DR SALEEM CHAPTER 3
Bayan tafiyan Alh tahir Alh suleiman yaje ya sanar da matarshi akan an tsaida ranan saleem da husna. matarshi kuwa bata nuna komai ba tace Allah ya sanya Alheri ya basu zaman lph. Amin yace. safiya kuwa bata san meke wakana ba sai data dawo daga yawanta sannan mamanta ke sanar da ita. ai zumbur ta mike tace whattt!!! wllhy bazaiyiwu ba sai dai muyi biyu babu. domin kuwa saleem nawa ne . wllhy Ammi shiyasa na tsaneta nake kishi da ita domin husna nada kyau. ninasan in dai har saleem yana ganinta a gidan nan toh wataran zaice yana sonta. kuma ma ammi bakowa bane zai kitsa wannan zancen sai mummy domin mummy ita zata hada su. dan dama ni ta tsaneni. Ammi tace ke kiyi kasa ksa da murya kafin wannan bakar dagan kakar taki taji mu. sai ta hau mana wa’azi. Ammi tace ki kwantar da hankalinki zamubi komai a sannu a hankali mu rabasu. Ai bawacce zata shiga gidan saleem in bakeba . yanzu kokari zakiyi ki jawo hankalinshi gareki kuma kar kiyadda wani ya gane cewa kinasonshi dan komai xamuyi shi cikin dabara da sirri ne. maryam ce ta katse su tace sirri ?meza’ayi cikin sirri. safiya tace ba’a sani ba banza sai son jin gulma. Ammi tace rabu da ita so take na tashi na hanbareta. maryam tace toh koma me za’a yi aji tsoron Allah domin kome mutum zaiyi Allah yana kallonshi . ammi wllhy banaso kuyi abinda zakuyi dana sani . Ammi tace danasanin kan ubanki” eyye nace dana sanin kan ubaki” kaga yar banza yarinya . ke wllhy daba a gida na haifeki ba zance chanji akai min dake . gaba daya kintsani farincikin mu . kedai baki da buri da yawuce ki faranta ma yan uwan babanki da wancan tsohuwar kakar taki dataki kwanta dama . haba Ammi” kika kuma magana Allah zanci ubanki. tace Allah ya baki hakuri. nusaiba tace hade da wucewa dakinta. tana tafiya safiya tace ai wllhy Ammi kibarni da yarinyar nan watarana sai na kusan ballata wata rana a gidan nan . Ammi tace bar shegiya muyi abinda ya damemu. nan sukaita kus kus . nusaiba najin shewarsa tace Allah ya shirya. ************** Bangaren saleem kuwa tunda aka sa rana hankalinshi a tashe yake domin yasan dole ya Auri husna koyana so ko bayaso domin zabin iyayanshi ne ba yadda zaiyi gashi husna wasan boyo takeyi dashi yanzu kwata kwata basa haduwa shikuma so yake su hadu domin yace taje ta samu su daddy tace a fasa Auren. nikuwa nace tab lallai kana da aiki saleem🤔 dan husna son Auren nan take. Bayan kwana biyu dai haka ya gaji da jirnasu hadu. ranan kuwa su yasmeen sunzo sunata ma husna tsiya wai zata Aura saleem toh wllhy ta shirya ma muguntarshi kuma sukace wllhy karta yarda ya rainata ta cire wannan tsoron . haka dai sukai tamata itadai sai dai tayi dariya. suna zaune saleem ya kira yasmeen tana dauka tace ango! a tsawace yace shut up! yaushe nafara wasa dake . tace ai gaskiya nafada. yace wllhy karki bari nazo na sameki dan saina zane ki baruwana da Auren da kikayi. cikin kunkuni husna tace da kenan wllhy yanzu bazan yarda ba dan mijina ma bazai kyaleka ba. saleem sarai yaji me tace amma sai yace me kike cewa ? tace bakomai ba da kai nake ba. kwafa kawai yayi . yace kituromin yarinyar nan. yasmeen tace ai yaya tana kasa wurin mummy tana bata abinci. yace abinci kuma. tace eh inace kana maganan dinar ne. tsaki yayi yace ke mayasa baki da fahimtane. sarai yasmeen tagane wayake nufi amma ta nuna bata ganeba. tace ai naji kace yarinyar nan e shiyasa na dauka dinar dan itace yarinya. saleem kuwa da ranshi ya gama baci ya daka mata tsawa yace yaushe na fara wasa dake . kice ma husna tazo ta sameni. kit ya katse wayan. yasmeen kuwa dariya tayi dayake dama wayan a handsfree tasa yasa duk suka kwashe da dariya. nusaiba tace ina tausaya miki idan ya saleem yakamaki. husna kuwa gaba daya tsoro ya kamata da kyar tasa hijab dinta . ganin yadda takeyi ne yasa yasmeen cewa wllhy zai rainaki ji yadda kikeyi a bayan idonshi ina ga agaban idonshi ai sai kuma sakin fitsari. wllhy husna idan baki cire tsoron saleem ba zaki sha wuya nidai nafada miki. husna kuwa barin dakin tayi jiki a sanyaye ta nufa dakin saleem . tayi knocking hade da sallama . shigo kawai yace. jiki a sanyaye ta shiga tasamu jikin bango ta rabe. shikuma yana zaune ga laptop a jikinshi yana latse latse. tafi karfin minti talatin a tsaye be dago ya kalleta ba gaba daya tagaji ga karfa ya sage. cikin jin haushi tace in baka da magana zantafi dan na gaji da tsayuwa . juyowa yayi ya tsura mata ido ita kuma ta kau da kanta gefe . gaba daya mamakinta ya kamashi. kafin yace wato kema sokike kizama yasmeen ko sunaso su koya miki rashin kunya . murguda mishi baki tayi. tace nidai inajinka dan nagaji da tsayuwa kuma ni ba soja bace . tasowa yayi yace toh bari kiji karkiga na kiraki ki dauka kamar sonake na ganki. dama magana zan miki. ke wai kina murna zaki aureni toh bari kiji in fada miki ni saleem nafi karfin ki nafi karfin ajinki bazaki taba iya mallakata ba. zadau ki iya amsa sunan matata a waje amma a gidana dake da babu duk dayane . husna bazan taba sonki ba bazan taba kaunarki ba kwata kwata baki da qualities din da zan soki . shiyasa tun wuri gwamma kije ki fada ma su daddy ba kyasona a fasa auren nan. husna kuwa fuskarta sharkaf da hawaye tace bazanceba . kai mezai hana kace . ko an fada maka nima sonka nakeyi nima banasonka. yace gafaracan yimin shiru wacce ko saurayi bata dashi saboda bakin jini. husna murmushin takaici tayi tace naji banda saurayi kuma na yarda inada bakin jini. bakin jinin ne ma yasa aka hadani dakai saboda kaima anga bakin jinin ne gareka. tas! tas!! ya mareta yace how dare you? toh bari kiji nafada miki bazan sokiba na tsaneki sannan kuma gidana in kika shigo sai ya zamar miki tamkar wuta domin bazaki taba jin dadin rayuwa dani ba. bazaki taba samun farinciki ba. husna tace ba komai duk wanda ya zalinci wani Allah zai saka mishi. bazan hanaka tanadan wulakanci ba amma ina so kasani wllhy Allah yana tare da me gaskiya. kuma na tabbata wataran sai kayi danasani kamar yanda ka sani zubar da hawaye kaima saika zubar. kuma kome zakayi kayi amma bazan taba iya ketara maganan mummy da daddy ba. kuka yaci karfinta yasa da gudu tabar dakin…. saleem kuwa gaba daya ya…….. husna sai da ta share hawaye ta gyra sannan ta shiga cikin side dinsu dakinta ta shiga ta kwanta. yasmeen ce ta biyota cikin dakin tace lph? husna kawar da kanta tayi tace lph sis. yasmeen zama tayi ta dafa ta tace wllhy husna shawaran dazan baki shine kada kisake kisa damuwa a ranki ahaka zaki lallace wllhy kicire komai kiyi ta addu’a kawai na tabbata yanzu haka saleem ne ya bata miki rai. sis duk wani namiji dakika gani kai bama namiji duk wani dan adam yanada weakpoint . dan haka zama zakiyi ki karanci saleem ki gane weakpoint dinshi toh kekuma ta nan ne zakisan abinyi. saleem dan uwanane kema yar uwatace sannan kuma ke yar uwatace mace dan haka bazan so naganki kina cikin damuwa ba. ki kwantar da hankalinki ayi auren tukunna na tabbata koda saleem yanzu baya sonki zai soki kuma kece zaki koya mishi sonki. nan dai yasmeen taita kwantar mata da hankali a haka har taita dariya sannan suka kama wata hiran. Bayan kwana biyu husna na zauna tana kwalema a cikin kwaleman ne taga card din mubarak daya bata wanda suka hadu a airport tace lah namanta ma da wannan bawan Allah gashi nayi mishi alkawari zan kirashi. husna wayanta ta dauko ta kirashi amma be dauka ba dan haka sai ta ajiye wayanta ta cigaba da abinda takeyi bayan tagama har tayi wanka ta sauko . ba kowa a falon kitchen ta nufa nan taga lantana na aiki tace sannu da aiki . tace yauwa. husna tace mummy fa ? tace tana daki tace zata kwanta kanta na ciwo oka kawai husna tace. falo ta dawo ta zauna ta kunna t.v. tana zaune kawai taji an fado falon dagowa tayi taga safiya a ranta tace ai sai wannan mahaukaciyan. kau da kai kawai tayi. safiya ganin ta kau da kai yasa tayi tsaki ta ajiye jakanta a daya daga ciki kujerun sannan ta nufa side din saleem . har taje bakin kofanshi sai kuma tace kash namanta banfaga motanshi ba . dat means yana office tsaki tayi kawai sannan ta koma side din mummy. zama tayi sannan ta kwala ma lantana kira tace ta kawo mata abinci da lemu. lantana tace toh . lemu tashiga ta dauko mata. sai data kawo mata tace ta koma bashi takeao ba five alive takeso . lanatana haka ta koma ta kawo mata. safiya tsiyayawa tayi a kofa tayi sipping sannan ta tashi ta dauko remote din dake kusa da husna. itadai husna tsayawa tayi tana kallon ikon Allah . ganin safiya ta chanza mata channel yasa tace yahaka . safiya hararanta tayi tace kamarya . husna tace ya ina kallo zaki chanza min . safiya tace na chanza ko kinada ikon hanani ne husna tace kwarai kuma domin nan gidan mune ke bakuwa ce. da’ace da kika shigo kin iya sallama dana san da zuwanki na mutuntaki toh amma sallama ma baki iya yinta ba balle gaida mutune. safiya tace ke malama dakata ke awa ? kibar yan gida suyi magana dan Allah da ace dana shigo naga dan gida a wurin nan mezai hana nayi sallama. STORY CONTINUES BELOW toh ni ko agola banganiba. dan ke baki kai matsayin agola ba . ke yar karere ce. husna tace eh koma dai mezakice naji. amma wllhy baki isa ina kallo ki chanza min ba. na luar baki da mutunci bakisan kawaici ba karkiga ina kyaleki ki dauka bansan me nakeyi ba ko ina tsoronkine. a’a kawai kinacin darajan mummy ne. safiya cike da masifa tace bansan inci darajan kowa kuma idan kin isa ga remote din ki dauka ki chanza. husna takai hannu zata dauka remote din safiya ta tureta. husna kuwa tana dagowa ta tsinka mata lafiyyan mari. takai hannu zata rama husna tayi maza ta rike hannu tace karki kuskura domin wannan shine zai zaman miki babban kuskure a rayuwanki dan saikinyi danasani. tafiya ta fara yi zata hau sama . safiya tace banza kawai jaka dabba wai har kece za’a aura ma saleem ni banga abin sha’awa ajikin kiba domin koni danake mace baki burgeniba balle na miji jiki dan Allah sai kwalakwalan ido. wllhy baki dace da matar saleem ba. husna juyowa tayi tace oho kice abinda kike jima haushi kenan kike kishi. kece bakiga abin so ba amma shikam saleem ya gani tunda gashi zai Aureni. safiya tace kika dai like mishi sannan kika shiga kika fita dan na tabbata saleem inda yana cikin hayyacinshi bazai yarda ya Aureki ba na dole akamishi. husna tace kanki akeji keki shiga kifita mana yasoki gwamma ni kwalliya ta biya kudin sabulu. kekuwa naga sai cusa kai kike ba kwarjini ba irin iyayi da kiss da kisisina da bakyayi amma ko kallo baki isheshi hasalima kyankyaninki yakeyi. mummy kuwa dake kwance kamar tana jin hayaniya yasa ta sauko ta duba taga meyake faruwa. safiya kuwa ta shaka da maganan husna. tace banza idan dayana kyankyanina bazai iya hada bakinshi da nawa ba. adaidai nan sukaji mummy nacewa wai meyake faruwa ne. husna datayi suman tsaye dajin kallaman safiya yasa ko amsa bata iya ba mummy ba. gaba daya jitayi jiri na neman dibanta. wane irin kishi tajj ya tokareta. mummy karasa saukowa tayi tace meyake faruwa ne nake tajin hayaniya husna? sai a lokacin husna ta tattari nutsuwanta tace bakomai mummy. safiya kuwa a wulakance ta gaida mummy . mummy amsa mata kawai tayi da lph. safiya daukan jakanta tayi tace toh na tafi mummy. mummy tace kigaida gida. husna kuwa daki ta wuce tana shiga ta fara kaiwa da komowa tana juya maganan safiya. tace kai anya saleem zaiyi haka kuwa saleem din da ma ko kulata bayayi gaskiya akwai abin dubawa. tace kai nasan karya takeyi tafadi hakane dan naji haushi. da kanta taba kanta amsa tace kai hakane ma. da haka taji sanyi a ranta ta dauki wayanta ta duba nan ta tarar da missed calls 3 zata kira kenan call ya shigo amsawa tayi da muryanta me dadin saurark sannan kuma cikin sanyi. Mubarak kuwa dajin muryanta yaji wani irin sanyi a zuciyarshi. yace gimbiyan mata barka da warhaka. dum taji gabanta yafadi . yace ya kike ? ya gida? tace lph lau. yace sai yau kika tuna dani. murmushi kawai tayi kamar yana ganinta. yace ai da baki kirani yau ba da inaga bazan iya bacci ba. tace saboda me? yace saboda tunaninki. haba Asma’ul husna ace kin manta da dan uwanki kullum sai na saurara kiranki amma a banza . koda yaushe cikin sa rai nakeyi da zaki kirank amma shiru. tace hmmm abubuwa ne suka min yawa . yace bakomai. nan dai yayita janta da hira danshi mutum ne me barkwanci. daga baya ya bukaci address din gidansu akan zai zo ya kawo mata ziyara. tace mishi zata tura mishi daganan sukai sallama . bayan sun gama wayan ne ta tura mishi. washegari kuwa sai gashi yazo . mummy taje ta sanar mawa da bakon ya iso mummy tace ta kaishi guest parlour. har ta juya zata tafi mummy ta kirata da husna. juyowa tayi tace na’am mummy . mummy tace karkimanta dai ariga an badake . idan yazone da maganan yana sonki ko zai Aureki karki boye mishi komai kifada mishi. toh tace ma mummy sannan ta nufa waje danta shigo dashi. megadi tasa ya bude mishj gate yaje yayi parking motanshi a parking space sannan ta kaishi guest parlour . komawa tayi ta kwaso mishi abin motsa baki ta kawo mishi sannan ta samu wuri ta zauna. mubarak kuwa kallonta yakeyi cike da burgewa domin gaba daya husna ta hada qualities din da yakeso a wirin mace. dan daga yanayinta daya gani yasan cewa kamilalliya ce kuma akwai nutsuwa a tare da ita. ganin yayi shiru yasa husna dagowa aikuwa suka hade ido ganin irin kallon dayake mata ne yasata cewa kasha ruwa mana. yace ai ni tunda naganki naji na koshi. murmushi kawai tayi tace a’a ai bazakazo har gidanmu kaki cin komai ba. yace toh ur wish is my command. lemu ya tsiyaya a cup . chan yace husna. dagowa tayi tace na’am yace toh dai bazan tsaya ina miki boye boye ba . nazo ne nagabatar miki da kaina domin gaskiya ni tun lokacin dana ganki nace na samu matar Aure . saboda haka idan zaki bani dama ni ba wasa bane ya kawoni ni Aurenki nakesonyi. idan kuma har ban kwanta miki ba pls don’t hesitate to tell me . karkiji kunya na. husna tace nagode da kanuna kana sona dan meson mutum yafi makiyinshi. tace amma sai dai kayi hakuri domin an riga an badani ansa min rana. duk da baiji dadin maganan ba amma haka ya daure yayi mata addua’an zabin Alheri. yace amma ina fata kuma zumuncin mu bazai yanke ba ki daukeni matsayin yayanki tace insha Allahu. nan dai ya tashi yace zaitafi . rakoshi tayi inda yayi parking suna tsaye aka wangale gate. saleem ne yashigo. yana shigowa husna idonshi ya hango mishi tare dawani. husna kuwa gaba daya ta dabirce ganin haka mubarak yace ya akayi ne? zata bashi amsa ba taga saleem na tunkaro su…… saleem yana zuwa kawai mika ma mubarak hannu yayi suka gaisa sai a lokacin husna ta sauke ajiyar zuciya . ya juyo ya kalli husna yace ki kaishi falon baki mana kin ajiye shi nan. tace a’a ai tafiya zaiyi daga chan muke . yace okay. sannan yama mubarak sallama ya tafi side dinshi. husna ba karamin mamaki ya bata ba kenan ya dada tabbatar mata dacewa baya sonta don da yana sonta da yan nuna kishinshi akanta. mubarak yana mata magana amma ina hankalinta yayi gaba. iska ya hura mata a fuska . murmushi ta sakar mishi yace yadai ? tace bakomai. yace toh bari na barki sis sai munyi waya. tace okay nagode da ziyara Allah ya bar zumunci Amin yace mata . sannan ya ja motarshi daga parking lot ya nufa gida. Some month later yanzu biki ya rage saura sati hudu shirye shirye akeyi sosai dan daddy kudi yaba mummy taje dubai ita dasu yasmeen suka hado kayana akwati sannan akayi order furnitures. shiko saleem ko ajikinshi dan gaba daya be dauka maganan Auren da muhimmanciba . mummy kuwa ta dage ba karamin gyara akema husna ba . gaba daya ta chanza kyalli kawai takeyi. ba inda take zuwa dama sun gama exams yanzu jirna result kawai sukeyi. su yasmeen bakaramin tsiya suke mata ba . su yasmeen ma kansu kullum suna gidan mummy acewarsu suma sunaso amusu gyaran jiki. indai mummy ta hado husna wani hadin sai sunsha. barin ma yasmeen dan ita nusaiba sai taji me zaki takesha. A kwana a tashi asaran me rai gashi nan yanzu biki ya rage sati daya . yau ne mummy ta kira su matar Alh suleiman suzo suga kayan akwati . sannan kuma itama husna wasu daga cikin dangin babanta zasuzo. aikuwa gida ya cika yayi makil. safiya ma sai datazo yasmeen kuwa sai habaici suke wurga mata dan gaba daya jininsu be hadu da safiya dan ita akwai rashin kunya ga jiji dakai kamar diyar wani shugaban kasa. dataga ba sarki sai Allah yasa ta kama gabanta tayi gida. koda ammi ta dawo kuka ta fashe mata dashi wai shikenan yanzu ta rasa yaya saleem kenan . mummy kuwa tace ina baki rasa shiba ai gidan saleem kamar kinshiga kin gama ki kwantar da hankalinki. yanzu dai bari ayi biki a gama zansa hanyar da zanbi ayi komai . safiya tace kai shiyasa nikesonki ammydomin ba kyason baccin raina suk abinda nakeso kinamin. Ammy tace toh in ban miki ba waan mawa . dariya sukasa dukansu. STORY CONTINUES BELOW Yau ne ranar daurin Aure jiya sukayi walima domin saleem yace shiba abinda zaiyi itama nata bangaren husna dama ba meson bidi’a bace . shiyasa sukayi walima wanda aka samu malamai sukazo sukai wa’azi. yau ne kuma daurin Aure. saleem kuwa sai da mummy tazo tai mishi ta tas sannan ya shirya dan abokananshi sunzo suna ta jiranshi gashi lokaci na tafiya daddy sai kiransu yake. saleem kuwa bayanda zaiyi haka ya shirya. abokananshi kuwa banda tsokananshi ba abinda sukeyi wai yana nuna bayaso sai nan da yan watanni sai dai suji ance husna ta haihu. yace Allah ya kiyaye mezaiyi da karamar yarinya. wani daga cikin abokananshi yace toh jifa inda za kabarmin ita wallhy inaso dan husna tayi ta kai mace iya mace wanda duk namiji zaiyi alfahari da samunta. saleem kuwa tsaki yayi yace wai ku uban waye ma ya gayyaceku ne? sukace mummy mana . yace kuka sani. wani yace kai baba jiya fa wllhy danaga husna gaba daya na dauka wata balarabiyace. saleem kuwa tsaki yayi yace ba balarabiya ba saura baturiya ni idan zaku tashi mutafi ku taso in kuma zaku zauna ne toh ni natafi. gaba daya ihu sukasa sukace ashe dai ana so eyye . ahaka dai sukai ta tsokanarshi har suka nufa wurin daurin Aure. bangaren husna kuwa gaba daya jikinta a sanyaye yake barin ma dataji an dayra aure nan fa ta fashe da kuka ita kanta ta rasa kukan me take na farinciki ne ko akasain haka . yasmeen ne taita rarashinta har ta sa kaya akamata makeup. nan fa akashiga hotuna. da daddare kuma aka kai amarya gidanta a sharada. husna tayi kukan rabuwa da mummy kamar me dan da kyar aka samu aka banbareta jikin mummy aka kaita . saleem kuwa yana chan kwance a dakinshi kamar ba angoba. su yasmeen ma dasuka gaji ganin har da shadaya tayi saleem beshigoba takira mummy a waya ta fada mata. mummy kuwa rai a bace ta isa side dinshi buga kofan ta shigayi shikuwa cikin bacci yaji ana buga kofa tsaki kawai yayi ya koma ya kwanta. ganin ba a daina buga kofan ba yasa ya tashi yaje ya bude. mummy kuwa batai wata wata ba ta tsinka mishi mari. yana dagowa ta kara tsinka mishi mari. tace idan kaga dama kar ka tafi gidan matarka ka kwana a nan . wllhy saleem zakaja namaka abinda baka taba tunani ba. tana cewa ta wuce bata tsaya jiran mezaice ba. shikuwa saleem rai a bace ya dauka key din mota ya tafi gidanshi. yana shiga ya rufe kofa. husna kuwa dama tunda su yasmeen suka tafi tayi wanka ta kwanta abinta. saleem nazuwa direct dakinta husna ya nufa yana tura kofa ya ganta tana shan bacci hankali kwance. buga mata duka yayi a firgice ta tashi. yace mayya wato kin hadani da mummy shine kikazo kina shan bacci hankali kwance ko? zatai magana ya tsinka mata mari. bata ankaraba ya kara mata wani yace wawoya kawai wannan kadan kika fara gani . wannan na bakine kyautar first nyt! mutum dan jaraba ko irin kunyan nan na Amare ba kyaji saboda kinsaba bada kanki a titi shiyasa har… be karasaba sakamakonn wani tsawa da husna ta mishi . tace karka kuskura kar ka taba ko a mafarki ka jefi da wannann kalman zan iya jure komai daga gareka amma bazan taba jure wannan ba. wllhy saleem na tsaneka . kuma na tabbata watarana zakayi dana sani sannan one morething wllhy duk ranan daka kara irin wannan maganan wllhy i will show the real Asma’u not d husna u know. tana gama fadin haka ta tashi tashiga toilet tana sauke ajiyan zuciya sai kuma ta fashe da kuka tap ta kunna ta zauna taci kukanta domin maganan saleem ya bata mata rai. shikuwa kamar statue haka ya tsaya sai daga baya yaja kafanshi ya nufa dakinshi ya kwanta. washegari tunda tayi sallah asuba ta koma ta kwanta a cikin bacci taji ana knocking hijab tasa ta fito kofar falon ta nufa ta bude lantana tagani . tace ah lantana kece shigo mana . shigowa tayi dauke da basket a hannunta husna amsan basket din tayi sannan suka gaisa daganan tace zata tafi dama mummy ne tace ta kawo musu. godiya husna ta mata sannan ta wuce. husna dakinta ta koma tayi wanka sannan ta fito direct dinng table ta nufa ta zauna taci ta koshi ta dauka kayan datayi amfani dashi ta wanke tsaf sannan tarinka bin ko ina a tana dubawa. gaba daya gidan ta zagaya tana dubawa bakaramin burgeta gidan yayi daganan ta wuce dakinta ta kwanta. saleem kuwa koda ya fito be tsaya bi takan breakfsast ba burinshi be wuce yaje wurin mummy y bata hakuri ba. parking lot ya nufa ya dauka motarshi yanufa gidan mummy. yana shiga ya gaisa da ragowan mutanen dake falon sannan ya nufa sama wurin mummy . knocking kofanta yayi tabada izinin shigowa. saleem tura kofan yayi jiki a sanyaye ya shiga ganin saleem ne yasa ta dauke kanta . durkusawa yayj har kasa ya gaisheta . bata kalli inda yakeba amma ta amsa mishi. saleem kuwa ganin haka yace dan Allah mummy kiyi hakuri kiyafemin . wllhy banaso ko kadan in bata miki rai dan Allah mummy kiyi hakuri. mummy sai a lokacin ta juyo tace niba kamin komai ba. Amma kar ka kuskura ka cutar da marainiyar Allah husna bata sonka kamar yanda baka sonta amma tayi mana biyyaya ta amince da aurenka. ta nuna mana cewa ita me biyayya ce amma kai baka dashi ka girma bamu isa dakai ba. yace dan Allah mummy kiyi hakuri. tace oho kai kasani ga husna nan in kaga dama kariketa amana in baka ga dama ba ka cutar da ita. Allah yana gani shi zai muku hisabi. daganan ta sassautar da murya ta shiga mishi nasiha . tare da samusu Albarka. AFTER ONE MONTH……