TAWA TA SAMENI CHAPTER 18 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
kabir ya kai min can gidan yakubu avenu,ta karasa
shigowa cikin bedroom tana fadin matsalarka kenan baka
son manyan kaya sai aukin dinkasu tazo kusa dani ta
tsaya tana kallon kayayyakin ni kam jikina rawa yake a
bayan labule gashi bata magana a hankali don tunda
dama haj yaya mafadaciya ce don haka ko maganar
arziki takeyi sai kaji tamkar tana fada ne, Yayanmu yana
tsaye a bakin kofa yace Haj menene kike nema ne tace
magana zamuyi yanzun maganar kayan nan fa ba kace
komai ba?yace kaya gasu nan ki diba dama inason rage
ma kabir ne don sun min yawa sosai kinga fa ko abikin
nan Nasir abokina set ashirin ya dinka min kuma duk
acikinsu ba yadin dubu goma sai sama da haka Haj tace ina ruwan Nasiru, ta cigaba dama zancen da nake son in maka akan abubuwan da kake yine,so nake ka gaya min menene tsakaninka da yarinyar nan Iman?ta kuma daga murya iye kai nake tambaya duk iskancin da kakeyi fa ina sane kar kayi zaton ban sani ba ina daga kafa ne kai amma naga alamar sai na warware ka naci mutuncinka ko na tozarta ka ko?sai sannan yayi
magana haj tsaya ki jini ya shigo shima zo muje falo miyi wannan zancen don Allah ta bishi suka fita tana fadin nidai ka fita hanyar su bana son hulda da Habiba da ahlinta yace Haj zauna Www.bankinhausanovels.com.ng
suka zauna duk da kasa kasa yake magana ina jiyo shi
daga inda na sandare don na tabbata in har tasan ina dakin kashi na sai ya bushe,yace Haj kin ga yarinyar nan tana dawainiya dani tunda na dawo garin nan abinci gyaran daki aike bafa biyanta nake yi ba san katse shi,don Allah ni rufa min bakinka baka da kannan da zasuyi dawainiya dakai?yace to Haj su wadannan yaran me suka iya?sam yarinyar nan ta fisu iya komai……ta kuma katse shi tunda an baka kaci kasha an baka cikin abinci ka kiyayeni, rannan aka ce min ka dauketa cikin motar ka, kaf gidan nan baya ga Kabir wa ya taba shiga motar?ko ni nan da na haifeka ban shiga ba na biyu kaimata dinkuna masu tsada ba kaima yan uwanka ba don wulakanci kuma sai ka ringa masu anko da matar da zaka Www.bankinhausanovels.com.ng aura,sannan jiya har cewa akayi ka rungumeta ko ba haka akayi ba?cikin daga sauti yace inji wa?Haj ki daina jin irin wannan surutan da shirri ne maganar shiga mota ta kuma kasuwa muka je ta siyo
kayan abinci da aka shiryawa abokaina da suka
zo daga England suka sauka gida Nasir,dinki kuma yana da kyau ka kyautata ma mai kyautata maka sannan ni ban wani rungumeta ba duk surutu ne,tace su Haj Lauren ne suke maka surutu ne?yace to in banda abun Momi mene nata na zuwa gun lunchn abin yara tsakani da Allah…ta katse shi to ni ynzu magana ta ta karshe shine ana gama bikin
nan ka tattara matar ka ku tafi England,ya danyi shiru sannan yace Haj mai ya kawo maganar tfy da mimi,kinga fa ba gida ke gareni ba a hotel nake ya zan kai matar aure hotel?tayi tsaki zancan banza ne kakeyi ba zan amince ba kaje da ita ku zauna a hotel din tare ta shiga fada don kar ya soma magiya ni zaka gaya wa zancan banza?bari kaji wilh wilh baka isa in maka kaffara ba tare zaku tafi in kuma zaka nuna min cewar ban isa bane to ina jira ta numfasa sannan ta cigaba hankalina zaifi kwanciya in kuna can bata jira yayi magana ba ta fice abinta ya bita a baya don Allah haj ki min hakuri mana,ko sauraronshi batayi ba jikina sharkaf da zufa na fito daga bayan labule a gefen katifa na zauna ina maida numafashina sama sama idona sharkaf da hawaye ba wai ina kukan cin fuskar da tayi min bane a’a ina kukan tafiyar da zasu yi,don ina ganin in har ya tafi da ita ni kuma shi kenan ba zan dinga ganinshi ba zanji muryarshi ba ba xanji kamshinshi WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
ba,tsaye yake bakin kofa yana dubana ya shigo tashi ki shiga ciki share hawayenki kinji karki damu wata rana sai Ibr cikin sanyin murya yake magana na mike ya matsa min na wuce. Yau asabar tara ga watan sha daya aka daura auran yayanmu da anty mimi a kofar gidansu dake Malali daurin auran ya sami halartar mutane da dama cikinsu harda matasa sun mafi yawa kasancewar shi fan kwallone sunyi walima bayan daurin aure kamar da gayya nice mutum ta farko da ya fara kira yace min an daura auran
a raina nace to ni ina ruwana amma a fili sai nace Allah ya sa alheri,yace me kikeyi?nace ba komai ina kwance yace kin san yau akwai dinner don haka ya kamata ki zama cikin shiri nace ina jin fa ba zan samu zuwa ba don kaina yana min ciwo bayan haka ga rigima nata faruwa kasan ma jiya banda Alhj ya sa baki da rigimar nan bata kasu ba don haka ina jin ba zan samu zuwa ba,yayi shiru yana son yayi sallama amma bai gaji da jin muryarta ba ya kan so tana magana yana kusa shidai baya gajiya da kallonta shi dai ya san yana sonta kuma yasha alwashin in dai yana raye sai ya aureta duk da karancin shekarunta,nace hello danaji shirun yayi yawa
yace Iman kin sha maganin ciwon kan?nace eh a takaice yace kin gane ina son gsky kije wurin dinner din nan in kinji kan naki yayi sauki amma ba dalilin wani shirmen fada ba can kin jini?nace in Mama ta hana fa? yace ba xata hana ba zan mata waya nace to sai anjima Amira dake gefena ta dubeni tace ke da wanene haka a waya,nace yayanmu ne Amira ta zuba min ido cikin tuhuma tana cewa anya wannan yayan naku bashi ne gayan nan da kike boye mana ba?na dubi Amira cikin rashin gsky nace haba dai Amira ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi tace Iman Www.bankinhausanovels.com.ng
bai kamata kina boye mana sirrinki ba musamman irin
wannan kina bukatar mai baki shawara sannan mu sai
mu dinga kwashe sirrinmu muna fadi maki duk zurfin
cikin fulani bana boye maki sirrina amma ke sai kiyi ta
nuku nuku,nayi shuru tabbas zancen Amira gsky ne sai dai ina jin nauyin ce mata ina son yayanmu ne dama dai muna yin soyayya ne shi ne amma fa nice nake haukana bai ma san inayi ba,ta yunkura zata dauki hijabi tace daina tunani Iman ban fa ce lallai saikin gayan matsalar ki ba ni kin gama tfy ta da sauri na jawo ta muka kara fadawa kan gado,sorry Amira zakiji ta zauna kusa dani sannan tace kin cika abin haushi ne Iman,na nutsu sannan na soma bata lbr sanda na soma son yayanmu nace wilh Amira da ban yarda wai ina sonshi bane na
dauki tsoron da na keyi ne yasa na kanji muguwar
faduwar gaba a duk lokacin da na ganshi sannan jikina ya shiga kyarma ashe wai duk so ne hawaye ya soma zubo min Amira nayi adduar nayi addua tamkar ina kara zuga son nayi kukan na tsine ma SO,so ko wahala nasa Allah ya isa ga duk wanda yace so na da dadi don nidai cikin wahala nake da kunan rai na soma kuka mai sauti nace Amira ni so bai min adalci ba sona da ya tashi ya kaini inda Allah bai kaini ba zuciyata ta kamu da son wanda yafi karfina na tsaya ina jan ajiyar zuciya Amira
batayi min magana ba ta barni nayi kukana mai isata bata hanani ba bata fara magana ba sai da nayi ya isheni sannan nayi shiru ta soma magana ki bar kuka kuma kibar zargin zuciyarki da ganin laifin tsuntsun sonki sannan ki daina cewa ya kaiki inda Allah bai kaiki ba gaya min dalilin da kike ganin cewa yayanmu yafi karfinki,nace na farko ba sona yake ba nayi ajiyar zuciya sannan na cigaba ni ba ajinshi bace sannan ga rashin shirin da ke tsakanin uwata da tashi ba zasu yarda mu auri juna ba WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
koda yana sona bare ma bai taba son ba Amira tace niko ina ganin kamar yana sonki abinda yake maki yafi karfin kyautatawa sai dai SO,nace banyi tsamanin ba shi da yake fadin ba zai auri karamar yarinya ba a gabana yasha fadin wannan zancan ke ko abokanshi sunsha cewa suna sona sai ya hau su da fada gami da cewa shi baya son raini basu san in suna cewa suna sonmu ba zamu raina su ba?na dubi Amira na cigaba da cewa kina ganin nasir abokinshi da yake son mami in da yabi ta yaynmu da bai nemi mami ba a gabana wata rana na kai musu abinci naji yana ce ma Nasir mai zaiyi da mami yar cikinshi dan dai rashin sawa kai girma gun kananan
yara,ga manyan babys a gari zai ce sai Mami wadda a
haihuwar kaji ya haifeta sannan kice zai soni? bayan
mami tama girme man da kusan shekara daya,Amira
tace to adduar dai zamu cigaba dayi sannan zamuga
shawarar da zamu baki ni da Mami sai in mun zauna
nace kar mu gayawa Mami,Amira tace dole ne Mami taji zancan nan don bamu boye ma juna sirri kin sani sarai dama ke ce mai mana nuku nuku kuma mun sani mun dai kyaleki ne nace ni dama don ga cewar yayanta ne shi yasa Amira tayi tsaki sannan tace dole ne ta sani nace aishi kenan, mukayi shiru na dan lokaci sannan nace ynxu ma shi yayi man waya wai na shirya muje dinner anjima nifa da bana son zuwa Amira tace me yasa ba zaki je ba?nace ban son abinda ran mama zai ta
baci a banza amma shi cewa yayi fadan da akeyi ba
dalili bane da zai hanani zuwa,Amira tace su mami ma
da kyar in zasu don naji suna cewa yaynku yace kar ya gansu a gun,nace to nima kan ba zanje ba Amira tace wilh sai kinje ai ta haka ne zaki samu ki cusa kanki gareshi kin gane shiga zakiyi ta alfarma ko ba haka ba shi fa da kanshi yace kije nace cewa yayi ma Zal sa aZO har gida a daukeni don ban ma san gun da Za‘ayi dinner din ba Amira ta mike tana dariya gami da cewa kune manya a gun. Na dubi kaina a madubi sannan nace kai Allah ya saka ma telolin shagon yaya sulaiman da alkhairi ganin yanda na fito cikin dinkin da ke jikina material ne blue mai filawoyi fari da bakake ga stones suna kyalli nasa sarka da yan kunne fashion blue jaka ta da takalmi karamin gyalena fari ina cikin fesa turare ne wayata ta soma ringin na duba yaynmu ne na dauka kin shirya ne? tambayar da ya soma yi min kenan,na shirya na ce cikin sanyaya murya ya dan ja numfashi to fito WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
waje na ga kwaliyarki kafin in wuce kinsan fa ni zanje can ne mu tafi tare da mimi nace to amma raina nace ina ruwana in ma da mamanta zaku,ya kashe wayar na dubi agogo takwas da rabi na dare nace anya mama zata barni na tafi kuwa mami ta shigo dakin itama cikin less fari tayi kyau nace zakije ne?tace zanje kinsan nasir zanbi nace yawwa har naji dadi tace su Bilki da Sa’a da kyar ne zuwansu amma suna dai can gidan amarya nace
har an kaita ne?mami tace an kaita mana daga can zaa dauketa nace mami mamanmu na falo ne?ina son fita bana son ta ganni zata iya cewa na koma dare yayi tace aa bata nan shigowata na ganta da tire tayi sashin Alhj nace yauwa dama yaynmu ne yake kirana nayi kyau
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG