KASHE FITILA CHAPTER 3 BY BATUUL MAMMAN

 KASHE FITILA CHAPTER 3 BY BATUUL MAMMAN

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shuhada ta zuge wata ‘yar madaidaiciyar  jaka bayan ta gama hada kayan da zata bukata. Tun washegarin dawowarta   ta yanke shawarar tafiya Kaduna wurin mamanta. Zama a gidan nan ko kadan bata jin zata tsinci wata riba. A kwana biyun da tayi babanta tamkar hoto haka take ganinsa. Bashi da wani motsin kansa sai abin da Anti Bebi tace. A wani firgice yake idan yana gabanta. Wannan abu ga rabowa da masoyinta Tajuddeen suka hadar mata suka karawa gidan zafi.+

Tana share hawaye yayar Tajuddeen ta kirata a waya. Tana dauka kuka suka saka a tare. Ko sati hudu Yayar batayi da dawowa Nigeria ba bayan ta raka mijinta conference Singapore. Kuma a gidan Shuhada suka zauna. Hakuri tayi ta bata sannan ta sanar da ita suna hanya ita da Gwaggonsu zasu zo bayar da hakuri har gida. Babansu ma yanzu zai bi Alh Maitama office ya bashi hakurin wannan cin fuska da aka yi musu. Shuhada cewa take yi babu komai ba sai sun zo ba amma suka dage. Tunaninta kada Anti Bebi ta wulakanta su.

Zama tayi jefi jefi tana leka taga  da ta ji karar mota. Tafi son ta fara hangosu idan sun iso taje ta tarosu. Tana cikin leken saboda jin an bude gate ta hango wata mota dark green ta shigo.

******

Kafin isowarsu Gimbi ta yiwa Anti Bebi text tana fada mata zasu shigo ta fito ta ganewa idonta yadda ta mayar da Awaisu.

Dan mayafinta da ta saba ta dan rufe rabin kanta ta fito waje. Yana gyara parking Gimbi tace ya fita su gaisa da Anti Bebi. Kallonta yayi shiru yana nazari sai kuma ya fita din.

Da sauri Anti Bebi ta karaso tazo gaban motar.

“Oyoyo, oyoyo yau ga  Awaisu a gidana”

Dan rissinawa yayi zai gaisheta tayi saurin dafa kafadarsa.

“Haba Awaisu dana. Ina kai ina durkusawa, sai kasa a kalleka ai”

Hannunta da tasa a kafadarsa taki cirewa harda karkade masa wani dan zare daga wurin wuyansa.

Wannan abu duk a idon Shuhada. Duk da bata kaunar Anti Bebi batayi zaton mugun halinta harda bin wasu mazan ba sai yanzu. Kuma tasan ko ta fadawa Daddy bazai yarda ba. Abu daya zatayi shine taje taci mutuncinsu daga shi har Anti Bebin ta huce haushi.

Gimbi tana daga cikin mota murmushin fuskarta ya dauke ganin Anti Bebi ta dafa mata miji. Fitowa tayi ba arziki tace su shiga ciki. A nan suka bar Awaisu yana jiran fitowarta.

Suna shiga Shuhada tana fara saukowa daga sama taji Anti Bebi tace “na manta uwar kishi ce kin wani bata rai don an taba miki miji. Dadin abin nima gidan aurena kika zo”

Cikin tsiwa ta amsa mata “Anti kece sai wani dafa shi kike yi. Ni yanzu dai babu yadda za’ayi Maamu ta bar gidan lokaci guda? Kafin na samo kanshi wallahi duk dare yana dakinta ki rasa me suke yi. Wani lokacin sai na fara gyangyadi yake dawowa”

“Gimbi anya baki fini tsiya ba. Wannan da nono na kika sha maza sun shiga uku mata sun ga ta kansu. Yanzu uwa da danta ma sai kin zargi wani abu. Ko don irinku Gimbiya da ina da da wallahi matarsa bata isa ta juya shi ba”

Tafawa sukayi kamar sa’annin juna.

“So nake yi ta koma garinsu kawai ya rinka yi mata aike. Zaman tare damu ne bana so. Duk abi a sawa mutane ido. “

Sai ta dan rage murya har sai da Shuhada ta dan kara bene biyu domin taji da kyau. Dayake wurin zagaye ne basa ganin juna

“Kuma ina so ko za’a dauke hankalin Mama daga kan gidana. Ai na fada miki ranar da tazo yadda muka kare”

Anti Bebi ta hangame baki ” Iyye, Gimbiya kina burgeni. Kin cika mace wadda tasan meye ‘yancin rayuwa. Wasu ‘yan bokon miji da danginsa suyi ta gasa su amma sai su rinka iyayi wai basa bin malamai. Kuma duk karya ne. Tunda da kanki kika nema to kisawa ranki Amina ta bar shiga sabgar da baki sakata ba”

Duk da Gimbi bata so abin ya kai haka ba amma ta fara jindadin mallaka da juya miji. Burinta karuwa yake yi  domin yanzu har ogansu a banki take son ya dena mata maganar latti.

Shuhada tana tsaye zuciyarta har bugawa takeyi don tsoron matan nan. Wannan wace irin masifa ce muke daukarwa kanmu akan duniyar da bazata dore ba. Komawa tayi saman a hankali jikinta a sabule. Sai a lokacin taji tausayin mutumin da hannun Anti Bebi ya taba. Lallai ya aurowa kansa masifa.

*****

Karfe biyar da rabi Laminde ta dawo gida. Tasan dama yaran suna Islamiyya. Rashin ganin Gimbi yasa tayi tunanin ko sun kai Maamu asibiti, kwarai taji tausayinta dazu. Ku6ewa ta zauna gurzawa kafin su dawo a bata shinkafar tuwo ta dora. Tana aikin su Rumana suka shigo. Dakinsu ta wuce ta cire kayan makaranta sannan ta shiga bandaki yin alwala saboda an fara kiran magariba.

Tana budewa ta ga Maamu a kwance ko motsin kirki bata yi. Ga jikinta alamun ta sake yin gudawa a wurin. Ihun kuka Rumana ta saka tana kiran Laminde. Sai gata a guje tare da su Haris.

Duk su biyun sun rude suna zaton ta mutu ne. Suna kokarin dagata su Awaisu suka dawo ya tsaya wurin maigadi Gimbi ta shigo. Daula ce ta fada mata Maamu babu lafiya tabi bayanta. Daga bakin kofar bandakin ta toshe hancinta.

“Hmmmm warin meye wannan haka”

Tana kallo da kyar Maamu take bude ido ta jingina da jikin Rumana ita kuma Laminde tana tara ruwa a bokiti da zata dauraye mata jiki tace .

“Maamu ce babu lafiya, a kwance nan muka ganta”

Tabe baki tayi “Toh, to Allah Ya sauwake. Gyara mata jikin kafin na dawo”

Tana fita ta ga Awaisu a falo Haris yana fada masa. Da sauri ta karaso da alamun gigicewa har tana jifa da mayafi.

“Abban Haris juya mu kai Maamu asibiti bata da lafiya.”

Duk yadda yake nuna rashin kulawarsa damuwa ce ta ziyarce shi ya ruga dakin a guje. Ganin Rumana ta kasa rike Maamu sosai kafin Laminde ta dauko musu nata sabulun saboda nasu saura guntu da suke amfani dashi anki basu wani. Mantawa yayi da kayan jikinsa ya shiga ciki ya dagata ya saka a bahu sannan ya soma dibar ruwan yana wanke mata jiki da hannunsa yana kiran sunanta cikin tashin hankali kada ta mutu. Da Laminde ta kawo sabulun hannun Rumana ta ja suka fita ta rufe kofar. Rumana tana son komawa Laminde ta girgiza kai.

“Ki bar Kawunki ya sami ladan mahaifiyarsa Rumana. Dauko mata kaya kafin ya gama”

“Namiji ne fa” ta fada tana yatsina fuska. Tuni Kawun nata ya fice mata a rai.

Laminde tayi murmushi “to naji bari naje ya bani nayi mata wanka”

Gimbi ce ta shigo tana tambayar yana ina suka nuna mata bandakin. Muryarsa taji yana cewa “Gimbi zo kiyi mata wanka zan chanja kaya muje asibiti”

Gabanta har faduwa yayi, wannan kazantar ta jikinta zata taba…..

Laminde tana kallonta sai ta shiga tace zata yi mata. Tsoro taji kada da gangan Gimbi ta saketa ta fadi.

Bayan anyi mata wankan ne Laminde ta kula hannunta daya ya kumbura ta wurin babban yatsanta ga dukkan alamu tayi targade. Haka ta shiryata Awaisu da Gimbi suka kaita asibiti. Suna can ya kasa zama har likita ya fito yace suna mata karin ruwa sannan anyi mata gyaran targade. Hankalinsa duk baya jikinsa sai da ya ganta. Da kyar take magana idanu duk sun fada ciki tace ya kirawo mata Harisu a waya. Gimbi jin an ambaci sunan daya makiyin nata ta kasa kunne sai dai bata jin me Awaisu yake fada da yarensu har ya gama wayar.

Juyowa yayi yace “Gobe in sha Allah Yaya Harisu zai zo da daya daga cikin matansa da Baaba Hure. Ina tsammani zasu taho da kanin Maamu ma. Ki kira Laminde a gyara musu dakin baki kafin mu koma gida”

Kirjinta ne ya buga, mutanen da ta raina zasu cika mata gida.

Awaisu bai lura da yadda Gimbi ta chanja da wuri ba daga jin maganar zuwan su Harisu ya mika mata mukullin mota.

“Kije gida ki taho muku da kayan bukata na kwana. Idan kin dawo sai na tafi da motar”

Zaro idanu tayi tana neman amsar da zata bashi domin gujewa kwana da Maamu. Itama Maamu da ta gane me ya fada murya can kasa saboda ciwo tace masa ya tafi da matarsa a kawo mata Laminde ko Rumana. Da ta ga zaiyi gardama tace saboda yara ne. A ranta kuwa cewa take gara ta kwana ita kadai da a barta da Gimbi.2

*****

Harisu dakin Baaba yaje ya fada mata Maamu babu lafiya. Hankalinta kuwa ya tashi tace to yaje ya sanarwa ‘yan uwanta. Har zai fita ta sake kiransa.

“Dangin mahaifin Awaisu ma ya kamata ka fada musu. Ai kana jin yadda suke yada mana magana wai ya tare a jikinmu baya musu komai”

Harisu ya sha kunu “haba Baaba har yaushe zaki bari zancensu ya dameki. Allah Yana gani yadda duk zuwansa garin nan sai yaje kuma yayi musu alheri. Neman rigima ne kawai”

“Duk da haka kaje ka fada musu ko zasu tura wani yaje dubiya”.

“Har na fadawa Awaisun kila muje da kanin Maamu ko wani dai cikinsu. Mu da zamu je dubiya kada kuma a dorawa iyalinsa wahala”

Baaba Hure tayi wani murmushi wanda ita kadai ta san ma’anarsa.

“Baka saba yi min musu ba Harisu. Nace ka fada musu yadda zasu tura wakilinsu dubiya. ‘Yan uwanka ma zan sa a kirasu a waya ko mutum biyu a samu. Cikin matanka ka dauki babar Rumana saboda ta gano ‘yarta tunda ka hana a kawota hutu. Sauran suma a hankali sai kaje dasu tare ko daya bayan daya”

Harisu kasa motsawa yayi jin wannan hadi na Baaba. Duk girman gidan Awaisu idan sukayi yawa zasu takura musu ne. Ga mara lafiya kuma ga baki da wanne zasu ji.

“Yaya kaki tafiya ne?”

Takalmansa ya saka yayi waje. Ita kuwa Baaba Hure ta gyara kwanciyarta tana jira ya dawo ya kira mata Awaisu ta ji yaya jikin Maamu. Ba komai yasa take son tarawa Gimbi jama’a ba sai bakar maganar da suka yi mata ita da Anti Bebi a rashin sanin bahaushiya ce. So take ta tabbatar Gimbi bata son dangin Awaisu da gaske ne ko kuwa dai ‘yar tsama ce irin ta mata da dangin mijinta.

*****

Gidansu Maamu ya fara zuwa inda duka yayyenta maza da kanne suke tare da iyalansu. Bangaren wani cikin ‘yan uwan yaje suka gaisa ya sanar dasu abin  da ke faruwa. Nan da nan ‘yan uwa suka taru ana jajantawa sannan suka ce zasuyi shawara wanda zaije a madadinsu.

Harisu yana fita Hajja Jume matar babban wan Maamu wanda ya dade da rasuwa ta dogaro sandarta ta taho.

“Yanzu labari yazo min za’a tafi wurin Safara’u dubiya ko”

Bashar wanda yake matsayin babba yanzu ya hade rai yana hararar Atika jikar Hajja uwar hada gurmi.

“Tikeke akan gulma zanyi maganinki”

Hajja ta daga sanda tana fada “wanda ya fasa Bashar, nace wanda ya fasa. Yarinya duk kun takura mata kamar ita kadai ce jika. Duk abinku a nan gidan zata zauna. Bani da kowa a gabana sai ita. Tunda tazo ku da iyalanku kun hade mata kai kamar ka jininku ba”

Tikeke ta sunkuyar da kai ita a dole a bar tausayi ce “Hajja babu komai dama na fada miki ne kada a gama rabon waye zaije Abuja gidan Kawu Awaisu a barmu a nan”

Hadi yayi caraf yace  “kada ma kusa rai, ni da Yaya Bashar zamu je. Ai ba gayya za’ayi musu ba”

“Wallahi baku isa ba Hadi. Ni zaku nunawa wariya don nawa mijin ya rasu. To ni da Tikeke kamar munje mun gama. Idan da kara ni ya kamata na fadi masu zuwa tunda yaron nan dana ne. Malam da Safa’ra’u ciki daya suka fito ba kamar wasu ‘yan uba ba”

STORY CONTINUES BELOW

Hayaniya ce ta kaure sosai a tsakaninsu karshe aka tsaya akan za’a tafi da Tikeke,  Kawu Bashar da matar Hadi. Idan basuyi haka ba tijarar Hajja bata tsallake kowa. Ba karamin aikinta bane ma tasa danta baban Tikeke ya kaisu tunda dreba ne.

****

Kasuwa Harisu ya koma can wurin masu gwanjo ya hadu da Bomai kanin baban Awaisu. Dattijo ne rigimamme na ajin karshe. Yana cikin masu yiwa Harisu habaici wai sun shanye Awaisu baya bi ta kansu. Bayan jarin gwanjon ma shine ya bashi.1

“Alh Harisu kenan, yau an leko mu”

“Kawu Bomai yaya kasuwa?”

Kan benci ya zauna yana zukar sigari kafa daya kan daya.

“Gata nan muna fama. Yaya akayi ne?”

Kamar yadda ya sanar da ‘yan uwan Maamu haka ya fadawa Bomai. Wani tsalle ya daka ya tashi dama shi ba jiki ba sai tsawo.

“Maamu tamu ce babu lafiya? Kace ban ga ta zama ba. Kayi kyan kai sosai da ka fada min. Asubar fari zanzo nan gidan naka mu tafi”

“Sai wuraren karfe tara zamu tafi. Nace su sauran zaka sanar dasu ko naje na fada musu. Awaisu yace jikin da sauki dai”

Matsowa yayi daf da Harisu “Tunda na sani ka bar maganar kawai ni zan sanar dasu.”

Sai kuma ya gyara tsayuwa yana kwantar da kai gaban Harisu “Maamu mutun ce, wato ba don haduwarta da Mal Sa’adu mai rasuwa ba dama ni naso na aureta saboda kula da maraya. Kuma gashi ni ban haihu ba. Shiyasa nake jin yaron nan a raina sosai. Kaga sau biyar fa yana bani jari. Yaro yayi halin iyayensa wurin karamci”

Harisu gyada kai kawai yake yi ya samu ya bar wurin. Baaba Hure ta hadashi da aiki. Me zai sa tace kowa sai yaje. Tausayin Awaisu da Gimbi wadda za’a hada da baki ne ya kama shi.

Yana kallo Bomai ya kulle gwanjonsa ya saba a kafada yayi hanyar titi.

*****

“Hinde maza maza fito ki fara hada kaya”

Hinde na bandaki ta fito da sauri bota a hannu. Ajiye botar tayi ta sa hannu ta toshe gefen hanci ta rangada guda tana tafa hannuwa

“Ayyiriririiiii, sai yau kaga damar sakin nawa, to ka sani kuma ka jira ina gama idda zan sami miji da ya amsa sunansa ba irinka ba kashi da rai. Nawa kayi min ne sakin”

Botar da ta fito da ita ya dauka ya kafa a baki ya sha ruwan sannan ya kuskure baki ya tofar.

“Dadina dake wutar ciki, baki ji bayani ba kin hau suki burutsu. To ai sai ki tafi nima na huta”

“To dai gaya min me ya faru idan ba sakin bane kake min wannan kiran”

Kan kullin gwanjon ya dare ya zauna “Abuja zamu koma gidan dana”

Wata muguwar shaka Hinde tayi masa har yana zaro idanu “munafuki ashe har da gareka ban sani ba. A wace tashar ka hadu da babarsa”

Hannunta yake duka da kyar yana cewa “Awai,aaaaw,awsu”

Sassauta rikon tayi yace “AWAISU ne fa dan marigayi yayana. Kasheni zakiyi ne?”

Hinde ta zauna shirim a gefensa tare da murza masa wuyan.

“Kaine baka iya kawo labari ba. Kace Awaisu na Maamu”

Nan ya labarta mata yadda sukayi da Harisu da kuma kudurinsa

“Yace kwana biyu zamuyi. Amma so nake ki hada kayan kamar na sati. Sai kuma mu saka kamar uku uku a jikinmu kada a ga Ghana mazigo din kayanmu da girma.  Idan munje zan sa ya nema min aiki. Kema ki rinka yiwa Gimbiyar nan ladabi. Kinsan durkusawa wada ba gajiyawa bane.”

Hinde sai murna zasu Abuja. Ko Bomai bai fada ba bata ga dalilin da zaisa idan sun je ta dawo Fika ba. Kallonta yayi ta shige daki ta fara fiddo kayansu zata wanke yace

“Hinde don Allah idan munje kada ki nuna hali, banda dauke dauke kinji ko”

Harara ta galla masa idonta kamar ya fado. Me zai kaita sata kuma yanzu, ita da tayi a gidan biki ‘yan mata sukayi mata duka sai da hakorinta na kasa ya cire.

******

Daren ranar Gimbi kasa bacci tayi. A haka ma don bata san mutum nawa ne masu zuwa ba. Sau biyu Awaisu yana farkawa ya ganta a zaune sai tace masa jikin Maamu ke damunta. Gashi likita yace harda rashin cin abinci sosai.  Harda kukanta tace

“My dear ko zaka tambayi Maamu me tafi so sai na rinka dafa mata. Gobe zan dauki hutu ko na sati ne na kula da ita”

“Kema kinsan bazasu baki wannan hutun ba. Ki bari kawai tunda akwai masu zuwa”

Murmushi tayi, don tana tunanin a goben Anti Bebi zata kaiwa Wangesi bukatarta akan ogansu. Sake marairaicewa tayi

“Duk laifina ne da nake zuwa aiki bana iya kulawa da ita yadda ya kamata. Kullum da safe idan naje fada mata zan fita Maamu sai tayi min addua. Yanzu idan suka zo aka ce na barta da yunwa fa.”

Kuka ta fashe dashi Awaisu ya rarrasheta. Karshe tace masa zata bar aikin kawai ta kula da gida. Ga mamakinta sai taga ya bata goyon baya. A zuci tace wato shima bakinciki yake da aikin. To yanzu ta fara.

*****

Da safe tunda babu Laminde gashi tana son burge Awaisu haka tayi farfesun kayan ciki da dankali ta hadawa Maamu Awaisu ya kai asibiti. Bayan su Haris sun tafi makaranta ta fadawa Anti Bebi halin da take ciki da bakin da zasu zo.

“Zage damtse zakiyi ki kyautata musu kada wani ya sami bakin magana akanki” inji Anti Bebi.

Ai kuwa ta wuni a kitchen tana girkin tarbar baki mutum hudu ko dubiya bata samu zuwa ba. Sai yamma likis suka iso mota biyu. Awaisu ma shigowarsa kenan kuma Haris yayi masa waya ya sanar dashi karin da aka samu yace ya amince duka su taho tare akwai wurin kwana. Sai dai kuma ya manta bai fadawa Gimbi ba. Jin tsayuwar mota tabi yaranta suka taho da gudu tarbarsu Baaba Hure. Sai ga Gimbi murmushi ya makale a gefen baki. Mutane ta gani wanda ta sani da wanda bata taba gani ba.

Baaba Hure, Anti Ummukulsum, Harisu, Maman Rumana, Kawu Bashar, Ammu matar Hadi, Tikeken Hajja, Bomai da matarsa Hinde. Mutum takwas. Tun a zuci ta fara kuka.

Zuciyar Gimbi harbawa ta rinka yi sosai saboda wani bacin rai da ya danneta. Kasa daurewa tayi duk iya kokarinta ta fashe musu da kukan bakinciki mai sauti. Ai kuwa hankalinsu Baaba Hure ya tashi matuka sun zata ko Maamu rai yayi halinsa ne. Da yake ta fara kwarewa da kissa irin ta Anti Bebi sai tayi saurin goge hawayen harda rungumo Baaba tana kallon Harisu a zatonta shi kadai yake jin Hausa.+

“Wallahi tsabar murnar ganinku ne Yaya. Tun jiya da yace zaku zo nake murna. Allah Sarki Maamu yau zan gani ni da ita wa yafi murnar zuwanku”

Daga gefe taji ance “kissa adon mata, Bomoi ka ga wadda ta fini”

Hinde ta fada da sunan rada duk da tasan ana jinta kuma da hausa.  Bomoi ya galla mata harara ya kalli Gimbi yana murmushin dole. Daga zuwansu zata nemi janyo musu bakin jini wurin matar gida.

A razane Gimbi ta kalli Hinde har cikinta yana kadawa. Sakin fuska tayi ba arziki kamar bata fahimceta ba tace su shigo ciki. Mukullin wani daki ta waje ta bawa Harisu inda ya taba masauki lokacin zuwansu Hajji. Nan suka shiga shi da Kawu Bashar da Bomoi wanda yake ta zuba surutun haduwar gidan dansa gudan jininsa.

Daula ce tayiwa Baaba Hure jagora zuwa dakin Maamu inda zata zauna. Wani daki a gefensa kuma Gimbi tace Ummukulsum, Maman Rumana, Ammu, Hinde da Tikeke su shiga suyi wanka sannan su fito cin abinci.

Tikeke ta zumburo baki “Haba Hajiya ko ruwa bamu sha ba zaki ce muyi wanka. Allah Ya gani sai naci abinci nake iya komai.”

Ammu ta riko hannun Tikeke tana kokarin fita daga dakin zata koma falo inda ta hango kwanukan abinci an jere su. Kokawar fizgewa Tikeke ta somayi Ammu ta canja harshe tace zata fadawa Kawu Bashar. Rai a bace ta kwace hannunta ta shiga bandakin tare ta bugu kofa.1

Jiki a sanyaye Gimbi ta fita daga dakin. Yau kuma irin bakin da tayi kenan ta fada a zuci. Falon taji kamar yana warin gumi a cewarta ta dauko air freshner ta shiga fesawa. Juyawar da zatayi ta hada ido da Baaba Hure tayi saurin ja da baya.

Baaba ta saki fuska

“Dama kwan fitilar bandakin ne naga ya mutu. Idan akwai wani ki taimaka a saka min don in yamma tayi ba gani nake sosai ba bare kuma a duhu”

Mamaki ne ya bayyana sosai a fuskar Gimbi jin Baaba tana hausa. Dazu ma taji wata tayi a waje. Yanzu bata isa ta juya harshe tayi gulmarsu a gabansu ba kenan.

“Baaba bari idan Abban Haris ya dawo sai a saka miki ki shiga”

Baaba ta dafata da hannu daya tana dan tafiya

“muje ki kaini naki sai nayi alwala a can. Banyi sallar la’asar ba ga magariba tana gabatowa”

Ba’a son ranta ta kai Baaba bandakinta ba. Maamu kuwa ko hanyar dakin bata taba takawa da kafarta ba. Tana zaune tana ji Baaba Hure tana kaki. Takaici ya isheta ta fita ta koma dakin Awaisu sannan ta kira Anti Bebi.

“Na shiga uku Anti, su takwas kamar ance musu ta mutu. Ina zan kaisu”

“Ba na son shirme kinji ko. Ki tashi ki je duk yadda suke so kiyi musu. Idan kika bari suka gane wani abu to karshenta su ki tafiya da wuri. Kinga garin neman gira kin rasa ido”

Maganar Anti Bebi gaskiya ce. Da saurinta ta shiga kitchen ta dora macaroni tunda dama shinkafa da miya tayi da kuma tuwon dare. Kafin ta gama Awaisu ya shigo ya tafi wurinsu Harisu suna gaisawa.

Sai da sukayi sallar magariba suka ci abinci sannan suka fara shirin tafiya asibiti gabadayansu. Gimbi tana ta raha da rawar kai ita me son surukai. Sun firfito waje Awaisu ya kira drebansa da yake kai yara makaranta ya bashi mukullin mota

STORY CONTINUES BELOW

“Sunday gashi ka debe su Yaya Ummukulsum ka wuce dasu asibitin da aka kwantar da Maamu. Zan tsaya a atm ne sannan na taho da su Baaba”

Sunday ya dan rissina a ladabce “Oga yaushene Hajiya babu lafiya, wane asibiti ne.?”

Awaisu yaji kamar ya raina masa hankali yace “Inda ka kai musu abincin rana mana”

“Ban fita ba tunda mun dawo da su Haris”

Idanun Awaisu suka kankance yana kallon Gimbi “da kanki kika kai musu abincin rana? Ina na daren ne ma ban ga an dauko ba”

Idanun Gimbi nan da nan suka yo waje ta rasa amsar bayarwa. Baaba Hure tana kallonta tasan bata da gaskiya

“Gimbiya kada kice min ba’a kaiwa Maamu abincin rana ba bare na dare”

“Uhmmm, uhmmm” nan fa jikinta ya soma rawa ganin idanu a kanta ga Awaisu yana wani huci kamar mayunwacin zaki. Irin wannan fushin nasa ba kasafai yake ba. Kuma a tunaninta yanzu da Wangesi ya gama masa aiki bai isa yayi mata ko da mugun kallo ba.

Tsawa ya daka mata kamar ya kai mata duka “ki bani amsa mana”

Harisu ne yayi magana ganin ransa da na Baaba Hure a bace yake. Yaran ya fara cewa su shiga motar Sunday sannan yace  “Awaisu meye haka ne kake yi mata tsawa gaban yara. Gimbiya an kai abincin?”

Kuka ta saka saboda tsabar bata damu da Maamu ba shaf ta manta da batun abincin. Na safe ma da tayi saboda ta burge mijinta ne yaji dadi.

“Wallahi Yaya Harisu ina ta aiki ne na sha’afa.”

Ummukulsum tace “wannan ba magana bace Gimbi. Akwai wani aiki da zai sha kanki sama da nata da take asibiti? Yanzu ga jinya ga yunwa daga ita har Rumana”

Ido sharbe da hawaye ta rinka basu hakuri. A ranta kuwa duk tsine musu take yi suna neman jaza mata masifa wurin miji.

Baaba Hure tamkar ta cinyeta da fada. Tana yi Awaisu yana yi don ya kule karshe. Harisu ne ya rinka basu hakuri. Su Tikeke kuwa an sami abin kallo da gulma. Marasa jin hausa sosai babu damar tofawa.

Duk wani haushin Gimbi da yake ji kwanakin baya ya kasa magana tun jiya da ya ga Maamu a wannan yanayin yaji kamar an bude masa ido. A fusace yace mata taje ta dauko abincin. Wani tsoron ya sake kamata domin batayi dasu ba. Hasali ma dai babu sauran abinci a gidan. Awaisu yayi fadan da hausa ya koma saka yarensa kamar ya kai mata duka. Baaba Hure ko a jikinta saboda tun maganar da sukayi akanta take jin Gimbi ba matar kirki bace. Harisu ya ja shi gefe ya soma nasa fadan

“Wani sabon salo ne ka koya zaka zubarwa matarka mutumci a gaban baki. Dubi yadda suke kallonka. Kana tunanin wannan labarin bazai je Fika ba”

Kwalla ce take barazanar fita daga idonsa saboda tunanin yaya Maamu ta wuni. Yaje da azahar daga wurin aiki amma ita dasu Laminde babu wanda ya fada masa

“Yaya ace tun abincin safe saboda Allah”

Harisu ya dafa shi yana murmushi “to kuka zaka yi min? Awaisu ‘ya’yanka hudu fa. Muje su koma suyi girkin kafin dare ya karayi a hanamu shiga”

“Bari kawai ma saya a hanya. Karfe tara suke hana shiga sai goma na safe kuma”

Tare suka koma suka shiga motocin. Wasu na motar Sunday tunda babba ce school bus sauran Awaisu ya diba. Gimbi tayi turus a waje ganin Bomoi ya shige gaba abinsa. A dakile Awaisu ya nuna mata bus din

“Idan zaki je ki koma bus din inda mata suke”

Ranta na kuna kamar tace bazata ba ta koma ta shiga tsakiyar Ammu da Hinde. Kallonta suka rinka yi ta kasa motsin kirki saboda sun matseta.

*****

Suna zuwa a kwance suka sami Rumana a gadon da yake gefen na Maamu tana bacci. A kasa kan abin sallah kuma Laminde ce take cin dafaffiyar gyada. Naira hamsin gareta shine ta siyo musu ita da Rumana suka ci suka sha ruwa. Maamu taki ci tana kwance tana hawaye. Yaushe ne danta zai waiwayeta???

Muryar Baaba Hure taji ta soma yunkurin tashi. Maman Rumana ke rike da hannunta ta karasa da ita bakin gadon saboda dishi dishi take gani. A haka ma don anyiwa idon aiki ne.

Hannu ta mika tana laluben Maamu. Ji tayi Maamu cikin muryar dake nuni da tana jin jiki tace “Baaba”

Baaba Hure sai hawaye “Maamu sannu, sannu ‘yar uwa. Kai Awaisu ku zuba mata abincin nan”

Gimbi ce tayi saurin mika hannu zata karbi ledojin ya harareta sannan ya bawa Maman Rumana. Ummukulsum tace “Maamu kin rame sosai”

Riko hannun Ummukulsum din tayi “hmmm kayya Ummu jikin tsufa ne kawai, Ina yaran , yaya wajensu Auta Zakiyya”

Rumana cikin bacci taji kamar muryar babanta. Firgigit ta tashi. Abin mamaki harda Mamanta da Baaba. Wani tsalle tayi ta diro ta kankame Harisu. Shi kam kunya ma ta bashi a gaban mutane. Ta tafi zata rungume mamanta ta harareta irin abin ‘yar fari. Sai kawai ta koma jikin Baaba ta kankameta.

Sun gama gaisawa Laminde da Rumana suna gefe suna cin abinci sauran suna ta hira. Basu bar asibitin ba sai shadayan dare. Nurses suna ta zuwa ana cewa su bar hayaniya.

Likita ya bukaci ganin Awaisu kafin su tafi. Fada sosai yayi masa duk da karancin shekarunsa akan shi na barin Maamu da yunwa. Duka allurai da maganinta tun azahar ba’a yi mata ba saboda bata ci abinci ba. Sannan jikinta ma yana nuni da alamun rashin kuzari saboda tana bukatar wasu sinadarai a jikinta. Shi dai sai hakuri yake bayarwa yana tunanin wai me Gimbi take yi har Maamu take zama da yunwa. A wani bangaren tuhumar kansa yake da rashin kulawa wadda bai san dalilinta ba

******

Wurin shabiyu da rabi kowa yaje ya kwanata Awaisu da Gimbi suna ta fada. Bashi hakuri take yi amma kamar tana ingiza shi. Bandaki ta shiga tayiwa Anti Bebi text ta sanar da ita. Shawara ta duk da batayi mata dadi ba haka ta karba kafin gobe ta nemi Wangesi.

Wurin Baaba taje tayi sa’a bata kwanta ba. Nan ta kwantar da kai ta bata hakuri ta roketa akan ta bawa Awaisu hakuri. A zatonta tuban gaskene tacewa Awaisu magana ta kare daga lokacin. Ya dai ce to amma juya mata baya ma yayi da suka kwanta. Kafin nan kuma yasa ta bawa Ammu da Maman Rumana dakinta saboda wancan yayi musu kadan. Ita Ummukulsum ta canji Laminde zata kwana a asibitin

Da safe matan suka tayata girki tana ta kokarin jansu a jiki.

*****

Anti Bebi karfe bakwai ta fice daga gida sai kauyen Nasarawa state inda Wangesi yake. Magunguna ya bayar da wasu layu da za’a binne a gidan. Kafin shabiyu ta dawo gida. Wanka tayi ta shirya sannan tace Alhaji yazo ya kaita dubiyar surukar Gimbi. Tun tana chan zazzabi ya kamashi a office ya dawo gida. Wani nau’in asirin akayi masa. Da ya dawo Shuhada ce ta tarbe shi ko kallonta yaki yi. Kudin mota take so ya bata itama ta bar musu gidan.

Suna fitowa daga daki Anti Bebi ta marairace wai yace Shuhada tazo suje tare saboda zaman gidan bazai mata dadi ba. Har ransa yaji dadin ta damu da yarsa amma ita Shuhada bata sonta. Dolenta ta fito suka tafi tare. Anti Bebi ta hakimce a baya Shuhada na gaba. Daga bayan mota take ta bashi umarni yana toh kamar wani bawanta. Kafin su je asibitin Shuhada har kuka tayi ganin yadda Daddynta ya koma a gaban mace.

*****

Alh Mudi da Mama suna bayan mota dreba na jansu zasu je duba Maamu. Fada sosai yayiwa Gimbi a waya bayan ya sami labarin rashin lafiyar a bakin Saminu. Su da suke garin ace basu da labari har su Harisu sun zo shi kuma Saminu yana hanya. Gimbi hakuri ta bayar kawai. Yadda bata damu da Maamu ba bata ga dalilin da sai sunzo dubiya ba.

Dakin yau a cike idan kaga Maamu da Rumana tamkar ranar sallah. Su Mama ne suka fara zuwa ana gaisawa sai ga Anti Bebi ta shigo tana fara’a. Tuni Gimbi ta rikice ganin kallon da Mama da Alhaji suke yi mata. Ita kuwa Anti Bebi don ta bawa Mama haushi ta tafi ta rungumo Gimbi

“Gimbiya yaya mai jikin. Tun shekaranjiya da kika fada min hankalina ya tashi. Jiya da kika min waya kuma baki ne dani ban samu nazo ba”

Mama ji tayi kamar ta rufe Gimbi da duka a wurin.

Kallon kallo aka rinka yi tsakanin Gimbi da iyayenta. Gashi maganganun Anti Bebi sun sa ta daskare a wurin kamar wata dutse. Anti Bebi tana lura dasu ta share tana dariya ita kadai a zuci. Wato don rainin wayo irin na Gimbi so tayi ta rinka morarta a bayan fage batare da ansan tana kula ta ba. In dai Anti Bebi ce bata isa ba. A ganinta duk abin da take yi neman ‘yanci ne. Saboda haka idan zaka sha giya gara kasha ta dubu.

Alh Mudi ba a son ransa ya gaisa da Alh Maitama ba. Shi fa komai da ya danganci Anti Bebi to baya baya dai. Lokacin da take auren wani dan unguwarsu tamkar zautacce ya koma. Duk inda ya zauna sunanta yake kira kuma ko a baya idonta baya taba saba umarninta.

Mama ta daure ta cigaba da hira da mutanen dakin tana tambayarsu yaya maijiki. Lokaci lokaci take kallon Gimbi wadda har yanzu bata farfado daga mutuwar tsayen da tayi ba.

Harisu da Alh Mudi da sauran mazan suka fita suna hira. Sai dai Alhaji hankalinsa baya wurin sosai. Karshe ma dai yace musu zasu tafi saboda yamma tayi sai gobe zasu dawo. Wayar Mama ya kira ita kuma a lokacin tana ganin Laminde ta hada kwanukan abinci zata kai mota tayi saurin bin bayanta.

“Laminde dan tsaya don Allah”

Laminde ta tsaya har Mama ta karaso ta sake gaisheta tana dan murmushi.

Fuskar Mama ta kalla mai nuni da damuwa. Mama tace “matar nan da ta shigo da mijinta kin taba ganinta a gidanku?”

“Anti Bebi ko? Inace kanwarki ce inji Hajiya”

Mama ta rike baki, lallai akwai abin da Gimbi take yi wanda basu sani ba.

“Tun yaushe kika fara ganinta a gidan?”

Dan tunani tayi sannan tace “gabanin zuwa Maamu ne”

Kuka ne kawai Mama batayi ba don takaici. A take zuciyarta take raya mata Gimbi ta fara bin sahun Anti Bebi. Hannun Laminde ta rike kana ganinta kasan cikin damuwa take sosai “ki taimakeni Laminde duk ranar da ta sake zuwa ki sanar dani. Kuma ni na baki dama kisa ido sosai akan uwar dakinki. Idan kinga wani abu da kike ganin tayi bai dace ba kada ki boyemin”

“To Mama in sha Allahu.”

Mama godiya tayi mata sannan ta wuce. Laminde har tausayinta taji. Iyayen Gimbi mutanen kirki amma ta rasa inda ta koyo wannan halin na cutar da uwar mijinta.

*****

A cikin dakin Anti Bebi ta sake tana ta yiwa bakin Gimbi hira tamkar sun dade tare. Alh Maitama yana tsaye shi kadai namiji cikin mata. Murmushi tayi don tasan izininta yake nema tace ya fita  gasu nan zuwa. Kamar an tsikare shi ya fice. Shuhada ta sunkuyar da kai don kunya sai ga hawaye. Wannan tozarci har ina. Dole ma ta bar gidan kafin bakinciki ya kasheta. Da tunanin Tajuddeen zata ji wanda yayi mata sakin wulakanci duk kuwa da son da suke yiwa juna ko yadda mahaifinta ya koma.

Baaba Hure ce ta kula da hawayen da Shuhada take gogewa tace ” ‘yan mata me ya sameki?”

Anti Bebi tayi caraf ta tashi harda rungumota a jikinta.

“Sharrin namiji, cikin dare mijinta ya dawo haka kawai ya dankara mata saki uku ba laifin zaune babu na tsaye. Ko sati uku ba’ayi ba. Idda ma take yi. Shuhadana ki rinka hakuri. Shiyasa fa nace ki fito kisha iska kada tunanin namiji ya sa miki hawan jini”

Tamkar Shuhada ta shige kasa don kunya. Yanzu me ya kawo fadawa mutanen da bata taba gani ba sirrinta. Tunawa tayi babu wanda yasan lokaci da yadda sakin ya faru sai Suhail shiyasa ta kalli Anti Bebi a razane. Wannan shegen murmushin ta sakar mata mai nuni da tasan komai. Tsanarta ta sake samun wurin zama a zuciyarta.+

Gimbi ta kasa zaune ta kasa tsaye tun bayan fitar Mama. Ita a tunaninta ma ko kiranta zatayi a waya aci mata mutumci. Shirun da taji yasa hankalinta ya dan kwanta. Fita tayi daga dakin zata leka ko sun tafi Anti Bebi tayi sallama dasu Maamu tabi bayanta. Dan nesa da motar Alh Maitama suka tsaya Gimbi ta juyo a tsiwace

STORY CONTINUES BELOW

“Anti Bebi ya zaki min haka? Meye na zuwa asibitin gashi yanzu Allah kadai Yasan me su Baba zasuyi min”

Gira ta daga tana yatsina fuska “sannu uwar munafukai, da cewa akayi dake ni bani da hankali. Kin iya kawo mijinki na kaishi a baki akalarsa a tafin hannunki amma bazaki nunawa duniya matsayina na kawar babarki ba. Haba Gimbiya, dube ni da kyau nafi karfin wani shege yabi ta kaina ya gina kansa sannan yasa kafa ya tureni.”

Gimbi ta fusata “nice shegiyar?”

“Yo nufinki nice? Kada ki kuskura kice zaki min rashin kunya Gimbiya, sai nasa ki raina kanki. Bar ganin na hadaki da Wangesi ba dashi kadai na dogara ba. Awaisun da kike takama dashi sai nasa a mayar min dashi tamkar wancan Alhajin. Idan naso albashinsa ma ni zai rinka bawa ajiya”

Gimbi taji cikinta na karar tsoro amma tace “mu zuba mu gani, sai na tona miki asiri”

“Bani da sirrin boyewa, ke dai matsoraciyar banza ki jira hukuncin iyayenki a kanki. Kuma kisa a ranki tamkar na rama wannan rashin mutumcin naki na gama. Bebi ce fa, Bebin maza mata su ganni su watse”

Duk da Gimbi tana tsoron Anti Bebi dakewa kawai take taja tsaki ta juya. Ido hudu sukayi da Shuhada wadda ta gama jin duk abubuwan da suka fada. Gimbi kara tsorata tayi sai dai Anti Bebi ko a jikinta. A wulakance ta kalli Shuhada ta nunata da yatsa

“Wannan fitsararriyar ma da taso nuna min ita wata ce kinga aurenta watansa shadaya na kaso mata shi. Kuma bata isa ta kara wani batare da amincewata ba. Saboda haka kema wannan kan naki da yake rawa ki daidaita shi. Idan ba haka ba uwarki Amina ma sai ta dana zawarci”

Ran Gimbi ya kara baci tace  “ba dai uwata ba sai dai….”

Maganar bata karasa fitowa ba saboda marin da Anti Bebi ta kwasheta dashi. Dafe kumatun tayi tana zubar hawaye. Tana tsoron daga murya su Awaisu su ji me yake faruwa. Sannan ga tsoron Anti Bebi ya sake tasiri a ranta.

Shuhada bata ce musu komai ba tayi gaba tana mamakin hali irin nasu. Su biyun duka abin tsoro ne gareta. Tana karasawa bakin motarsu nan ta samu su Harisu a jiki suka jingina suna hira. Su Mama kuma lokacin motarsu ta fita.

Awaisu yana gani ta tsaye jikin wata motar yayi mata alama da hannu ta karaso. Bude bayan motar yayi yana mata murmushi

“Kanwata shiga ki zauna kada ki gaji da tsayuwa”

Daga inda take Gimbi ta hangosu taji kamar an soka mata kibiya. Anti Bebi kuwa murmushin mugunta ta bita dashi. Anya bazatayi maganin Gimbi da Shuhada ba ta hanyar sanya Awaisu son Shuhada kuma ta matsawa Alhaji ya yarda da auren. Da wannan tunanin ta shige gaban mota suka tafi saboda idon mutane.

******

Alh Mudi da Mama har suka isa gida babu mai cewa komai. Tana shiga daki ya bi bayanta da hula a hannu.

“Me Bebi take yi a asibitin nan Amina?”

Dama jiransa take yi don tasan sai yayi magana “nima nayi mamaki, yadda ka ganta haka na ganta”

Daga murya yayi yana mata tsawa ” ‘Yar uwarki ce kiyi mata magana ta nesanta kanta da iyali na.”

Wani kallo Mama ta bishi dashi saboda haushin maganarsa da taji.

“Abin da zaka fada min kenan Alhaji? Da bakina fa na fada maka irin abubuwan da Bebi take yi tun kafin ya fito fili duniya ta sani. kuma na nemi shawararka akan yanke hulda da ita saboda kare mutunci da addini.”

Kuka ta soma yi sai jikinsa yayi sanyi. Ya manta rabonsu da fadan da zai janyo ya daga mata murya. Amma yau saboda Gimbi da ta janyo Anti Bebi gashi iyayenta sun sami sabani.

Sassauta murya yayi “Kiyi hakuri Amina, kamar yadda kika sani Gimbi tun tana karama bata son komai nata ‘yan uwanta su taba. Saboda wannan halin kin sha dukanta ina hanawa. Tsoro nakeji kada dalilin zuwan surukarta ta canja hali”

“Nima abin da ya dameni kenan, zanyi bincike akai amma dole ka kirata ko bayan bakinsu sun koma ne ka nuna mata bacin ranka” daga haka ta tashi zata shige ciki ko kallonsa bata yi.

Alh Mudi yayi murmushi “Haba Aminatu ban sanki da fushi ba, kiyi hakuri tsawar da nayi miki”

Yadda ya langabe kai sai ya tuna mata da lokutan da sanda suke da kuruciya. Dariya tayi a ranta tace Bebi ba kyau. Yanzun nan sai ta kashe aure da kisisinarta.

******

Bayan kwana biyu su Harisu suna tunanin tafiya washegari cikin dare jinin Maamu ya hau sosai likitoci suka taru a kanta. Haka suka hakura da tafiya sai sun ga an sallameta. Tsabar fargabar tafiyar mutanen Fika ne ya dameta. Duk halin Tikeke da Hinde har da Bomoi baisa taji haushinsu ba. Ganin idanunsu ya kawo sauki a zamantakewarsu da Gimbi da Awaisu. Yanzu tattalinta yake sosai yadda yake yi a baya. Ita kuma Gimbi rashin sanin me Anti Bebi ta tanadar mata yasa ta kasa sukuni. Duk irin luguden da akeyi mata a gida hankalinta baya kai. Wulakancin da ta soma na saka turaren wuta ko ta fesa na ruwa idan sun tashi daga wuri duk ta dena. Tunaninta kaf ya koma wurin neman wani bokan wanda yafi Wangesi. Idan ba haka ba kuwa tana ji tana gani Anti Bebi zata kashe mata aure ta tagayyara mata rayuwa.

So take yi ta fita ma amma kullum a  asibiti suke yini. Cikin dare ta kasa bacci sai juyi take yi tana neman mafita. Wata shawara ce ta tsaya mata da sassafe kuwa ta aiwatar.

Dreban Anti Bebi ta kira Balele ta kwantar da kai sosai tace tana son yazo batare da saninta ba. Alqawarin dubu dari tayi masa yace gashi nan zuwa. Duk wahalar da yake da Anti Bebi bakar rowa ce da ita. Daga dubu ashirin sai talatin ke rabasu.

Da yake dan hutun da aka bata na jinya ya kare tunda ga su Ummukulsum ta koma aiki yau. Office yaje ya sameta. Babu wata rufa rufa ta fada masa abin da take nema.

“Idan kin shirya ko yau sai na kaiki wani kauye can jihar Neja. Mutumin bala’i ne me zaman kansa. Amma sai kin saki kudi “

Gimbi tayi murmushi “indai kudi ne kada ka damu. Ko yanzu zamu iya zuwa domin a matse nake.”

Mukullin motarta ta bashi dama drebansu yanzu daga kai yara makaranta sai asibiti. Wayar ogansu ta kira ta fada masa jikin surukarta ya tashi tana ICU. Sunyi tafiyar awa uku sannan suka isa wani kauye. Gidan duk yara da mata. Dakin Malamin tsibbun Balele ya kaita inda ta fadi bukatunta akan mijinta da babarsa da kuma Anti Bebi. A take yace ta bashi dubu dari uku. Babu musu ta kirga ta bayar. Ya hado mata wani ruwa a jarka yace ta yayyafa duka gidan tana kiran Maamu da Awaisu a duk zubawa. Anti Bebi  kuma daren yau zai karya duk wani tsafi da ta taba yi.

Gimbi taji dadi sosai ta karba tana ta godiya ta fita. Balele ya koma dakin ya kalli yayansa

“Kirgo min nawa nayi sauri mu tafi”

Wan nasa yayi murmushi ya dauko dubu dari da hamsin ya bashi suka tafa suna dariya ya fice.

A hanya ta sauke shi ta wuce gida. Ko mayafi bata cire ba ta fara aikin yayyafa ruwan dattin da suka bata.

Laminde tana kitchen ta dawo saboda su Amir zasu dawo daga makaranta taji motsi. Lekawar da zata yi ta hango Gimbi tana zuba ruwan tana cewa

“Safara’u! Awaisu!”

Hantar cikin Laminde ta kada sosai don tsoro. Komawa tayi ta rufe kitchen din yayin da Gimbi ta shiga daki ta ajiye sauran ruwan ta fice daga gidan.

Laminde ta fito ta yafa mayafinta jiki na bari. Ayatul Kursiyyu ta karanta tana ta tofawa a gidan. ‘Yar purse dinta ta dauko domin daga nan gidan Mama ta nufa. Kofar gidan taji an taba Gimbi ta sake shigowa. Sako ta barwa maigadi ya fadawa Laminde yace ai tana ciki. Itama a tsorace ta dawo.

Suna hada ido duk suka rude. Gimbi ta dake tace “kinji shigowata?”

Bakin Laminde ya soma rawa. Hakan ya tabbatarwa Gimbi ta ga abin da tayi.

“fada min nawa zan biyaki ki bar maganar nan a gidan nan”

“Shawara kawai zan baki ki dena bin malamai akan Maamu. Duk duniya babu halittar da Allah Yake ambaton bautarSa tare da yi musu da’a bayan ManzonSa kamar iyaye. Me Maamu tayi miki haka kika canja har kike musu asiri”

Gimbi ta kirkiro murmushin dole “kai Laminde ashe baki fahimceni ba maganin tsari ne na yayyafa saboda kariya “

Laminde ta kalleta ta watsar saboda duk ta sire mata girma ya fadi, hanyar waje tayi Gimbi tana binta da sauri hankalinta a tashe.

“Ki tsaya muyi magana ta fahimta. Zan biyaki sosai yadda ko kin dena aiki zaki sami jari”

Sauri Laminde ta kara tana bude gate Gimbi a gigice don bata san ina zata ba ta cewa mai gadi ya kamota. Jin umarnin da aka bashi akanta yasa ta kwasa a guje sai dai bata duba titin nasu ba mota ta taho da gudu tayi gaba da ita sai jini ne ya wanke wurin.

Wata muguwar kara Gimbi ta saki tare da dora hannu a ka ganin yadda jini yake bin jikin Laminde. Duk abinta tana tsoron yin kisa. Mai motar ya tsaya ya fito a guje shima yana fatan Allah Yasa baiyi kisan kai ba. Motoci ne suke tsayawa ganin yadda jama’a suka fara taruwa a wurin saboda gidan nasu a bakin titi yake.+

Ana kokarin sanya Laminde a motar mutumin da ya bugeta sai ga ‘yan sanda biyu daga wurin junction din da ake bayar da hannu. Tambayoyi suka danyi na sanin wacece sannan sukace a wuce asibiti. Sai da suka isa National Hospital sannan Gimbi hankali ya fara tashi da irin tambayar da suke mata. Daya cikin ‘yan sandan yace a cikin ‘yan kallo wani yace biyota akayi ko me zata ce game da hakan.

Nan fa ta kara rikicewa tana nemarwa kanta mafita kada asirinta ya tonu. Karya ta sharo a take a wurin irin wadda ko Laminde tayi rai baza’a yarda da abin da zata ce ba tunda mai aikice.

“Ai na fada muku mai aikina ce. Sata na kamata zatayi min shine ta gudu”

Dan sandan yace “kina da shaida akan hakan?”

“Tambayi mai gadi shi nace ya tsayar min da ita”

“Zamu jira likitan ya fito domin ji daga bakinta”

*****

Zaune Awaisu yake yana sa hannu a wasu takardu Ummukulsum ta kira shi. Gabansa har dan faduwa yayi kafin ya daga yana tsoron ko jikin Maamu ne. Muryar Baaba yaji da alamun bacin rai

“Anya Awaisu kai da matarka kuna kyautawa kuwa? Ace mara lafiya tun abincin safe har yanzu shiru “

Ajiye biron hannunsa yayi ya mike tsaye “Baaba ina Laminde?”

“Kaniyarka, Laminde kake aure? To tun dazu ta tafi don sauri ko dreba bata jira ba baiwar Allah tace zata jira yara su dawo ta bayar da abincin. Kuma su Tikeke ma gida zasu koma idan an kawo saboda likita yace muna cika dakin”

Hakuri ya bata sannan ya kira Gimbi. A lokacin tana ta tararrabin farkawar Laminde da abinda zata fada sai waya ta shigo mata. Har wani zabura tayi don tsoro. Yana kira yaji wayarta busy.

*****

Sunan Ogansu ta gani. Jiki a mace ta dauka tana tunanin karyar da zata sake yi masa.

“Mrs Awaisu kin tayar mana da hankali. Sama da awa hudu kince mother in-law dinki tana ICU. Ina ta kira tun dazu baki dauka ba”

Yawun bakinta taji ya kafe ta kasa magana. Shi kuwa ya cigaba.

“Da naji shiru na kira maigidan naki”

Bata san lokacin da ta daga murya ba

“Ka kira wa??? Ya dauka???”

“Ban same shi ba shiyasa na sake kiranki. Idan mun tashi zamu biya asbitin mu dubata ni da sauran staff.”

Kafin ta tattaro kalmomin da zatayi amfani dasu domin dakatar da zuwan nasu ya kashe wayar. Ji tayi gabadaya duniyar tayi mata zafi. Kiransa take shirin yi sai ga ba Awaisu ya shigo. Dan sauran kuzarinta a take ya kare taji cikinta ya duri ruwa. Tana amsa kiran ta jiyo muryarsa kamar zata fasa mata dodon kunne.

“Wane irin wulakanci kike yi min ne? Kin barmin uwa da baki a asibiti babu ke babu Laminde. Wannan aikin naki wanda na lura duk tsaurin banki kin mayar dashi wurin gantali shi zan hana kowa ya huta”

Ita mamaki take yi yadda ta kashe kudi har dubu dari hudu lokaci guda amma komai ya rikice mata haka. Sauke murya tayi har ta fara saduda

“Muna asibiti da Laminde”

Wani mugun tsaki yaja “to kiyi maza ku karasa dakin a kai musu abinci. Yau ni da ke ne wallahi idan na dawo. Sai kin fada min what you have against my family”

STORY CONTINUES BELOW

Tuni ta amincewa ranta Anti Bebi tasa Wangesi ya warware sauran aikinsa sannan an kara mata da na bakinjini. Bayani tayi masa na inda suke yayi saurin fitowa babu shiri. Abinci ya tsaya ya sayawa su Maamu sannan ya wuce asibitin. Bayan yaje ya fada musu inda zashi tare da Harisu sannan ya kira dreba akan yazo ya dauki su Maman Rumana zasu je suyi girki bayan sun gama cin abincin.

Asibitin da aka kwantar da Laminde suka wuce. Suna zuwa ya wuce emergency inda Gimbi tace likita na duba ta, ga kuma police a gefe. Da isarsu likitan ya fito ya sanar dasu an samu jinin da take zubarwa sakamakon wani karfe a gefen titi da ya soke mata cinya ya tsaya. Sannan ta sami karaya a hannu ga kuma fuska da ta kumbura saboda buguwa. Bayan ya tafi Awaisu ya kalli Gimbi tana ta rarraba idanu.

“Abin da ban fahimta ba shine me ya kaita fitowa bayan dreba ne yake mayar da ita idan ta gama girki”

Shiru tayi babu amsa.

“Baki ji me nace bane? Wai ke ma din me kike yi a gida a wannan lokacin. Kina maaikaciyar banki amma sai kiyi ta yawonki son rai”

Tsoron kada ya dawo da fadan kanta tace “kamata nayi a dakinka zata yi sata. Shine da ta ganni ta fito da gudu har hakan ta faru”

“Laminden?, shekara biyu da rabi bata taba sata ba sai yau?”

“Karya kake nufin ina yi mata ko me? Ka bari ta farka ka tambayeta mana”

Harararta yayi yana ji a jikinsa karya take yi masa.

“Dazu na tambayeki babu amsa. Nace me ya kaiki gida lokacin aiki?”

Kafin ta samu karyar da zata yi masa Harisu ya janye shi gefe.

“Wani sabon salo ne ka fito dashi na yiwa matarka fada ko bakaken maganganu a gaban mutane? Ba daidai bane iyalinka tayi maka laifi ka rasa wurin tsawatarwa sai bainar jamaa”

“Yaya wallahi tun ranar da kuka zo na rasa dalilin da yasa nake jin haushinta. Amma idan ka duba zaka ga da gaske laifin take yi. Gani nake kamar tana boye min wani abu”

Tausayi ya bawa Harisu hakan yasa ya dafa kafadarsa.

“Kada ka bari zamanku na shekaru ya baci a yanzu da kuka tara iyali. Idan Allah Yasa Maamu ta warke komai ya daidaita mun tafi ka samu kuyi magana ta fahimta.”

Shawarwari Harisu ya cigaba da bashi ita kuma Gimbi tana gefe ranta ya gama baci. Ba komai ke damunta ba sai tunanin Harisu ne yake ingiza Awaisu yana mata wulakanci yanzu. Ji tayi komai ya dagule mata ta fice daga wurin. Balele ta kira zata yi korafin rashin ganin sakamakon aikin bokansa.

*****

Anti Bebi na mota tana jiran Balele da yake tsaye ana zuba mai taji wayarsa na kara. Daukowa tayi zata mika masa ta taga ta kula an rubuta *hajiya gimbi*.

Wata irin dariya ta fashe da ita daga Balele har mai zuba man sai da suka tsorata. Yana shiga motar ta bukaci ya fada mata meye hadinsa da Gimbi. Sanin hatsabibancin uwardakin nasa yasa ya fada mata komai.

Cinya ta daka tana tafa hannuwa “lallai Gimbi tana cikin matsi. Shine don wulakanci ka kaita gidanka. To bata ga yaranka ba gari guda.”

Dukar da kai yayi kada tace ya dawo da kudin.

“Wannan kudi kaci rabonka a jikinta. Neman boka yanzu ta fara ma. Wani abin sai na kamata a hannu. Bari dai Shuhada ta gama idda “

Balele ya zaro ido “Hajiya me zaki sake yiwa Shuhadan? Da kin barta haka tunda auren ya mutu”

Yana tausayin yarinyar ganin yadda Anti Bebi ta juya musu rayuwa ita da iyayenta lokaci daya.

“Aure zanyi mata ba wata tsiya ba”

*****

Bayan Laminde ta farka kumburin bakinta ya hanata magana. ‘Yan sandan suka ce zasu dawo washegari. Awaisu yasa Gimbi ta kira wadda ta kawo mata ita domin a sanar da danginta. Da ma bazawara ce, danta daya Nafi’u dan kimanin shekara sha bakwai saboda tayi auren wuri. A hannun kanin babansa yake tun bayan rasuwar mijinta. Da suka ji sakon Nafi’u ya sha kuka suka yi shirin zuwa Abujan shi da kawunsa. Kawun nasa kuma yayi alqawarin ta dena aiki kenan. Gara ta nemi wata sanaar a kusa da gida.

*****

Washegari har yamma Laminde babu bakin magana. Mutanen Fika sun je dubiya tare da Maamu wadda aka sallama a ranar aka bar Hinde a wurinta.

Mama itama ta kadu da jin wannan mummunan labari taje ta dubata tare da wata mai aikinta wadda zata rinka kwana da ita.

Nafi’u da Kawunsa sunzo inda Awaisu yayi ta basu hakuri. Suma a gidansa sukayi masauki. Kawun yace ana sallamarta gida zasu tafi da ita. ‘Yan sanda kuma jira suke ta fara magana su dauki jawabinta.

****

Su Maamu na zuwa gida Baaba tace zasu koma Fika washegari tunda sun kwana biyu. Maamu ta rasa yadda zatayi. Tana son fadawa Baaba matsalarta a gidan Awaisu amma tana son rufa masa asiri. Da kunya ta kare rayuwarta a alfarma duk da sun dauketa tamkar jininsu. Ita da take burin Awaisu ya cigaba da kyautata musu ace kuma ita kanta ya gagara rikonta. Gashi bata da ‘yar uwa mace da zata iya fadawa domin neman shawara. Tana ji tana gani washegari suka tafi. Tikeke da Hinde duk tijarar da suka tanada abubuwan sa suka faru a gidan suka sa su yin lakwas. Bomoi kuwa yayi alkawarin dawowa nan da dan lokaci cin arzikin gudan jininsa. Suna bakin mota Rumana tana ta kuka har Gimbi na zolayarta wai ta zama ‘yar yaye. Ita wasan ma tsoro ya bata don bata saba ba.2

Dayake tafiyar sassafe ce suna tafiya itama da yaran dreba ya kaisu makaranta. Bandaki ta tafi ta rufe kanta tana kuka. A nan Yusra ta sameta. Bayan tambayoyi da kyar ta sanar da ita komai game da zamanta da kawunta.

“Da nice ke Rumana da tuni kowa ya manta na taba zaman Abuja. Ai wallahi da haukan gaske da na karya zan gudu. Rannan Umma take cewa na tambayeki ko baki da lafiya kike ta ramewa ashe yunwa ce. Kuma kika ki fada min” ta kare da hararta.

Rumana  bata amsa mata ba, hankalinta ya tafi tunanin maganar Yusra…anya ba haukan zatayi musu ba kuwa. Har fargaba take a tashi ta koma gida.

*****

A tsattseye suke gefen gadon da Laminde take tare da ‘yan sanda biyu sai Awaisu da Gimbi da kuma Kawu da Nafi’u.

A hankali saboda kumburin bakinta Laminde ta tashi da salati. Tana hada ido da Gimbi ta razana ta fara cewa 

“ruwan asiri”

Kasa kunne duk suka yi domin gane me take fada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *