DOCTOR EYSHA CHAPTER 4 BY FANAN_A.A

DOCTOR EYSHA CHAPTER 4 BY FANAN_A.A

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wasu zafafan hawaye ne suka Fara Ambaliya a fuska ta saboda kullum idan Na tunu iyaye Na Dole sai Na zubar da hawaye saboda irin mutuwar da sukayi ta ƙasƙanci,

Tashi nayi Dan ina da patient din da zan duba .

*Doctor Kareem*

Zaune yake a office dinsa duk abin duniya ya dame Shi Akan *doctor eysha* da doctor Aryan,

Saboda duk yadda yaso ya haɗa wani tuggun sai sun kawu karshen Shi,

Maganar zocin da yake d CE ta Fara fitowa “tabbas sai nayi yadda nayi Na shiga tsakaninsu yadda koda a hanya suka hadu baza su Kali juna ba , hhhhhhhh “, wata muguwar dariya CE ya Fara yayin da yake dauko wata takkada sannan ya raba ta zuwa gida biyu , “yadda Na raba wannan takaddar gida biyu haka Zan lalata alakar Ku my dear eysha, ts ts ts ts poor eysha , nasan menene raunin ki ” wata muguwar dariya ya Kara kecewa da ita sannan yace ” ke da doctor Ibrahim kunyi yadda zakuyi Kun rufe asalin Ki a tinanin Ku Babu Wanda ya sani ,hhhhhh ” knocking ɗin office dinsa da ake ne ya dawo dashi daga duniyar tinanin da ya shiga .

“yes ,come in”.

Matar datayi knocking dince ta shigo office din ,ya bata izini ta samu wuri ta zauna .

“dear Dr zahra kece anan ?” ya fada yana washe baki “ai Na dauka bazaki zo ba ,gaskiya yau ina daya daga cikin masu sa’a a *KASHMIR*.

” AI Kaima kasan zanzo dazu messenger yaje office Dina yace kana nema Na ,tohm akwai patient din da nake dubawa shiyasa kaga na ɗan Daɗe Dana taho kuma Na biya office din dad ” takai karshen zancen tana gyara gashin ta daya zubu ya rufe Mata fuska .

“dama abin daya saka Na Kira ki shine ina da wata shawara Akan yadda hospital dinnan, Amma nasan idan nine najewa da doctor Ibrahim da wannan maganar bazai dauka ba ,kinsan yanzu kema daƙyar zai ɗauki zancen ki ,gaba ɗaya yanzu baya Jin shawarar kowa sai ta masoyiyar sa doctor maryam ” ya fada yana marairaice fuska kamar wani abin tausayi .

” Dakata Dr kaseem ,ka fadi duk abin da kake so ni Kuma nayi alkawarin sai Na saka Dad yayi Shi,yau Dole ya zaba tsakaninmu da doctor maryam” ta Fada Rai a ɓace .

Wani mugun murmushi ya saki Dan kuwa yanzu ya kamu bakin zaren ” calm down dear ai nasan zaki iya ,abin da nake so fa ba wani Abu abane illa ina son a bude *Luxury ward* a nan hospital din .

Gani nayi yayi hanyar ya saka Ni saurin Dago kai ina niyar yi masa magana, 
Kafin na daga baki na kawai naga yayi wurgi dani da yarinyar daga asibitin, cikin rashin sa’a kaina ya Bugu da flower base din dake kusa dani, 
Saurin Mikewa nayi na yi wajen sa ina fadin “Haba doctor wannan wani irin Abu ne kaga fa halin da yarinyar nan ta…..”.
” dakata eysha, Ni ina ruwa na idan ta mutu, karfa ki manta wannan asibitin kudi ne kuma mu customers muke Nima, shiyasa nayi ma mutane magana akan cewa zamu kula da ita, Amma gaskiya badai a wannan Asibitin na, 
Yanzu haka Kinsan kina da surgery wanda za’ayi ma alhaji baba dala Kinsan yana da mahimmanci sosai ” ya fad’a ku juyo wa baiyi ba. 
Nan ya barni a tsaye Kamar wacca aka zarewa rai danni yanzu Al’amarin doctor kaseem ya daina bani mamaki ya Koma bani tsoro 
” Wannan tsayuwar bayi maki zatayi ba kawai ki taho muje muyi mata surgery, Dan nasan indai doctor kaseem ne bazai bari ba Dan shi a wajen sa babu abinda yafi kudi “
Ya fad’a yana ‘ko’karin daukar yarinyar da tun a ambulance muka yi mata alurar bacci. 
Binshi na ringa yi muna shiga daga hanyar sirrin da Likitocin Asibitin kawai suka santa, da taimakon Kati na har muka samu muka isa wajen. 
MUN samu nasarar yi mata aiki Amma dole ne ya saka na dauke ta na mayar da ita hannun tsohuwar kirki wacca ta rike Ni a gidan marayu. 
*ASALIN DOCTOR EYSHA*
Doctor umar Muhammad
Ya Tashi a hannun kanin mahaifan sa dalilin rayuwar iyayen sa tun yana yaro, yaro ne mai matukar basira Dan Allah ya basa baiwar basira, hakan ya saka ta saurin kammala karatun sa na Likitocin, 
Doctor umar da doctor Ibrahim abokai ne sosai Dan Kuwa babu abinda ke raba su saidai bacci sun shak’o da juna sosai Amma saidai an samu akasi daya wajen halayen su sun bambanta, Dan Kuwa shi Doctor Ibrahim mutum ne mai saukin kai sosai bashi da wani matsala, yana girmama patients dinsa. 
Akasin haka aka samu a wajen doctor umar Dan Kuwa mutum ne shi ma muguwar zuciya gashi bashi da kirki ko kadan, gashi baya daukar mutane da daraja ko kadan, 
Hakan ne ya saka halayen su suka bambanta. 
Doctor umar ya hadu da doctor nasiba inda har soyayya ta shiga tsakanin su har takai ga aure, 
Akwana a Tashi asarar mai rai, Allah ya bama doctor Nasiba ciki Karka so kaga murna a wajen doctor umar a wajen doctor umar Dan Kuwa ko ‘kuda baya so ya taba ta, daya ke dama hali yazo daya da ita doctor Nasiba din dashi Doctor Umar din hakan yasa tayi kicin kicin ta raba su da doctor Ibrahim Dan Kuwa ganin ta bata son Kuwa ya rabi mijin ta, basu dade ba a haka ta haifi diyar ta Mai matukar kyau ba Dan Kuwa daga Doctor Nasiba din harshi Doctor umar din asalin kyawawa ne, 
Aiko yarinya taci sunan Aisha Amma ana kiran ta *EYSHA*. 
Haka doctor Umar da Nasiba suka cigaba da cin Karen su babu babbska ita da mijin ta Dan Kuwa yanzu sun dauki ran mutane Kamar na dabbobi babu wanda ya isa ya taka masa burki Dan Kuwa abinda suke so suke, 
Hausawa na cewa rana daya ta barawo daya kuma ta Mai kaya, 
Wata rana wani mutum ya kawu matar sa tana nakuda, kasancewar shi talaka ne bashi da kudin da za’a yi mata aiki a ciro Dan haka suka aje matar a kasa tana neman agaji Amma ko kallo bata ishe su ba 
“Dan Allah likita ki taimaka man karda na mutu ina cikin wani hali “
Mai nakudar ta fad’a tana rike kafar Doctor Nasiba. 
Cikin fushi ta saka kafa ta shuri matar Dan ita a ganin ta ya za’ayi wannan kazamar ta taba ta” dalla malama ja baya Ni ina ruwa na idan kin mutu ” ciki rashin sa’a ta fadi akan cikin ta ko shurawa ba tayi ba tace ga Garin ku nan, 
Hakan yayi dai dai da isowar mijin ta da ‘Yan jarida Dan Kuwa Yan jarida duka sun dauki abinda ke faruwa, kafin Kace me gaba daya vidion ya yadu Kamar wutar daji, hakan ya harzu’ka mutane sukayi ta zanga zanga karshe ma suka samu damar kwatar Doctor Nasiba daga hannun hukuma suka cinna mata wuta ta rasu a gaban mijin ta hakan yasa shima ya hadiyi zuciya ya mutu 
Mutane sunyi ‘ko’karin ganin sun kashe *EYSHA* AMMA Allah bai basu sa’ ar hakan ba saboda doctor Ibrahim daya buye ta daga nan ya turata England tayi karatu Dan ta zama Likita hakan zai dauke Idon mutane a kanta. 
Bayan shekaru sha biyar ta Dawo lokacin ta gama karatu har ta zama budurwa mai shekara 20, 
Batayi wahala ba
wajen neman aiki ba kasancewar yanzu doctor Ibrahim yana da babban hospital daya bude Dan Kuwa yanzu yana daya daga cikin asibiti da suka fi kowanne a Africa. 
*Doctor Aryan* yana daya daga cikin manyan likitocin da Ake ji dasu acikin *KASHMIR HOSPITAL* kasancewar mutum ne shi mai amana D jajircewa akan Aikin sa tohm kunsan duk mutumin da aka ce yana da rukon amana dole zai ringa haduwa da kalubali iri iri. 
*DOCTOR Maryam* kyakkyawar Likita ce yar kimanin shekaru 40, Itace shugabar Likitici mata a asibitin, mutum ce ita mai hakurin gaske ga kuma kirki, hakan ya saka *EYSHA* ta dauke ta Kamar uwa.
*DOCTOR kaseem* yana daya daga cikin jagororin asibitin Dan Kuwa gaba daya kudin asibitin daga hannun sa suke shiga da fita, mutum ne shi mara kirki bashi da mutunci ko kadan, mutanen asibitin suna ganin shi yana mugun son kudi Amma ba haka bane danshi daukar fansa ta kawu sa hospital din. 
*DOCTOR Zahra* ‘ya ce daya tilo a wajen doctor Ibrahim yana sonta sosai kullum ‘ ko’karin sa yaga ta zama mutuniyar kirki, Amma ita ba haka bane saboda bata da babban aboki wanda ya wuce kaseem hakan ya saka taken mugun daukar shawarar sa. 
*FANAN_A.A* 🥰🥰🥰🥰🥰🥰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *