DIYAM CHAPTER 6
Washegari Baffa da kansa ya tisa keyar mu daga ni har Sadauki muka je islamiyya, ya saka muka bada hakuri sannan shima ya bayar, ya kuma ce duk sanda wani abu makamancin wannan ya sake faruwa su sanar dashi shi kuma zai dauki mataki akan mu. A take kuma yayi Asma’u register ya ce kullum tare zamu ke zuwa da ita . Wannan ya kawo karshen gudun islamiyya ta amma kuma ya kawa hauhawar kiyayyar Sadauki a gurin Inna, yanzu yakasance ko gaisheta yayi bata amsawa shi kuma bai fasa gaishetan ba kullum. Takance “shegen naci irin na uwa, kamar tsohon maye”.1 A karshen term din muka rubuta jarabawar common entrance. A lokacin shi kuma Sadauki ya rubuta jarabawar shiga ss3, qualifying exam, kuma dukkanin mu munyi nasara. Naci makarantar day science ta nan garin kano. Ina karbowa na taho gida da murnata na kuma yi sa’a Baffa yana gida, suna palon sa shida Sadauki suna lissafe lissfen da suka shafi gareji. Na durkusa na gaishe shi sannan namika masa takardar, ya karba ya karanta yana murmushi yace “very good Inno. Kinyi kokari sosai Allah yasa albarka a cikin karatun ki” nace “ameen Baffa” yace “sai dai ba day science zaki tafi ba, nayi magana da wani abokina wanda yake malami ne makarantar kwana ta yammata dake garin Taura a jahar Jigawa, yace in kaiki zasuyi miki interview in kinci sai a kaiki can” na taba rai cike da confusion nace “taura? Gari ne haka din? Makarantar kwana?” Sai na juya na kalli Sadauki wanda shima Baffa yake kallo yace “Baffa boarding fa kace, Diyam? Baffa Diyam bata da girma manyan dalibai zasu ke cin zalinta kuma….” Sai ya hadiye sauran maganar saboda kallon da Baffa yayi masa, Baffa ya miko min takardar yace “ki kaiwa innarki ta adana miki, gobe da safe ki shirya zamuje kiyi interview din” na karba jikina a sanyaye na wuce dakin inna. Na kai mata ta bude tana gani fuskarta da murmushi duk kuwa da cewa ba wai sanin abinda aka rubuta tayi ba. Na zauna a kusa da ita nace “Inna naci day science, makarantar su Rumaisa” ta ninke takardar ta ajiye tace “Rumaisa ai jeka ka dawo take yi, ke kuma makarantar kwana zakiyi” na fara hawaye nace “Inna Baffa yace wai gobe za’a kaini a gwada ni, inna ni bana son zuwa dan Allah kiyi masa magana kar a kaini” tana kallona tace “saboda me?” Na rike hannunta nace “bana son barin gida Inna bana son rabuwa daku” sai ta zame hannunta daga nawa tace “ko dai bakya son rabuwa Sadauki? Ni kuma saboda shime nake son akaiki makarantar kwanan ko hankalina ya kwanta, kuma idan ba kya ganinsa a hankali zaki manta dashi. Kafin Allah ya taimake mu ya tattara ya koma gidan ubansa” jin haka yasa na fahimci bani da hope a gurin Inna, ba zata rokar min Baffa ya fasa kaini boarding ba. Dakin Ummah na tafi ina sharar kwalla, ta rike ni tana tambayata, “Diyam lafiya? Wani abu ne yake yi miki ciwo?” Na zauna ina kara sautin kukana nace “Ummah wai boarding za’a kaini inji Baffa, dan Allah Ummah ki bawa Baffa hakuri” tayi ajjiyar zuciya tace “Diyam, ai ba laifi kikayi masa ba ballantana in bashi hakuri, zai kaiki boarding ne saboda yana ganin hakan shi yafi dacewa dake” nace “to ni yanzu Ummah me zanyi? Me zanyi ya fasa kaini?” Tana shafa kaina tace “kiyi addu’a, kiyi fatan Allah ya sa hakan shi yafi miki alkhairi” Washegari tun da assuba Baffa ya leko yace min in tashi in shirya, karfe takwas na safe muka dauki hanyar Taura, Sadauki ne yake jan motar sai Baffa a gaba ni kuma ina baya ni kadai, wannan yasa na kwanta wai ko za iya bacci amma bacci yaki zuwa ina ta jero duk addu’ar da tazo bakina akan Allah yasa kar inci interview din nan. Su Baffa ma ba sosai suke hira ba sai jefi jefi, shima kuma duk akan harkar garejin su ne. Karfe goma saura muka isa makarantar, aka bude mana gate muka shiga har bakin staff room sannan Baffa ya kira number din abokin nasa wanda shine vice principal a lokacin, inanan dai a kwance yazo, naji suna gaisawa da Baffa sannan Sadauki ya gaishe shi, sai ya bude kofar baya yana kallo na yace “manu wannan kawai bar mana ita za’ayi anan, a aiko mata da kayayyakin ta” Baffa yace “shi kenan kuwa kaga mun huta da sake dawowa” ina jin haka na kifa kaina a jikin kujera na fara rera kuka, Sadauki ya juyo yana kallona yace “wasa suke yi miki fa, ke baki san wasa ba? Ya za’ayi a kawo ki makaranta a lokacin hutu” sai kuma na tuna ashe hutu akeyi, na fara goge hawayena ina cewa “Sadauki bana son makarantar nan” yace “kiyi shiru kar Baffa yaji yayi miki fada” daga waje naji abokin Baffa yana kira na, na fita ina goge hawayena da hijab dina. Staffroom babu malamai sosai saboda ana hutu, office din principal muka shiga, na gaisheta a darare ta kalle ni daga sama zuwa kasa sannan tace “too young” vice ya matsa kusa da ita ta fara yi mata bayanin cewa karamin jiki ne dani amma eleven years nake a lokacin, ya nuna mata birth certificate dina da sauran takardu. Ta gyada kai sannan ta bani wata exam question paper tace in zauna in amsa. Na zauna ina dubawa, obj ce, dan haka nayi ta cike shiririta ta wata question din ma ko karantawa banayi wai ni a lallai so nake in fadi. Ina gamawa na bata na fito raina fes saboda nasan nayi messing up. Baffa ya mike yana kallon vice yace “to ya akayi? I hope taci?” Vice yayi dariya yace “ai ba’ayi marking ba, amma abinda ta rubuta a paper doesn’t matter, tunda ina gurin ai babu wani abu, maybe ma ni za’a bawa in yi mata marking. Kawai da lokacin kawo yara yayi ka shirya ta ka kawo ta. Ya dan daki kaina cikin wasa yace “kaga manyan yan boarding” naji kamar in rufe shi da duka dan haushi.2 STORY CONTINUES BELOW A cikin hutun na harda ciwo nayi. Inna da Baffa kuma duk sunsan abinda yake damuna amma babu wanda yabi ta kaina, sai ma shirye shirye da suke yi. Aka dinkamin uniform, aka siyamin manyan trollies dina guda biyu daya ta kayan sawa daya ta kayan abinci. Vice ya rubutowa Baffa duk abinda ake bukata Baffa kuma ya bawa Sadauki yaje ya siyo min. Akan haka sai da akai rigima da Baffa da inna tace ina ruwan Sadauki da siyayyar makaranta ta? Amma Baffa bai fasa bashi ba. Idan Baffa ya bashi list din sai ya zauna ya kakkara wasu abubuwa yace ai duk zan bukace su, sai da Baffa yace “Sadauki ya isa haka in ba so kake ka talautani akan Diyam ba, muma ai muna bukatar kudi a gidan”. Ranar da zan tafi, tun da na tashi nake yan koke koke na amma Inna ko ta kaina bata bi ba tace “kya yi kya gama. Gata akeyi miki ke baki sani ba”. Sai ga Ummah tazo da kanta da kaya cikin leda, da cincin a cikin wani dan karamin plastic container mai murfi tace “Diyam gashi ki tafi dasu makaranta, ki rike addinin ki kinji? Kuma kar kike wasa da cikin ki ki tabbatar kina cin abinci akan kari, duk abinda kika ga ya kusa karewa ki saka ayo waya gida a fada” na karba ina share hawayena nace “to Ummah na gode” Inna ko daga kai bata yi ta kalleta ba. Sadauki da Baffa ne suka kaini, tun daga gate nake kuka har muka shiga ciki aka gama cike ciken takardu, malamai suna ta tsokana ta wai daga gani na sabun shiga ce. Sadauki ya durkusa a gaba na yana share min hawayena yace “zaki yi ciwon kai na gaya miki. Ki daina kukan nan haka” na rike hannunsa nace “ni karka tafi ka barni” ya kakalo murmushi yace cikin wasa “ai babu hostel din maza” sai kuma yayi dariya shi kadai ba tare dana taya shi ba. Yace “zanke zuwa ina ganin ki. I promise. Amma sai kin daina kuka in ba haka ba bazan ke zuwa ba” na langwabar da kai nace “ai kukan ne yake zuwa da kansa” yace “to kiyi, amma kadan”. Ina kallonshi yana ta delaying shiga mota da zasu tafi, har sai da vice ya tisa keyata zuwa class sannan na jiyo tashin motar su. Ina zuwa nayi kawa Jidda, itama yau aka kawo ta tana ta kuka sai class master din mu yace mu zauna a seat daya kuma daga yau mun zama kawaye tunda mune masu kuka a aji. Duk yadda na dauka rayuwar makaranta zata zo min ba haka tazo ba. Kafin inyi sati na warware sosai ina harkokina, nayi suna a ajinmu saboda kokarina da kuma surutuna. A hostel kuma nayi suna saboda kankantata da kyau na. Seniors suna sona sosai, wadansu su kance ina musu kama da baby doll saboda yar karamace ni babu tsaho babu kiba, gani fara tas kamar babu jini a jikina sai uban gashi mai tsaho da santsi wanda baya kitsuwa sai da kyar. Daga wannan senior din ta dauke ni tace kanwarta ce ni sai waccan ta dauka, ayi tabani kayan dadi ina ci, in an tare yan makara dani sai ace “wannan in aka dake ta ma ai sai a balla ta, tashi ki tafi, karki sake makara” dutse kuwa sai da aka samo wanda yafi komai sauki, sharar verandah sannan aka bani. Amma fa wannan ko da second daya baisa na cire Sadauki daga raina ba, kullum dashi nake kwana dashi kuma nake tashi. Wani lokaci sai im zauna inyi ta rubuta masa letters ins bashi labarin rayuwar makaranta ta, in zana flowers a jiki da hoton heart da arrow da sunansa a jiki “Aliyu Haidar”. Rannan jidda ta gani ta dauka tana karantawa tace “wanene Aliyu?” Nayi murmushi nace mata “saurayi na ne”. Sai da nayi wata daya sannan rannan muna class aka aiko inzo anzo min visiting. Na mike da sauri ina murna a raina ina kwadayin Allah yasa tare da Sadauki aka zo. Ina fitowa aka nuna min bayan staffroom akace inje can. Na tafi da sauri na, banga motar gidan mu ba amma sai na hango Sadauki shi kadai a tsaye ya jingina da daya daga cikin bishiyoyin gurin. Na kwasa da gudu, ya juyo yana kallona yana dariya amma da yaga da gaske jikinsa na nufa sai ya dakatar dani da hannunsa daya sannan ya girgiza min dan yatsa. Na bata rai na turo baki na juya baya nace “ni fushi ma nakeyi da kai” ya zagayo ta gabana kyakykyawan murmushi kwance a kyakykyawar fuskarsa yace “me kuma nayi? Allah sarki Aliyu bawan Allah” na rike kugu nace “ai kasan laifin ka” ya kama kunnensa yace “na tuba, duk da bansan me nayi ba” na nuna shi da dan yatsana nace “ba cewa kayi zaka ke zuwa ina ganin ka ba? Amma shine tunda aka kawo ni ba ka taba zuwa ba?” Yace “aiya, Halima wata daya ne fa kadai” nace “eh, ai duk sati nake so kazo” yayi dariya yace “duk sati ai suma kansu makarantar ba zasu bari ba” ya kama hannuna muka zauna a daya daga cikin benches din dake gurin yace “kinga, visiting card guda uku suka bamu, suna nufin sau uku aka yarda azo ganin ki. In na ce zanke zuwa duk sati ai ko wata ba zakiyi ba cards dinki zasu kare. Kuma kinga su Inna ma si zasu so suxo su ganki ko?” Na danyi murmushi naji ina missing Inna nace “ya suke? Ya Baffa da Asma’u?” Yace “duk suna lafiya, basu san dai na taho ba sai Baffa kadai. Ke kuma fa? Ya makarantar? Ba’a cin zalinki ko?” Ya kama hannuna yana checking ko yayi kaushi ko kanta yace “ba’a saka ki labour? Noma da shara mai yawa?” Na gyara zamana ina wasa da hannuna na bashi labarin duk irin yadda nake enjoying makarantar, yace “wato it sometimes pays to be smallish ko?” Muka yi dariya. Sai kuma ya bani labarin tasa makarantar, yanzu sun shiga ss3, ya fada min an bashi prefect, yace “guess me aka bani” na karkatar da kai ina kallon murmushin fuskarsa nace “labour prefect” yayi dariya yace “you are a smart one, aren’t you?” Nace “to kar dai kake cin zalin yayan mutane” ya daga hannu sama yace “ba zalin wanda zanci, kar alhakin su yasa aci min zalin matata” sai kuma naji kunya na rufe ido. Mun jima muna hira, jin mu muke kamar masu yawo a saman gajimare har sai da aka zo ake ce masa time up sannan muka fara sallama, rai ya fara baci kuma. Yace “hope kayan abincin ki basu kare ba” na gyada kai kawai ina goge hawaye, yace “okay, to bara in koma da sweets din dana zo miki dasu tunda kuka zakiyi” nayi sauri na jawo ledar gabansa na turo baki ina kunkuni. Na bude naga kayan alawa, chocolate da biscuits ne kawai a ciki. Ya miko min kudi yace “inji Baffa, yace ki fada in kina son wani abu” na girgiza kai, yace “to kiyi min dariya mana in gani. Kuma ko sammin sweets din ba zaki yi ba?” na bude ledar na dauko chocolate guda daya na bare na bashi nace “gashi nan, ladan ganin ido” A tsakiyar term su inna suka zo min visiting suma. Sadauki ne ya tuko su amma babu Baffa kuma babu Ummah sai Asma’u Mama da su Rumaisa. Nace “ayyah, Inna da kun sani kun taho da Ummah, nayi missing dinta” babu wanda yace dani ci kanki a cikin su. Ranar nayi murna har na rasa inda zan saka kaina, su kuma suna ta yimin dariya. Suka zo da abinci kula kula muka hadu muka ci tare ana ta hira, amma Sadauki tunda muka gaisa ya koma mota, sai da muka gama cin abincin sannan na zuba na kai masa, ina mika masa kuwa inna ta kira ni in dawo haka na taho bamuyi magana ba. Sai da zasu tafi ya dauko bakar leda ya miko min yace inji Ummah, garin karba naji ya saka min takarda a hannu na sai nayi sauri na saka ta cikin aljihuna, yayi murmushi kawai ya daga min hannu suka tafi.+ Bayan na koma hostel ina jejjera kayan dasu Inna suka kawo min, na duba ledar da sadauki ya bani naga dambun nama ne da yaji attaruhu da tafarnuwa, just the way I liked it. Nayi murmushi na dauko takardar daya bani na bude ina karantawa. My dearest star. Am sorry ba mu sami damar magana ba, but ganin kina lafiya kadai ya ishe ni farin ciki. Ga dambun nama nan inji Ummah tana gaishe ki. PS I love you.2 Na dora takardar a kirjina ina jin wani iri. Na sani cewa akwai wani abu a tsakani na da Sadauki amma bai taba furtawa direct ba sai yau. And it feels great. A hankali nace “I love You too Aliyu”. Haka rayuwa ta cigaba da kasance wa, har cikin ikon Allah muka shiga third term na js1, a lokacin shi kuma Sadauki suke zana ssce dinsu. Kullum in naga yan ss3 dinmu suna exam sai inta yiwa Sadauki addu’a, Allah ga Sadauki nan, Allah ka bashi sa’ar exam din nan. Wannan term din gaba daya baizo min visiting ba. Sai ranar da mukayi hutu suka zo daukana shida Baffa, ko dan ma kwana biyu ban ganshi ba? Sai naga ya kara girma ya kara kyau. Naje na shige gaban mota na barshi da daukan kaya yana sakawa a booth, Baffa kuma ya tafi zaiyi signing dina out. Na dauko powder da lipstick ina shafawa wai duk kyalliyar zuwa gidan ne, sai kawai naji kamar ana kallona, nayi sauri na kalli mirror muka hada ido dashi, ya tsaya da jaka a hannunsa kawai ya zuba min ido ta mirror, muna hada ido sai kuma kunya ta kamashi yayi saurin dauke kai kunya a rubuce a fuskarsa. Dariya kawai nayi wai namiji da kunya. A cikin hutun ne muna gida na fara period. Ranar ina kwance a dakin Ummah ina tashi kawai naji danshi a kasana, na saka hannu na shafa kawai sai naga jini a hannu na, na kalli Ummah naga itama ni take kallo. A lokacin Sadauki yayi sallama nayi sauri na koma na zauna ina boye hannu na a baya na, ya tsaya daga bakin kofa yana kallona yace “ke kuma lafiya kike rarraba ido kamar bera a buta?” Ummah tace “ina ruwan ka da ita, tsabar sa ido me kazo yi ma gida a yanzu?” Ya shigo yana cewa “babu aiki a garejin, shine nazo gida in huta. Diyam tashi ki bani abinci” na kwabe fuska kamar zanyi kuka Ummah tace tana nuna masa kofa “tashi ka fita” yace “Allah ya baku hakuri, daga tambaya?” Sai ya mike ya fita yana waige na. Yana fita Ummah tace “tashi in gani” na mike, tace “kin san menene?” Na gyada mata kai. Tabbas nasan jinin haila da hukunce hukuncen sa tun a islamiyya, na kuma kara sani a kansa a makarantar boarding. Akwai yan ajin mu da suke yi, kuma seniors din mu ma sunayi dan sukan aike ni wajen wata matron in siyo musu pad, amma ban taba tsammanin zaizo gare ni ba ni Diyam, at least not now, ni ban shirya girma ba gaskiya. Ummah ta saka ni naje drawers dinta na dauko wasu undies data siyamin da niyyar in zan koma makaranta zata bani, ta saka na dauko pad itama a dakinta takoya min yadda ake sakawa sannan tace min inje toilet in gyara kaina. Ina dawowa na tarar ta gyara inda na bata a kujerar ta, sai kuma ta zaunar dani ta sake yi min bitar wankan tsarki da sauran abubuwa da suke shafi haila, ta kama kunnena tace “babu wasa da maza daga yanzu, babu wasa da Sadauki” nayi kyar kara sannan ta cika min kunne na. A lokacin Sadauki ya shigo yace “ya naji ana ambatar sunana?” Sai kuma ya kalli irin zaman da mukayi yace “hirar me kuke yi ne haka?” Na tabe baki zan saka masa kuka ya juya yace “na fita, in tayi tsami zanji”. Sai da muka gama maganganun duk da zamuyi da Ummah sannan tace min in tashi inje in gayawa Inna. Na zaro ido nace “Inna? Ni bazan iya gaya mata ba” tayi dariya tace “ai kuwa sai kin gaya mata. In baki gaya mata ba ke da ba’a gida kike zaune ba ta yaya zata sani?” Nace “dan Allah Ummah kije ki gaya mata” tarike baki tace “ni? Babu ruwana, ke zaki gaya mata da bakin ki” naji duk hankalina ya tashi, sai tace “bara in baki shawara. Kinga, yanzu ki tafi dakin ta, ki saka pad a jikin pant ki ajiye akan gado inda tana shigowa zata gani. Da kinji ta taho sai kiyi sauri ki shiga toilet ki buya”. Haka nayi kuwa, na ajiye akan gado sai da naji ta taba kofa sai nayi sauri na shige toilet. Na jima aciki,a tunani na ta fita sai na fito ai kuwa sai gata azaune a kan gado ta tasa pant dina a gaba, nayi sauri zan koma toilet tace “ke! Zo nan” na dawo ina karkarwar jiki na tsaya. Ta nuna pant din tace “wannan na waye?” A hankali nace “nawa ne” sai kuma tayi shiru tana kallona sannan tace “yaushe kika fara?” Nace “dazu” sai ta zaunar dani itama ta dora daga inda Ummah ta tsaya a nasiha da bayanan sabon yanayin dana samu kaina a ciki. Sai data gama sannan tace “saura kuma in sake ganin kun rike hannu ke da wancan bakin munafikin”. Muna gab da komawa hutu exam din su Sadauki ta fito. Alhamdulillah, ya samu nasara sosai. Duk da dai ba distinction ya samu ba amma ya samu credits a duk subjects din daya kamata. Mukayi murna sosai. Sai da jamb ta fito sannan murnar mu ta koma ciki, yayi kokari nan ma, sai dai bai samu points din ake bukata ba a mechanical engineering wanda shine abinda yake so ya karanta. Ranar haka ya wuni ransa babu dadi, ni kuma harda kuka na zauna inayi masa, Ummah kuwa dariya tayi tace “wa kuka taba ganin ya samu abinda yake so lokaci daya? Kuje jami’ar ku tambayi daliban kuji wadansu da yadda suka samu admission din. Ko kuma ku samu mutumin daya ke da daukaka ya baku labarin yadda ya samu daukakar tasa. Babu wani abu mai kyau da ake samun sa cikin sauki”. Baffa yana duba takardar yace “babu komai Sadauki, kar ka damu, akwai next year ai insha Allah sai ka sake gwadawa. In the meantime kuma zan nema maka computer school kayi diploma kafin ka sake jamb din”.Shekara tazo ta wuce. Lokacin na cika shekaru goma sha uku shi kuma sadauki yana sha tara. A cikin ta babu abinda ya ragu sai ma karuwa da abubuwa suke yi a tsakani na da Sadauki, musamman yanzu da yake jin sa ya kara zama saurayi tunda gashi har ya kammala diplomar sa a computer science. Ya sake zana jamb, kuma wannan karon yaci abinda ake bukata din, sai dai kuma cikowar dalibai masu neman admission da kuma rashin hanya yasa ya gaza samun admission din, Baffa yaji takaicin wannan abin dan yana ganin hakan kamar gazawa ne daga bangarensa a matsayinsa na uba.+ Ni kuma a bangare na, na kammala jss2 lokacin ina da shekara goma sha uku amma ina nan jiya i yau, babu abinda na kara a girman jiki sai dan tsaho da kuma hankali. A lokacin kam zan iya cewa duk wanda yake tare damu ni da Sadauki yasan something is going on, including Baffa, Ummah da Inna. Baffa baice komai ba, haka ma ummah, basu taba encouraging din mu ko discouraging din mu ba. Babban problem din, kamar yadda duk muka yi tsammani shine daga gurin Inna dan sosai take nuna kiyayyar ta ga tarayya ta da Sadauki. Hutun da muka zo na third term din jss2, ina shiga palon Ummah hannuna rike da Asma’u da take ta murnar gani na, na tarar da akwati a ajjiye a kofar palo. Bayan na gaisheta nace “Inna wannan kayan fa?” Ta hade rai tace “naki ne, hutu zaki tafi” naji zuciyata ta buga nace “hutu Inna? Ban gama ganin ku ba fa ina zan tafi hutu kuma?” Ta harare ni tace “gidan Alhaji Babba zaki tafi, in muna son ganin ki mu zamu zo mu ganki” nayi ajjiyar zuciya a boye, dan dai sharada? Nasan Sadauki ko da adungure zai je ya ganni. Kwana na daya a gida na tafi sharada. Ni da Rumaisa ne zamu je muyi hutu a can yayin da Inna ta yi mana rakiya. Rumaisa tana ta murna saboda ita kam tana son zuwa gidan Alhaji Babba. Ni kuma ina yake saboda kar Inna ta harbo jirgina na plans din da mukayi da Sadauki.1 Now, let’s talk about Alhaji Babba da family dinsa. Kamar yadda na fada Alhaji Babba shine babban yayan su Baffa, shi ya fara zuwa Kano neman kudi kuma a lokacin yafi dukkansu dukiya, dama baffan mu ne baya. Allah ya jarrabi Alhaji Babba da mugun son yaya maza sai kuma ya hana shi su, wannan yasa ya kasance mai aure aure duk a tunanin sa da burinsa hakan zai saka ya samu cikar muradinsa. Matarsa ta farko yar uwa ce daga Kollere, ya daya ta haifa masa Adda Zubaida, daga nan bata sake haihuwa ba sai ya auri Hajiya Babba wadda tashin farko ta haifa masa muradinsa na ɗa namiji wanda muke kira da hamma Saghir. Hajiya Babba jinin sarautar kano ce, hamshakiyar macece mai mulki da izza wadda hatta kishiyoyinta inka gansu a gabanta zaka iya dauka cewa yaranta ne. Bayan shi ta sake haihuwar mata biyu, Aysha da Salma. Daga Hajiya Babba kuma sai Hajiya Yalwati wadda tafi duk sauran matan yawan yaya kuma wannan shine kadai abinda yake zaune da ita a gidan. Hajiya Yalwati kawar Inna ta ce dan haka duk sanda muka je gidan a dakinta muke zama, kuma nima saboda babbar kawata a gidan, Murja, yar Hajiya Yalwati ce dan haka nima na zama yar dakinta. That plus daga ni har Inna babu wanda yake iya jurar mulkin Hajiya Babba. Sauran vacant space din guda daya kuma na mai rabo ne, wannan ta shiga wannan ta fita. Hamma Saghir shine da daya tilo da Allah ya bawa Alhaji Babba, dan haka zama bayyana cewa dan gata ne bata lokaci ne. An haife shi tun kafin Baffa na yasan zai auri Inna ballantana a haife ni, dan a lissafi ya bani shekaru goma sha shida da watanni. A kullum idan naji mata suna lissafa siffofin mijin da suke so su aura sai inga kamar lissafin kamannin hamma Saghir suke yi, fari, dogo, kyakykyawa, mai saje, marar son surutu, mai kudi, mai class blablabla. Hamma Saghir is all that and more. Labari ya zo min cewa makarantar da hamma Saghir yayi ma kanta daban take da ta sauran yaran gidan dan Alhaji Babba cewa yayi “a samo min makarantar da yayan masu kudi suke zuwa a garin nan, ita zan saka Saghiru” a haka yayi primary da secondary dinsa, sannan aka saka shi a buk yayi degree a economics ya fita da pass. Alhaji Babba yace “ba wani abu, dama an saka ka a makarantar ne saboda ka samu ilimin juya dukiya ba wai dan ka nemi aiki da takardun ka ba”. Sai kuma Alhaji Babba yayi masa irin abinda Hardo yayi masa shima. Ya debi dukiya msi yawa ya bashi yace “tafi ka nemi arzikin ka” Saghir ya gyara zama yace “China zan tafi Alhaji, tunda can ne cibiyar kasuwanci ta duniya a yanzu. In naje sai in nemi Company in saka hannun jari a ciki. Maybe kafin shekara sai kaga nazo na bude nawa Companyn”1 STORY CONTINUES BELOW Haka ya shirya aljihu fal kudi ya tafi China, daga nan ba’a kara jin labarinsa ba har sai da ya shekara uku sannan sai gashi ya dawo daga shi sai jakar kayan sa yace “yan damfara na hadu dasu Alhaji, gaba daya kudina sun salwanta da kyar na tsira da kudin jirgi na dawo gida” Alhaji Babba yace “kasuwanci ya gaji haka dama, yau riba gobe faduwa hakan kuma ba zai saka mu karaya ba” sai ya debi wadandu kudaden ya kuma bashi, shi kuma ya karba yace “Dubai zan tafi wannan karon inke saro kaya ina aikowa dasu gurinku kuna siyar min”. Wannan karon ma tunda ya tafi ba amo ba labari ko waya babu, amma sai iyayen suke boyewa kullum suna nuna kamar yanayi musu waya “abubuwa ne suka yi masa yawa amma yace yana gab da zuwa gida”. Yazo gidan kuwa bayan shekara biyu, sai dai wannan karon ko akwatin kayansa bai dawo dashi ba ballantana kudi “Dubai bata karbe ni ba Alhaji. Kudi na gabaki daya sun salwanta ba bu abinda ya rage a hannu na” Alhaji Babba yace “kasuwanci bai karbe ka ba Saghiru. Dole sai mun zauna munyi maka adduoin neman sa’a sosai. Kuma ina kyautata zaton akwai nasara sosai a rayuwar ka shiyasa kake samun tangarda” Hajiya tace “musamman ma shi da yake da tarin makiya, gaskiya kam sai an hada da addu’a”. Bayan an gama rarraba wa malamai kudi sunyi adduoi, sai kuma Alhaji yace “gwara ka zauna a kasar nan saboda muke ganin abinda kake yi muna kuma baka shawara” amma sai Saghir yace “gaskiya Alhaji ko zan zauna a kasar nan to ba’a Kano ba, saboda anan an saka min ido dayawa”. Haka rayuwa ta cigaba masa, yau yana wannan garin gobe yana wancan duk da sunan neman kudi, in kudin hannunsa sun kare ya dawo Kano ya karbi wadansu ya kara mai. Tunda nake bazan iya cewa ga ranar da hamma Saghir yazo gidan mu ya gaishe da Baffa wanda yake kanin babansa ba ballantana Inna da take cousin din babansa kuma matar kanin babansa. Ni kaina ganin da nayi masa a duniya a lokacin bashi da yawa sai dai a jikin katon hoton sa dake kafe a main palon gidan. A ranar da muka je gidan, kamar yadda muka saba, part din Hajiya yalwati muka fara zuwa muka ajiye kayayyakin mu muka huta sannan muka fita muka zagaya muka gaishe da sauran matan gidan. Bayan mun dawo palon Hajiya Yalwati ne Inna take tsokanar Murja “Murja ya na ganki a daki ne yau kamar matar kulle? Tunda muka zo gidan nan banga kin fita ko babban palo ba?” Hajiya Yalwati tace “uhmm ina zata fita taje, boss din su yana gidan? Tun safe nace musu suyi zamansu a daki kar wadda ta fita in ba haka ba sai kiga an dawo da kumburarriyar fuska ya kama su ya mara, komai akayi ai shi laifi ne a wajensa, magana ma mai karfi in sunyi cewa zaiyi sun hana shi bacci duk ya hada su yayi musu duka. Kuma ban isa inyi magana ba” Inna tace “wai Saghir kike nufi? Yazo garin kenan. Oh ni yaushe rabon da inga Saghir?” Kamar da hadin baki kuwa sai gashi ya shigo palon. Ya dafa kujera daga tsaye yace “Hajiya barka da gida” Hajiya Yalwati tayi yake tace “Barka kadai Saghir, anzo lafiya” yace shortly “lafiya lau” sai ya juya zai fita, Hajiya Yalwati tace “ga gwoggonka fa, gwoggo Aminan baffa Usman” ya dan juyo yana shafa kai yace “lah gwoggo ai ban lura ba. Ya gida? Ya Baffa?” Inna tayi murmushi tace “lafiya lau Saghir, ya kasuwa? Allah yayi jagora” yace “ameen” sannan ya fice ba tare daya ko kalli inda muke zaune ni da Rumaisa muna kokarin gaishe shi ba. Yana fita Inna ta juya tana kallon Hajiya Yalwati tace “kai masha Allah. Saghir ya zama babban mutum sosai” Hajiya Yalwati ta tabe baki tace “eh fa. Yo mutumin da yake kokarin cika shekara talatin a duniya ai kuwa dole a kira shi da babba. Ni in dai gatan gaskiya kuke yi masa ma aure ya kamata kuyi masa maybe ko ya haifa muku jika namiji” Inna tayi dariya tana tafa hannu, Hajiya Yalwati tace”a’a to bai isa auren bane ba? Ko dai kuyi masa aure wallahi ko kuma ya dauko muku abin kunya dan duk abinda yake aikatawa a garuruwan da yake zuwa muna sane, in munyi magana kuma ace hassada muke yi masa” Inna ta watso mana harara ni da Rumaisa, sum sum muka tashi muka basu guri dan munsan ma’anar hararar. Muna fita Rumaisa tace “zo mu tafi palon Hajiya Babba” na makale “ke ni bana son zuwa gurinta tayi ta mulka mutane tana kallonsu sama sama” ta kuma jan hannu na “dalla can kizo muje, wani abu zan nuna miki”. Muka je muka sameta a dan karamin palonta tana kishingide yar aikinta tana yi mata tausa. Muka sake gaisheta sannan muka zauna a gefe muna kallon tv. Muna zaune ya shigo, yana shigowa na kama hannun Rumaisa da niyyar ta tashi mu basu guri amma sai ta rada min “ki bari muyi kallo” na koma na zauna na zubawa tv ido. Ya zarce gaban Hajiya ya zauna. Tace “kaje duk ka gaishe su?” Ya yamutsa fuska yace “naje” sai kuma yace “Alhaji har yanzu bai fito bane?” Tace “na gaya maka ai baya jin dadi ya kwanta. Wani abu kake bukata?” Yana shafa kai yace “dama kudi nake nema, akwai wasu kayana da aka kawo min daga porthercout shine nake so inje in karbo” tace “kaje drawer ta ka gani ko zasu ishe ka” ya mike zai tafi Rumaisa tayi sauri ta gaishe shi, ya dan bata rai yana kallon ta sannan ya amsa, wannan yasa nima na gaishe shi, ya amsa a ciki ciki irin irritatingly dinnan. Hajiya tace “ba ka gane Diyam ba” ya juyo ya kalle ni yana yamutsa fuska yace “bangane taba. Yar uwar mu ce?” Hajiya ta danyi dariya tace “Diyam fa, babbar yar baffan ka Usman” ya danyi shiru sannan yace “ohh, that little baby da akayi jegon ta anan? Wannan mai cika mana gida da kuka?” Hajiya tayi dariya tace “ita fa” ya dan karkata kai yana kare min kallo sannan yace “sam ban gane ta ba. Bata kama da iyayenta” Hajiya tace “ai kuwa Diyam kamar su daya da innar ta, dan karamin jikin ne dai ta dauko na babanta” ya sake kallo na yace “no Hajiya, gwoggo Amina ai kyakykyawar bafulatana ce, wannan kuma sai naga tana min kama da bararoji” gaba dayan mu sakin baki mukayi muna kallon sa har hajiyan, tace “bararoji kuma Saghir? Diyam kuwa ai kowa yana yaba kyanta” ya sake kallona sannan ta tabe baki yace “still, ni ban gani ba”.7