DR MUHSEEN CHAPTER 5 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝………………..A cikin hijaf dinta Yana neman tugemata gashi,cikin zafin nama Faruk ya rike hannun shi Yana yimashi alamar yi hakuri da ido.
“Sorry sir Sojan mu”cewar Jabeer da yake matsowa kusa da su.ita dai Seeyerma har zuwa wannan lokacin tana jikin Faruk tayi lamo tana faman raba idanu saboda tsabar kaduwa da diyan cikinta sukayi ji take kaman zata saki fitsari.
A hankali ya cire hannun shi daga saman gashinta,Daman ko hula bata saka ba,sai daure shi da tayi da rebom.
A hankali ta Kara sauke ajiyar zuciya jin yadda kanta yake wani zogi kaman ta ji rauni a wurin.Duk abinda suke yi Kaka tana kallon su,Amma bata tanka su ba.
Tsam Faruk ya mikar da ita tsaye suka nufi hanyar fita daga falon.kaka bata hanasu ba sai binsu tayi da ido har suka fice daga falon.
Cikin gajiya da jin bacci Muhseen ya zauna saman doguwar kujera Yana lumshe idon shi,saboda wani zafi da ya ji suna yimai.
Duban Kaka yayi ganin taki cewa komai yasa shima yayi shiru Yana faman danna wayar shi.
Jabeer ne ya mike yana ce “yaya zan je wurin Aliyu,sakon dinkunan nan zamu anso”.
“To”kawai ya ce ba tare daya dago kansa ba Yana cigaba da danna wayar sa.
Bayan ficewar Jabeer Kaka ta kurbi tea din da yake cikin cup a gabanta tana Kara kallon jikan nata.
A ranta ta ce “miskili kafi mahaukaci ban haushi”
A hankali ta jiyo muryar shi ya ce “granni ki bani hura na Sha,banyi break ba”.steal kanshi na bisa screen din wayar shi.
Shiru tayi kaman bata ji meya ce ba.tana kokarin danna remote dan kamo tashar Sunna tv.
Cikin mutuwar jiki ya mike,bakin freaged din ya nufa,hurar ya dauko ya dawo mazaunin shi.cikin karamin cup ya tsiyaya kafin ya fara kurba Yana latsa waya ga dukkan alamu chat ne yake yi.
Seeyerma tunda Suka fita ta sakama Yaya Faruk kuka,ita kanta ciwo yake kaman zai fita,haka yayi ta faman rarrashinta har suka karaso part din Uncle Yusuf.A falon suka riski Aunty Hajara tana goge-goge.ganin yadda suka shigo tana aikin kuka yasa ta nufo su tana tambayar “Kai Faruk lafiya meya faru haka?ko wani ne ba lafiya?”.
Saida ya kontar da ita kafin ya labarta Mata abinda ya faru.
Batayi mamaki ba,Dan tasan ada can ma idan suka hadu to sai ya ce ga laifin da tayi masa.basa jituwa,musamman yadda shi Faruk ya Kara shagawabata.dan Seeyerma akwai tilin tsiwa da rashin ji.
Tayar da ita zaune tayi bayan ta ciremata hijaf din ta fara duba kanta dan ganin ko yayimata rauni.da sauri na zaro idona 😳 saboda tsabar kaduwa da nayi ganin yarinya karama da wannan uban gashin irin na larabawa,Kai Allah yayi halitta anan.
Sosai Aunty Hajara ta duba Amma babu wani rauni a wurin,kawai tana jin zafi ne saboda an taba Kan ne.
“Ai Kinga maganin Wanda baya son kitso kenan,ka ganta nan ko jiya saida nayi fama da ita akan ta tsaya nayi mata Koda kalaba ne,Amma ta kiya”cewar Aunty Hajara tana Kai dubanta inda Faruk yake tsaye.
Murmushi yayi Yana kallon yadda Seeyerma take faman runtse ido,saboda ita a rayuwarta ta tsani ta ji an taba kanta,wannan ne yasa ko kitso bata yadda ayimata.
Ficewa yayi daga falon Yana cewa “Anjima da yamma ki shirya zamu je cikin gari a anso dinkunan ku”
Can kasan makoshinta ta amsa da “to”tana mayar da kanta bisa jikin fillon kujerar .shiko tuni ya fice daga part din.itama Aunty Hajara cigaba tayi da aiyyukanta.
Dr muhseen tun bayan daya karasa shan hurar,ganin Kaka taki kulashi yasa ya shige dakinta yayi konciyar shi.ko jakar kayan shi tana cikin mota ya baro ta.
A Sudan kuwa Lalaih ce take faman kuka Ummeey sai aikin rarrashinta take yi,Amma fir yarinyar taki ta tsagaita kukan da take yi.
Cikin harshen Larabci take cema yarinyar “kiyi hakuri Lailah nafi tunanin yayan naki bacci yake yi,nasan idan har yaga Kiran bazai ki dauka ba,Bari muga zuwa jimawa idan lokacin salla yayi nasan zai tashi”da haka tayi ta rarrashin yarinyar hardai ta samu tayi bacci.kafin ta gyara mata konciyarta kafin itama ta fice daga dakin,a ranta tana tunanin meya hana son picking call dinta.
Cikin wannan tunanin taci gaba da ayyukanta,tana addu’ar Allah yasa ba wani abun ne ya samu Seeyerma ba.
Dr muhseen kuwa tun baccin daya dauke shi a Kan gadon na Kaka,shi ne bai farka ba sai karfe daya saura,kasantuwar ranar juma’a ne har an fara Kiran sallar farko a masallacin cikin estate din nasu.
Da addu’a a bakin shi ya sauko daga saman gadon.wayar shi ya dauka da take saman karamar drower dake gefen gadon.
Ganin irin miscall din da aka yimashi yasa ya fara dubawa.dana Ummeeyn shi ya fara cin karo har kusan sau shida ta Kira shi.cikin azama ya fara kiranta.jin ta daga yasaka shi sauke ajiyar zuciya cikin yaren larabci ya ce “afuwan Ummeey lokacin da kika Kira Ina bacci,Kuma yanzu lokacin salla yayi,Amma da zaran na dawo zan Kira”
Cikin farincin jin muryar dan nata ta amsa Da “to saika dawo,Daman Lailah ce take son yin magana da Seeyerma,shi ne da ta ji baka daga ba tayi ta faman kuka kafin tayi bacci”
“Allah sarki kanwata tayi hakuri da zarar na dawo zan hadata da ita”
Cewar muhseen.
Da haka ya katse Kiran.
Cikin sauri ya fito ganin Kaka bata nan ya wuce part din shi dan yayi shirin zuwa masallaci.
Karfe daya da mintuna samarin da yan’mata,manya da yara,da dattawa suka fara fitowa daga gidajen su Dan zuwa masallaci,cikin shirin su na sallar juma’a.
Kasancewar akwai tazara tsakanin gidajen su da estate din saboda shi Yana ta kusa da islamiyya cikin gate na farko kenan.shiyasa wasun su suke hawa motoci wasu ko mashin din roba-roba ne.
Manyan ne sukafi takowa a kafa,kama daga iyaye maza da Mata.
Dakyar Seeyerma ta yadda ta shirya suka nufi masallaci ita da Aunty Hajara.dan Uncle Yusuf tuni sunyi gaba shida su Uncle Muhammad,da Uncle Ahmed da sauran yan’uwan shi.kasancewar basa hawa mota sukan taka da kafar su.
Haka Suma su Faruk,Jabeer,Aliyu,da sauran samarin gidan Wanda akalla yawan su ya haura goma Suka nufi masallacin.
Bayan ficewar su da kadan Suma yan’matan suka taho cikin Shirin Kamala,da manyan hijaf din su har kasa.
Layin su Ameerah ne a gaba ita da Safna,Hindatu,Zeenat,sai Rukayya a gefen barin Daman su.
Layin bayansu kuwa su Halimatu ne da Fatima,khadija sai Ameenatu.tunda suka taho ba wacce tayi magana.
Wasu casbaha suke ja, wasun su kuwa waya suka faman latsawa.
Daga bayan su Aunty Hajara ce ita da Seeyerma.tafe suke suna hailala da salati tare da addu’o’i yayin zuwa masallaci.
Dr muhseen shi ne karshen fitowa daga gida.ganin lokaci Yana Kara tafiya yasa ya doshi parking lot dan shiga mota.wooooooooo Masha Allah shi ne kalmar dana furta lokacin dana ga wannan kyakkyawar halittar, tamkar Balarabe sak haka ya koma,saboda irin shigar da yayi.ta fito da ainahin surar shi ta cikakun Larabawa.farar Jallabiya ce ya saka mai dogon hannu da links.kasancewar shi fari yasa ta kara haska fatar jikin shi.sai farin hirami daya dora saman kanshi da bakin abu irin na larabawa mai kyau anyi dinkin shi da golding din zare a saman hiramin,black din takalmi ne ya saka plant ne irin Mai gidan yatsa din nan.turaren Arabian uhd ne ya fesa sai tashin kanshi yake yi.sosai na ware idona akan shi ganin yadda kamanin shi da Seeyerma suka Kara bayyana karara.saidai ya fita cikar fuska kasancewar shi ne babba.ikon Allah yau ga Balarabe a kasar Hausa 🤔.
Cikin takunshi mai cike da natsuwa ya fara takawa zuwa inda ake ajiye motoci.saida yayi addu’a kafin ya shiga.
A slow ya fara tukin masu gadin gate din suka wangale mai gate ya fito.
Tun daga nesa yake hango masu tafiya zuwa masallacin.maza da mata.wanda mafi yawan su duk suna da ababen hawa,saidai suna ra’ayin tafiyar kasa ne.
Harta dan gota kadan yaga Aunty Hajara ta ruko hannunta suna tafiya.
A hankali yayi rebas Yana dawowa baya.ta saitin su ya tsaya kafin ya sauke gilass din ta dayan site ba tare da tayi magana ba.
Itako Sarai ta gane shi.saida suka zo saitin shi ganin Aunty Hajara na kokarin tsayawa yasa ta kwace hannunta tayi saurin yin gaba.dan ita kam bata ra’ayin sake ganin fuskar wannan dan barikin.
Har saida Aunty Hajara ta shiga bayan motar kafin ta ankare da basa tare da Seeyerma.
Shima bai damuba ganin yadda ta wuce ya ja Motar shi yayi gaba.
Da haka duk suka hallara a cikin masallacin.kasancewar bangaren maza da ban,na Mata da ban.hakan yasa akwai shinge a tsakanin su.har suka idar da sallar jam’in Aunty Hajara bata ce da ita komai ba.bayan huduba mai ratsa jiki da suka Sha.
A ka’ida idan an idar da salla akwai gaishe-gaishe da ake yi.kafin kowa ya wuce gidan shi.yauma hakan ce ta kasance ita dai Seeyerma har gajiya tayi ga yunwa ta fara ji.cikin wurga ido irin na marassa gaskiya ta kamo hannun Khadija tana cewa ke zo mu tafi nidai wallahi na gaji.
Gaba sukayi suna taba hira.kafin sukaga suma sauran sun taho.
Yan’mata da samarin kuwa direct part din Mama Suka yima cinke.anan akayi ta fito da abinci kowa ya fara ci.
Sai a lokacin Seeyerma da khadija Suka shigo.ganin kowa ya kama abinci yasa tayi saurin cire hijaf dinta tana cewa “ni ku matsaman na zauna”tana ture fatima.
Sanin masifarta yasa tayi saurin matsa mata ta saka cokalinta.
Duk sunyi shiru baka jin karan komai saina cokulla.bayan sun idar suka kora da lemuka masu sanyi.
Hindatu ce ta kalle su one by one ta saka dariya tana cewa “ka ji yan’samari anji girki mai dadi kowa yayi mit sai kwasar gara ake yi” tana kallon su Jabeer da suke gefe daya suna cin abinci.
Cikin daka tsawa ya Faruk ya ce “idan baki rufemana baki ba,wallahi yanzu Zaki ci na jaki”tun kafin ya rufe bakin shi ta mike tsam ta wuce dakin su tana faman gimtse dariyar da take son kufcemata.
Bayan sun idar da cin abincin wasu fita sukayi,wasunsu ko hira suka ci gab da yi akan yadda family meeting din su zai kasance a gobe Asabar.
*WASHE GARI*
A washe garin Asabar da misalin karfe hudu da rabi na yamma holl din ya fara samun halartar mutanen cikin estate din.
Tuni an kawo kayan abinci da abin sha,kama daga flate da cokulla,sai lemuka masu sanyi.a fannin abinci kuwa kusan kala akwai aka kawo,sai Wanda mutum ya zaba kafin zai ci,mayan su suka fara halartar wurin sai iyaye Mata da kananun yara.Amma cikin yan’matan ba wacce ta fito,haka suma samarin sai Aliyu da Jabeer da suke ta faman shigo da kaya.holl din ya tsaru sosai kowane set Yana dauke da kujeru masu kyau anyima wurin kwalliya da filawowi tamkar za’a gabatar da wani kamu a wurin.
Sit din da su Uncle Yusuf suke Jabeer ya nufa a hankali yadan duko Yana gaishe su ya ce “Uncle a Kara yimana hakuri gasunan fitowa”cewar Jabeer.
Cikin jin haushi Uncle Ahmed ya dube shi Yana cewa “wallahi ka fadama su Faruk da Muhseen ransu zai baci,su wadancan idan yan’mata ne sun tsaya kwalliya to su me Suka tsaya yi ne?to tunda ku kuka haife mu dole muke tsayawa zaman jiran ku” ya Kai karshen zancen Yana mai jin haushin yadda yaran suke neman bata masu lokaci.
Shidai Jabeer hakuri yake ta Basu kafin ya fito farfajiyar holl din.
Wayar shi ya ciro daga cikin ajjihun gaban rigar sa.Faruk ya fara Kira bayan ya sanar mai da sakon Uncle Ahmed,kafin ya Kira Hindatu kasancewar ita ce babba a cikin yanmatab.dan tun jiya iyalan Uncle Mustapha suka iso daga Abuja,kasantuwar acan yake hada-hadar kasuwancin sa.
Cikin rige-rige yan’matan suke kokarin shiryawa tun bayan sunji sakon Uncle Ahmed Dan sunsan halin Shi mafadaci ne na gaske idan kayi da wasa tuni yake dukan ka.
Duk wannan saurin da suke yi sai a lokacin Seeyerma ta shiga wanka.ta Jima a toilet din kafin ta fito.zuwa lokacin wasun su har sun karasa shiryawa cikin ankon shadda gizna kalar pink dinkin dogayen riguna.sosai shaddar ta anshi jikin su,hasken su da kyawunsu ya kara bayyana.
“Dan Allah Khadija ki tsayani mu tafi tare,kingafa da nisa”cewar Seeyerma tana marairaice murya.
Da sauri Khadija ta ce “cab lalaima Seeyerma kina ji ance Uncle Ahmed Yana ta fada munki hitowa da wuri,sannan ki rinka batun Wai na tsaya ki,wallahi bazan tsaya ba kingama tafiyata”tayi saurin ficewa daga dakin.
Saboda wani takaici daya kama Seeyerma kasa cewa komai tayi,sai cigaba tayi da murza mai a fatar jikinta.itama Ameerah ficewa tayi bayan ta rataya jakarta a kafada.wurin parking lot suka nufa,haka Jabeer da Aliyu sukayi ta faman kwasar yan’matan suna diresu a bakin holl din.saida suka kaisu tas kafin Suka shiga.shidai Jabeer baiga Seeyerma ba Amma ba Wanda ya tambaya dan yasan halin rigimarta kila bazata zo ba.
Cikin takun shi mai cike da kwarjini da haiba Dr muhseen ya nufi wurin daya ajiye motar shi,wata hadadiyar gizna ce a jikinshi kalar blue ko hula bai saka ba sai faman zuba kanshi yake yi, tsintsiyar hannun shi daure da agogon kamfanin Gucci mai tsada yatsunshi duk ya jera zobunan gold a azurfa,cover sheus ne a Baki a kafar shi,harya kama murfin zai bude kome ya tuna ya mayar da ita ya rufe.part din Mama ya nufa.a can kasan makoshin shi yayi sallama.jin ba kowa a falon yasa ya fara dan zagaye falon.ji yayi kaman motsi ta cikin dakin dake passing din shi.dan haka ya nufi dakin.cikkin sanda ya buda labulen dan ganin koma waye yaki tafiya wurin taron.
A lokacin Seeyerma ta juya baya kokarin dauke kanta take yi Amma ta kasa saboda santsi da tsawon shi.ga towel din dake daure jikinta sai faman zamewa yake yi tana mayar da shi.cikin gajiyawa da jin haushi ta sauke hannunta tayi cilli da bant din tana mayar da numfashi,ga makara tayi dan yanzu tuni tasan an fara gabatar da taron.duk abinda take yi Yana kallonta.saida ya tabbatar daya rufe kofar kafin ya fara taku cikin kasaita zuwa inda take.ita dai ko motsin shigowar mutum bata ji ba,sai ji tayi anyakice towel din dake daure a kirjinta.cikin tsoro,fargaba,tashin hankali,da tsinkewar zuciya tayi kokarin juyowa dan ganin kowace Yar iskace zata yimata haka,Dan bata kawo a ranta namiji zai shigo dakin ba.nunashi ta farayi da hannun cikin tsoron abinda zai yimata ta fara alamar motsa bakinta zatace wani abu taji wufffffff ya tura b…..Wufffffff yayi saurin tura halshen shi cikin dan karamin bakinta,sosai Dr muhseen yake bata wani mahaukacin hot kiss Wanda ya kusan tafiya da numfashin Seeyerma,sosai wannan lamarin nashi ya fara bata tsoro,lallai yau ta kara tabbatar ma kanta ya Muhseen cikakken dan bariki ne.
Cikin lokaci kalilan jikin Seeyerma ya dauki karkarwa jin kafafuwanta sunyi sanyi tana neman zubewa kasa yasa ta fara kokarin tureshi daga mugun rikon da yayimata,Amma abinda ya Kara tsorata ta ganin ko alamar motsawa baiyi ba,saima Kara yimata wani kyakyawan riko ya yi jin tana neman zamewa daga jikin shi.
Cikin jin haushi Seeyerma ta lalubo harshen shi bai tantance ba jin ya Lula wata duniya ta daban wadda tasa yake neman mantawa da wacce yake tare.
Da sauri ya tureta jin ta gantsara mai cizo a harshe.tangal-tangal yayi zau zube yayi saurin dafa jikin mirror Yana mayar da numfashi.Ji yake gaba daya jijiyoyin jikin shi sun saki.Seeyerma kuwa da sauri ta janyo towel dinta gefen gadon,cikin sauri ta daura ta shige bayi ji kake gammmmm ta sakama kofar toilet din key.
Sai a sannan ya ankare da Bata a wurin.bakin kofar ya nufa jin wata muguwar hajijiya tana kwasar shi.da sauri ya dafe marar shi jin ta wani juyamai da karfi Yana sakin wani dan marayan kara.
Bakin kofar ya jingina Yana dafe da marar shi.cikin fisgar numfashin wahala ya bude bakin shi dakyar ya ce “please kiyi sauri ki shirya Ina jiranki a Mota”da sauri ya juya jin numfashin shi na neman daukewa.
Tunda ya zauna cikin motar ya kontar da kanshi saman sitiaring Yana jin kaman marar shi zata tsinke saboda azabar kullewa da tayi,sosai yake mukurkusu a wurin,sai sunan Allah yake ambata can kasan makoshin shi,saboda muryar shi ko fita bata yi sosai.
Tunda taji alamar ya fice daga cikin dakin ta sulale nan kasa jikin kofar tana fashewa da wani marayan kuka mai ciwo da cin rai sosai take kukan kafin ta mike ta nufi cikin bahon wankan tunawa da tayi ga inda zata je.sosai tayi wankan tana Kara wanke bakinta saboda ji take kaman yanzu ne ya saka bakin shi cikin nata.
Bayan ta fito cikin nutsuwa ta shirya dukda haryanzu rabin tunaninta ya tafi ga taron da ake gudanarwa.
Sosai Holl din ya cika da mutanen familyn,kowane set dauke yake da mutane zaune bisa kujeru.an aje lemuka da ruwa,duk sunyi tsit suna sauraren Uncle Yusuf da yake koro bayani bayan sun gabatar da Addu’ar bude taro.
Kamar yadda kuka sani muna gudanar da wannan taro duk bayan wata ukku to yauma Allah ya zagayo da mu wannan rana,Muna yima kowa barka da zuwa.sannan kafin mu fara gabatar da tsare-tsaren wannan estate zamu baku dama ga duk Wanda yasan Yana da wani korafi to yayi jawabi kafin mu dora sauran bayani”bayan ya idar da bayanin ya dawo da kallon shi ga Uncle Ahmed cikin yin kasa da murya ya ce “Yaya nifa banga Muhseen ba,yauma kadafa ace bazai zo ba”
Cikin jin haushi Uncle Ahmed ya ciro wayan shi daga cikin ajjihu ya fara kokarin Kiran nomber Dr muhseen.
Shiko muhseen sai a lokacin yaji nutsuwar shi ta fara dawowa jikin shi.da sauri ya mike zaune jin karan wayan shi.
Dafe kanshi yayi da hannu ganin sunan Uncle Ahmed akan screen din wayar.a fili ya furta “Yasalam wato shidai bazai barni na huta ba”aje wayar yayi ya bude murfin motar ya fito.Daidai itama Seeyerma ta fito daga cikin gidan hangota yasa ya dakata Yana Kara jingina jikin motar.sosai ya kafeta da manyan idon shi ganin yadda take takunta cikin sanyi da kasala.bata lura da irin kallon da yake yimata ba saboda yadda take ta kokarin daura agogo a hannunta amma ta kasa.
Saida ta zo gab da jikin motar kafin ta samu agogon ya dauru.tana dago da kanta karaf idon shi cikin nata.murguda baki tayi cikin kasa da murya ta ce “Allah ya isa mugu Dan bariki”zaro idon shi yayi Yana Kara kuramata ido jin abinda tace,bayyi mamaki ba Dan daman tasaba fada a bayan idon shi.
“Me kikace”haka ta tsinci muryar shi.
Shiru tayi tana Kara yin kasa da kanta.
Shima bai Kara cewa komai ba ya juya ya shiga motar.
Tsuru tayi a tsaye tana so taki shiga,Amma tana tunanin nisan wurin ga takalmin data saka masu tsini ne dakyar take tafiyar.
Cikin dakiya ta zagaya zata bude murfin motar taji shi gam a rufe.dolenta ta shiga gaban motar.
Ko kallonta bayyi ba ya tayar da motar da gudu suka fice daga wurin suka nufi hanyar Holl din.
Cikin takaici Uncle Ahmed ya aje wayar Yana kallon kanen nashi ya ce “Hmmm ai na fadamaku wannan yaron ya rainamu,baya da lokacin daukar wayarmu,ka fito da takadda a sanar da su sakon Hajiya Kaka tunda haka Suka zaba,ban………….
Hango shigowar su cikin Holl din Yana rike da hannun Seeyerma shiya saka Uncle Ahmed yin shiru Yana kallon ikon Allah.
Kowa dake cikin Holl din hankalin su kacokam ya koma gunsu Dr muhseen da Seeyerma.Jerowa sukayi hannun shi na sarke cikin na juna sosai sukayi mugun kyau.giznar jikin shi dark blue ita Kuma pink,sai siririn mayafinta data aje shi a kafada.yar karama Jakarta kalar takalmin milk color.sosai suka haska.Daidai Ameerah ta dago kanta da zummar zata yima Hindatu magana. hangosu da tayi yasa tayi saurin mikewa tsaye.da sauri Hindatu ta zaunar da ita tana hararta.
“Banza ki zauna saikin kwafsa mana,ko kin manta abinda Hajiya tace Mana dazu?to ki nutsu kada ki jawomana abin kunya”cewar Hindatu tana harar Ameerah.
Har saida suka karaso tsakiyar dakin taron kafin ya saki hannunta ta nufi bangaren data hango yan’matan zaune.
Jabeer,Faruk,Aliyu da suke zaune wuri daya duk shiru sukayi ba Wanda ya ce kala cikin su.sai Faruk da yake faman danne zuciyar shi jin yadda take neman faso kirjinshi ta fito.
A hankali Muhseen ya zauna bisa kujerar da take kusa da Jabeer ba tare daya kalli kowa ba, Movement dinsu kawai yake tunawa da yarinyar nan,Wai shi meyasa daya rabu da wannan mai kama da aljanun sai yaji kaman zazzabi na neman rufeshi.Cikin sanyi yakai hannun shi jikin wuyan shi Yana tabawa,jin alamar zafi yasa yadan muskuda Yana kallon saman sitep din ganin irin harar da Uncle Ahmed yake jefomai.
Uncle Yusuf ne ya mike da laspicer Yana ci gaba da bayani.
Tunda Seeyerma ta zauna duk jinta take yi a wani takure,gani take yi kamar kowa yasan abinda wannan Dan barikin yayi mata.a hankali ta matsa kusa da Khadija tana tabota da hannu,ganin ta shareta yasa itama ta sunburi Baki ta kawar da kanta tana gunguni.
Cikin sauri ya mike tsaye da zummar ya fice daga cikin holl din,ganin Ummeey tana Kiran shi.
Daidai yakai bakin kofar fita ta cikin laspicer yaji Uncle ya ce
“Hajiya Kaka ta bayar da Umarnin Saka ranar Auren mutane ukku,gasu kamar haka,Faruk da Hindatu, Jabeer da Rukayya,sai Muhseen da ………………..?¹¹