AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA 

Bacin ran da ya sanya ta kasa yin abin da ta ke dokance da yi, zuciyarta ta yi duhu matsananci. Kawai sai ta kashe komai ta ture gefe ta koma ta kwanta, ta lumshe idanunta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai da suka gama kimtsa komai ya sallami Danfulani, ya zuba ruwa a karamar tukunya ya dora a ‘gass’ ya kunna. Nan da nan ya yi zafi, ya dauko ledar “‘cous-cous’ cikin katon dinsa ya farke ya juye rabi. Ya kashe ‘gass’ din. Ya kwashe gabadaya a (food-warmer) ya diba a ‘plate’. Miyar da ransa ya biya da ita tun dazu ya diba ya zuba a kai ya sanya mata sauran a firji yadda ya ganta, ya ja gefe kan karamin ‘dining’ din cikin ‘kitchen’ din ya ci ya koshi.
Ya kora da ruwa mai sanyi ya fito ya yi dakinsa.
Karo ya ci da katon din (sanitary pad) da macleans din ( beverly hills formula ) da ya saya mata a falo har da shampoo din (pert-plus) a cikin


ZAMU TASHI 

katuwar leda don haka ya dawo da baya ya dauka ya fasa shiga nasa dakin ya nufi nata. Daga kwanciyar da ta yi barci ya dauke ta, ga ciwon kai. Ya yi sallama har sau uku bai ji ta amsa ba, ya yi niyyar ajiyewa a nan bakin kofa ya tafi sai ya tuna da system dinsa, kuma zai yi amfani da ita yanzun. 

Babu tunanin komai a ransa ya murda kofar dakin ya shiga don a tsammaninsa ma ko tana ‘toilet’ ne. 

Barci ta ke yi, ta saki jikinta sosai tana bacci bilhaqqi. Gashin kanta ya wargaje a kan filo bakikirin da shi mai sulbi da sheki, amma tsayinsa bai wuce dokin wuyanta ba. Abin da bai taba gani a matan da ya taba sani ba sai na kanti, musamman Mu’azatu kullum cikin adon gashin kanti ta ke shi ya sa ya Www.bankinhausanovels.com.ng fahimci ba ta da gashin ne, kuma ba ta son a gane. Ga wata irin tattausar fata mai hasken da babu surki da mayukan kanti (natural), bakinta jazur dan mitsitsi gwanin ban sha’awa. Gashin idonta mai tsayi ya bi fatar idon ya kwanta a kan matsakaitan idanunta. Doguwar riga ce a jikinta mara hannu irin ta robar nan ta bi fatar jikinta ta kwanta a ko’ina, kalarta (orange). Kirjinta bai cika sosai ba, amma cikar kugunta ya nuna Allah ya ajiye mace nan da wani dan lokaci. Bai san tsayin mintunan da ya kwashe a tsaye yana kare mata kallo ba har sai da ta motsa ta juya, ta ji kamar inuwar mutum a kanta. Da sauri ta bude idanunta da suka sauya kala saboda bacci ta sauke su a kan Abdul’ azeez Dakata, wanda ya yi hanzarin sunkuyawa zai dauki ‘system’ dinsa. Nata hannun ta kai ta dafe 

‘system’ din. Wani gefen yake kallo bai yarda ya juyo sun sake hada ido ba balle ta ga kwayan idanunsa. 

“Zan dauki ‘laptop’ din ne”. Ya fada ( in subdued ). 

“Ban yi ba”. Ta fada da murya irin ta wanda ya tashi daga barci. Tuni ya manta da komai, ya juyo ya dube ta da mamaki. Ba ki yi ba? Amma na gaya miki ki hanzarta ko? Za su rufe kuma ni ma ina amfani da shi’. Tura baki ta yi gaba ta kyabe shi abin dariya. 

“Na kunna zan yi, hoton ‘yammata ya hana ni ganin ‘ icons’ din”. Ta sakar masa abarsa ta shiga tattare takardunta da suka watse a kan gadon. Kasa dauka ya yi, mamaki kamar zai kashe shi. Shi yarinyar nan ta ke kyabewa baki? Ya girgiza kai ya dauki abarsa, bai ga laifin kowa ba sai kanshi, shi ya bada kafa har ta soma raina shi. Sanda ba ta ganinsa ta isa ta cuno masa baki ne har ta ce ya zuba ‘yammata a Www.bankinhausanovels.com.ng computer ? Kwafa ya yi wadda ta zame masa al’ada in abu ya ba shi haushi. Yanzu haka hoton Mu’azatu ta gani shi ne za ta yi masa sharri wai ‘yammata. Kamar irin ya zuba hotunan mata kala-kala din nan. 

Har ya kai bakin kofa ya rasa abin da ya saukar da haushin da ta bashi, sai ya dakata, ya juyo ya mika mata hannun damansa, na hagun na rike da ‘laptop’. 

“Ba ni takardun ni in yi miki’. Ba musu ta tattara ta mika masa, idanunta na kallon taga. Dawowa ya yi ya amsa, ya fice yana murmushi. Al’adar maza ne jin dadi in matansu na gida sun nuna suna kishinsu ko me? Ita din yarinya ce karama da ya tabbata ba ta san mene ne so ba, amma ta Samu zuciyarta da kishinsa. Bai san me ya sa hakan ya darsa abin da ya ji a zuciyarsa ba. Bayan ya gama cike mata takardun cike da mamakin hazakarta a dukkan makarantun da ta yi a Jeddah da Brussels ya yi ‘submitting’, sai ya dauko tangamemen hoton Mu’azatu da ke dakinsa ya dawo da shi falo ya kafa. Kana shigowa falon da shi za ka fara tozali. Ba ita ta fito daga daki ba, sai da yunwar cikinta ta hana ta jin dadin kwanciyar da ta ke ta yi tunda ta yi sallar isha’1. A hankali ta sauko daga gadon ta nufi ‘kitchen’. Nan ta tadda ‘plate’ da cokalin da ya ci abinci da ‘warmer’ a kan ‘dining’. Da sauri ta bude inda ta tadda farin ‘cous-cous’, a ‘plate’ din da ya ci ta zuba, ba tareda ta tsaya wankewa ba saboda yunwa, ta bude firji ta zuba Www.bankinhausanovels.com.ng miya ko dumamawa ba ta tsaya yi ba ta zauna ta hau zubi. Sai da ta yi kat! Ta yi gyatsa ta yi hamdala ta sha ruwa sosai, ta wanke kayan da suka bata, sannan ta bar kicin din. Ba ta yi tozali da hoton Mu’azatu ba sai washegari. Sai da ta gwammace da ta sani ba ta yi magana a kai ba. Dauke kai ta yi daga kan hoton ta ci gaba da sabgoginta kamar yadda ta saba. Amma abin ya yi mata ciwo sosai, da ma an ce mutum shi yake bada dama a gane abin da ba ya so. Za 

kuwa ta ba shi mamaki, ko a fuska ba zai kuma gane ba ta son Mu’azatu ba. A daki ta tadda wata katuwar leda da ta lura tun jiya ya ajiye ta, zama ta yi a gefen gado ta jawo ta ta bude. Kunya ce sosai ta kama ta ganin abin da ya sayo mata, sai dai ta ji dadin ‘macleans’ din sosai, kuma wanda ta ke so ko a Brussels tunda suka dawo ba ta same shi ba (beverlyhills formula). Da kuma ‘Harpic’ da ‘parazones’ na wanke ‘toilet’ sannan ‘air wicks’ har kala uku. Ta ji dadi sosai a ranta, wannan ya nuna yana daga cikin mutane masu gano laifukansu da kansu su gyara, ba zalunci da rashin adalci ba ne da ta yi inkari da su. Musamman da ta shiga ‘kitchen’ ta bude firij da ‘freezer’ sosai ta yi istighfari na kuskuren fahimtar da ta yi masa a farko. 

Shi kadai ya san yadda daren jiya ya kasance masa a tarihin rayuwarsa. Wani sabon al’amari da ya bakunci gangar jikinsa don ba zai ce da zuciya ba. Ita zuciya ‘so’ ne a cikinta, gangar jiki kuwa ba ka iya katange shi daga abin da ya ga dama. A shekarunsa a duniya talatin kuma_ cikakken musulmi mai tsantseni, wanda bai taba yin zina ba, yake rokon Allah kullum ya tserar da shi daga aikatata, Ubangiji Subhana ya amshi du’a’insa bai taba aikatawar ba har zuwa yau da aka dauko wata mace da bai so aka mallaka masa da igiyoyin aure. 

A tunaninsa yadda ta shigo, haka za ta koma inda ta fito, saboda bai yi tanadin hada rayuwa da ita ba ta kowacce fuska. Sannan a perception dinsa ba ka sha’awar mace sai kana sonta. Ya yarda ya amince har zuciyarsa ba ya son Suhaanah, babu soyayyarta ko rabin cokali a zuciyarsa, amma ganin da ya yi mata jiya tana bacci ya tunatar da shi cewa shi ma namiji ne, yana bukatar mace for now . Ba sai ana son mace kadai ake sha’awarta ba. A cire duk wata maganar gangar jikinsa, so ko rashinsa, (he need a wife). Gane hakan da ya yi bai hana (criticsms) iri-iri zuwa cikin kansa ba… ““Wannan al’amari da gangar jikinsa ke bukata a yanzu ba’a farawa don a daina… what of idan ta yi ciki? Ya ya rabuwar za ta kasance mai sauki idan da Da a tsakani? Wane uzuri zai kawowa Mammah idan ya mayar mata yarinya da ciki? Runtse idanunsa ya yi da karfi ya ci gaba da juyi a makeken gadonsa cikin wani hali na kakani-kayi! Wata zuciyarsa ta kawo shawarar ya kai ta asibiti a yi mata (family planning), da gaggawa wata zuciyar ta hana ta hanyar cewa, hakan zalunci ne, babban zalunci!!! Ba ta taba haihuwa ba, idan ka lalata mata mahaifa sannan ka sake ta, Allah ba zai barka ba! 

Cikin halin da ya kwana kenan, ya rasa inda zai sa Www.bankinhausanovels.com.ng kansa. Duk shawarar da ya kama in ya zurfafa tunani, sai ya ga ba mafita ba ce. Mafitar guda biyu ce; ya sa mata ido ta koma a yadda ta zo. Ya auro Mu’azatu su shimfida ingantacciyar rayuwa mai ma’ana da soyayya mara yankewa. Ko kuma, ya maida Hafsat cikakkiyar matarsa, amma babu rabuwa, kuma babu Mu’azatu… !!! Sosai yake girgiza kai in resentment ….. “zan iya jure komi in dai zan same ki Mu’azatu!!! Ya fada a fili cikin rashin sanin abin yi, da ciwon mara mai tsanani ya kwana. Bai taba ganin dare mai tsayin na yau ba a kafatanin rayuwarsa. Idan haka sauran watannin da suka rage musu za su kare, ashe ba zai kai su da sauran numfashi ba. 

Mataki biyu Abdul’ azeez ya dauka don kare auren kwangilar sa ya zauna lafiya ba tare da ya kara fadawa halin da ya samu kansa jiya ba. Na farko ya daina shiga dakin Hafsat, in ganin lafiyar tata ya zama dole, zai dinga jiranta a falo. Mataki na biyu, zai sai mata waya ya dinga kiranta yana jin lafiyar ta don rage kusanci na gani da ido a tsakaninsu. Zai ci gaba da kin dawowa gida sai ta kure. Rashin Mu’azatu ma ya taimaka wajen samun sararinsa da har wata mace za ta yi kokarin kutsowa cikin rayuwarsa. Mu’azatu ba ta barinsa haka nan ba sa tare, sai in yana bakin aiki, in tana gari suna tare, in ba sa gari daya koyaushe suna manne a waya. 

Don haka washegari Hafsat ba ta sanya Abdul’ azeez a idanunta ba ya fice ofis da sassafe. Da ya tashi office gidansu ya wuce, a can ya Ci abinci. Sai da Mammah ta ga karfe tara ta yi ba shi da niyyar komawa gida ta ce ya tashi ya tafi. A nan yake gaya wa Mammah zai saya wa Hafsat waya tunda ta ki zuwa gidansu, kuma ta hana shi kawo ta.Ta yi Www.bankinhausanovels.com.ng murmushi cikin ranta ta ce, Mu je zuwa… wai mahaukaci ya hau Kura”.A (Bannex) da ke Wuse 2 ya tsaya ya yi cinikin wata karamar (Iphone) ya saya da sunan Hafsat. Har jikin (receipt) Hafsat Dakata aka rubuta. Sanda ya iso gida ta dade da kulewa a daki. Ya so ya tadda ita a falon ya ba ta wayar, hakan bai 

yiwu ba. Ga shi kuma ya sa wa kansa takunkumin daina shiga dakinta. Sai washegari zai fita ita kuma ta fito daga kicin suka hada ido, rabon da ta ganshi tun shekaranjiya. Shi ya fara dauke idonsa, zuciyarsa na harbawa. Akwai wani maganadisu mai kama da magnet a cikin kwayar idanunta, wanda duk lokacin da ya yi kuskuren hada ido da ita sai ya ji shi a jikinsa. Neman kujera ya yi ya zauna, ya dafe kansa ya kasa ce mata komai. A sanyaye ta zagaye kujerar bayansa, ta zagayo ta tsugunna a gabansa, ta ce. 

Good morning”. Da ka ya amsa, ta hanyar daga kansa da ke cikin hannayensa, amma ba ta yi nasarar samun kallo daga gare shi ba. Inda sabo ya ci a ce ta saba, don haka ba ta wani damu ba ta mike za ta wuce. A sanyaye ya cira kai daga cikin hannayensa ya ce, “Hafsah?” Dakatawa ta yi ba tare da ta juyo ba. Cikin mamakin wai ashe yana sane da sunanta? “Dauki wayar nan taki ce”. Dawowa ta yi ta dauki wayar ta duba, sai kuma ta mayar ta ajiye ta a inda ta dauke ta tana girgiza kai. “Ba abin da zan yi da ita Yaya Azeez”. Cikin mamaki ya ce, “Ba za ki dinga kiran Mamanki ba? Ni ma zan dinga kiranki in ina office”. 

Ga mamakinsa, sai hawaye suka balle mata. Ta ya ya za ta gaya masa cewa, mahaifiyarsa ta daina sonta? Tunda ta kawo ta nan ta aje yau kusan watanni hudu ba ta kara waiwayarta ba. Sai ta mike kawai tana share hawaye ta nufi dakinta. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Haushi, takaici, mamaki su suka taru suka rufe Abdul’azeez. Bai san lokacin da ya bi ta dakin ba a fusace. Tana zaune a kujerar gaban mirrow ta kifa kanta a kan madubinta tana kuka. Hannunta ya fizga ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna. Kafadunta biyu ya rike ya girgiza ta. Na yi kama da sa’anki Haleem da za ki dinga kawo min raini?” 

Ta fiddo jajayen idanunta tana dubansa cikin firgici. 

Ya sassauta rikon da ya yi mata ganin ta tsorata sosai yadda yake so, ya ja hannunta ya zaunar da ita a gefen gado, ya ci gaba da tsayuwa a kanta. Muryarsa akwai sassauci a sa’ilin da yake cewa. 

“Jiya na yi miki abin arziki na ba ki ‘system’ dina, ki ka saka min da rashin kunya. Ban daddara ba yau na sake yi miki abin arziki na sayo miki waya don ki dinga magana da Mamanki da ‘yan uwanki, nima in dinga jin lafiyarki, in daina tunanin na jima a office ban san halin da ki ke ciki ba, shi ne za ki yi min rashin kunya ‘again’ wai ba kya so?” 

Cikin girgiza kai hawaye na ci gaba da fita ta ce, “Ba rashin kunya ba ne. Yanzu misali in ba ka ‘system’ dina, kana kunnawa ka ga hoton namiji ya ya za ka ji? Waya kuma abin da ya sa na ce maka bana bukatarta saboda da ma don Mammah nake sonta, kuma Mammah ta dade da mantawa da ni, ta daina sona… tunda ta kawo ni gidannan ba ta kara nemana ba alhalin ta san ba ni da kowa sai ita…” ta zame daga tsayuwar ta koma kan stool din ta zauna. Ta kifa kanta cikin cinyoyinta, ta ci gaba da kuka sosai mai taba zuciya. Hannun Abdul’azeez ta ji a saman kafadunta ya cira ta tsaye, kokari yake ya raba tafukan hannayenta da fuskarta, amma ta ki bari. Ya ce, “‘Suhaanah, in kin yarda ni Yayanki ne Azeez, kamar yadda ki ka fada dazu, ki dube ni…..” 

Sosai ta rage kukan domin abin da bata taba zata bane daga gareshi. Hannunsa ya kai habarta ya dago fuskarta daidai tashi, ya shiga share mata hawayen da yatsun hannunshi. Runtse idanunta ta yi sakamakon jin wani sabon al’amari na bin illahirin gangar jikinta. “Bude idonki Hafsah ki dube ni, magana za muyi”. A hankali ta ke bude idon, amma ta kasa bude su gaba daya ta dube shi cikin ido, kamar yadda yake nufi. Yana da wani irin girma na Www.bankinhausanovels.com.ng musamman a idanunta ba tun yau ba. Burinta ya daina kai hannu saman fuskarta don haka ta bude idon. Janta ya yi suka zauna a gefen gadonta yana kallon agogo, da mamaki yau shi ne har karfe tara na safe a gida saboda diyar Mammah. Sai da ya ga ta nutsu sosai, sannan cikin tattausar murya ya ce, “Ashe mutum yana fushi da iyayensa Hafsat?” Kai ta girgiza masa. “Amma ke ki ke fushi da Mamanki?” Sunkuyar da kai ta yi tana kallon yatsun kafarta. Mikewa ya yi ya koma falo, ya dauko wayar ya dawo ya dora mata a saman cinyarta, “C’mmon, call your Mammah….” Ta dago ta dube shi kamar za ta ce, a’ah, ya tsare gida sosai. Ya sanya layin ‘etisalat’ a ciki yayi ‘charging’ wayar sosai. Kamar yadda ta haddace karatun sallahr farillarta, haka ta haddace lambobin uwarta da na Baba Azumi. Da sauri ta shigar da lambobin ta kasa danna ‘call’ amma don ba ta san karbar da Mammah za ta yi wa kiran nata ba, sai gani ta yi Abdul’azeez ya danna mata. Runtse idanunta ta yi lokacin da kiran ya shiga kafin ta ji tattausar muryar Hajiya Maryam na fadin, 

Assalamu alaikum”. Wasu tawagar hawayen dadi suka sauko mata, ta kasa amsawa. Daga can bangaren Mammah ta ji shiru, ta ce “wa ke magana ne?” 

Bude idonta ta yi suka sauka cikin na Abdul’ azeez, ya daga mata gira cikin karfafawa. Muryarta ta yi rauni sosai, ta ce, “Mommah!”. Sai kuka. Duk duniya babu mai kiranta haka sai Addar ta, murmushi ta yi, ta ce, “At last ya sayi wayar?” 

Abdul’ azeez juyawa ya yi ya fita don ya basu dama suyi maganarsu, ya dauki jakar system , wig da gown dinsa ya bar gidan yana mamakin irin wannan soyayya da ke tsakanin mahaifiyarsa da Suhaana. Zai iya rantsuwa shi bai samu rabinrabinta ba. Ya ya za ta ji ranar da ya dawo mata da Suhaanah da takardar saki? Zuciyarsa ya ji ta birkice, kwakwalwarsa ta hautsine ta daina aiki na wucin gadi. Sai dai wani bangare na zuciyarsa na gaya masa no matter what ba zai iya jure Www.bankinhausanovels.com.ng 

rashin Mu’azatu ba. Uwarsa ce, dole watarana za ta yafe masa ko min fushin da zata yi. Kuma zai san yadda ya yi Suhaanah ta wanke shi tunda ita 

ce (apple of her eyes), his love to Mu’ azatu is estimable, and hence; inevitable. Tunda ya yi biyayya ya yi abin da suke so, shi ma sai a ba shi hakkinsa. Fisabilillahi ya yi kokari da ya kawo wannan lokacin bai mallaki abar sonsa ba. Amma a kwanakin nan sosai yake jin tausayin Hafsah ‘image’ dinta kuma na yawan gilmawa a idanunsa. Ya kara samun kwarin gwiwar son taimakon rayuwarta ta kowanne fanni. 

Mammah da ‘yarta a waya ana shan hira. 

“Tunda ya yi hankalin saya miki wayar alhamdu lillahi. Na sa masa ido ne ai in ga kamun ludayinsa. Wa’adin da na diba na zuwa gidanku ya kusa cika ai ko ba ki kira ba Addah…..” 

“Amma Mommah wata hudu… babu ke babu Daddy ko Baba Azumi, babu ko su Haleem? Mommah me na yi miki da zafi haka? Kada ki sa in ci gaba da yarda da kaina cewa; kin daina sona…”. Sai kuka. 

Murmushi Hajiya Maryam ta yi, irin murmushin nan na UWA ma’abociyar kawaici da yakanah. 

“Me ya yi zafi na wannan kukan Addah? Ashe uwa na daina son danta? Akwai dalilai da yawa da suka sanya babu wayata kuma babu kafata a gidanku. Amma tunda kin dauka haka da zafi, zan gaya miki wasu don in wanke kaina daga wannan zargin naki Addah. 

Aurenku ba aure ne na soyayya irin sauran aurarraki ba. Ina da karfin iko a cikinsa, wanda in na Sa za’a yi, in na hana za’a bari. Bana son wannan karfin ikon nawa ya ci gaba da tasiri a cikinsa. So nake ku shaku da juna, ku so junanku 

ba tare da sa hannuna ba. Idan na zo na ganki cikin wani hali, ko ki ka gaya min wani abu wanda zuciyata ba ta gamsu da shi ba, ba zan jure ba sai na murza wannan kambun nawa. Ki fahimce ni Addah, bana son ji ko ganin komai da ya shafe ku ba so da kaunar junanku ba. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kuma na fara samun abin da nake so alhamdulillah. A jiya na fahimta. Duk da haka kuna bukatar karin ‘lokaci’ ki gafarce ni, ki kara min watanni biyu a gaba kafin in tako kafafuna gidanku. Amma daga yanzu na amince ki kira ni duk yadda ki ke so, ko sau dari ne a rana”’. Dariya ta yi, dadi har cikin ranta. Duk da in Hausa mai tsauri ce ba ta fahimtarta. Yanzun ma ba ta fahimci wani muhimmin abu cikin zantukan Mamarta ba. Ta dai fahimci ba daina sonta ta yi ba, tana da dalilinta na rashin zuwan da rashin kiran. Tana so sai sun shirya sun saba da juna sun kaunaci juna don kansu. Tausayin Hajiya Maryam ya tsirga a zuciyarta, shin ya ya za ta ji ranar da ta fahimci duk wannan hakilon nata a tutar babu zai tashi? Abdul’azeez ba fara sonta zai yi ba? Kuma ba zai taba son nata ba, yana da wadda zuciyarsa ta riga ta mutu ta rube a kanta? 

Hawayen tausayin Mammah suka zubo mata, don ta kawar da tunanin da ya addabi zuciyarta Sai ta ce, 

Mommah ya cike min JAMB”. Fassara farin cikin zuciyar Hajiya Maryam ba zai rubutu ba, “Na ji dadi sosai Addah, wane ‘course’ ya sa maki?” Ban sani ba Mommah, kuma ba ni da zabi. Na 

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *