya yayi a kan kujera ya rufe idanuwan shi yana tunanin abinda ke faruwa da kuma yadda zai bullo ma su Abba. Wayar shi ce tayi ringing.. ko da ya duba sunan abokinshi ya gani. Bayan yayi answering ne abokin shi yace “hey how far… ka je gida kuwa?? me su Abba suka ce??” Sauke numfashi yayi sannan yace “they already found out tun ma kafin in dawo abokina..” Cike da mamaki Fahad yace “what??? how?” MK yace “I really dont know my friend but kasan Abba ai.. yana da contacts everywhere not just in this country… probably some random people told him” STORY CONTINUES BELOW Fahad yace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un… toh yanzu ya kenan??” Anan dai MK ya ba Fahad labarin abinda ya faru da ya je gidan. Shi dai Fahad thesame shawara da Hafsah ta bashi shima irinta ya bashi- ya fadi ma iyayen su abinda Maleeka tayi mishi wanda hakan is a fact good enough to make him take up a second wife amma kamar yadda ya fada a baya yace bazai fadi ba. Haka dai abokin shi ya cigaba da bashi shawarwari na yadda zai bullo ma su Abba wanda kuwa idan har basu gamsu ba dole ne ya fadi musu issue din Maleeka idan dai ba so yake ya qara losing Ummi ba..5 Ni kuwa nace ‘ah toh’ ************ Wuraren qarfe daya na dare ne MK ya miqe ya nufi sashen Ummi. Ya sani sarai tayi bacci a wannan lokacin. Dama dai tunda ya dawo da gangan ya qi zuwa wurinta domin kuwa ya san zata yi ta zabga mishi tambayoyi wanda bai san amsar da zai bata ba. Har missed calls tayi mishi wadanda yana kallo amma ya kasa picking. Murda qofar dakin yayi ya shiga. Gani nayi ya tsaya cak yayinda ya hango ta kwance a tsakiyar gado rungume da teddy bear dinta tana bacci. As usual ta dunqule kamar wadda take tsoro. Qarasowa yayi bakin gadon ya zauna a gefe ya sa mata idanuwa. Sanye take cikin rigar baccinta na wandon three quarter da T-shirt pink colour… A gaban T-shirt din anyi rubutu kamar haka: ‘I am a princess’ Gashin kanta duk ya baje a kan pillow da part of her face sannan hular da ke kanta ma ta fara zamewa yayinda tayi revealing gashin da ya kwanta a gaban goshinta da yake bala’in so.2 She looked so cute. MK ya sani cewar idan aka raba shi da yarinyar nan a wannan karon shima fa mutuwa zai yi.. connection din da yake tsakanin su is so strong that he feels bazai taba iya yin wani abu ba a rayuwarshi idan babu ita. Ya zaiyi da su Abba?? ta ya zaiyi convincing dinsu su amince da auren nan without bringing up his issue with Maleeka?? MK dai sossai ya shagala a kallon Ummi yayinda yake ta saqe-saqe a ran shi. Maganar Hafsah ya tuno inda tace: “You, Muhammad Kabir have fallen deeply in love with Ummi” Shafa kan shi yayi da hannuwan shi biyu sannan yace “Have i???”6 kasa ba kanshi amsa yayi don haka ne ya miqe ya janyo Duvet ya rufe ta sannan ya nufi wurin switch ya kashe mata wuta ya fita. ************** Washegari wuraren qarfe goma na safe yana zaune a cikin Jacuzzi bath na lafiyayyen bathroom dinshi yayinda yayi zurfi cikin tunani. kusan awan shi biyu a nan yayinda ya kasa fitowa. MK dai throughout the night bai samu baccin kirki ba.. tunani kawai yake yi na yadda zai bullo ma al’amarin… me zai ce ma su Abba su bar shi ya cigaba da zama da yarinyar? how is he supposed to convince them?? must he really bring up his issue with Maleeka?? Ummi ce ta turo qofar bathroom din ta shigo. Tun jiya da daddare take ta jiran dawowar shi don ta ji abinda su Abba suka ce. Sossai hankalinta yake a tashe.. tayi ta kiran wayar MK amma bai amsa ba.. tana zaman jiran shi ne har bacci ya kwashe ta. A yau kuwa tun wuraren qarfe takwas da rabi ta shigo dakin shi amma ta tarar babu shi.. a dalilin ta ji motsi a bathroom din ne ta san yana ciki don haka ne ta koma falon shi ta zauna zaman jiran shi.. gashi kusan tsawon awa biyu amma shiru bai fito ba. STORY CONTINUES BELOW A yanzu da ta dawo da bata ganshi bane hankalinta ya tashi.. how can somebody spend almost two hours a bathroom?? Ba tare da tunanin komai ba kuwa ta sa kai ta shiga bathroom din. Gani nayi ta zaro idanuwa yayinda ta qarasa wurin jacuzzi bath din.. Hankalinta kuwa yayi mugun tashi ganin idanuwan shi a rufe sannan baya motsi. Zama tayi a gefe yayinda ta sa hannu ta taba shi tare da fadin “Hamma… Hamma me ya same ka???” Da sauri ya bude idanuwan shi wadanda suka yi ja. Ajiyar zuciya ta saki yayinda ta dafa kanshi tace “Hamma me ke damun ka?? baka da lafiya ne?? meyasa baka gaya mun ba ai…” Da sauri yace “ssssshhhh… Baby I am fine, kai na ne yake dan ciwo” Cike da tausayawa tace “Allah sarki Hamma.. sannu” daga nan kuma sai ta fara yi mishi massage yayinda take fadin “meyasa baka fadi mun ba Hamma? don Allah ka dinga gaya mun ka ji??…” MK dai shiru yayi yayinda ya lumshe idanuwan shi yana jin dadin yadda hannuwan yarinyar suke messaging kan nashi.. toh ya ma za’a yi ya rabu da yarinyar nan?? yarinyar da ta damu da shi fiye da kanta.. Ji yayi tace “Hamma ka daure ka fita daga cikin ruwan nan.. yayi sanyi kuma zai iya sanya ka mura” MK dai ya kula kamar bata gane cewar he is seated in the bath naked ba don haka ne yace “kin tabbata in tashi babu matsala???” A nan ne ta ankara da halin da yake ciki.. aikuwa da sauri ta miqe tace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un…”1 Zata gudu kenan ya riqo hannunta yace “tsaya mana… ina zaki je??” Idanuwanta a rufe yayinda muryarta tana rawa tace “Hamma don Allah ka sake mun hannu.. ni fa wallahi hankali na a tashe ne da har na manta cewar babu riga a jikinka..” Shi dai MK qare mata kallo kawai yake yi yayinda yake mamakin how very much beautiful she is.. sanye take cikin kayan baccin da ya ganta da su jiya… sossai suka yi mata kyau… Ji tayi yace “Baby you are beautiful..” Murmushi tayi tace “nagode Hamma.. don Allah ka bari in tafi” Ya saki hannunta sannan yace “toh tafi.. zan tashi” Aikuwa a guje ta bar bathroom din yayinda ta bar shi yana dariya. ********** Ummi tana tsaye a qaramin falon shi ya fito sanye cikin kayan da take masifar so.. qananan kaya. Idanuwa ta sanya mishi wanda har ya qaraso wurinta ya ja kumatun ta yace “kallon fa??” Murmushi tayi tace “kayi kyau..” Shima yana murmushi yace “nagode Babyn Hamma..” Tace “ya kan naka?? ya daina ciwo??” Yace “eh ya daina..” Tace “Alhamdulillah.. yanzu mu je ka ci abinci toh” Haka ta ja shi suka yi hanyar kicin wanda suna tafe yana mamakin yadda yarinyar take kula da al’amuran shi.. it’s like her mission in this life is just to look after him.. how can he not like the girl? how can he not feel she is a part of him?? how can he not want to be with her for the rest of his life?? how can he not protect her with his life??1 Ko da suka shiga kicin din zama yayi a kan kujerar Island yayinda yace “Baby ki bani Cappuccino kawai..” Tace “haba dai Hamma.. jiya ma fa baka ci abinci ba.. ko ka ci a gidan Ab…” Bata qarasa maganar ta ba kuma ta dawo kusa da shi tace “yauwa Hamma.. me su Abba suka ce?? sun amince in zauna tare da kai ko…” Hannun ta ya kamo ya zaunar da ita a kan kujerar da take kusa da shi yace “ki kwantar da hankalin ki Baby.. basu amince ba tukun amma zasu amince insha Allah” Jikinta yayi sanyi sossai yayinda ta shiga damuwa. Murmushi yayi tare da Jan kumatun ta yace “Baby what? ba nace kar ki damu ba?? please dont worry.. komai zai daidaita.. oya tashi ki hada mun Cappuccino dina” Ba tare da tace komai ba ta miqe amma fa jikinta a sanyaye. MK dai haka ya bi ta da kallo yayinda take ta yin komai cikin sanyin jiki. Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “anjima ki shirya Fatima matar Hamma Fahad zata zo ku fita” Tace “toh Hamma.. ina zamu je??” Yace “Yawo zaku je Baby….” ♧♧♧♧♧♧♧♧