JARIRI CHAPTER 4 BY AMEERA ADAM
Adam da ke riƙe da Inno gyara mata kwanciya ya yi a akan kujera shima ya rufa musu baya dan ganin an shawon kan Goggo, dan tun da tace bazata bisu a mota ba sun san ta zauna kenan. Halifa na ganin Adam na binsa ya wurga masa key yace. “Maza ka taho da motar, sai ka rufe gidan.”+
Adam ɗaukan mukullin ya yi ya juya ya tayar da motar sannan ya fito ya koma ya janyo gate ɗin ya rufe ya zura sakata sannan ya shiga ta ciki ya buɗe ƙaramar ƙofar ya fito yana fitowa ya datse ta da ƙarfi.
Halifa bai taɓa sanin Goggo na da gudu haka ba sai da wannan tseren ya haɗasu, da ƙyar ya sha gabanta yana haki yace. “Goggo dan Allah ki tsaya kiji, yanzu idan muka koma gida babu ke me zamu cewa su Daddy?” Goggo itama mayar da numfashi take saboda tsabar gudu zaninta ya tattare ya koma kusan gwiwa, takalmanta duk sun shige wajen idanun sawunta kamar yadda yara suke zura ƙafafuwansu cikin igiyoyin takalmin. Sai da ta ja numfashi ta ce. “Halifa kasan Allah yau ko Ubanka Salisu ne yazo bazan shiga motarka ba, haka kawai hatsabibin yaro sai nuna mana salawaitun siddabaru yake yi. Kai bari ma kaji muddin muka koma gida ana yiwa Rakiya sutura zaka sakar mini jika” Goggo na zuwa nan ta fara ƙwallah tana cewa.
“Allah sarki Rakiya ke kuma ta wannan hanyar tazo miki. Mutuwa kenan rigar kowa Halifa wallahi tsakanina da kai Allah ya isa da baka yiwa Nusaiba ciki ta haihu ba ai Ɗanka bazai kashe mini ƴar uwa ba. Kaico rayuwa zan idar da salawaitun tsautsayin da ya sameni ni ɗiyar me Salati.” Haushi ne ya fara kama Halifa yace.
“To muje idan munje gidan duk abinda kika ga dama sai ki faɗa, amma wallahi idan sama da ƙasa zata haɗe ba wanda ya isa yasa na saki matata. Kuma karki ƙara yi mini Allah ya isa haka kawai tsofaffi kwata-kwata bakinku baya furta alheri.” yana rufe baki Adam ya ƙaraso da motar ya kashe ta sannan ya fito ya zagayo gurinsu.
Goggo tana daga tsaye ta faɗi daɓar irin zaman ƴan bori, hannu ta ɗora aka ta fara kuka kamar wata ƙaramar yarinya, Adam ne ya tambayi dalilin kukanta aikuwa kamar me jira ta kuma rushewa da kuka ta kalli Adam ta ce. “Adamu wai yau ni Halifa ya nunawa salawaitun iyakata. Ya nuna bani na haifi ubansa ba har yake yi mini salawaitun rashin kunya. Maza ka bashi mukullin motarsa ta tun bai rufeka da salawaitun duka ba ya ƙwaci abinsa” Adam yasan rikicin su sarai dafe kai ya yi ya ce.
“Goggo dan Allah ki tashi mu tafi kinga mutane sun fara kallonmu…” A hassale ta katse shi da cewar.
“Adamu wacece ni a gurinka?” Adam a daƙile kamar zai yi kuka yace. “Wace ce kuwa ban Kakata” Goggo sakin baki tayi tana rafka salati sai da ta gama cikin ƙunci tace.
“Haka kake bawa Nadabo amsa dama, gatsal ba ladabi ni kake cewa haka kamar bani da wata salawaitun alaƙa da kai.” Goggo ta rushe da kuka tana share majina da gefen zaninta tace.
“Allah na tuba dama wace salawaitun alaƙa garemu? Na san dai nina haifi Ubanka Nadabo bayan wannan sai me kuma? Dama nasan tsaf sai ka kwaso mugun halin uwarka dan wannan ba salawaitun halin Nadabo bane.”
Ana cikin haka ya hango Ɗan sahu da sauri ya tsayar da shi dukda Goggo ta ƙona masa rai yace. “To muje ga Adaidaita sahu nan na taro mana” alama ya yiwa Halifa yana miƙa masa mukulli.
Goggo ta yunƙura ta miƙe tana cewa. “Haka kawai da ka nacewa motar kamar gadon ubanka. Me ake da Halifa ni da Ɗansa ya kashe mini ƴar uwa wallahi har abada Halifa ka ƙara yi mini salawaitun magana sai na ɓalɓalce ka.”Halifa ƙwafa ya yi bai kulata ba ya shiga mota ya bata wuta ya barsu Goggo anata kiciniyar shiga Adaidaita sahu.
Halifa shi ya riga su Goggo zuwa gida lokacin da suka ƙarasa ana ta kiciniyar kwantar da Inno akan tabarma, Goggo na shiga taje gabanta ta fara matsar ƙwallah.
Ruwa Mommy ta ɗebo aka fara yayyafawa Inno a hankali ta fara buɗe idonta, cikin juyewar kai ta fara kallansu da suke tsaitsaye akanta. Ɗago hannuwa biyu tayi alamun roƙo tace.
“Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Annabi muhammadu bawansa ne kuma manzan sa ne. Saboda wannan ranar aka koyar da mun dan gudun ɗebe mana albarka. Salloli biyar basa wuce ni harda nafila da dai Hansai ce nasan bata cika ƙara farilla akai ba, Wa saumu ramadana har na alhamis da litin baya wuce ni.
“Gabaɗaya ido suka zurawa Inno dake kwance tana ta sakin zance cikin gigita, Halifa na ganin haka ya ja guntun tsaki ya bar gurin saboda ya lura tsabar ruɗewa ce take damun Inno. Daddy ne ya russuna yace. “Sannu Inno ya jikin?” Inno wani marayan kallo ta bi Daddy da shi kamar bazata tanka masa ba zuwa wasu ƴan sakanni ta ce.”Eh to, zakkar ce dai ban samu ikon fitarwa ba ƴan kadarorina basu kai a fitar da zakka ba, gonar bayan gidan Idi me saniya ce sai awaki biyu. A yanzu kam bakin alƙami na ya bushe amma da ana komawa da babu tantama Salisu zai bayar da zakkar a madadina” Goggo na jin haka ta ja da baya ta kife a gurin ta rushe da wani irin matsanancin kuka, gurin shiru ya ɗauka dan da alama kansu ya fara ɗaukan zafi.+
Goggo sharce hawayenta tayi ta ɗago ta ce. “Kai jama’a yau ina ganin salawaitin tashin hankali a gidan nan. Amma dai Allah ya tattaro salawaitun albarka ya kwashewa wannan hatsabibin jaririn, ku dubi yadda yasa akayi jinkirin kai Rakiya har matambaya sun dafeta tun daga gida. Wallahi bazan ɗauki wannan salawaitun rashin imanin ba wallahi sai dai hukuma ta rabamu, nikam ba zan yi salawaitun ja’inja da wancen hatsabibin ba amma wallahi yadda aka kashe mini ƴar uwa sai ankashe Halifa da Nusaiba har lahira” Juyowa sukayi suna kallon Goggo saboda yadda ta rikice musu ga Inno take ta zabgo surutai.
Abba ne ya tsugunna gurin Goggo cikin lallashi yace. “Goggo dan Allah kiyi haƙuri kiyi shiru Inno fa ba mutuwa tayi ba rikicewa da tayi”
Goggo wani kallon tsana take bin Abba da shi, saboda takaici rasa abin faɗa ta yi cikin takaici ta rufe Abba tayi da duka hannu bibbiyu ta ce. “Wallahi Na dabo da ba dan bakin Uwa kaifi gareshi ba da babu abin da zai hana in kwashe maka salawaitun albarka ba ka ɓalɓalce kowa ya huta.” Abba tashi ya yi yana ƙara bata haƙuri amma Goggo ko ta kansa bata bi ba tana cewa.
“Wallahi Na dabo ko kaine akan Rakiya sai hukuma ta rataye ka bare Nusaiba, yadda Ɗansu ya kashe mini ƴar uwa sai anhukunra su.” ta ci gaba da kuka sannan ta ce. “Sai dai idan kuɗi zaka bayar a sake su amma ko cikin dare ne sai na bi na datse igiyoyin numfashinsa.”
Babau wanda ya tankawa Goggo ana cikin haka Family Doctor ɗinsu ya shigo hannunsa ɗauke da kayan aiki, da sauri suka tare shi suna yi masa barka da zuwa. Yana zama ya buƙaci da su ɗan basu guri saboda yana buƙatar ya dubata cikin nutsuwa, Goggo ƙaddabe ƙasa tayi akan babu inda zata sannan ta baɗe shi da maganganu.
“Kai yaro dube ni da kyau karka nuna mini salawaitun cin mutumci ido biyu, wanne ha’incin ne basu iya ba iye? Gaya mini meye bakwa yi salan na fita ka cicciri sassan jikin ƴar uwa sabo
da salawaitun rashin imani. To wallahi kurwar ƴar uwata kur…” Abba ne ya katse ta ya cewa. “Haba Goggo wannan fa likita kuma shi ne fa yake kula da mutanen gidan nan babu wani abun cutarwa da zai…” a hassale Goggo ta ce. “Kai Na dabo ka saurara mini wallahi bar ganin ka tara abin duniya ka yi mini salawaitun duniyanci kar nake kallanku sakarkaru.” Dr Muhsin ne ya kalli Abba yace. “Barrister ka ƙyale ta babu damuwa.” Goggo ta bishi da harara tana yin ƙwafa.
Abba da Daddy kan kujera suka koma suka zauna Dr Muhsin ya matsa gaban Inno da ke kallonsu da shanyayyun idanuwanta, a hankali ya fara gwaggwada ta yana dubata sannan ya saka mata tare da allurar bacci, ba’a ɗauki lokaci ba bacci ya yi awon gaba da Inno ta fara sauke wahalallen numfashi.
Dr Muhsin ya fara tattara kayansa da niyyar haɗa su kafin ya yiwa su Daddy bayanin abin da yake damun Inno da halin da take ciki, Goggo na ganin haka da sauri ta shaƙo wuyansa katamau tana cewa.
“Alƙur’an babu inda zaka je. Baza ka tafi ko’ina ba sai sai ƴar uwata ta tashi” Dr Muhsn cikin wata irin murya yace. “Baba lafiya me nayi miki ne?” Kafin Goggo ta yi magana Daddy da Abba sun taso kan su Goggo cikin tsananin jin kunyar Dr suka fara magana.
“Haba Goggo dan Allah meye haka kike yi yanzu abin da kikayi kin kyauta kenan?” Daddy ya ƙarasa faɗa yana ƙoƙarin ɓamɓare hannun Goggo daga wuyan Dr Muhsin. Goggo ban da nishi babu abin da take yi saboda yadda ta taƙarƙare ta sa ƙarfi ta maƙure Dr Muhsin, Shi kuma kawaici ya yi ganin Mahaifiyarsu da Daddy ce kuma ga girma dan bazai iya hankaɗe ta. Da ƙyar da siɗin goshi suka cire hannun Goggo daga wuyan Dr Muhsin. Ana cire hannunta Dr Muhsin ya yi caraf ya miƙe ya yi gefe yana maida numfashi.
A gagguce ya fara musu bayani dan ba ƙaramin shaƙa ya sha a hannun Goggo ba.
“Barrister ba wani babban ciwo bane yake damunta ta ɗan shiga firgice ne na ɗan wani lokaci, amma da zarar ta tashi daga bacci zata koma normal. Akwai magungunan da zata dinga sha zan rubuta musu sai a siyo mata, kar a dinga yawan barinta ita kaɗai saboda kar ta dinga yawan tunani.
Yana gama faɗa ya fice daga falon ko waiwaye baya yi, Goggo miƙewa tayi ta ƙarasa gaban Inno da take bacci tana ƙarasawa ta share hawayenta a hankali ta ce. “Allah ya baki salawaitun lafiya Rakiya” Daddy da Abba babu wanda ya tanka mata gabaɗaya suka fice daga falon.
Inna sai da ta shafe sama da awa huɗu tana bacci sannan ta farka, tana farkawa a cen gefe ta hango Goggo tana ta zabga gyangyaɗi a hankali ta ce. “Hansai” da sauri Goggo ta buɗe ido aikuwa tana ganin Inno ta tashi zaune ta fara yekuwa a cikin falon, nan da nan mutanen gidan suka ɗauko zuga suka shigo falon.
Tana hango Nusaiba da Halifa ta miƙa hannuwa biyu ta ce. “Ku matsa wallahi karku ƙaraso mini idan ba haka ba sai na ɗebe muku albarka duk kun ɓalɓace.” Kallan kallo aka fara yi kowa yana kallan ɗan uwansa babu wanda ya fahimci ga da wanda take. A hassale Inno ta ce. “Halifa wallahi ko a lahira na ganku a kusa da ni saina ɗebe muku albarka.” Halifa baya ya ja a hassale ya ruƙo hannun Nusaiba zasu fita. Nusaiba ta marairaice fuska ta ce. “Hubby karka biyeta kasan rikici irin na su Inno” Inno na jin haka ta ce. Uwarki ce me rikici sakarya maras ɗa’a kai Salisu wallahi idan baku dakatar da su Halifa ba zan bar muku gidanku na shiga duniya dan na Allah basa ƙarewa.” Goggo tayi karaf ta ce. “Wallahi ƙafa ta ƙafarki dan ba zan zauna ganin salawaitun rashin ɗa’a da cin mutumcin da za’a yi wa ƴar uwa ta ba.”
Halifa da sauri ya fisgi hannun Nusaiba suka fice daga ɗakin yana huci ya wuce falon su Hajiyansa.
Bayan kwana biyu jikin Inno ya dawo dai-dai kuma Halifa da Nusaiba sun dawo gida gabaɗaya da zama saboda Inno da Goggo sun ce Allah ya kashe su bazasu ƙara zuwa gidansa su zauna ba, Kuma tun daga ranar babu wani abun firgici da suka ƙara gani. Ana gobe suna gidan cike yake da baƙi daga ɓangare daban-daban, Kayan miya a sayo da kayan abinci kala-kala na ƴan suna. Kayan drinks da kayan gift ɗin da za’a bawa ƴan suna.
Da daddare bayan sallar isha”i Hajiyan Halifa ta shiga cikin store, tana shiga kamar almara ta hango ɗan dunƙulallen mutum ya juya bayansa. A gaban kabewa ta hangoshi ya zage iya ƙarfinsa sai gwaguyar kabewa yake, jikinta na tsuma ta ja gefe banda karkarwa babu abin da take ji, Jariri na jin motsinta ya juyo hannunsa ɗaya ɗauke da rabin ƙatuwar kabewa, da sauri ya fara takowa yana tafe yana tura ciki gaba yana wata rangwaɗa. Yana zuwa gabanta ya fisgota da ƙarfi har ta kai ƙasa, kabewar hannunsa ya miƙa mata cikin wata irin murya yace. “Ungo zauna ku sha tare” Jariri ɗuk abin da ya gani ya ɗauka ya ci idan ya rage sai ya wurgowa Hajiyan Halifa yace ta cinye. Fakar idonsa tayi ta miƙe saɗaf-saɗaf ta fice daga store ɗin, har ta kusa shiga babban Falo ta Jariri ya ta ho da gudu ya cafko zaninta, Hajiyan Halifa iya ƙarfinta ta zage ta fara kwarara ihu. Jariri bai fasa ba har sai da ya ga ya fisge zanin jikin ta.Hajiyan Halifa na ganin ya fisgi zaninta daga ita sai ɗan fatarin ciki ta miƙe ta shiga cikin falon, da sauri tafi da gudu ya cafko siket ɗinta yana niyyar fisge shi shima gabaɗaya. Da ƙyar ta saau tayi ta maza ta hamɓare shi da ƙafa ta samu ta shige cikin Ɗaki, Daddy na zaune ya ga shigowarta da sauri ta banka ƙofar ta rufe. Daddy da mamaki yake kallonta yace. “Mommyn yara lafiya me yake damunki?”+
Mommy dake sauke haki ta ce. “Wallahi aljani ne ba mutum ba jaririn Halifa aljani ne da idona naga yana cin Kabewa” zaro ido waje Daddy ya yi yace. “Jariri kuma? Wai me yake faruwa ne ke kince Jariri su Inno sun ce Jariri wai kaina fa ya kulle” Mommy ta ce. “Wallahi nima na gani da ido na, dubi fa har zani ya cire min Allah me kaɗai yasan abin da ya yi niyyar aikata mini, wallahi kamar wacce zai haikewa haka naga yana ƙoƙarin farmaka ta.”
murmushin takaici Daddy ya yi yace. “Dan Allah ki daina faɗar haka karma wani yaji, kema ruɗa kanki zakiyi ne kamar yadda su Inno suke gigita kansu, wannan zancen banza ne dan Allah wuce ki ɗau zani ki ɗaura Allah yasa ƴaƴanki basu ganki a haka ba.” Mommy ta ce. “Amma fa…” Ya katse ta. “Amma me?” ki wuce ina da abin yi banasan jin wani abu.” Cikin ƙunan rai Mommy ta wuce tana ƙwafa dama tasan idan zata kwana tana faɗa bazai yarda ba.
Cikin tsakiyar dare Daddy ne zaune a falo ya jona laptop yana wani aiki, gidan shiru babu motsin komai sai ƙarar keyboard ɗin laptop ɗin da yake dannawa. Yana nan zaune yaji an jefo wani abu da ƙarfi, yana waigawa yana ƙafafauwan ragon guntulallu da jini yaɓe-yaɓe a jikinsu, da sauri ya zaro ido cikin mamaki yana ture Laptot ɗin gefe.Yana ƙoƙarin tashi ya takun tafiya ƙwas ƙwas ƙwas yana kallon bakin ƙofar yana Jariri hannunsa saɓe da kan rago ya rungumo shi gigin-gigin kamar zasu faɗi tare, Jikin Daddy ne fara ɗaukan tsuma yana yunƙurin tashi ya ga Jaririn ya datse ƙofar falon sannan ya sunkuyo da kan ragon yana lasar jinin da ke ɗiga daga jikin kan ragon.
Daddy ja ya fara yi da baya yana karkarwa da sauri Jariri ya wurga masa kan ragon yace. “Ungo tayani ci tunda da kai muka haɗu.” Daddy kallan kai ragon ya yi yaga anyi masa ɓuloli ta ko’ina, tsugunnawa Daddy ya yi yace. “Dan Allah ka yi haƙuri ka mun rai bazan iya cin ɗanyan nama ba.” Jariri kallan tsaf ya yiwa Daddy yace. “To cire rigarka” ba musu Daddy ya tuɓe rigarsa daga shi sai gajeren wando kuma har lokacin jikinsa sai ɓari yake.” Jariri yace. “Wallahi ko ka ɗauki kan rangon kaci ka na saɓa kamanninka” Daddy ya tsaya yana kallon Kan jaron sunan da aka siyo na jaririn da za’a yanka, a zuciyarsa ya ce. “Ina ɗayan ragon badai shima ya cinye s
hi ba, ashe dai maganar su Inno a hanya take?” Jariri kamar yasan abin da yake zuciyar Daddy yace.
“Na cinye ɗayan ragon da kuka siyo ba dan ni kuka siyo ba? To wannan kai zaka cinye shi.” Daddy yayi tsumu yana zare idanu, Jariri na ganin haka ya nufi gurun da Daddy ya jona laptop ɗinsa ya fisgo chager, riƙewa ya buga tsalle ya ranƙwalawa Daddy kan cazar a kansa da ya sha ƙwaryar molo. Daddy durƙushewa ya yi a gurin yana lailaya kai cikin azaba, bai yi aune ba yaji Jariri ya kuma rankwala masa a kai.
Cikin tsananin azaba Daddy ya dafe kai yana cewa. “Wayyo Allah jama’a ku cece ni zai kashe ni” Jariri tsalle ya buga ya dira a kan tumbulelen tumbin Daddy ya fara sukuwa a kai, Daddy tun yana iya roƙo har ya fara kasa magana. Jaririj ɗaga shi ya yi, ya koma kan kujera ya zauan. Wani tsoronsa ne ya ɗarsu a zuciyar Daddy saboda wahala ko motsi ya kasa yi. Daga gurin da yake Jaririn yace.
“Tashi tsaye” Daddy jiki na ɓari ya yunƙura da ƙyar ya tashi kansa har yayi ƙullutu biyu gurin da Jariri ya ranƙwala masa kan caza. Daddy na tsaye Jariri yace. “Maza kayi mini rawar Ɗan maliyo maliyo” Daddy hawayen wahala yake yi yace. “Ranka ya daɗe wallahi ban iya ba” yana rufe baki Jariri ya diro ƙasa ya dafe kai da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya dafe ƙugu da shi, turo ciki gaba ya fara yi idan ya yi taku ɗaya sai ya tura baya har wata rangwaɗa yake yi yana cewa. “Ɗan maliyo maliyo, maliyo. Ɗan maliyo nawa, Maliyo.” idan yace maliyo sai ya dafe ƙeya ya girgiza ciki.
Yana gamawa yace. “Maza kayi irin rawar da nayi yanzun nan” Daddy hannunsa biyu yasa ya riƙe ƙugu yana yana cewa. “Ɗan maliyo maliyo, maliyo.”
(🤣🤣😂 Mai karatu ka harsaso min muryan Daddy yana waƙar ɗan maliyo maliyo)
Jariri na jin haka ta ja guntun tsaki ya fisgi cazar laptop ɗin ya ƙara ranƙwala Daddy a ka yace. “Haka nace masa hannuwa biyi zaka riƙe ƙugu da su? Ba hannu ɗaya a ƙugu ɗaya a ƙeyar ka zaka riƙe ba.” Daddy kuka yake shaɓe-shaɓe ya miƙe ya ci gaba da dafe ƙeya yana tura tumbi gaba yana waƙa.
Sai da ya jima yana abu ɗaya har ya galabaita banda gumi babu abin da yake yi, Jariri ya dakatar da shi sannan yace. “Yanzu kuma rawar salawaitun salo zamuyi” A wahalce Daddy yace.
“Dan Allah ka yi mini rai” Jariri yace. “Ai mun dinga rawa kenan dana yanzu har wayewar gari kuma wallahi duk wanda ka gayawa yadda na gwaguye kan ragon cen haka zan yi maka” Daddy ya hau muzurai yana raba ido wannan karan hawaye sharara yake yi.
Jariri ya miƙe tsaye ya tale ƙafarsa sannan ya sunkuya yace. “Ka ga yadda na yi?” Daddy ya gyaɗa kai. Jariri yace. “Maza kayi haka” ba musu Daddy ya sunkuya kamar me ruku’u sannan ya tala ƙafafauwa, Jariri ya dinga gyaɗa kai daga sunkuye yana ya dafe kwankwaso yana kaɗawa. Daddy na ganin haka ya basar aikuwa Jariri ya ɗago ya buga masa ƙafa a baya, sai ga Daddy ya tafi ta ka ya faɗi rigijib. Jariri yace. “Maza-maza ta shi mu ci gaba” Daddy ya tashi ya yi yanda Jaririn ya yi sannan suka fara waƙar salawaitun salo.
Daddy yana kuka rera waƙar . “Salawaitun salo” ana cikin haka sai ji kake kiriff Daddy ya kife a gurin.