DIYAM CHAPTER 8

DIYAM CHAPTER 8

Abinda na tarar a gidan mu dana koma banji dadinsa ba, harkoki kawai ake yi ana wadaka da abinci, wato shi wanda akayiwa mutuwa shi kadai ta shafa ko? Shi kadai yasan me yake ji? Wato mutuwa ba zata zamo izna ga sauran mutane su nutsu su daina biyewa duniya ba? An bubbude koina har palon Baffa mutane ne a ciki, bedroom dinsa ne kawai a rufe.+ Dakin mu na wuce da niyyar in kwanta inji da abinda yake damuna amma sai na tarar da yammata ne fal a dakin, suna ta dauke dauken hotuna da kallon videos a waya suna kyalkyatar dariya. Ko magana banyi musu ba na fito da shiga part din Ummah, babu kowa anan kofar palon ma a saye take dan haka na tura na shiga na mayar na rufe. Direct dakin Sadauki na tafi na bude na shiga. Dan karami ne dai dai size din dakin mu ni da Asma’u, katifa ce kawai a dakin sai wardrobe, standing fan, sai kuma tarkacen takardu a gefe. Sai hoto guda daya a jikin bango. Na tsaya a gaban hoton ina kallonsa kamar yau na fara ganinsa, Ummah ce da Baffa a zaune akan kujera, sai Sadauki a durkushe a gaban baffa sai ni kuma akan cinyar Ummah da shubeya a hannu na. Na tuna sanda aka dauki hoton da wata sallah ne lokacin Inna tana da cikin Asma’u, babu yadda Baffa baiyi ba ita ba akan tazo ayi hoton taki tace sai dai yaje mu dauka daga ita sai shi sai ni. Shi kuma yaki. Na zauna a gaban hoton ina jin kewarsu tana kara mamaye ni, ina jin kamar inyi rewinding din rayuwar mu ta dawo baya in cigaba da ganin su, in cigaba da ganin Sadauki a gidan mu. Inna tuna cewa Sadauki bai san anyi mutuwar nan ba sai inji zuciya ta duk ta narke, bansan yadda zai dauke ta ba, ina gudun kar wani abun ya same shi shima. In na tuna yanzu bashi da kowa a duniya sai inji kamar in tashi in koma asibitin in zauna a wurinsa. Hope dina daya shine na yaya ladi zata kaishi gurin mahaifinsa tunda nasan dole zata san waye shi, in ma bata sani ba shi wanda ya hada auren ai zai sani. Amma kuma in nayi wannan lissafin sai inji zuciya ta ta kara tsinkewa saboda tunanin rabuwa da Sadauki. Kuma what if shi uban baya bukatarsa? What if shine yakori Ummah da jariri yace baya so? Anan dakin bacci mai nauyi ya dauke ni saboda kwana ukun nan duk bana samun bacci mai nauyi. Na jima ina yin baccin sai naji magana kamar a tsakiyar kaina ance “Diyam? Uban me kike yi anan?” Na tashi zaune ina mitstsika ido amma na kasa bude idona saboda fitilar da aka haske ni da ita. Aunty Fatima tazo ta kama ni muka mike “tun dazu ake ta neman ki, babu inda ba muje ba duk hankali ya tashi mun dauka an sace ki ne” nace “kuyi hakuri, bansan bacci ya dauke ni ba, hayaniya ce ta yi yawa acan ni kuma ina so in zauna ni kadai” sai kuma sukaji tausayina, amma inna sai da tace “kuma ki rasa inda zaki je ki kwanta sai nan dakin? Ba gwara ki tafi makota ba?”. Sai da aka sake kwana biyu sannan na kuma samun dama na tafi dubo Sadauki, wannan karon tare da Rumaisa muka tafi kuma sai da na saka tayi min alƙawarin ba zata gaya wa kowa ba. A zaune muka tarar dashi yaya ladi tana ta fama dashi akan yaci abinci. Tun a fuskarsa na gane yaji dadin zuwana sosai. Yace “kun taho da waya? Ina son in kira Ummah, ina so kuma inji ya jikin Baffa” na girgiza masa kai nace “bani da waya ai ka sani, kuma bansan zaka bukata ba shi yasa ban karbo wata na taho da ita ba” ya jingina kansa a jikin gado yana runtse idonsa yace “a gurin da muka yi accident aka dauke min waya ta, ita kuma wannan tsohuwar wai tata ta lalace” na jawo kujera na zauna ina karbar kwanon abincin daga hannun yaya ladi nace “duk suna lfy Sadauki, ummah cema tace inzo in duba mata kai. Kasan ba zata iya barin Baffa ba Musamman yanzu da bashi da lfy” ya gyada kai yana murmushi yace “ji nake yi kawai ina so in ganta” ina kallon Rumaisa ta tashi ta fice daga dakin. Na zuba masa tuwon alkama miyar danyar kubewar da yaya ladi tayo masa na zauna ina bashi a baki, ba musu yake karba idanuwansa a kaina ko kiftawa baya yi har sai da ya cinye wanda na zuba masa tas, yaya ladi tace “oh, tun safe nake fama da shi akan yaci abinci yaki ci, shifa yace inyi masa tuwon amma shima ya bar ni da abina, amma da yake ke kece gashi nan ai ya cinye tas” ya juya yana kallonta yace “baki iya tarairayar miji ba ne shi yasa” da alama so yake suyi wasa irin yadda suka saba amma sai ta kasa mayar masa, sai ta hau tattara kayan gurin ta fita dasu. STORY CONTINUES BELOW Na saka tissue ina goge masa bakinsa sai ya rike hannun yana kallona cikin ido yace “kin rame, kinyi duhu, idonki sun kumbura” na kirkiro murmushi nace “ka manta daga makaranta na dawo, kuma exams muka gama bama samun isashshen bacci” ya saki hannuna yace “fada min gaskiya, ya jikin Baffa, is it bad? A ina ya karye?” Na kasa kallon idonsa nace “a hannu ne kuma da sauki” yace “hannu kuma? I thought kafa ce ma saboda shi yake driving” na dago ina kallonsa da mamaki dan nasan Baffa hardly drives in dai da Sadauki a motar. Nace “me ya faru?” Ya sunkuyar da kai yace “rami muka daka sai taya ta fashe, daga nan motar ta fara a dungure akan titi, sai data daki wata bishiya sannan ta tsaya” na gyada kaina ina rike hawaye na. Muna komawa gida muka tarar da inna a tsakar gida tana alwalar magrib tace “daga ina kuke?” Rumaisa tace “makota muka shiga”. Shikenan bata kara ce mana komai ba. Washegari bayan nayi sallah na kwanta akan kujera amma ba bacci nake yi ba, na rufe idona ne kawai saboda bana son kowa yayi min magana a lokacin. Ina ji akayi ta hidimar abinci sannan aka fito palo aka baje kowa yana ci ana ta hira, cikin hirar naji Inna tana bawa yan uwanta da suka zo daga Kollere labari: “Wallahi in gaya muku, daga zuwanta da yaron nan ya dauki son duniya ya dora akansa, komai Sadauki komai Sadauki, ni na dauka ko rashin haihuwa ne ya saka haka amma sai gashi bayan na haifa masa yaya har biyu amma sadaukin nan dai ya fiye masa duk su biyun. To in ba asiri ko maita ba me zai jawo haka? A ce agolan da aka haifa a wani gidan koma a wani titin ne oho, tunda babu wanda yasan ubansa amma ace yafi yayanda mutum ya haifa da cikin sa? Ai shari’a tsakani na da zainabu sai a lahira za’a karasa ta. Tun yaron nan yana dan mitsitsinsa aka fara bashi mota a gidan nan, kullum ‘sadauki zo ka kaini guri kaza, Sadauki zo muje guri kaza’ nayi magana amma a banza tunda dama ni ba jin magana ta yake yi ba. Shine ranar nan yace “Sadauki zoka kaini Taura mu dauko Diyam’ to gashi nan bai kaishi taura ba ya kaishi lahira” naji kaina ya sara, ina so in tashi in gaya mata cewa ba Sadauki ne yake driving a ranar ba amma nasan ba yarda zata yi kuma zata tambayeni wa ya gaya min.2 Wata ta tambayeta “to ina yaron yake yanzu?” Tace “yana asibiti yana karbar magani, kinsan irinsu bada wuri suke mutuwa ba” sai na tashi tsam na wuce su na shiga daki. I can’t take sunan sadauki da sunan mutuwa a sentence daya, not now da nake ganin ya samu sauki sosai. Not now da nake ganin nafi bukatar safiye da koyaushe. Washegari akayi sadakar bakwai. Jama’a sun taru sosai bangaren Baffa da na Ummah, ga kuma makota da abokan arziki. Yaya ladi ma da sassafe tazo ta bude dakin Ummah inda mutanen su suka zauna. Ana gama yin adduoi aka yi sadaka sai kuma kowa ya fara watsewa, har yan Kollere ma duk sun gama shirin su ana gama wa suka yi sallama suka dauki hanya. Muma kuma sai Inna ta fara hada mana kaya amma ni sai na koma na zauna a tsakar gida na takure a guri daya ina sheshshekar kuka. Yanzu shikenan barin gidan mu zamuyi? Gidan da aka haife mu muka tashi a ciki, me yada zamu barshi mu koma gidan wasu mu zauna a karo? Bayan muna da rufin asirin mu. Ina kallo aka fara fita da kayan mu ana zubawa a motar da Alhaji Babba ya aiko da ita. A lokacin ne kuma ya shigo. Kansa still a nade da bandage hannunsa kuma sanye da carnula. Ya tsaya yana rike da kofa for support idanuwansa a kaina, na mike nima ina kallonsa ina hango tsantsar tashin hankali a idonsa. Ko ba’a gaya min ba nasan ya sani. “Ina Ummah?” Ya tambaye ni da wata irin murya, sai na fara sheshshekar kuka na kasa ce masa komai. A lokacin ne Inna ta fito da wani akwati a hannunta ta ajiye tana kallonsa tace “sun sallamo ka kenan, dama yanzu nake tunanin yadda za’ayi a fitar maka da kayanka zamu rufe gida” ya kalleta kawai sannan ya sake mayar da dubansa kaina yana kallon yadda nake kuka babu sauti, hawaye wani na korar wani. Sai ga yaya ladi ta shigo afujajan, tana ganin shi ta sauke ajjiyar zuciya “yanzu shine ka fito daga asibitin ka taho nan Aliyu?” Kallo daya yayi mata sai ta saka kuka itama. Na tafi a hankali har inda yake tsaye na rike hannayensa a nawa, sai kuma na dora kaina a kirjinsa a hankali nace “Sadauki Ummah ta tafi ta barmu, Baffa ma ya tafi ya barmu, sun mutu Sadauki ba zamu sake ganin su ba. Mu dasu sai dai muyi musu addu’a kuma sai kuma a lahira in munje muma” Baice min komai ba bai kuma yi magana ba amma ina jiyo yadda zuciyarsa take bugawa kamar zata bar jikinsa, ya saka hannu ya ture ni daga jikinsa ya fara tafiya kamar zai tafi dakin Ummah sai kuma ya juyo, yayi kamar zai fadi na tafi zan rike shi sai ya dakatar dani da hannu daya daya hannun kuma ya dafe kirjinsa dashi. Ya dan jima a haka sannan ya sake straightening ya doshi hanyar waje, da sauri ni da yaya ladi muka rufa masa baya muna kiransa amma sai Ummah ta damko rigata a dawo dani baya “in kika bar gidan nan sai na kakkarya ki” ta harari waje “muma duk marayun ne, mun rasa iyayen mu kuma mun hakura”.2 Sai daga baya na fahimci ashe wasu kawayen Ummah ne suka je duba shi a asibiti shine suka yi masa gaisuwa, basu san cewa bai sani ba, shine ya gudo daga asibitin ya taho gida dan ya tabbatar. Ni dai a bangare na zan iya cewa tunda akayi rasuwar nan banyi kuka mai yawa irin na ranar nan ba dan a tsakar gida na zauna nayi tayin abu na, ina kukan tausayin kaina ina kuma kukan tausayin Sadauki. Menene makomar mu ? Menene makomar soyayyar mu? Babu wanda ya kula ni sai Asma’u da take makale dani tana taya ni kukan itama. Can naji Inna tana cewa “su kenan kayan sun kare, in muna bukatar wani abu ko Diyam sai tazo ta daukar mana tunda babu nisa” Mama tazo ta tashe mu ni da Asma’u “ku daina kuka kunji? Ai ba barin gidan kuka yi ba gaba-daya zaku dawo in innar ku ta gama takaba” na gyada mata kai kawai. Muna ji muna kallo aka tisa keyar mu zuwa waje aka rufe gidan, a raina ina tunanin kayan Sadauki fa? Kayan Ummah fa? Ai bamu kadai muke da gidan ba tunda dai a tunani na Ummah tana da gado dan haka Sadauki ma yana da gado kenan. Ina shiga mota kamar ance in kalli side sai na hangoshi a tsaye a jikin bishiyar da take opposite gidan mu, hannayensa a rungume a kirjinsa, idanunsa a cikin nawa. Nayi kamar zan fita sai Inna ta tura ni ciki ta shigo ta rufe kofa. Driver kuma ya tayar da mota muka tafi. Na juya waiwaya baya ina hangoshi ya matso tsakiyar layin mu yana kallon motar mu har muka sha kwana na daina ganinsa. Na juyo idona ya sauka akan dashboard din motar, agogo na kalla,time 3:15 date 25th August and it occurred to me cewa yau ne ranar Birthday dinsa, a yau ya cika shekaru ashirin cif a duniya. So young and so alone. Sai na rufe fuskata da hannayena ina sake wani sabon kukan.3 Assalamu alaikum wa rahmatullah Ina neman afuwar wadanda littafin Diyam ya saka kuka a kwana biyun nan, ina rubutu ne dan in faranta muku badan in bakanta muku ba. Amma ina so ku sani ita rayuwa is full of ups and downs dole sai ansha wuya sannan za’a sha dadi. Ina so duk sanda kuke karatu ku saka a ranku cewa kirkirarren labari ne, non of this happened in real life duk da cewa zai iya faruwan. But labarin Diyam kirkirarren labari ne.2 Daki ne aka bamu a gidan Alhaji Babba, dakin a babban palon gidan yake. Ciki daya ne da banɗaki mai dauke da gado da wardrobe a ciki, asalin dakin an yi shine saboda baki in sunzo daga Kollere anan suke dauka amma sauran matan gidan kowa in tayi baki to part dinta suke tafiya. Muna zuwa matan gidan duk suka firfito harda Hajiya Babba da kanta, aka zauna a palo ana ta kara yiwa juna gaisuwa da kuma jajanta abinda ya faru sannan aka saka yan aiki suka kara gyara mana dakin aka kai mana kayan mu can sai kuma kowa ya watse ya bar mu mu kadai.1 Nina fara tashi na shiga dakin da aka bamu ina kare masa kallo, babu laifi yana da girma kuma da toilet a ciki amma kuma it doesn’t change the fact that aro aka bamu, aron kuma da nia ganina bama bukata. Na tuna yawan dakunan da suke gidan mu, Inna daki biyu da palo, Ummah daki biyu da palo sannan ga dakin Baffa ciki da palo ga kuma dakin waje, amma wai duk mun ajiye su mun dawo daki daya mun zauna da sunan taimako, taimakon me? In taimaka mana za’ayi ni a ganina ai food stuff ya kamata ake kai mana can gidan mu kamar monthly haka ko duk sanda aka samu dama, ko ake bamu kudi muna siyan abin bukatun mu da kan mu amma ba gurin zama muke bukata ba. Kuma ko kudin ne ma ni aganina zamu iya kula da kan mu ba sai mun dogara da kowa na. Yes, Baffa ya mutu amma bai bar mu fakirai ba, ya bar garejin sa da yake running for over twenty years, zamu iya cigaba da running kayan mu da kan mu, Sadauki can do that tunda yasan komai dashi ake komai kuma duk costomers din Baffa sun san shi. Ni a ganina da mun yi zaman mu a gidan mu mun dora Sadauki akan komai kuma nasam as hard working and dedicated as he is zai iya yin komai. Ya cigaba da zamansa a gidan for security tunda za’a ce ba zamu zauna mu kadai babu namiji ba, in ma kuma Inna bata son zamansa a cikin gidan tana ganin ba muharramin mu bane ba zai iya zama a dakin waje ai, kuma yadda yake da kwarjini din nan babu wanda zai kawo mana raini a unguwa. Sadauki yana da gado a gidan da garejin, so it will be a mutual relationship wanda ni nake ganin mu zamu fi benefitting akan sadauki.1 Ina ta tunanina har Inna ta shigo tana ta jera mana kayan mu a wardrobe din dakin, Asma’u tana tayata tana kuma mitar cewa wardrobe din tayi mana kadan sai dai mu bar wasu kayan a cikin akwati. Bayan sun gama na tashi na sake goggoge dakin na wanke toilet na jera mana toiletries dinmu da kuma kayan shafe shafen mu, sannan nayo wanka da alwala nazo nayi sallah tare da jera adduoin neman nasara akan Inna in samu ta saurare ni ta kuma yadda da shawara ta. Da dare sai ga kwanukan abinci nan daga duk matan gidan kowa ta zubo ta aiko mana dashi, Inna ta karba tayi godiya amma daga ni har ita ba wani cin kirki mukayi ba Asma’u ce ta danci da yawa. A lokacin da muke cin abinci ne naga chance dina na magana da ita dan haka na zayyane mata duk tunani na da plans dina na kara da cewa “inna in mukayi hakan kamar mun dogara da kan mu kenan, ba ruwan mu da abinda za’a bamu da abinda ba za’a bamu ba. Duk wanda ya ke ganin zai taimaka mana saboda zumunci sai yaje har gidan mu ya taimaka mana in ma ba’ayi mana ba bamu da damuwa tunda muna da abin hannun mu. Inna dan Allah ki duba maganar nan”. Tunda na fara ta ajiye spoon dinta tana kallona har na gama sannan ta fara girgiza kai tana kallona tace “yayi daidai Diyam, ya kamata a jinjina wa wannan tsarin naki. Amma bara in tambayeki, sanda kike yin wannan tsarin mune a ranki ni da Asma’u ko kuma bakin yaron can? Iye? Wato bakin cikin ki shine mun taho nan gidan an raba ki da shi shine kike so mu koma saboda ku cigaba daga inda kuka tsaya ko? Kuma ke yanzu a tunanin ki duk duniya in rasa wanda zan dauki ragamar rayuwata ni da yayana in bawa sai wannan yaron? Bani da yan uwane? Ko shi mahaifinku bashi da yan uwan da zasu kular masa da sana’arsa su kuma kular masa da iyalinsa? Ai ina sane na karbi shawarar Alhaji Babba ta cewa mu dawo gidan sa mu zauna saboda in raba ki da wannan yaron. Ina so ki saka a ranki cewa Alhaji Babba yayi mana mutunci yayi mana karamci daya dauko mu ya kawo gidan sa cikin iyalinsa saboda baya son mu zauna mu kadai cikin kunci da kewar mahaifinku dan haka daga ni har ku kamata yayi mu gode masa mu kuma yi iyakacin kokarin mu gurin faranta masa. Maganar gareji kuma shi Alhaji Babba da yake da mutum ne mai budadden ido kuma wanda ya san mutane na tabbatar zai san abinda ya dace ayi dashi. Magana ta karshe Diyam, daga yau sai yau, kar ki sake yi min maganar yaron nan”. STORY CONTINUES BELOW Bayan na kwanta na jawo bargo na lulluba sai na tambayi kaina ko a ina Sadauki zai kwana? Ko a wanne hali yake ciki? Sai kawai naji baccin ya dauke daga idona baki daya. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan in samu in san halin da yake ciki. Kwanan mu biyu gidan Alhaji Babba kuma so far bamu da matsala. Muna samun kulawa da sympathy sosai daga jama’ar gidan amma ni a gurina na gaji da “Allah sarki” da “kuyi hakuri kunji” da kullum akeyi mana wanda babu abinda yake rage min a zuciya ta sai ma kara karyar min da ita da yake yi. Sannan kuma ga tunanin Sadauki daya addabi zuciya ya kullum sai karuwa yaje yi har cikin baccina wanda da kyarnake samu nake yi amma mafarkin Sadauki ne, ko inyi mafarkin rayuwar mu a baya ko kuma inyi mafarkinsa wai shi kadai a titi, har ganinsa nake yi a kwance abskin hanya ruwan sama yana dukansa duk kuwa da cewa nasan yaya ladi ba zata rabu dashi a titi ba, akwai makotan mu da akayi zaman mutunci dasu nasan ba zasu barshi a titi ba, akwai kuma marikin Ummah nasan shima ba zai bar Sadauki a titi ba, wannan sai yasa nayi tunanin to in duk wadannan ba zasu barshi a titiba why Inna? Ita me yasa ta barshi a titin ba tare da ko kayan sawa ba, wacce irin zuciyace da ita? Me yayi mata mai zafi haka? Bayan mun kwana hudu Mama tazo dan ganin yadda mukayi settling down, ta kuma taho mana da yan abubuwan da take ganin zamu bukata. Bayan sun kebe da inna ne take cewa “ni kuwa Adda ina so muyi magana dake a kan yaron nan dan wajen zainabu. Wallahi ranar nan ba karamin tausayi ya bani ba ke kuwa dan Allah ki sauko da zuciyarki akan sa, ji nakeda zainabu kukayi kishin ku kuma zainabu yanzu kasa ta rufe fuskarta haka zalika shima wanda akayi kishin a kansa, shi kuma yaron ina ruwansa?”. Inna ta kuta tace “ni yanzu wani abu kika ga nayi masa, ko kallon banza banyi masa ba ballantana tsawa ko hantara. Abinda nace shine babu ruwa na dashi yayi gabas inyi yamma tunda wanda ya haɗa din ya raba yanzu. Ba shikenan ba.” Mama tace “amma at least magana mai dadi ma ai sadaka ce musamman ga maraya, yaron nan bashi da wani gata fa yanzu sai Allah” Inna tace “wai ni Hafsa kin manta da irin wahalar da nasha ne a dalilin uwar yaron nan, kin manta da irin kiyayyar da aka nuna min saboda ba’a aure ta ba? Saboda ita ake so bani ba? Kin manta? Kin manta har sakina akayi a kanta aka kuma dauki yata aka bata. Babu irin kokarin da banyi ba dan in jawo hankalin mijina zuwa gareni amma har ya bar duniya idanunsa ita suke kallo, zuciyarsa baki daya tana gunta duk kuwa da cewa nice uwargidan sa, nice uwar yayansa, ni ce yar uwarsa kuma ni ce wadda ya aura a budurwa ita kuma bazawara. To yanzu sai kiga laifina dan nace bana bukatar duk abinda ya shafe ta? Dan nace bana son ganin abinda zai tuno min da ita?” Mama tayi ajjiyar zuciya tace “shikenan. Allah ya kara sanyaya miki zuciyarki amma zan sake tuna miki da cewa yaron nan yana da gado a dukiyar da hamma Usuman ya bari, dai dai abinda zaki samu shima haka zai samu shida yaya ladi. Dan Allah Adda a fitar musu da abinsu a basu kinsan shi gado wuta ce, annabi ya fada cewa da mutum yaci gadon maraya gwara ya cika cikinsa da wuta.” Inna tace “wannan kuma masu rabon gadon ai sunsan wannan karatun, kuma nasan zasu basu abinsu duk samda aka zo rabawa” Mama tace “yaushe za’a zo rabawar? Ai yanzu ne yake bukatar su, tunda kin ki daukarsa ai kamata yayi a raba gidan a bashi kason uwarsa sai ya fitar da kofa ya zauna a ciki” Inna tace “wai ni Hafsa ki gayamin kina baya na ne ko kina bayan yaron nan ne?” Mama tace “ina bayanki Adda, wannan kuma shi yasa nake gaya miki gaskiya”. A haka mukayi sati biyu a gidan, kallo daya zaka yi min kasan gabaki daya hankali na baya tare dani duk na kara ramewa dama ni ba jiki ba, kullum ina cikin tunanin halin maraicin da muka shiga ciki da kuma tunanin halin da Sadauki yake ciki. Ko wajen gate bani da damar fita saboda kullum ina tare da Inna ko aike na waje ba’ayi saboda akwai yan aiki da masu gadi. Rannan naji Hajiya Yalwati da tazo dakin mu tana cewa “wannan yarinyar kuwa anya ba sai anyi mata rubutu ba? Ita kadai sai inga kamar tana zabura” Inna tace “haka take yi wallahi, ina lura da ita ko baccin kirki bata yi” nan Hajiya Yalwati ta saka ni a gaba da nasiha akan yarda da kaddara mai kyau da marar kyau sannan tace inzo muje dakinta ta bani littafin wasu adduoi da zasu taimaka min. Naje na karba kenan na taho ina hanyar dawowa sai ga Murja da sauri tazo gurina tace “Diyam wai kizo wani yana kiranki a waje” nayi sauri na toshe mata baki muka matsa can gefe na tambayeta waye “to ni ina zan sani, mai gadi ne dai yazo ya a kiranki sai ya ganni ya fada min, wai wannan wanda yake zuwa gurinki sanda kika zo hutu” naji wani adrenaline rush yazo min, nayi kamar zan tafi dakin Inna sai kuma na dawo da baya na zare hijab din jikin Murja na saka nace “Please kar ki gaya wa kowa yanzu zan dawo” sai na wuce da sauri ita kuma ta bini da ido. Da sauri na nufi inda muke zama in yazo, ji nake kamar inyi tsuntsuwa ko zanfi sauri. Tun daga nesa na hangoshi kuma na gane shi sannan naji dadin ganin sa sosai. He looks good, and that was all that matters to me a lokacin. Ina karasawa na lura da kayan jikinsa sababbi ne kuma masu kyau, he smells good too. Sai dai fuskarsa ce tayi betraying emotions dinsa dan idonsa ya fada ciki sosai kuma zagayen idonsa yayi baki alamun baya samun isashshen bacci. “Sadauki” na kira sunan sa da karyayyiyar murya, bai amsa ba sai murmushi da yayi min mai kokarin boye damuwarsa. Muka karasa zagayawa bayan dakin maigadi, Sadauki ya zauna akan ginin suckaway, wannan ya bani damar ganin gefen kansa inda akayi masa dinki. Na zauna nima a kusa dashi ina fuskantar sa kawai sai hawaye suka fara zarya a kumatu na, bai hanani kuka na ba sai ma ya miko min handkerchief dinsa na cigaba da kuka na, sai dana gama na share hawaye na sannan yace “dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, ke din dama kuka baya miki wahala” nace “Allah yaji kan Baffa da Ummah” yace “ameen. Naje na kai musu ziyara kaburburan su. Suna kwance a sides din juna kuma ina fata da zaton suna aljanna a tare” sai naji dadi sosai a raina, dadin yadda naga ya dauki abin nima sai naji na samu courage din facing rayuwa a koya tazo min. Nace “kai kuma fa? Wanne hali kake ciki? A ina kake a zaune?” Yayi murmushi yace “ina gurin Alhaji Bukar (mutumin da yaya ladi take gurinsa) and they are treating me well, too well even. Ya gaya min cewa zai kaini gurin mahaifina, ya san shi ashe” na bude ido da baki “wow. Congratulations Sadauki, yaushe zaku je?” Ya girgiza kansa yace “I don’t know. Ban san shi ba Diyam, bansan waye shi ba and for all I know zata iya yiwuwa ma bai san nayi existing ba, zai iya yayi denying dina yace ni ba dansa bane ba” Nace “amma ta yaya zaka sani in baka je ba? Nasan Sadauki na babu abinda yake tsoro just go kayi clearing doubt dinka and move on” ya gyada kai yana kallona yace “so I have your blessings kenan ko?” Nace “of cause you do”. Sai kuma na tambayeshi abinda yake raina tunda na ganshi “Sadauki me yasa kazo? Bayan abinda Inna ta tayi maka bayan yanzu babu Baffa kuma gashi ka samu wani mai rikon gashi kuma zaka je gurin babanka, me yasa kazo gurina? Ba ka gudun a wulakanta ka?” Ya dan bata rai yana kallona yace “me yasa ba zanzo ba to? For starters I love you, always have and always will. Na biyu duk abinda ya faru dani babu abu daya da yake laifinki dan haka baxanyi fushi dake akan abinda ba ke kika yi min ba. Na uku Baffa, a gurina darajar Baffa ta wuce in yi fushi da iyalinsa dan babu ransa, sannan……..” Sai yayi shiru yana kallona, nace “sannan me?” Ya sauke idonsa kasa Yace “sannan lokacin da mukayi accident din, he looked at me straight in the eyes ya ce in wani abin ya same shi in kula daku ke da Asma’u”.3 Na sunkuyar da kaina inajin sabbin hawaye suna zubo min. Yace “amma bansan ta yadda zan iya kula daku ba Diyam, innar ku bata so na na sani, bansan ta yadda zan iya juyo da hankalinta ta soni ba tunda bansan abinda nayi mata wanda ya saka bata son nawa ba balle in daina. Diyam ina tsoron kar lokacin auren ki yayi in nema a hana ni akan dalilin da ni kaina ban sani ba, I don’t think my heart can take that”. Mun jima muna hirar yadda future dinmu zata kasance, sai daga baya yace “bara in tafi Diyam kar in jawo miki fada. I just want you to know cewa am okay, dan haka kema ya kamata ki rage wannan koke koken haka ki tsayar da hankalinki guri daya. And everything is going to be alright” nayi murmushi nace “ai na samu strength daga gurinka Sadauki, kayi sharing strength dinka dani” ya mike tsaye yana kallona yace “Aliyu shine sunan, Sadauki shine inkiyar, so ofcause am going to be alright”. Muka yi sallama yana yi min alkawarin in sun saka ranar zuwa gurin babansa zai zo ya gaya min saboda inyi masa addu’a. Shine a gaba ni ina binsa a baya, muna fitowa yayi hanyar gate ni kuma nayi hanyar cikin gida ina waigensa, a lokacin ne kuma aka budewa Alhaji Babba gate ya shigo gidan sukayi clear da Sadauki kafin Sadauki ya fita. Na kara sauri kafin yayi packing Ina jin bugun zuciyata yana karuwa amma ina kama handle din kofa naji muryar Alhaji Babba a baya na yace “Diyam, zo nan”3 Na juyo na ganshi a tsaye a gaban motarsa yana kallona, na dawo baya a zuciya ta ina karanto duk addu’ar da tazo bakina na durkusa a gabansa nace “gani Alhaji” ya nuna hanyar gate “waye wancan da na ganku tare?” Nayi shiru kaina a kasa “ya sunkuyo yace “ba’a koya miki in manya suna magana ba’a yin shiru a rabu dasu ba?” Na sake yin shiru ina jin hawaye yana taruwa a idona, ya kama kunnena ya murda, nayi kara na mike tsaye yace “waye wancan nace miki” cikin azaba nace “Sadauki ne” ya sake ni ya kwalla wa maigadi kira, baba audu ya taho dagudu ya durkusa a gabansa yace masa “wanene yace kake barin ƴaƴan iska suna shigo min gida?” Dattijon ya kalle ni sannan yace “bansan baka so ya shigo ba Alhaji, da yake naga duk sanda tazo gidan nan yana zuwa gunta ne na dauka dan uwanku ne” Alhaji Babba yace “babu abinda ya hada mu dashi, daga yau in ka sake barinsa ya shigo gidan nan a bakin aikin ka. Ina fatan ka fahimta” yayi saurin gyada kai “na gane Alhaji, insha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba, ayi hakuri Alhaji”.+ Alhaji Babba ya juyo kaina yace “ke kuma muje gurin Amina ta gaya min idan da saninta kike shigo min da kattin banza cikin gida” na juya da sauri ina tafiya blindly, kafafuwana suna hardewa kamar zan fadi har na shiga dakin Inna na tarar da ita ita kadai da charbi a hannunta tana lazumi, ta dago tana kallona da mamaki “ke kuma lafiya kamar wadda aka koro? Me ya faru” ban bata amsa ba Alhaji Babba ya shigo dakin, ta mike da sauri dan hardly ne ka ganshi ya shigo cikin main gidan saboda part dinsa a waje yake. Yana nuna ni yace “kinsan Sadauki yana zuwa gurinta?” Ta bude baki tana kallona da mamaki sannan ta fara tafa hannu tana salati “Diyam? Yanzu sai da kika jajibo mana yaron nan har gidan nan? Wato duk abinda nake fada ta bayan kunnenki yake bi yake wucewa ko?” Yace “mai gadi yace min dama ya saba zuwa gurinta a duk sanda tazo gidan nan. Wato yar mitsitsiyarta da ita har ta fara jawo mana yaran banza marasa asali da tushe zuwa gida ko?” Inna tace “Alhaji kayi hakuri, anyi an gama insha Allah ba za’a sake ba. Yarinyar nan bata jin magana, babu yadda banyi da ita ba akan yaron nan tun kafin ta kai haka amma taki rabuwa dashi. Yadda kasan yadda Zainabu ta shanye marigayi haka shima yaron nan ya shanye Diyam” Yace “au kice min tafi ƙarfin ki kenan bata jin maganar ki” ya kuma kama kunnena, na saki karar azaba yace “ni in nayi magana ba’a tsallake ta a gidan nan, daga yau sai yau babu ke babu Sadauki” ya sake ni ya juya yana cewa “shi kuma duk sanda ya sake zuwa gidan nan sai ya gane bashi da wayo, sai na rufe shi naga wanda zai fito dashi, sai naga wanda ya tsaya masa a garin nan”. Bayan ya fita Inna ta bini da kallo ina rike da kunnena ina kuka, ta koma ta zauna a bakin gado tana kallona ina jiran ta dora daga inda Alhaji ya tsaya amma sai naji tayi tsaki tace “ba kya jin magana Diyam. Ke indai akan wannan yaron ne ba kyajin magana wallahi” ta dauke kai ta cigaba da jan charbin ta sai kuma tace “zo inga kunnen” na rarrafo nazo gabanta, ta duba kunne na ta shafa min vaseline. Ranar haka na karasa ta cikin kuncin rai da kunan zuciya tare da fargaba, ni bawai fadan Alhaji Babba ne ya dame ni ba illa furicin da yayi akan sadauki, cewa da yayi zai sa a kama Sadauki duk sanda ya sake zuwa gidan nan, na kuma san alkawarin da Sadauki yayi min cewa zai dawo yayi updating dina akan duk abinda ake ciki dangane da mahaifinsa kuma nasan Sadauki baya karya alkawari idan yayi kuma bana jin zai fara daga yanzu. Option dina daya ne dole in nemi Sadauki in yi warning dinsa kuma in hana shi zuwa duk da cewa hakan yana nufin zamu kara nisanta da juna, amna gwara hakan akan abinda za’ayi masa in yazo din. Bayan kwana biyu duk na kara diriricewa, ko yaya naji hayaniya a waje sai inji gaba daya hankalina ya tashi inyi tunanin ko Sadauki ne yazo aka kama shi. Rannan dai sai wata dabara ta fado min. Da daddare muna zaune da Inna nace mata “ni kuwa Inna ina so in tambayeki ko muma za’a saka mu a islamiyya ni da Asma’u. Kinga duk ana wuce mu a karatu muna zaune a gida” Inna tace “Wallahi nima zancen islamiyyar nan yana raina tunda muka zo na dauka za’a saka ku amma har yanzu shiru. Amma bari in hafsa tazo sai insa Mukhtar ya kai ku ko kuma in saghir ya zo gari in roke shi ya saka ku” nace “Inna yanzu islamiyya ma sai mun jira wani yazo ya saka mu? In kin yarda kawai in bi su murja in tambayi malaman abinda ake bukata na sabon dauka” ta danyi tunani tace “shikenan, ki bisu din”. Ai kuwa na samu chance. STORY CONTINUES BELOW Washegari na shirya na kama hannun Asma’u muka je islamiyya na tambayar mana komai aka yi min bill, kamar yadda nayi tunani sai yasaiyadin yace mu shiga aji mu zauna, dai na tura Asma’u ajin su ni kuma nace zan je in dauko Alqur’ani na daga nan sai na kama hanya. Bani da ko kwandala dan haka na dauki hanya a kafa ina ta zabga sauri kamar zan tashi sama amma a raina sam banga nidan tafiyar ba, nasan gidan Alhaji Bukar inda yaya ladi take anan bayan layin mu yake dan haka nan na dosa, a ringa bi ta lunguna in tsallaka wannan titin in shiga wannan lokon bansan cewa na gaji ba sai da na ganni a kofar gidan, na tsaya a gaban mai gadi ina haki shikuma yana kare min kallo, sai da na gama tsaida numfashi na sannan nace “dan Allah baba Sadauki nake nema. Allah yasa yana nan” ya ajiye radiyon hannunsa yace “dazu ya shiga, bara in dubo miki shi” sai naga ya doshi boys quarters ana jima wa sai gasu sun fito a tare Sadauki ya doso ni da sauri fuskarsa cike da damuwa “Diyam? Lfy? Daga ina kike haka?” Na danyi masa murmushi sai naga yayi ajjiyar zuciya, ya kalle ni yace “kar dai kice min a kafa kika taho” na gyada masa kai sai ya jani zuwa kujerar mai gadi na zauna shi kuma yayi kneeling a gaba na yana mammatsamin kafata yace “me yasa kika taho a kafa Diyam? Ko menene ba zaki bari inzo ba sai ki gaya min? Yanzu da wani abin ya same ki kuma fa?” Nace “You don’t understand, gaya maka zanyi kar kazo din ai” sai na bashi labarin abinda Alhaji Babba yace. Sai naga fuskarsa ta chanja gaba-daya yace “Diyam mai nayi wa mutanen nan ne wai? Su kansu ba zasu taba iya fadar abinda nayi musu ba haka nan kawai suke ji a ransu basa sona” ya dago kai yana kallona yace “Diyam ni nasan ba zasu bani ke ba” nayi saurin girgiza kaina nace “da sauran lokaci ai Sadauki, ka tuno abinda Baffa yace? Sai na gama makaranta na shiga jami’a tukunna? Kafin nan zasu chanja ra’ayinsu zasu fahimci ko kai waye ne. Yanzu ka yarda Alhaji Bukar ya kai ka gurin abbanka tunda wannan zai kara sassauta zuciyarsu tunda suna cewa baka da asali” ya gyada kai yace “you are right. Gobe dama nayi niyyar zanje in gaya miki cewa jibi zamu tafi. Maiduguri yace zamu je” na bude ido ina mamaki, sai kuma na fara sharar hawaye, yace “sarkin kuka, kukan menene kuma kike yi?” Nace “Maiduguri fa da nisa” yace “kuma ce miki akayi a can zanyi ta zama. Nima ai bazan iya zama a can ba zanje in gansu ne kawai in dawo nan ko dan makaranta ta ma” sai kuma ya bani labarin wani abokin Baffa da Baffan ya hada su dan yayi masa hanyar admission, yace “ranan nan bayan nayi welcome back din layina sai ya kirani yayi min gaisuwar Baffa yace min insha Allah wannan admission din dani a ciki. Kinga zan dawo ko dan makaranta ta, besides, ni bazan iya rayuwa nesa dake ba” Na makale kafada nace “Allah yasa dai kar Borno tayi dadi ka manta da Diyam” yayi murmushi yace “maganar kike so, sau nawa zan gaya miki cewa babu rayuwa a tare da Sadauki in babu Diyam ba. Life without you will not be just unbearable it is unimaginable. I can’t imagine me without you”. Sai kuma muka shiga hira kamar bamu da wani problem, yana ta tsara min yadda yake yana planning din rayuwar mu tare, hatta fasalin yadda zai gina mana gidan mu a filin da Baffa ya siya masa sai da yayi min. Ga iskar gurin tana yi mana dadi. Jin mu muke a saman gajimare, tamkar together zamu iya facing duk mutanen duniya1 Mun jima tare sannan ya duba agogon hannunsa yace “Diyam, tashi maza in raka ki ki hau daidaita ki tafi, ashe lokaci ya tura bamu sani ba”. Sai naji kuma kamar bazan iya tafiya ba kamar inyi zamana a gurinsa mu tafi Maidugurin tare amma nasan hakan ba zai yiwu ba, shima ganin yadda na damu sai duk jikinsa yayi sanyi. Ya dauko biro ya kama hannuna ya rubuta min number dinsa yace “ga numberta nan, ba wai rubutawa zakiyi a wani wajen ki boye ba a’a haddacewa zakiyi a kanki, if anything happens kafin in dawo, if you need anything ko menene ki samu aron waya ki kira ni. Kafin ki koma makaranta insha Allah zan dawo. Ki ringa yi mana addu’a” na gyada kai ina karajin jikina yana kara sanyi.1 Ya raka ni waje ya tarar min adaidaita ya bashi address ya biya kudin, sai kuma ya tambaye ni in inason kudi. Na girgiza masa kai, kamar ba zai matsa ba yana kallon fuskata sai da mai adaidaitan yayi masa magana tukunna sannan ya ja baya muka tafi. Na waiga ina kallonsa sai yayi murmushi ya daga min hannu. Daga dan nesa da gidan Alhaji Babba nace a sauke ni, ina sauka na juya da niyyar in karasa sai naji daga bayana ance “Diyam daga ina kike?” Na juya muka hada ido da kawu Isa shida wani mutum suna tafiya a kasa, na durkusa na gaishe su fuskata cike da rashin gaskiya, ya sake maimaita min tambayar, cikin in ina nace “Inna ce ta aike ni gidan Mama” ya gyada kai yace “to ki gaisheta, amma dan sahun ai daya karasa dake ciki” sai nace “zan biya ne ai ta islamiyya in tafi da Asma’u”. Nayi sa’a ina zuwa gida na tarar an taso yan makaranta na shiga cikin su muka shiga cikin gida. Bana jin dadi kuma bana so Inna ta gane dan haka nace da Asma’u ta tafi ta gaya mata mun dawo ni kuma na bi Murja muka tafi part din Hajiya Yalwati. Muna zuwa na kwanta a kujera ina jin kamar zanyi zazzaɓi, Hajiya Yalwati ta tambayeni “lafiya?” Sai na gyada mata kai inajin kamar zanyi kuka, sai kawai ta rabu dani tana tunanin ko Baffa na tuno. Kwana biyu bayan nan, ranar da nake lissafin su sadauki sun tafi Maiduguri, mun fito zamu tafi islamiyya sai muka tarar da Alhaji Babba, kawu Isa, Inna da Hajiya Babba suna zaune a babban palo da alama magana mai muhimmanci suke yi. Muka gaishe su har zamu wuce sai ji nayi kawu Isa yace “Amina ki daina aiken Diyam ita kadai gwara kiyi wa Hafsan waya ta bawa Mukhtar ko menene ya kawo miki” na kara sauri kamar zan tashi sama, na kusa gate kenan naji an kwalla min kira, na runtse idona na kasa motsi, “Diyam ki zo ana kiranki” murja ta dafa ni tace “number dinki ta fito, good luck, ni nayi gaba”3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *