DR MUHSEEN CHAPTER 23 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝……………….Sosai Seeyerma take jin dadin zama cikin Yan’uwanta,Haka da dare zasu taru a falon Mama ayita hira ana shan dariya.su Khadijah suyi ta tsokanarta ta auri tazuru.
A bangaren Dr muhseen kuwa dauriya kawai yake yi na rashin Seeyerma kusa da shi.yau tsawon sati Ukku kenan da dawowarshi Daura yayi fishi baya Kiran kowa,Yana kallo Seeyama take Kiran shi yaki dagawa,so yake ya nunamata kuskurenta danya fahimci harda hadin bakinta.
Itako Seeyerma baiwar Allah abin dukya dameta ta dawo bata da walwala.wato fishi yake yi saboda ance ta zauna sai bayan ta haihu.Haka itama ta kyale shi taci gaba da harkonkinta,Amma abin Yana damunta.
Ranar wani weekend Yana dawo daga masallacin sallar la’asar Yana takawa a kafa zai koma gidan shi yaga Kiran Ummeey saida gabanshi ya fadi,Dan tunda ya dawo baiyi waya da kowa ba.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yayi picking call din tare da cewa “Assalamu Alaikum”
Bayan ta amsa ya gaishe da ita cikin ladabi.
A sanyaye ta amsa kafin ta tambaye shi
“Rainamu ne kayi shiyasa kake fishi da mu”
Girgiza kanshi yayi tamkar Yana gabanta ya ce “A a Ummeey Ni na isa na rainaki”
“Ok tau idan na fahimceka saboda an amsar maka mata shi ne kayi fushi ko,Kai baka tausayinta ne?to kome kake yi ka zo ka ganta na fadamaka”.
“Umme………….”
Kit ya ji ta katse Kiran.
Da sauri ya kalli wayar ganin da gaske ta katse ya sake kiranta,Amma wayar taki shiga.
Jiki a sabule ya karasa dakin shi.nan take ya fara hada kayanshi Daman a shirye yake.,key kawai ya dauka da wayoyinshi ya saka jakar shi a booth ya figi motar ya doshi hanyar fita daga bareak din.
Wadanda suke duty a gate din ganin kyakkyawar motar ogan nasu ta doso gate din a guje yasa sukayi saurin mikewa tare da dagamai karfen.ko saurarensu baiyi ba ya haura titin ya nufi cikin Daura.
Komawa sukayi suka zauna tare da al’ajabin abinda ya faru har yasaka oga yin irin wannan gudun.
Shiko cikin mintunan da basu haura biyar ba ya karasa bakin first bank.
Wurin injin ciran kudi ya nufa ganin layi ne sosai yasa ya ciro ID card dinshi ya nunamasu.Aiko dandanan suka bashi wuri ya cire fifty Thousand ya fice Bayan yayimasu godiya.
Tunda ya fice Yar matashiyar yarinyar da take rakube gefe daya take kallonshi.har saida yabar wurin kafin ta dafe kanta tana jin yadda zuciyarta take bugawa da sauri-sauri.
Duk abinda take yi Wanda yake gefenta duk Yana kallonta.
Tabe baki yayi Yana dubanta kafin ya ce “Hmm Mata masu abin mamaki,da sunga kyakkyawa saisu makale shi suke so,to Bari ki ji baiwar Allah gwamma ki shafawa kanki lafiya wannan yafi karfinki, cikakken Balarabe ne kuma bafillanin asali,sannan soja ne”
Da sauri budurwa ta kalli mutumin tana Kara mayar da hankalinta gareshi.
Gefe ta matsa hakan yada Suma Suka bi bayanshi ita da kawarta.
Cigaba yayi da cewa “Yana da Mata wacce yanzu haka tana gaf da haihuwa,ko cikin bareak yan’mata rububinshi suke yi,Amma ba wacce yake kulawa,wani abu da zai Baki mamaki Duk kyawun Dr muhseen da kudinshi Allah ya kiyaye shi baya neman Mata,Duk yadda soja sukayi kaurin suna a harkar Mata wasu harda na shaye-shaye to shi duka bayayi,idan yaga wani yanayi to yakan yimai wa’azi”.
Sosai Suka mayar da hankalinsu suna sauraren tarihin wannan kyakkyawan saurayin.
“Koda kin dora ranki akan saiya soki to tabbas zaki saka kanki cikin wahala,Ina mai baki shawara ki cireshi daga ranki”.
Shiru Suka yi kowacce da tunanin da take yi.
Godiya tayimai da shawarar daya bata kafin lokacin layinsu ya zo.bayan sun cira suka tasayar da Mai adaidaita Suka tafi.
Cikin mintuna da basu gaza Arba’in ba ya shigo da hancin motar shi cikin estate din.
Harya karaso gate na biyu bai gaisa da kowa ba.
Wurin parking ya shiga,ya dade a cikin motar kafin ya bude tare da ziro farar kafarshi daya waje.kira’ar da yake saurare ya kashe ya kwashi wayoyin shi ya fito.Direct part din Hajiya Kaka yayima tsinke Yana jin zuciy shi ba dadi,tabbas su Ummeey fishi suke yi saboda ya dauke kafarshi.
Shiru ya ji falon alamun duka suna part din Mama.bedroom ya karasa Yana sallama.
Hajiya Kaka da take fira da Asabe mai aikinta shiru tayi tana saurare jin kamar muryar jikannata.
Jin an Kara maimaitawa yasa Suka amsa kafin ya shiga.
Saman gadon ya konta Yana dafe kanshi.
Kallonshi tayi tana cewa “Asabe kawomai fira Mai sanyi ya Sha”
Da sauri Asabe ta nufi falon.
Shidai Muhseen harzuwa wannan lokacin baice komai ba.bayan ta kawo saman kafet din ta aje ta fita zuwa dakinta.
A hankali ya sauko kasa ya zuba firar a cup ya fara kurba.
Saida ya shanye tass kafin ya koma ya konta.
Kaka ji tayi ya bata tausayi,Amma dole yayi hakuri tasan Jikanta kamilin ne.
Ya dade a haka saida ya ji ya dan samu natsuwa kafin ya tashi zaune.
Gaishe da Kaka yayi.Bayan sun gaisa ganin karfe shida harta gota yayimata sallama ya nufi din Ummeey.
Laila ya gani tana goge Dinning table.da gudu ta dafeshi tana cewa “Oyoooyo yayana ka gudu ka barni Yaya Sadik ya duke ni”.
Saida ya zaunar da su saman kujera ya shafa kanta Yana cewa “sorry Kanwata kinyi rashin ji ya duke ki ko?”
Da sauri tayi kwalkwal da ido tanasan yin kuka ta ce “Wai dan na fadi a test din Agriculture shi ne ya duke ni”
Rarrashinta yayi kafin ya ce ta fadama Ummeey ya zo.
Da gudu ta nufi bedroom din Ummeey.
Fitowa tayi tana cewa “Ta ce ka shigo”.
Anan ya barta nufi dakin da sallama dauke a bakin shi.
Saida ta amsa kafin ya shiga.
Kasan kafet din ya zauna Yana sadda kanshi kasa.
A hankali ya ce “Ummeey Ina kwana na sameku lafiya?”.
“Lafiya Lau Alhamdlillah”.
Dukansu shiru sukayi kowa da abinda yake tunani.
Daurewa yayi yace “kiyi hakuri wal………..”
Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar cewa “Tashi kaje gurin Auntynku”.
Sadaf ya fice daga part din.
Part dinshi ta wuce ya aje wayoyinshi ya fada toilet.wanka ya sake yi tare da dauro alwala, sallar magriba ma anan cikin dakin yayi kafin ya nufi part din Aunty Hajara ga yunwa Yana ji daka ganshi fuskarshi ta dan fada alamar ya rame.
A falon ya tadda ita sai Faruk da yake wurin da alama wata maganar suke tattaunawa.
Batayi mamakin ganinshi ba,Dan tasan halin Ummeey dazu haka tayi ta fada akan tunda ya tafi bai zo ba.
Cikin sanyi ya karasa saman kujerar ya zauna.gaishe da ita yayi kafin shima Faruk ya gaishe shi.
Kallanshi Aunty Hajara tayi ganin yadda fuskarshi ta fada sai idanuwanshi y Kara fitowa.
Mikewa tayi ta kawomai abinci da abin sha.
Cikin natsuwa yake cin abincin,su Kuma Suka ci gaba da tattaunawa.
Saida ya kammala kafin ta dube shi tana cewa “Tashi ka je ka huta gobe zamuyi magana”.
Cike da jin dadi ya fita,Daman ya gaji Yana bukatar ya huta.
Saida ya tabbatar yayi sallar isha’i kafin ya dauko kayanshi daga cikin mota.
Da dare wuraren karfe tara da Yan mintuna Aunty Hajara ta leka dakin dasu Seeyerma suke,ganinsu tayi suna kallo. Harsunyi Shirin bacci.
“Seeyerma saka Hijaf dinki ki same ni a falo”cewar Aunty Hajara ta juya ta fita daga dakin.
Dakyar ta sauko daga gadon gashi yau tana jin cikin ya Kara yimata nauyi sati Ukku Bata yi awo ba,sai Ya Faruk ne ya kaita Alheri chilinic aka dubata.
Safnah ta sakamata hijaf din kafin ta fito da silifas a kafarta.
Wani babban Joge ta mikamata tana cewa “Yi sauri ki kaima yayanki Yana part dinshi”.
Rasssss ta ji gabanta ya fadi ta fara tambayar kanta “Yaushe ya zo?”
Ganin Aunty Hajara ta shige dakinta ta barta anan sororo yasa ta juya cikin dakinsu.
Su Khadijah taba joge din su kai Suka kiya.Dan haka ba yadda zata yi dole ta tafi da kanta.
Tana taba kofar falon ta ji a bude kawai ta shiga.
A hankali take takawa harta shiga cikin falon.Hangoshi tayi saman kujera Yana lumshe idonshi ga dukkan alamu ba bacci yake yi ba.
Sallama tayi tana kokarin ajewa.
A hankali ya bude lumsassun idanuwanshi ya zubasu a kanta.sosai yaga ta Kara Kai.
Zaune ya tashi Yana Kara binta da kallo.
Ganin haka yasa tayi saurin cewa “Ina yini”stell idanuwanshi na kanta Kuma bai amsa gaisuwarba.
Kasa tayi da kanta tana jin wani iri,yau tsawon sati Ukku basuga juna ba,ita kanta tana kewar shi.
Cikin mutuwar jiki ya motsa labbanshi ya ce “Zo nan inaso na gaisa da Abokina”.
Dakyar take daga kafafuwanta ta karasa wurinshi.kamota yayi ya azata bisa cinyar shi Yana kokarin fitar da Hijaf din jikinta.
Sosai yaga cikin ya Kara girma Kuma yayi kasa alamun ta kusa haihuwa.
Saida ya daga Yar yaloluwar rigar baccin ya shafa cikin kafin ya ce “Aboki Ina fatan bakayi fishi da ni ba,kasan ba laifina ba ne,Mamanka ce take guduna”
Da sauri ta kalle shi jin abinda ya ce.
Kawar da kanta tayi tana Jin wani iri a cikin jikinta ganin ya fara sauya kalar gaishuwar.
Haka yayi ta surutanshi ita dai tana Jin shi,Amma bata ce komai ba.karshe daga ta ji ya sabule rigar Yana cewa “Yau dai dole a bani hakkina tunda gani na zo”
Da sauri ta ce ” Uhm Ya Soja bazan iya ba cikina yayi girma Kay…………”
Da sauri ya saka bakinshi cikin nata Yana tsotsar shi.sun Dade a haka kafin ya zare harshen shi Yana kallanta.
Cikin dauriya ya ce “Dan Allah ki daure ki bani wallahi zan biki a hankali kin ji”
Lunshe idonta tayi tana Jin babu dadi a ranta.tasan hakkin shi ne,but Mama tayimata kashedi akan cikin Yana iya samun matsala idan bata kiyaye ba.
Haka yayi ta nadeta da kalamai masu dadi karshe ba yadda zata yi haka ta bishi bedroom bayan ya rufe kofar falon.kadan ya sha Zobon data kawomai.
Cikin kwarewa ya fara sarrafata.
A hankali ya manne fatar jikinsu wuri daya tare da zira bakinshi cikin nata hannunshi daya Yana saman
…………….Hannunshi Yana saman kirjinta,dukda Yana jin wani tausayinta yana ratsashi Amma hakan baisa ya kyaleta ba.
Ranar Seeyerma taga tsagoran soyayya tamkar sun shekara basu hadu ba.koda Asuba tayi suka kimtsa shiya jasu jam’i suka gabatar da salla kafin suka koma bacci.
Sai wuraren karfe goma kafin ya farka ganin tana ta baccinta,zare jikinshi yayi ya mannama cikinta kiss kafin ya sauka daga saman bed din.
Saida ya kammala shiryawa kafin ya fara tashinta.Dakyar take bude idonta saboda baccin da yake damunta.
Soyayi ta shirya,Amma fir ta kiya a dole ya kyaleta tare suka fito bayan ya sakamata hijaf dinta.dakyar take takawa saboda yadda cikin yayimata nauyi ga Ya Muhseen dukya gajiyar da ita.
A hankali suna tafiya Yana yimata fira suka karasa part din Aunty Hajara cikin sa’a suka tadda ba kowa a falon.Har dakinsu ya rakata, Khadijah suka tadda tana Assignment na islamiyya.shiyasa hadamata ruwan wanka ya kaita har cikin toilet din,kin tsayawa tayi yayimata shiyasa ya fito.Site din drower ya bude wata doguwar riga ya fitarmata marar nauyi yadda zata sha iska ya aje bisa gadon.Ganin haka yasa Khadijah ta fito daga room din ta koma falo daidai lokacin Aunty Hajara ta fito daga kitchen.
Yana nan zaune harta fito jikinta daure da towel.shiya shiryata ya murzamata lotion kafin ya kamo hannunta suka fito falon.
Anan ya gaishe da Aunty Hajara Yana wani sadda Kai,ita dai batace da shi komai ba sai Khadijah data saka ta kawomasu kayan breakfast.
Anan falon suka baje shiya hadamasu tea ya zuba doya da kwai a plate Yana bata a baki harta koshi.itako Aunty Hajara tuni ta shige dakinta.Khadijah kin tashi tayi anan taci gaba da aikinta,Amma duk abinda suke yi tana kallonsu.
Akan weekend din daya zo saida ya Kara Two days akai kafin ya koma cike da kewar Seeyermar shi.
Bayan tafiyar shi da kwana biyar ranar wata juma’a tun gaf da magriba Seeyerma take jin ciwo kadan-kadan har dai ta ji abin ba Mai karewa bane ta fadawa Khadijah.Aiko da gudu taje ta sanar da Aunty Hajara sai gashi sun shigo a tare.
Nan ta fahimci ciwon yayi nisa da Alama nakuda ce daman cikin wannan week dinne date dinta yake cika.
Aikawa tayi aka Kira mama,saiga Faruk ya shigo nan take ya janyo mota aka sakata suka nufi hanyar Asibiti bayan an sanar da Uncle Yusuf.
Duk abinda ake yi Ummeey bata sani ba sai bayan sallar isha’i Khadijah ta shiga tana sanar da ita.Nantake ta fara Kiran wayar Aunty Hajara bata daga ba aiko dandannan hankalinta ya tashi ta saka hijaf dinta ta nufi part din Hajiya Kaka dan Dadyn su Muhseen baya nan yayi tafiya zuwa Abuja.
Cikin rudewa ta shiga part din hankali tashe tana tunanin halin da yarinyar take ciki.
A falo ta riski Kaka tana kallo ko gaisuwa bata tsaya yiba ta sanar da ita abinda ke faruwa.
Ganin ta rude yasa tace ta Kira Faruk ta tambaye asibitin da suke.Haka kuwa tayi bugu biyu ya daga.Baiyyi niyyar sanarmata ba,Amma sai ya ji muryarta cikin damuwa tana tambayar shi asibintin fa suke.
Anan ya sanar da ita kafin ta katse Kiran ta fara Kiran nomber Jabeer.
Tuki yake yi ya dawo daga cikin gari yaga Kiran Ummeey yana shigowa wayar shi,cikin sauri yayi pecking da sallama.
Saida ta amsa kafin ta sanar da shi ya zo ya kaita federal hospital da to ya amsa Yana Kara gudun motar shi.
Cikin mintuna kalilan ya shigo estate din anan ta sanar da ita ya karasa.
Ita kadai ta fito ya budemata kofar baya ta shiga ya rufe suka tafi.
Kwatsam su Aunty Hajara suka gansu harzuwa wannan lokacin kuwa Seeyerma bata haihuba.
A kalla sunkai awa daya a wurin kafin nurse din ta fito tana doso inda suke.da sauri suma suka mike suna tambayarta ta sauka.
“Ku kontar da hankalinku ta sauka lafiya ta damu baby boy,Amma ita tana bukatar jini saboda ta zubar da jini sosai”…
Cikin sauri Faruk ya ce “Doctor muje a dauki nawa zaiyi daidai da nata”
“Ok” ta amsa kafin yabi bayanta zuwa lab.
Nan take fuskokisu suka nuna tsantsar farinciki jin ta sauka lafiya.Daidai lokacin Muhseen Yana ta faman Kiran wayar Faruk bai daga ba ya koma Kiran ta Aunty Hajara.
Itako wayar tana cikin jaka sai a sannan ta tuna da ita.tana cirowa Yana Kara Kira da sauri tayi picking.
Saida ya sauke ajiyar zuciya kafin yayi sallama Yana tambayarta lafiya Yana ta Kira sunki dagawa.
“Seeyerma ce muka kawo Hospital,Amma ta haihu yanzu jini ne za’a karamata”.
Da a konce yake Yana jin haka yayi saurin tashi zaune Yana Kara sauraren abinda take cewa.
“Aunty Yanzu boy na yazo duniya,Kai Alhamdlillah lallai Ni Mai sa’a ne,Aiko ganinan zuwa yanzu”Yana saukowa daga gadon.
Saurin dakatar da shi tayi tana cewa “A a son yanzu dare yayi kayi hakuri dai gobe idan Allah ya kaimu saika taho”.
Ba haka yaso ba,Amma dole ya hakura.cikin mintuna kalilan aka gama daukar jini.Anan aka Basu okeyn su shiga su ganta.
Gaba dayansu Suka shiga,duk karar Ummeey amma yanzu itace Kan gaba tana jin dadi yau itace da jika,jikanma na son dinta da mafi soyuwa a gareta.
Bacci take lokacin da suka shiga,sai boy aka basu.Aunty Hajara ta fara amsarshi yaro tubarkalla tamkar Muhseen yayi kaki ya aje.
Haka sukayi ta daukar shi suna yimai addu’a.
Anan Faruk ya dauki yaron hotuna masu kyau Yana cikin kayan sanyi ya turawa Muhseen.Aiko Muhseen saboda tsabar murna saida yayi sujada.ranar haka yayita kallon hoton yaron Yana karawa.
Bayan sun fito Doctor ta ce mutum daya ake bukatar ya tsaya tare da ita.Sai Aunty Hajara ta zauna su Kuma suka koma gida sai Faruk ne ya dawo ya kawo masu abinci Wanda tun bayan haihu ta sanar da Hindatu ta hada komai.
Karin jinin aka sakamata ta koma baccin.sai wuraren karfe Shabiyu kafin ta farka.karin jinin aka ciremata bayan ya kare ta kaita toilet tayi wanka da brosh kafin ta hada kata ruwan tea Mai kauri.
Cikin sa’a yaron baya da yawan kuka daya farka aka bashi mama ya Sha shikenan zai koma bacci.
Da haka Suka Kai har asuba Koda Seeyerma ta anshi yaron bata san lokacin da wasu hawaye Suka zubomata ba tunowa da tayi Wai yau itace da da Wanda ta Haifa da cikinta.
Godiya tayi ga Allah yada azurtasu da wannan kyauta.
Tunda Muhseen ya farka gabanin sallar Asuba bai Kara komawa bacci ba.
Zuwa time din salla tuni ya kammala shiryawa ya saka komai nashi a mota.yana fitowa daga sallar asuba ya dauki hanyar katsina…………….⁴⁷