ZUCIYA CHAPTER 15
Ganin yanda jikin Nafi yai sanyi yasa Little tace ” Me ya ce miki?” Nafi tai murmushi tace ” tambaya ta yai kawai yaushe zamu dawo nace wasu yau mukuma sai gobe.”+ Little ta dan tab’e baki tace ” akan haka ne naga ya zuciya?ni wlh na d’aukama ko laifi kikai.” Habib yai dariya yace ” kinsan yayan naki ai Gimbiya.” Haka dai sukai ta hira sama sama sannan sukai sallama tare da tafiya da kayan Nafi yanda gobe sai dai ta taho ita kad’ai. ******** Shikam Ashraf har ya isa gida zuciyarsa batai sanyi ba, sai ma kara tunano abinda tamai kawai dayakeyi, sannu yaya? Lalai kalman nan ta bala’in b’atamai rai ya cije leb’e tare da yin kwafa lalai yarinyar shi zata dizga??? Da karfi ya shiga gidan ko mai gadin bai kalla ba ya fito tare da rufe kofar motar da karfi yai bangarensa. A falo yaga Anisa tana ganinsa ta taso da sauri tana neman rungumeshi gocewa yai ya wuceta yai gaba. Kallan takaici ta bishi dashi tana kallo ya shige d’aki tare da rufo kofar da karfi, wanda har sai dayasa tadan razana. Yana shiga ya cire kaya ya wuce toilet, ya dade yana zuba wa kanshi ruwa kafin ya fito. Ya kwanta akan gado tare da daura hannu akan goshinsa, Anisa ce ta shigo cikin kissa ta zauna a gefenashi tace ” Dear muje kaci abinci ko?” Juya mata baya yai yace ” banasan magana yanzu bacci zanyi.” Kallansa tai tace ” Amma……” Wani kallo daya mata yasa ta mike tai waje. ****** Nafi ce bayan isha’i zaune a hostel itada Ferry da Jibiya suna cin abinci, sai wasa kawai take da cokalinta sam ta kasa kaiwa bakinta, Ferry ta kalleta tace ” banga laifinki ba Feena gaskiya Ashraf ya hadu karshe sannan rashin maganarsa da hade fuskarsa charm dinsa ne.” Nafi ta buga mata harara, Ferry tace ” sai dai bawai ina nufin haduwarsa da charm dinsa ba ko kudinsa sune zasusa yafi karfinki ba ko ki karaya ba, sai dai……” shiru tai batare da ta karasa ba. Nafi jiki a sanyaye tace sai dai me?? Ferry tace ” sai kinyi da gaske dan irinsu ko suna san abu in har ka nuna musu soyayya dayawa to fa zakasha wahala, kinada kyanki ga gashi gaki ‘yar chas in har kika bi yanda ya kamata Ashraf bazai miki wuyar samu ba.” Nafi ta kalleta sannan ta dan yi murmushin yake tace ” Ferry ni fa ba ‘yar gidan bace, na dade inaso in sanar da ku hakan.” Harararta Ferry tai tace ” Nasani ai.” Mamaki ne ya bayyana a fuskar Nafi ta kalleta tace ” How? When?” Ferry tai dariya tace ” kin manta nasan sunanki?sannan sanda muna Junior ai kowa yasan bafulatana ce ke kuma kema dakanki kin fada kince daga karamar hukumar gwaram kike.” Nafi tai dariya sannan tace ” lalai Ferry.” Ferry tace ” bansan matsayinki a gidan ba sai dai inaso ko ma meye matsayinki karki bari wannan ya rage miki daraja.” Nafi ta kalli jibiya tace “Jibiya lalai ki kiyaye yayan nan taki kwakwalwarta a cike take fam da plan.” Sukasa dariya, nan suka shiga hirar bikin jibiya wanda za’ayi bayan sun koma ba da dadewa ba. A ranar dai basuyi bacci ba dan hirar karshe a makaranta. STORY CONTINUES BELOW Washegari da safe kuwa suka shirya suka kamo hanya, Ya Nabil ne yazo ya d’aukesu, a hanya ma hira sukai tayi Nabil na kara sasu dariya dan mutum ne mai tsananin barkwanci. Nafi suka fara ajiyewa sannan sukai sallama, ganin gidan yasa Nabil ya kalli Ferry bayan Nafi ta shiga ciki yace ” Farida dama a gidan Marigayi Abbas Saleh take?” Ferry tace ” ka sanshi ne?” Nabil ya juyo yace ” kin manta? Ta kalleshi tace me fa? Ya harareta yace ” inda Dad yai aiki da ai company dinsa ne.” Ta mai kallan mamaki tace ” haba?inda ya ajiye aikin bayan mai company din ya rasu?” Nabil yace “Bingo! Kinsan ai da Secretary din marigayin ya fara daga nan har ya zama Chief Director.” Jibiya tace ” me yasa dan ya rasu ya ajiye aikin?” Nabil ya girgiza kai alamar bai sani ba sannan yace ” kawai dai nasan ya taba cewa mutuwar mutumin akwai conspiracy.” Sunyi mamakin jin hakan sai dai agun suka bar maganar sukai gaba. ******* Nafi kam bangaren Mumy ta fara zuwa bayan sun gaisa ta mata murnar gama makaranta sannan tace “taje tai wanka ta kuma ci abinci.” Nan Nafi ta mike ta fito tai b’angarensu, Little ba tanan dan dama tasan nazata sameta ba sakamakon jarabawar da sukeyi a makaranta. Wanka tai tana fitowa taga an aiko da abinci inji Mumy, sai data shirya tai sallah sannan taci abinci ta kwanta akan gado, ko minti goma batai ba bacci yai gaba da ita. Ashraf wanda ya kasa samun Little yana shigowa gida yai b’angarensu, knocking yai yaji ba motsi bai kawo komai ba dan baima san Nafi ta dawo ba ya murd’a kofar dakin. Tsayawa yai daga bakin kofa ya kura mata ido, a hankali ya tako zuwa cikin d’akin ya tsaya tare da kallan fuskarta, bacci take sosai ba wani kwalliya tai ba, ya kalli jikinta riga ce doguwa mai ba wai ta bacci bace sai dai ta bi jikinta ga hanun rigar karami ya mata kyau sosai ‘yar kanti ce. Kansa ya girgiza yace ” me kake kallo?” juyawa yai zai tafi yaga tad’anyi motsi, ya juyo ya kalleta sannan ya juya zai wuce.1 Hannunsa yaji an rike, juyowa yai tare da hadiyar wani abu, Nafi tace “Yaya?” Ta fad’a cikin muryar bacci, kallanta yai tare da dakewa yace “Yaushe kika dawo?” Ta saki hannunsa sannan tace ” d’azu.” Kai ya jinjina alamar to sannan ya kara kallanta, ta daure tace “me kake anan?” “Little, little nake nema.” Batanan, abinda ta fada kenan ta juya mai baya tare da rufe ido, ya kalleta, is that all? Yauma? Ba ko gaisuwa? Ya dauka ko in ya fqra tafiya zata kulashi amma sai yaji dif, ya juyo yaga har yanzu bata juyo bama, komawa yai rai a b’ace yasa hannu da karfi ya zaunar da ita. Kallansa tai cikin tsoro, tace cikin tsoro mai nai kuma?” Yatsa ya nuna mata yace ” ni wanene?” Tace “ban gane ba?” A zuciye yace “waye ni? Just answer nake so.” Tace ” Ya Ashraf mana.” Ya ce “ok good, in har zaki kirani da yaya ban isa ki gaidani ba ko me?” Kallansa tai sannan tadan shagwabe fuska tace “Bacci fa nakeyi ka tasheni.” What? Tace ” sannan naga kamar baka fiya san gaisuwa ba dan naga da in na gaida kai ba koda yaushe ma kake amsawa ba.” Wata irin dariya yai yace “And so?” Tace “nima shiyasa naga in kana cikin mood din amsawa sai inyi gaisuwar.” Kallan mamaki ya shiga yi mata, kanta ta d’auke ta juyar dashi gefe, a zuciye yasa hannu sai juyo da fuskarta ita kuma tai saurin gocewa gashi gaba dayanshi dama ya gama sakar jiki, ya kara sa hannu ai kam ta matsa da sauri ta koma can karshen gado. Mamaki ya kamashi yace ” ni kike gudun ma?” Ya fad’a tare da hawowa gadon yazo kamata ta tai saurin kwanciya, tare da yin rufda ciki. Babbakewa yai ya juyo da ita da karfi, nan shima kuwa ya fada kan gadon sukai facing din juna, kallan juna suka shiga yi, Nafi ta daure ta d’auke fuskarta, cikin wata irin murya yace “Yaushe kika zama haka?” Ta kalleshi gabanta na fad’uwa tace ” Na zama me?” Hannunsa yakai kan bakinta yace ” fitsarariya mana.” Hannunsa ta ture tace ” ni ka tashi ka tafi……….” Bakinta taji cikin nata, gaba daya numfashinta ne ya tsaya, shikansa bai san me yakeyi ba, sai dai ya kasa daina abinda yakeyi. Nafi anyi luf ana karbar sako, sai can ta farga da abinda sukeyi, tureshi tai iya karfinta, Ashraf takaicin kansa ya kamashi, da sauri suka mike zaune.1 Nafi ta sauka daga kan gadon har yanzu hannunta bai bar rawa ba tace “Yaya me kake yi hakan?” Jitai yace ” wannan ita kadai ce hanyar saita bakin da bashida kunya, ki cigaba da min fitsara ni kuma zan koya miki hankali.” Da sauri tai hanyar toilet tana ‘yan kokoni.” Ya bita da kallo, cikin takaicin abinda ya aikata ya mike, shikenan yasan ta gama rainashi yanzu kam, ya gaka jama kansa raini, amma me ya sashi yin hakan? Bayan ko Anisa da suke gida daya tun suna kanana bai taba sha’awar tabata ba har sai da sukai aure???? Itakam a toilet, gaban sink ta tsaya jikinta na bari……. Yau kwananta biyu kenan da dawowa, Little na zaune tana karatun jarabawa ita kuma Nafi tana zaune tana ninke underwears dinsu data wanke, Little ta kalli Nafi tace “Feenah haryanzu bakice komai ba.” Nafi tace “Name kenan?” Hararta Little tai tace “Alamin mana kinsan dai yanda yake neman sanin lokacin da zaki dawo.” Nafi ta ajiye ninkin sannan ta kalli Little tace ” Little nifa wlh ko kadan ba san Alamin nake ba, banaso sam na yaudareshi ne shiyasa kikaga ina baya baya dashi.” Little ta maida hankalinta kan Nafi tace “I know that, sai dai in har kikace da haka zakiyi soyayya kina ganin zai yiwu?” Nafi ta mata kallon alamar tambaya ? Little ta gyara zama sannan tace “tunda kikazo garin nan wa kika kula? Samari dayawa namin zancen suna sanki sai dai ganin yanda kike dauke fuska yasa kowa yake shakkar miki magana, sai yaushe ne zaki saki zuciyarki ki sami mai sanki saboda Allah?” Nafi a ranta tace “Little bazaki gane bane.” amma a fili sai tace ” Little nifa soyayyar ce sam bata gabana.” Hararta Little tai sannan tace “ko dai akwai wanda kike so?” Da sauri Nafi ta mike, sam bata kula karfen bra ya makale a rigar material din dake jikinta ba.” Kallan Little tai da sauri tai hanyar waje tana cewa “lalai Little na kula yau tambaya mara amsa kike neman yi.” Waje tai da sauri tana fita tai ajiyar zuciya daga nesa ta hango motarshi yayi parking, ta dan kurama motar ido sannan tadan harari gun tace “duk laifinka ne kasa Little na neman tsuyeni.” Tafiya ta fara cikin nata salon, shikuma ya fito daga mota ya tsaya kallanta, tun randa abin nan ya faru bai kara sata a idansa ba, sai dai ji yake kamar yayi wata d’aya bai ganta ba, pride dinsa kuma bazai bari ya nemeta ba da kuma tsoron karta rainashi. Ganin yanda yake kallanta yasa ta kara canza tafiya tare da dauke kai daga gunsa shikuma ya jingina da jikin mota, murmushi tai a ranta sannan ta cigaba da tafiya, sai datazo kusa dashi sannan ta kalleshi tace ” Yaya Ina wuni?” Bai bata amsa ba sai kallanta da yake ta karaso kusa dashi sosai sannan ta hade rai tace “shi yasa banasan gaisheka sai ka ga dama kake amsawa.” Ganin bashida niyar bata amsa yasa haushi ya isheta ta juya zata karasa kitchen, hannu yasa ya rikota harta giftamai kadan, ya dawo da ita gabansa, ta kara bata rai tace “Hanuna.” Bai saketa ba sai dai ya matso da kansa saitin kunenta jikinsa na taba nata kallansa tai gabanta na faduwa, ganin a waje suke. Jitai yasa hannunsa ta kugunta, tsoro ya kamata a hankali tace “Yaya me kake yi haka?” Bai tanka mata ba sai kara matsota dayai, tace “Yaya a waje muke fa me kake yi hakan?” D’agowa yai sannan ya mika kata bra d’in yace ” Bakya kunyar mutane susan size dinki?” Idanu ta zaro cikin tsananin kunya ta wafta tare da b’oyewa a cikin rigarta, da sauri ta juya ciki, tafe take tana sauri, shikuma sai murmushi yakeyi. Nafi tana shiga ta jefar da bra din akan gado tare da kwanciya itama da karfi ta hau birgima kamar karamar yarinya, Little ta kalleta tace “Me kuma ya faru?” Nafi tana juyi tace “shikenan na gama nikuma.” Little tace “menene wai?” Kai Nafi ta girgiza sannan ta d’an jade rai tace “Little bakiga bra ta makale ajikina ba sanda na fita?” Little tasa dariya tace “haba? Garin yaya!” Nafi ta baza tagumi tace “shikenan ni kuma.” STORY CONTINUES BELOW Kallanta Little tai tare da guntse dariyarta tace “to menene? Ai ba abin kunya bane, wani ne ya ganki?” Nafi ta dan harareta tace ” ba abin kunya ba kamar ya???” wayyo ni….” Little tai dariya tace ” to menene? Ai kowa yasan kinkai lokacin sawa kuma ansan haka kawai da saninki bazaki fita dashi ba.” Nafi ta kwanta tare da rufe kanta da bargo. Wayar Little ce tai kara ta daga tare da cewa to yaya. Tana kashewa ta kalli Nafi tace “Yaya yace ki amso kai lunch dinsa ki kaimai.” Ido Nafi ta zaro tace “ni kuma? Ina matarsa?” Little tace “inkinje wannan kya tambayeshi.” Gyara kwanciyarta tai little tace “ya?incemai bazaki kai ba.” Nafi tace “kice bacci nake.” Little tace “ba ruwana.” Tafi minti 15 akwance kamar bazata mike ba sannan ta tashi fuska a had’e tai waje, Little ta bita da kallo tare da dariya. Nafi kitchen ta nufa ta amso mai abincinsa sannan tai hanyar b’angarensa. Bayan ta kwankwasa ya zo ya bud’e tare da komawa cikin falo, Nafi kam tana shiga ta ajiye mai akan dinning ta juya da niyar fita, jitai ance ke zo nan. Cak ta tsaya bata kuma je ba haka kuma bata tafi ba, Ashraf dake zaune yana kallo yace “bada ke nake ba?” Nafi bata amsa ba, yace “Ke Nafisa!” Juyowa tai tace “na kasa tantancewa ko da ni kake shiyasa na tsaya.” Wani murmushi ya saki yace ” da alama mu goma ne a falon.” Ta kalli falon sannan tace “na sani ko matarka na kusa?” Kallan mamaki ya mata yace “Matartawa ke nake ce mata?” Fuska ta kara daurewa tamau tace ” to nima kuwa ba sunana haka ba.” Ta juya, jitai yace “Nafisa bakiji nace kizo ba?” Kallansa tai batace komai ba, yace “au yanzun ma da bra din kika fito?” Da sauri ta shiga duba bayanta ya saki murmushi, ganin ba komai yasa Nafi ta shagwabe fuska tace “haba yaya?” Mikewa yai ya karaso gunta sannan yasa hannu ya riko habarta yace ” ba na hanaki min fitsara ba? Ko rannan baki daddara bane?” Tace “yanzun kuma me nai?” Yace ” wlh kin canza gaba daya.” Ta kwace fuskarta tace ” ni ba wani canzawa danai.” Hannunta ya kama ya jata zuwa dinning ya nuna mata kujerar dake kallan tasa yace “zauna.” Kallansa tai tace ” inzauna inyi me? In ma abinci ne ni naci nawa.” Dariya taga yayi yace “Ohh abinda kikeso kenan? So kike ince muci abinci tare?” Ta zaro ido cikin mamaki tace “yaushe nace haka ko kuwa haka ka fassara?” Ashraf ya zaunar da ita sannan ya koma ya zauna, kallanta yai yace ” ki zauna ki jirani naci abinci.” Tace “ni? Akan me?” Yace “haka kawai.” Wata irin dariya tai tace ” wannnan kuma banaji aiki nane.” ta fada tana neman mikewa. Yace zauna. Kallansa tai fuska a hade, yace ” ba dake nake ba?” Zama tai tare da juya kai gefe, yace ” zubamin.” Tace “me fa?” Da ido ya mata alama da abinci. Tace “yaya nikam menai ma ne yau?” Kuramata ido yai yace “bansan ni kaina me nakeyi ba sai dai kawai naga inasan inga kinmin abinda nace.” Labanta tadan ciza sannan taja plate ta fara apkamai abinci sai data kusa cika plate din ya kalleta yace ” Me kike hakan?” Gabansa ta tura mai sannan ta mike ta fara tafiya, mikewa yai da sauri ya fizgota, tare da sata a bango, ta kalleshi idanunta sun fara ja, yace “wai Nafisa meke damunki?” Ta kalleshi tace ” na kasa fahimtar dalilin sani abubuwan nan sai dai yanzu na gane, u take me as a joke.” Idanunta ya kalla zuciyarsa na raya masa wani abun, ya daure yace ” joke? Taya zaki fassara shi a haka?” Hannunsa tadan ture batace komai ba ta juya zatai gaba, bai san sanda ya rungumeta ta baya ba, dif kamar an dauke wutar lantarki haka tai. Cikin wata irin murya wanda bata taba jinshi da ita ba taji yace ” Ni kaina bansan me nakeyi ba.” Shiru tai sai dai jikinta duk ya mutu, yacigaba ” shiyasa nakesan ki cigaba da zama inda nake har sai na san me nakeyi tukunna.” Shiru tamai hakan yasa ya juyo da ita yace “Uhmm?” Kallansa tai sannan tace ” in zauna a kusa dakai kamar yaya?” Ya dan juya kai yace “kamar yanda na kiraki yanzu.” Hannunsa ta dan zare tace ” after that?” Kallanta yai tace ” eh after that, then what?” Ya shafa kansa yace ” ban fara wannan tunanin ba.” Murmushi tai sannan tace ” I am sorry.” Kallanta yai yace ” for what?” Tace ” bazan iya abin da kace ba, me yasa a koda yaushe zuciyarka ita kadai ce mai amfani agunka? Me yasa baka tunanin tawa?” Ya kalleta yace ” Me kike nufi?” Kai ta girgiza sannan tace ” Ka dinga ajiye matarka akusa dakai ba ni ba, nima daga yanzu zan fitar da wanda naga yana sona inyi aure.” Tana kaiwa nan tai waje, kallo ya bita dashi sannan ya runtse ido ya bud’e tare da naushin iska yace ” Ashraf meke damunka? Me yasa duk lokacin da ka shirya abu daidai pride dinka ke hanaka???? Wata iska ya furzar ta takaici….. Nafi kam tana fita hawayen datake boyewa suka fara zubowa tafiya kawai takeyi sam bata kula da Asim ba wanda suke zaune suna hira. Shikuma yana ganinta ya mike tare da shan gabanta yace “ke yar iska?” Kallansa tai da jajjayen idanunta, yasa dariya yace “au har kwarton naki ya fara b’ata miki rai? Ki dawo guna ni zankula da ke sosai.” Hararsa taicikin takaici tace ” ni nafi karfin karuwa kuma inma karuwancin ne mai zanyi dakai? Tana kai nan tai gaba, Asim kam ya kai kolowa gun bacin rai, ya juyo da niyar zaginta yaga wayam, hucci yai yace “lalai za’a kai gawar ‘ya garinsu….” Nace hmmmm…… Nafi kam a falo ta zauna ta dafa kanta itakam Allah ya yaye mata wannan abun dan bata ganin akwai riba a cikin wannan san da takema Ashraf. Kwanciya tai daga nan bacci yai gaba da ita akan kujerar. Sai la’asar ta tashi tana shiga taga Little ma bacci take nan tai sallah sannan ta tasheta itama tai, kitchen ta nufa dan kara samun fasaha akan girki. Sai 6 ta fito tana shiga bayan sunyi magrib aka aiko wai ana sallama da ita, mamaki ya kamata ta tsare Little da ido, Little tace ” ba Alamin bane Allah dan shi baima san kin dawo ba.” Nafi tace “to waye??” Little tai murmushi tace “ki shirya sai ki dubo mana.” Harararta Nafi tai tace “wani shiri kuma? Bansan waye ba kawai sai in hau kwalliya sai kace mai neman saurayi?” Little ta sa dariya tace ” to da mecece?ai duk budurwa nema take har sai ta samu tsayaye.” Nafi ta tabe baki ta zari mayafi tai gaba Little na tsokanarta. Waje ta fita mota d’aya ce a gun hakan yasa ta tsaya daga dan nesa tana tunanin karasawa, fitowa yai tare da zama a saman motar yace “My Feena ko sai na zo da kaina?” Jin muryar Nabil yasa tai murmushi sannan ta karasa, kallansa tai cikin zolaya tace ” da alama rashina ya hanaka sukuni?” Ya dafa kai yace “Feenah taba kiji inaji zazzabi ne ke neman kamani saboda missng dinki.” Tai dariya tace “Ya Nabil to ya? Nayi mamakin ganinka a daren nan.” Ya kalli agogo yace ” ko isha’i batai ba shine dare?” Tai dariya sannan tace “Ina Aminiya?” “Tana gida nima wucewa nazo yi nace bari na tsaya mu gaisa.” Murmushi ta sakeyi tace “aikam na gode.” Ya kalli gidan yace “dama a gidan Marigayi Abbas kike?” Kallan mamaki tamai tace “kasanshi ne?” Dariya yai yace “ina fa mutumin daya rasu kafin muyi wayau.” Tace “then?” Yace ” A company dinsa dai Dad yai aiki.” Cikin mamaki tace haba? Ya daga mata kai sannan yace “Amma tun bayan rasuwarsa shima ya ajiye aikin.” Nafi tace “me yasa?” Iska ya dan tara a bakinsa sannan ya furzar yace “bansan dalili ba.” Kallo ta tsareshi dashi tace ” Kace wallahi.” Yai murmushi yace ” me nene matsayinki a gidan?” Ta kalli gidan sannan tace “nima bansani ba ganinan ne dai kawai.” Dariya yasa yace “ban gane ba.” Tace Wallahi dagaske.” Kallan mamaki ya mata yace ” kiyi a hankali to da irin wannan gidan manakisa da sharrinsu yawa gareshi, dan mutuwar Abbas din……..” Bakinsa ya guntse jin yana shirin yin baran barama, Nafi ta kalleshi fuska dauke da mamaki tace ” Me? Akwai sa hannu ko me?” Juyar dakai yai yace ” Hmm yaushe zakizo gida?” Tace “Ya Nabil?” Kallan gate yai yace “ga wani can ya fito da mota.” Nafi ta kalli gun, motar Ashraf ce idanunta ta kaida kan Nabil tace ” Ya Nabil dan Allah me ka sani??” Kifta ido yai yace “bazai miki fada ba?” Hade rai tai tace ” akan me kenan?” Zaiyi magana yaga an dallesu da fitilar mota wanda sai da Nafi ta juya, ta tabbata so yake yaga waye, shiyasa tana juyawa ta maida kanta gun Nabil. STORY CONTINUES BELOW Ashraf kam wanda suka fito shida Anisa. Ya tsaida mota batare da ya kashe fitilar ba, Anisa ta kalleshi ya had’e rai tare da kafe Nafi da ido, mamaki ya kamata. Shikam Nabil kallan Nafi yai yace ” Feenah da alama ke ake jira kar inja a miki fada bari na tafi.” Da sauri tace a’a yaya taimakamin karka tafi please. Yace “Ba kya tsoro?” Kallansa tai fuska dauke da murmushi tace ” mu shiga motarka mudanyi gaba please, sannan banaji zan barka ka tafi baka karasa fadar abinda zaka fada dazu ba.” Kallan mamaki ya mata, ta shagwabe fuska tace “please ” Sauka yai sannan ya zagaya ya bud’e mata mota ta shiga sannan shima ya shiga tare da tada mota. Anisa ta kalli Ashraf tace “wai me mukeyi anan ne?” Bai ma san tanayi ba dan wani irin abu ne ya tasomai yana ganin sun hau kan titi ai kuwa shima ya taho da gudu da mota ya sha gabansu saura kiris motoci biyun su bigi juna, Nafi kam da Anisa duk sun runtse ido kowa na tsoron abinda zai faru shikanshi Nabil ya tsorata, Ashraf a zuciye ya kashe mota sannan ya fito ko kofa bai rufe ba yazo Kofar da Nafi take ya bud’e da karfinsa. D’agowa tai cikin tsoro tana kallan idanunsa da suka kada sukai ja sai hucci kawai da yakeyi, hannu yasa ya fizgota da karfi, Anisa ganin haka yasa ta fito tare da shan gabansu tace “Ya Ashraf me kakeyi hakan? Ina zaka bayan kasan unguwa zamu?” Kallanta yai cikin idanunsa da sukai ja bai bata amsa ba kawai ya zagaya ta gefe ya sa Nafi a bayan motarsa ya shiga ba tare da ya kuma kallan Anisa ba yai reverse sannan ya ja motar a zuciye. Nabil kam wannan abu ya d’aure mai kai shima a hankali yaja tasa motar yai gaba yabar Anisa wacce ta tsaya kamar gunki. Ta dade agun kafin ta koma gida, gun Umma ta nufa tai sa’a Asim nanan nan ta zayyane musu abinda akai tare da fashewa da wani irin kuka. Umma ta mike tsaye tace ” Asim dole ne musan abinyi dan nikam na gaji da wulakancin wannan dan marasa tarbiyar.” Asim a zuciye yai waje ya nufi bangaren mahaifinsa…… Shikam Ashraf gudu kawau yakeyi, Nafi kam tayi shiru a baya sai dai har yanzu tsoron abinda Ashraf yai takeyi, gashi sai gudu yakeyi ga dare. Addu’a kawai take a ranta, can karshen titin Naibawa ya tsaya, wajen fly over sannan yai parking ya fito tare da bud’e kofar Nafi. Ta kalleshi cikin tsoro. “Fito!” Abinda taji yace kenan, ta danne tsoro sannan tace “in fito inyi me??” “What?” ya fada yana kara kallanta. Ta murguda bakinta tace ” Haka kawai ka jawoni ka kawoni nan sannan in fito inyi me?” Kallan mamaki ya mata tai saurin kallan gefe, shiga yai kusa da ita tai saurin matsawa tare da harde hannayenta ta maida kallanta gefe. “Waye waccan d’in?” Tace wa kenan? “tambaya ma kike? Wanda yake neman sa ki a mota ku tafi wani guri a daren nan.” Baki ta turo tace “Wani ne.” Yace “wani? Bakida hankaline bakisan mutum ba kike neman shga motarsa? In ya lalataki fa?” Dariyar da ta nemi taho mata ta guntse tace ” to meye a ciki? Tunda so na yake?” Me? Bakida hankali ne?” ya fada a zuciye, ta kalleshi tace ” ni so nake ma in aureshi dan na gaji da zama a inda na sona ake ba.” ” who said that?” shikansa baisan sanda ya fadi hakan ba. Kallan sa tai fuskarta da alamar tambaya, ya juya kai sannan yace ” karki kuskura inkara ganinki da wani namijin balle har ki samu mai dariya ko shiga motarsa.” Tace” Akan me?” Yace ” Tambaya ma kike? So kike wani abu ya sameki ace nine?” Haushi ya kamata ba haka taso ji ba, ta juya kanta tace ” bazan iya rabuwa da shi ba.” Hannu yasa ya rike kafadarta da karfi tare da juyo da ita saitinsa, yace ” ni kike fadawa haka?” Baki ta turo batace komai ba, kallanta ya tsaya yi, batai auni ba taji bakinta cikin nasa, nan ta fara kokarin kwacewa sai dai ya riketa da kyau tun tana kokarin kwacewa har tai la’asar….Wani sakon ni suke ba juna wanda su kadai suka san ma’a narsa, sun dade sosai a haka sannan a hankali suka saki juna, idanuwansu dake lumshe suka bud’e a hankali. Idanunta suka ciciko cikin sanyin murya tace ” Yaya why are u doing this to me?” Jawota yai jikinsa ya rungume ta yace ” Nafeesa ni kaina bansan me nakeyi ba.” Tace ” ba so na kake ba me yasa kakeyin hakan to?” Ya kara kankameta yace ” Na rasa me ke damuna, ni kaina abin na damuna.” Ta dago da jikinta tace ” karka sake tabani har sai ka san abinda ke damunka.” Kallan mamaki ya mata yace ” Ke halal dina ce bawai haram dina ba.” Wani murmushin takaici tai tace ” Halal? Since when did i became your halal?” Yace ” What?” Ta rufe ido sannan ta bud’e tace ” Halal din da ba wanda ya sani? Halal din da ni kaina ban san halal bane? Halal din da kake tsoron kar mutane su sani? Halal din da kai kanka baka tabbatar dashi ba?” Kallanta yai sai dai kalamanta sunsa jikinsa yai sanyi, ta sake murmushin takaici tace ” ko ma meke damunka nidai karka kara tabani sai ka tabbatar dashi sannan sai na yarda da hakan.” Tana kai nan ta juya kanta tare da share kwallar da ta zubo mata. Jiki a sanyaye ya bud’e motar yai waje ya koma mazauninsa ya zauna a hankali ya tashi motar sukai gaba. Yana kallanta ta madubi jefi jefi tana share hawayenta, ya sani sarai shine silar kukan ta, me yasa yake zama dalilin hawayen ta? Why did he always cause her pain?” Jiyai gaba daya jikinsa yai sanyi jiyake kamar ya jawota jikinsa ya lallasheta, bayaso ko kadan yaga tana kuka dan har zuciyarshi abin ke tabawa…….