UMMI CHAPTER 4 MK
-TECH SOFTWARE COMPANY+ Zaune yake a kan executive chair dinshi yayinda yake wani aiki a macbook dinshi. Fahad ne ya qwanqwaso qofar ya shigo. Ganin yadda abokin nashi ya duqufa a gaban macbook dinshi ne yace “hey na ga kamar you are busy… bari in je in dawo don dama na zo mu dan yi hira ne” Da sauri MK yace “haba abokina.. qaraso don Allah. Nima na gaji…” Ya dan dafa kanshi yayinda ya cigaba da fadin “…na ji kaina ma zai fara ciwo” Fahad wanda ya zauna cike da tausayawa yace “ayyah sorry… ko a kawo maka magani ne??” Yace “No buddy… kaima ka san bana saurin shan magani.. I prefer massage. it does the magic faster” Fahad yayi murmushi yace “toh abokina… massage kuma sai dai ka koma gida wurin Babe dinka. na tabbatar da ta fara yi maka zaka ji garau”4 MK yana murmushi yace “Aikuwa bata iya ba don wallahi the last time she gave me a massage kan nawa qara ciwo yayi”3 Fahad ya fashe da dariya yayinda yace “a bakinka dai aka ji..” MK wanda shima dariyar yake yi yace “yeah but I still and will forever love her” Fahad ya girgiza kai yace “uhm na manta ban tambaye ka yarinyar nan ba.. is she still stuck in your head??” MK wanda ya kwanta akan kujerar shi ne na ga ya rufe idanuwan shi sannan ya bude yace “i really dont know my friend… na dai ganta sau daya bayan mun dawo kuma I felt thesame way I feel whenever I see her… I dont even understand wallahi…” Ya shafa kanshi da hannuwan shi biyu ya cigaba da fadin “…there is this funny thing.. haka kawai I kinda feel i understand her even without talking to her…. could you believe cewar I derive pleasure in just talking to her and listening to her voice???”3 Yana kallon Fahad in a confused state yace “abokina am I even making sense??” Fahad wanda yake kallon abokin shi cike da mamaki ne yayi murmushi sannan yace “ofcourse you are making alot of sense my friend. My question is simple… are you in love with her??” Cike da mamaki da bacin ran abinda abokin nashi ya fada ne yace “what??? haba Fahad… she is just a small girl…” Katse shi Fahad yayi yace “small girl?? how old??” Ya dan yi shiru kamar yana tunani sannan yace “maybe seventeen or eighteen??” ya qarasa maganar cikin tambaya.3 Fahad dai fashewa yayi da dariya yayinda yace “and you call her a small girl??… haba Mk you…” MK ya dakatar da shi yayinda yace “look abokina it’s like you are misunderstanding me… I see this girl thesame way I see Hafsy-a sister. I love and will continue to love only one person a rayuwar nan… MALEEKA”1 Da kyau Romeo..2 Fahad yace “it’s okay abokina.. I understand amma gaskiya ina son ganin yarinyar” MK yace “ka je gidan Mummy zaka ganta” ni kuwa nace tana nan a cikin gidan ka.. ah toh!!3 Fahad yana dariya yace “rufa mun asiri.. Fatima ta ji labari ta bani red card” MK wanda yake dariya yace “ita ma kenan mai sanyi..” STORY CONTINUES BELOW ♧♧♧♧♧♧♧♧ ●●●●● Ummi dai tuni ta warware a gidan, ta fahimci lallai idan tana yin ayyukanta a daidai lokacin da take yin su bazata taba haduwa da shi ba. Asali dai dama gidan akwai Chefs wadanda aikin su shine girka abinci. Ummi dai nata gyare-gyare ne. Kullum zata gyara ko ina tas sannan ta koma kicin inda take kallon yadda chefs suke dafa abinci, idan sun gama ta gyara ko ina tas. Maleeka kuwa dama dai bata cika son zama wuri daya ba. dukda kuwa a ‘yan kwanakin nan bata yi tafiya ba a kullum takan je boutique dinta don ganin yadda abubuwa suke tafiya sannan wasu lokutta tayi hanging out da friends dinta, wasu lokuttan kuma takan gayyaci friends din nata gidanta su sha hirar su. MK da Maleeka kuwa suna ta kwasar soyayyar su iri-iri.. a duk lokacin da yake gida tana nan maqale da shi amma fa babu abinda take yi mishi a bangaren kula da harkokin shi. MK dai shi yake gyara dakin shi da kanshi.. hatta gyaran gado Maleeka bata taba yi mishi ba. Underwears din nashi ma bata iya sanya mishi a washing machine ta wanke balle kuma gyaran closet dinshi da sauran su. Komai shi yake yi ma kan shi all by himself.1 Babu abinda take buga mishi sai shagwaba.. Wani lokaci ma idan ta dauko mishi shagwaba sai kayi tunanin wata mai dauke da qaramin ciki ce. Shi kuwa a kullum yana daukar ta tamkar wata baby, baya son bacin ranta ko kadan. Burin shi a rayuwan nan bai wuce ya faranta ma Maleeka rai ba domin kuwa babu abinda yake so sama da ita duk fadin duniyan nan. Maleeka dai tana nan tana shan pills dinta a duk lokacin da suka sadu. daidai da rana daya bata taba missing ba don haka kuwa bata yi conceiving ba. MK kuwa tun yana qorafi har ya haqura ya bar ma Allah. Jameela takan ba qawarta shawara akan ta daina shan pills din kar suyi mata illa a jiki amma sam ta qi. A haka kuwa har lokacin tafiyar Jameela yayi ta tafi Ingila. Maleeka dai tayi kewar qawarta… dayake dai tana yawan zuwa Ingila a dalilin business dinta shiyasa damuwarta ta ragu. Ta sani cewar zata ga qawarta a duk lokacin da ta je qasar. A yanzu haka akwai wani fashion show din da zata yi attending soon a qasar Ingila don haka duk ta bi ta qagara lokacin yazo don ta tafi. wannan kenan!! ●●●●● ♧♧♧♧♧♧♧♧ After two months… MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO ABUJA Kwance yake a kan cinyarta a falon shi yana kallon Monday night Raw yayinda take chatting da Jameela a waya. Ji nayi tace “Honey I swear I am missing my friend terribly… can’t wait to see her in 3 day’s time” Kai tsaye yace “ni kuma bana so ki tafi babe… I am going to miss you alot. don dai na riga na amince kiyi one week amma da nace immediately after the fashion show ki dawo” Turo baki tayi tace “haba honey.. instead of ka qara mun one week ma.. kaima fa kullum kana office sannan baka dawowa sai dare..” Gani nayi ya dago hannun shi ya ja kumatunta sannan yace “kiyi haquri babe… I am a CEO, I have to work very hard towards achieving my goal. kin san dream dina ai” Tashi yayi zaune ya janyo ta jikin shi yayinda ya zura hannun shi ta cikin rigarta ya fara wasa da boobs dinta sannan ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “I love you My Maleeka and I will forever love you…” STORY CONTINUES BELOW Maleeka dai tuni tayi laushi a dalilin abubuwan da MK yake ta yi mata.. lumshe idanuwa ta dinga yi yayinda ta qara mannewa a jikinshi kamar chewing gum. Muryarta qasa-qasa tace “Honey tashi mu je mu kwanta..” Yana kissing wuyanta ne yace “toh je ki hado mun Cappuccino dina ki kawo mun first…” Turo baki tayi cikin shagwaba tace “Honey ka san fa ban iya ba.. na sani cewar kullum idan nayi hakanan kake shanyewa ba don yayi dadi ba… ni gaskiya….” Da sauri yace “ssssssshhhh..” tare da kai bakinshi saitin kunnen ta yace “practice makes perfect babe.. besides have I ever complained??” Ta girgiza kai alamar a’a. Ya ja kumatun ta yace “Okay toh.. be a good girl and go get it for me kin ji..” Haka ta tashi cike da laziness ta bar falon yayinda ya bi ta da kallo yana murmushi. Abu daya da MK ya tilasta ma Maleeka yi mishi kenan ‘prepare his morning and night Cappuccino’ Maleeka kuwa saboda laziness ta kasa tsayawa ta koyi yadda ake yi.. sai complain. kullum sai ta buga mishi shirme kuma a haka nan din yake sha. He just wants her to learn to do little stuff all by herself amma da alama hakan bazai yiwu ba tunda dai common Coffee ta kasa hadawa da kyau. Haka Maleeka ta je ta hado mishi coffee dinshi ta kawo mishi. kamar kullum haka nan ya sha ba don yayi dadi ba. Tana kallonshi tace “Honey fadi gaskiya baiyi dadi ba ko??” Janyo ta yayi jikinshi ya kai cup din saitin bakinta yace “sha ki ji…” Da sauri ta matsa tace “No please… ni bana son Coffee” Murmushi yayi yace “ni da nake sha nace yayi dadi” Bayan ya gama ne ta tashi tare da fadin “toh yanzu ka sha hankalinta ya kwanta ko??” Murmushi yayi yayinda ya miqe ya janyota jikinshi yace “yes my babe…” Ko kafin tayi magana kuwa ta ji ya dauke ta cak yayinda nufi hanyar dakin shi..” Sagala hannun ta tayi a wuyan shi sannan tace “Honey mu je dakina…” Yace “kuma dai??” MK dai a kullum Maleeka dakin ta take janye shi suyi bacci daddare..!! why??5 Ji yayi tana fadin “yes Honey… ai da dakina da naka duk daya ne” Yana murmushi yace “toh gimbiyar MK…” ************** Tsawon lokaci suna gurzar soyayyar su kamar kullum. Maleeka da MK dai suna bala’in jin dadin kasancewa da juna.. sossai suke gamsar da junan su sannan basu gajiya da juna. Ko da suka sarara sun dan taba hira Gradually kuma bacci ya kwashe su wanda kuwa a zahiri MK yayi bacci amma Maleeka pretending tayi. Da ta tabbatar lallai MK yayi bacci ne ta janye jikinta daga nashi ahankali sannan ta sauka daga kan gadon. Gani nayi ta nufi wata drawer ta Vanity table dinta ta bude sannan ta janyo Emergency Contraceptive pill dinta. A daidai lokacin da take qoqarin shan maganin ne MK ya dan farka wanda kuwa ya hangota ta dim light din da ke kunne a dakin.7 toh fa… Sossai yayi mamakin ganin Maleeka tana qoqarin shan wani abu da bai tabbatar da ko meye shi ba. MK dai qin tashi yayi yayinda yake ta kallonta har ta mayar da sachet na maganin cikin drawer sannan ta juyo. A lokacin ne ya rufe idanuwan shi don kar ta gan shi yayinda yayi pretending kamar yana bacci. Haka ta dawo ta haye kan gadon ta kwanta ta maqale a jikinshi kamar dai yadda take yi kullum. MK wanda ya cika da tsananin mamaki da fargaba sossai yake tunanin abinda ya gani. Gaba daya hankalinshi a tashe ne yayinda yake addu’a Allah yasa ba abinda zuciyar shi take raya mishi bane. Tsawon lokaci MK yana ta qoqwanto akan ya duba abinda Maleeka ta sha ko kar ya duba. Ban ankara ba na ga ya zare jikinshi daga nata ahankali sannan ya sauka daga kan gadon ya taka har zuwa wurin drawer din. Ghen ghen ghen… Gani nayi ya runtse idanuwan shi sannan ya bude yayinda yake cike da fargaban abinda zai gani. Duqawa yayi ya bude drawer din yayinda ya dan birkita. Hannun shi ne ya kai kan sachet na pills din wanda yayi saurin daukar daya daga ciki. A dalilin rashin isashen haske a dakin ne na ga ya nufi bathroom. MK wanda yake tsaye a bathroom din gani nayi yayi freezing yayinda zuciyar shi ta buga a dalilin ganin pills din. Tuni zuciyar shi ta fara tafasa tana zafi. Kan shi ya daure sossai yayinda qafafuwan shi suka yi sanyi.1 Muryar shi tana rawa na ji yace “emergency contraceptive pill?? for what?? Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. No it’s not possible” Gani nayi ya jingina da bango yayinda yace “Maleeka why???”2 Runtse idanuwa yayi sannan ya bude yayinda ya saki wata nauyayyar ajiyar zuciya. sai zufa yake yi yayinda Idanuwan shi suka yi jajawur.2 Gani nayi yayi composing kanshi sannan yace “I have to confirm what these does.. bazan yi saurin yanke hukunci ba…” Can kuma na ji yace “But…” Ya qara runtse idanuwa tare da girgiza kai yace “No no no MK don’t conclude on this just yet” Kusan mintuna Goma sha biyar yana cikin bathroom din yana ta saqe-saqe yayinda yake cikin tsananin tashin hankali. Daga baya ne na ga ya fito. Kai tsaye wurin drawer din ya nufa ya bude sannan ya kwashe duka pills din ya wuce ya fita daga dakin!!! MK-TECH SOFTWARE COMPANY Zaune yake a ofis dinshi dafe da kai yayinda yake tuno conversation dinshi da Dr. Davis an hour ago. “Emergency contraception is a way to prevent pregnancy after unprotected sex. this pill works by delaying the release of an egg during the monthly cycle… it is most effective when taken as soon as possible after unprotected sex… so yes Mr. Muhammad Kabir your wife does not want to get pregnant.. atleast not yet” Ji nayi MK yace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. meyasa zakiyi mun haka Maleeka?? shin me hakan yake nufi kenan??” Sossai hankalin shi yake a tashe yayinda na ji yace “yanzu ya zanyi da ita??”1 Fahad ne ya qwanqwaso qofar shi ya shigo riqe da laptop dinshi. Ji nayi yace “hey buddy.. can you help me look into…” Bai qarasa bane yace “hey…” Da sauri ya qaraso ya zauna a kujera cike da mamakin ganin yanayin da abokin nashi yake ciki. Ji nayi yace “MK me ya same ka?? kan ne??” Girgiza kai yayi alamar a’a Fahad yace “Maleeka??” Ajiyar zuciya ya saki sannan ya miqe ya nufi fridge ya bude ya dauko dan madaidaicin goran swan ya bude ya shanye shi tas. Fahad ne ya miqe ya nufi wurin shi ya dafa shi tare da fadin “hey talk to me please.. me ke faruwa?” MK dai baya so ko kadan ya fallasa abinda yake faruwa a gidan shi.. dukda kuwa ya dauki Fahad tamkar dan ‘uwa gani yake kamar bai dace ba. Toh amma at this point ya riga ya zama confused, abu daya da yake burin samu a duniyar nan bazai samu ba.. toh ya zai yi?? he surely need to talk to someone.. who better than his best friend Fahad.. Bai ankara ba ya ji Fahad ya riqo hannun shi suka koma kan kujera yayinda yace “MK ka dai san you can trust me akan koma menene ko?? ka tuna cewar na dauke ka tamkar dan uwana na jini.. duk matsalarka a rayuwar nan matsala ta ce don haka please…” Bai qarasa maganar ba ya ji MK yace “she doesnt want to have a child with me” Cike da mamaki Fahad yace “what?? why?? I thought she loves you” MK wanda ya dafa kanshi da hannuwanshi biyu ne yace “na sani cewar tun kafin muyi aure Maleeka bata son zancen haihuwa.. a duk lokacin da muka fara zancen sai tayi ta kawo mun excuses on why she doesnt want to have a child…” Gani nayi ya shafa fuskar shi da hannuwan shi biyu yayinda ya saki ajiyar zuciya ya cigaba da fadin “…abokina ka sani cewar ina bala’in son yara.. ka sani cewar babban buri na a rayuwar nan in ga dan da Maleeka zata haifa mun.. she is the love of my life for crying out loud.. har roqonta nayi akan ta bani just one child and I am okay.. all these while ina sa ran ganin ta samu ciki only for me to find out she has been preventing herself from getting pregnant..” Fahad wanda ya zama confused ne yace “how did you find out??” MK ya girgiza kai yace “emergency contraceptive pills take sha…” Daga nan kuwa MK ya bashi labarin yadda ya gano da kuma conversation dinshi da Dr. Davis. Fahad wanda ya saki baki cike da mamaki yace “this is serious abokina.. Yanzu bata tunanin shan maganin yana iya haddasa mata matsala?? toh wait.. what are you planning on doing??” STORY CONTINUES BELOW MK yana kallon abokin shi yace “I really dont know abokina.. the thing is I really love her and…”3 Da sauri Fahad yace “toh kenan ka haqura da haihuwar?? MK why are you being soft on Maleeka?? lokutta da dama I swear idan na ga yadda kuke tafiyar da al’amuran ku nakan yi tunanin tayi jinxing dinka ne.. like it’s okay to love unconditionally but honestly speaking Maleeka is taking advantage of your unconditional love for her” MK yace “toh ya zanyi yanzu??” Fahad ya girgiza kai sannan yace “it’s simple abokina, just confront her…” ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO ABUJA Kwance yake a kan gadon dakinshi da daddare yayinda yake ta saqe-saqe a zuciyar shi. Ya zaiyi da Maleeka?? Maleeka ce ta shigo dakin sanye cikin wata nighty mai zafin gaske. MK wanda idanuwan shi suke a rufe jin ta yayi ta kwanta a bayan shi yayinda ta rungume shi tana shaqar qamshin shi. Bakinta ta kai saitin kunnen shi tace “honey har ka fara bacci ne??” Ba tare da ya motsa ba yace “no my babe..” Ji yayi ta fara sakar mishi kisses a wuyan shi zuwa gefen fuskar shi. MK wanda yake kallonta sossai ya cika da sha’awarta.. shi dai Allah ya sani bala’in son Maleeka yake yi.. Allah ya sani baya iya resisting dinta. Laifi tayi mishi amma ji yake kawai ya yafe mata.2 Gani nayi ya sa hannu ya janyo ta ya manna ta da jikinshi yayinda ya fara sakar mata kisses irin wadanda suke haukata ta.4 Ahankali suka fara haukata juna. Muryarta qasa qasa tace “honey don Allah ka nuna mun soyayyar da baka taba nuna mun ba a yau please..” Bata ankara ba ta ji ya daga ta yayi pinning dinta a gadon yayinda ya koma saman ta. Cikin hanzari suka raba juna da kayan jikinsu yayinda suka shiga hidima da juna. Soyayya mai zafi suke kwasa kamar yau ne daren farkon su. Da qyar suka sassauta haka nan amma fa suna nan manne da juna. MK wanda yake kwance a kan qirjin Maleeka ne yace “babe I love you very much… soyayyar ki yawo take yi a cikin jini na” Maleeka wadda take cike da farin ciki ce ta shafa kanshi tare da qara matse shi a jikinta tace “nima sonka nake yi dan uwana.. ka cigaba da zama nawa ni kadai ka ji??” Yace “insha Allah my babe… Allah ya nuna mun ranar da zaki haifa mun Baby.. ” Maleeka dai dauke wuta tayi yayinda ta kasa magana. Ita kam har ga Allah bata son zancen haihuwa.. Gani nayi ta dan zabura a dalilin tuno pill dinta da tayi. Ji nayi tace “uhm Honey, bari in je dakina.. yanzu zan dawo” MK wanda ya riga ya gane abinda take son yi ne yace “me zaki je yi at this time of the night?? qarfe biyu fa yanzu” Zare kanshi tayi daga jikinta yayinda ta sauka daga kan gadon ta duqo tayi mishi kiss sannan ta janyo nighty dinta ta zura tace “just one minute.. ina zuwa” Haka MK ya sanya mata idanuwa har ta fita. Zuciyar shi sai zafi take yi yayinda na ji yace “why Maleeka?? why do you have to do this to me??”2 *************** Tsaye take a dakinta yayinda take ta birkita drawer din. Hankalinta a matuqar tashe na ga ta fara wurgi da duk wani abu da yake cikin drawer din. Ji nayi tana fadin “na shiga uku.. where is it??” STORY CONTINUES BELOW MK wanda yake tsaye jikin qofar dakin yana ta kallonta yayinda hankalinta yayi nisa da bata ma san ya shigo ba. Bata ankara ba ta ji yace “babe me kike nema??” Gani nayi Maleeka ta zabura yayinda tayi saurin dago kai tana kallon shi. Murmushi yayi tare da dago hannuwan shi biyu yace “sorry na baki tsoro” Matsowa ya fara yi yayinda Maleeka tayi freezing a tsaye. jikinta sai rawa yake yi yayinda ta duqar da kanta qasa. Ji tayi yace “the pills… su kike nema??” Da sauri ta dago kai ta kalle shi yayinda zuciyarta take ta bugawa. Maleeka dai ji tayi kamar ta nutse a qasa don kunya. Runtse idanuwa tayi yayinda muryarta take rawa tace “ka bani..”3 Girgiza kai yayi tare da kamo hannunta yace “zo ki zauna mu yi magana…” Da sauri ta fizge hannunta tace “ni ka bani pills dina”2 MK wanda ya cika da mamaki gani nayi yayi turus yana kallonta. shi fa tayi ma laifi amma kuma tana yi kamar ita ce victim din. Yana kallonta yace “shin kin sani cewar pills dinnan da kike sha suna da side effect?? shin kin taba zama kika yi tunanin matsalolin da pills din zasu iya janyo miki a gaba??? ” Cike da borin kunya ta fashe da kuka yayinda tace “ni fa ka qyale ni.. bana son haihuwa kuma bana son yara… da in haihu gwara na mutu..” Cike da tsananin mamaki MK yace “Subahanalillah… lafiyarki kuwa??” Cikin masifa tace “lafiya ta qalau.. nace bazan haihu ba dole ne??” Girgiza kai yayi yace “ba dole bane babe I am sorry” Yana qoqarin janyo ta jikin shi ne ta ja baya da sauri tace “ni don Allah ka bani pills dina.. I need to take them now” MK dai sossai yake qoqarin danne fushin shi. Gani nayi ya shafa kan shi da hannuwan shi guda biyu yace “unfortunately pills dinki basu kusa..” Zaro idanuwa tayi yayinda ta sa hannuwan ta biyu a bisa kanta tana kuka tace “na shiga uku, akan me zaka yi mun haka?? ashe dama kai mugu ne ban sani ba? Allah ya isa tsakani na da kai… I hate you”8 kai🙄 A guje ta ruga ta shige closet dinta ta rufe qofar. MK wanda ya bi bayanta kuwa ji nayi yana fadin “babe tsaya mana… I swear idan ba kya son maganar haihuwar bazan qara ba.. ki fito kawai mu yi…” A dayan bangaren ne Maleeka tace “leave me alone.. I hate you I hate you. kawai ka fita ka bar mun daki” MK wanda kalaman Maleeka suka yi mishi zafi a zuciya ne na ga ya juya ya bar dakin. ************* Washegari.. 8:00am Kwance yake a kan gadon shi yayinda yake ta mamakin abinda yake faruwa a tsakanin shi da Maleeka. It’s barely 5 months da yin auren su amma har an fara samun matsala. A tunanin shi wannan abu ne da zasu iya zama suyi resolving ba tare da wata hayaniya ba.6 Shi kam ya so su zauna suyi magana ta fahimtar juna, ya so ya ganar da ita illar abinda take yi, dukda bai ji dadin abinda tayi ba ya so ya sanar da ita ya haqura su cigaba da zama yadda take so har zuwa lokacin da ta shirya samun haihuwa. Ayyah… bawan Allah!!9 A dalilin bala’in son Maleeka da yakeyi he can sacrifice and forfeit duk wani abu da buri na rayuwar shi just to make her happy. Tambaya yake yi ma kanshi… why was she being overly dramatic?? ita da yakamata ta lallaba shi tunda ita tayi laifi but she kept on playing the role of the victim.. Gani nayi ya tashi zaune yayinda ya kalli agogon dakin shi. Sauka yayi daga kan gadon ya sanya slippers dinshi yace “na tabbatar kinyi calming down by now don haka dole mu yi magana”5 ************** MK dai ko da ya shiga dakin Maleeka gaba daya ya duba ta bai ganta ba. Gani nayi ya fita yayinda ya fara bin ko ina a gidan yana neman ta. A lokacin da ya shigo sashen visitors ne Ummi ta bude qofar dakinta. Aikuwa tana dago kai ta hango shi ne na ga tayi saurin komawa ta rufe qofar tare da sanya key. Jingina tayi a jikin qofar tare da dafe qirjinta tana ta sauke numfashi. Ita dai ta rasa dalilin da ya sa take jin wani iri a game da shi. Bata ankara ba ta ji footsteps dinshi.. daga baya kuma sai ta ji yana magana kamar a waya.. ko da ta sa kunnuwan ta ji tayi yana fadin “abokina wallahi ban ganta ba..na kira boutique dinta sun ce bata je ba.” shiru yayi sannan yace “gobe ne yakamata ta tafi ai.. nayi waya da Ken shima yace bata je airport ba….” Ya qara yin shiru yace “I can’t believe this abokina.. ni da tayi ma laifi ban yi fushi ba sai ita??” Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “bari in je gidan in duba ta…” Daga nan kuma sai ta ji footsteps dinshi alamar ya fita. ************ MK dai a gurguje ya nufi dakinshi yayi wanka ya shirya ya fito. A yau dai ko Cappuccino dinshi bai sha ba.. haka nan ya fita. Ummi wadda take maqale a jikin window ce ta hango shi ya fito yayinda ya nufi parking lot zai shiga mota. Kamar kullum dai ma’aikatan gidan suna ta kawo mishi gaisuwa yayinda yake ta amsawa sama-sama. Dukda hankalinshi a tashe ne sossai yayi kyau. sanye yake cikin qananan kaya na black wandon sweat da black polo. Har ya shiga motar ya bar gidan Ummi tana nan tsaye tana kallon shi. Sossai ta shiga damuwa ganin yadda yake cikin damuwa. Bayan security ya rufe gate ne ta saki curtain yayinda na ji yace “Allah ya kawo maka sauqin damuwar da ka shiga Hamma..” ♧♧♧♧♧♧ MK yana tafe a kan hanya yana trying line din Maleeka amma it keeps sending him straight to voicemail. daga baya ne yayi deciding ya ajiye mata voice message Ji nayi yace “Babe please ki dawo gida.. idan dai bakya so ki haifo mun Baby there is no problem but please come back.. I don’t want to..” Bai ankara ba ya ji ana yi mishi horn. Ko da ya dago kanshi gani yayi ya saki lane dinshi wanda kuwa kafin yayi wani abu tuni ya bugi wani dakali.1 Nan da nan qura ta tashi yayinda mutane suka taso a guje don kawo agaji.9 WILDOT CLINIC ASOKORO, ABUJA+ Gaba dayan su suna cikin daya daga cikin dakunan asibitin yayinda yake kwance a kan gado yana bacci. Kusan awa biyu kenan da aka kawo MK asibitin. A zahiri dai bai yi sustaining injury ba amma likitoci sun yi mishi x-ray don tabbatar da lafiyar shi. A yanzu haka ana jiran result din ne yayinda ake jiran farfadowar shi. Daddy wanda yake magana da Abba a waya ne na ji yace “a yadda aka ce dai he wasn’t driving with high speed.. yayi missing lane dinshi ne” Shiru ya dan yi sannan yace “Its possible stress ne amma dai yanzu bacci yake yi.. sai ya farka zamu ji” Murmushi yayi yace “okay dan uwa.. I will keep you posted” Bayan ya kashe wayar ne Mummy tace “toh wai ya akayi wayar Maleeka bata shiga?? ina ta je??” Hafsah ce tace “ko dai ta tafi England din ne??” Mummy ta girgiza kai sannan tace “ai ko jiya da nayi waya da ita ta fadi mun cewar gobe ne tafiyar” Fahad wanda yake sauraron su kuwa shi kanshi ya zama confused domin kuwa a tunanin shi zai tarar da Maleeka a asibitin. A yanzu dai ya tabbatar abokin shi bai yi sa’ar mata ba.4 Mamy ce tace “mu jira ya farka sai mu ji abinda yake faruwa..” **************** Dr. Davis wanda yake dauke da file a hannun shi ne ya gyara glasses din idanuwan shi yace “the report says he is okay but I will have to run one last test on him to confirm he is absolutely…” Muryar shi suka ji yace “there is no need for that doc.. I am fine now” Gaba dayan su suka juyo suna kallonshi yayinda suka cika da murnar ganin ya farka. Tuni suka fara yi mishi sannu yayinda Mamy wadda take kusa da shi ta shafa kanshi tare da fadin “sannu.. ina ke maka ciwo?” Muryar shi qasa-qasa tace “I am fine Mamy, babu inda ke yi mun ciwo” Gani suka yi ya tashi zaune yayinda yake qoqarin cire cannula din hannun shi. Shi kam MK cike yake da tsananin damuwa na yadda ya farka bai ga Maleeka ba.. Kenan ba gida ta je ba?? toh tana ina??? Mamy ce tayi saurin riqe hannun shi tana fadin “meye haka??..” yayinda likita ya qarasa wurin shi da sauri yana fadin “hey stop..” MK wanda ya riga ya zare cannula din ne yace “I said I am fine doc.. please discharge me already” Dr Davis kuwa sanin halin MK ne na kafiya yace “okay I will… but you will have to promise me that you will remain at home for atleast 3 days with zero stress” Kai tsaye MK yace “I give you my word doc… thank you” A lokacin da Dr. Davis ya gama ‘yan rubuce-rubucen shi ne yayi musu sallama sannan ya fita tare da Hafsah wadda zata karbo maganin shi. Gani suka yi MK ya yunqura zai sauka daga kan gadon. Muryar Daddy ya ji yana fadin “ina matarka take??” Zuciyar shi ce ta buga yayinda ya rasa me zai ce. Shi kanshi neman ta yake yi.. shin zai fadi musu abinda ya faru ne ko kuwa?? Gani nayi ya daga kai ya kalli abokinshi wanda shima kallonshi yake yi. STORY CONTINUES BELOW Muryar shi qasa-qasa yace “uhm.. ta tafi England yau da safe..” Cike da mamaki Mummy tace “tafiyar ba sai gobe ba MK??” Ya dan sosa kai sannan yace “an samu change of plan ne Mummy.. I am sure jirgin su bai sauka ba ma yanzu” Daddy ya kalli Mummy yace “da zarar an same ta a waya a sanar da ita halin da mijinta yake ciki don haka duk abinda take yi ta bar shi ta dawo gida” Mummy tace “insha Allah Daddy” MK ne yayi saurin fadin “but I am fine ai Daddy.. a barta ta gama abinda take yi.. it’s very important to her” Mummy ce tace “more important than you?? haba MK.. ai duk abinda take yi dole ne ta bar shi ta dawo” Shi dai Fahad sai sauraron su yake yi yana mamakin halin MK, shi da yayi tunanin zai fadi musu ainihin abinda ya faru amma shine ya boye… ya rasa wane irin so yake yi ma Maleeka. Daddy ne yace “but what happened?? ya akayi ka samu accident a cikin gari just like that??” MK ne yace “uhm.. Daddy I just lost control ne. I am sorry” Mummy tace “harda stress MK, you need to rest kamar yadda doctor ya fadi..” Hafsah ce ta shigo riqe da ledar Magani yayinda tace “your medication Ya MK, prescriptions din are attached” Yace “thanks Chubby” turo baki tayi tace “Mamy kin ga ya fara ko?? dagaske zan koma in ce ma likita kar a sallame shi” Gaba dayan su dariya sukayi yayinda Daddy yace “qyale shi Hafsatu.. gwara a kira mutum chubby din da a kira shi slim kamar bulala” Haka dai suka dinga dariya. Mamy ce ta kalli MK tace “toh kai yanzu mu tafi gida na tunda matarka bata nan ko kuma ka tafi da Hafsah..” Da sauri Hafsah tace “ni bazan je ba tunda chubby yake kira na” MK wanda yayi mata gwalo ne yace “yi zaman ki chubby..” Ya ba Mamy side hug yayinda ya kwantar da kanshi a kan kafadar ta yace “hey I am fine..” Ya nuna jikinshi yayinda yace “it’s not as if na ji ciwo ne fa… dagaske I am fine and I can take care of myself” Tana riqe da hannun shi tace “don Allah kayi qoqari ka zauna a gida ka huta kamar yadda likita ya buqata ka ji??” Girgiza mata kai yayi yana murmushi yace “I will sweetheart” Hafsah ce tace “sweetheart ko?? sai na gaya ma Abba kana kiran matar shi sweetheart” Gaba dayan su suka fashe da dariya. Mamy ce ta kalli Fahad tace “kai kuma idan har ya zo office within the 3 days da likita yace ya samu hutawa ka kira ni ka sanar mun” Fahad yana dariya yace “insha Allah Mamy” ************* Fahad ne ya tafi da abokin nashi gida yayinda su Mummy da su Mamy suka shiga motocin su suka tafi gida. ************* Tafe suke a kan hanya yayinda ya kwantar da kan shi a seat… idanuwan shi a rufe suke yayinda zuciyar shi take zafi. Tunda MK da Maleeka suka taso basu taba samun matsala ba sai wannan karon.. basu taba yin fada ba… why after marriage?? a time that they are supposed to get closer… Ji nayi ya saki numfashi. Fahad wanda yake tuqi ne yace “abokina meyasa baka fadi musu abinda yake faruwa ba?? how sure are you Maleeka tana Ingila??” STORY CONTINUES BELOW MK wanda ya dan bude idanuwan shi ne yace “wallahi abokina idan na fada ba qaramin baci rayukan iyayen mu zasu yi ba especially Daddy.. na tabbatar har dukan tsiya sai yayi mata banda fushin da zaiyi da ita”1 Idanuwan shi ya rufe yayinda ya cigaba da fadin “I am sure tana neman space ne just to calm herself down… na tabbatar kuma she will come around. I know she loves me just the way I do, I am sure komai zai koma normal” Fahad ya girgiza kai yace “I hope so abokina” ♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO ABUJA Ko da suka shiga gidan sashen shi suka nufa. MK dai kwanciyar shi yayi a kan kujera yayinda Fahad yake zaune a kujerar da take kusa da nashi. Fahad yana kallonshi yace “ka tabbatar bazamu lallashi chubby ta zo tayi zaman jinya ba kuwa??” MK yayi murmushi yace “ai Hafsah da kake gani muguwar ‘yar shirme ce.. ko ta zo I swear babu wani amfanin da zata yi mun.. the girl is always busy with her books and gadgets.. besides I am okay” Ajiyar zuciya yayi yace “I think zan je England in a day or two.. I really want to talk to Maleeka.. I really want to apologize for everything..”5 Da sauri cikin masifa Fahad yace “just shut up abokina… how do you even know she is there???wallahi babu inda zaka je kuma ka ji nayi rantsuwa bazan yi kaffara ba you are going nowhere… haba don Allah, wannan ai ko asiri tayi maka sai haka. Ya za’a yi ka bi ta bayan kai tayi ma laifi? soyayya ai ba hauka bace abokina.. laifin ka nake gani a dukkanin abubuwan da suke faruwa… tun farko kai ka shagwabar da ita ka bata ta da har take yi maka abinda ta ga dama. A matsayin ka na mijinta ta isa tayi maka abinda tayi ne?? now look at it.. she even left the house without your permission.. you just had an accident a dalilinta, banda don Allah ya tsare who knows what would have happened to you”2 Ya nuna MK da yatsa yace “I swear idan ka bi ta wallahi I will disown you..”7 Cike da mamaki MK yake kallon shi yayinda yace “don Allah ka daina wannan maganar abokina..” Fahad ya miqe tare da fadin “just try going after her and I will show you how serious I am… I will keep you posted with regards to office and incase you need anything just give me a call… Allah ya qara sauqi” Bai jira MK yayi magana ba ya fice abinshi. MK dai jikin shi ne yayi sanyi yayinda ya ji duk bai ji dadi ba. Allah ma ya sani yana bala’in son Fahad… he just cant imagine life without a friend and a brother like him. Gani nayi ya dauko wayar shi yayi typing message kamar haka: “abokina please I am sorry.. I wont go after her, I give you my word”3 A lokacin da saqon ya shiga wayar Fahad kuwa ya tada motar shi kenan zai bar gidan. Gani nayi ya girgiza kai yana murmushi yace “that’s like a good boy.. da ban yi mishi haka ba I am sure sai ya bi ta..” Saqo ya tura mishi kamar haka: “apology accepted my friend… wishing you a quick recovery. take care” ♧♧♧♧♧♧♧ THE DORCHESTER HOTEL LONDON-ENGLAND Kwance take a kan gadon suite din yayinda take ta rusa kuka. Jameela wadda take kallonta cike da takaici ce tace “a gaskiya kin kwafsa qawata… why the hell did you run away??? ke fa kika yi mishi laifi sannan da alama ma bai dauki abun da zafi ba..you should have stayed and listened to what he has to say” Cikin kuka Maleeka tace “toh wai in tsaya in saurare shi akan me? tun farko ba shi ya janyo abinda yake faruwa ba?? da bai yi insisting on wanting to have a child ba duk da haka bata faru ba… ba’a taba sanya ni a spot irin wannan ba a rayuwa ta. I just… I hate him” Jameela dai fashewa tayi da dariya tace “lallai Maleeka qwalwar ki tana da matsala I am sure.. you hate him?? toh why??…” Ta gyara zama sannan tace “look Maleeka… nasani cewar tabarmar kunya ce kike qoqarin nadewa but trust me you are doing it the wrong way. yanzu tell me, da kika ce after the fashion show bazaki koma ba me kike nufi?? shi kike jira ya biyo ki ya baki haquri ko me??? wai meyasa kika cika girman kai ne a rayuwar ki??” Maleeka ta share hawayen ta sannan tace “I know what I am doing Jay.. ni kam babu inda zan je sai ya zo da kanshi… kuma I am sure idan dai Honey ne zai zo”22 Jameela ta girgiza kai sannan tace “Allah ya baki sa’a qawata.. but I swear you might just be making the biggest mistake of your life..”2