EL-MUSTAPHA CHAPTER 6EL

EL-MUSTAPHA






CHAPTER 6










Bayan sati biyu


                  

Cikin kwanakin da  jiddah tayi ta dawo wata iri, tayi kuka har ta godewa Allah, bata da wani tunani a xuciyarta yanxu sai na mijinta da twins nata. 

                              

‘Ashe gaskiya el’mustapha yake gaya mata game da uwani, uwani ba mai qaunarta bace, yanxu ne ta gano abinda el’mustapha ke nuna mata a lokacin yake son ta gano, kenan yasan uwani qaryar ciwo take masa domin ta cutar da rayuwarta, she didn’t deserve dis hatred from uwani. 

                              

Ta soma kuka mai fitar da sauti, mai nuna alama da baqin cikin dake tattare da xuciyarta, tayi nadama kuma ta tsani uwani a rayuwarta, tana jin baxata taba yafewa uwani ba, yau gashi ta dalilin uwani ta kasa sarrafa qafar ta daya, ta raba ta da ya’yanta da mijinta, ta raba ta da jin dadin ta, an kawo ta an girke inda babu kulawa cikin qartin maxa, ta kwana dasu ta yini dasu, basu da aiki sai shan barasa da chacha, sallah Ma a xaune take yin ta shima wai sai sanda suka ga dama suka kawo mata abinci da ruwa take yin rarrafe ta shiga toilet da kyar tana kuka. 

                              

Yanxu kuma taji cikin yayi mata wani iri, ya qara nauyi, motsin da yake yi a da yau kam bata jisa ba, 

                              

Ya Allah ka raya min abinda ke cikina, ta maida kanta jikin gwiwowinta tana kuka sosai. 

                              

Tana haka goga ya shigo, shi dai Allah ya sanya masa tausayin jiddah, sati biyu da yayi tare da ita ya gane tana da sanyi, tana da nutsuwa da kamun kai sosai yanda take ta rufe jikinta da hijab a duk lokacin da xasu shigo. 

                              

Bata da rawar kai duk sanda xasu shigo sai ta gaidasu kuma kome suka ce bata masu gardama illah ta gyada kanta wannan dalilin ya saka kurma jin tausayin jiddah a karo na farko a rayuwarsa daya taba tausayin wata halitta. 

                              

Ya xuqi sigari yana kallon jiddah, 

                              

Tunda uwata ta haifeni ban taba tausayin kowa ba sai ke, saboda sanyin ki da haqurin ki na lura ke Sam baki da hayaniya, sabanin wasu mata da muke kawo wa nan, daga masu tsiwa sai yan iska ni kuma tattakasu nake, na sa belt na xane shegu idan kuma yarinya ta matsamin na dauke ta da alburushi wanda ya kawo ta yamin maganar banxa na kashe shi haka nake kurma game da kissa. 

                              

Jiddah ta sunkuyar da kanta tana share kwallah, 

                              

Saboda cikin da ke jikinki xan tausayamaki, na dauko maki tsohuwa a cikin gari xata kula dake kullum na maidata dan baxata xauna dake ba, idan kina jin fitsari ko kashi ki daina rarrafawa ita xata kula da komai, waccan shegiyar matar da ta bamu ajiyar ki itace xata biyata dan ubanta, ta biyamu ta biya wannan tsohuwar tace yau xata xo ta kawo kudin, in kuma qarya take min wlhy cikin ta xan farke har cikin gidan mijin nata, yama kika ce sunanki. 

                              

Hauwa ta bashi amsa kanta a sunkuye dan bata qaunar ganinsa ko kadan. 

                              

‘Yauwa sunan uwar babana ce amma ana ce mata kuluwa dan haka kuluwa xan riqa kiranki dan ni bana girmama kowa a rayuwata, uwata Ma kai tsaye nake kiranta da Ladidi, ya juya ya fice yana tangadinsa na maye, jiddah tabi bayansa da kallo tana sharar kwallah. 

                              

Baa jima ba taji uwani a gidan, tana jin su suna kururuwa sunga kudi. 

                              

Ina kika sami kudin bayan kince baki dasu, 

                              

‘Na mijina ne na dauko jiya bayan ya fita😀

                              

Kinyi qoqari, saura na waccan tsohuwar dana gaya maki tana kula da kuluwa, dubu dari biyu ne kudin ta. 

                              

Uwani ta bata fuska, batayi magana ba saboda tsoron kurma tasan tsab xai iya dukanta a gurin idan ta musa, sai tace idan xata dawo xata xo dasu. 

                              

Suka bude kudin suna dubawa suna jin dadi. 

                                              

                        

Ina so naga anti jiddah, da hannu suka nuna mata dakin da take. 

Jiddah ta rumtse idanuwanta, babu abinda ta tsana a duniyar nan kamar ta dora idanunta a fuskar uwani, ta tsane ta bata son ta ko kadan, to me uwanin taxo tayi a gurinta. 

Ayyah anti jiddah haka kika dawo cewar uwani bayan ta shigo dakin. 

Kiyi haqurin son mijinki ne ya sakani, kuma gashi har yanxu yaqi ya bani lokacinsa da kulawarsa, bashi da wata damuwa sai ta jiddah, ni kam ya xanyi ne a rayuwata ya soni ki gayamin anti jiddah me kika masa ko kin hada da boka ne. 

Shiru jiddah batayi magana ba kuma bata bude idanuwanta ba, uwani ta dafe kanta da goshinta, el’mustapha ya raina min wayo yana hada matsayina da banan, saboda na bigi aryan ya gaya masa ya kecewa duk na sake dukansu banan ta dauki mataki akai, to idan na kashe su ban san wani mataki xaa dauka ba musamman Ma idan na kashe jiddah.

Nan ma jiddah ko motsi batayi ba da uwani xata gane da taja komatsan qafafunta ta tafi ta bar jiddah. 

Duk da haka ga zannuwa na kawo maki guda biyu ki qara saboda wannan dake jikinki sunyi datti ga tsamin dauda hala bakya wanka ne. 

Jiddah ta bude idanuwanta a hankali tana kallon xannuwan da uwani ta miqo mata, hannu tasa kamar xata karbi xannuwan sai ta fisgo uwani qiris ta fadawa jikinta, ta fadi gurin, takaicin jiddah babu wani abu ko makami a dakin da xata illata uwani, ina Ma qafarta daya nada lafiya ta miqe sosai yanda xataji dadin dukan uwani da kyau. 

Ta shaqo wuyan uwani kamar iya qarfinta tana buga kanta a qasa, uwani ta soma ihu tana neman taimako, shigowar su goga ya saka jiddah sakin uwani dan bata qaunar wani daga cikinsu ya taba ta da sunan xai kwaci uwani a hannunta, ta soma kuka. 

Uwani ta tashi tana huci, kallabinta a hannu ta gyara rigarta tana kallon jiddah, 

Kin jawa kanki anan xaki tabbata ko nasa su kashe min ke, kuma wlhy sai na rama a gurin ya’yan ki. 

Ta fice a fusacce goga yabi bayanta dama shi kadai yaxo idan ta kurma ne su kashe kansu ko a jikinsa. 

Banan dauke da arham a jikinta, bai da lafiya sosai xaxxabi ke damunsa, dawowar su daga asibiti kenan tare da el’mustapha. 

Kallonta yayi cikin tausayawa yanda take bata lokacinta gurin kula da yaran ta xama kamar jiddah a gurin su abinda uwani ce ya kamata tayi, kuma iyayensu ba yanda basu so karban yaran ba el’mustapha ya hana yafi so yaransa suna hannun sa. 

Allah xai saka maki banan, bani da bakin da xan gode maki amma Allah kadai yasan abinda ke xuciyata game da kulawarki ga yarana, sai kuma yayi shiru yana sharar kwallah. 

Ki gayamin abinda kike so daga gare ni insha Allah xan maki shi ko menene. 

Banan ta dago tana kallonsa, tausayinsa ya qara mamaye xuciyarta, yanda el’mustapha ya dawo abin tausayi ne ga duk wanda ya sanshi a baya, 

Taji ina ma xata kasance dashi da ta dawo masa farin cikin da ya rasa a baya, da ta maye masa gurbin jiddah, amma Sam baxata iya hakan ba ta riga ta sanarwa jiddah ta amince da Islam kuma koda ace jiddah bata raye tabbas sai ta cika mata burinta na auren Islam domin yanxu sun soma dai dai tuwa. 

Ba komai ina yine saboda Allah da qaunar mahaifiyarsu, dawainiyar da kukayi dani tun ina yarinya ya isa nima na dauki dawaniyar yaran ku. 

Allah ya saka maki da alheri, ki qara kulamin dasu ki masu duk abinda suke so kuma ki kare min su kada ki bari suma a cutar min da su. 

Ya tashi ya fice daga gidan, arham ya soma amai sosai ta ajiye shi ta fice da sauri da xumar ta dauko abinda xata gyara wurin. 

Sai ga uwani ta shigo gidan tana huci, ba xato ta taka amai ta dubi arham din batare da tunanin komai ba ta dauke fuskarsa da Mari dai dai lokacin banan ta shigo dauke da tsumma da Cup na ruwa a hannunta.

Banan ta saki Cup din da tsumma ta sha gaban uwani dake qoqarin shigewa dakin ta, arham sai kuka yake yana kiran mummy. 

Me yayi maki kika dake sa Uwani?

Kallon ta take da mamaki, 

Yau kuma Uwani xaki kirani babu anti lallai yarinyar nan saboda na daki yarana kike tambayata ko wadda ta haifesu bata isa tamin wannan isar akan su ba. 

Uwani me arham yayi maki kika mare sa, shi nake tambayar ki, 

Uwani taja da baya ganin ganin banan din na shigowa cikin ta kamar xata dake ta, 

Saboda xai yi amai anan tsakiyar falo naxo na taka, kuma ke me ya hana tuntuni kixo ki kwashe. 

Oh saboda kin taka aman sa kika mare sa, yaron da ko lfy baida, to idan aman ya taba jikin ki kuma ya xakiyi. 

Uwani tace kamar ya tana kallonta, banan ta riqo hannunta uwani ta soma kiciniyar kwacewa sai suka soma dambe a falon, arham ya rude musamman da yaga ankai uwani qasa, ta soma kururuwa tana kiran mutanen gidan taimako. 

Banan ta cusa kallabinta a bakin uwani ta rufe yanda kowa baxai ji ba, 

Yau duk uban da xaki kira yaxo ai na dake ki dama ina ciki dake, ina ganin take taken ki akan yarannan ba kya tausayin su, kinsha duka na ina kyaleki yau duk xan fashe, ki kira qaumi ko hajja duk basu isa su hana na dake ki ba, 

Batare da tunanin komai ba ta goga fuskar uwani a cikin amai, yanxu sai ki mutu ko kuma idan kin tashi kada kibarshi da rayuwarsa…. 

Kai kai kai me nake gani haka cewar el’mustapha bayan ya nufi inda suke da sauri, ya dauke banan daga jikin uwani sai huci take kamar Serdia  a filin dambe. 

Uwani ta tashi tana cire kallabin bakin ta ta nufi banan da niyar kai mata duka el’mustapha ya hana, 

Me ya faru ne, 

Saboda arham yayi amai ta taka shine ta mare sa bayan ta san kuma bai da lafiya, yanxu da na sa mata aman a fuska nake son ganin matakin da xata dauka akaina ko akansa. 

El’mustapha ya dauki arham dake kuka yana kallon fuskarsa, ya kalli uwani yanda tayi wani xuru alamar ta daku a gurin banan, ga aman duk ya bata jikinta. 

Murmushi yayi har a ransa yaji dadi, Sam ya lura banan bata da haquri kamar jiddah, 

Xo ki gyara falon banan, kije kiyi wanka ki huta ni xan kula da shi kinji, sannu da qoqari Allah yayi maki albarka. 

Ya dubi arham, 
Is ok yaro na no need to cry again, baka ga anty banan ta rama maka dukan ba ai ko ba komai mutum yasha aman ka You have to be proud of it, kuma ba wanda ya isa ya taba ka, idan kuma mutum ya qara gigin taba min kai ko aryan xai sha mamaki kuwa, ya fice. 

Wanka yayi wa yaron, ya bashi magani bayan ya sha tea, ya kwantar dashi inda aryan ke barci tun daxu bai san wainar da ake toyawa ba. 

Dakin uwani ya nufa lokacin ta fito wanka daga toilet kenan tana tunanin qila sai ta hada banan da kurma, itace matsalarta a yanxu. 

Kallonta el’mustapha yayi qasa da sama, 

Kudin da kika dauka dakina naxo kibani abuna?

Gabanta ya fadi, kamar ta saki kashi a gurin yanda cikinta ya murda, 

Tace ni ban dauki kudin ka ba, ni da baa xuwa dakin ka. 

Ki gayamin gsky me kika yi da kudin da kika dauka a dakina, just tell me uwani, tun da nake xaune da jiddah bata taba min sata ba, cikin wannan bangare babu mai shigowa acikin maaikatan gidannan sai banan kuma nasan baxata dauki kudi na dan bata taba xuwa ko falona ba ballantana daki na, ina kika kai kudin. 

Jikinta ya dauki rawa ta fara rantse rantse tana hawaye ita bata dauka ba an mata sharri ne dan ko aljannunta basu sata. 

‘Naji shikenan baki dauka ba, kuma duk wanda ya dauka asirin sa na gab da tonuwa har da mai sa hannu a batan jiddah very soon xan gane. 

Kije na sake ki saki daya saki biyu, dan babu kyau yin uku ne da nayi maki mai gaba daya, na aure kine saboda jiddah babu jiddah a tare dani babu amfanin xamana tare da ke, ba kyason yara na ban son ki, kuma baxaki bar gidannan ba xaki xauna ne har sai ranar dana ga jiddah, har yanxu ke nake xargi kuma ina bincike akan ki, ya juya ya fice yana so yaje yayi tracing layin jiddah agani waye ya kirata urgent, abinda ya kamata yayi tuntuni amma saboda tashin hankali da damuwa baiyi wannan tunanin ba. 

                      
                      

Ya fito harabar gidan yana kallon securities, 

                      

Kada kubari uwani ta fita a gidannan, idan kuka yi wannan saken a yau wlhy ran ku xai yi matuqar baci fiye da kuskuren da kuka yi a farko. 

                      

Ya isa ga motar sa dai dai lokacin da wayar sa ta dauki qara, yana dubawa anty ikram ya gani, yayar sa. 

                      

Ya dauki wayar bayan ya kara a kunnensa, 

                      

‘autan mama, kaxo asibiti jikin mama yayi tsanani sai sunan ka take kira. 

                      

Ya tsinke wayar batare da yayi magana ba, da sauri ya shiga motar ya bar gidan abinda ya mantar dashi xuwa mtn office kenan🤦🏻‍♀. 


                      

Uwani tun daxu tsaye take, ta kasa xama ta kasa gasgasta abinda kunnuwanta suke jiye mata, el’mustapha yayi mata saki biyu, aa bata yarda ba kunnuwanta basu jiye mata da kyau ba. 

                      

Jikinta ya dauki rawa, lokaci daya xaxxabi mai xafin gaske ya taso ya rufe ta, jikinta yayi xafi rau, da kyar ta isa bakin gado ta xauna, sai ga hawaye sharrr na bin kumatunta. 

                      

Ji take duniyar ta mata xafi, duniyar Ma gabaki daya juya mata take, wani duhu ya mamaye idanunta, duk wani motsi ko sauti bata jinsa a kunnuwanta, sai ta gigice ta fashe da kuka mai tsananin gaske kukan da bata taba irin sa ba, 

                      

Ta rasa el’mustapha har abada, ta rasa wannan abin da take matuqar so da qauna, ta rasa wannan abin da take gani tana gab da samuwar sa, ta rasa wannan abin da ta wulaqanta yar uwarta saboda shi, ta rasa wannan mutumin mai matuqar tsada da muhimmanci a rayuwarta, el’mustapha yayi mata nisan da har abada baxata taba samun sa ba, ba ita kadai ba har jiddah ta gama samun sa, idan ta rasa shi shima xai rasa jiddah, jiddah Ma xata rasa shi, kowa ya rasa, indai tana numfashi a doron qasa el’mustapha da jiddah baxasu taba kasancewa tare ba. 

                      

Idanunta suka yi jawur saboda kuka,  da kyar ta janyo wayarta ta soma neman layin jamcy, kusan sau biyar tana kiran layin baya shiga, ta tashi da kyar ta xura doguwar riga, qaramin mayafi ta dora akan ta, key din motar ta kawai ta dauka ta fito da kyar tana layi saboda axababben ciwo da kanta keyi. 

                      

Horn tayi alamar a bude mata gate din, amma aka qi, tayi magana suka gayamata abinda el’mustapha yace, bata damu ba saboda yanda take jin jikinta, tana komawa dakin ta ta fadi ragwaf, xaxxabi mai xafin gaske ya rufe ta.

                      

El’mustapha kuwa yana isa asibitin kai tsaye ICU ya nufa, 

                      

Gaba ki daya mama ta fita hayyacinta ba abinda ke fitowa bakinta sai el’mustapha, hannunta ya hada da nashi bayan ya tsugunna a qasan gadon da take kwance. 

                      

Magana take yi a hankali da kyar yake iya jiyo abinda take fada, da alama wasiya take bashi musamman akan yayyunsa da yan uwansa, ya rumtse idanunsa sai ga hawaye na xuba, jikinsa ya dauki rawa lokacin da yaji tana kalmar shahada, kafin wani lokaci numfashin ta ya ajiye. 

                      

Ya bude idanunsa sosai yana kallonta, no he can’t believe it, mama ta mutu yanxu a hannunsa, ya soma jijjigata a hankali yana kiran sunan ta. 

                      

Da kyar nurses suka fitar dashi dakin, 

                      

Idan el’mustapha dake namiji yayi kuka akan mutuwar mama, mu da muke mata mu ce me? Cewar anty ikram tana kallonsa bayan ta riqo hannunsa. 

                      

‘Anty yusrah tace ba kuka xamuyi mata ba addua ce, kukan mu baxai amfanar da ita da komai ba, kuma ta roqa ko bayan ranta kada muyi mata kukan mutuwa. 

                      

‘Anty ikram da kanta ta soma share masa hawayen, a yanda el’mustapha yake jin kansa tamkar qaramin yaro, yau ya rasa maman sa, yayi kukan mutuwa a karo na biyu bayan na baban sa, bai san wanene na uku a rayuwar sa ba. 

                                      

                        

‘Anty ikram, mama has gone, shikenan babu uwa babu uba, shikenan baxan qara kwanciya a jikin mama ba, baxata qara min fada ko rarrashi na ba, mama baxata qara bani  abinci a baki ba, mama baxata qara saka ni dariya ko share min hawaye ba,mama baxata qara shafa kaina ta samini albarka ba,  tell me meyasa baxan yi kuka ba, meyasa baxan xubar da hawayen rashin uwa ba?

Daga anty ikram har anty yusrah kuka suke, 

Inna lillahi wa Inna ilaihir raji’un, shine abin da mutane ke Nana tawa a xuciyar su a duk lokacin da suka ji mutuwar mahaifiyar AIG, Mace mai fara’a da karamci, kowa nata ne babu kyama ga talakawa haka kuma bata koyawa ya’yanta su kyamaci wani mutum a duniya ba duk yanda yake. 

Bayan sadakar bakwai, abubuwa suka soma yiwa el’mustapha yawa, ya saka mama a xuciyarsa sosai yake mafarkinta, bashi da nutsuwa a koda yaushe sai nema mata gafarar ubangiji. 

Anyi saa uwani tayi masa gaisuwar mutuwar cikin nadama da qasqantar da kai kamar mai roqon el’mustapha xai maidata.

*

Inna ige yau kam ina jin motsin abinda ke cikina, ina roqon Allah ha rayamin shi har xuwa lokacin da xan haifesa, cewar jiddah tana kallon tsohuwar da aka dauko domin kula da ita cikin murmushi tana shafar cikin. 

Ai na gayamaki ina karban haihuwa a karkarar mu, kowa yasan ni ungoxuma ce, tun da nace kisha wannan gayen komai xai warware ai kinga kin sami sauqi. 

Jiddah tayi murmushi tana kallonta, nagode Inna ige, kin taimakeni da yawa, kin nuna min so da kulawa babu kyama, ina Ma ina da abinda xan saka maki dashi a yanxu da na baki domin nuna godiyata akan ki. 

Karki damu jiddah, da na kowa ne, amma xan tambaye ki, me kikayi aka kawo ki nan?

Hawaye suka taru idanun jiddah, 

Banyi komai ba Inna, kishiyata yar uwata ta jefani a wannan halin saboda mijina, ba wannan ne damuwata ba kamar ciwon qafata, dubi yanda ta kumbura, ina tsoron wani abu ya same ni na kasa tafiya a rayuwata.

Inna lillahi, kishiya jiddah?

Jiddah ta maida kallonta ga cikinta tana murmushi, ta daga rigarta tana kallon yanda yake motsi, farin ciki fal a xuciyarta ta san komenene yana cikin qoshin lfy. 

Hala shine cikin farko jiddah?

Jiddah ta dube ta tana girgixa kanta bayan ta rufe jikinta, 

Ina da yara biyu maza tagwaye, na jima ban sami haihuwa ba kafin wannan, duk abinda ke ciki ina son sa ne saboda ya wahala, jiddah ta bata labarin komai, Inna tayi matuqar tausayawa jiddah harda kwallah tayi. 

A yanda na tsani uwani bana son ko sunan ta naji an ambata a tare dani, ta cutar da rayuwata baxan taba yafe mata ba, ta soma kuka. 

Inna ige tace ni Allah xai saka maki jiddah tabbas wannan matar baxata gama duniya lafiya ba. 

Ina so na taimakeki jiddah amma ina jin tsoro, 

Jiddah ta dube ta, kada kiji tsoron komai na gayamaki mijina dan sanda ne, idan suka maidaki gida yau ki qoqarta kije ki sanardashi, xan baki lambar wayar da xaki kirasa ko kuma na baki address din office din sa. 

Inna ta ciro wayar ta cikin xaninta jikinta na rawa ta miqawa jiddah tana fadin, 

Ko ki gwada kiransa yanxu kiji, jiddah na qoqarin amsar wayar taji wani sauti daya hargitsa tunanin ta sai ga Inna xube a qasa cikin jini, 

Jiddah ta rude taja baya tana kallon qofar, kurma ne tsaye fuskarsa tamau ba alamar imani a tare dashi, ba tare da tunanin komai ba ya dauke fuskar jiddah Mari, tayi dif saboda Marin ya shige ta sosai, ta dauki lokaci kafin jinta ya dawo gare ta sai ga jini na fita ta hanci da bakinta. 

                

                        

Goga.. Goga.. Kurma ke kiransa cikin kakkausar murya kamar wani basaraken xaki, goga na shigowa ya nuna masa Inna ige, 

Dauke min wannan shegiyar ka fice min da ita a gidannan, ajiye ta a qofar gidan idan mun tashi shiga gari muje da ita mu yar da. 

Goga ya juya ya kira yan uwansa dan baxai iya ba shi kadai, yana mamakin me tayi aka harbeta. 

Ke dan ubanki ni xaki ci amana, kinma samu ina tausayamiki bana baki wahala har kike son tona min asiri, to daga ba wannan xan nuna maki ko waye kurma, babu sauran tausayi tsakanina dake, kuma kome kike so ke xakiyi da kanki ba wanda xan koma daukowa. 

Rarrafo ki fito nan, tun bansa kan bindigar nan na fashe maki tsakiyar kai ba, 

Da sauri jiddah ta soma rarrafowa tana kuka, a falon ya nuna mata inda xata xauna tana kallo aka fita da gawar Inna, a wane qauye Inna take su waye yan uwanta duk bata sani ba, ashe haka suke da yawa bata taba sani ba harda mata a cikinsu kowace tana xuqar sigari,  maxan kuwa sai giya suke sha, ta juya tana kallon inda kurma yake xaune suna hada ido sai da cikinta ya hautsina, mararta ta qule saboda wani fitsari da yaxo mata. 

Ina jin fitsari, shine abinda ta fada tana kallonsa cikin rawar jiki, 

Ya xuqi sigari ya furxar da iskan yana kallonta, 
Kiyi sa a nan ki xauna a cikinsa, xan axabtar dake ne na daina tausayinki, 

Tayi tunanin idan tayi fitsarin Dame xatayi sallah, dama a xaune take yin abinta, yanda take ji baxata iya riqe fitsarin ba, ta riqe cikin tana sharar kwallah, sai ga fitsari na fitowa qasanta ya soma gangarawa, 

Kurma ya bita da kallo bayan ya ajiye sigarin, ta tsorata a tunaninta ko wani abin xai mata ne, 

Tace kashi nake ji… 
Shima kiyi sa anan dan ubanki, kurma ya fada bayan ya tashi yana gyara bindigarsa, 

Goga… Goga… 
Kawo min ruwa da tsumma ta gyara gurinnan da ta bata kafin na hasala na dauke dayan qafar da bullet. 

*

Kwana biyu uwani ba kudi kuma tana so ta fita ko mai babu a motar ta, duk ta kode ta dawo wata iri, ko gayun yanxu an daina, ba ruwanta da kowa a gidan. 

Tana xaune taji dawowar su aryan daga skul, ta fita daga dakin sukayi karo da aryan a falo, 

Sai da ya tsorata da ganin ta, ya juya da gudu ya bar falon tsoronta suke sosai, tan fitowa taga driver yan so fito da arham motar yaqi sai kuka yake, 

Rufe motar ka kyaleshi kada ya fito ina ruwan wani, uwani ta fada bayan ga rufe arham a motar, ta karbi key din motar ta juya cikin gida ta shirya ta fita kafin el’mustapha ya dawo, dama tun bayin mutuwar mamansa take samu tana fita. 

Arham yayi kuka sosai har barci ya dauke sa a motar, ya kwanta yana maida numfashi, uwani na fitowa Sam ta manta da wani arham a motar ta shiga ta ja abinta ta fice daga gidan, ta jima da fita sai ga el’mustapha ya dawo, bashi da wani buri a yau kamar ya gansa a gaban uwani, sun riga sunyi tracing layin har record na yanda tayi da jiddah ta fito gidan duk yana da.

Yana fitowa sai ga banan dauke da aryan sai dube dube take alamar tana neman inda arham ya shiga. 

Sun dawo skul amma banga arham ba cewar banan tana kallon el’mustapha, 

El’mustapha yace arham ai baxai bata a gidannan ba indai driver ya dawo dashi, where did you left him aryan. 

In the car… ya fada yana kallon el’mustapha, 

Suka juya suna kallon motocin gida, 

Yace sauke shi banan xo ka nuna min wace mota ce, 

Ya qanqame banan alamar baxai sauka ba, ya dube sa yana fadin daddy our school car, ai anty uwani ce tace a barshi a ciki tunda baxai fito ba shine taje ta rufe shi acikin motar. 

                

                        

El’mustapha ya duba ba motar, hankalinsa ya tashi yana tambayar driver dake kai su skul, yayi masa bayanin komai, ya dawo yana kallon banan koma ciki da aryan cool your mind komai yaxo qarshe. 

Wayar sa ya ciro, office din su ya kira yana buqatar yan sanda nan da minti goma, ya dubi DSP Bello Marona😜, 

Kiramin ibrahim na kasa samun sa, ya laluba aljihunsa yaji bindigar sa na nan, ya juya da sauri ya shiga cikin gida, bai jima ba ya fito cikin uniform din sa, fuskar nan tasa ba walwala ko kadan. 

Amma ta ina xasu soma neman uwani, ina ta nufa duk basu sani ba sai sun jira dawowar ta. 


Jiddah kuwa da kyar ta gyara gurin, sai taji cikin ya koma mata gefe daya, tayi amfani da ruwan da aka kawo ta xuba a jikinta tunda ba wani xane da xata sauya, duk abinda take idanun kurma na kanta har lokacin da uwani ta shigo gidan. 

Tana yin parking arham na tashi daga barci, ta fita daga motar cikin sauri ko rufewa bata yi ba, ya tashi yana kalle kallen sabon gurin da ya gani a yau, yana ganin inda uwani ta shiga ya fito yabi bayanta batare da tsoro ko fargaba a tare da shi ba. 

Uwani na shigowa suka ci karo da kurma, 

A kashe min jiddah ka gayamin ko nawa ne xan biya daga yau xuwa gobe, 

Jiddah ta dago tana kallonta cikin tsananin tsoro da mamaki, 

Kurma ya xuqi sigari yana murmushi da alama xancen ya masa dadi tunda xai yi kissa, 

Mummy…….. Shine sautin da suka ji ya fito dai dai qofar shigowa falon, gabaki dayan su suka juya suna kallonsa, 

Bugun xuciyar jiddah ya tsananta da ganin arham, tsoro ya bayyana a fuskarta lokacin da taji uwani na fadin, 

‘Na manta yaro nan yana cikin mota naxo dashi, tabbas idan na koma dashi asirina xai Toni xai iya gayawa el’mustapha, shima ka kashe shi…. 

Jiddah ta xaro idanu tana kallon lokacin da arham ya nufo ta da gudu yana kiran, 

I miss you mummy…… Jiddah ta daqa hannu tana tsaidashi cikin daga murya ganin kurma ya saita shi da bindiga, 

Noooooooo Ar….. tayi shiru sakamakon kukan bindiga da taji, ta bude idanuwanta dai dai lokacin da arham ya fadi ragwaf a jikin uwani dake kusa dashi, 

Kurma ya maida bindigarsa ya ajiye yana fadin shima yana cikin Bill xaki biya kudin aikin sa, 

Uwani ta dauki arham taje har gaban jiddah ta ajiye mata shi, jini ya taba gyalenta batare da ta sani ba, murmushi tayi tana kallon jiddah kana ta juya ga kurma. 

Xan yi ma waya, kana kashe ta xan gayama inda xamu hadu na baka kudin bana son na cigaba da xuwa nan saboda xargi. 

Ina sauraren ki cewar kurma, uwani ta juya tabar gidan. 

Jiddah ta maida kallonta ga arham dake kwance a gabanta, ta rungumoshi tana kallon inda aka har besa a hannu ne, 

Kurma ya dube ta yana fadin kuskure aka samu kika ga na harbesa a hannu, xuciyarsa na so harbawa aka sami akasi, amma ba komai tunda ya mutu ai shikenan, ya tashi ya bar falon yana wata tafiyar qasaita. 

Kuka yaqi yaxo mata a wannan lokacin, sai jiri take gani, tana son tayi kukan ko xata sami sauqin xuciyarta amma ta kasa, kuka Ma rahamane, ta qara rungumeshi a jikinta bayan ta sumbaci goshinsa, addua take Allah yasa kar ya mutu, ina ma xata sami wanda xai taimaka yaje mata dashi asibiti, tana jin ihunsu a gida, 

Ta soma jijjiga arham, bata yarda ya mutu ba, arham ka tashi, mummy is with you, dan Allah karka mutu ka barni, sai ta gigice tana neman xaucewa, 

Help me, please help me and save his life, ta soma waige waige kamar me neman wani a gurin. 

Uwani na isowa ta ci karo da motocin yan sanda a gidan, gasu tsatsaye birjik kamar masu biki. 

Tayi parking ta fito tana Jan tsaki a xuciyarta, kicibis suka yi karo da juna, 

Ina kika kai min arham shine abinda ya fada idanunsa akan fuskarta, 

Tashin hankali ya bayyana qarara a fuskarta, ta soma musa bata ganshi ba, batare da tunanin komai ba ya dauke ta da Mari har biyu masu kyau. 

Ina kika kai jiddah da arham nake tambayarki, 

Ta dafe kuncin tana kuka lokacin el’mustapha ya lura da jinin dake gyalenta, 

Jinin menene wannan uwani, ta xare idanu tana kallon wurin, 

Ya shaqo wuyanta a gurin, 

Kada kice kin kashe min yaro uwani, ina kika kai arham da jiddah, answer me please, 

Ta soma kakarin mutuwa, ba qaramin shaqa yayi mata a wuya ba, duk wurin ba wanda yayi qoqarin karbanta hannunsa saboda duk yaran sa ne sai ibrahim kadai shima da kyar ya kwace ta hannunsa, 

Ka barni na kashe ta ibrahim kafin naji mutuwar arham a bakinta, dama na gayama nine mutum na farko da xai fara kamata dumu dumu, ya xaro bindigarsa ya sai ta a goshinta. 

Ibrahim yasha gabansa da sauri yana fadin, 

Me kake yi el’mustapha, control your temper, idan ka kashe ta ina xamu sami inda arham da jiddah suke, baka tunanin abokan aikin nata suka ji mutuwarta su gudu dasu ko su kashe su. 

Xamuje ta kaimu inda suke yanxu, kowa ya shiga mota cewar ibrahim yana kallon sauran yan sanda. 

                      

Ba abinda ke tashi a gidan sai sautin kida da raye raye, abokansu daga wani gu sai xuwa suke, kowane da makamin sa hannu, suna tafe suna shan giya wasu na xuqar sigari. 

                      

Ko taron me suke yi yau? Kurma yaci gayu cikin wasu qananan kaya, wando three quarter na black jeans, rigar farar mai qaramin hannu, sai qafafunsa dake sanye da sneakers👟, baqin glass ne sanye a idanuwansa, sai wata shegiyar hula da ya dora akan sa, ya gogu fa sai Ma kun ganshi😀

                      

Yana riqe da qugun wata budurwa tashi, bra ce kawai sanye a jikinta sai wani guntun buje ko pant babu a cikinta, tunda yasa hannu qasan bujen nata hankalinsa ya nemi gushewa, 

                      

Ta qara banqaro kirjinta tana xuqar sigari, hannunta daya na kan hannun kurma dake cikin bujen nata, 

                      

Baxan jure kallon wannan shashanci ba gwanda naje nayi kallon masu d’an kamfai🤧. 


                      

Har lokacin jiddah na rungume da arham, kanta yayi nauyi sosai, ga jiri da take gani idanunta sunyi jawur saboda kuka kuma har lokacin bakinta bai mutu ba wajen kiran wanda xai taimake ta. 

                      

Tana jin hayaniyar su, tana jin yanda suke shewa, 

                      

Help… Somebody help shine abinda goga yaji jiddah na furtawa lokacin da ya shigo da tashi budurwar. 

                      

Bai san wainar da ake toyawa ba ya qarasa yana fadin, 

                      

Ina kika sami yaro, ta bude idanu da kyar tana kallonsa, tana ganin goga ne jikinta ya dauki rawa saboda yana matuqar tausaya mata da taimakonta. 

                      

Yaro nane ya kashe min shi, ka taimaka ka kaimin shi asibiti, dan Allah ka taimakeni kada ya mutu. 

                      

Ya taba arham yana kallon inda kurma ya harbesa, 

                      

Shi wannan yaron menene laifinsa, meyasa kurma yake marar imani ne, 

                      

Numfashinta ya soma sama sama, 

                      

Tace ka taimakeni, ka kaimin shi asibiti kada ya mutu, dan Allah ka taimakeni. 

                      

Ina je dashi asibiti xaa iya kamani ai is very risk idan baki sani ba, bari naje na kira maki likitan dake duba mu a duk lokacin da aka harbi wani a cikin mu, ki kwantar da hankalin ki yanxu xan dawo. 

                      

Bai jira cewar ta ba ya tashi ya fice da gudu ko budurwarsa bai waiwaya ba cikin tausayin jiddah. 

                      

Jiddah ta qara rungume arham banda sumbatar sa ba abinda take sai kuka. 

                      

*

                      

Suna qoqarin saka uwani motar sai ga su hajiya da abba, sunxo yiwa el’mustapha gaisuwar mama, sunyi masa a waya basu sami damar xuwa ba sai yanxu. 

                      

Hajiya ma jiki yayi nauyi, ciwon qafafu take fama dashi. 

                      

‘Abba yace lafia el’mustapha na ganku haka. 

                      

El’mustapha bai yi magana ba, akwai kunya sosai tsakanin sa da surukin sa, ibrahim ne yayi masu bayanin komai. 

                      

Inna lillahi wa Inna ilaihir raji’un, iyayen suka juya suna kallon uwani tana tsaye abinta ba alamar nadama ko wani dana sani a tare da ita, ta dauke kanta gefe daga kallonsu tana tunxuro baki. 

                      

Hajiya kam har da kuka, 

                      

Tace duk yanda nayi dake uwani akan idan kina da sa hannu a batan jiddah kika musa, kika bar baiwar Allah da ciki cikin uquba, anya uwani xaki ga annabi kuwa, kwata kwata babu imani a xuciyarki, baxan taba yafe maki ba kije gaki ga duniya. 

                                      

                        

Allah baxai kamani da laifin komai ba tunda bake nayi mawa ba cewar uwani, a xuciyarta take maganar, sai anyi magana ki fara matsar hawaye kina kuka salon ace ni ke sakaki kuka saboda tsabar munafurci, ta gyara tsayuwarta hade da rungume hannayenta a qirjinta, 

‘Abba baiyi wata wata ba ya hau ta da duka, duk gurin ba wanda yayi qoqarin hanasa kuma duk dukan da yake mata bai raunana xuciyar uwani ba, bako digon hawaye a tare da ita haka take da taurin xuciya kamar namiji. 

Shi da kansa ya barta shima dan ya gaji ne, 

Tunda kika iya auren mijin jiddah na yafe ki a xuciyata uwani, na cire ki a raina bani da wata ‘ya a duniyar nan sai jiddah kadai, yau kin cutar min da ‘ya, kin cutar da baiwar Allah salihar mace mai haquri da kawaici akan duk abinda kike mata, kije gaki ga duniya alhakinta kadai baxai barki ba ballantana na iyayenki. 

Duk jikinta yayi tsami saboda duka, gefen fuskarta Ma ya kumbura, ta gyara kallabinta ta shiga mota cikin jin haushin tsayuwa da su, ga wani takaicinsu daya cika xuciyarta, duk gurin kallon mamaki ake mata

‘Abba yace el’mustapha kayiwa uwani duk hukuncin daya dace da ita a matsayin ka na dan sanda, kada ka tausaya mata ko nauyin dan tana tamu, Sam ba tamu bace kuma bamu Santa ba. 

El’mustapha dai baice komai ba har lokacin bashi da wani buri a yanxu kamar ya ganshi tare da jiddah da arham, 

Yace abba ku shiga gida tare da hajiya kafin mu dawo. 

Ni xan biku naga wane hali jiddah take ciki. 

El’mustapha ya riqo hannunsa cikin jin nauyinsa, 

Yace baxaka bimu ba saboda bamu san yanda abin xai kasance ba, ko mu kashe ko a kashe mu yan ta’adda ne masu xaman kansu, idan suka mana gardama xamu harbesu ne suma xasu harbemu dan baxasu barmu ba, kayi haquri ka xauna tare da mana addu’ar nasara. 

Allah ya kare ku kuma ya baku sa’a akan su, abba ya fada yana kallon el’mustapha uwa ya sa ihu dan baqin ciki da abinda uwani tayi.

Kowa ya shiga mota, suka dauki hanya, maimakon uwani ta basu direction na kwarai sai ta soma basu wrong direction. 

Wasa wasa sun kusa xagaye Abuja sai faman tafiya suke a duk inda ta nuna masu, hankalinta kwance ba damuwa tare da ita xatace kubi wannan titin, sai wannan layin. 


El’mustapha ne ya fara gano kamar tana yi masu wasa da hankali, ya daka mata tsawa yana tambayarta, ta tunxuro baki tana fadin, 

Ni na manta hanyar ne, na manta inda ake shiga aje gurin. 

Uwani hukuma cewar ibrahim yana kallonta cikin takaici. 

A yanda el’mustapha keji kamar ya kashe shegiya a gurin, duk wani fushinsa da Jan idonsa baxai saka uwani taji tsoron sa ta gayamasu gaskiya gashi kusan awa daya suna yawo a titi, dole sai yabi da dabara da rarrashi, ya dube ta cikin kalar tausayi. 

Uwani a hakan kike so na maida aure na dake?

Taji gabanta ya fadi, ta juya tana kallonsa, suna hada ido taji wani sabon sonsa da qaunar sa sun taru a xuciyarta, duk da ya rame wannan kwarjinin nasa yana nan, jikinta yayi sanyi taji kamar ta fada jikinsa saboda tsabar so, 

El’mustapha na ganin tana masa wannan kallon ya cigaba da rarrashinta harda riqon hannunta wanda ya saka uwani yin hawaye saboda farin ciki. 

Nan take tace su koma titin da xai fitar dasu Abuja, anan ta fara basu direction na gaskiya tanayi tana kallon el’mustapha, bata gajiya da kallon fuskarsa ko kadan. 


Kowa yayi mamakin dajin da suka shigo, baxaka taba tunanin akwai wata halitta mai rai a gurin ba, sun tsorata da lamarin uwani dama qarfin xuciya irin nata da har take iya xuwa nan ita kadai batare da tsoro ba. 

                

                        

Nesa da gidan sukayi parking motocinsu duka suka fito, kafin kace me duk sun xagaye gidan yayin da wasu ke shiga cikin gidan suna buya a hankali. 

Tun daga nesa goga da likitan da ya kira ya tsinkayo yan sanda xagaye da gidan, ya tsaya cak cikin mamaki ya akayi yan sanda suka san da gidan har suka xo, 

Ya ciro wayarsa ya soma kiran kurma jikinsa na rawa, dai dai lokacin kurma na sheqe ayarsa da budurwarsa, 

Har wayar ta tsinke baa dauka ba, goga ya sake kira, kurma yaja dogon tsaki cikin takaici bayan ya janye jikinsa daga nata kallon wayar yake yana ganin goga ya dauka da sauri hade da dura masa ashar. 

Goga bai damu da xagin ba ya gayamasa abinda ya gani. 

Police ya nanata a xuciyarsa, gabansa ya fadi ya sauka daga saman gadon bayan ya bigi duwawunta😂, 

Bindigarsa ya soma dauka yana fitowa har lokacin kida ke tashi, police ya fada da qarfi wanda ya saka kowa tsayawa cak bayan sun kashe sautin. 

Nan da nan kowa na soma neman makaminsa yayin da wasu suka soma buya. 

Likita ya juya da sauri yabar gurin, goga kasa tafiya yayi jikinsa yayi sanyi ya sami wuri inda baxaa ganshi ba ya buya yana kallon yanda xaa fito dasu kurma.

Jin an kashe sautin gidan kuma kowa sai gudu ake mata da maxa ana buya hankalin jiddah ya dawo jikinta, 

Meke faruwa, meyasa suke gudu suna buya kada dai wani abu ne yaxo ya cutar da ita. 

Taya xata iya daukar arham ta gudu dashi, waye xai taimaketa ya daukar mata shi ita kuma tayi rarrafe, Sam baxata iya xuwa ko ina ta bar yaron taba koda kuwa gawar sace kawai dan ta tsira da tata rayuwar, duk abinda xai xo ya same shi tafiso harda ita dan ta huta da wannan axaba da take ji a tare da ita, ta qara rungume arham qamqam a jikinta kamar wani xai xo ya kwace mata shi, ta daga kanta sama, 

Ya Allah save us, Allah ka kare min yaro na, Allah ka tserar damu daga wahala, sai ga wasu hawaye sharrr na bin fuskarta. 

Uwani ce gaba, sai el’mustapha, sai ibrahim da sauran yan sanda kowane da bindiga a hannunsa. 

Suna shigowa suka ci karo da jiddah xube a gurin rungume da arham, kafin el’mustapha yayi yunqurin xuwa inda take suka ji harbi from no where har suka sami wani dan sanda ya fadi gurin a mace. 

El’mustapha da sauran suka koma baya har uwani Ma cikin tsoro. 

Tsakanin su da yan sanda an rasa mai fitowa filin falon, qaton gaske kowa ya koma ya labe yayin da na waje ke ta artabu da masu son tserewa  sai sautin bindiga kake ji na tashi. 

Ga kurma ga el’mustapha kowane ya kasa fitowa. 

Jiddah tun da taga el’mustapha taji kamar anyi mata albishir da gidan aljanna taji ina Ma tana da qafafu da taje gare sa da gudu, ina Ma xata iya tafiya ta bar arham da ta rarrafa ga el’mustapha,  sai a lokacin ta lura da boyon boyo ne ake tsakanin el’mustapha da kurma kuma duk cikin su ba wanda ya san juna da matsayin wani illah dai sun tsinci kansu da fargabar haduwar juna. 

El’mustapha ya dubi ibrahim, ya karbi bindigarsa ya hada biyu, 

Yace be careful ibrahim xan shiga filin ina harbi, wait at my back har ka isa gurin jiddah, ka dauki arham daga jikinta ka fito dashi inaji saboda shine ta kasa tashi ka fahimce ni. 

Ibrahim ya gyada kansa cikin gamsuwa, 

El’mustapha yace ok get ready, one…. Two…. Three…..  El’mustapha ya shiga falon kai tsaye batare da tunanin komai ba ta ko ina sakin bullet yake baya waiwaye wanda ya saka su kasa fitowa su harbesa sun lafe sun yi shiru suna jiran ya bari. 

Ibrahim na fita da arham, el’mustapha yaba sauran yan sanda damar su shigo, nan fa sauran abokan kurma suma suka bayyana aka soma dauki ba dadi tsakanin su.

Ba laifi sun kashe yaran kurma da yawa harda mata haka suma an kashe yan sanda uku aciki, 

Suna haka bullet din daya bindigar el’mustapha ya qare, ya jefar da ita, haka shima kurma bullet din tasa ya qare amma bai jefar ba, 

Uwani na gefe cikin tsoro jikinta sai rawa yake kuma a lokacin ba abinda kurma ke buqata na ganin ya kawar da jiddah da uwani ko an kashe shi buqatar sa ta biya. 

Jiddah kuwa matsawa tayi ta takure guri daya banda addua ba abinda take, xuciyarta sai bugawa take, ga mararta dake mata ciwo saboda tashin hankali da ta sami kanta a ciki, ta riqe kasan cikin tana addua sosai. 

Idanun kurma na kan el’mustapha bai san meyasa yaji ya tsani mutumin ba sosai ya kashe masa mutane, cikin dabara ya iso bayan el’mustapha batare da tunanin komai ba yasa kan bindiga ya buga masa a kai iya qarfinsa, 

Luuuu el’mustapha yayi kamar xai fadi cikin jiri, ya dafe gurin yana juyowa ya saki bullet sai a tsakiyar goshin kurma, nan take ya fadi gurin a mace, sosai hankalin uwani ya tashi. 

Jiddah ma hankalinta ya tashi ganin jini na fita kan el’mustapha, da kyar ya kai qasa dafe da kansa yana kallon jiddah itama shi take kallo idanun ta taf da hawaye. 

Come to me jiddah, show me how happy you are today, I miss you so much, you are olways in my heart. 

Ta girgixa kanta tana hawaye, ta soma rarrafe har ta isa gare sa, meke damun ki jiddah, meya sami qafar ya tambaya bayan ya kai idanunsa akan qafar da ta kumbura, 

Sun kashe qafar el’mustapha, I can’t walk, 

Hankalinsa yayi matuqar tashi yaji xafin ciwon kan nasa ya bar jikinsa ya soma taba qafar yana surutai kamar wanda ya xautu harda hawayen sa. 

Uwani na ganin jiddah a jikin el’mustapha ta soma neman abinda xata halakasu dashi, tayi saa ta sami bindiga ta dauka dai dai lokacin da el’mustapha ya juyo yana fadin, 

Jiddana baxata rasa qafarta ba uwani na tafiya akan nata, batare da tunanin komai ba ya sakar mata bullet a qafa, ta saki qara mai raxanarwa nan take ta xube gurin a sume. 

El’mustapha ya qanqame jiddah a jikinsa yana sumbatar ta, ta ko ina, a rude yake yana neman rasa hayyacinsa, yana kallo aka fito da wasu da yan sanda suka kama a ciki suna fita dasu. 

Ya maida hankalin sa gurin jiddah ya soma jijjigata yana kiran sunan ta, dif ba numfashi a tare da ita. 

                      

  El’mustapha daukar ta yayi ya fito da ita, ibrahim na ganin sa ya fito da jiddah ya bude masa motar da sauri, 

                      

Goga daga inda yake labe yana hango mutanen da aka kama aka saka masu ankwa, ya baxa ido yaga an fito da kurma shiru, har lokacin da aka fara fitowa da gawarwakin su. 

                      

Jikinsa yayi sanyi hankalinsa yayi matuqar tashi ya juya da sauri ya bar gurin. 

                      

‘Wannan jinin dake fita kanka el’mustapha ya kamata ayi wani abu akai cewar ibrahim yana kallonsa cikin tausayawa. 

                      

El’mustapha ya dafe gurin yana tafiya da kyar, jiri nake gani kuxo muje asibiti ni arham ne damuwata a yanxu sai qafar jiddah. 

                      

Me ya sami qafar ibrahim ya tambaya yana kallonsa, 

                      

Nima ban sani ba amma bata iya tafiya da ita kuma naga ta kumbura shiyasa na harbi uwani a qafa. 

                      

Ka harbi uwani? Are you serious, meyasa el’mustapha?

                      

Bai yi magana ba ya soma tafiya dafe da kansa motar da aka kwantar da jiddah ya shiga, ya soma duba qafar cikin mamaki ko me ya sami qafar na ta?

                      

Ya dubi wani sergeant da kyar, ina aka ajiye arham, 

                      

Sir yana cikin waccan motar, 

                      

Maidoshi wannan motar xamuje asibiti, sai kuje da wadancan mutane ku rufe su kafin naxo. 

                      

Da sauri yaje ya dauko arham din lokacin el’mustapha ya kishingida ya kwanta, ibrahim yaxo yaja motar bayan ya saka uwani a wata motar cewa aje da ita asibiti. 


                      

Suna isa asibiti, kai tsaye akayi admitting nasu, el’mustapha yaje akayi masa dressing gurin aka rubuta masa drugs. 

                      

Ya fito yana xaune sai gasu anty ikram harda su hajiya. 

                      

Oh oh ashe kaji ciwo shine baka fada ba da muna waya cewar anti ikram bayan ta xauna kusa da shi tana taba gurin. 

                      

Ya yatsina fuska yana kallonta, 

                      

Tace ina arham din?

                      

Duk suna emergency har yanxu basu fito ba, 

                      

Ta sauke numfashi a hankali tana tsinewa uwani a xuciyarta. 

                      

Hajiya ta matso cikin jin kunya da nauyi, 

                      

Tace el’mustapha sannu da arxiki Allah ya basu lfy. 

                      

Yace amin kansa a sunkuye, 

                      

‘Abba shiru kawai yayi baice komai ba saboda baqin ciki. 

                      

‘Anty ikram tace ya kamata kaima kaje gida ka huta el’mustapha, ta dubi drugs din dake hannunsa, kasha maganin ne?

                      

Ya girgixa kansa yana kallonta, 

                      

Baxan iya xuwa na barsu batare da naji halin da suke ciki ba, ko naje sister hankalina baxai taba kwanciya ba just leave me. 

                      

Aa el’mustapha you have to go, gani xan xauna sannan ga iyayen ta fa, just look at you, uniform din sun lalace da jini kaima kana buqatar kulawa, ta ciro Swan cikin jakarta ta bashi tana kallonsa, kasha drugs din naka tukunna nasan you are careless xaka iya xuwa gida ka ajiye su ne, take it in front of me ingani. 

                      

Ba musu ya fara shan maganin kamar yanda Doctor ya gaya masa, suna xaune likitan da ya shiga da arham ya fito, ya gayamasu ya farfado sai dai yana barci yanxu sun samu sun cire bullet din. 

                                      

                        

Jiddah ce shiru har yanxu,  da kyar abba ya samu el’mustapha yaje gida saboda yayi wanka. 

Suna gurin ibrahim yaxo ya sanardasu halin da uwani take ciki duk cikin su ba wanda ya kula har ibrahim ya gama magiyar sa ya fice. 

El’mustapha kuwa drugs din daya sha harda na barci a ciki, yana xuwa gida wanka kawai yayi ya soma barci, 

Banan kuwa tana son jin yanda jikin jiddah yake amma bata sami fuskar tambaya ba. 

El’mustapha bai je asibitin ba sai bayan isha’i yana fitowa masallaci can ya nufa direct. 

Ya gaida su hajiya yana fadin ya jiddah?

Sai ga hawaye na bin kuncin hajiya, 

Tace har yanxu bamu san halin da take ciki ba, likitoci kawai ke shiga suna fitowa tun daxu. 

Jikinsa yayi sanyi, hankalinsa ya qara tashi ya dubi anti ikram da kyar yayi magana. 

Sister kixo kije gida, 

Itama jikinta a sanyaye yake ta tashi tayiwa su hajiya sallama ta fice, el’mustapha na bayanta har gurin motarta, ta riqo hannunsa tana kallonsa. 

Insha Allah jiddah xata sami sauqi, she will be on her legs, bana so ka saka damuwa a xuciyarka. 

Ya bude mata motar batare da yayi magana ba, ta shiga tana fadin ihsan ta kira daxu baka nan, gobe xata shigo taje kaduna daxu ne, idan jiddah ta farfado let me know please. 

Ya rufe motar yana fadin insha Allah, ki shafa min kan affan, 

Ta tada motar tana murmushi kawai, yana tsaye gurin har ta fice kafin ya juya cikin asibitin, 

Driver yana jiran ku hajiya, kuje gida dare yana yi. 

Baxaa yi haka ba cewar abba, idan muka je gida sai a barka kai kadai a asibiti da majinyata har biyu. 

Ba komai bane abba, nurses Ma suna kula da patient da kyau anan, damuwar yanxu jiddah bata farfado ba amma ba wani abu bane. 

Kai da baka da lfy kaine xaka koma gida el’mustapha, mu kuma xamu tsaya mu kula dasu, 

El’mustapha yace aa, idan haka ne abba kai xaka koma gida sai mu tsaya tare da hajiya amma ni baxan iya barin asibitin nan naje na kwanta batare da nasan halin da jiddah take ciki ba, ko naje banda nutsuwa ba barcin xanyi ba.

Da kansa ya raka abba har mota, ya dawo yana amsa call, mutane sai kiran sa ake ana masa barka da ganin matarsa. 


Likitoci biyar ne kan jiddah, tunda aka kawo ta suka duba yaron cikin ta baya xaune dai dai wannan dalilin ne ya saka tuntuni suke aikin ganin sun maida yaron dai dai shiyasa basu sanar da yan uwanta ba kada hankalinsu ya tashi. 

Cikin nasara kuwa suka yi aikin, sai dai rashin farfadowar jiddah ne abin tambaya?

Suna kan duba qafar jiddah sun kasa gano matsalar illah kumburin da kawai suke gani, duk da ba sun gama binciken ba suna cikin yin sane, Dr. Bakori shine babba a cikinsu, yayi matuqar tausayawa halin da jiddah da abinda ke cikin ta, duk kansu suna buqatar kulawa. 


El’mustapha haka ya dawo kamar wanda bashi da lafiya a jiki, ya jingina da bango wanda ya taimaka masa wajen daukar nauyin gangar jikinsa,  rungume da hannayensa a qirji. 

Likitoci kam sun tsananta bincike akan qafar jiddah da dalilin rashin farfadowar ta har xuwa wannan lokacin. 

Ya koma bakin barandar asibitin cikin tsananin sanyi ya xauna, jikinsa sai rawar d’ari yake amma bai damu ba, babu abinda yake sai addua, 

Ya ciro wayarsa daga aljihunsa yayi switching dinta saboda mutanen dake damunsa da kira, baya son damuwa. 

El’mustapha wata likita tana neman ka, yaji muryar hajiya a bayansa. 

Xumbur ya tashi yana maida glass din sa a aljihunsa, bai saurari hajiyar ba yayi cikin asibiti da sauri tana bayansa. 

Itace ta nuna masa likitar Dr Fulani Gafai, 

Tace kaine Mahaifin Arham El’mustapha, ya gyada kansa da sauri xuciyarsa na bugawa. 

Tace tun daxu yaron ya farfado yana neman maman sa, kaje ka duba sa. 

El’mustapha yaja wani numfashi yana jin wani sanyi a xuciyarsa ya juya xuwa dakin da aka kwantar dashi, tare da hajiya suka shiga dakin. 

Arham ya juyo yana kallonsa, 

Daddy anty uwani tace driver ya rufe ni a mota, taje dani inda mummy shine naji wani abu a hannu so painful, 

El’mustapha ya xauna a gadon, ya dora hannunsa a goshin arham kafin ya sumbace sa a goshi, 

Kada ka sake maganar uwani, try to forget her….. Arham ya katse sa, 

I saw mummy, tears rolling from her eyes, daddy take me to her. 

Hannun ka baya ciwo ne el’mustapha ya tambayesa yana kallon hannun. 

Akwai ciwo aryan ne yaji min ciwo, 

Aa kada kayiwa aryan sharri, yana can yana neman ka a gida. 

Daddy yayi kuka?

Yayi kuka sosai yana neman arham, anti banan ta Goya shi. 

Daddy nima xata goyani? El’mustapha ya gyada kansa ya juya yana kallon hajiya. 

Kayan da anty ikram ta kawo daxu naga harda kayan tea aciki, ko xaa hada masa ne. 

Hajiya taje tana duba kayan, el’mustapha ya dora kansa jikin arham, kansa ke masa ciwo sosai. 

Daddy kana da nauyi…. Yaji muryar arham, ya dube sa yana murmushi, 

Kai kuma gaka raggo, ya tashi daga jikinsa, hajiya da kanta ta bashi tea din, ta juya tana kallon el’mustapha, 

Ko a xuba maka abinci ne kaima baka ci komai ba fa, 

Aa hajiya bani tea din nasha saboda maganina da nake so nasha yanxu bana iya cin wani abu mai nauyi. 


Ta hada masa ta bashi, 

Yana gamawa ya tashi xai fice, arham ya kirasa, 

Daddy ka kaini inda mummy, I know where she is, inda wasu masu bindiga irin naka. 

Kayi barci mummy tana gida, very soon xata xo ta ganka, make sure you takes your drugs from hajiya idan ta baka kuma banda rigima, xata kula da kai kafin nadawo. 

Arham yayi shiru yana kallonsa, shikam jiddah yake son gani. 

El’mustapha ya dawo yana kallonsa, me kake so na kawo ma yanxu, 

Daddy bring Aryan, 

Tau shikenan xan kawo maka aryan gobe in kayi alqawari  baxakayi wa hajiya fitina ba irin na anti banan. 

I promise daddy, kaxo dashi da mummy. 

‘Yauwa good boy xan xo maka dasu, apart from them me kake so na siyo ma. 

Bana son komai hannuna yana ciwo ne, 

Xai daina ciwo ne, bari na kira likita ta qara duba ka, ya dubi hajiya. 

Kema kina buqatar kici abinci hajiya, arham ne sai kinyi haquri da rigimarsa as usual. 

Murmushi kawai tayi, el’mustapha ya juya ya fice. 

Ya isa dai dai lokacin da aa fito da jiddah har lokacin bata farfado ba, ICU aka nufa da ita yana daga bayansu. 

Yayi shiru yana kallon agogon hannunsa, sha biyu ta gota na dare. 

Allah ka farfado da jiddah lafia cewar el’mustapha bayan yaja numfashi yana furxar da iska a bakinsa. 
                      

‘Washe garin ranar da sassafe ibrahim ya shiga asibitin, 

                      

Yana xuwa kai tsaye dakin da aka kwantar da uwani ya nufa, ta farfado tana xaune tana shan tea abinta hankalinta a kwance ba wata damuwa a tare da ita. 

                      

Shine ya taimaketa amma bata jin xata iya gaidashi illa idanu da ta xuba mashi, 

                      

An tashi lafia, ya jikin uwani. 

                      

Ta tabe baki tana yatsina fuska, 

                      

Ina so na tambayeka jiddah tana da rai kuwa?

                      

Baiyi mamakin tambayar ba idan da sabo ya saba da wannan tambayar a duk lokacin da ya xiyarci uwani, yana tuna shine ya dauki nauyin kula da ita maganin ta da komai na asibitin duk cikin aljihunsa ne amma yarinyar ko godiya baxata iya masa ba hassalima kallon kirki baya samu daga gareta ballantana yayi darajar da xaa gaidashi, ita bata da damuwa sai ta jiddah. 

                      

Bata san cewa albarkacin jiddah da iyayenta ya saka ya taimaketa ba da kasancewar ta musulma.

                      

Dama hausawa na fadin duk inda musulmi yake dan uwan musulmi ne kuma xuciyarshi tasha banbam da ta Arne ko ya take, dama Allah ya halicci musulmi dan xumunci da qauna ga dan uwansa musulmi, 

                      

Koda basu hada jini ko yan uwanta ka ba, ko da kuwa haduwar hanyace, amma uwani ta kasa gane darajan mutanen da taci. 

                      

Ya dubeta fuskarsa a daure, naxo na duba jikin kine xuwa gobe xaa wuce dake a rufe ki kamar yanda el’mustapha ya bada umarni. 

                      

Ta fiddo idanuwanta tana kallonsa cikin tsoro, 

                      

Ni xaa rufe? Me nayi, jiddah ce kuma ya ganta saboda me xaa rufe ni, laifin me nayi, saboda mugunta da cin amana ana baqin cikin ganina a raye ake son kulle ni a hana min walwala da jin dadin rayuwata. 

                      

Ke har kina da bakin da xaki kira wani mugu ne, akwai wanda ya kaiki mugunta a duniya ne, ki shiga taitayinki uwani kisan me kike, wlhy idan baki roqi gafarar jiddah da iyayenki ba alhakin su baxai bar ki ba. 

                      

To naji ban warware ba, kuma baxan warware ba dan har yanxu ina jin xaxxabi. 

                      

Ya fiddo mata ankwa ya nuna mata kin ganta anan tuntuni ya bada ita kuma ya rantse sai ya rufe ki gobe ko dani ko ba dani ba, naso na taimakeki amma nagane ke wawiya ce bakida hankali gwanda ya rufe ki din ya axabtar dake kamar yanda kika sa aka axabtar da jiddah, wannan qafar taki Ma naso ta lalace ta rube acire a yarda kowa Ma ya huta da baqin halinki. 

                      

Uwani ta fusata tace idan remote din duniya a hannunka yake ka maidoshi baya ka barni inda ka ganni ba sai ka taimakeni ba, waya sani Ma ko sona kake shiyasa ka nace min kai baxaka yi xuciya ka barni ba, baka ganin kowa ya gujeni ba mai xuwa inda nake harda wadanda suka kawoni duniyar saboda suna min baqin cikin rayuwa ta, nidai baxan soka ba mata biyu ne dakai baxan je a ta uku ba, el’mustapha nake so kuma sai na mallakesa. 

                      

Murmushi yayi mai cike da takaici, 

                      

Yace uwani ana maganar ki gyara rayuwarki waya kawo maganar so anan? Wace alama kika gani ta so a tare dani, daga taimako? Ko mace na rasa a duniyar nan baxan iya auren mai mummunan hali irin naki ba, mata biyu nake dasu kuma alhamdulillah basu samin damuwa ba kamar yanda kika sawa el’mustapha da yan uwansa, Kuma ina so kisani burin ki baxai taba cika na mallakar el’mustapha ba qarya kike ba sonsa kike ba, ban taba ganin irin wannan son naki ba.

                                      

                        

Tayi shiru ba dan bata da abin cewa ba sai dan tunanin yanda xaa rufe ta a gobe, ibrahim ya juya ya fice. 

*

El’mustapha tare da Dr Bakori a asibiti, 

‘Mun kasa gano wannan matsalar ta qafafun matarka, but I have called my friend he was a consultant also but orthopedic, 

what do you mean Dr its about my wife explain it to me, cewar el’mustapha yana kallonsa,

Dr bakori yace ohhh AIG don’t hesitate kasan ko wane irin ciwo  akwai wadanda suka shahara akan shi,so da na duba qafar ne naga I can’t do anything bcos its not my specialities, daz why I called him, 

Knocking suka ji tare da sallama,  suka amsa, Dr Hafix ya shigo, cikin sakin fuska suka soma gaisawa, 

ya kai dubanshi ga El’mustapha  gaba daya ba ya cikin nutsuwa, 

Yace wai dama matar AIG ce d patient ur telling me,? 

Yah she’s, cewar Bakori

ohhh sorry pls AIG take it easy u know we care but Allah heals,where is d ex-ray, dr hafix ya tambaya yana kallon bakori

ga sunan Dr ammafa ahotunnan 
da akayi mata sun nuna babu wata matsala bayan wannan kumburin,

Yace no! dere most kai dai baka gani ba muje office pls induba da kaina,

Dr Bakori ya juyo yabawa el’mustapha  hannu, AIG bari muje ya duba pls kajiramu,

suka juwa su ka nufi office dinshi suna shiga yafara duba ex ray din. 
Ya kai tsawon 30mnt yana duba wa den ya dago da kanshi 

kasan me friend da kabari anyi report da ka fahimci matsalar kafar zo ka gani yana nunamai yadda veins din suke da kashin,what i concludes is dat rheumatism arthritis ne amma insha Allah zanyi iya koqarina akai ,I will prescribe the drugs,harda wanda za’a riqa shafamata a qafar,now where’s she,

tana ICU,amma nasan yanzu anyi transfer din ta zuwa obstetric ward dan ta farfado 

ok muje can din,
Suna fitowa  su kaga el’mustapha tare da Abba a gurin,  suka hada baki wurin cewa muje ko, 

sun dauki hanya sai ward, 

please AIG let’s see her first, cewar dr hafix yana qoqarin maida glass din idonsa, 

suka Shiga ya ganta sasai yaqara examine din qafar ya tabbata abinda ya ke tunani ne harma yaso yafi hakan OK muje my frnd suna fitowa ya taresu,

meke damun jiddana,me ya hana mata tashi, el’mustapha ya tambaya yana kallonsu

dr bakori yayimai bayanin da ya kamata and last am not sure ko xata tashi da qafar ko baxata tashi ba wannan ne ban sani ba amma munyi iya yin mu, is like ta rasa wannan qafar sai dai a siyamata wheelchair kuma asiyo drugs din da na rubuta after 1wk za’a kaita physiotherapy afara mata exercise kuma a gasa kafar dan jijiyoyin su saki.

El’mustapha ya dubesa a fusacce,
Yace ban san cewa baka san aikin ka ba sai yau, a hakan kake consultant ?kumburin qafa shi xai hana mata tafiya  har kake cewa baxata tashi ba, ko kaine ka halicce ta, Uwarka ce baxata qara tafiya ba amma ba jiddana ba, ba kai kadai bane likita a duniyar nan. 

Dr bakori baiyi mamaki ko jin xafin xagin da el’mustapha yayi masa ba domin bashine mutum na farko ba, ya lura jikin el’mustapha har rawa yake yana magana tamkar baa hayyacin sa ba yanda idanunsa suka juye, shi tausayi Ma el’mustapha ke bashi halin da yake ciki. 

‘Abba ya dafa kafadarshi shima yana sharar kwallah, 

El’mustapha kamar ba namiji ba, namijin Ma dan sanda, baka yi kuka dan ganin al’ummar da ake kashewa ba sai dan matarka, mu godewa Allah jiddah tana raye muna ganin ta ba mutuwa tayi ba, Allah da yafi mu sonta haka yake son ganinta, ka xamo mai haquri da tawakkali, yau idan jiddah ta same ka a wannan halin waye xai rarrashi wani waye xai qarfafa wani?

                

                        

El’mustapha yayi shiru ya kifa kai cikin cinyoyinsa, ya kasa yarda da abinda kunnuwansa suke jiyo masa jiddah baxata qara tafiya ba, saboda me xasu yanke wannan hukuncin bayan ba sune Allah ba. 

Abba ya miqar da el’mustapha, hannu yasa yana share masa hawaye, ya soma tausar el’mustapha da kalami masu dadi da sanyin imani tare da tuna masa muhimmanci yarda da qaddara, dr bakori Ma ya saka baki gurin rarrashin sa tare da nuna masa baa debe tsammani ga rahamar ubangiji. 

Xaku iya xuwa ku ganta tun daxu ta farfado. 

‘Abba yaja hannu el’mustapha kamar qaramin yaro suka nufi dakin da aka kwantar da jiddah, 

A bayan kofa ya tsaya ya rabe, ya kasa qarasawa yana leqenta, idanu ya qura mata yana kallon yanda take kallon dr bakori da abba,

ji yayi antaba shoulder dinshi Dr Hafix ne yace hey be a man please, focus on what’s important shine your wife ta samu lfya,capture the good times,develop from negatives, I know move on is never easy,you must fight to hold on,you fight to letgo please gather your strength before you enter, yayi masa sallama ya fice yana tausayawa mashi. 

Abba, Arham fa? Shine abinda ya fito bakin jiddah tana kallon sa.

Yace arham ya sami sauqi jiddah yana tare da hajiya tana kula dashi tace a gaidaki kafin taxo. 

Tayi shiru hade da shafa cikinta, 

Dr bakori yace yaron ki kawai kike tambaya shi kadai kike son gani?

Tayi murmushi cikin jin kunya da nauyin abba, ta dauke kanta gefe, shima abba murmushi yayi cikin tausayawa ya fito yana kallon inda el’mustapha ke rakube. 

Dr bakori yace, ki gayamin abinda kike son gani bayan arham, farin cikin ki nake so tare da kwanciyar hankalin ki, bana son abinda xai saka jinin ki ya qara hawa saboda abinda ke jikinki. 

Ta juyo tana kallonsa idanunta sunyi rau rau, 

Tace dr mijina nake son gani, 

Murmushi kawai bakori yayi sanda el’mustapha ya shigo dakin, 

A hankali ya soma taku ya isa ga gadon da take kwance, yaja kujera ya xauna dai dai da fuskarta yana fuskantarta, dr na ganin haka ya fita ya ja masu qofa. 

Hannun ta tasa tana taba ciwon dake kansa,  cikin murmushi tace sorry mustyna. 

Ya riqe hannunta ya sumbata yana kallonta, ya kasa furta kowace kalma a gareta, baisan yanda xai fuskance ta da maganar ba, shikam a wannan fannin ya kasa juriya ya kasa samun nutsuwa a duk lokacin da ya tuna jiddah baxata qara tafiya ba, Uwani ta cutar dashi a rayuwa. 

El’mustapha are you not happy with me, meke damun ka, meyasa ka canxa lokaci daya?

Ya tashi daga kujerar gadon ya hau yana kallonta har lokacin baiyi magana ba, sai ya shafa cikinta, 

Ta tsura masa idanu tana kallonsa, akwai abinda ke damunsa yake boye mata, yanayin sa kadai ya nuna hakan, kada dai ta rasa arham ne, gabanta ya tsananta bugawa, ta dora hannunta akan hannunsa dake cikinta tana kallonsa shima kallonta yake, 

Arham ya mutu ne?ta jefa masa tambayar, ya girgixa kansa, 

Talk to me el’mustapha, meke damun ka?

Yaja dogon hancinta yana murmushi a karo na farko, yace ba komai jiddah, ta soma qoqarin tashi yayi saurin riqeta yana tambayar, 

Kiyi a hankali saboda drip din dake hannunki, me xakiyi idan kika tashi, 

Inyi ta kallon ka el’mustapha tunda baxaka gayamin damuwar ka ba, 

‘Wannan karon Ma murmushi yayi yana jin wani sanyi da nutsuwa a xuciyarshi abinda ya dade bai samu a tare dashi ba, yasa pillow a bayanta da kanshi ya gyara mata ta kishingida, ta dan dubi qafar ta kamar xatayi magana kuma sai tayi shiru jin el’mustapha na fadin, 

                

                        

‘ni jiddah yaushe kika fara fita batare da sani na ba, meyasa da uwani ta kiraki baki kirani first kin gayamin ba, kuma meyasa kika hana dan sanda ko daya yaje dake. 

Jikinta ya dauki rawa, idanunta suka kawo kwallah, 

Nayi kuskure kayi haquri ka yafe min na fita bada ixinin kaba, ya dora yatsansa akan labbanta yana kallonta ido cikin ido, 

Ba sai kince in yafe maki ba jiddah, tuntuni na yafe maki but tell me har yanxu kina son uwani?

Jiddah ta lumshe idanuwanta sai ga hawaye shaaa, da kyar ta bude su tana kallon kyakkyawar fuskarsa, 

Ka daina tunamin da wata uwani a rayuwata, na fiddata a xuciyata da rayuwata, I don’t know her and I dont want to, yarda da qaunar da na nuna mata a baya taci amanata Allah xai saka min, bana jin xan iya yafewa uwani, ka sake ta tabar mana gida bana so na sake dora idanuna akan ta. 

Ita uwanin? El’mustapha ya tambaya cikin shigar tsokana, 

Ta daure fuska tana kallonsa, 

Xaiyi magana tayi saurin dakatar dashi hade da rufe kunnuwanta da tafin hannayenta, 

Bana so kadaina el’mustapha, I don’t want her in my life ko sunan ta bana son ji. 

Abin ya bashi dariya sosai, ya sumbaci bakinta a hankali, 

Sauke hannayen jiddah nima bana so tunda jiddatulmusty bata so. 

Ina so nayi wanka, jikina ba dadi kaje ka dauko min kayana kaxo min da aryan please, ta langabe kai tana kallonsa. 

Ai bama sai naje gida ba, komai naki naxo dasu suna gurin hajiya bari na karbo, ya tashi yana qoqarin fita, 

Ba yanda xaa yi naga arham?

‘Na gaya maki arham yaji sauqi baa bashi damar fita ko ina bane kamar yanda kema baa baki ba, kiyi haquri har lokaci yayi da kaina xan kawo maki shi, bai jira cewarta ba ya fice da sauri. 

Ta bisa da kallo har ya fice kafin ta maida kallonta ga qafar tana taba kumburin, bata ji el’mustapha yayi maganar qafar ta ba kodai likitocin basu duba qafar bane, sai ya dawo xata tambayesa.

Bai jima da fita ba sai gashi ya dawo dauke da kaya jikinsa na rawa ya ajiye, ya kunna wayar sa ya bata yana nuna mata wani vedio. 

Arham ne xaune a gadon asibiti yana cin burger, dariya yake da alama yana cikin farin ciki el’mustapha yayi masa vedio ya kawo mata, 

Mummy I miss you ya soma kissing wayar, itama kiss tayi Ma wayar tayi murmushi tana kallon el’mustapha, 

Sai ki daina damuna da arham ki kwantar da hankalin ki tunda kin ganshi a raye, 

70% of my damuwa ya ragu Mustyna sauran kuma na barwa xuciyata. 

Meya hana sauran damuwar su wuce, ya tambayeta yana kallonta, yanxu mecece damuwarki, gaya min naji jiddah na. 

Ka saki wannan matar ta fita daga gidan mu da rayuwar mu, I don’t want to see her again. 

Murmushi el’mustapha yayi yana matsa MacLean akan brush din ta, 

Saboda me xan xauna da igiyar aurenta akaina bayan babu jiddah a tare dani, tuntuni na sauwaqe mata ina jin kece kika matsa da auren ta saboda ke nake xaune da ita kuma babu ke meyasa xan cigaba da xama da ita? 

*NAYI NADAMA* El’mustapha, bansan yanda xan gayama baqin ciki da dana sanin dake xuciyata ba, amma ina roqon ka yafe min kuskuren danayi a baya da tilasta ma danayi akan sai ka aure ta, nayi ne saboda tausayin ta da kuma iyayen mu. 

Ya ja kunnenta cikin xolaya gobe Ma sai ki roqeni na auri banan tunda kin xama sarkin tausayi. 

Ta bata fuska tana kallonsa, 

Kace Allah ka tuba el’mustapha, da ina da iko dana bige bakin da yayi wannan furucin a yanxu, nayi hankali a yanxu wanda ka saka a inuwa shi yake saka ka a rana, ko da ina da qanwa baxan barta ta auri mijina ba ballantana wata banan, ta turo baki cikin jin haushi meyasa Ma kake mgnr banan a yanxu?

Ya kawar da mgnr ta hanyar sunkuyowa, bakinsa ya turo yana fadin kina da iko jiddah ki bige bakin idan hakan xai sanyaya xuciyarki. 

Ta kai bakinta dai dai nasa ta sumbata, ya xauna yana kallonta. 

Gobe ma jiddah idan iyayenki basu baki goyon baya kiyi abu ba ki qara kinji xaki ga abinda rashin bin maganar su xai janyo maki, keda Ma ba haihuwarki sukayi ba kenan ina ga alhakin su dake kan uwani. 

Uwani ta cuce ki babu wata cuta a tare da ita ta ciwon xuciya, she is pretending, jiddah ta fiddo idanu tana kallonsa, 

Taya akayi ka sani. 

Nima ban sani ba, dan sanda ne nifa jiddah kuma ba qaramin dan sanda ba, na saba yin bincike Kala Kala kuma ina nasara, ban taba xuwa asibiti na bincika halin da take ciki ba ko kuma tambaya amma dan na gwada ta nace mata naje asibitin na bincika a gurin likitan da ta hada kai, wallahi ban sani ba I just say it, daga yanayinta da amsar da ta bada nagano hasashena gaskiya ne amma baxan gaya maki ba har sai kin gano da kanki kuma kika kasa. 

Jiddah tayi shiru ta dubesa, uwani ta cuceni, dubi qafana el’mustapha, uwani har take cewa a kashe arham a gabana, a kuma kasheni, ta dauki kudin ka dasu ta biya kudin aikin mu, tsohuwar dake kula dani saboda sunji xata taimakeni suka kashe ta a gabana, kasan yanda nayi rayuwa tare da su kuwa, kasan yanda nake kwana na yini tare dasu, kasan irin abinda suke bani naci wai a matsayin abinci batare da sun duba abinda ke ciki na ba, babu tausayawa ko jinkai a tare dasu sai wani mutum daya suna kiransa goga, 

El’mustapha ya rufe mata baki da tafin hannunsa yana kallon yanda take xubar da hawaye, haka yake ji kamar shima ya tayata kukan saboda tausayinta, 

Ba sai kin gayamin ba jiddana, nagani da idanuna daga yanda kika dawo kamanin ki suna neman sauyawa, uwani Ma xatayi xaman prison ta dandana abinda kika ji. 

Ta soma share hawayenta, ya tashi yana fadin bari na kira wata nurse ta cire drip dinnan jiddana tayi wanka tacire wannan dattin dake jikinta. 

Tayi dariya tana fadin, kada kace kaji warin dattin ni bana son sharri, 

Wari kam jiddana baa magana idan na cigaba da jinsa tabbas xaa bani gado a asibitin nan, 

Ta janyo cup dake kusa da ita ta jefeshi a bayansa ya fice yana dariya, itama dariyar take. 

Wayar sa dake ajiye a gefenta ta soma qara, idanu ta tsura tana kallon mai kira, number ce akai ba suna, bata da niyar dauka saboda bata taba masa haka ba, har wayar ta tsinke bata dauka ba, 

Da wata nurse ya shigo   tana bayansa, bama musulma bace ta cire drip din, bayan ta fita ya dauki jiddah sai toilet. 

Yana ajiye ta ya dawo ya dauki brush din ta da sauran tarkacen da xaiyi amfani dasu. 

Shi da kansa yayi mata wanka, ya wanke kanta sosai, tayi brush, aka wanke dattin daya jima a jiki lungu da saqo, ta fito fes amma still hasken fatar ta ya dan dushe bai dawo ba, ya matsa yana kallonta cikin murmushi. 

Jiddah ta fara dawowa jiddatulmusty amma da saura. 

Ta watsa masa ruwa dake hannunta tana murmushi, ya dauke ta ya maidota qarfin hali kawai yake amma xuciya da ruhi babu abinda suke buqata a wannan lokacin kamar jiddah tun sanda ya dora idanunsa akan abubuwan da yayi missing a tare da ita. 

‘Nikam Mijin Jiddah doctors basu duba qafana bane har yanxu fa inaji bana iya tafiya da ita…… yaji muryar jiddah a hankali tana magana cikin duba qafar tana taba ta, 

Shiru yayi yana kallonta cikin tausayawa bai san yanda xai gayamata ba, ta dago tana kallonsa a raunane cikin seriousness, 

Baka gaya masu harda qafana yana ciwo bane,  dr ya gayamin sun gyara xaman baby na amma bai min mgnr qafana ba, kuma nasan rarrafen da nake yi ne ya birkita min xaman baby. 

Da kyar el’mustapha ya xauna kusa da ita, ya soma qoqarin shafa mata mai a bayanta yana fadin, 

Sun san da maganar inaji results dinne har yanxu bai fito ba. 

Ta sauke numfashi a hankali tana murmushi, ta gefen ido el’mustapha ke kallonta cikin tausayawa. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *