DR MUHSEEN CHAPTER 12 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝………… Uncle Yusuf ne zaune saman kafet din da yayiwa falon Hajiya Kaka kawanya.kanshi a duke yake ga dukkan alamu Yana sauraren bayanin da take yimai ne.
Saida ya Bari ta idar kafin ya dago kanshi,murya cike da ladabi ya ce “kiyi hakuri Hajiya abinda yasa na kawo wannan batun duba nayi ga yadda Seeyerma take yarinya karama,sannan duk wani kulawarta Yana karkashin shi Muhseen din,to a maimakon ace ya tafi da ita hakanan babu aure a tsakanin su tunda na muharramar shi ce ba,to gwamma ace akwai igiyar aure a tsakanin su,dukda Ameerah ta girmeta Amma nasan Seeyerma zata iya zama da ita tunda ni a ganina kamar auren su bai haramta ba,saiya tafi da su duka biyun,ita Seeyerma ya sakata taci gaba da karantunta”.
Shiru yayi ganin tana kallonshi ga dukkan alamu tana nazarin maganganun shi.
Shiru ce ta ratsa tsakanin su,kafin ta nisa tana ci gaba da cewa
“Yusufa kada ka manta ni mahaifiya ce a gare ku,Amma meyasa jikina yake bani akwai abinda kuke boyeman Wanda ga dukkan alamu ba abune mai kyau ba”.
Ji yayi kirjinshi yayi wani irin bugawa jin kalaman mahaifiyar tasu.
Cikin dauriya da son daidaita natsuwar shi ya nisa kafin ya dora da
“A a Hajiya babu komai,kawai naga yiwuwar hakan shi ne zai saka nutsuwa a zukatanmu,saboda idan har ya tafi to ba lallai ya rinka kula da ita kamar da ba,duka shima Faruk Yana iya bakin kokarin shi”.
“Tau shikenan ka sanar da sauran yan’uwanka inason ganinku saimu tattauna asan yadda za’a bullowa al’amarin”cewar Kaka,dukda tana jin wannan hadin bai konta Mata a rai ba,saboda tamkar za’a Kara hada rigima tsakanin iyalanta dana Hajja mariya.da haka ya fita Yana kokarin Kiran Ummeey ganin tunda Suka fara magana da Hajiya Kaka yake kiranta.
“Wallahi ki kiyaye ni Ameerah idan har bakibi a hankali ba to wannan miskili yaron da kike gani Yana iya bijirema aurenki ,ke kenan kullun Baki da aikin yi sai kula samarin banza kamar wata akuya,to bari ki ji abinda baki sani ba idan har kikayi saken da kika bari wannan shashashun samarin naki Suka gama rarakeki to wallahi saikin gane kuranki a wurin Muhseen,Dan tsaf yake sakoki Koda zaki mutu”cewar Hajiya Mariya da ta tasa Ameerah a gaba tana surfa mata ruwan masifa kamar zata dake ta.
Cike da tsiwa Ameerah ta ce “yooooo kawai sai a hana mutum yaji dadin rayuwar shi,shi wayasan abinda yake aikatawa”
Sosai Hajiya Mariya take kallonta jin abinda tace.cike da takaici ta ce “to ki mayar da hankali ki su Kara zubamaki wani cikin Dan ubanki saidai ki haifeshi bazan Kara yin kisan Kai ba,kusan sau ukku fa ana zubar maki da ciki Wanda har zuwa yau nakasa sanar da Mahaifiyar ki,saboda nasan laifina zata gani”.
Daga haka tayi shuri tana Jin wani takaici Yana Kara rufeta tunawa da tayi Ameerah halin mahaifiyarta ta dauko,Dan lokacin mahaifiyar ta tana budurwa tayi rashin ji sosai,har saida Balaraba ta rinka bin malamai kafin ta samu ta samomata mijin aure.
Da sauri Ameerah ta Kara matse wayarta jin alamun Kira Yana shigowa,tasan Kuma wani tsohon kwartonta ne Mai suna Nurah,Wanda akalla sun dauki tsawon shekara hudu suna tare.sosai yake kashemata kudi shiyasa ta ki rabuwa da shi.
Sim-sim ta wuce dakinta jin Hajiya Mariya bata Kara yin magana ba.
Tana shiga dakinta ta sauke ajiyar zuciya,wayar ta fito daga cikin rigarta tayi saurin yin picking call din.
Hirar soyayya Suka Sha kafin ta katse Kiran tana murmushi tuno da yadda Nurah ya iya sarrafa mace,shiyasa duk cikin samarin da take mu’amulla da su tafi son Nurah,Dan bariki ne na karshe sosai yasan takan mace.
Tunda suka karasa gidan su Rabi’u yayi konciyar shi,haka sukayi ta fama da shi akan ya sanar da su matsalar shi ganin yadda a cikin kwana daya duk yabi ya rame kamar Wanda yayi cutar sati guda.
Murya cike da rauni ya bude Baki ya ce Seeyerma ce……….. “Seeyerma ce bata da lafiya”shiru yayi zuciyar shi tana gargadin shi kada ya sake ya sanar da su abinda ya shiga tsakaninshi da ita.
Jin ya dakata da magar da yake yi saka Rabi’u yayi saurin cewa “Wallahi Kai dai done man baka haduba,kawai dan yarinya bata da lafiya shi ne kaima zakabi duk ka tayar da hankalin ka,haba Kai kamar ba soja ba towai meye ma yake damunta ne haka da kaima harya saka ka a cikin damuwa?”.
Still shiru yayi masa Yana dafe da barin kanshi,can wata dabara ta fadomai yayi saurin cewa “Daman haka take fama kasan irin larurarsu ta Mata duk end of month sai tayi wannan rashin lafiyar”.
Cike da mamaki Lameer ya kalloshi jin wata karya daya shatata,shidai yasan daga jin wannan maganar kasan karya ne kawai bayasan sanar da su gaskiya ne.
Shiru ya dan ratsa tsakanin abokan guda ukku,ba Wanda ya sake cewa uffan kowanne sai faman sake-sake yake yi a zuciyar shi.
“Hmmmm Kai dai ka sanar da mu gaskiyar al’amari,kodai ka turmushe Yar mutane ne shiyasa duk kabi ka rude haka,Dan wallahi raina ya bani cewar wannan maganar ba gaskiya ce ka fada ba,taya za’ayi ace kawai dan tana fama da larurar on duk kabi ka tayar da hankalin ka irin haka,kamar ance maka mutuwa tayi”.cewar Lameer daya tsareshi da kallo Yana son gano gaskiyar maganar da yaji ya fada.
Ji yayi gaban shi yayi wata bugawa da karfi sakamakon jin furucin da aminin nashi yayi.
Cikin dakewa da bata fuska ya ce “Kai matsalarka kenan akan yan’mata, idanma hakane to Kai Ina ruwanka ne?”.mitsssssss yaja dogon tsaki Yana Kara gyara konciyar shi a bisa gadon na Rabi’u.
Hahahahahah da karfi Lameer ya saka dariya jin amsar da Muhseen ya bashi.sosai yake cin dariyar shi Yana Kara nuna Muhseen da hannun shi.
Muhseen tsabar kulewa da bakinciki kasa cewa komai yayi,sai konciyar shi daya Kara gyarawa ya juyamasu baya,soyake yayi bacci Amma zuciyar shi taki barinshi ya huta.idanuwan shi ya runtse Yana dan sai yanzu yake jin takaicin abinda ya aikata.
Uncle Yusuf ne Murya mai dauke da tsantsar rauni ya fara labartawa matar shi Hajara yadda Suka yi da Hajiya Kaka akan batun Seeyerma,dukda ya boyemata ne saboda wasu dalilai Koda zata ji to ba yanzu ba,sai zuwa gaba idan komai ya lafa zai sanar da ita.
Sosai Aunty Hajara ta nuna farincikin ta da jin wannan batu.Amma ta wani bangaren tana jin dakyar Seeyerma ta iya da makircin su Hajiya Mariya da Ameerah,dukda tana da fada Amma akwai yarinta a tare da ita.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa da “Allah ya zaba abinda yafi zama alhairi a rayuwarmu gaba daya.
Uncle Yusuf amsawa yayi da “Amin”
Kafin ya fita zuwa kasuwa,ita Kuma dakin Seeyerma ta koma dan ganin kota farka daga baccin.
“Ni nasan idan har kayi aiki sai ya ci,Amma ya akayi a wanna karin aka samu matsala?inhar dan cikon kudi ne da ban baka ba to gasu na zo da su”Zahara’u kenan da take kiciniyar bude jaka.
Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar dagamata hannu,ba tare da ya ce komai ba mutumin yaci gaba da yin wani Zane a babban farantin dake gabanshi mai cike da farin raire mai kyau.
Sosai ya dukufa Kan zanen,da yayi saiya goge ya sake zana wani,sai a zanen karshe da yayi kafin ya bishe da dariya mai cike da tsabar farinciki.
Sosai ya mayar da hankalin shi Kan Zahara’u da take faman kallon shi.ita nutsuwa tayi ganin yadda hankali shi kacokan ya dawo wurinta.
Budar bakin malamin ya fara cewa “ki sani yanzu hankali shi kacokan Yana Kan yar’uwar shi,wacce yayiwa fade a daren jiya ta hanyar kwayoyin Kara karfin sha’awa da yarinyar tayi amfani da su a nufinta nasan ganin ta rama abinda yayi Mata”
Cikin tsabar dimuwa da kidima Zahara’u ta ce “Haba malam mekake son ka sanar da ni ne? kenan Daman yaudarata kake yi ka ce zai aure Ni,to wallahi baka isaba duk kudaden da kasan na baka to saika dawoman da kayana”tana murguda baki saboda yadda take jin maganar tamkar ya daba mata wuka a makoshi,Dan yadda take mutuwar san Muhseen to tana jin Koda kisan Kai ne zata iya aikatawa akan ganin ta mallake shi.
Cike da jin haushi ta mike tsaye tana ci gaba da cewa “mugu azzalumi tunda kaci kudina sai Allah ya saka min”ta fice daga dan karamin dakin tana gunguni.
Hartakai bakin kofar da karfi cikin dan daga murya ya ce “Duk inda zaki ce to ki je,nidai na fadamaki iya abinda na gani duk Wanda ya ce zaki auri wannan mutumin to karya yake yi,Dan wannan yaron ba mijinki bane”
Fit ta karasa ficewa cikin sauri tamkar zata kofe saboda takaici.
Seeyerma ita ce bata farka ba sai wuraren karfe 11 am na safe,da salati ta farka dauke a bakinta,a hankali ta fara bude idonta harta waresu a saman pop din dakin.
Ji tayi jikinta yayi sauki sosai ba kamar dazu da asuba ba.cikin lalalbawa ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya.
Kanta ta jingina da allon gadon ta Lula duniyar tunani.sosai abin yake Kara dawowa kolwarta tamkar yanzu abin ya faru.
Runtse idon tayi tana jin wani abu mai daci ya tsaya a makoshin ta.
A zuciyarta ta ce “Ashe daman ya Muhseen mugun nufinshi kenan akanta,nasan ganin ya lalata rayuwarta da farincikin ta,itakam sai Allah ya saka Mata,saboda ita data sakamai maganin kawai danta rama wulakancin da yake yimata ne,Amma sai gashi abin ya Kare a kanta,shiyasa ake son mutum ya rinka kasancewa mai hakuri da juriya,idan an cutar da shi ya rinka yafiya,Amma tayi amfani da kalmar nan da Bahaushe yake cewa “Rama cuta ga macuci ba laifine ba,Amma mafi kyawu mutum yayi hakuri,Amma hakurin shi ne abu mafi wahala a halin Yanzu”da sauri ta ware idonta a bakin kofar jin alamun wani zai shigo.
Aunty Hajara ce hannunta dauke da wata kula mai kyau da tsada sai jug da yake cike da kunun tsamiya da ya ji kayan hadin Itatuwa.
Saman dan madaidaicin table din ta aje kayan kafin ta karasa jikin gadon,ganin ta sake rufe idonta yasa ta Kira sunanta “Seeyerma!”
Bude idonta tayi kafin ta amsa.
“Sauko ki Kara yin wanka,saiki sha dahuwar Naman kaza nayimaki shi da romonshi”.
Batace komai ba haka ta fara saukowa daga Kan gadon,A hankali take daga kafarta dukda bata jin zafin da yawa Amma saboda dinkin da akayimata dole zata lallaba kodan lafiyar ta.
Fita Aunty Hajara tayi ganin Faruk Yanata Kiran wayarta.
Bayan ta fito turare kawai ta fesa sai wani doguwar riga marar nauyi data saka.kulan ta janyo tana dagawa har ji tayi yawunta Yana tsinkewa saboda kanshi da taji ya doki hancinta.
Bismallah tayi kafin ta fara jin Naman.
Saida ta kusan cinyewa sai faman Shan yaji take yi saboda zafin tarugun.
Kunun tsamiyar ta tsiyaya a cup tana kurba.turo kofar akayi kofar take kallo.
Yaya Faruk ne yake kokarin shigowa.
Aje cup din tayi tana Kara yin kasa da kanta saboda yadda taji gabanta yayi wani mugun bugawa tamkar zai tsaga kirjinta ya fito.
Cike da natsuwa ya karaso jikin dakin Yana kallon yadda duk tabi ta rame a cikin kwana daya da yini daya.
Saman wata doguwar kujera mai cin mutum biyu ya zauna still idonshi Yana kanta.
Jin ta kasa gaishe shi yasaka shi cewa…………²⁵