DR TAHEER CHAPTER 3 BY UMMU ASHRAF
Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan Daren ma kmr wancan Sam Taheer bai samu bacci ba sai dayai sallahn asubah…hakan yasa bai tashi da wuri ba sai after 10….bayan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya as always ya nufi part din ummi…tana zaune parlor tana kallon wani program ya zauna kusada ita bayan sun gaisa tace”ya ciwon kan naka”….yace “to da sauki zaace ummi nasan stress ne idan na samu hutu zai Dena…tace”ya kamata dai ka samu kayi hutun gsky”…yace InshaAllah..baby bata tashi bane?Ummi tace “kmr dai bata tashin ba don tunda na fito banji duriyarta ba…ya mike Yana fadin bari in duba mgn nake sonyi da ita…tana tsaye gaban press dinta tana neman kayanda zata saka ya shigo dakin..ta juyo da murmushi a fuskarta tace”good morning Daddy”Yana murmushin shima ya amsa
Mata”morning..zo muyi wata mgn”ba musu ta dawo gefen gado ta zauna tareda maida hankalinta gareshi…Saida ya kauda kanshi snn ya fara mgn”Usman ne dama yace Yana sonki and he wants to marry you”Layla ta zare ido da mamaki tace ban gane he wants to marry me ba daddy..wane Usman din ma kke mgn in the first place?ya kamo hannayenta ya rike snn a hankali yace”dama mgnr daya kaimu Dutse knn…Alhaji ya fadamin Usman yace Yana sonki Kuma suna son hada aurenki dashi amma sai da amincewarki…idan bakiso ba Wanda zai maki dole”Layla tayi shiru na tsawon lokaci tana tunani kafi tace”daddy to Kai yanxu zakamin aure ne?bakace sai na gama school zakamin aure ba”Taheer ya lumshe ido ya bude snn yace”haka na fada baby Amma bazan iya musu da Alhaji ba…kinga a ka’ida Yana da right din da zai badake ga duk Wanda yakeso amma sbd karamci irin nashi sai baiyi hakan ba..ya kirani ya sanar dani snn yace a tambayeki..amsanki kawai muke sonji kina sonshi ko baki sonshi??Saida tadan tabe baki snn tace”am not used to loving u know..ban taba son kowa ba apart from you sai su ummi so ban San ya so din yakeba..amma daddy Kai ka amince ne..I mean kanason in aureshi?Taheer yai shiru kawai Yana kallonta ji yake inama zai iya fitowa ya sanar da ita shima yana sonta..inama zai iya nuna Mata babu Wanda ya Dace da ya aureta face shi…tunanin hakan yasa zuciyarshi ta sake karyewa da kyar ya daga Mata Kai alaman ya amince…sai ta saki murmushi tace”Nima na amince daddy..ban San ko Ina sonshi ba amma na amince sbd Kai..nasan InshaAllah with time zanyi developing feelings for him”ya Dan kakalo murmushi snn yace “alright bari inje in kirashi sai in sanar dasu kinyi accepting..bai jira cewarta ba ya fita a dakin da sauri..baibi takan breakfast din bama ya wuce abinshi.+
Yana shiga daki ya Kira alhaji ya sanar dashi ta amince..alhaji ya nuna farin cikinsa sosae snn yace zai sanar da Usman ta amince ko a waya sai su fara mgn da ita kafin ya samu lokaci sai yazo Abuja su sake fahimtan juna.
A bangaren Taheer kuma ya yanke ma kanshi hukunci zai fara yin baya baya da Layla..a tunaninshi hakan ne kadai zai saukaka mai abinda yakeji gameda ita… snn kuma bazai iya jure yana kallonta tana waya da wani a mtsayin Wanda zata aura ba…so it’s better ya rage shiga harkanta kawai…kazantar da baka gani ba akace tsafta ce.
Wannan kenan
Kwanaki nata tafiya yayinda shakuwa me karfi ke shiga tsakanin Layla da Usman…dukda bai taba zuwa Abuja ba amma kasancewarshi mai raha da son mutane cikin lokaci qarami Layla ta fara sabawa dashi snn ga uwa uba soyayyan da yake gwada mata…duk da har yanxu bawai zatace ta fara sonshi bane but tanajin dadin kasancewa tare dashi.
Saidai wani abu dake damunta shine canji data gani tattare da daddynta..Sam bata San laifinda ta aikata mai girma haka da har zaisa daddy ya fita harkanta gaba daya..he no longer cares about her kmr yanda yakeyi a baya…abun ba karamin damunta yake ba kuma ta rasa wanda zata fadawa…ko mgnr aurenshi da anty Samira a bakin ummi taji tasan da Dane da bakinshi zai fada Mata tunda yasan tanaso yai auren…gaba daya she’s confused bata San laifinda ta aikata ba…kodai don tayi accepting Usman ne??ta tambayi kanta sai Kuma wata zuciyar tace ba haka bane ay Saida ya nuna amincewarshi snn itama tayi amma why daddy zai juya Mata baya haka?
STORY CONTINUES BELOW
Kamar yadda Taheer yai alkawari ya kawo Sameera har gida ta gaida ummi..snn sati mai zuwa ummi tace zataje kano tayi mgn da uncle dinshi kan yazo ya nemamai aurenta…shidai Taheer Sam baiso hakan ba don har yanxu baiji yanason auren ba bawai Kuma don baya bukatar auren bane…aah sedai wadda yakeda bukatar ya aura din tayi masa nisa..duk ya tuna cewar an tsaidama Layla da mijin aure sai yaji kmr ya kashe kanshi sbd bakin ciki…gashi har yanxu ba abunda ya ragu cikin sonda yake Mata sai ma karuwa da yakeyi…dukda yadda yake kokarin nisanta kanshi da ita amma abun yaci tura…shi kadai yasan dauriyar da yake…kullum idan bai ganta ba ji yake kmr zaiyi hauka tun yana kokarin kar ya gantan ma har ya hakura…don yasan ganin nata shine samun saukinshi…haka duk dare bayan ya tabbatar da kowa yayi bacci zai lallaba yaje dakinta…yakan dauki tsawon lokaci a haka yana kallonta kafin ya Mata addu’a ya Mata off din light snn ya fita.
Yau da wuri ya dawo gida sbd baijin dadin jikinshi..bayan yai wanka yayi changing ya nufi part dinsu…Layla ce kadai kwance a parlorn idanunta a rufe…kmr kar ya karaso parlon sai Kuma ya daure ya shiga ya zauna tareda kauda kanshi gefe…tunda ya kalleta sau daya dama bai sake kallon inda takeba…da sauri Layla ta bude idonta jin kmr kamshin perfume dinshi don bataji shigowanshi ba…ganin yanda ya dauke Kai kmr bai ganta ba wasu hawaye suka zubo Mata…shima Taheer dukda ba kallonta yakeba jikinshi ya bashi tana kallonshi and for sure yasan hawaye take… baiso ta karya mai da zuciya sai ya mike da sauri zai bar parlon kawai yaji ta rungumeshi ta baya tareda fashewa da matsanancin kuka…jikinshi har shivering ya fara jin irin force din da tayi applying a hug din…ya lumshe idanunshi shima hawaye masu zafi suka wanke mai fuska…he missed her kaman yayi hauka and jinta a jikinshi ji yake tamkar tana sake gayyato wasu al’amura ne zuwa jikinshi…Sam bayason yanayin daya shiga yai tasiri a kanshi don haka yasa hannu ya janyota zuwa gabanshi bayan ya share hawayen dake fuskarshi…Yanata kokawa da baki da Kuma zuciyarshi kawai yaji ta sake hugging nashi wnn karon ta gaba…baida zabin daya wuce yasa hannayenshi shima tareda sake manneta da jikinshi gam…ya sauke wata ajiyar zuciya…son da yakema yarinyar nn is beyond expectation..as a doctor da yasan akwai maganinda idan mutum yasha zai dena son duk wani abu dayakeso da yasha…amma babu….a hankali ya jata suka zauna kan kujera…ya shiga goge Mata tears din da hanunshi yace”baby mana..kukan ya isa haka..I hate to see you crying you know it…so stop crying kinji babynah”ba musu ta tsaida kukan tareda sa hanu ta fara share hawayen fuskar”tell me what exactly is your problem”ya fada idanunshi a kanta…a hankali ta sunkuyar da Kai snn tace”Ni ban San laifin da nayi maka ba kake fushi Dani…gaba daya ka canja daddy don Allah let me know…idan laifi nayi maka I’ll apologize…idan Kuma bazaka iya fadamin ba then yell…shout at me.. ko dukana ne ma kayi as long as zaka Dena fushi cox I can’t take it any longer…am tired please…ta karashe tareda fashewa da wani kukan…gaba daya ta gama kashe mai jiki…yasa hanu ya share Mata hawayen yace”babu laifin da kikamin baby…aiki ne kawai sukamin yawa…you know bazan taba hurting naki purposely ba koh…”to ko Dena Sona kayi ne daddy”?ta fada idonta a kanshi…shiru yai kawai Yana kallonta kmr mirror…wai ko ya Dena sonta?….well he wish dena son natan is as easy as yanda tayi pronouncing dinshi a baki…da tun tuni yayi hakan ko zai samu sassauci…amma inaaa it’s never possible…yai cupping fuskarta da hannayenshi idanunshi a kanta yace”who told u so”…a hankali tace”your actions..ka dena kulani..ka Dena cin abinci Dani…ka Dena fira Dani snn ka Dena zuwa unguwa dani…idan na gaisheka you used to answer with a very short reply…indai ba dena Sona kayi ba then what makes you change towards me haka?…shiru ya sakeyi yana kallonta sai Kuma ya girgiza kai tareda rungumeta a jikinshi yace”never in my life…bazan taba iya Dena sonki ba baby nor matter what…so ki dena wnn tunanin pls…ur Daddy loves you so much infact I love you more than any other thing in the whole world…I love you to the moon and back…baby I love you so much”…ya karasa tareda dago kanta ya manna Mata peck a forehead dinta followed by cheeks dinta…Layla ta lumshe ido don dadi…bata taba sanin tayi missing peck din nn ba sai da yayi matashi yanxu…she missed him like crazy…ta sake hugging nashi tana dariya tace”I love you more my daddy…nayi missing dinka sosae…please don’t punish me with this cold attitude again… mutuwa zanyi Allah”ya shiga shafa gashin kanta yace I will not InshaAllah…ta dago tana kallonshi still smiling tana nuna forehead dinshi tace”I want to peck you too Daddy”…ba musu ya sunkuyo da kanshi itama tayi mai peck kmr yanda yake Mata… Taheer Banda kallonta ba abinda take…wani irin farin ciki yakeji just by having such conversations with her…haka nan yaketa punishing kanshi ta hanyar avoiding dinta…well he’ll never make such a mistake in future…zai cigaba da addu’a kawai Allah shi yasan yanda zaiyi dashi… ringing din wayanshi ya dawo dashi daga tunanin da yake…ya karkata ya zaro phone din a aljihunshi”Sameera”shine sunan daya gani…yaja Dan siririn tsaki…gaba daya yarinyar ta dameshi wlh…haba duk tabi ta takura mai da Kira sai kace bata da wani aikinyi sai Kiran nashi…Saida ta kusa katsewa yai picking tareda karawa a kunnenshi without saying anything…a daya bangaren Sameera najin anyi picking ta saki ajiyar zuciya tareda fadin”am sorry if am disturbing you doctor…kayi hakuri plss…na damu ne da naga inata Kiran wayanka baka picking..I was very worried about you but am sorry pls”…a takaice yace da ita”it’s okay…how are you?tace”am fine doctor just missing you…don Allah yaushe zakazo in ganka wlh nayi missing dinka sosae…at least tunda kayi accepting dina yanxu ya kamata ka ringa zuwa Ina ganinka or Better still ni ka ringa barina inzo in ganka…bazan iya daukan tsawon lokaci without seeing you ba ka taimaka plss”…shiru yai yana kallon Layla dake kallonshi tanata aikin murmushi…sai Kuma ya Dan gyara murya snn yace”Ina clinic ne yanxu…idan na samu lokaci zanzo”…da sauri Sameera tace”then am coming to the clinic right away….tun kafin ta karasa yace Mata”No Sameera ba saikinzo ba…idan na gama aiki da wuri zan biyo ta gidan naku”…tana kokarin yin mgn yace”na riga na gama mgn Sameera…so am hanging up inada aiki a gabana…dif ya kashe wayar tareda maidata cikin aljihunshi…Layla na kallonshi cikin tsantsar farin ciki tace”wow!am very happy daddy…anty Sameera loves you so much…am sure she can take very good care of you as a wife…Nima Ina sonta daddy”…murmushi yai snn yaja hancinta yace”wato she can take very good care of me as a wife koh…zakiyi explaining wnn mgnr”…tasa dariya snn tace”but daddy pls why bakason zuwa gidansu?…ya kamata ka daure kaje yau tunda kana free please I beg you…ya kama hanunta cikin nashi yace”wato ke Zaki koyamin koh…well zanje…but only if kema Zaki shirya muje tare”…Layla ta zare ido tace muje tare Kuma daddy?…ya daga Mata Kai alaman eh…snn yace kuma idan bazakije ba nima am not going…da sauri Layla tace”no daddy zanje…Bari inje in shirya kaima kaje ka shirya sai mu tafi…yakai hanun nata bakinshi yai kissing snn yace”good girl”…a tare suka mike shi ya nufi part dinshi ita kuma ta nufi dakinta don shiryawa.
Suna tafe a hanya sai labarai take bashi…da gani ba karamin farin ciki take cikiba…shima hakan bakaramin faranta mai yayi ba…he always wants to see her happy.
Maimakon gidansu Sameera bakin wani shopping mall taga yayi parking…tana Shirin yin mgn ya Dora Dan yatsanshi kan bakinta yace”shushshsh…just wait for me hear i will be right back….batace dashi komai ba har ya fita ya shiga wurin…after like 10 minutes ya fito daukeda leda a hanunshi…ya bude back seat yasa ledan a ciki snn ya shiga yai reverse suka fita daga wurin…cikin lokaci kankani suka isa unguwan su Sameera…daidai kofar gidansu yai parking snn yayi dialing numberta… ringing daya tayi picking…a takaice yace Mata”am at the gate”…wani uban ihu data fasa Saida ya sauke wayan daga kunnenshi for some secs snn ya maida…tun kafin yai mgn tace”ka shigo ciki doctor gani nan zuwa yanzun nn”…ba tareda yace kala ba yai hanging snn ya doshi gate din yai horn…Saida mai gadin ya leko snn ya bude mai gate din ya shiga ciki…bayan ya samu wuri yayi parking Yana kokarin sake kiranta kawai ya hangota ta nufo inda suke…doguwan rigane a jikinta fitted na atampa…dinkin ya matseta gam…ta kawo Dan siririn mayafi ta Dora a kanta…fuskanta ba wani mk up sai Jan baki da zaka iya hangoshi from miles….tanata doka murmushi har ta karaso wajen motar…Saida ya tabe baki a ranshi yace”wnn ta cika rawar Kai”..snn ya bude motan ya fito….wani wawan runguma ta kaimai batayi la’akari da ko mai gadi na kallonsu ba..Layla dake cikin mota ta Dan zare ido sai Kuma ta fashe da dariya tana fadin”look at yanda daddy ya firgita don Allah”….da sauri ya tureta a jikinshi yana Mata mugun kallo yace”are you mad…bakida hankali ne Zaki wani yi hugging Dina a bainan nasi…Sameera ta daga hanunta alaman ban hakuri tace”am really sorry my doctor…it’s just that nayi missing dinka da yawa but am sorry pls bazan karaba…yanxu mu karasa ciki”…ya dauke Kai kmr yace bazai shigaba sai Kuma ya bude motar Yana kallon Layla yace”baby let’s go inside”…ta Dan marairaice tace”daddy I’ll wait for u hear”…ya shiga girgiza Kai yace”No.. bazan barki ke kadai a nn ba so come Dawn mu shiga ciki”…bata sake cewa komai ba ta bude motan ta fito…ta karasa inda Sameera tana murmushi tace”ina yini anty Sameera”..Samira ta Dan kakalo murmushi tace”lfy Lou baby..ya kike”…a hankali tace Mata”am fine”.. snn ta juya gareshi tace”Dan Allah daddy kuje zan zauna a nan..don’t worry I’ll be okay”…da sauri Sameera tace”ka kyaleta mana doctor tunda tace she can manage…beside ba dadewa zakayi bafa zaka fito”…bai ce komai ba ya fara tafiya…da sauri Sameera ta bishi a ranta Fadi take”sai nayi mgnin yarinyan nn wlh…wnn jaraba har Ina”.
Parlo da suke saukan baki ta kaishi…ya samu wuri ya zauna rabin hankalinshi duk na kan Layla…a hankali Sameera ta zauna kan hanun kujeran da yake zaune tareda dora hanunta kan lallausan gashin kanshi dake nan kmr na mace…ya juyo ya kalleta da sauri sai Kuma ya cire hanun nata Yana kokarin tashi ta fada jikinshi tareda hugging dinshi tight…Saida yai da gske snn ya tureta a jikinshi yana Mata mugun kallo yace”so is this the reason da yasa kika dage sai nazo koh…good…to bazaki sake ganina a gidanku ba…kafin yakai kofa ta mike da sauri tasha gabanshi…hawaye har ya wanke Mata fuska tace”na rokeka da girman Allah kar kamin haka doctor..wlh ba halina bane…ban taba rike koda hanun namijin da ba muharrami na bane..it’s only you…when it comes to you bana iya controlling kaina doctor snd son da nake maka is over…but I promise bazan Kara ba Dan Allah kar kace zaka horani da rashin ganinka…I can’t take it plsss”sai ta durkushe a wurin tana cigaba da kuka… Taheer duk sai yaji jikinshi yayi sanyi cox he know how it feels…yasan yanda takeji sbd shima same thing yake going through…a hankali ya durkusa kusa da ita yace”na fahimceki Sameera…but this is not good…kinsan shaytaan is real and banaso ya kaimu ga aikata abunda zamuyi Dana sani nan gaba..so plss kiyi hakuri and be more patient…da zaran munyi aure kinga we are free to do anything we want…stop crying…ba musu ta share hawayenta tana mai murmushi snn tace”na gode doctor…I love you so much”…shima yai Mata murmushin snn ya mike yace”Bari inzo in tafi kinga nabar baby a mota…I promise zan dawo some other time…dukda batajin dadin tafiyan da yace zaiyi ba haka ta hakura tana mitan bai taba komai a kayan da aka kawo mai ba…Saida ta rakashi har mota snn suka tafi tana waving musu hannu.Suna tafe a hanya ba Wanda ke mgn sai Layla dake fakan idonshi tana mai dariya time to time…duk yana lura da ita basarwa kawai yai…sai da suka isa gida bayan yayi parking sai yasa lock a motar ya juyo yana kallonta yace”so na zama abokin wasanki koh”da sauri ta girgiza Kai still dai dariyan takeson yi….yai murmushi kawai snn ya Mika hanu ya dauko ledan daya ajiye a baya ya Mika Mata….tasa hanu ta amsa snn tace”mene a ciki daddy?…ya cire lock din dayasa snn yace”towels dinki ne…ki ajiye wadancan ki dena amfani dasu kwata kwata infact ki debosu ma dukansu ki kawomin…wnn sunada girma so dasu Zaki na amfani yanxu…no more kuncewan towel a gaban jama’a….lol(kunji mutuminku bai manta ba😆)Layla tadan turo baki tace”a gaban jama’a Kuma daddy…a gabanka nefa kawai…and ni zan iya cire kayana ma a gabanka ai Kai babana ne ba kunyanka nakeji ba kum….da sauri ya katseta da fadin”naji baby jeki dasu ciki toh Nima yanxu zan shigo….bata sake mgn ba ta bude motan ta fita…shima ya fito ita tayi part dinsu hanunta rikeda towels din nata shima yai nashi part din yana murmushi.+
Bayan kwana Hudu….
Tun safe ummi ta tafi asibiti sakamakon Ramla dake labour…tun safen Kuma take fama har zuwa yanxu da ake sallar magrib Allah bai yanke ba…Layla ce kadai a gida sai mama hauwa…tun dazu take zuba idon ganin daddyn nata tace mai itadai ya kaita asibiti wurin ummi amma har yanxu bai shigo ba….ta mike for the third time ta duba part dinshi har yanzu a rufe alaman bai dawoba knn…ta juya knn zata koma taji tayi karo da abu…aiko ta kwallara Kara zata diba a guje yai nasarar kamota ya rungume a jikinshi…gaba daya jikinta rawa yake don ta tsorata sosae ba kadan ba….Saida yaga ta Dan nutsu snn ya dagota yana kallonta yace”matsoraciya…meya fito dake?tace”daddy I came to check on you ne…tun dazu nake zuwa baka dawoba and inaso ka kaini wajen su ummi plss….ya shiga girgiza Kai yace”baby dare yayi ki Bari da safe…ta kamo hanunshi har ta fara hawaye tace”nidai daddy ka kaini yanzu dn Allah…ai ba dadewa zamuyi ba zamu dawo plss”…dukda baiso ba haka ya juya yace ta dauko hijab sai ta sameshi a mota….ta koma ciki da sauri ta dauko hijab din snn ta sanar da Mama hauwa zasuje asibiti.
Basu suka dawo gidaba sai after ten…Layla har tayi bacci a mota…har zuwa lokacin kuma Ramla bata haihu ba….ya bude motan ya fito bayan yayi parking ya dauketa zuwa ciki…mama hauwa na parlo da sauri ta mike tace”tun dazu naketa zuba ido najiku shiru likita…Allah dai yasa lfy”..yace”lfy Lou mama hauwa…haihuwar cedai har yanxu da saura..zuwa Safiya dai in bata haihuba inaga kawai cs zaa Mata…hauwa tace”oh Allah dai ya yanke Mata yarinyar nn Allah ya rabasu lfy…ya amsa da Amin snn ya nufi dakin Layla….ya kwantar da ita kan gado tareda zare Mata hijab din jikinta…ya shiga binta da kallo yanaso ta sa sleeping dress dinta Kuma bai son tadata a bacci…a hankali ya zame gown din dake jikinta…Allah ya soshi akwai inners a jikinta da baisan ya zaiyi ba…rigan bacci kawai ya dauko ya sa Mata tareda gyara Mata kwanciya…ya lullubeta ya Mata addu’a snn ya kashe Mata wuta ya fita.
(Asuba ta gari babyn daddy😁).
Ramla bata haihuba sai wurin 2 na dare…ummi taso kiranshi a Daren Amma tace Bari zuwa Safiya tasan yanxu bacci yakeyi…
Washegari…
Bayan ya dawo daga masallaci ya dauki wayanshi ya shiga Kiran ummi…nan take sanar dashi good news ta sauka lfy..snn an samu baby girl…a lokacin yace gashi nn zuwa…ko wanka bai tsaya yi ba yasa kaya kawai ya fita…lokacin da yaje an gama musu komai sallama kawai suke jira…da kanshi yaje office din doctor ya amso sallama snn yazo yace an sallamesu…mijinta dake wurin da wata aunt dinshi sukace zasu tafi da ita gida zasu kula da ita a can tunda haihuwan fari ne…ummi ta roki alfarman a barta ta tafi da ita…haka suka daukota suka nufo gida mai gidanta Kuma yayi alkawarin zai biyosu da kayanta Dana baby.
Wannan knn
STORY CONTINUES BELOW
Mai jego da baby na samun kulawa sosae wurin ummi…umma itama Saida akai kwana ukku da haihuwa tazo…kusan kullum sai anyi rigima da Layla kan daukan baby amma ummi Sam zatace baza’a bata ba wai ba wani hankali gareta ba😹
Yau ma kmr kullum umma nayiwa jaririyar wanka…ummi Kuma na gefe tana ninke kayan babyn da aka wanke…for the second time Layla ta sake cewa”kinji ummi Dan Allah ki bani in dauketa ko na minti 5 ne”…ummi ba tareda ta kalleta ba tace”sai kiyi Kuma ai yarinya…ba mahaukaciya nakeba da zan dauki yarinya sabon haihuwa in baki kije ki wurgar Mata da ‘ya”…yanxu ummi nice zakice bazan iya daukan baby ba…shekara na 17 amma ace bazan iya daukan jariri ba”..Layla ta fada tana turo baki…ummi Kam banza Tai da ita taci gaba da abinda take…umma data gama yima jaririyar wanka ta mikama ummi tana fadin”ai tsakaninki da Layla sai Allah Yaya…yanxu mutum na shiga Zaku bashi kunya..da nace dai kiyi hakuri ki barta ta dauketa mana”….ummi ta tabe baki tace”ai sai kuyi”snn ta amsa yarinyan ta sa a bayanta ta goya…Layla sai ta fara hawaye(abunku da ta6ararriya)…ita kanta Ramla dake zaune kan gado tana sauraren su dariya suka bata…ta juya zata fita sai ga Taheer ya shigo dakin…sai ta fasan fitan taje ta fada jikinshi tana kuka….yasa duka hannayenshi ya rungumeta Yana shafa bayanta idonshi a kan Ramla yace”waya tabamin ita?…ba tareda tayi mgn ba ta nuna ummi da hanunta tana kokarin boye dariyan dake son kufce mata….ya wani rausayar da kai a shgwabe yace”ummi mana…laifin me tayi don Allah…you could’ve told me…ni nasan yanda zanyi daita…banson kukan nn nata wlh”….ummi ta zabga mai harara tace”sannu shugaban marasa kunya…ai ba tsoronku na faraji ba da zan dauki jaririya sabon haihuwa in ba Layla ta dauka…haka kawai taje ta doka musu yarinya da qasa tasa mukhtar ya kullacemu”…Taheer bai sake mgn ba Saida ya zauna kan kujera ya zaunar da ita kusa dashi still tana jikinshi…wnn karon maimakon ummi sai ya maida kallonshi ga umma yace”umma a bata ta dauka mana pls…rikewa fa kawai zatayi ba wani wurin zataje da itaba…umma na dariya tace”sha’anin Yaya ne sai Allah Taheer…ba yanda banyi ba ta bata yarinyan ta dauka ko a zaune ne amma taki….Ummi ta mike zata bar dakin tace”sai kuyi tayi ai…kema Aisha na fuskanci har yanxu akwai sauran kuruciya tareda ke…in ba hakaba Ina Zaki goyi bayan a bama ta6ararriyar yarinyar nn jaririya ta dauka…Laylan da ko jikinta ma da kyar take daukanshi tsabar son jiki…wnn duk ya gama ta6ar6arata wlh(tayi pointing Taheer da hannunta)…Allah dai ya fiddamu kunya a wajen yaron nn Usman… InshaAllah bazaiga laifina ba saidai yayita ganin na uban…Allah ya shiryeku….tana gama fadan haka ta fita a dakin abunta….umma ma ta mike tareda kwashe kayan da tayima baby wanka duk ta kaisu inda ya dace snn ta fice tana dariya….Taheer yakai dubanshi ga Layla da har yanxu ke kuka a jikinshi…cikin sigan lallashi yace”kukan ya isa haka mana baby…kar ki damu ni zan dauki yarinyan da kaina in baki ki dauka so ki dena wnn kukan kinsan banaso…Saida ta share hawayen snn ta dago tana kallonshi tace”daddy wai ummi fa har yanxu kallon kid takemun…ya zaai ace bazan iya daukan jaririya ba sai kace mahaukaciya…Taheer yai murmushi yace”don’t mind her tanaso ta saki kuka ne kawai…snn tazo tana ce maki ta6ararriya….ki dena biye Mata kinji…ta daga mai Kai a hankali…ya mike itama ya mikar da ita tsaye suka fita daga dakin…Ramla ta bisu da kallo kawai zuciyarta na Mata sake sake.
Ana gobe suna mutanen porthacourt suka iso…nan gida ya sake kacamewa…da yawa daga family dinsu ma na kano duk sun iso.
Ranar suna yarinya taci suna Nasreen…mijinta yayi rawar gani sosae hakama ‘yan uwanta dana mijin nata.
Bayan kwana biyu…
Zuwa yanzu mutane duk sun koma…Nafeesa kawai ya rage da yaranta suma Kuma gobe zasu tafi…mama hauwa da umma na kitchen sunata girke girke don babban bako zasuyi daga Dutse…Usman ne zaizo ganin amaryar sa🤪tunda Taheer yaji lbrin zuwan nasa dama yasa a ranshi yau duk bazai zauna a gidan ba…tun safe ya fita ko gaisawa da iyayen baiyiba…ummi sai mita take wai sirirkinsa zaizo kuma ya kama hanya ya fice(Niko nace ummi ai ba sirikinshi bane rival dinshi ne😆).
Nafeesa da mai gidanta wato mahaifin Layla duk sunyi farin ciki da jin batun Usman din da Layla…sedai Allah ya tabbatar da alkhairi.
4:00pm daidai Taheer ya shigo cikin gidan…sakamakon kiranda ummi ta ringa rafka mai kan yazo su gaisa da Usman kafin ya wuce…Kai tsaye part dinshi ya wuce…mamaki ya kamashi ganin kofar parlonshi a bude…kodai a bude ya tafi ya barta?…bai sake kawo komai a ranshi ba ya shiga ciki…abinda ya gani ya sashi sandarewa a nan inda yake…tareda zura musu ido kmr ba gobe….Layla ce zaune kan one seater…tana sanye cikin dogon riga na material…bata daura dankwali a kanta ba sai mayafi data Dora a kan…Usman Kuma na zaune gefenta hanunshi rikeda glass cup mai daukeda drink yana kokarin kaiwa bakinta….zuciyarshi yaji tayi wani bugu da karfi…sai Kuma ta koma ta cunkushe a wuri daya…yanda zuciyarshi ta cunkushe hakama ranshi gaba daya yaji ya cunkushe…yanata kokarin ya bude baki yai mgn amma ya kasa….he never thought haka akeji idan akaga masoyi tareda wani sai yanxu….zuciyarshi zafi takemai yanajin tamkar ya karasa ya shake Usman har sai ya Dena numfashi…how dare he trying to feed her…how dare he”
Da sauri Usman yaja baya tareda sukuyar da kanshi kasa….ba karamin kunya yaji ba…ita Kuma Layla mikewa tayi zuwa gareshi tana mai murmushinta me kyau tace”welcome back my daddy….tun dazu ummi ke nemanka….Saida ya tattaro sauran jaruntan daya rage mai kaff snn Yana kakalo murmushi yace”actually…I…I was occupied with work ne a office so bansan time ya wuce haka ba….Usman ya taso daga inda yake yazo ya durkusha a gabanshi…still idonshi qasa yace”barka da yamma daddy…fatan mun sameku lfy”…a hankali yace lfy qlou Usman ya su alhaji da hajiya?….ya amsa da suna nn lfy..duk suna gaisheku…..”MashaAllah”kawai ya fada snn ya juya ya fita daga dakin kmr ana tunkudashi….part din ummi ya nufa don yasan ko ya bar gidan ma ummi ba Dena kiranshi zatayi ba…duk suna zaune parlor da gudu su Al’ameen sukaje suka rungumeshi suna mai oyoyo….ya hadasu ya rungume gaba daya a jikinshi yanajin yanda har yanxu heart beat dinshi bai koma normal ba.
Ya karasa parlon ya nemi wuri ya zauna gefen nafeesa ya jingina jikin kujeran tareda lumshe idanunshi….bai San tsautsayin daya kaishi part din nashi ba yasan for sure abunda ya gani bazai taba gogewa cikin zuciyarshi ba.
Nafeesa na kallonshi cikeda tsokana tace”my big barchelor bro how far”…ya bude ido yana hararanta snn yai kokarin daidaita kanshi yace”yarinyar nn kin rainani wlh….kika sake cemin barchelor saina Kira mijinki nace mai ya Kara aure dama ke kin fara zama cus”….Nafeesa ta zaro ido tana dariya tace”ai ba tsoron kishiya nake ba…don Allah ka kirashi ka fada mai din kaga idan bai gwasaleka ba”…ya girgiza Kai kawai snn ya sake lumshe idon tareda komawa yai luff a jikin kujeran…nafeesa ta bishi da kallo snn a nutse ta fara mgn”let’s keep joke apart bro Allah ya kamata kasan me kake ciki…it’s high time u settled down with your own family….Ina mgnr Wanda ummi ta fadamin??da sauri ummi tace”kema dai kya fada mai nafisa maybe ke yaji naki mgn….tuntuni nace zanje kano in sanar da kawunshi yazo kan mgnr auren Amma kememe Dan nn ya hanani.A hankali ya daga jajayen idanunshi ya sauke kan ummi…kmr zaice wani abu sai Kuma ya sake maida idon ya lumshe…umma ta Dan harari nafeesa tace”ke ba ruwanki dashi…kar Kuma ki sake irin wnn mgnr a gaban yara”…kema yaya kiyi hakuri a bar mgnr nn haka don Allah…Ni zanyi mgn dashi da kaina amma as for now ku kyaleshi yaje ya huta can’t you all see he’s exhausted?…ummi dai batace komai ba…umma ta mike zuwa inda yake ta kama hanunshi tana fadin”stand”…ba musu ya mike sai kawai yaga ta fara janshi har zuwa dakinta.
Ta maida kofa ta rufe bayan sun shiga dakin snn ta karasa gefen gado ta zauna tareda zaunar dashi a gefenta…idanunta a kanshi tace”fadamin Taheer…what exactly is wrong with you?..
Da mugun mamaki ya dago yana kallon umma…Allah dai yasa ba asirinshi ne zai tonu ba….yanzu idan umma ta gane ya zaiyi da ranshi…umma ta katseshi tana cewa”yane Ina mka mgn kayi shiru Taheer…kafiso in barka da Yaya koh…a hankali ya girgiza Mata Kai snn a hankali yace”umma ba abinda ke damuna fa…it’s only stress Kuma da zaran na samu hutu I’ll be alright”…umma na mai kallon tuhuma tace”karya kakeyi Taheer…abinda nakeso ka sani shine….the earlier you said abinda ke damunka the better for you…na tabbata idan nayi rantsuwa wani abu na damunka bazanyi kaffara ba…amma tunda you can’t share it with me shknn…a hankali ya matso jikinta tareda dora kanshi kan kafadanta kawai sai hawaye sharr ya shiga bin kuncinshi….umma ta dafa kanshi jikinta duk yayi sanyi…tausayinshi ya kamata don tasan duk abinda ke damunshi ba karami bane….cikin raunanniyar murya yace”kawai kici gaba dayimin addu’a ummata… InshaAllah I’ll be back to normal again”…umma naci gaba da shafa kanshi cikin sigan lallashi tace”InshaAllah son… amma ka dena wnn kukan Taheer sai kace namiji ba….kayi hakuri kaji…snn ka ragema kanka damuwa don zai iya ja maka matsala”…shi Kam Taheer ji yai kukan na sake tahowa…dama he’s longing for a shoulder to cry on sai gashi Allah ya kawo….Saida ya kwashi almost 30 minutes yana kuka a jikinta snn yai shiru…umma duk tausayinshi ya cikata hadda ‘dan kwallarta itama…she’s wondering wani irin Abu ne zaisa matured mutum kmr Taheer kuka mai tsayi haka…kuka na gasken gaske hadda su majina haka….anya yaron nn ba wani matsalan gareshi yake boyewa ba….Taheer ya katse Mata tunani ta hanyar daga kanshi daga shoulder dinta ya zaro hanky daga aljihunshi yai wiping tears din dake fuskarshi….yasa hanunshi ya kamo nata yana kokarin Dora murmushi a fuskarshi yace”ba komai fa umma…ba wani abu bane”…umma na kallonshi da kyau tace”shknn Taheer…yanxu ka kwanta Bari in kawo ma abinci….da sauri yace”No umma inaso in farayin wanka”…then use this bathroom tunda part dinka akwai baqo”umma ta fada tana pointing bathroom dake dakin…tana kokarin fita yace”umma kayan da zansa fa?…tace”zan aiko a kawo maka”…tana fadan haka ta fita a dakin…wayan Layla ta Kira ta sanr da ita data dakko light kaya ta kawoma Taheer Yana dakinta…ba bata lokaci ta shiga bedroom dinshi ta dakko mai wani well ironed jallabiya ta nufi part din ummi dashi….lokacin umma na kitchen tana kokarin hada mai abinci…su ummi Kuma har yanxu suna parlon…Layla na kallon Al’ameen dake game a gefe tace”Ina daddy na yake?…”dakin umma”… Al’ameen ya fada hankalinshi na kan wayanshi….ba bata lokaci Layla ta nufi dakin umma…shiganta yayi daidai da fitowanshi a wanka…Yana tsaye gaban mirror yana goge jikinshi…ta sunkyar da kanta da sauri tace”am sorry daddy…umma tace in kawo mka wnn”…ta nuna jallabiyan dake hanunta…bai ko kalli inda takeba yace”drop it”ta karasa ta ajiye gefen gado tana kallonshi zatayi mgn yace”get out”…Tai tsaye cak tana kallonshi kmr wata sokuwa…ganin taki tafiya ya juyo a fusace yana kallonta yace”ki 6acemin da gani nace”…kawai saiga hawaye…dama tasan hakan zai faru…ba yanda batayi da Usman kan bataso ya bata drink din a baki ba amma yaqi…yanxu gashi zai ja mata matsala wurin daddy….a hankali ta fara tafiya zata zauna gefenshi kawai ya mike ya kama hannunta tareda bude kofa ya turata waje cikin muryar gargadi yace”kar ki sake dawomin nan…I want to be alone”….yana gama fada ya koma dakin snn ya maida kofa ya rufe…Layla sandarewa tayi a wurin stabar mamaki…yanxu ita daddy ke treating haka sai kace stranger…wasu hawaye suka sake wanke mata fuska…tanajin footstep alaman ana tahowa ta nan wurin tayi saurin goge tears din nata…umma ta karaso tana kallonta tace”ke me kikeyi a nn wurin har yanxu?..”ba komai umma…dama yanxu zan tafi..tana gama fada ta bar wurin da sauri…umma tabita da kallo.+
STORY CONTINUES BELOW
A gefen gado umma ta sameshi sanyeda jallabiyan da Layla ta kawo…yana ganinta ya saki murmushi snn ya tashi yana kokarin amsan tray din dake hanunta ta hanashi…Saida ta janyo table ta Dora tray din a Kai snn ta shiga zuba abincin a plate…yana kallonta har ta gama ta zuba drink a cup snn ta dago ta kalleshi tace”oya yi sauri kaci abinci son…nasan hadda yunwa ke damunka…ya karkatar da kai a shagwa6e yace”saidai kiyi feeding Dina umma…I don’t feel like eating”…murmushi kawai umma tai snn ta dauki spoon ta shiga bashi abincin a baki…ci kawai Taheer yake ba don yanajin dadin abincin ba…bai so ya bata mata rai ne kawai….ya danci kusan rabi yace mata ya koshi…ta dauko drink data zuba a cup ta nufi bakinshi dashi…ya lumshe ido zai sha kawai scene din dazu ya dawo mai… exactly yanda Usman ke Shirin bama Layla a baki…kawai sai ya dauke dai da sauri Yana salati…da mamaki umma ke kallonshi tace”Kai lfynka kuwa”…ya Dan shafa Kai yace sorry umma…kaina naji ya saramin…tace karbi kasha sai ka samu ka kwanta…baiyi musu ba ya amsa drink din…umma ta tattara kayan zata fita tace”ka kwanta ka samu hutu dn Allah…kar ka kuskura in ganka a parlor sai lokacin sallahn magrib…yana murmushi yace Mata”an gama ummata”tayi murmushi itama snn ta fita tareda rufe mai kofan…Taheer ya kwanta kan gadon tareda lumshe idanu…”I really am lucky to have u as my second mom..I love you ummata”ya fada a hankali.
Kmr yanda umman ta fada bai fito ba sai da aka Kira sallahn magrib…ya shiga bathroom ya dauro alwala snn ya fito…wnn karon ba kowa a parlon da alama duk sunje yin sallah ne…don haka direct ya wuce masjid.
Bai dawoba sai da akayi isha’a…ya samu gaba dayansu a dinning zasu fara dinner…umma ta karaso kusa dashi tareda kama hanunshi tace”dama yanxu nake Shirin kiranka…muje kaci abinci”baiyi Mata musu ba ya bita zuwa dinning din…da kanta tayi serving dinshi ta Mika mai snn ta zauna itama ta faracin nata…Layla duk hankalinta na kanshi…wani irin tsoronshi taji ya diran mata don bata taba ganin bacin ranshi a kanta irin Wanda ta gani dazu ba….ummi ce ta lurada Layla bacin abincin take ba tace”ke lafiyarki kuwa…ya kowa Yana cin abinci ke kin zauna kina tunani….a hankali Layla tayi qasa da kanta kawai sai ta fara hawaye…da mamaki ummi tace”lfy…meke damunki?…Saida ta saci kallon Taheer snn tace”ummi don Allah kice yayi hakuri…ni bazan Kara ba”…sakato ummi tayi tana kallonta kafin ta maida idonta kan Taheer din dake ta faman cusa abincin gabanshi irin bai da wani damuwan nn….”kai…meya hadaka da Layla?..tambayan da ummi tayi mai knn…ya dago Kai Yana kallon ummin a nutse yace”ba abunda ya hadamu mana ummi…laifin me zatayi min ni….da sauri Layla ta sake fashewa da kuka tace”don Allah ummi nidai kice yayi hakuri…wlh fushi zaitayi Dani na sani….ummi tace”to me kika masa da zaiyi fushi dake…kema ki kyaleshi mana yaje yayita fushin nasa…ya dade baiyi fushi dakeba mugu kawai”…gaba daya occupants din dinning din kallonsu kawai suke…Layla kuwa sai aikin kuka…umma na duban Layla itama tace”sai ki fadi laifin da kikai masa…don nasan haka nan Taheer bazai dauki fushi dakeba”…a fusace ummi tace”yo ai ba fada zatayi ba Aisha…wlh ko zaki shekara kina tambaya ba fada zatayi ba…shima Kuma ba fada zaiyi ba ko kin tambayeshi…haka suke wnn munafurcin…duk Taheer ya 6ata ‘yar nan da gulma da munafurci wlh….dariya kawai umma tayi snn taci gaba da cin abincinta…nafeesa na dariya itama tace”ummi baki saniba ko laifi tayi mai…nasan haka kawai bazai dauki fushi da Layla ba yanda akeji da ita din nan”…”may Allah bless you”…Taheer ya fada yana goge bakinshi da tissue…ummi Kuma ta tabe baki taci gaba dacin abincinta.
Taheer ne ya fara mikewa…umma na dubanshi tace”badai har ka koshi ba son?…ya langwabar da kai Yana shafa tummy dinshi yace”na koshi Mana umma…kinsan ban jima dacin abinci ba”…ta jinjina Kai snn tace”alright kaje…zanzo dakin naka muyi mgn”ya amsa da toh snn ya ma kowa good night ya bar wurin…Layla ta bishi da kallo don ita kadaine bai cema Saida safe ba ya wuce abinshi…ta sake rushewa da kuka kmr Wanda akama mutuwa snn ta mike a guje tayi dakinta(wnn yarinyan ta cika ta6ara da yawa wlh😏haba komai kuka sai kace jaririya)
Kamar yanda umma ta fada ta samu Taheer a part dinshi…Yana zaune parlor yana kokarin Kiran Sameera don misscalls kusan 10 ya gani nata umma ta shigo….ya ajiye wayan a gefe Yana kallonta da murmushi yace”umma kece?…Saida ta zauna kusa dashi snn tace”nice mana Taheer…ai nace maka zanzo”… ya jinjina Kai alamar hakane snn ya maida hankalinshi gareta…cikin zuciyarshi Yana addu’a Allah yasa ba asirinshi ne zai tonu ba…Sam bayaso kowa yasan Yana kaunar Layla don abun kunyane a gareshi…”inaso ka fadamin tsakaninka da Allah meya hadaka da Layla”mgnr umma ta dawo dashi daga tunanin da yake…ya dago yana dubanta a rikice yace”umma cewa tayi nayi Mata wani abun ne?…umma na girgiza Kai tace”bata fadaba…amma na tabbata akwai laifin da tayi maka…Taheer yai shiru kawai yana tunano abunda idanunshi suka gane mai dazu…umma ta dafa shoulder dinshi tace”bai kamata kana fushi da ita ba irin haka…kasan dole hakan yai affecting dinta don ba haka ka sabar Mata ba…it’s better kayi mata fada if possible ma ka zaneta…ai she’s your kid…ba Wanda zaiyi questioning dinka don tayi laifi ka mata hukunci”….da sauri ya dago yana kallon umma…har cikin ranshi yaji kalmar duka data ambata…sai Kuma ya shiga girgiza kai yace”umma ni…ni Taheer kike ganin zan iya daukan hannu na in zane baby dashi?…no…never…umma wnn abune wanda ko a mafarki ban jin zai iya faruwa so ki dena ma mgnr duka plss…babu laifinda zatamin ince zan daga hannu in dora a jikinta da sunan duka…bazan ma iya bane”….shiru umma tayi tana kallon yanda duk ya gigice kawai sbd tace ya daketa…cikin zuciyarta kuwa tunani ne kala kala…to kodai yaron nan son Layla yakeyi ne?ta tambayi kanta sai Kuma da sauri ta kawar da tunanin tace”it can never be possible…ya akai ma nayi wnn tunanin…hanunshi da taji ya riko nata yasa ta dawo daga tunani da take ta dubeshi…yana murmushi yace”umma wnn mgnr a barta for God sake…kema ki manta kawai kije kiyi baccinki it’s getting late”…bata sake cewa komai ba tayi murmushi kawai snn ta mike tana kallonshi tace mai”to Saida safe”ya amsa da Allah ya tashemu lfy umma…Yana binta da kallo har ta fita….ya sauke ajiyar zuciya tareda jingina jikin kujera yana tuna maganganun umman…”wai in zaneta”kam duk ranar da hakan ya faru nasan nima for sure saina Zane kaina…Allah ma ya kiyaye.
Washegari….
Flight din 10 Usman yabi…don bai samu tafiya jiyaba ummi tace ya kwana kawai tunda dare yayi…nan ya kwana a boy’s quaters… first thing in the morning yai sallama dasu ya tafi…ba tareda yayi sallama da Layla ba…don baccin karya tayi tanajinshi taki fitowa…a cewarta shine Wanda ya hadata fada da daddynta.
Da yake su Nafeesa jirgin 2 zasubi so Usman ya rigasu tafiya.
Taheer ma bai fitoba sai around 1 lokacin ya gama shirinshi tsaf..Yana saukesu airport zai wuce clinic coz he’s on evening duty today…bayan ya dawo daga masallaci ya nufi cikin gidan…sun gama shiryawa…don haka aka Debi kayansu aka kai mota…shima ya gaisa dasu ummi yace su Nafeesa su zo ya kaisu akwai patients da zai duba by 2.
Bayan sun gama sallama da koke koke finally dai suka shiga mota aka tafi…Layla na zaune front seat sanyeda zumbulelen hijabinta…fuskanta ya kumbura sosae sbd kuka…hankalin Taheer ba karamin tashi yayi da ganin yanda fuskan nata ya komata…dukda har yanxu bai huce ba amma tausayinta yakeji sosae…bayason abunda zai bata ranta Sam…har suka isa airport ba wani walwala tattare dasu…bayan sun gama fitowa a mota…Nafeesa na kallonshi tace”to bro mu zamu tafi sai ranan da ka kiramu Kuma”…yadan bude ido yace”rananda na kiraku Kuma?..tana dariya tace”Ina nufin muda mu dawo sai bikinka…Dan Allah bro ka daure dai kayi auren nn ko don ummi”ya Dan kakalo murmushi yace Mata”karki damu yarinya…very soon zaku sake dawowa InshaAllah”tana murmushi ta jinjina kai tace”Allah ya yadda…and for your information…wannan(ta nuna Layla dake tsaye gefe)itace yarinya badai niba…yara ukku gareni so mind you ka Dena Kiran wnn sunan”…dariya kawai Taheer yai snn yace”naji…Bari inzo in wuce banso lokaci ya kure ban isa ba…Allah ya saukeku lfy…ta amsa da ameen sai munyi waya…sukayi sallama da Layla snn suka nufi waiting area…su Kuma suka shiga mota suka tafi.Ko a hanya ba Wanda yace kala…ita Layla tana Satan kallonshi…Kuma tanaso tamai mgn amma ta kasa…da kyar tayi gathering courage tace”Daddy”..ya Mata banza yanaci gaba da driving dinshi…ta share hawayen idonta a hankali ta sake cewa”daddy plea…maganan ya kakare sbd wani wawan burki da taji yaja…ta shiga waige waige taga suna gefen titi snn ta dawo da kallonta gareshi…kallon nata yake shima fuskan nn a tamke…saika rantse bai taba dariya ba…a kausashe ya fara mgn”I think I’ve told you…I’ve worned you kar ki sake yimin mgn…for as long as am concern bamu hada komai dakeba…so stay away from my life…and am staying away from yours too”..da sauri ta shiga girgiza kai tana sake fashewa da kuka…tama kasayin mgn…shi Kuma ya kunna motan snn yaci gaba da tafiya…yanaji tanata kukanta baice Mata kala ba har ya isa kofar gidansu…yai parking nan waje ba tareda ya kalleta ba yace”you can go”…ba tareda ta kalleshi ba itama ta bude motan ta fita da gudu…daidai zata shiga gidan tayi tuntube da gate din ji kake timm ta Fadi a kasa…mai gadi dake gefe Yana kallonta ya taho da sauri yana salati…yana Shirin dagata Taheer daya iso wurin shima da gudu yace”don’t touch her”…a tsorace mai gadi yayi baya ya shiga zare idanu yana kallon Taheer din…bai taba ganinshi cikin yanayi irin wnn ba…shiko Taheer daukanta kawai yai yayinda taketa rusa kuka ya nufi cikin gidan da ita…ummi ta mike da sauri tana kallonsu tace”na shiga uku ni Maryam…me zan gani haka…Taheer meya sameta?…baice Mata kala ba ya nufi dakin Layla…kan gado ya ajiyeta tareda daga kafanta yana dubawa…he’s praying Allah yasa bataji ciwo ba…ya kwashi kusan 15mins yana examining jikinta ganin ba wani ciwo ya ajiye Mata kafan a hankali snn ya fita…part dinshi ya koma ya dauko pcm ya dawo…a parlor yaci karo da Mama hauwa…tana fara’a tace”aah likita zaa tafi wurin aikin ne?..yai Dan murmushi yace”tafiya zanyi wlh mama…gashi na kusa makara ga wnn…ya Mika Mata maganin hanunshi snn yace”ki taimaka ki mikama baby pls..kice Mata lallai ta tashi tasha yanxu sai ta koma ta kwanta”…mama hauwa ta amsa tana fadin”yanxu kuwa zaa Kai mata likitan likitoci…Allah ya tsare”ya amsa da ameen Yana murmushi snn ya juya ya fita…ita Kuma ta nufi dakin Layla don ta isar da saqo.+
Kwana biyu umma ta Kara snn ta koma kano ba don ummi taso ba haka ta kyaleta ta tafi.
Bayan Sati uku…
Yanxu Ramla nada sati hudu knn da haihuwa…inda a gobe suke Shirin tafiya kano gaba dayansu…ita Ramla idan taje sai ta cika kwana 40 da haihuwa snn zata dawo yayinda ita Kuma ummi zataje kan mgnr neman auren Taheer da takeso kawunsa yazo ya nema mai…dole ummi tasa Taheer daukan leave na one week a office don da farko cewa yai shi bazaije ba…ita kuwa Layla ba wani farin ciki take da tafiyan ba sbd yanda har yanxu Taheer bai bar fushi da itaba.
Suna zaune parlor gaba dayansu da daddare…ummi na kallonta tace”iceko dai kin gama hada kayanki Layla…banaso sai gobe kizo kina cewa bakiga kaza ba ko kin manta kaza”..a hankali Layla ta daga Mata Kai tace”na gama tun dazu ummi”…toga abincin Taheer can dauki kije ki Kai mai naga har yanxu bai shigo ba”…ba musu ta mike zuwa inda abincin nashi yake ta dauka snn ta tafi..a zuci take addu’ar yau dai Allah ya dorata a kanshi ya saurareta.
Bata ganshi parlor ba don haka ta ajiye abincin snn ta nufi bedroom dinshi.. Saida tayi sallama a bakin kofan ya amsa snn ta bude kofan ta shiga ciki…Yana zauna kan gado da system a gabanshi ya tattara hankalinshi gaba daya kanta..da alama abu mai muhimmanci yakeyi a ciki….a sanyaye Layla ta karasa ciki ta zauna kan bedside kanta a kasa tace”daddy ummi ne tace in kawo maka abinci”..ya Dan kalleta ta gefen ido kafin yace”ohk”…a hankali ta baro inda take tazo tayi kneeling a gabanshi tana hawaye tace”daddy Dan girman Allah kayi hakuri…wlhy ba laifina bane”ba tareda ya kalleta ba yace it’s ohk…ya riga ya wuce ai”…ta shiga girgiza kai tace”wlh daddy nasan baka hakura ba…kullum haka kake cewa amma baka dena yin fushi Dani ba”…a hankali ya ture system din dake gabanshi tareda saukowa daga gadon Yana kallonta yace”ba damuwa kije abinki…nace maki ya wuce koh”yana gama fadan haka ya juya zai shiga toilet…Layla ta mike da sauri zatai hugging nashi yace”Maryamm”…cak ta tsaya tana zaro ido…tun tashinta zata iya irga sau nawa ya kirata da sunanta…ko Layla baya fada amma yau shine ya kirata da”Maryam”…tasa hanu ta toshe bakinta kar kukan dake cinta ya fito snn ta juya da sauri ta fita daga dakin….Taheer kasa shiga bathroom din yayi…ya koma gefen gado ya zauna tareda dafe kanshi da hannu bibbiyu yanajin yanda zuciyarshi ke tsalle tana bugawa kmr zata bar kirjinshi…yasan abinda yake ba daidai bane Amma ya kasa Bari…dukda tausayinta dake cinshi kullum amma da zaran ya tuna zata auri wani zaiji kaman zai zauce…harda wnn dalilin yasa ya kasa sakin jiki da ita bayason abubuwan dayake ji a zuciyarshi gameda ita…kmr Wanda akama allura ya mike zumbur tareda ficewa daga dakin…direct ya nufi part dinsu…ba kowa parlor don haka ya wuce dakinta.
STORY CONTINUES BELOW
Tana kwance tana rusan kuka kmr zata shide kawai taji yasa hanu ya dagata zaune…da mamaki ta tsaida kukan tana kallonshi…sai kuma ta shiga murza idonta wai ta tabbatar ba mafarki take ba…ganin shi din ne yana Mata murmushi ta fada jikinshi tareda fashewa da matsanancin kuka…a hankali Taheer ke shafa bayanta yanajin kukanda take har cikin brain dinshi…Saida tayi me isarta snn ta dago ta bude baki zatayi mgn yai saurin dora yatsanshi a kan bakin yace Mata”shishshssh…don’t say anything okay?…just relax kiyi baccinki…we shouldn’t talk about it at all…not now not ever…banason jin mgnr kwata kwata”…a hankali ta daga mai Kai snn tace”Amma daddy ka denayin fushin Dani?…zaka koma yanda kake a da?…yai murmushi ya shiga share Mata tears din fuskarta yace”ni dama ba fushi nakeyi dake ba baby…wnn daddyn(yayi pointing kanshi)bazai taba iya fushi da wnn babyn ba”(itama yayi pointing dinta)…Layla batasan sanda wani kyakykyawan murmushi ya subuce Mata ba…ta sake rungumeshi tace”na gode sosae daddyna…I love you”…Saida ya lumshe ido snn ya bude don dadi…he wish I love you din nn ba a matsayin daddy take fada mai ba…a matsayin hubby yakeso yaji tace I love you din nan…da hakan zai faru ko da baisan farin cikin da zai samu kanshi a ciki ba…a hankali yai breaking hug din tareda kwantar da ita…ya lullubeta tareda yi mata peck a goshi…yana murmushi yace Mata”to Saida safe”…a hankali ta amsa mai da good night snn ta lumshe idonta..shi Kuma ya kashe mata hakse snn ya juya ya fita…he’s feeling extraordinary happy…shima duk sanda yake fushi da ita tamkar Yana fushi da kanshi ne…bai taba samun peace of mind har sai an shirya…Yana zuwa daki ya fada bathroom yai wanka tareda Shirin bacci snn ya kwanta..aiko nan da nan baccin daya jima bai samuba yayi gaba dashi.
(Umh asuba ta gari daddyn baby😜)
Washe gari da wuri suka kammala shirinsu.. driver ya kwashesu sai airport…basu bata lokaci sosae ba kuwa suka shiga jirgi sai Kanon Dabo✈️
Sun sauka a gidan umma…bayan an huta anci abinci…sai aka dasa hira a nan parlor..shikuwa Taheer ficewa yai zuwa wurin wani friend dinshi.
The following day bayan sunyi breakfast sunyi wanka…gaba dayansu suka nufi Sallari gidan qanin mahaifin Taheer mai suna Alh Adam Jakada.
Bayan sun sauka an gama gaggaisawa ummi ta sanar dashi abunda ke tafe dasu…yayi farin ciki sosae ya Kuma tabbatarwa ummi cewa zaizo Abuja next week zaaje ayi mgnr auren Taheer kmr yanda ta bukata…su ummi nata murna amma Taheer abinda yakeji is not close to murna at all…Sam bayajin dadin ma mgnr.
Sun jima a gidan don sai wajen 4 snn suka koma gida…Taheer ya sanar da ummi kan zasuje Danladi Nasidi shida Layla..gidan wata cousin sis dinshi mai suna Amina Aminu Kibia…’yar qanwar dad dinshi ce and ba karamin shiri sukeyi da itaba.
Suna tafe a hanya duk inda sukazo sai ya fada Mata sunan unguwan haka har suka isa Danladi Nasidi.
Daidai kofar gidan Sis tashi yai parking snn ya dau waya ya shiga dialing number dinta..Allah yasa bataje wurin aikiba don bai sanar da ita he’s coming ba..he wanted to surprise her… ringing biyu tayi picking call din tace”doctor yau an tuna dani knn”…Taheer yai Dan dariya snn yace”yanxu dai kina Ina?..tace Ina gida wlh..yau Ina off”…bai sake cewa komai ba kawai yai hanging wayar…ya kalli Layla yace”let’s go tana ciki”..ya bude motan ya fita snn itama ta fito suka shiga cikin gidan…daidai entrance din gidan suka tsaya…Taheer ya danna doorbell…ba’a dau lokaciba wata yarinya tazo ta bude musu kofan..”sannunku da zuwa”yarinyar ta fada snn ta basu hanya suka shiga ciki…Saida suka zauna a parlor yarinyar ta gaishesu snn tace Bari in kirata…ba bata lokaci sai gata ta shigo parlon…kyakykyawa da ita tanada dan qiba amma ba sosae ba fuskanta dauketa fara’a sosae ta karasa ta zauna idonta a kan Taheer tace”dama saida jikina ya bani wlh…inajin ka kashe waya nace maybe you are coming”Taheer yai dariya yace”ai muna kofar gidan nn ma na kiraki…mun shigo gari ne nace gsky bai kamata in koma ba tareda nazo mun gaisa ba…Ina Maimunatou?…Amina na dariya tace”aiko ba karamin kyautawa kayiba wlh…jiya muka gama mgnrka da abban Hanan yace kwana biyu yajika shiru… Maimunatou tana bacci wlh Bari insa Abu ta taso muku ita ku gaisa”…da sauri yace”no a barta tayi baccinta”…Amina na kallon Layla da fara’a tace”baby koh”…Layla dake kallonsu tun dazu tana murmushi tace”eh nice…Ina yini”…lfy Lou baby ya skul…Layla tace alhamdulillah ya Maimunatou…”Maimunatou tana nn qlou wlh… Abu…ta kwalama mai aikinta Kira sai gata ta shigo ta risina tace”gani anty”…Amina tace”ki kawo musu lemuka da abinci snn kije dakin Maimunatou tana bacci ki kawo musu ita su ganta”…yarinyar ta amsa da toh snn ta mike ta fita…Saida ta cika musu gabansu da kayan ciye ciye snn ta tafi dauko Maimunatou…Taheer yai pouring drink a cup ya mikama Layla ta amsa…shima ya zuba a wani cup din Yana sha yace”so yau kina off knn”…Amina tace”wlh kuwa…jiya na gama night yanxu sai nayi off din kwana Hudu snn zan juya evening…ya aiki..yasu ummi”…yace”aiki alhamdulillah ana nn ana fama wlh…ummi itama tana nn kano…tana Janbulo gidan qanwarta…tace tana gaisheki sosae”…Amina tace”Allah sarki ummi Ina amsawa wlh…Ina nn zuwa Abuja ai Amma sai bikinka”Taheer yadan harareta yace”aiko Zaki dade baki jeba yarinya”…daidai nan mai aiki ta kawo musu Maimunatou…Taheer ya karbeta yana kollonta yace”MashaAllah…kiga yadda yarinyar nn tayi girma…kmr su daya da babanta”.. Amina na dariya tace”ai Maimunatou akwai saurin girma…duk Wanda ya ganta sai yace tayi girma”…a hankali Layla ta taso daga inda take ta matso kusa dashi tana murmushi tace”daddy Dan bani in dauketa nima please…yarinyan tamin kyau”..ba musu Taheer ya Mika Mata Maimunatou ta karba…tayi shiru kawai tana kallon yarinyar kyakyakyawa da ita…su Kuma sunata hirarsu…basu suka bar Danladi Nasidi ba sai after magrib…shima da kyar Amina ta barsu suka tafi don cewa tai saiya jira mijinta ya dawo sun gaisa…ta cika Layla da kayan mk up su turaruka snn ta rakosu har mota suka tafi.
Washegari suka sake fita yawo hadda umma da ummi…Ramla cedai batajin dadi ta zauna a gida tareda mai aikin umma…sunje parks da dama snn sukai shopping daga karshe suka koma gida.
First thing in the morning driver ya kaisu airport suka wuce Abuja.
Yau Monday Layla ta gama shirinta tsaf don yau zatayi post ume…Taheer kawai take jira…shima bai bata lokaci ba ya shirya…ya dauketa suka nufi Baze University bayan sunyi sallama da ummi tana binta da addu’an samun nasara.
Tun a hanya taji cikinta ya Dan fara ciwo har suka isa school din…9 daidai suka shiga exam din…Taheer na waje yana jiranta tareda yi Mata addu’a Allah ya bada sa’a.
After 11 ta fito daga exam din…kmr jira ake ta fito maranta ya kulle sosae…da kyar ta karaso inda yake ta bude motan ta shiga…ya rikota da sauri Yana tambayan meya faru…amma ta kasa mgn…da sauri ya kunna motan suka tafi…don ya manta shaf date din period dinta ya cika.
Basu dade a hanyaba suka isa gida sbd gudun da yakeyi duk ya gigice…yana parking ya kinkimeta yai cikin gidan da ita…taimako ya shiga bata kmr yanda ya saba duk in ta fara period…Saida ta samu bacci snn ya samu yaje masallaci shima…duk ya zama wani kala kmr shine mara lafiyan.
Bayan kwana uku ta warke garass snn shima ya samu nutsuwa…sai a lokacin ya koma normal activities dinshi.Kamar yanda Alh Adam Jakada(uncle din Taheer)yai alqawari yau ya dira garin Abuja…da safiyar gobe Kuma shi da wani friend dinshi dake nn Abuja…sai old friend din mahaifin Taheer din InshaAllah zasuje nema ma Taheer auren Sameera kmr yanda ummi ta bukata.
Daren yau Yana zaune part din mahaifin Taheer…inda a nan ne yake sauka duk yazo Abuja…ummi da Taheer na zaune cikin parlorn suma… Alh Adam na kallon Taheer yace”for the last time ina tambayanka watanni nawa kakeso a sanya maka bikin?…Taheer dake zaune kan carpet idanunshi a kasa yace”kmr nan da shekara ko zuwa da rabi haka”…a tare ummi da Uncle din nashi suka kalli Taheer din…”Kai bakada hanakali ne…are you mad…ya zakace a sa maka biki shekara daya da rabi…what’s your problem?…a hankali Taheer da har yanxu kanshi ke kasa yace”ai ana sawa uncle..har shekara biyu ma ana saw…bai karasa ba uncle din ya katse da fadin”you are not serious…Kai me kake jira da zakace a Sanya maka shekara…akwai abunda baka gama bane?..ka shiga hankalinka Dani wlh…idan bakai auren yanxu ba sai yaushe knn zakayi…you are not getting any younger so in zaka dena wnn mafarkin ma ka dena…ummi dake gefe ta tabe baki snn tace”ai na fada maka dama Alh…indai Taheer ne 6ata mana rai da lokaci kawai zaiyi…ni inta nawa nema nanda wata biyu nakeso ayi bikin…ay shi ya kawota yace zai aureta ba dole akayi mai ba”…cikeda gamsuwa uncle ya girgiza kai snn yace “shikenan…tashi ka tafi”ba musu Taheer ya mike ya fita daga dakin…ummi ta bishi da harara😹
The following day Alh Adam sukaje neman aure gidansu Sameera…an Kuma sa biki next two months kmr dai yanda sukayi da ummi…farin ciki a wurin ummi baya misaltuwa…sai Kiran family and friends take a waya tana sanar dasu ansa bikin Taheer wata biyu…duk wanda ta kira yakan tayata murna snn yayi addu’ar fatan alkhairi.
Ta ko wane bangare murnan sa wnn biki ake…umma ma da taji ba karamin farin ciki ta samu kanta ciki ba… finally Taheer zaiyi aure..Allah ya basu zaman lfy…Nafeesa ma da labarin ya risketa ji tayi tamkar tayi tsuntsu tazo Abuja don farin ciki…haka Layla ma baa barta a baya ba…she’s super happy daddy zaiyi aure…shknn shima daddy zai haifa ‘da ko ‘ya and she can boldly call him/her”kanina ko kanwata”
Bangaren Taheer kuwa baiji dadin sa bikin watanni biyu ba Sam…har ga Allah yaso a sa ko 6 months ne idan ma bazaa sa shekara ba…tun daga lokacin kuma ya zama wani iri…gaba daya baida walwala sosae…Kuma sai karewa yake kmr kudin guzuri…duk ummi na lura dashi amma taki kulashi…ko me zaiyi sai anyi auren nn Bi’iznillahi…Allah ya gani shi ya fara kawota a matsayin wadda zai aura so ba auren dole zaa mai ba.
Suna zaune dinning Layla na kokarin serving dinshi…for the 5th time wayanshi ya sake daukan ruri…a fusace yai picking yana cewa”for God sake menene haka Sameera…idan kika Kira kikaga banyi picking ba Ina wani abun ne and in naga missed call zan kiraki…why kiketa jera min Kira haka sai kace mara aikin yi”… Sameera ta Dan goge hawayen daya zubo mata snn a hankali tace”am sorry”…ba tareda ya sake cewa komai ba yai hanging wayar tareda Jan tsaki…ummi dake zaune parlor tanajin duk abunda ke faruwa ta karaso dinning din tana mai mugun kallo tace”wato bakada kirki ko Taheer…matar taka kake ma wnn ihun kawai sbd ta damu da kai ta kiraka a waya…you are trying to become stubborn koh…to kaci gaba Allah ya baka sa’a…and let me remind you..in har kan mgnr auren nn kake haka…to wallahi kaji na rantse ba fashi…sai anyi auren nn…idan yaso in an daukota an kowa maka sai kayi gunduwa gunduwa da ita tunda baka shirya yin auren ba..shahsasha kawai”…Layla ta dan rausaya Kai tace”Kai ummi…yanxu da girmanshi zakina mai fada irin haka”…tun bata karasa ba itama ummi tace”kinci ubanki kema…komai girman nashi ai bashi ya haifeni ba…nice nan na haifeshi…sbd haka ki kama kanki kema tun kafin in hadaku keda uban naki incicci ubanku wlh…shashasha kema mara kunya..duk sai nayi maganinku wlh…tana gama fadanta ta wuce abinta…Layla ta bita da kallo tana turo baki kafin ta maida kallonta ga Taheer daya dafe Kai da hanunshi…ta dawo kusa dashi tareda kamo hanun nashi ta rike cikin sigan lallashi tace”kayi hakuri daddy pls”..a hankali shima ya dago yana kokarin yin murmushi ya daga Mata Kai snn ya mike kawai ya bar dinning din…direct part dinshi ya wuce ya wulla kanshi kan gado yana sauke numfashi.
STORY CONTINUES BELOW
Ummi na shiga dakinta ta dauko waya ta shiga Kiran umma… ringing biyu ta daga tareda sallama…ko gaisawa basuyi ba ummi ta fara mgn”yanxu tsakani da Allah Aisha abinda kike kinyi daidai knn…asa maki bikin ‘da kusan sati biyu knn amma har yanxu kin kasa zuwa garin nn…abubuwan da suke gabanmu fa yawa ne dasu”…Saida ummi tayi shiru snn umma tace”kiyi hakuri Yaya don Allah…akwai abunda ya tsai Dani Amma InshaAllah wani satin zan shigo”…ummi tadan tabe baki snn tace”shknn Allah ya kaimu..snn ki Kira Taheer ki gaya masa idan baiyi wasa ba bazamu rabu dashi lfy ba a cikin gidan nn…yaro duk yabi ya lalace sai iskance iskance yake tsirowa dasu duk sbd yanaso a fasa biki.. to wlh tun wuri ma ki sanar dashi bazaa fasa bikin nn ba..snn ya shiga hankalinshi dani don idan ya kaini bango ba jin dadina zaiyi ba dagashi har ‘yar tashi wlh”ummi ta karasa mgnr tana huci(easy ummi..ai abun baiyi zafi haka ba😆)umma data gama sauraranta dariya tayi snn tace”InshaAllah zanyi masa fada Yaya..kiyi hakuri zai gyara”…ummi tace shknn Allah ya bamu alkhairi…daga nn ta kashe wayarta.
Two weeks later…
Taheer ya shigo bedroom din ummi sakamakon kiranda tayi masa…ya samu wuri ya zauna kanshi a kasa snn yace”gani ummi”…ba tareda ta kalleshi ba tace”makullin gidanka nakeso ka bani…zan aika a gano min gidan idan akwai bukatar wani abun ayi tun lokaci bai kureba…naga idan na tsaya bi ta kanka batamin lokaci zakayi”…ba tareda ya dago kanshi ba yace”dama yau nakeso inje gidan ummi…ki barshi kawai idan naje sai in duba”…ummi ta kalleshi da kyau snn tace”bana son bata lokaci Taheer…idan kasan bazakayi akan Kari ba ka bani key zan aika a gano min”…yace”InshaAllah zaayi yanda kikeso ummi…kiyi hakuri”…shiru ummi tayi kmr bazatace komai ba….sai Kuma tace”shknn tashi ka tafi”…baiyi musu ba ya mike kafin ya karasa kofa tace”saura Kuma gobe kaje kayi zamanka a clinic…kasan Aisha jirgin rana zata biyo…so make sure kayi picking dinta on time”…yace InshaAllah ummi”snn ya fita a dakin…ummi ta bishi da kallo zuciyarta cike da tausayinshi…Allah ya sani idan tace rashin walwalan nn nashi bai damunta tayi karya… pretending kawai take kmr bai damunta…but Allah ne kadai yasan yanda abun ke damunta…kullum cikin tunanin dalilin wnn damuwan nashi takeyi amma ta rasa…har rama taga yayi cikin kwanakin nn…wani lokacin sai taji kmr zatace idan auren ne bayaso a fasa amma tasan inhar tace hakan to Taheer bai San Annabi ya faku ba…snn Kuma bazai tsaya ya maida hankali yayi auren ba ita Kuma babban burinta shine taga auren Taheer…snn taga ‘ya’yanshi…shi kadai Allah ya bata don haka dole taso ganin jininshi itama…shi kadai gareta.
Karfe 3 yayi ma Taheer a airport…jirginsu umma na sauka ya dauketa suka tafi gida…tun a hanya umma ke tambayan meke damunshi amma amsa daya yake bata shine ba komai…gaba daya umma binshi da kallo takeyi don tasan karya yake yace mata ba abinda ke damunshi…har suka isa gida bata sake tambayanshi ba…ya bude mota ya fito bayan yayi parking itama ta fito…snn ya dauki kayanta suka shiga ciki…ummi da Layla na zaune a parlor…itama umma ta zauna suka shiga gaisawa da ummi…shi Kuma Taheer ya Kai Mata kayan daki Yana Shirin fita a parlon umma tace mai”zo nan Taheer…ai bamu gama mgnr da mukeyi ba”…ya dan rausaya Kai snn yace”umma to ki fara huta gajiya anjima sai muyi mgnr”…tun bai rufe bakiba umma ta mike tana fadin”nida ba mota na biyo ba ai bana tareda wani gajiya…sbd haka ka wuce muje kawai”..Taheer ba don yaso ba ya bita zuwa dakinta…ummi ta bisu da kallo cikin ranta tana addu’an Allah sa Taheer ya fadama umma damuwar shi…Sam batajin dadin ganinshi haka.
Suna shiga dakin umma dake nan fess kmr akwai mutum a ciki…umma ta zauna gefen gado snn tace mai ya zauna shima…ba musu ya zauna…idanunshi a kasa yaji umma tace”yau bazaka bar dakin nan ba saika fadamin mene damuwarka”…da sauri ya dago yana kallon umma snn yace”don Allah umma kiyi hakuri…wlh bazan iya fada ba”…”sbd bani na haifeka ba”.. umma ta fada idonta a kanshi…da sauri ya shiga girgiza kai sai Kuma ya fara hawaye a raunane yace”umma wlh auren nan ne banaso…don Allah kice ma ummi tayi hakuri ta karamin lokaci zanyi auren amma ba yanxu ba”…shiru kawai umma tayi tana kallonshi…yanxu Kam ta fara yadda da mgnr ummi da take cewa Taheer baida lfy…itama ta tabbatar baida lfy din…inba hakaba ya matured namiji kmr shi zaina kuka kawai sbd baison yin aure…Allah ya taimaka ta taho da magungunan da ummi tace a karbo mai…idan yayi amfani dasu da izinin Allah zai samu lfy…shiko Taheer jin umma tayi shiru ya share hawayen da yake snn yace”kinji umma ki taimakamin don Allah”…a hankali umma ta kalleshi snn tace”shknn Taheer zanyi mgn da ita…amma sai ka Dena wnn damuwan snn ka ringa cin abinci…banason ganin wnn ramar…da sauri ya shiga gyada Kai yace zanyi umma…zanyi…just talk to her pls”…umma tace to shknn yanxu kaje in anjima ka dawo akwai abunda zan baka…ya mike tsaye yana goge face dinshi yace”zanzo InshaAllah umma…I love you”.. umma tamai murmushi itama tace”I love u too my son”…tana kallonshi har ya fice daga dakin.
Kmr yanda yayi ma umma alkawari ya dawo bayan sallahn ishaa…suna dakin ummi zaune suna aikin lissafin kayan lefe da suka fara hadawa…ya Kai dubanshi ga Layla dake kwance can karshen gado waya kare a kunnenta tana mgn kasa kasa…ko baa fada ba yasan da Usman take waya…wani abu yaji ya taso ya tokare mai a wuya…sai Kuma ya dauke kanshi a kanta snn ya karasa ya zauna kusada umma yace”umma gani na dawo”…umma ta ajiye pen and paper dake hanunta tace”yawwa dan albarka…tasa hannu ta dakko wani leda a bayanta snn ta Mika mai tace ga wnn…bai musu ba ya amsa Yana kallonta don bai fahimci menene ba…umma ta dubi Layla tace”ke Layla tashi ki koma dakinki kiyi wayan nn…ko kunyarmu bakiji tun dazu kin zauna kina waya a gabanmu…a hankali Layla ta sauko daga gado zata fita…har taje bakin kofa ta fita bata lurada Taheer ba…wani malolo ya sakejin ya taso mai amma yai kokarin dannewa…umma na fuskantarshi bayan Layla ta fita tace”magunguna ne gasu nan na taho maka dasu…akwai bayanin yanda ake amfani dasu…kowanne an rubuta a jikinshi…sai ka fara sha daga yau snn kullum ka tabbata kasha don baa son tsallake kwanaki…cikeda mamaki Taheer ya bude ledan tareda dauko gora daya na maganin ya shiga karantawa…Saida ya gama ya dago Kai Yana kallon umma…ranshi ba karamin baci yayi ba…wato har yanxu kallon mara lfy suke mai knn… zaa wani kwaso magunguna a bashi yasha…duk kallon unable man sukeyi mai knn…kmr zaiyi mgn Kuma sai ya fasa…ya maida maganin ciki snn ya mike kawai ya fice daga dakin…cikin ranshi yake fadin”wai ni mutanen nn sukema kallon incomplete man…ni Taheer sukema kallon unable man…well ku bani auren ‘yarku mana ku gani…anan zaku tabbatar da cewa ni lafiyayye ne.😆
A parlor ya tadda Layla…har yanxu Kuma bata gama wayan ba…tana ganinshi tai saurin ajiye wayan tace”laa daddy dama kana ciki wai?…wlh ban kula dakai ba lokacin da na fito”…Taheer bai tanka ta ba ya wuce fuskan nn a tamke…a ranshi yake cewa”Ina Zaki lura dani dama tunda kina soyayya.