DR MUHSEEN CHAPTER 4 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 4 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

      📝………………..Cikin mutuwar jiki ya ci gaba da maimaita kalmar Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un,har zuwa tsawon wani lokaci bai gusa daga inda yake ba saida ya yayi addu’o’i sosai domin shidai tunda ya bude yaga kamar mutum zaune bisa kujerar falon nashi.Amma cikin ikon Allah da karfin addu’a ya daina ganin mutumin.ba tare da yayi kasa a gyuwa ba ya shiga gidan da kafar dama Yana ci gaba da neman tsari daga sharrin abinda ya gani.

A katsina kuwa a lokacin da ya bude dakin shi yayi daidai da farkawar Seeyerma daga nannauyan baccin daya dauketa.bakinta dauke da Addu’a ta juya ganinta konce kan gado yasa tayi 

saurin ta shi tasan tuno abinda ya faru Amma ta kasa.shigowar Aunty Hajara yasa tayi saurin Kai dubanta bakin kofar tana girgiza kanta.

     Da sauri Aunty Hajara ta karaso bakin gadon tana yimata sannu.

Ita dai bata amsa ba,sai gyada kanta da tayi.

Ganin hawaye nabin saman kumatunta yasa Aunty Hajara tayi saurin kamo hannunta tana cewa “sorry Seeyerma taso mu je kiyi Alwala, lokacin salla yayi,kiyi hakuri ki yawaita addu’a,zo mu je kafin Uncle din ki ya amso maki magunguna sai ki fara amfani da su”tana kokarin mikar da ita tsaye.saida ta kaita  har cikin toilet ta hada Mata ruwan wanka kafin kafin ta fito tana jin alhinin faruwar wannan abin al’ajabi.

Seeyarma ta dade sosai tana wankan kafin ta dauro alwala ta fito.kayanta ta gani Aunty Hajara ta ajemata a bisa gadon.ko mai bata tsaya shafawa ba turare kawai ta murza a jikinta kafin ta saka doguwar rigar ta atamfa.bayan ta shimfida prayermate ta saka dogon hijaf tare da kabbara salla.cikin nutsuwa ta biya sallolin da aka biyota.ta Jima ta addu’o’i ga iyayenta da neman sauki a rayuwar ta.abinda yafi dauremata Kai shi ne yadda aka fara bibiyar rayuwar ta,sannan tun daga lokacin da taga ya Muhseen Amma ba da ainahin sufar shi ta ganshi ba shi ne abinda ya tsorata ta.Aunty Hajara ce ta Kara shigowa hannunwanta dauke da babban tray sai kayan abinci da aka jera a saman shi.

Kusa da ita ta aje tana umartar ta da ta ci abincin yanzu zata amso Mata maganin ta sha.tana juyawa zuwa part din Uncle Yusuf.

Cikin sanyi ta cire hijaf din jikinta ta fara zuba abincin.kadan taci faten doyar ta ji ta koshi.shiru tayi hannuwanta bisa kumatunta tana ci gaba da tunaninta.

“Mhammadu kayiwa Allah ka maido da matarka,ni bazan yimaka Baki ba akan zaman ka da Mariya,Amma bazan gaji da jaddadama ba Mariya ba matar kirki ce ba,bawai Ina zarginta ba,Amma ni da ahalina a kullun Muna addu’ar Allah ya toni asirin duk Wanda yake da saka hannu a cikin rudanin da muke fuskanta.”cewar Kaka da take zaune bisa abin sallah kanta jingi ne jikin doguwar kujera.kallon shi ta Kara yi a karo na biyu ganin yadda kolla take zuba daga idon shi.ajiyar zuciya ta Kara saukewa ganin kalamanta sun fara ratsa jikin shi.tabbas an fara samun ci gaba idan lokuttan baya ne ko saurarenta bazai yi ba.

“Kayi hakuri muhammadu kowane bawa da irin kaddarar shi,Amma hakuri shi ne ke maganin komai”

Shi dai ko uffan baice ba,sai faman sharar kolla yake yi.shiru sukayi dukan su,har tsawon wani lokaci kafin ya mike jin mahaifiyar tasu bata ce komai ba.harya fice tana kallon shi kafin ta girgiza kanta tana tunanin wasu lokutta da suka shude.

Dr muhseen ne ya fito daga part din shi ya nufi cikin area asibintin dan duba masu jinya.yayi nisa sosai da tafiya ,saboda akwai tazara mai Dan nisa daga dakunan su zuwa cikin asibitin.zuciyar shi cunkushe take da tunani iri-iri,jin Karan wayar shi ya saka saurin laluba ajjihun farar jallabiyar da take jikin shi,ganin sunan Ummeey akan secreen din wayar yasa ya Kara jin faduwar gaba,Dan yasan zata tambaye shi jikin Seeyerma ne.saida ya Bari ta katse kafin ya danna calling nomber,wata Yar inuwa ya nufa Yana tsayawa.

Cikin sallama ta daga wayar jin muryar Dan nata abin soyuwa a gareta.cikin yaren larabci take tambayar shi jikin Seeyerma,cikin sanyi yake cemata da sauki, Anan yayi Mata bayanin matsalar.

Sosai taji tausayin yarinyar Dan tasan tabbas magautan su a cikin estate din suke,Anan ta Kara bashi shawarwari tare da Kara kontar mai da hankali.kafin suka yi sallama.ya katse Kiran,ya karasa cikin asibitin .Dan Muhseen Al’adar shi kenan,inhar Yana nan to sai ya ziyarci masu jinyar.

Faruk ne yake kokarin bude part din,Amma jin kamar ana magana a gefen part din yasa ya juyo da sauri,cikin sanda ya nufi wurin Yana Kara kasa kunnen shi,jin irin kalaman da suke fitowa daga bakin wacce take tsaye.da sauri ya koma Yana labewa ganin kamar zata juyo.ji yayi tana Kara cewa.

“Idan har kayi sake daga ni har Kai zamu fada wata zazzafar rijiya wadda zurfi da kwazazza fan da suke cikinta zasu hallaka mu”nisawa tayi tana cigaba da cewa “kaga Alhaji na gaji da gafara sa Banga kaho ba,tsawon shekaru Muna faman turin mota Amma tana neman tashi ta bademu da kura,ko kasan abinda zaka yi da mu,ko ni na dauki mataki da hannuna”banji amsa da aka Bata ba tayi saurin juyowa   cike da mamaki Faruka ya Kara bude idanuwan shi dan tabbatar da wacce ya ….Da sauri ya juya bayan fulawowin da suke gefen shi,ganin tana kokarin juyowa site dinda yake, gani yayi ta ci gaba da tafiya harta karasa bakin kofar part dinta .saida ya tabbatar data shige  kafin ya fito daga inda ya buya,cike da mamaki yake jinjina kanshi tare da al’ajabin maganganun da kunnuwan shi suka jiyoma shi, domin lamarin ya matukar daure mai Kai ,Amma yayi alkawarin bazai sanar da kowa ba,zaiyi iya bakin kokarin shi dan ganin ya ci gaba da bibiyar su har ranar da Allah zai tona asirin su.da wannan tunanin shima ya karasa part din Kaka dan amsa Kiran data yimai.

  Cikin ikon Allah Dr muhseen harya karasa duba masu jinyar baiyi cin karo da Zahara’u ba,Daman bayasan su hadu saboda yarinyar sam bata da kamun kai.saita dinga wani firirita da iyayi,yasan duk dan saboda shi take yi,Amma zaiyima tufakar hanci.haka yayi ta tafiya cikin best din Yana Kara kallon yanayin gine-ginen wurin kowane block da yanayin tsarin shi ,kamar yadda kowanne da rank din shi,to a fannin wuraren zama ma hakan ne mafi yawan manyan su suna block din da yake off-site ne sai masu daki daya-daya,wasu daki daya mutum biyu saboda suna da yawa.Block din su Dr muhseen kusan shi ne block na biyu a yanayin tsaru.yana gaf da karasawa part dinsu ya jadu da Aminu.cikin sauri Aminu ya Sara mashi cikin harshen turanci ya ce “Evening sir”

Dr muhseen saida ya fadada murmushin shi kafin ya amsa da “Evening Aminu,how are you”

Sai a lokacin Aminu ya sauke hannunwan shi daga kamewa ogan nashi da yayi cike da girmamawa ya amsa da “fine sir”haka suka gaisa cikin harshen turanci kasancewar Aminu muslmi ne Amma Yana da yare,hakan yasa bai iya magana da Hausa ba sai jefi-jefi irin yanzu yake kokarin koya.

Bayan sun rabu tafiya kadan ta kaishi dakin nashi,Dan a lokacin an kusa fara Kiran sallar magriba.

Kana shiga wani hardaden karamin falo ne mai dauke da full set na kujeru masu kyau da tsada.a gefen shi ta barin hagu kuwa wurin dinning  table ne mai dauke da set din kujeru na dinning ,ta gefen shi kitchen ne dan madaidaici cike yake da kayan bukata kama daga electrics, kulas masu kyau da tsada,sai katuwar feradge ta kamfanin LG.a da aka ajeta gefen dinning, cikin falon kuwa bayan kujerun da sukayima falon kawanya sai kafet a kasar tiyels din mai kyau da daukar ido kalar kujerun.sai falisma like jikin bango ta jikin bangon falon daga gabas, .sai toilet guda da aka yishi a cikin falon daga bakin kofar da zaka shigo.daka bar falon zaka bi wani Dan karamin hanyar da zai sadaka da bedroom guda biyu da suke passing din juna masu girma ne kowanne Yana dauke da babban toilet,an saka pornitures masu kyau da tsada,bed da mirrow sai wardrobe wadda take like jikin bango.hatta labulayen wurin kalar kayan ne.hakan take ga sauran dakunan komai na bukata akwai sai abinda baza’a rasa ba Wanda mutum zai zo da shi.

Cikin sauri yayi alwala,key din shi ya dauka sai phone din shi ya shiga mota ya wuce masallaci.

      “Faruku kada na Kara jin wannan maganar ta fito daga bakin ka,idan ko harka saki yarinyar nan ta ji to akwai gagarumar rigimar da zata iya hadaka fada da sauran yan”uwan ka”cewar Kaka da ta tsare Faruk da ido,jin wani soki burutsun zance da yake neman kawo Mata.

A hankali ya dago Kai Yana kallon tsohuwar.saida yayi kamar zaiyi magana,Amma saiya fasa saboda wani tunani da yayi a ranshi.

     Jin yayi shiru yasa ta ce “kasan yarinyar nan tamkar iyayenta haka ta dauke ku,sannan Koda babu wannan to ni ban amince da wannan batun ba,kadai zabi wata Amma banda wannan,sannan shima Mai gidan zai dawo daga Daurar ya zo ya tadda ni,Amadu ya sanar da ni yadda Suka yi da shi,akan maganar fitar da Mata,to ni idan na yanke hukunci bana canzawa”tana laluben inda ta ajiye wayar ta.

Mika mai tayi tana Kara cewa “Anshi nan ka kiraman shi naji dalilin shi na kin zabar matar da zai Aura,Dan bai isa ya Auro Yar Daura ba”tana Kara mikawa Faruk karamar wayarta.saida ya amsa kafin ya ce

“Kinga yanzu dai lokacin salla yayi, nasan ya shiga masallaci,Nima salla zanje nayi anjima zan dawo”Yana mikewa tsaye bayan ya aje Mata wayar a kusa da ita.

Har yakai bakin kofar falon yajiyo sautin muryarta da dan karfi tana cewa “ja’irin nan sauran Kuma kaki dawowa,na saka iyayenka su nemoman Kai,shima wannan Jabirun zai zo ya tadda ni,nan da wata ukku sai dai ku tadda matan ku a gidajen ku gwamma ma ku zaba da kanku”.

    Shi dai bai jira karshen zancen ba ya fice masallaci da sauri jin za’a tada ikama.a ranshi Yana jin haushin mitar Yar tsohuwar.wani lokacin kam takan bashi dariya.

      Tun bayan faruwar lamarin Seeyarma har yanzu tana part din Uncle Yusuf.haka Yan estate din suka yi ta tururuwar zuwa dubata,kama daga manya da yara,Amma har yau da akayi tsawon kwana ukku da faruwar lamarin Ameerah da Safna basu je sun dubota  ba.bata yi mamaki ba dan tasan daman Ameerah kiri-kiri take nuna mata tsana a fili ta rasa laifin da tayi mata, take kinta.Itama Safna wani lokacin suna yawan yin fada dukda da kadan ta girmeta hakanyasa suka kaman sa’anin juna.dan ta lura da ita duk lokacin da ya Faruk ya kawo Mata wani abu to ranar Safna tayi ta faman jin hushi da bata rai.sai taga Seeyarma taki kulata kafin zata kyaleta.

Dr muhseen a tsawon kwana ukkun da yayi baya katsina kullun saiya Kira Aunty Hajara dan jin ya jikin yarinyar yake,saboda shi harga  Allah asalin shi mutum ne mai tausayin na kasa da shi.jin Aunty tana cewa ta ji sauki saboda magungunan da take amfani da su masu karfi ne yasa hankalin shi ya dan konta.haka shima ya sanar da Ummeeyn shi da suka yi waya.

A ranar Juma’a tunda safe Seeyerma ta shirya,sanar da Aunty Hajara tayi zata je ta gaishe da kaka.dariya Aunty Hajara tayi tana cewa “wato hankalin ki Yana gurinta,kun kwana biyu baku Kara fada ba ko,to jeki inanan zan ji ku”tana dariya.

Seeyarma gaba tayi tana cewa “hmmm Ai kinsanta idan kana kusa da ita bata barinka ka huta”daga haka ta fice daga site din.ba wata kolliya tayi ba.ko mai bata shafa ba sai rigar dake jikinta ta yadi ce,ta dora babban hijaf akai.sai silifa fashion data saka.

Cikin natsuwa ta doshi part din na kaka.tafe take tana tunanin “to Ina Soja ya tafi bai zo ya dubata ba”,wani bangare na zuciyar ta ya bata amsa da “may be tunda ya koma bakin aikin Shi ya manta da ke”da sauri ta girgiza kanta tana dafe kirjinta da hannu.abinda ta tuna ranar daya danneta harta suma.A fili ta furta “yanzu daya rusaman rayuwa”da sauri ta Kara girgiza kanta tana cewa “Kai nasan bazai yiman haka ba”daga bayanta ta ji ance waye bazai yimaki haka ba”

Cikin zabura da tsoro ta juya,Ajiyar zuciya ta sauke tana fadada murmushin ta ganin ashe ya Faruk ne.tsayawa tayi tana kallon shi,ganin yadda shima ya tsareta da idon shi.

      Turo baki tayi cikin sunbiro baki irin na shagwababun yara ta ce “Ya Faruk Wai ko na canza kama ne,kake ta kallo na”.

   Gani tayi ya lumshe idon shi tare da Kara bude su akan kyakkyawar fuskar ta.saida ya rausayar da kanshi bisa kafada shi kafin cikin sanyi ya ce “Dear naga kin Kara kyau ne,da kikaga na tsaya Ina kallon kuwa ganinki nayi tamkar matashiyar barewa tana gudu a cikin daji,shiyasa nake Kara yimaki addu’ar Allah ya Kara kareman ke daga sharrin makiya”ya karashe maganar Yana kallon cikin kwayar idonta dan jin amsar da zata bashi.

Sosai ta Kara fadada murmushin ta,Dan taji dadin addu’ar da yayi Mata,  itama shagala tayi da kallon shi.bata ankare ba taji ya saka yatsar shi a jikin dimple din kumatunta.da sauri ta saka dariya tana rugawa haka shima ya bita har suka karasa bakin part din na Kaka.

     Kaka tana zaune sai faman mitar halin yaran nan take yi,duk sun lalata Mata falo yayi kaca-kaca sai ji tayi an rungumota ta baya.da sauri ta juya zata fara masifa,ganin Yar jikallenta ta yasa ta ce “Amma wannan yarinya akwai marar jin magana,wato so kike ki kayar da ni ko?”.

Ita dai Seeyarma sai faman dariya take yi.sai a lokacin ta tsagaita ganin shigowar ya Faruk.

     Duban shi Kaka tayi tace “Au ashe tare kuke tafe ,ni matsa na zauna kada ki kayar da ni”.matsawa tayi jikin kujerar tana Kara yimashi dariyar ta rigashi shigowa.

Dubanta Seeyarma tayi kafin ta ce “Ni wallahi saina tashi nayi tafiya ta,ko oyoyo baki yiman ba,harkin fara fadan naki”.

      Sosai taba Kaka dariya ganin yadda ta sha toka ita a dole an bata mata rai.

Lallashinta tayi kafin suka fara hira,shi dai Faruk sai ya zama dan kallo Dan yasan akwai kauna tsakanin Kaka da Seeyerma,tun kafin rasuwar iyayenta duk cikin yaran Estate din jinin su yafi haduwa dana tsohuwar.sai Dr muhseen da take Kiran shi da mai gidan dan sunan mijinta kenan.shiyasa bata iya Kiran sunan shi Kai tsaye inhar ba mahimmiyar magana zasu yi ba.

Suna cikin wannan hirar suka tsinkayi sallamar Dr muhseen a bakin kofar falon,duka-duka lokacin ko karfe goma bata yi karasa ba.a bayan shi kuwa Jabeer ne yake biye da shi.Ai Seeyerma da gudu ta taso ta dane jikin ya Jabeer tana faman dariya dan ita harga Allah Bata lura da Dr muhseen ba.shiko Jabeer sosai ya riketa Yana juyata sai faman gaggaba dariya suke yi.ganin haka yasaka kowa na wurin ya tsaya Yana kallon su.cikin masifa Dr muhseen ya daka masu tsawa data sanya Jabeer direta kasa ba tare daya shirya ba.cikin haki da gajiya Seeyerma ta zauna jikin Ya Faruk tana mayar da numfashi.sosai Dr muhseen ya tsuramata ido Yana kallonta.dan haushin su yake ji.cikin zafin nama da bacin rai ya damko gashin kanta da tayima dauri da bant.azabar da ta ji ta ratsa kolwar kanta da gangar jikinta yasa ta buga wani uban Kara cikin  karkarwa da  jin zafi ta ce “wayyyyyyyooooooo Kaka ku taimake ni zai cireman kai”cikin fargaba da tsoro Jabeer da Faruk Suka mike da sauri ganin yadda dr muhseeen ya saka hannun shi a cikin…………………⁹

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *