TAWA TA SAMENI CHAPTER 24 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

TAWA TA SAMENI CHAPTER 24 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

ya dubeta wanene?ta dan tsina baki ko Adams yake ne oho?haushi ya kama shi me yasa yarinyar nan batada kunya ne yanxu?amma zaiyi maganainta yace fita anan banza kawai ni zaki cewa baki san Adams ba? ta fita tana yin kuna kunai na gaji da wulakancinka komai kace sai an maka ni ko gsky ko a gidanmu ban kauda tsinke bare wani girki ina dan wanda zan iya kai kuma kana ganin kasa wata yana jiyota sai dai bai san me take fada ba yace zaki gane kuskurenki. Ya sami Adams zaune shima da shiga irin ta Maska Adams ya dubeahi kace ka shirya Maska ya zauna sai dai ban karya ba,haba baka karya ba kai da kake da iyali ma,Maska yace kasan bata da Ify gata dama da son jiki sam bata son aiki Adams yace sai hakuri nidai Allah
yasa nayi dace in har ka dace ka sameta din to Adams
kar kayi shakka zaka sami yanda_ kake so,Adams ya ce ya kake cewa in har na sameta?kana ma shakka
kenan?kar ka manta fa har na biya sadaki an sa mana rana kuma kaine ma ka tsaida min har na sanar da manya,Maska yayi wani murmushi Adams ya kalleshi

Maska bana son wannan murmushin naka fa tuni na sa mashi suna murmushin mugunta dan ko a fili muke
gurin wasa abokan wasa suka sako mu a gaba kana
irin wannan murmushin sai kaga Allah ya bamu
nasara,Maska yace tashi mu tafi a can zan yi break
kafin mu shiga fili. Ni kam lokacin ina kauye ranar
kwana na sha takwas daga sati daya ina jikin tsohuwa Www.bankinhausanovels.com.ng
kakata tana fadin daga ni takwara kar ki karasa ni nace
kai dan Allah ki barni na dan huta mana infa na tafi sai na dade zan zo tace ai ba zaki kawo min Adamu mu gaisa ba?nace ni ina naga wani Adamu yana can
kasashen turawa yana kwallo tace ai Ball yake?ynxu
dan Ball din zai rike ki?nace to ai tasu ta gaske ne ba irin ta nan ba,ta tureni ke ja can da ban haushi baga su nan muma muna dasu ba yan bal din yanxu jibi yaron nan na gurin karima shima aikinshi kenan bal asubar fari yasa gajeran wando da wani kwandallelen takalmi raf raf ya tafi bal kusan shekara biyar ance har yau baa taba nuno shi a cikin talabijin ba shi bai tsaya yayi
noma ba shi kuma bai tafi rani ba,sai dai yau yana
waccan unguwa gobe yana waccan yawon bal.,tunda ta soma magana nake dariya,tace dariya ma na baki?
dama wannan shirmen Adamun keyi shine za’a bashi
mata?ko mu da muke karkara dan gidan karima an
hanashi mata,na kuma tuntsurewa da dariya ta dau
mafici ta bini ki bani guri ta kai min duka da gudu na
fita ina kwasa dariya sai naji tsayuwar mota da sauri na
leka motar babana na gani da gudu na fita na
taroshi, Ya kira wasu yan samari suka shigo da kayan
abinci na rike mishi hannu muka shigo, dakin Baba ya
soma shiga kafin ya shiga dakin Tsohuwa na nufi
madafi na dauko masa abinci a kwano na debo masa
ruwa a randa na aje a gabanshi ina fadin Babana kamar nasan zaka zo na yi abinci da yawa,yace to na
gode,nace yasu Mama?yace suna Ify sune ma suka
matsa min akan na daukoki daga sati har kin kusa wata Www.bankinhausanovels.com.ng
jiya Alh ya kirani a waya yace in mashi kwatance yaje ya daukeki,nadan yatsina fuska nace ni ban son tfy tsohuwa tace to ai ya zama dole nace muna gama bikin su Mami zan taho nan,baba yace a’a muma muna son ki zo mana kafin bikinki daga nan nayi shiru ban sake magana ba,tsohuwa tayi caaraf tace yawwa ashe kai yanzu Adamun dan bal ne?shi ne zaku bashi yar? Babana yayi dariya sannan yace ai sana’a ce sosai suna samun kudi fa shima dan mai gidan Habiba kwallon yake tare ma suke, ai shi kenan amma ko ga tarihi bal ance bata da kyau,yace to ai wasu malaman sunce za’a iya yi in ta zama lalura saboda kishin kasa tace tunda kuna so ai komi ma cewa zakuyi ni dai ina jin su har suka gama.
da misalin tara text din da aka saba yi min tsawon
watanni kullum ba fashi ya shigo,very soon zamu
kasance tare domin nasan i am always lucky akan duka abinda nakeso,ban ma gama dubawa ba na kashe yau kamna gane Adams ne yake min text yana boye no haushin shi ya kara kamani na hau fada ina cewa nufin
shi sai ya min haka zan so shi?to yayi kuskure ni ba
sonshi nakeyi ba zan dai aure shi ne dan hujjar da na
ba yaynmu nace kai bari ma in mashi karara don ya
daina damuna na soma neman layinshi ai cikin sa’a na
sameahi ashe lokacin suna tare da yaynmu a wani club
ya dubi yaynmu yace ga yar gidana sannan ya
dauka,in kaga yaynmu zaka dauka bai damu da wayar da Adams keyi ba amma ya tattara dukkan hankalinshi gurin sauraron Adams dan ta maganr da Adams keyi zaka gane me nace,ni kam Adams na dauka nace hello Adams menene na boye no kana yi min text in ma kana yi ne dan ka birgeni to wilh haushi ma kake bani,tunda na soma maganar bai tare ni ba sai da nayi shiru,yace calm down my wife wllh ba ni bane ba ban ma taba yi maki text ba nace to wanene?ina zan sani inji adams sannan yace don Allah kiyi hakuri karki damu kanki kashe na kiraki,nace yanzu zanyi shafai da wutiri ne sai Www.bankinhausanovels.com.ng
da safe yace sai da safen yanda ya amsa har tausayi
ya bani,Maska ya dubi Adams dan san jin karin
bayani,Adams me Iman tace maka ne?Adams yace wai
cewa tayi ina boye no ina kiranta wai bata so
Maska yayi murmushi to dama kai kake mata ko? Adams yace bani bane Allah maska yayi tsaki sannan yace kaga abinda nake gaya maku ko ku nemi manyan babys ynxu gashi kana yi ma yar cikinka rantsuwa ita kuma sai masifa take maka ynxu ina girma?babu babba wani abun ma sai taga gadon kwananka Adams yayi murmushi yace wannan ra’ayinka ne kawai niko ina son in auri yarinyar dan na more sadakina da kyau Maska yace in ka samu big girl shine zaka more sadaki Adams yace mu bar zancen haka Maska yace kai dai ka sani yaushe zan bar yar yarinya ta juyani? ai ni in babbar ce ma sai ta raina kanta in tace zata kawo min iskanci Adams yace in baka sonta ba ba in kana sonta komai zatayi maka zaka jure sai kaga karamar ta juya ka babbar bata juya ka ba,tsaki Maska yayi sannan yace baka gama sani na ba har ynxu don ina son mace tayi kadan na jure iskanci, sannan ya mike ya tafi Adams na mishi dariya.
Muna zaune a dakinmu muna aikin gyaran katunan
bikin su Mami yau saura kwana takwas bikin kuma
yaune su yayanmu zasu iso shine babban abokin ango
kuma babban yayan Amare,na dubi Mami nace ya kan
Badarawa,Malali,da Unguwar sarki ya kamata muje dan
yan skull zamu gayyace sosai mun dade bamu hadu ba
mami tace haka ne yi sauri mu biyama Amira,tare
muka shiga gari sai magriba muka dawo sai dai in
lokcin sallah yayi mana mu tsaya muyi,shirye shirye
sunki karewa saboda wasu abubuwan bada su Sa’a
zamu hada ba walima ce kawai tare sai Sisters day da
su Anty Mariya suka shirya a gidan yaynmu in sun iSo a Yakubu Avenue amma mu zamuyi lunchn sannan
angwaye sun shirya dinner mun dawo mun sami Www.bankinhausanovels.com.ng yaynmu ya iso saboda gidansu sai an gyara da yan share share gurin su Sagir na sami lbr isowarsu sai ga kuma wayar Adams yana ce min sun iso ynxu suna tare da ango nace to sannu da zuwa me zan shirya maka?yace komai ma nace to an gama nadai daure ne nayi wannan maganar dan kar ya ce ban yi murna da
zuwansa ba amma zahiri hankalina yana kan yayanmu
da kuma masifar son ganinshi,nan na dan yi girke girke na san Adams na zaci zan sameshi tare da yaynmu a dakin yaya kabir din ina sai shi kadai na samu dan haka shi kadai yayi ta surutanshi Adams ya dubeni kin kara cika fa yar gidana ina son Maska ya ganki shi da yake
cewa zan auri yar cikina nace um! Sama sama mukayi
hira sannan na koma gida shi kuma ya nufi gidan Nasir
har ranar lalle banga yaynmu ba ko anty mimi ban
gani ba mu da yake gidansu Amira mukayi namu lallen
su kuma gidan Anty Hadiza sukayi,sisters day shine abu na farko da kamar kar naje mami tace in banje ba bazata ba dole tasa nace to zanje,da yake dama gurin babana naje na amshi kudi na shiga kasuwa materials da lace sai da naga karshen tsada na sai mana takalmi da jaka ai fadi ma bata bakine ganin abin rabawa na
buga jaka na buga bokitai na roba sai na buga agoguna har fada mama tayi min wai naje ina amso kudi masu yawa haka shi kuma ya biye min,nace to mama kiyi hakuri yana cewa in basu isa ba zai kara min wasu wai dan ni kadai yake neman kudi,mama tayi
tsaki ta shige daki mu da Amira ba muje shirya gurin
da zaayi sisters day din ba dan gudun rikici sai bayan
an gama komai an soma kai kawaye sannan muka
shirya,jan material dan dubai shi na dinka riga da siket
nasa duk yanda mutum ya kai ga hassada ba Zai
kusheni ba a wannan rana takalmi da jaka bakake nayi Www.bankinhausanovels.com.ng
amfani dasu kafin amira ta gama shiri na shiga gidan
mu na fito wata mummunar faduwar gaba naji sanda na hangi yaynmu a kofar dakin yaya Kabir shi da Nasir sanye yake da wando jeans baki da riga fara ta kama jikinshi kyau annuri ne ke fita a fuskarshi yana da kyau na karshe fatar shi ta kara zama smooth giran gashin shi kuwa abin birgewa ne,kamar na juya sai na dake tunda bai ganni ba gara na nuna ban ganshi ba sai da nazo daf da su sai Nasir yace kai Iman wannan dauke kai haka?na juya da sauri ango ban ganka ba ne,na isa
wurinsu na dubi yaynmu wanda yayi wani kicin kicin da fuska nace sannu da zuwa yaynmu kunzo lfy?a ciki yace Ify duk sai naji ba dadi dan haka sai nace Nasir a kirata ne?yace a’a ba gurinta nazo ba sai na wuce ciki,ganin yaynmu sai tsohon ciwona ya tashi wutar sonshi ta soma ruruwa a cikin zuciyata ranar dai sai a hankali mun isa gidan yaynmu sai naga ma ashe duk yanda suke bada Ilbr haduwar gidan ya wuce nan gefen da ake sister day lambu ne yanda suka shirya yayi kyau Amare kaya iri daya suka sa tunda muka zauna bamu
tashi ba sai da aka soma liki sannan ne na shiga nima
na bada tsoro da kudi na fito,anty mimi tayi kyau sosai
cikin farin tattausan leshinta rigar fitet ce don haka cikinta ya dan fito dan das daga mun hada ido Sai ta dalla min harara har Amira ta lura da ita tace ke kefa matar can take harara nace tayi ta gama abinda yasa
ma bata neme ni da rigima ba dan tasan yanxu bama
shiri da mijinta ko ince an samin rana shiyasa Amira
tace haka ne kam,wayata ta soma ringin na duba sunan
yaynmu na gani gabana yayi mummunan faduwa na
dauka yace ina jiranki a falon gidan nan cikin in ina na Www.bankinhausanovels.com.ng
ce ban san hanya ba ki tambaya sai ya kashe wayar na dubi Amira kinji yaynmuda rikici ko wai na sameshi
falonsu bayan dazu da ya ganni sai ya wani daure
fuska Amira tace kije mana nace to ai tana kallona
matarshi Amira ta ce to zauna ina ruwana,na mike na
nufi hanyar waje nan na kirashi nace ban gane hanyar

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *