KWASAR GANIMA CHAPTER 4 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN

KWASAR GANIMA CHAPTER 4 BY FAUZIYYAH D. SULAIMAN

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Lambar Gidan Gona

MUTUM ne shi mara son kula da iyalan sa. A kullum ya na tafe a duniya kamar tsuntsu. Abin ya kan dami matar sa. A lokacin da ta doshe shi da maganar sai ya kama yi mata masifa kamar zai cinye ta danya. Sai ta koma ita ce mai ba shi hakuri. Ranar wata Alhamis ya dawo daga wata tafiya da ya yi ta tsawon mako hudu. Matar da ’ya’yan su ka kama murna. Aka dinga kawo masa abinci kala-kala na saukar baKo.
Sai dai washegari da yamma ya kuma hada kayan sa zai koma. Hankalin Hajiya Maimuna ya tashi. Ta je kusa da shi ta kashe murya ta ce, “Alhaji, da ka yi haKuri ka bari zuwa ranar Litinin sai ka tafi, tunda ka ga makarantar yaran nan sun aiko da takarda ta taron iyayen yara, su na kuma kukan cewa kowa baban sa ya na zuwa amma nasu ba ya zuwa. Shi ya sa ma su ke ta murna da su ka ga ka dawo.”

Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya hade girar sama da ta Kasa, ya ce, “Saboda za a yi wani taron iyayen yara sai na fasa zuwa neman kudi na. Idan ba a samo kudin ba da me za a biya kudin karatun nasu? Ki gaya wa Auwalu ya raka su. Ga gudunmawa ta nan.” Ya mika mata kudi cikin madaurin su. Ta amsa jiki babu Kwari, don dai babu yadda za ta yi ne. Tana kallo ya nufi Kofa. Ta bi shi da sauri ta na fadin, “A dawo lafiya. Sai yaushe kuma za ka dawo?” “Da yake Chaina za ni kin san ina jimawa a can, amma ba zan wuce wata ba.”
Da haka su ka rabu, ta dawo gida. Abin duniya duk ya dame ta, amma yaya taiya da ran ta? Dole ta haKura. * Washegari da yamma, ta na zaune a babban falon ta na shaKatawa ta na hutawa sai ta dauki waya ta na wasa da ita. Sai ta ji zuciyar tana gaya mata ta buga waya gidan gonar Alhajin ta ji abin da za ta ce. Babu wani bata lokaci Www.bankinhausanovels.com.ng
sai ta kama kiran layin wayar. Cikin sa’a sai ga wayar ta na Kara: Kir! Kir! Kirrr! Zuwa can sai taji an daga ance, “Hello.” Sai ta yi shiru. Akace, “Wake magana?” Babu ko tantama muryar Alhaji ce. Cike da mamaki, ta ce, “Alhaji, kai ne da gaske?”
Ya na jin muryar matar sa sai gaban sa ya fadi. Shi kenan, yau asiri ya tonu! Amma sai ya maKe murya, ya ce, “Wannan lambar da ki ka kirawo ta gidan gona ta daina aiki na wucin gadi. Ki sake bugowa wani lokacin!” Wai shi a dole komfuta ce ta ke maganar. Sai da ya maimaita sau uku sannan ya kashe wayar.
Ita abin sai ya ba ta dariya ma. Lallai wannan mutumin wai ita zai raina wa hankali! Da daddare sai ga shi ya shigo gidan ya na wani mazurai.
Dariya ta kama ta, amma ta danne. Ta ce, “A’a, Alhaji har ka dawo, kai da ka ce Chaina za ka tafi?”
Ya kuma shan kunu ya ce, “Kin ga, kar ki raina mini wayo. Ba dazu ki ka kirawo wayar gidan gona ba har na yi miki wasa ba? Ai da gangan na ke. Ban samu tafiyar ba.” Ya na kaiwa nan sai ya shige dakin sa ya na mazurai. Abin ya kuma ba Hajiya Maimuna dariya. Ta girgiza kai, ta ce, ““Na gano lagon ka ai, mai lambar gidan gona!”

Me Ya Dace NaYi?

Adaidai lokacin da na kammala difiloma ne mu ka hadu da shi. Sadisu mutum ne mai gaskiya da nagarta, sai dai talauci ya hana shi cimma muradan rayuwar sa. Takalman roba ya ke sayarwa a Kofar Wambai.
Iyayen sa ma da shi su ka dogara; shi ke ciyar da su da Kannen sa uku.
Abu kamar wasa, soyyaya ta yi Karfi a tsakanin mu. Duk wanda ya san ni ya na mamakin yadda na ke son sa. Gidan mu ba masu kudi ba ne, amma ‘yan boko ne. Kowa ya na aikin sa; ni ma an samar mani aikin koyarwa a wata makarantar sakandire. Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokacin da na bayyana shi a gidan mu, Baba kadai ya ba ni goyan baya; su kuwa yayye na da mahaifiya ta mita su ka kama a kan me zan yi da shi, su ka ce matakin karatun sakandire ne da shi. Nace naji na gani. Da dan albashi na dinga ba shi ya na hada kayan lefe har aka yi biki. Babban wa na da ke aiki a Abuja ne ya ba mu aron gida mu ka zauna.
Mu na tarewa, abin da na ce ya fara shi ne komawa karatu. Da taimakon baba na ya samu gurbin karatun digiri a Jami’ar Bayero. Tun da ya fara karatu, sai zuawa kasuwa ya gagara, sai Kanin sa ke zuwa. Sai ya zamana abin da aka samu a kasuwa ana ci gaba da hidimar iyayen sa, ni kuma na dauki hidimar gida da ta karatun sa. Hatta kudin mota ni ke ba shi.
Mu na zaune zaman lafiya da kwanciyar hankali. Sau da da yawa jari sa ya na karyewa, ni ke kuma dorawa. Daga Karshe na saya masa irin babur din nan ‘Tsuntsun Soyayya.’ Kullum tare mu ke fita, ya sauke ni a wurin aiki na, ya wuce makaranta. A wannan lokacin na sami ciki, to kuma sai matsala ta kunno mana. * Ni ce na ga bai dace a ce mun fara tara yara a wannan halin da mu ke ci ba domin ina ga wahala za ta Karu. Shi kuma ya na da son haihuwa, don haka ya ce bai yarda na zubar masa da ciki ba. Wannan ne sabanin farko da mu ka fara samu. Amma daga Karshe dole sai da na haKura. *Ya’ya biyu na haifa, duk maza.
Mahaifi na ne ya yi hakika, yayin da ni kuma na yi duk hidimar komai, Abin da dai na guda ne ya faru, wato matsalar babu, tunda yara sun Karu, Kafin wata ya Kare sai mun shiga rance. A haka ya kammala karatun nasa, Mahaifina ya amshi takardun sa, ya bai wa wani tsohon abokin sa da magiya ya samar masa wani aiki a wurin shi a can Legas. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun yi farin ciki da samun aikin nan tunda akwai albashi mai kyau. Sai dai nisantar da za mu yi da juna ta fi damun mu. Haka ya fara aiki, mu ka fara fasowa. A lokacin da na kuma samun ciki, na haifi ’yan biyu, su ma maza, An sha shagali.
Sai dai daga tafiyar shi ta bayan haihuwar na fara shiga matsala. A da, mako biyu zuwa uku ko wata ya kan dawo, ga shi waya a kullum ya yi mani sau uku ko hudu. Amma a wannan karon sai da ya yi wata uku. Sai ya yi sati bai kira mu ba. Idan na kira shi kuma sai ya ce aiki ne ya yimasa yawa amma zai kira ni, ba kuma ya kiran nawa. ‘Dan aiken da ya ke mani ta banki ni da iyayen sa, ya daina.

*

Wata uku da kwanaki, ya zo garin. Ban yi zaton zan iya ko kallon sa ba, amma tsananin son da na ke masa ya sanya ni saurin saukowa, musamman bayan ya baibaye ni da dadin baki da karanto mani matsaloli. Lokacin da zai koma, ya cika mu da hidima ni da iyayen sa, abin da ya dan faranta mana rai. Sai dai tun da ya shura ya tafi tsawon wata uku hudu sau uku ya bugo waya ya neme mu. Hankali na ya tashi matuKa, musamman da na ji duk layukan wayar da na ke samun sa an daina amfani da su. Duk kafar da zan ji wani labarin sa babu, har aka yi wata shida.
Da na iske mahaifin sa da maganar sai ya ce in daina damun kai na, shaKiyanci ne ya sanya shi yin haka.
Ni da mahaifiyar sa mu ka gaza hakuri. Kullum mu na cikin fargaba. Lokacin da ya cika watanni tara haKuri na ya Kare, na hada kaya nana nufi Legas. Ban sanar wa da kowa ba bayan mahaifiyar sa tunda ita kadai ta gane halin da na ke ciki. Kowa ya na fadin in share shi kawai. Da na isa Ikko, ban sha wahalar samun kamfanin su ba tunda fitacce ne.
Ina zuwa, na sami shugaban kamfanin, na yi masa bayani. Bayan dogon bincike da su ka yi mani, su ka kwatanta mani gidan sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Babban gida ne, irin wanda ake kira da aljannar duniya. Sa’ilin da na isa, na sha binkice; da Kyar aka bar ni na shiga. Wani tangameman falo na fara shiga da sallama. Wani Katon hoto kamar girman wundo na fara cin karo da shi; an rubuta da manyan baki: MARIGANYIYA FATIMA. Na tsaya ina kallo cike da mamaki. A daidai lokacin, wata mata mai kimanin shekaru arba’in ta fito daga wata Kofa, hannun ta dauke da kwanon tangaran. Mu na hada ido sai ta saki kwanon a rude, ta kwasa da gudu ta na fadin, “Honey! Honey! Fatalwa!” Na tsaya a nan cike da tashin hankali, ina Kare wa hotunan su da su ka zagaye dakin kalilo. Babu ko tambaya, matar nan da ta kusa haihuwa matar sa ce. Daga can Kofar da ta shiga, na jiyo alamun tafiya an nufo falon. Na jiyo muryar sa ya na fadin, “Ke dai kawai kin tsorata ne. Aiko a da daki ka ji ana cewa an ga fatalwa, to aljanu ne ke rikidewa!”
Maganar ta tsaya cak a daidai lokacin da su ka iso falon mu ka yi ido hudu. Nan da nan jikin sa ya dauki rawa, ya fara hada gumi. Ganin haka ya sanya matar ta ce, “Ka gan ta ko? Wallahi fatalwa ce! Inna lillahi…” Ta fara tofa mani miyau, wai ita addu’a take yi. Ni kuwa wani bakin ciki ya tokare mani wuya, kai na sai juyawa ya ke yi kamar ana hajijiya da ni. Can na jiyo muryar sa ta na rawa, ya na cewa: “Fatima, ki yafe mani don Allah!” : Anan na yanke jikina fadi. * Sai farkawa na yi a gadon asibiti. Ina bude ido na, na yi arba da shi da matar nan da kallon ta ke tafasa mani zuciya. Fuskar Sadisu ta yi zuru-zuru. Kawai sai na fashe da kuka. Matar ce ta fara magana. Ki yi haKuri tunda son da ya ke mana ne ya sanya ke ya boye miki zai yi aure, yayin da ni kuma ya ce mini kin mutu. Haka Allah ya Kaddara mana…” Cikin ihu na katse ta da fadin, “Ki yi mini shiru malama!” Na juya gare shi tare da nuna robar da aka maKala mani a hannu, na ce a fusace: “Ka sanya a cire mini wannan abin na tafi gida! Ba ni fatan na Kara kallon mayaudariyar fuskar ka!”
Ya kama lallashi na, amma ban saurare shi ba. Na fincike ruwan, na mike ina tangadi. Ya kamo ni ya na magiya. Na fincike. Www.bankinhausanovels.com.ng
Fata na bai wuce in gan ni a gaban iyaye na ba, don aure ni da shi har abada. * Lokacin da iyayen sa da nawa su ka ji abin da ya faru, baKin ciki kamar ya kashe su. Amma su ka ce in rabu da shi.
Bayan kwana uku, ya biyo ni don hankalin sa ya kasa kwanciya. Sai dai garin tahowa a mota ya yi hatsari. Da aka gaya mana, mu ka nufi asibiti a tsorace. Mu ka tarar da shi a cikin mawuyacin hali; an yanke Kafafun sa saboda sun samu matsala. Da amarya ta ji labari, ta garzayo Kano a rude. A ranar da ta iso ta ce dole sai ya sake ta domin ba za ta iya ci gaba da zama da gurgu ba. Cikin ka kuma na zubar da shi tuni,” inji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *