RABO AJALI
CHAPTER 2
Cikin tsantsar tashin hankali da zallar firgici Neehal ya d’ora hannunshi saman bakinshi had’i da zaro dadaran idanuwanshi waje,
bak’on al’amarin da Neesah taji ne yasa tsayawa cak a sunkuyen da take,
hannayenta duka biyun saman fuskarta cike da mamaki,
dan tunda Neesah take bata tab’a sanin zafin mari da duka a rayuwar ta ba sai yau,
dan haka ta diririce gaba d’aya ta fita daga hayyacinta,
cikin rawar jiki Neehal ya k’arasa ga Neesah ya sanya hannunshi ya d’oga ta,
cikin shagwab’a Neesah ta kalli Neehal had’i da sanya kuka,
kamar k’aramar yarinya haka Neesah ke kukan cike da shagwab’a,
” I’m very sorry Neesah….!, cikin zafin rai Najwah tace ” au baku daddara ba kenan….!?
Bai kula da maganar da Najwah take yi ba yace ” kiyi hak’uri Neesah please,
cikin kuka tace ” please kai ni bedroom d’ina,
” kam bura uba wallahi baki isa ba, a gaban nawa kike nufin zai shigar dake bedroom,
ni kuma na tsaya sokoko ina kallanku ko me….!?
Daga Neesah har Neehal babu wanda ya kula Najwah, idanshi kan Neesah yace ” ina ne bedroom d’in naki….!?
Da hannu Neesah ta nuna mishi, yana rik’e da ita ya nufi hanyar data nuna mishi,
gaba d’aya idan Najwah ya gama rufewa bak’in kishinta yakai mak’ura,
jikinta na rawa ta sha gabansu tana huci tace ” wallahi sai dai idan bana raye ne zaka shiga bedroom da wata ‘ya mace,
amma muddin ina raye hakan bazata tab’a faruwa ba,
pure red eyes d’inshi ya d’aga ya zubawa Najwah cike da zallar bak’i ciki,
da takaicin halayyarta yace ” gafara Najwah…..!,
” wallahi bazan matsa ba sai dai idan gawa ta zaku fara tsallakewa ku wuce,
” I said move, ki matsa ki bani hanya, yayi maganar cikin d’aga murya,
kuka Najwah ta sanya tana cewa ” Allah ko kashe ni zaka yi bazan tab’a bari ka shiga bedroom da wata ‘ya mace ba,
cikin zafin rai yace ” haka kika ce….!?
“Eh….! ta bashi amsa cikin matsanancin kuka,
” who is she please….!?
Neesah ta tambaye shi, cike da jin kunya yace ” she is my wife,
sosai Neesah ta zaro ido had’i da cewa ” what….! she is your wife….!?
“Yes, yace kanshi k’asa, d’an guntun murmushi tayi had’i da cije lips tace ” ayya no karka damu,
kuje kawai mayi magana letter Neesah ta fad’a tana shafa k’irjin Neehal,
cikin ranta kuma tace ” I will definitely tech her a lesson,
ganin yadda Neesah ke shafa k’irjin Neehal tana cije lips yayi masifar d’agawa Najwah hankali,
a haukace Najwah ta kuma yin kan Neesah da niyyar da cakume ta,
da sauri Neesah ta k’ank’ame Neehal had’i da cewa ” hey…! you idiot fuck your self,
waye ubanki cikin k’asar nan har da zaki shigo villa house ki mare ni,
na kyale ni sannan ki k’ara wani yunk’urin duka na,
ina tunanin kina hauka ne ko kuma kin samu tab’in hankali,
then…! get out from here ko in saka k’atti su fitar dake yanzu,
ta k’arasa maganar tana cusa hannunta cikin k’irjin Neehal,
da k’arfi Najwah ta runtse idonta cike da zallar bak’in ciki tace ” mari kau na mari banza, ko kina buk’atar k’ari….!?
Cikin murmushi Neesah tace ” oh! yeah karki damu ko mari nawa kike so kiyi min kiyi kawai kanki tsaye,
revenge day has come,
kana ta mayar da kallanta ga Neehal had’i dayi mishi kiss a baki tace ” kaje mayi magana letter,
kanshi kawai ya iya d’agawa, ya taka da nufin d’aukar files d’in dayazo dasu,
Neesah tace ” no ka barsu zamuyi magana,
bayyi iya cewa komai ba ya fita, da sauri Najwah tabi bayanshi har tana neman fad’uwa,
zuciyarshi na bugawa da k’arfi da k’arfi ya bud’e motarshi ya shiga,
yana ganinta tana nufarshi yayi saurin jan motar yabar wajen,
da sauri itama ta hau motar data zo da ita ta rama mishi baya da gudu,
a hankali yake jan motar idan ka ganshi sai ka rantse babu komai cikin ranshi,
amma can k’asan zuciyarshi Allah kad’ai ya san meke faruwa,
cikin nutsuwa ya bud’e motar ya fito batare daya rufe ta ba yayi shigewarta part d’inshi ya rufe,
dai-dai lokacin Najwah tayi parking jikinta na kerrrrma ta fita daga cikin motar tayi part d’inshi da gudu,
har tana yin tuntub’e,
jin k’ofar rufe yasa ta shiga bugawa tana kiran sunanshi,
Neehal kuwa dan kar yaji bugun k’ofarta da kukanta ya karya mishi zuciya,
yasa shi shigewa bedroom had’i da rufe k’ofa,
zama k’asa Najwah tayi tana rusa uban kuka had’i da bugun k’ofar da iya k’arfinta.
Direct part d’in Nana (mahaifiyarta) Neesah ta shiga da gudu tana rusa kuka wiwi kamar ranta zai fita,
a kid’ime Nana ta mik’e ta tari Neesah hankalinta ya kai mak’ura a tashi,
jikin Nana Neesah ta fad’a tana kuka cikin shagwab’a wanda hakan ba k’aramin d’agawa Nana hankali yayi ba,
” lafiya meke damunki….!?
Nana ta tambayi Neesah muryarta na cracking,
k’in yin magana Neesah tayi sai sautin kukanta data k’ara har da shid’ewa,
” soul meke damunki dan Allah ki sanar dani damuwarki….!?
Still shiru Neesah tayi, babu irin tambayar da Nana batayiwa Neesah ba amma tak’i magana,
jikin Nana na tsuma tayi dialing number President mahaifin Neesah,
bugu d’aya yayi picking, batare da Nana ta jira abinda President zai ce ba tace ” ka bar duk abinda kake yi ka dawo gida ba lafiya….!,
gabanshi na fad’uwa yace ” lafiya meke faruwa….!?
Bata b’oye mishi ba ta fad’a mishi abinda ke faruwa,
cikin matsanancin tashin hankali President yace ” tun yaushe ta fara kukan….!?
“Tunda ta dawo daga wajen meeting d’in daka tura ta, lafiya lau ta fita ta dawo tana kuka,
” what….! me yaron yayi mata…!?
“Ban sani ba danna tambaye ta bata bani amsa ba,
cikin hargagi President yace ” wallahi zan iya k’arar da zuri’ar Lagosa gaba d’aya kaf muddin wani abu ya samu ‘yata,
yanzu zan kira ubanshi nayi mishi kashedi, gani nan zan baro duk abinda nake na zo,
yana k’arasa maganar ya kashe,
zuciyar President na zafi yayi dialing number Alhaji Bilal Lagosa,
sai da ta kusa tsinkewa kana yayi picking yana murmushi yace ” ranka ya……!,
bai k’arasa ba, President yace ” dakata dan Allah ba wannan ne dalilin dayasa na kira ka ba,
ga tilon ‘yata can wacce nafi santa fiye da komai tana kuka tun bayan meeting da d’anka,
wallahi duk alak’ar dake tsakani na dakai zan iya rufe idona ruf na b’atar dashi muddin wani abu yayi mata,
yana kaiwa nan a magana yayi dropping call d’in,
sosai hankalin Alhaji Bilal Lagosa yayi masifar tashi, ba wai dan tsoran President ko dan wani ba,
a’a kawai dai saboda shi d’an kasuwa ne yasan kuma duk shaharar da yayi a duniya idan ya sake yayi fad’a da gwamnati akwai matsala,
cikin matsanancin b’acin rai da bak’in cikin duk kashedin da yayiwa Neehal,
amma bai ji ba sai da ya haifar mishi da matsala, Neehal na kwance yana tunanin mafita da abinda zai cewa Dady,
wayarshi ya soma ringing a hankali ya mik’a hannu ya d’auki wayar,
ganin sunan Dady yasa gabanshi mahaukaciyar fad’uwa a tsorace ya tashi zaune yana juya wayar,
had’i da tunanin abinda zai cewa Dady har wayar ta katse Dady ya sake kira,
Neehal bai d’aga ba yana shawarwarin abinda zai fad’awa Dady wayar ta sake katsewa,
ganin haka ya tabbatarwa Dady lalle akwai matsala babba,
dan haka take yayi cancel duk wani abu nashi yayo Nigeria,
a ranar Dady da President suka isa Nigeria kasancewar private jet ne dasu ba wani b’ata lokaci.
Ganin ya rasa mafita yasa shi tunowa da Nauman,
kanshi ya dafe tunawa da gayi da tun ranar da abin nan ya faru bai k’ara nemanshi ko tuntub’arshi ba,
haka bai ko je ya duba Umaima ba,
take yaji shi kanshi bai kyautawa aminin nashi na rai da rai ba,
cikin mutuwar jiki yayi dialing number Nauman,
Nauman na kwance saman bed ya d’aga kanshi sama yana kallan ceiling,
ya tsunduma duniyar tunanin yau kwana takwas kenan da zuwa gidan Neehal ,
amma kwata-kwata Neehal bai nemi shi ko a waya yaji ya yake ba,
bai kuma zo duba Umaima ba, sosai abin yayi mashi zafi da ciwo,
inda wani ne can daban yayi mishi hakan da babu abinda zaiji,
amma ace amininshi na mutuwa, lalle tabbas ya yarda mace tana iya shiga tsakanin d’a da iyayenshi,
balle abota, ringing d’in da wayarshi ta soma yi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya ke ciki,
ganin sunan Neehal ya sashi jan uban tsoki, had’i da gyara kwanciyar shi,
sau biyar Neehal yana kiran Nauman amma yak’i d’agawa,
ganin haka yasa Neehal sanin fushi Nauman yake yi dashi,
cikin mutuwar jiki ya mik’e yana sanye da kayan jikinshi,
sai neck tie da ‘yar saman cot d’in daya cire,
ta k’ofar baya ya zagaya ya fita danya san har lokacin Najwah na zaune bakin k’ofa,
har ya fito ya shiga motarshi ya tayar bata sani ba, sai da taji k’arar bud’e get kana tayi saurin mik’ewa,
amma kafin ta isa gare shi har ya fice abinshi, ya barta nan tsaye,
da gudu ta fad’a mota tayi gidansu dan a zatonta gidan yayi,
hospital ya fara zuwa aka shida mishi Nauman baya nan yana gida,
dan haka ya nufi gidan, bayan yayi parking ya fito part d’in Mama mahaifiyar Nauman ya nufa,
a parlor ya iske ta suna zaune harda Umaima da k’anan Nauman,
cikin da girmamawa ya durk’usa har k’asa ya gaida Mama,
ta amsa mishi cikin sakin fuska, yace ” Mama ya jikin Umaima….!?
“Lafiya lau, Alhamdulillah, cikin jin kunya ya bada hak’uri sosai kan abinda ya faru da Umaima,
Mama tace ” haba ai ba komai Neehal Allah ne ya k’addaro da hakan zata faru,
dan haka karka wani damu kanka kaji…!,
kanshi k’asa yace ” nagode sosai,
kana ya mayar da kallanshi ga Umaima fuskarshi a sake yana murmushi yace ” ya jikin naki….!?
Kanta ta kawai gefe tace ” nayi fushi Yaya, tunda sai yau zaka zo duba ni,
cikin murmushi yace ” ayya sorry sister ban nan ne nayi tafiya, kiyi hak’uri kinji….!?
“Lah Yaya wasa fa nake yi maka, ka daina bani hak’uri,
Mama ta mik’e tana cewa ” bari na kawo maka abinci,
da sauri yace ” a’a Mama a k’oshe nake daga gida na fito,
ya fad’a duk da uwar yunwar da yake ji, amma bai jin tension zai barshi yaci komai,
tayi mamaki sosai dan tunda take bai tab’a k’in cin abincin gidan ba,
ido ta tsora mishi sosai kasancewar tayi mishi farin sani,
tace ” lafiyarka kuwa Neehal….!?
Murmushin yak’e ya k’ak’aro yace ” lafiya lau Mama, dan karta kuma yin magana,
ko ta tambaye shi wani abu wanda zai saka dole yayi mata k’arya,
shi kuma babu abinda ya tsana kamar k’arya, bai san yayiwa wani daban k’arya ma balle Mama dayake yi mata kallan tamkar mahaifiyarshi,
yace ” bari na shiga wajen Nauman, ” to kawai Mama tace,
kwance ya iske Nauman yayi rigingine kusa dashi Neehal ya zauna a bakin gado,
ya k’ura mishi ido, sarai Nauman yasan Neehal ya shigo amma yayi kamar bai sani ba,
murmushi Neehal yayi yace ” Aboki kayi hak’uri mana tunda gani nazo,
Nauman baiko juya ya kalli Neehal ba balle yayi mishi magana,
dariya Neehal yayi yace ” please ka tashi muyi magana,
d’an tsoki Nauman yaja batare dayace komai ba,
Neehal yace ” eh..! naji dai bakomai,
tsoki Nauman ya kuma ja yace ” you’re my headache & my problem maker ,
kaje bani da lokacin magana dakai, kaje can ku k’arata,
” dan Allah ka tashi muyi magana ,
tsoki Nauman ya sake ja yace ” please live me along,
” amma dai kasan babu abinda nafi tsana kamar tsoki ko….!?
Da sauri Nauman ya mik’e zaune had’i da cewa ” nayi maka tsakin ya fad’a yana k’ara jan dogon tsoki yace ” kayi abinda zaka nayi d’in,
dariya Neehal yayi yace ” babu abinda zanyi, kaga yanzu ai gashi na tashe ka,
” har zaka ce min baka san tsoki naga matarka kusan kushe mu tayi ni da sister ta,
amma ko a jikinka, even waya ma ta gagara tsakanin mu,
wallahi yanzu ma nasan ba banza ce ta jawo ka ba, duk yadda akayi ta kuma b’allo maka wani ruwan shine kazo neman mafita,
” ni dai dan Allah kayi hak’uri ka tsaya muyi magana,
” ina jinka, Nauman yace had’i da komawa kwancen ya juyawa Neehal baya,
” yanzu a haka zamuyi maganar….!?
“To ba kunne ne ke ji ba, shiru Neehal yayi wanda yasa Nauman d’ago kanshi ya kalle shi yace ” ko ba kunnan ne ke ji ba….!?
“Please ka tashi ka saurare ni muyi magana a nutse, ina cikin babbar matsala wallahi,
dariya Nauman yayi yace ” ahab ai dama nasan ruwa baya tsami banza, uban me ta kuma b’allo maka…..!?
“Hummmm kai dai bari kawai Najwah ta b’allo min teku bama ruwa ba,
” me tayi ….!?
Nauman yayi maganar yana kallan Neehal
” jakwal ne sosai dan harda President da tilon ‘yarshi Neesah da Dady na,
zumbur ya mik’e zaune yana zaro ido yace ” meya faru….!?
Cikin sanyin murya Neehal ya fad’awa Nauman duk abinda ya faru tun daga farko har k’arshe,
idon Nauman nakan Neehal harya dasa aya, Nauman ya tab’a baki had’i da cewa ” Allah ya kyauta to,
“Amin, dan Allah meye shawara….!?
” Wa ni kake nufin zan baka shawara akan wannan mahaukaciyar k’idahumar, mai dod’add’iyar kwakwalwar matar taka….!?
” Wallahi kwata-kwata Najwah bata da hankali, kai ni ina tantama ma kan lafiyar kwakwalwarta,
gaskiya ku kaita Dawanau likitan mahaukata ya duba lafiyarta,
ayi mace babu abinda ta iya sai tijara, tirere da bankad’a gaskiya ya kamata kayi maganinta,
ka kuma koya mata hankali tunda na lura bata da hankali kanta hayak’i yake yi…….!
kasa jure munanan maganganun da Nauman ke jefar Najwah dasu Neehal yayi,
da k’arfi ya runtse idonshi cikin ranshi ya soma danasanin fallasa da tona sirrinsu da ita da yayi wajen Nauman,
a hankali ya bud’e idonshi ya sauke akan Nauman daya kafe shi da ido,
Nauman yace ” love is not blind an madness, is better ka farga daga duniyar makafarki ka dawo real world,
” ka ga ni dai bani shawara yadda zanyi da Dady yanzu,
” babu wata shawara da zata kareka kawai ka saurari Dady da abinda zai zaitar kanka,
yayi maganar yana shigewa bathroom.
Bayan Najwah ta k’arasa gida ta iske baya nan sosai bak’in ciki da takaici ya turnuk’e ta,
ranta ya bata ai kawai wajen Neesah ya koma bata hak’uri,
dan haka ta zauna nan tana dirzar kuka, a fusace Dady ya fito daga cikin mota batare daya bari ta k’arasa yin parking ba,
a parlor ya iske Najwah tana rusgar kuka wiwi bai damu da kukan ta ba,
yace ” ke..! ina mijinki….!?
Sosai gabanta yayi razananniyar fad’uwa, bakinta na rawa tace ” ban san inda yake ba,
jikin Mamy na rawa ta mik’e tana kallan Dady tace ” lafiya Alhaji meke faruwa…!?
Bai bawa Mamy amsa ba yayi dialing number Neehal,
Neehal na ganin kiran Dady yace ” ya Salam…!,
” lafiya…!?
Nauman yace yana saka kaya,
“Dady kawai yace bakinshi na rawa,
” to kayi picking mana, ” no ban san me zan ce mishi ba,
” idan baka d’aga ba kana k’arawa kanka laifi ne, dan haushi zai sake ji, gwara ka d’aga kawai,
Neehal na shirin d’agawa kiran ya katse, ganin bai d’aga ba yasa Dady kiran layin Nauman danya tabbatar suna tare,
kiran na shigowa wayar Nauman, Nauman ya kalli Neehal yace ” Dady ne,
Neehal yace ” please karka d’aga,
” kamar yaya karna d’aga nima so kake ka ja min….!?
Neehal na shirin yin magana Nauman yayi picking cikin girmamawa ya gaida Dady,
bayan sun gama gaisawa Dady yace ” ina Neehal….!?
“Gashi nan muna tare, ” ka kawo min shi nan da 5 minutes,
” to in sha Allah, Dady bai kuma magana ba ya kashe wayar,
Nauman ya kalli Neehal yace ” Dady yace na kai mishi kai, dan haka ka tashi muje,
jikin Neehal a sanyaye ya mik’e suka fita suka nufi gidan.
President zaune yana rungume da Neesah dake ta faman kuka cike da tsantsar shagwab’a,
President yace ” please soul ki sanar dani abinda yayi miki,
Nana tace ” wai me yayi miki ne soul….!?
Babu irin tambayar da President da Nana basu yi mata ba amma tak’i yin magana,
a fusace President ya mik’e had’i da cewa ” wallahi duk uban da ya tsayawa yaron nan cikin k’asar nan sai na ga bayanshi,
da sauri Neesah tace ” no Dad…!, karka yi mishi komai,
” idan kina san karna yi mishi komai ki fad’a min abinda yayi miki,
cike da shagwab’a tace ” Dad kasan matarshi ‘yar waye,
” yes…! nama je d’aurin auren ai ‘yar Ubayyu ce General custom controller na k’asa,
cikin kuka Neesah tace ” she slapped me….!,
” what…..!?
President da Nana suka ce lokaci d’aya,
“Eh…! mari na tayi saboda kishi,
tsantsar mamaki ne yasa President zama jiki ba kwari.
Nauman na gaba Neehal na biye dashi a baya suka shiga cikin parlor’n,
Mamy na zaune saman sofa yayinda Dady ke ta faman zarya,
Najwah na gefe dan tasan gaba d’aya laifinta ne,
k’asa suka zube had’i da had’a baki suka ce ” Dady ina wun……..!,
dakatar dasu yayi ta hanyar d’aga musu hannu yana kallan Neehal yace ” me kayiwa ‘yar mutane….!?
Kanshi ya sunkuyar k’asa batare daya ce komai ba,
baya Dady ya juya musu yace ” Nauman tambaye shi me yayiwa ‘yar mutane,
shima bayyi magana ba ya sunkuyar da kanshi k’asa,
Dady yace ” baka ji na ne….!?
“Kayi hak’uri Dady…!, Nauman ya fad’a a d’an tsorace,
” Okey kasan abinda ya faru kenan….!?
Kanshi ya sunkuyar k’asa, gabanshi na fad’uwa,
Dady yace ” nace ka fad’a min abinda ya faru ko….!?
Kallan Najwah Neehal yayi da jajayen idonshi, a hankali ta sunkuyar da kanta k’asa hawaye na zubo mata,
matsananciyar tsawa Dady ya daka musu gaba d’ayansu yace ” baku ji na ne….!?
Jikinsu na rawa suka had’a bakin wajen cewa ” Najwah ce ta mare ta,
“Me….!?
Dady yace, kana ya kuma cewa ” mari…..!?
“Eh….!, cikin rawar baki Neehal ya fad’awa Dady abinda ya faru tun daga farko har k’arshe,
cikin b’acin rai Dady ya kifawa Neehal gigitaccen mari,
yace ” dan uwanka ba sai da nace karka tafi da ita ba…..!?
“Duk irin kashedi da jan kunnan danayi maka kan karka jamin matsala ashe sai da ka ja min,
kasuwanci na dana yi shekara da shekaru ina ginawa,
cikin zafi, sanyi, rana, damuna shine zaka wargaza min…!?
” Kasan irin abubuwa da k’alubalan dana fuskanta kafin na kawo iyanzu….!?
“Idan ita mahaukaciya ce tana hauka kai ma mahaukacin ne….!?
Cikin matsanancin kuka Najwah tace ” kayi hak’uri Dady ba laifinshi ban…..!,
kyakkyawan maruka guda biyu Dady ya d’auke ta dasu,
yace ” dake nake magana ko dashi….!?
“Ko ni sa’anki ne da ina magana zakiyi min katsalandan,
ko’an fad’a miki kishi hauka….!?
” Haka kikaga saurin mata nayi….!?
” Kinjawa mahaifinki dan nasan wallahi President bazai tab’a kyale maganar nan ba,
damma yarinyar tana da hankali tasan me take yi ba irin ki bace,
cikin kuka Najwah tace ” am very sor….!,
” sorry for your self nonsense kawai get out from here idiot tun kafin na fasa miki baki,
jikinta na rawa ta mik’e ta fita,
idon Neehal runtse gam yana jin tamkar zuciyarshi zata kama da wuta saboda bak’in ciki da takaici,
dan sosai yaji zafin marin da Dady yayiwa Najwah,
Dady ya kalle shi yace ” ko zaka rama mata ne….!?
Kanshi ya sunkuyar k’asa had’i da cewa ” wane ni Dady, dan Allah kayi hak’uri.
A fusace President ya d’auki wayarshi da niyyar yayi kira,
Neesah tace ” no Dad ka barni na d’auki mataki da kaina,
Nana tace ” me zakiyi…..!?
“Neesah ta mik’e zaune had’i da kallan President da Nana, tace ” ba saboda kishin na rungumi mijinta yasa mare ni ba….!?
“Eh…! Nana tace, Neesah tace ” abu biyu nake so, na farko ina son a kawo min mahaifinta da ita tare lokaci d’aya,
dukkansu su zo gaba na, dan ina san na yanke hukunci a gaban idonta,
President yace ” uhummm sai na biyu,
a hankali ta mik’e tsaye had’i da takawa tace ” na biyu so nake nayi MAGANIN JAHILIN KISHINTA,
ina so na koya mata hankali, I want tech her a good lesson ta yadda zata gane kuranta,
Nana tace ” ban gane ba, me kike nufi….!?
A kid’ime President ya mik’e tsaye had’i da zubawa Neesah ido,
batare daya iya furta ko da kalma d’aya ba,
cikin rashin fahimta Nana tace ” what….!?
“Ban gane ba wai kina nufin aurenshi zaki yi….!?
” Yes Nana….!, ko da wata matsalar ne….!?
Muryar President a d’age yace ” halan kin manta nan da next 10 days d’aurin aure ki ko….!?
Baki Neesah ta turo tana k’ok’arin yin kuka tace ” I know! but I love him Dad…!,
a fusace President yace ” baki da hankali Neesah, so kike ki mayar dani mutumin banza….!?
“Kin san harkar siyasa yanzu hakan yana iya jawo matsala,
ko ya haifarwa da jam’iyya matsala da fitina, tun farko inda kin san baki sanshi da baki bari an saka biki har ya zo gab da gab ba,
sai da aka gama buga kati aka raba invitation card sannan kice baki sanshi….!?
Kuka Neesah ta kuma sakawa had’i da diddira k’afa tace ” wallahi ni dai Neehal nake so,
kuma shi zan aura babu wanda ya isa yayi min auren dole,
tana gama fad’ar haka ta shige bedroom d’inta had’i da banko k’ofa,
President zayyi magana Neesah ta fito tace ” karka manta da batun kawo min mahifinta da ita kanta,
sannan ina san ganin Neehal dan zanyi singing a contract d’in nan,
dan haka ina san ganin su gaba d’aya gobe, sannan ka kira siriki na Alhaji Bilal Lagosa ka bashi hak’uri,
kace mishi karya damu babu komai,
President zayyi magana Neesah tace ” no…! Dad just call him now,
tayi maganar da k’arfi tamkar tana magana da yaronta kamar yadda yaran turawa keyi,
bisa mamaki na sai naga President ya zaro wayarshi cikin Aljihu yayi dialing number Alhaji Bilal Lagosa,
instead of yayi mata fad’a koya nuna mata batayi dai-dai ba,
wayar Alhaji Bilal Lagosa ta soma ringing dai-dai lokacin yana tsaye gaban Neehal da Nauman yana zazzaga musu ruwan bala’i,
kasancewar shi mai matuk’ar zafi da fad’a dan baya wasa,
kamar bazai d’aga wayar ba, sai kuma yakai duba ga wayar dake aje gefe,
ganin sunan President yasa shi saurin mik’a hannu ya d’auka tare dayin picking ya kara a kunnenshi,
Neesah na tsaye a gefen President ta tsura mishi ido hannunta sark’e gaban k’irjinta,
bayan sun gama gaisawa ne President yace ” I’m very sorry da maganar dana fad’a maka d’azu,
Neesah ta sanar dani ba laifinshi bane, so dan Allah karka d’aga hankalinka komai yana nan kamar yadda yake,
sannan gobe zan saka hannu a kwangilar, sai kazo ka amsa,
da sauri Neesah tace ” no…! bashi ba ya turo Neehal d’in dai, I want see him,
idan kaga yadda Neesah ke bawa President oder yana bi saika rantse ita ce ta haife ba shi ya haife taba,
saboda tsakanin k’aunar da yake yi mata yasa yake yi mata biyayya wacce ita ce ya kamata tayi mishi,
da sauri Alhaji Bilal Lagosa yace ” Alhamdulillah nagode sosai mai girma President,
goben in sha Allah zanzo da kai na,
” no…! ka aiko Neehal d’in gida sayya karb’a a hannun Neesah,
tunda su suka fara sai a barsu su k’ara abinsu gwara ma su fara koya tun yanzu tunda ba’asan me Allah zayyi gaba ba,
” haka me kam, Alhaji Bilal Lagosa ya fad’a yana murmushi irin na manya.
Bayan su Alhaji Bilal Lagosa sunyi sallama,
Neesah ta kalli President tace ” call her useless father,
ba musu President yayi dialing number Alhaji Ubayyu,
bugu d’aya shima yayi picking cike da girmamawa ya gaida President,
ba wani dogon bayani President yace ” gobe kazo villa house kai da ‘yarka,
sai da ya d’an suruna tamkar yana gaban President yace ” wacce daga cikin yaran nawa…!?
A dak’ile President yace ” surukar Alhaji Bilal Lagosa, ya fad’a had’i da dropping wayar,
cike da tsantsar farin ciki Neesah ta rungume President had’i dayi mishi kiss,
tace ” thank you…! thank you so much Dad, yana murmushi ya shafa kanta yace ” kinyi farin ciki yanzu….!?
“Sosai Dad, ” good Soul babu abinda nafi so a rayuwata ta duniya kamar na ganki cikin farin ciki,
” I love you, Neesah tace, kana ta kalli Nana dake tsaye tana kallansu,
cike da so da k’auna da kuma zallar farin ciki, tace ” I love you Nana,
kanta Nana ta shafa tana murmushi tace ” I love you too,
bayan Alhaji Bilal Lagosa ya aje wayar kana ya kalli su Neehal yace ” Allah ya taimake ka,
komai yayi settling, gobe ka shirya da yamma kaje ka karb’o takardun contract d’in,
sannan inkaje ka maimaita abinda kuka yi kunji,
kansu k’asa sukayi godiya kana suka fita,
suna fita waje Nauman ya tuntsure da dariya sosai,
Neehal ya kalle shi a k’ufule yace ” kai kuma uban me kake yiwa dariya….!?
Nauman bayyi magana ba ya cigaba da yin dariyarshi har da rik’e ciki,
sarai Neehal ya gane abinda Nauman yake yiwa dariya marin da Dady yayiwa Najwah ne yayi mishi dad’i,
tsoki ya ja yana kallan Nauman yace ” kai…! wai me kake yiwa dariya ne, ko kaga abin dariya a jiki na…..!?
Nauman bayyi magana ba, ganin Nauman bashi da niyyar yin magana yasa shi jan uban tsoki,
had’i da shigewa cikin mota ya tayar, Nauman yana dariyar yace ” bari na zaka yi nan….!?
Neehal bayyi mishi magana ba yaja motar yabar harabar gidan,
dan tuni Najwah ta dad’e gida tun korar da Dady yayi mata bata tsaya ba tayi gida direct,
Alhaji Bilal Lagosa yayi murmushi dan yana bayansu yace ” kyale shi Nauman rarrashi zai tafi yayi sakarai lusari kawai,
da sauri Nauman ya juya jin muryar Dady, Dady yace ” ka amshi key hannun driver sai ka d’auki duk matar da tayi maka ka tafi gida,
sosai Nauman yayiwa Dady godiya dan wannan ce mota ta biyar da ya bashi,
” ba nace karka sake yi min godiya kan duk abinda na baka ba….!?
Hak’uri ya bawa Dady kana ya shiga d’aya daga cikin jibga-jibgan motocin dake harajar gidan ya tafi gida,
Neehal na danna kai cikin parlor ya fara jiyo sautin kukan Najwah,
da sauri jikinshi na kerrrrma ya k’arasa shiga ya isa gareta ya durk’usa gabanta,
yana k’ok’arin yin magana wayarta ta soma ringing,
tana kukan ta kalli wayar taga sunan Abbanta, kallan Neehal tayi tana kuka tace ” Dady ya fad’awa Abban mu abinda ya faru ko….!?
“No..! gaskiya bana tunanin haka kema kin san Dady bazai tab’a yin haka ba,
wayar na gaf da tsinkewa Neehal ya d’aga had’i da sanya wayar a hand free,
bayan sun gaisa Abban Najwah yace ” ka cewa Najwah ta shirya gobe zamu je villa house President na nemanmu,
yayi maganar so calm dan tunda shugaban k’asa ya kira shi gabanshi ya shiga fad’uwa yana dukan uku-uku sosai,
yana tunanin abinda yasa President ke nemanshi shi da Najwah,
amma bai kawo komai ranshi game da Najwah ba dan bai tab’a tunanin zata iya aikata aikin da har President zai nemeta ba,
jin abinda Abban Najwah yace yasa gaba d’aya k’irjinsu bugawa da k’arfin tsiya,
jin sunyi shiru yasa shi cewa ” hello…!, ko baku jina ne…!?
Neehal ne yayi k’arfin halin cewa ” muna jinka Abba,
Abban yace ” lafiya kuwa…!, kodai kun san meke faruwa….!?
Shiru suka k’ara yi gaba d’ayansu wanda ya tabbatarwa Abban tabbas sun san meke faruwa,
kuma akwai wani abu k’asa, dan haka yace ” ku fad’a min koma meye dan nasan ta yadda zan b’ullowa al’amarin tun wuri,
bakin Neehal na rawa ya sanarwa da mahaifin Najwah abinda ta aikata,
” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,
dama baki da hankali Najwah baki san me kike yi ba….!?
Yayi maganar kamar zai faso ta cikin wayar yazo ga Najwah,
a tsorace Najwah ta shige cikin Neehal had’i da k’ara sautin kukanta,
da k’arfin mahaifin nata yace ” rufe min baki munafuka muntuniyar banza,
wallahi ki sani duk abinda ya faru gobe kanki zai k’are shegiya,
kafin suyi magana yayi dropping wayar, cikin matsanancin kuka mai cin rai da zuciya,
had’i sa karya zuciya, gangar da ruhin ma’abocin sauraro Najwah tace ” wallahi Allah ban san abin zai kai haka ba,
ido na ne ya rufe ruf gaba d’aya, na kasa controlling kai na,
but I’m very sorry na haifar maka da matsololi da dama, na jawa sanadiyyar fushin iyayen mu akan mu,
dan Allah ka yafe min kar abin yayi min yawa please my heartbeat,
take santa, k’aunarta da tsananin begenta da yake yi sukayi tasiri wajen karyar mishi da zuciya,
tsakanin tausayinta ya lullub’e shi, har bai san sanda kwalla ta cika mishi ido ba,
cike da zallar shauk’in so Neehal ya rungume Najwah tsam a jikinshi,
yana sauke ajiyar zuciya gami da shafa kanta yace ” bakomai my Happiness komai ya wuce,
ki daina damun kanki kina kuka kar kiyi ciwon kai kinji, bana san wani abu ya sameki dan idan wani abu ya same ki,
bazan tab’a yafewa kai na ba, so please ki kwantar da hankalinki mijinki yana tare dake koyaushe,
a ko’ina a kowanne lokaci, cikin kowanne irin yanayi na rayuwa،
yayi maganar cikin rawar murya, deep down yana jin kamar yayi hauka saboda k’unar da zuciyarshi keyi mishi,
maimakon yaji zafin Najwah sai take yaji zafin Neesah da tsantsar tsana da k’iyayyarta sunyiwa zuciyarshi k’awanya,
in banda umarnin Dady ne zuwanshi gobe da babu wani abu da zai k’ara had’a shi da Neesah ko’a lahira,
jikinshi ta k’ara shigewa tana k’ank’ame shi sosai tace ” am sorry dear nayi maka alk’awarin ban k’arayin kwatankwacin abinda nayi,
nayi maka alk’awarin zan canja, zan daina duk abinda nake yi,
zan daina bak’in kishi zan rink’a controlling kishi na,
zan zame maka mace ta gari matar rufin asiri,
cikin jin dad’i Neehal ya shafa kan Najwah yana murmushi yace ” thank you so much,
an I promise to be with you for ever an ever, I will be by your side always, an i will make you happy, happier woman in the whole earth,
zan zama naki ke kad’ai zan kuma dawwama a naki har abada,
nayi miki alk’awarin bazan tab’a yi miki kishiya kona k’ara aure ba,
kamar yadda kike ke kad’ai a zuciyar Neehal haka zaki kasance ke kad’ai a zuciyar shi har abada,
kiss ta shiga manna mishi ta ko’ina shima yana mayar mata da martani.
Washe gari a villa house, Neesah zaune makeover tana tsantsara mata kwalliya ta garari,
jikinta sanke da doguwar rigar material irin ready mate d’innan,
wacce Indian, da turawa ke sawa idan zasu fita party,
rigar kalar dark purple mara hannu da k’ok’on bra a gabanta,
tun daga k’asan rigar har zuwa cinya a tsage yake, santala-santalan cinyoyinta waje, farare tasss dasu, ta saka takalmi high hill mai shegen tsayi,
kashin ganta yasha gyara sosai idan ka ganta sai ka rantse bata tab’a sanin musulunci ba,
balle yaran Hausa/Fulani, jikinta sai fidda sihirtaccen k’amshi yake na mutuwa,
duk kamun kan d’a namiji idan yaga Neesah sai wani abu ya tsarga mishi.
Cikin isa da tak’ama Neesah ta taka zuwa parlor inda Neehal ke zaune,
yana zaman jiranta, jikinshi sanye da d’anyar shadda Gezza,
d’inkin sosai yabi da shaddar yayi kyau sosai, k’uruciyarshi ta k’ara bayyana,
Neesah ta k’arasa gareshi fuskarta d’auke da shu’umin murmushi,
mai d’auke hankalin ma’abota kallan fuskarta, yana ganinta ya mik’e tsaye,
fuskarshi babu annuri sosai , tana isa ta rungume shi had’i dayi mishi kiss,
kamar yadda tayi jiya kana ta zauna kusa dashi had’i da mik’a mishi files d’in,
tace ” an gama komai, saura kuma fara aiki,
“Okey, kawai Neehal yace ya soma k’ok’arin mik’ewa,
mayar dashi ta yi zaunar had’i da hawa kan cinyarshi tace ” ya naga kana sauri haka ‘yan samari ina zuwa….!?
Fuskarshi babu walwala sosai, yace ” am busy,
” har akwai busy dayafi wannan….!?
Shiru yayi baice mata komai ba, tace ” idan wani abun ke damunka ka fad’a ba damuwa,
tayi maganar tana rik’e da kumatunshi, tunani yayi kamar na 10 seconds wanda ya sashi yin murmushi,
had’i da rik’e k’ugunta ya gyara mata zama sosai kan cinyarshi,
cike da yaudara Neehal ya kalli cikin kwayar idanta da narkakkun idanuwanshi,
yace ” please ina san ki yafewa Najwah,
ki yafe mata Allah yana san mutane masu yafiya, masu saurin manta sharri suyi rik’o da alkhairi,
please karki yiwa mahifinta komai, karki ci masa mutunci saboda abinda ‘yarshi tayi miki,
kar laifin Najwah ya shafi mahifinta ki tuna ko Allah baya kama wani da laifin wani,
please forgive her for my sake Neesah,
ajiyar zuciya Neesah ta sauke kana tace ” zan yafe mata zan kuma janye kiran da nayiwa mahaifinta bisa sharad’i d’aya,
idan ka yarda….!?
Neehal ya kalle ta cike da mamaki yace ” wanne iri sharad’i kuma….!?
Tayi murmushi tana shafa fuskarshi tace ” marry me…!,
” what….!?
Neehal yace cikin kid’ima da rud’u, ” yes mana ko ban kai ka aure ni bane….!?
“No…! No…! Neesah, I can’t…! bazan iyaba,
yayi maganar duk ilahirin jikinshi na tsuma,
” Okey ba damuwa Neesah tace tana mik’ewa had’i da tab’a baki,
da sauri Neehal ya rik’e ta ya shiga rarrashinta yana bata baki,
har ta sauko tace ” tou na yarda na yanje maganar aure amma bisa wani sharad’in,
da sauri yace ” fad’i muji,
” ka fara yi min alk’awarin zaka yarda dashi,
shiru Neehal yayi na tsayin lokaci kana yace ” okey ba damuwa,
Neesah tace ” yau saura kwana tara biki na, ina san ka kasance saurayi na na kwana tara,
kafin aure na, idan har cikin kwanaki taran nan baka ji kana so na ba,
bazan matsa maka ba, zan auri Nabeel saurayi na wanda zan fara,
amma bisa sharad’in kayi alk’awari tsakanin ka da girman Allah,
zaka fad’i gaskiyar abinda ke cikin zuciyarka,
shu’umin murmushi mai cike da fassarori da dama Neehal yayi,
cike da izza, tak’ama da zallar yarda da kanshi yace ” ba damuwa na yarda na amince,
daga nan suka shiga hira sosai kana Neehal yasa Neesah ta kira President a gabanshi ta fad’a mishi ta fasa san ganin Ubayyu,
sosai hakan yayiwa President dad’i dan shima ba’a son ranshi bane,
dan dai dole ne bashi da yadda zayyi yasa shi amsa mata,
daga villa house Neehal wajen Nauman ya wuce danya bashi labarin haukan Neesah na soyayyar kwana tara,
a parlor’n Mama ya iske Nauman yana cin abinci, kasancewar shima yanzu hankalinshi a kwance yake yasa shi zama yaci sosai,
bayan sun gama cin abincin suka fito harabar gidan suka zauna saman mota,
Neehal yace ” kai wai kasan me….!?
“Ai dama tunda na ganka yanzu na san akwai labari bani nasha,
Neehal yana dariya yace ” Neesah bata da hankali ina ga fa, kana ya shiga bashi labarin abinda ya faru tsakanin shi da nisa, yana dariya,
ido Nauman ya k’ura mishi har ya dasa aya kana Nauman ya sauke ajiyar zuciya gami da cewa,
” baka tunanin zaka iya fad’awa tarkonta….!?
Cak Neehal ya tsayar da dariyarshi kana ya kalli Nauman yace ” what do you mean….!?
“Kana tunanin ni Neehal Bilal Lagosa zan fad’a soyayya da Neesah…!?
Cikin mamaki Nauman yace ” me kake nufi da kai Neehal ko itama kana ganin kafi k’arfin ka so ta…!?
“Wallahi sosai ma kuwa, kamar ni Neehal ne zan so wannan abar mai kama da ‘yar tsana,
mai zubin Babyn roba, kai baka tab’a ganinta ba ne…!?
Cikin al’ajabi da tsantsar mamaki Nauman yace ” sosai ma,
ina following d’inta ma a Instagram da Twitter, yanzu wannan d’ince kake cewa kafi k’arfinta Neehal…!?
“Shin baka k’are mata kallo bane…!?
” Sosai ma kuwa ni da har zama kan cinya ta tayi, Allah babu abinda zanyi da wannan abar,
Allah ya kyauta ni Neehal Bilal Lagosa nayi dating da wannan wai dan hauka har da maganar aure,
turrrr wuce nan na wuce da saninta da tunanin ta wallahi,
idon Nauman ya k’urawa Neehal ya kafe shi da ido cike da zallar mamaki,
yace ” yarinyar data fika wayewa, ilimi, bud’ewar ido,
yarinyar da tayi karatu a America, tayi huld’ar da kusan gaba d’aya jinsin duniya,
yarinyar da take da madarar kyau, Allah ya zanata ya bata halitta mai kyau,
Neehal me kafi yarinyar nan ko me matarka Najwah takai ta balle ta fita…..!?
Cike da izza da tak’ama gami da self confidence yace ” wallahi na wuce auren Neesah nesa ba kusa ba, jikinta ko wanne tom & jerry ya gama gani,
yayi maganar in arrogant,
” ka wuce me, dame kafi k’arfin ta….!?
“Kaga idan kana santa go ahead ni zanyi maka jagora ma,
ido kawai Nauman ya k’urawa Neehal yama rasa me zaice mishi,
deep down yana tunanin hali da d’abi’un shi, idan yace yafi k’arfin Umaima da Umaina but how zaice yafi k’arfin Neesah ta ina ta yaya…..!?
Duk abinda yake tak’ama dashi itama tana tak’ama dashi,
kyau, kud’i, ilimi, gata, nasaba, da kuma alfarma wasu daga ciki ma ta fishi,
shi dai yasan babu abinda Najwah takai Neesah balle ta fita,
idon Nauman kan Neehal yace ” WACCE IRIN MACE KAKE SO….!?
Cikin rashin fahimta yace ” kamar ya, bayan Najwah har akwai wata mace da zan kuma buk’ata ne….!?
” Hummm kana bani mamaki Neehal idan kace Umaina da Umaima yara ne,
Neesah ai ba yarinyar bace, tunda zatayi sa’arka,
idan kace Umaina da Umaima ‘yan k’auye ne basu waye ba, ai Neesah ba ‘yar k’auyen bace,
duk inda mace takai Neesah ta kai, haka ma Umaina da Umaima suna da halitta mai kyau,
amma dukka kushe su,
ANYA NEEHAL KASAN SO….!?
“KASAN ZAFIN SO DA RAD’AD’IN SOYAYYA KUWA….!?
“KASAN ME AKE KIRA DA KALMAR SO, KA TAB’A D’AN D’ANAR ZAFI, K’UNA DA D’ACIN SO….!?
KASAN TRUE LOVE KASAN SOYAYYAR GASKIYA….!?
” An ya Neehal ba gigin yarinta da k’uruciya ke d’ibarka ba….!?
“Neehal anya baka da ZAB’IN RANKA, baka da tsarin zuben macen da kake so a can k’asan ranka…..!?
” Neehal na fara tunanin giyar k’uruciya ke d’ibanka amma har yanzu baka san so ba,
baka san me ake kira da so ba, tabbas akwai wani abu bunne cikin zuciyarka,
akwai abinda Allah kad’ai yasan meye shi a zuciyarka wanda ko kai da kanka baka san meye shi ba,
baka san meye a cikin zuciyarka ba, baka san meye binne a gefen zuciyarka ba,
kai kanka baka san waye kai ba, baka san meye b’oye cikin k’ark’ashin zuciyarka ba,
baka san meye so ba, baka san wa kake ainahin so ba, baka san ainahin meke cikin zuciyarka ba,
tabbas na tabbatar akwai wani abu gefen zuciyarka,
akwai abinda Allah kad’ai yasan dashi cikin zuciyarka kaima baka sanshi ba.
Tsoki Neehal yaja yace ” kaji shirmen banza kai ban ce maka baka san meye so ba sai kai ne zaka ce ban san meye ba,
kai da baka da aure baka da budurwa kayya kamata a tambaya meye so,
amma ni tuni na wuce wajen Neehal yayi maganar yana dariya,
” hummmm Neehal kenan kana da ji da kanka, kana da tak’ama da kanka had’i da cika baki,
wallahi ka kiyayi rayuwa da illar so, ka kikayi mace, ina yi maka addu’ar kar Allah ya jarrabe ka da mahaukacin makahon so…!
kiran sallar da aka kwala ne ya hana su cigaba da maganar, lokaci d’aya suka kalli agogon hannunsu,
kana suka sauka daga saman motar suka shiga part d’in Nauman suka d’aura auwala suka nufi masallaci,
bayan sun idar da sallah Neehal yayi gida, a hanyar gida ya tsaya yayi take away,
kana ya nufi gida, tun daga harabar gidan Neehal ya fara ganin fasassun glasses zube k’asa,
ganin haka yasa shi tsayawa cak yana kallan broken glasses d’in kana ya kalli part d’in Najwah,
da sauri ya shiga part d’in ya iske Najwah zaune zaman dirshen a tsakiyar parlor’n,
wayar ta gabanta ta zubawa wayar ido tana kollo,
a hankali yabi parlor’n da kallo ganin duk wani abu ma glass dake parlor’n a fashe yake,
gaba d’aya parlor’n an fasa komai an tarwatsa komai, komai a hargitse yake,
hannun Najwah yana zubar da jini ta yayyanke sosai, gashin kanta buzu-buzu kamar tab’abb’iya,
ta d’aga pure red eyes d’inta ta kalli Neehal dake tsaye kamar an dasa shi ya kasa koda furta kalma d’aya,
a hankali ya ajiye ledar dake hannunshi ya k’arasa ga Najwah had’i da mik’a hannu da niyyar ya tab’a ta,
cikin k’araji ta yarfar da hannunshi gefe tana huci,
” lafiya meke faruwa dake …..!?
Yayi maganar kamar mai koyan magana danya tabbatar ba lafiya ba, deep down gabanshi na muguwar fad’uwa,
jikinshi na rawa kamar mazari,
batare da tayi magana ba ta mik’a mishi wayarta, hannunshi ma rawa ya amsa video ya gani wanda yasa gabanshi fad’uwa,
hannunshi na rawa yayi playing, zaune ya ganshi a sofa a villa house Neesah na zaune saman cinyar shi,
suna kallan kwayar idon juna, da alama kwararre masanin computer sosai,
yayi editing video domin daga inda Neesa tace ” bisa sharad’in zaka aure ne, sai inda Neehal yace ” eh na amince, na yarda, wato wajen dayace mata ya yarda da batun soyayyar kwana tara,
aka had’a da inda Neesah tace zaka aura ne sai abin yayi tamkar lokaci d’aya akayi maganar,
while Neesah na zaune saman cinyarshi hannunshi rik’e da k’ugunta,
wata irin razananniya fad’uwa gaban Neehal yayi, k’irjinshi ya buga da k’arfi, ya d’ago kanshi ya kalli Najwah dake rik’e da sharb’eb’iyar wuk’a idanta kanshi,
tana gurnani kamar zakanya ko bujumin sa,
a fili Neehal yace ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un dan yasan babu irin bayanin da zai gamsar da Najwah,
wuk’ar hannunta ta d’aga tana kallan Neehal kana ta nufi shi a haukace…………….!Saboda tsantsar tsoro da zallar tashin hankali Neehal kasa motsi yayi,
ya tsaya tsaye cak had’i da zuba mata ido tana k’arasowa gareshi,
cikin zafin rai da ta d’aga wuk’ar da niyyar burmawa Neehal k’irjinshi da ita,
bayyi yunk’urin guduwa ko matsalawa ba yana nan tsayen cak yadda yake,
idanshi kanta, had’a idon da Najwah tayi da Neehal ne yasa ta tsaida hannunta cak,
a dai-dai k’irjinshi a firgice ta kalli hannunta da wuk’ar ke rik’e kana ta kalli Neehal zuwa k’irjinshi,
sai a lokacin hankali da nutsuwarta suka dawo jikinta,
ta fuskanci abinda take da niyyar yi wanda yasa ta saurin yin jifa da wuk’ar gefe,
tana yarfe hannunta had’i da durk’ushewa k’asa ta toshe kunnenta da duka hannunta,
duk ilahirin jikinta na rawa gami da tsuma, ta sanya wani irin kuka mai cin rai tana cewa ” why…! Neehal why….!?
Ido ya kafe ta dashi batare dayace komai ba, ganin yadda jikinta ke kerrrrrrma,
yana tsuma duk ta furgice yasa take yaji tsananin tausayinta ya lallub’e duk ilahirin jikinshi,
cikin sanyin jiki ya sunkuya kusa da ita had’i da mik’a hannunshi da niyyar ya tab’a ta,
a firgice ta ture hannunshi tare da ja baya a kid’ime tamkar ya d’ora mata bakin wuta,
tana girgiza kanta had’i da kallan tafin hannayenta tace ” me nake shirin yi….!?
” Da wad’annan hannayen nayi k’ok’arin kashe farin cikin raina….!?
” Ni da kaina da hannaye na nayi k’ok’arin kashe ka…!?
“Zanyi sanadiyyar tsinkewar rayuwar wanda nafi son ya rayuwa sama da kowa,
nafi so da k’auna sama da kowa, nafi san kasancewa tare dashi sama da kowa,
ni da kaina nayi k’ok’arin kashe kai na da rugujewar farin ciki da annurin rayuwata….!?
Cike da tsantsar tausayawa yasa hannunshi ya jawota jikinshi ya rungume ta tsam,
had’i da shafa kanta yana bubbuga bayanta, batare daya iya furta koda kalma d’aya ba,
” wallahi ba abinda nayi niyyar yi ba kenan, bada sani na nayi hakan ba,
bana cikin hayyacina sanda nayi attempting kashe ka but am very sorry,
kayi hak’uri ban k’arawa in sha Allah I promise,
bayyi magana ba ya cigaba da shafa kanta yana lallashinta,
a hankali ta zame jikinta daga cikin nashi ta fuskance idonta cikin nashi,
bakinta na rawa tace ” please abinda na gani a waya yanzu gaskiya ne ko mafarki ne….!?
Tayi maganar tana nuna wayar cike da tsoro, sai da gabanshi yayi gigitacciyar fad’uwa,
kana yace ” hu….ummm….. unnnn….. da…ma…!,
cikin k’araji Najwah tace ” what….! kana nufin da gaske ne….!?
“Yes..! but I…..!, cikin masifa ta fizge data cikinshi tace ” but what Neehal…..!?
“Please calm down I will explain everything to you now,
” explain what….!?
“You have nothing to say,
” please relax an listing to me, idan baki yadda da abinda zan fad’a miki ba na baki damar d’aukar duk matakin daya dace kai na,
” what Neehal bayan abinda ido na ya gani…!?
“Ka zaunar da mace akan cinyarka kana kayi mata alk’awarin aure,
bayan ina duniyar…..!?
Tayi maganar k’asa-k’asa tana nuna kanta,
a hankali ya mik’e tsaye had’i da mik’a hannu zai tab’a ta,
cikin masifa tace ” don’t dare you touch me,
” wallahi mutuwa zanyi Neehal, mutuwa zanyi, rayuwata tazo k’arshe,
bazan iya rayuwa da kishiya ba, bazan tab’a iya sharing d’inka da wata ‘ya mace ba,
kai nawa ne ni kad’ai Neehal, dan ni kad’ai aka halicce ka ba’a halicce ka dan mu biyu ko wata mace ba,
tayi maganar cikin k’araji da wutar ruwan bala’i tana harguwa,
kana a haukace ta isa gareshi taci kwalarshi ” wallahi kai nawa ne ni Najwah ni d’aya,
Neehal kai mallaki na ne, kama sawa ranka haka, matuk’ar kana neman zaman lariya da kwanciyar hankali,
karka soma gigin yiwa Najwah kishiya idan ba haka ba dukkan mu zamu mutu,
danna gwammaci mutuwar mu kan rayuwa da wata tsakiyarmu,
Neehal bana san kishiya bana san kishiya, tayi maganar da k’arfi tana jijjigashi,
ganin yak’i cewa komai ya tsaya kawai yana kallanta ya k’ara hasala ta,
tace ” da gaske kenan auren zakayi….!?
Still shiru yayi mata while idanshi kanta, ” Neehal mutuwa zanyi, zuciya ta na gaf da tarwatsewa,
dan haka kafin zuciya ta ta tarwatse bari na kashe kaina,
tayi maganar tana nufar wuk’ar data jefar k’asa, a haukace,
ganin haka yasa cikin zafin nama Neehal yayi wuf ya d’auke wuk’ar,
gaba d’aya ta haukace ta fice fit daga cikin hayyacinta da nutsuwarta,
kwata-kwata bata jin komai bata ganin komai, tana ihuuuu ta cakumi Neehal tana cewa “ka bani wuk’ar na kashe kaina na huta,
shi kuma ya rik’e wuk’ar gam, ganin haukan nata yayi yawa yasa shi daka mata tijararriyar tsawa,
wacce duk ilahirin gidan sai da ya amsa,
” kina hauka ne ko baki da hankali…….!?
“Eh nayi hauka Neehal, in dai akanka ne ka kira ni da kowanne irin suna zan amsa,
wata tsawar ya k’ara daka mata mai kama da saukar aradu,
wacce ta sanya kayan cikinta yamutsawa, a d’an tsorace taja baya jikinta na kerrrrrrma,
cikin d’aga murya yace ” wai me kika mai da nine…!?
“D’an iska..!, mazinaci…!, fasik’i kome…..!?
“Na rasa yadda zanyi dake Najwah, gaba d’aya kin fara birkita min tunani da lissafi na,
ace kwata-kwata matar ka ta sunna bata da yak’ini akanka,
babu yarda a tsakaninmu dake, sai zargi da kokwanto had’i da tuhuma,
ke da kanki kina neman kiyiwa rayuwarki illa, ni kuma kin hana min rayuwata sakat,
ko kina tunanin fasik’i ne ni….!?
“Ko kina tunanin zanci amanarki ne…!?
“Wallahi ko babu ke a cikin rayuwata bazan tab’a yin zina ba,
ko da ace ni saurayi ne bani da aure bazan tab’a kusantar zina ba,
haka kuma ko mata sun k’are bazan tab’a auren wannan k’ek’ashashshiyar ba….!
mace duk a tsotse, jiki ba tsoka, idan na tab’a wannan naji me a jikinta….!?
“Jikin da yake tamkar k’ashi da rai, wallahi kamar D’AN UWANA NAMIJI haka NAKE JIN NEESAH,
ban tab’a jin wani reaction game da ita ba,
mace kwata-kwata babu shape, yama za’ayi k’ugunta ya iya d’aukar marata….!?
“Mazantakata da k’irfin jijiyata yafi k’arfinta idan na hau wannan ina iya b’abb’allata,
dan mararta bazata iya d’aukar nauyin mazakuta ta ba,
sannan joy stick d’ina yafi k’arfinta, nafi k’arfin ta d’and’ani albakatu na,
kina ganin abu duk abushe a rame a k’ek’ashe, ke kanki kin san bana san ramammiyar mace dan bata b’ata burgeni ba,
nafi san duk inda nakai hannuna naji tsoka, na rink’a cika hannuna da kayan alatu,
amma ina ni ina Neesah, bayan duk ta gama tallata jikinta kowa ya gani a free,
sannan ni na kwasa nakai gida….!?
“Allah ya kiyaye kuma ma ai…….!
yadda Najwah ta tsare shi da ido ne ya hana shi k’arasa maganarshi,
kanshi ya d’aga mata had’i da juya idonshi dake kanta k’uri yace ” me….!?
Ido Najwah ta kafe shi dashi na tsayin lokacin, ta dad’e tana kallanshi eyeball to eyeball,
kana cikin sanyin murya tace ” kana bani mamaki…!,
idonshi kanta yace ” name….!?
“Neehal ace kowacce mace a duniya sai ka kushe ta, sai ga gano makusarta,
tun ina jin dad’i har na dawo ina kokwanto, daga k’arshe kuma ka fara bani tsoro,
cikin rashin fahimta yace ” kamar ya ban gane ba…!?
Idan kace Umaina yarinya ce 12yrs ai Umaima ba yarinya ce tunda she’s my age mate,
idan itama kace yarinyar ce to NEESAH fa…!?
“Tun da kaima sasanin kanka ne kai kanka baka girmi Neesah ba,
idan kace Umaima da Umaina ‘yan k’auye ne kai sanin kanka ne ko bature Neesah tafi k’arfin ya kalle ta yace mata ‘yar k’auye,
tunda daga ni har kai tafi mu wayewa, tafi mu ilimi da bud’ewar ido,
tafi mu shiga duniya da iya huld’a da mutane, tunda ita har Masters tayi kuma a America tayi karatu,
still itama ka kushe ta, gaskiya Neehal ka fara bani tsoro,
” tsoron me kuma….!?
Tsoro na d’aya kar ni ma ba so na kake ba, ina tsoran kada ace nima kana kushe ni cikin ranka,
ko kuma ka gano makusata nima, ina tsoran kada ace kana da zab’in irin kalar macen da kake so cikin ranka,
saboda duk macen daka gani sai ka kushe ta,
na fara kokwanton kar ace kana da tsarin zubin halittar macen da kake so,
kake kuma mafarkin mallaka Neehal, ina tsoran kada nan gaba kad’an ka fara ganin muni da makusa ta,
ina tsoran kada ace auren yarinta da k’uruciya mukayi,
ina gudun kada ace so da tsantsar soyayyar da muke yiwa junan mu yarinta ke d’iban mu,
ina tsoran kada ace har yanzu baka san SO!!! ba, saboda har yanzu kai yaro ne you’re 25yrs,
ina tsoran kada sai ka mallaki hankalin kanka, ka san ciwon kanka, ka fita daga k’uruciya,
sannan ace zaka san SO!!!, ina gudun kada ace giyar yarinta ke d’ebanka kake min soyayyar k’uruciya,
ina tsoran gaba Neehal ina tsoran me gaba zata haifar gaskiya,
I’m very scared Neehal, rungumo ta yayi jikinshi yana dariya,
yace ” don’t be afraid my Happiness, har abada Neehal naki ne ke kad’ai,
kada kiji komai, dake kad’ai na zan zauna, dake kad’ai zan rayu har abada,
shigewa jikinshi tayi tana cewa ” please don’t live for ever please,
dariya yayi yana yace ” haba ke kuwa, waye zai raba ni dake idan ba Allah ba,
kuma ina fatan kada ya raba mu har abada, duniya da lahiya,
zatayi magana ya d’ora hannunshi saman lips d’inta had’i da cewa ” shhhhhh no argument,
muje muci abinci muyi wanka sai mu kwanta ko….!?
A hankali ta d’aga mishi kanta, ya taka zuwa inda ya saki ledar abincin,
ya d’auka kana ya zauna saman sofa bed ya zaunar da ita saman cinyarshi,
ya shiga bata abincin a baki itama tana bashi suna ciyar da junansu cikin shauk’in so,
har suka k’oshi kana sukayi wanka suka kwanta,
tana rungume a faffad’an k’irjinshi yana shafa kanta kamar baby har tayi bacci,
maganganun Najwah da Nauman ne suka shiga yi mishi yawo cikin ranshi,
ya dad’e yana tunani bai gano komai ba,
kallan fuskarta yayi had’i da sakin k’ayataccen murmushi kamar tana kallanshi,
sosai ya k’ura mata ido yana kallanta, bai daina kallanta ba sai da ya tabbatarwa kanshi,
duk duniya babu macen dayake so sama da ita, ya kuma kasa gano makusarta ita,
murmushi yayi a karo na biyu had’i da manna mata kiss ya matse ta sosai a jikinshi,
yace ” I love you so much rigimammiyar mata ta.
Bayan sati d’aya komai ya zama normal kamar wani abu bai tab’a faruwa tsakanin masoyan biyu ba,
Neehal zaune office d’in Nauman suna hira,
Nauman ya kalli Neehal yace ” wai ni aboki na ya maganar soyayyar kwana tara dake tsakaninka da Neesah naji ka shiru baka ce min komai ba, kodai har an dai-dai ne….!?
Zaman shi ya gyara saman sofa kana yace ” hummm na manta ban baka labari ba, ni da yarinyar nan ta had’a min jakwal,
” jakwal kuma…! name….!?
“Da naje wajenta ba na baka labarin ta zauna kan cinya ta ba….!?
“Eh…! ka fad’a min,
sai da Neehal ya sauke numfashi kana yace ” ashe tayi video recoding shegiyar yarinyar nan ban sani ba,
sosai Nauman ya zaro ido yaje had’i da cewa ” kamar yaya ban gane ba….!?
Labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k’arshe Neehal ya bawa Nauman,
sosai tsananin mamaki ya kama Nauman cike da al’ajabi Nauman yace,
” amma nayi mamaki, kamar Neesah da hankalinta da iliminta da komai amma tayi haka….!?
“Wallahi kuwa, dan haka kayi hankali sosai, dan abinda naji matan yanzu nayi kenan,
wai idan kayi amfani dasu, ko wani abun ya shiga tsakaninku,
sai tayi video record tayi amfani dashi ta amshi mak’udin kud’i a hannunka,
ko kuma ta matsa maka dole sai ka aure ta, ko kuma idan ka yaudare ta,
sai ta sakarwa duniya shi, ko ta turawa iyalinka da iyayenka,
a matuk’ar razane Nauman yace ” kai haba…!?
Yayi maganar kamar idanuwanshi zasu fad’o k’asa,
Neehal yace ” seriously fa dan naji labarin irin haka ta faru da yawa,
Nauman yace ” to Allah ya kyauta, ” Amin ya Rabbi, cewar Neehal,
kana Nauman yace ” amma fa Najwah ta ban mamaki da banji labarin ta fasa maka kai an kaika hospital ba,
ko sai mu data raina take san kashewa…..!?
” Kai ai ta sakko sosai ta rage kishin tayi min alk’awarin bata k’arawa har abada,
“she is lied, why it lies, you very well know it’s, now why you’re so blink to see Najwah from the other angry where peoples seen her,
Najwah is a back of the sit, she is a boom that any time can booming you an……!,
” hey…!hey…guy, take it easy man, you must to realise that my wife talking about here,
Nauman ya sauke ajiyar zuciya had’i da cewa ” Okey! am sorry Neehal but….!,
da sauri Neehal ya dakatar dashi “wai kai meyasa kake jin haushin Najwah ne….!?
“Saboda halinta, kaima dan baka san ciwon kanka bane, amma da zarar ka sani zaka fara jin haushinta,
da sauri Neehal yace ” ever….!, God forbid naji haushin Najwah,
ai kome Najwah zatayi bazan tab’a jin haushinta ba,
murmushi Nauman yayi had’i da cewa ” haka kace….!?
“Eh…! zan kuma cigaba da cewa har k’arshen rayuwata,
” okey, amma ni na k’alubalanci wannan maganar taka,
ka aje a ranka, wata rana koda bana raye sai ka tuna da wanann ranar da kuma maganar,
dan nasan wallahi sai ranar tazo, Neehal ya tab’e baki had’i da kauda kanshi gefe,
Nauman ya cigaba da cewa ” kuma matsawar muna tare sai ka yiwa Najwah kishiya wallahi sai dai idan na mutu,
Neehal ya zaro ido gami da cewa ” what…! kana tunanin Najwan zanyiwa kishiya…!?
“Eh…! matuk’ar muna tare ba,
” kai…! me yayi zafi haka…!?
“Ina ruwanka matarka ko tawa, matsalarka ko tawa…!?
“Yau naga k’arfin hali, Nauman yace ” ai bakaga k’arfin hali bama wallahi,
” imma kana tunanin ni Neehal Bilal Lagosa zanyiwa Najwah kishiya ka daina,
imma mafarki kake to ka farka, shege dama data tsareka a gida na bari ta kawar da mak’iyinta,
” wane ita, kai nayiwa kara ai,
Neehal ya sanya dariya sosai had’i da cewa ” kai kaga idonka kuwa a lokacin….!?
“Allah kamar ana wujijjiga mage, jikinka sai tsuma yake yana kerrrma,
saboda tsoro ka kasa cewa komai, amma yanzu ka addabemu,
dama ban temake ka ba, na bari ta kaika k’arr,
” hummm kai dai ka sani ni dai ina k’ara fad’a maka kishiya wa Najwah ta zama dole koka k’iya bare ka so,
sai da Neehal ya shak’i iska kana ya busar yace ” wallahi duk duniya babu wata ‘ya mace da aka haifa,
wacce ta isa ta shiga tsakani na da Najwah,
babu wata ‘ya mace da zan so balle harna aure ta,
babu wata ‘ya mace da mace ta haife ta da zanyiwa Najwah kishiya da ita,
” humm ni ko k’arfin hali irin naka Neehal yana bani mamaki,
kamar kasan me gobe zata haifar, ko wanda k’addarar rayuwarshi take a hannunshi,
Neehal ka taka a hankali kabi duniya da al’amarin Ubangiji a sannu,
ka sani k’addara mace ce mara tabbas da akoyaushe tana iya sauyaw…..!,
da sauri Neehal yace ” Allah yayi mana tsare da irin wannan mummunar k’addarar,
zamu rayu mu biyu kacal daga mu sai yaran mu kawai for ever…..!,
wayarshi data soma ringing yasa shi katse maganar dole,
cike da girmamawa yayi picking wayar Mamy had’i da gaida ita,
ta amsa mishi cike da kulawa, ya amsa tace ” Dadynka yace na kira ka na shaida maka takardar *TAKARDAR TAFIYARKA BAUTAR K’ASA TA FITO!!!*,
(CALL OFF LETTER) haka nan Neehal yaji gabanshi yayi mahaukaciyar fad’uwa, har saida ya sanya hannu ya dafe k’irjinshi,
a fili yace ” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,
cike da mamaki Nauman yayi saurin kallanshi had’i da cewa ” lafiya dai….!?
Kanshi ya girgiza mishi alamar bakomai, itama Mamy sai da ta tambaye shi lafiya,
yace bakomai, Mamy tace ” to kazo gida yau dan kaji sauran bayanan,
jiki a sanyaye yayiwa Mamy sallama kana ya kashe wayar had’i da kishingid’a jikin sofa,
ya lumshe idonuwanshi yana sauraren yadda zuciyarshi ke harbawa da tsananin k’arfi,
lokaci d’aya jikinshi yayi mugun sanyi, Nauman yace ” lafiya meke faruwa Aboki….!?
Idonshi lumshe yace ” bakomai,
amma yanzu fa kake normal but daga yin waya saika canja, please tell me meke faruwa,
idonshi lumshe yace ” tafiya ta service ce tazo, Nauman yace ” shine kuma abin damuwa….!?
“Wallahi haka nan naji gaba na ya fad’i, kuma jiki na ya mutu,
” to kodai rabuwa da Najwah ne….!?
“May be..!, Neehal yace batare daya bud’e idonshi ba,
ya dad’e haka while gabanshi na cigaba da fad’uwa,
kana cikin sanyin jiki Neehal ya bud’e idonshi yace ” muje gida naji inda aka kaini,
ba musu Nauman ya mik’e suka fita, Nauman ne yaja motar har suka isa gida,
yana ta zubawa Neehal surutu amma bai kulashi ba,
suna yin parking su Suhaima suka fito da gudu, suma sama-sama Neehal ya amsa musu,
sai Nauman keta biye musu, da suka isa parlor’n babu kowa sai su Suhaila,
Suhaira ya aika ta shaidawa Mamy ya iso, Mamy tace ace musu su shiga tana parlor’n Dady,
cikin ladabi da nutsuwa suka shiga, suka samu waje suka zauna gefe,
kasancewar har lokacin Dady fushi yake da Neehal yasa bai d’aga kanshi ya kallesu ba,
dan ya lura sai an dawo dashi hayyaci, hankali da nutsuwarshi,
ya lura dole sai anayi mishi haka kana zai shiga hankalinshi,
cikin girmamawa suka ce ” Dady ina wuni…!?
Ko kallan Neehal bayyi ba ya kalli Nauman fuska a sake yace ” lafiya lau Alhamdulillahi,
kallan Mamy Neehal yayi tayi mishi alama daya k’ara gaidashi,
Neehal yace ” Dady ina wuni…!?
“Lafiya, Dady yace batare daya kalle shi ba,
Neehal yace ” Dady k…..! hannu ya d’aga mishi kana ya mik’awa Nauman papers d’in,
yace ” gashi nan ka bashi, hannu biyu Nauman ya sanya ya amsa kana ya mik’awa Neehal,
a fili Neehal yace ” k’auyen *SUNKHANNI K’ARK’ASHEN K’ARAMAR HUKUMAR HARD’O-KOA’LA JIHAR TARABA*
*(SUNKHANNI UNDER HARD’O-KOA’LA LOCAL GOVERNMENT TARABA STATE)*
Mamy tayi murmushi had’i da cewa ” kace garin dangi aka tura ka….!?
“Garin fulani, ai gwara kaje kodan ka koyo al’adu da wasu abubuwan kuma koba komai kaga al’adun fulani,
murmushi yayi kana yace ” Mamy ban tab’a jin sunan garoruwan nan ba, banda Taraba itama ba tab’a zuwanta nayi ba,
Mamy tace ” ai dan hakan nema naso garin nayi murna,
saboda kwata-kwata babu abinda kuka sani daya shafe ni,
sai abinda ya shafi Maiduguri da Barebari kawai kuka sani,
Dady yayi murmushi danya lura da biyu tayi maganar,
cikin sanyin jiki suka mik’e zasu fita, dan har lokacin gaban Neehal baibar fad’uwa ba,
Mamy tace ” ku jira ni a parlor,
“to suka ce suna fita, bayan sun fita Mamy ta kalli Daddy tace ” meyasa har yanzu kake fushi da Neehal bayan ya baka hak’uri….!?
Dady yayi murmushi had’i da cewa ” tunda kike dani kin tab’a gani nayi fushi da wani a duniya….!?
Mamy tace ” a’a, dan duk fad’a da zafin Daddy bashi da ruk’o,
idan kayi mishi laifi ya nuna maka nan take shikenan shi ya wuce a wajenshi,
anjima idan ya ganga zai washe maka baki kasancewar shi mutum mai fara’a da faram-faram, shi dai raini ne kawai baya d’auka,
dan sosai Dady ya tsani rainin wayo,
Dady yace ” to balle d’an dana haifa da ciki na, ke kanki kin san koda zanyi fushi da kowa banda Neehal,
bayan ke da kanki kin san duk cikin ‘ya’yana nafi san Neehal,
ba fushi nake nayi dashi ba, nayi hakan ne saboda karya ga fuska yace bazaije garin da aka tura shi ba,
dan matuk’ar yaga fuska yana iya cewa garin yayi nesa saboda karya rabu da matarshi,
ni kuma kin san hali na ban tab’a neman alfarma akan abinda aka zartar ga ‘ya’ya na matuk’ar bai sab’awa shari’a ba,
kin san bana bambamta yara na dana talakawa, idan shi Neehal yana da gata da uba aka canja mishi gari,
shi wanda za’a kai kin san waye shi, ko shi ba mutum bane, ko ba iyaye ne suka haifashe ba….!?
“Kinfi kowa sanin d’an kowa nawa ne, dan d’a da arziki ba’ayi musu bak’in ciki da mugunta,
saboda Allah ne kad’ai yasan me morarsu, shiyasa tunda nake ban tab’a nemarwa d’ana alfarma ba,
dan yiwa yaro haka yana sawa yaji kamar shi daban ne, ko yafi wani, sai kiga yaro ya fara girman kai da raina mutane da wulak’antansu,
gwara a nuna mishi shima yasan dai-dai yake da kowa, babu wanda yafi,
shiyasa kika ga nayi haka saboda kar yace bazai je ba,
Mamy tayi murmushi tana mik’ewa tace ” yayi kyau Alhajin Allah,
tashi muje muci abinci, ba musu Dady ya mik’e suka fita,
gaba d’aynsu suka zauna suka ci abinci wanda har lokacin zuciyar Neehal bata bar bugawa ba,
bayan sun gama Mamy ta zuba wani a food flask ta sanya cikin basket danya kaiwa Najwah,
ya d’auka had’i da yi mata godiya yayi musu sallama suka fita,
Nauman na tuk’i Neehal yace ” please ka san wani a Taraba State….!?
“Nauman yace ” me zayyi maka…!?
“So nake mu tambaye shi yadda garin yake, yayi maganar cikin sanyi,
Nauman yace ” ban san kowa a Taraba State ba, amma bari zan bincika maka,
“okey thank you, Nauman yace ” no thanks between us,
har suka isa gida basu k’ara magana ba, Neehal ya sauka ya shiga gida, Nauman kuma ya wuce,
cikin sanyin jiki ya shiga gidan ya iske Najwah na gyangyad’i,
murmushi yayi had’i da aje basket d’in abincin kana ya isa gareta,
ya sanya hannunshi ya tallafo ta jikinshi, k’ara shigewa jikinshi tayi tare da turo baki tace ” ina ka tsaya ka barni ni kad’ai….!?
” Call off letter nace ta fito ta tafiya service,
da sauri ta mik’e zaune tana zaro ido tace ” tafiya service….!?
Yace ” eh, baki ta fara tab’ewa zatayi kuka tace ” yaushe zaka tafi…!?
“Next week zamu shiga camp,
” kwana nawa zaku yi a camp?
“3 weeks, ” tab Allah ban iya yin har 3 weeks ban ganka ba, ka sani fa tunda mukayi aure bamu tab’a rabuwa ba,
tayi maganar cike da shagwab’a,
” kiyi hak’uri my Happiness tafiyar ce ta zama dole, kuma Taraba State aka tura ni,
aiko tana jin Taraba ta soma kuka tana diddira k’afa cikin shagwab’a tace ” Allah nima zani ka tafi dani kawai,
” haba dai tunda kike kin tab’a jin wanda zai tafi service ya tafi da matarshi….!?
“To ai sai a fara ta kan mu kaga mun kafa tarihi kenen,
” a’a sai dai kije gidan Mamy ko gidanku kafin na dawo,
sosai Najwah ta fara kuka ganin da gaske dai tafiyar zayyi,
sai da kyar ya samu ya rarrashe ta, taci abinci tayi wanka suka kwanta,
babu irin binciken da Neehal da Nauman basu yi wajen neman cikekken bayani kan garin da aka tura shi ba,
amma ko wanda yasan garin basu samu ba, dan haka dole ya hak’ura ya fauwalawa Allah,
ana gobe Neehal zai tafi Najwah kwana tayi tana kuka wiwi kamar ranta zai fita,
ko runtsuwa ba tayi ba, idanuwanta sukayi luhu-luhu suka kumbura suntum,
washe gari kuwa anga budiri bured’e wajen rabuwar Najwah da Neehal,
da tamkar zararriya haka Najwah ta rink’a hauka tuburan muraran,
sai da Daddy yayi da gaske kana suka rabu, dakyar aka danna ta cikin mota Nauman yaja,
shima Neehal har kukan yayi,
a cikin Camp Neehal ya samu cikekken bayani kan garin da aka tura shi wajen wani d’an Local government d’in Hard’o-Koa’la,
shine yake fad’awa Neehal Nomadic primary school ce kawai a garin,
(ita makaranta ce da gwamnati ta samar domin Fulani makiyaya masu tafiye-tafye daga gari zuwa gari)
sannan idan lokacin damuna yayi ruwan kogi ya kawo, kogi ya cika mota bata iya zuwa sai bayan wata shida,
sai dai jaki, ko rak’umi, da kwale-kwale.
idan kuma ba lokacin damuna bane sau d’aya tak a wata mota take zuwa k’auyen kusa da garin wanda tazararsu akwai nisan kilometers 50,
Sunkhanni k’auye ne na gagari garin babu wutar lantarki,
garin fulani ne na asali wanda ko Hausa basa ji, kad’an daga cikin ‘yan garin ne ke jin Hausa,
suma ba wata cikekkiyar Hausa suke ji ba, sannan garin basu da ginannun gidaje,
sai dai bukkoki, kuma gaba d’aya bukka batafi 30 ba, jefi-jefi,
a warwatse impact *(FULANIN DAJI NE)* ko da Neehal yaji wannan mummunan labarin sosai hankalinshi yayi masifar tashi,
saboda yasan babu yadda za’ayi ya iya rayuwa cikin k’asurgumin dajin,
sama-sama Neehal ya gama rayuwar Camp ya koma gida,
duk tsananin k’iyayyar mutum da Najwah idan ya ga yadda ta koma cikin sati uku,
sai yayi mata kuka tayi muguwar rama ta k’ek’ashe, ranar da Neehal zai koma gida,
murna kam ba’a magana dan bakinta k’in rufuwa yayi, tun around 11:00am na safe,
Najwah ta dawo harabar gidan ta tare, babu yadda Mamy batayi da ita,
kan takoma koda falo bane, amma Najwah tak’i, su Neehal basu k’araso ba sai 5:20pm na yamma,
amma Najwah na nan zaune tana faman jiranshi tana ganin sun shigo tayi kan motar da gudu,
shima jikinshi na rawa ya bud’e motar ya fito tun kan ta k’arasa tsayawa,
suka rungume junansu cike da tsantsar kewa, bege da so basu damu da cewar a gidan iyayensu suke ba,
sun dad’e haka basu saki juna ba, sai da su Suhaila suka fad’a jikinshi,
kana ya tuna a gida yake dan haka yayi saurin sakinta ya rungume su Suhaima,
a fili Najwah taja uban tsoki, bai kalle ta ba ya cigaba da abinda yake yi,
abincin da Mamy da masu aiki suka dafa mishi kala-kala suka zauna dinning table,
suna ci suna hira har da Daddy anan Neehal ya fad’a musu labarin garin da aka kaishi,
ya shiga rok’on Daddy yana yi mishi magiya kan yayi magana a canja mishi gari,
Mamy tace ” dan Allah Alhaji ka taimaka mana,
duk maganar da Mamy da Neehal keyi Daddy bayyi magana ba,
har ya gama cin abincin shi, kana ya kalle su a nutsu yace ” idan shi bai gama sanin hali na har yanzu ba,
aike kinfi kowa sanin waye Bilal Lagosa, idanshi bai san waye mahaifinshi ba,
aike kin san waye mijinki, ina da tabbacin ba Neehal kad’ai aka tura garin ba,
so wad’anda aka tura basu da rai ko iyaye ne….!?
“Ko kuma su ba mutane ne kamar shi ba, ko ba iyaye ne kamar mu suka haife su ba…!?
Neehal yace ” but Dad…..! dakatar dashi Daddy yayi ta hanyar d’aga mishi hannu,
kana ya d’ora da cewa ” wallahi Allah kaji ma na rantse bazan tab’a canja maka ba,
can zakaje kamar yadda kowa zaije inda aka tura shi,
jin Daddy ya rantse yasa babu wanda ya sake cewa kowa komai,
Neehal ya k’udurce a zuciyarshi idan ya tafi ko zai mutu bazai dawo hutu ba har sayya gama,
hmmm tashin hankali wanda ba’a saka maka rana, dan hauka da d’ibar albarkar da Najwah tayi abin har ba’a magana,
dan ya wuce hankali da tunanin mai karatu sosai ta rink’a hauka tuburan tana ihun kuka,
tamkar wacce gaba d’aya ahalinta suka mutu haka Najwah ta rink’a ihuuuu,
dakyar da jib’in goshi aka raba Neehal da Najwah, a Taraba Neehal ya tsaya ya siyi,
generator, gas cooker, tukunya, indomie, sardine, taliya, makaconi, couscous, tumaturin kwankwani, fridge, ‘yar yawo, duk wani abu na amfanin gida da kayan girki dana abinci Neehal ya siyi abinshi mai uban yawa,
har katifa, bargo, pillow, carpet, drinks da faro ko 30 30 cartoon ya soya, snacks da biscuit ko ba’a magana, sai da kayan Neehal suka cika akorikura taf,
kana ya shiga Local government d’in Hard’o-Koa’la da kayan mutane nata kallanshi,
shiko yasan me yake yi, daga can aka had’a shi da mata biyu da zata tafi k’auyen Sunkhanni tare,
dayake baizo da mota ba a motar haya yazo, dakyar akorikurar ta iya shiga k’auyen Sunkhanni,
tsaye cak Neehal da ‘yan matan sukayi ganin irin k’auyen da suke ciki tsaye,
garin a tsakiyar dokar daji yake, sannan duk garin tuka-tuk’a d’aya ce dasu,
kuma mutanen garin basu fi 100 ba manyansu da yaransu,
garin dai irin asalin k’auyukan man ne ma gagari, k’auyen futuk.
Jagora wani matashin saurayin bafulatani yayi musu gaban sugaban k’auyen,
suka zauna saman tabarma while gaba d’aya ‘yan k’auyen na zagaye dasu,
shugaban k’auyen ya fara magana kamar haka ” barkanku da zuwa bak’in mu,
munyi matuk’ar murna da farin cikin zuwanku, sai dai muna da dokoki da sharud’a a k’auyen nan,
kafin nace komai dai wad’annan matan matanka ne….!?
Yayi maganar direct to Neehal, Neehal ya kalli k’ediran matan,
asalin inyamurai christian wad’anda ko ci kanka da Hausa basu sani ba,
irin murd’a-murd’an jigaggun matan nan ne tik’a-tik’a,
yayi saurin cewa ” a’a cike da kyama,
shuganban yace ” to ina matarka….!?
“Tana gida, Neehal ya bashi amsa,
shugaban k’auyen ya cigaba da cewa ” mu’a wannan k’auyen Namiji baligi baya tab’a zama babu aure,
wannan yana d’aga daga cikin sharud’an mu baligin namiji baya zamar nama bashi da mata,
dan haka dole cikin uku ayi d’aya na farko kodai ka kira matarka tazo nan ku zauna tare,
na biyu ko kuma kayi aure ina nufin ka auri wata matar,
na uku ko kuma mu kashe ka dan haka dokar garin nan take,
dole cikin ukun nan ayi d’aya zab’i ya rage naka…………….!!!!!
Cikin tsantsar tashin hankali, firgici da kid’ima Neehal ya d’ago kanshi,
ya kalli mutumin dake magana cike da isa wanda ko darajar mai gadin gidan su bai kai ba,
d’an shiru Neehal yayi yana tunani dan a zatonshi baiji abinda mutumin yace ba,
dan haka Neehal ya sake kallan mutanan dake zagaye dasu,
tamkar wad’anda suka aikata wani mugun abun kana Neehal,
ya mayar da kallanshi ga mai garin yace ” banji abinda kace ba,
mutumin yayi murmishi a karo na biyu kana yace ” cewa nayi mu’a garin mu ba’a zama babu aure,
domin kujewa b’arna yasa yaran mu maza suna da shekara sha shida,
16yrs) muke yi musu aure yayinda yaran mu mata ke da sheraka,
goma zuwa sha biyu (10 to 12yrs), yawancin mu duk sai da akayi mana aure kana muke balaga daga baya, bayan munyi auren,
mazan mu da matan mu daka gani anan gaba d’ayan mu haka aka yi mana,
tun iyayen mu da kakanin mu wannan dokar take cikin garin nan,
dan haka koda bak’o ne yazo baya zamar mana a gari babu aure,
dan haka na baka zab’i cikin uku ka d’auki,
na farko kodai ka kira matarka tazo nan ku zauna tare,
ko kuma kayi aure a garin nan cikin mu idan da wanda zai iya bawa bak’o ‘yarshi,
sayya baka danya fanshe ka ko kuma mu kashe ka, saboda idan mu bamu kashe ka ba,
kai zaka kashe mu ko kuma ka turo mana ‘yan sanda su kama mu dan ku ‘yar birni imani da tsoran Allah ba isarku yayi b……..!,
tunkan shugaban k’auyen ya k’arasa maganarshi, Neehal yayi murmushi had’i da cewa,
” karka damu bakomai indai dan zuwan mata ta ne babu matsala,
zanzu zanyi waya gida zuwa gobe sai a kawo min ita,
shugaban k’auyen yace ” to..! to…! madalla kira ta,
batare da Neehal ya kuma yin magana ba, ya ciro wayarshi cikin aljihu,
yayi dialing number Najwah,
deep down yana tunanin yadda Najwah zata iya rayuwa cikin wannan k’asurgumen dajin,
dan bama za’a kira shi da k’auye ba sai dai daji,
” but I know she can do anything akan ayi mata kishiya,
zata iya zama koda cikin dokar daji ne inda babu mutane da ayi mata kishiya,
yayi maganar cikin ranshi while yana dialing number ta bisa mamakinshi sai yaji wayar not reachable,
k’ara dialing number yayi still not reachable, a k’alla Neehal yayi dialing number Najwah yakai sau 30 but not reachable,
d’ago kanshi yayi yaga gaba d’ayan mutanan k’auyen sun zuba mishi ido suna kallanshi,
d’an muguntun murmushin yak’e yayi wanda iyakacinshi labb’anshi,
hannunshi na kerrrrrma yayi dialing number Daddy, shima Neehal ya kirashi yakai sau 20 amma baya shiga,
daga Daddy ya kira Mamy sau 20 itama number bata shiga, ya kira Nauman ko yakai sau 50 bata shiga,
duk danginshi har wad’anda basa magana basa wani zumunci ranar sai da Neehal yayi ta neman numbers d’inshi bata shiga,
kamar daga sama Neehal yaji muryar shugaban k’auyen yana cewa,
“yaro dena wahalar da kanka a banza kana bawa kanka wahala abanza,
saboda bamu da HANYAR SALULA , dan kwata-kwata bamu da hanyar sadawarta,
wata irin fitinanniyar fad’uwa gaban Neehal yayi, cikin tsantsar rud’ewa da zallar tashin hankali ya kalli shugaban k’auyen yace “what….!?
“Ba….. ba… ba… bangane abinda kake nufi ba,
kana nufin kona kira bazata shiga ba….!?
Shugaban k’auyen yayi murmushi had’i da d’aga mishi kai alamar eh,
da sauri Neehal ya mik’e tsaye hannunshi na rawa ya soma daddana wayarshi,
ganin gaba d’ayan wayoyinshi babu services d’in ya d’auke,
durk’ushewa Neehal yayi a wajen had’i da tallafe kanshi, shugaban k’auyen yace ” yaro kuje kuci abinci ku huta zuwa gobe ma nemeku,
kana ya mayar da kallanshi ga wasu matasan masari,
yace ” kuyi hak’uri ku basu sababbin bukkokinku da kuka yi,
inyaso sai ku sake wasu cikin girmamawa matasan suka ce ” to ranka ya dad’e,
kana ya kuma kallan Neehal yace ” kuje su raka su yanzu za’a kawo muku abinci,
Neehal bai mik’e ba ya cigaba da zaman dirshen, cikin bak’in ciki da takaici yadda kasa an aiko mishi da sak’on mutuwa,
shugaban k’auyen ya kuma cewa ” yaro ka tashi kuje ko….!?
Banza Neehal yayi dashi, shugaban k’auyen yayiwa Neehal magana a k’alla sau uku amma baiko d’aga kanshi ya kalle shi ba,
balle ya bashi amsa, kasan fulani da zafin rai gami da k’eta,
take ranshi yayi masifar b’aci ya kuma kudiri niyyar yiwa Neehal halin nasu na fulani,
wato mugunta amma a zahiri sai yayi murmushi tare da mik’ewa,
ya umarci gaba d’ayan mutanan k’auyen dasu watse, aiko ba musu kowa ya kama gabanshi,
aka bar Neehal zaune nan shi kad’ai cikin d’acin rai da k’unar zuciya,
yadda aka tafi aka bar Neehal haka ya kwana nan baiko motsa ba,
ko sallah bayyi ba, haka ya kwana yana ta dialing numbers ta kowa da kowa duk da yaga babu service kwata-kwata a garin,
amma hakan baisa shi ya hak’ura ba, ko kallan bak’in tuwan dawa da miyar kukar da aka kawo mishi bayyi ba,
da ganin tuwon zayyi tauri kamar dutse, haka Neehal ya kwana bai runtsa ba,
ko gyangyad’i bayyi ba balle bacci, yadda yaga rana haka yaga dare,
Sai da yaga alfijir ya fara ketowa lokacin sallar asuba ya wuce kana ya mik’e yaje inda aka sauke mishi kayanshi,
ya d’auki robar ruwa yayi alwala ya fara rama sallar ishshar da ake abinshi,
kana ya gabatar da sallar asuba har gari waye tangaran Neehal na gaban Allah yana ta addu’a,
kan kada Allah yasa ayi ko d’aga cikin sharud’ansu,
Allah ya d’ora shi kansu, haka Neehal yayi ta jera addu’o’i yana kuka har mutanen garin suka soma fitowa.
Ba k’armin mamaki sukayi na ganin Neehal yana nan inda suka barshi ba,
ga idanunshi nan sunyi jajir kamar gauta, da gani bayyi bacci ba,
lokaci d’aya tausayinshi ya dira a zuciyar Malam Liman, wanda shine limamin garin,
gidanshi ya koma ya anso d’umamen abinci ya d’auka ya taho dashi,
cikin nutsuwa magidancin Limamin ya zauna kusa da Neehal,
batare daya kalli Neehal ba yace ” sau tari abubuwan da muke tsammani basu ne ke faruwa damu ba,
haka abinda muke tunanin basu fiye faruwa a rayuwarmu ba,
haka mafarkan mu basu fiya zama gaskiya a duniyar mu ta zahiri ba,
da gani babu abinda ke damunka face zafin so da soyayya,
yaro kai yaro ne har yanzu kar kayi sake da biyu a rayuwa,
na farko damarka na biyu lokaci, dukkaninsu abubuwa ne da suke zuwarwa mutum sau d’aya tak a rayuwa,
mutum mai sa’ar gaske ne yake samunsu sau biyu a rayuwa,
dan haka kayi amfani da lokacinka tun kafin ya k’ure maka,
haka kayi amfani da damarka tun kafin ta kufce maka,
dan haka kayi addu’a ka barwa Allah komai, ka bari Allah yayi maka zab’in haske da abinda yafi alkhairi,
ka bar Allah yayi maka komai ya kuma baka abinda ya dace da rayuwarka,
kada ka sake kayiwa Allah shisshigi ko ka shiga hurumin Ubangiji,
ga abinci nan kaci yayi maganar had’i da mik’ewa, har Malam yayi jawabinshi ya gama,
Neehal ko d’aga kanshi bayyi ya kalle shi ba,
bayan Malam Liman yabar wajen Neehal ya kalli kwanon daya aje,
yaga samira ce a rufe bai k’ara kallan inda ya aje abincin ba,
yana nan zaune shugaban k’auyen da jama’a suka iske shi,
cike da mamaki ya kalli Neehal yace ” da alama bakayi bacci ba ko…..!?
“Naga kamar ko abincin ma baka ci ba ko…!?
Neehal bai d’aga kanshi ba balle ya kalleshi, shugaban k’auyen ya kalli wani yaro yace ” maza jeka kira min sauran bak’in da suka zo tare,
ba’a jima ba saiga su tare suka zauna daga gefen Neehal yayi saurin matsawa,
shugaban k’auyen ya kalle su yace ” to ku na dawo gare ku,
kuna auren ku ma ko kuwa….!?
Kasancewar basa jin Hausa yasa su kallan Neehal dako motsi bayyi ba,
suka ce ” Mr Lagosa what’s going on here….!?
” We see you in tension, since yesterday is everything fine….!?
A hankali ya d’aga kanshi ya kalle su kamar zayyi musu bayani,
sai kuma yayi shiru yace ” they ask you about your marital status,
are you single or engaged or married….!?
“We’re all married and we have kids,
shugaban k’auyen ya kalle su kana yace ” kai bana san shak’iyanci kuyi min magana yadda zan gane,
ko wani abun kuke shiryawa ne….!?
Ido Neehal ya zuba mishi na a k’alla minti biyu zuwa uku, kana yace ” basa jin Hausa ko fulatanci,
kallan juna mutanan k’auyen suka fara yi kafin daga baya shugabansu ya sauke numfashi,
had’i da cewa ” idan basa jin Hausa da Fulatanci sai wane yaren suke ji….!?
“Inyamurai ne daga yaren su sai turanci kawai suke ji,
” to wanne yare naji kuna yi yanzu dasu….!?
“Turanci…! Neehal ya bashi amsa a dak’ile,
” wani yare ne kuma haka….!?
Shugaban k’auyen ya kuma tambayar Neehal, tsoki Neehal yaja cikin ranshi batare daya ce mishi komai ba,
shiru aka d’anyi na wucin gadi, kana shugaban k’auyen yayi gyaran murya,
had’i da numfasawa yace ” to yaro mu dawo kan maganar mu, wanne hukunci ka yanke….!?
” Ka samu matar taka ko kuwa har yanzu….!?
“Ban same ta ba, amma ina san naje na taho da ita, Neehal yayi maganar idanshi kan shugaban k’auyen,
shugaban k’auyen ya sanya dariya sosai sai da yayi me isarshi kafin yace ” zancen banza inji mutanan banza,
ko kana tunanin saboda mu ‘yan k’auye ne a karkara muke zaka iyayi mana wayo saboda kai d’an birni ne….!?
” Ai bazaka tab’a fita daga k’auyen nan ba face ka zab’i abu d’aya cikin biyu,
ka daina tuna yanzu sauranka zab’i biyu kawai,
imma dai kayi aure ko kuma mu kashe ka,
Neehal yayi shiru had’i da sunkuyar da kanshi k’asa yana tunanin,
ya za’ayi ya yiwa Najwah kishiya, ta yaya zai iya karya tarin alk’awarirrikan da yayiwa Najwah,
ta yaya zai iya sanar da Najwah zayyi aure, zayyi mata kishiya,
ya tuno irin tarin haukan da take a duk lokacin da mace ta kalle shi kawai,
ya tuno haukan da take yi idan mace ta rab’eshi, even blood sisters d’inshi tana kishinsu,
ta yaya zai k’ara aure, bayan yasan hakan dai-dai yake da mutuwarta,
yasan muddin taji yayi aure zuciyarta ce zata buga ta mutu,
yasan rayuwarta tazo k’arshe shi kuma yasan muddin babu Najwah cikin rayuwarshi,
to tabbas zai kasance ne cikin k’unci da uk’ubar rayuwa,
zai rayu ne tamkar mutum mutumin wanda bashi da amfani kwata-kwata,
yasan babu shi babu farin ciki, nutsuwa, walwala da jin dad’in duniya,
to tayaya shi da kanshi zai tarwatsa rayuwarshi, zai lalata duniyarshi,
zai wargaza tarin farin ciki da jin dad’in su, a hankali ya d’ago kanshi ya kalli mutanan k’auyen,
yaga tabbas zasu iya kashe shi, dan yasan jahilai ne tuburan muraran,
yasan bazasu d’auki ran mutum wata tsiya da wata daraja ba,
dan ya lura basu da imani da tausayi zasu iyayin komai domin al’adarsu,
muryar shugaban k’auyen ce ta katse mishi tunani ” yaro meka yanke….!?
Cikin rawar baki Neehal yace ” gaskiya bazan iya k’ara aure ba,
saboda nayiwa matata alk’awarin bazan tab’a yi mata kishiya ba,
” ka zab’i ka mutu kenan….?
Neehal yace ” a’a,
” yanzu bawan Allah kai ka zab’i ka mutu ka barta ita a raye ta auri wani…..?
“Ka zab’i ka mutu saboda ita kan kayi mata kishiya zaka mutu,
bayan kasan idan ka mutu dole wani namijin zata aura musamman idan yarinya ce,
Neehal yayi shiru yana tunani danya san tabbas haka ne, duk irin zafin so da soyayyar da Najwah take yi mishi,
k’ark’ari tayi 5yrs ba aure dan yasan dole komai lokacin da zata d’auka zatayi aure,
ta rayu da wani su had’a jiki da gado, ta kuma manta dashi musamman ma dayake yasan basu da d’a basu haihu ba,
duk da yasan haka ya gwammaci ya mutu kan ya karya alk’awarin da yayi mata,
wanda zayyi sanadiyyar mutuwarta,
” gaskiya bazan iya yi mata kishiya ba,
Neehal ya fad’a yana kallan Malam Liman dan shi yayi maganar,
Malam Liman yace ” kana ganin kamar bazasu iya kashe ka ba ko….!?
“To wallahi zasu iya dan kafin kai anyi wasu,
kai Neehal ya girgiza batare da yayi magana ba, shugaban k’auyen yayi murmushi had’i da yin gyaran murya,
ya kalli wasu matasa yayi musu magana da yaren fullanci,
cikin girmamawa suka ce amsa masa da fullanacin suma, kana suka bar wajen,
ba’a d’auki lokaci ba sai gasu sun dawo, suka ce ” mum gama,
shugaban k’auyen ya mik’e tsaye had’i da kallan sauran jama’a yace muje,
yana gaba suna biye dashi har suka k’arasa inda matasa suka kakkafa icce,
sudai inyamuran matan nan da ido kawai suke binsu dan basa jin abinda ake fad’a,
shugaban k’auyen ya kalli jama’a cikin fullanci yace ” to jama’a kamar yadda kuka sani kan dokar mu,
dan haka zamu kashe wannan kamar yadda yafi buk’atar mutuwar kan rayuwarshi,
tunda ya zab’i mutuwarshi kan aure, yana gaba fad’a gaba d’ayansu suka shiga kuwwa suna maganganu,
sai da shugaban k’auyen ya d’aga hannu kana sukayi tsit,
umarni ya bawa wad’annan matasan na farko,
yace ” ku kafeshi sannan ku tsire shi, matasan sukayi kanshi,
da sauri Neehal ya runtuma a kuje suka bishi, inyamurai suna ganin Neehal ya zunduma a guje suka bi bayanshi, suna ihuuuu da kuka suma,
sosai Neehal yake gudun mutuwa dan tsira da rayuwarshi,
shugaban k’auyen ya saka matasa suka k’ure mishi gudu suka kamo shi,
Neehal yayi wujiga-wujiga kasancewar gudun dayayi ga yunwa da k’ishirwar ruwa,
dan rabonshi da saka wani abu a bakinshi har ya manta, ga rashin bacci jiki ba kwari,
Neehal yana kuka da haki ya shiga rok’on su yana yi musu magiya kan suyi masa hak’uri su kyale shi,
amma babu wanda yake k’ala, sai Malam Liman dayace ” har yanzu kana da sauran dama da lokaci na ceton rayuwarka,
idan baka manta ba na fad’a maka amfanin dama da lokaci,
Neehal yana kuka wiwi yana rok’onsu amma shugaban k’auyen ya kuma umartar matasan dasu yi kamar yadda yace,
k’attin matasa suka kama Neehal suka bank’areshi suna niyyar tsire shi,
ganin mutuwa muraran yasa Neehal cewa ” na yarda zanyi auren,
gaba d’ayan mutanan k’auyen suka saka dariya banda Malam Liman,
” ja’irin yaro ashe kana san rayuwarka….!?
Cewar shugaban k’auyen yana dariyar k’eta,
Muryar Neehal na rawa yace ” eh..! na yarda zanyi auren,
” ashe kasan dad’in rai, da ka tsaya kana neman kashe kanka kan wata banzar mace,
wacce idan ka mutu aurenta zatayi ita,
Neehal na haki yace ” zanyi auren…!,
yayi maganar yana haki, shugaban k’auyen yace ” ka tabbatar zakayi…..!?
Da sauri Neehal yace ” eh…..! zanyi,
juyawa shugaban k’auyen yayi ga sauran jama’a yace ” waye zai iya bashi ‘yarsa….!?
Gaba sukayi shiru, ya kuma cewa ” akwai wanda zai iya bawa bak’o auren d’iyarshi….!?
Still babu wanda yayi magana,
” babu wanda zai iya ceton ranshi da rayuwarshi ya bashi auren ‘yarshi…..!?
Rad’e-rad’e suka fara yi suna magana k’asa-k’asa,
“tab…! wa zai bawa bak’o wanda ba’a sanshi ba, ba’a san asalinshi da inda ya fito auren ‘yarshi,
musamman ma wannan mai taurin kan, mutum yaje ya bashi ‘yarshi ya yaje yana bata wahala,
ji fa yadda yake san matarshi akanta ya gwammaci mutuwa kawai mu bashi ‘yarmu yaje ya kashe ta,
wama ya sani ko d’an yankan kai ne,
haka dai mutanen k’auyen sukayi ta maganganu Neehal naji,
matan inyamurai sun had’e sun dunk’ule waje d’aya suna kuka jikinsu sai kerrrrrma yake,
shugaban k’auyen ya kuma cewa ” bazaku iya taimakonshi ba….!?
Gaba d’ayansu suka ce “eh…!, jikin Neehal na kerrrrrma yana b’ari ya shiga yi musu magiya yana rok’onsu,
amma babu wanda ya saurareshi, shugaban k’auyen ya kalli Neehal cike da tausayawa,
yace ” kayi hak’uri babu wanda zai iya baka ‘yarshi ka aura,
saboda tsoro da k’abilanci irin na fuld’e🤪🤪,
sunga irin taurin kanka da tsananin soyayyarka ga matarka,
suna tsoran karka bawa ‘yarsu wuya,
dan haka dole mu kashe ka, sosai Neehal ya k’ara sautin kukanshi,
yana rok’onsu, ya jima yana rok’onsu amma basu saurare shi ba,
dan haka ya saddak’ar mutuwa zayyi yace ” wata k’ila saboda haka na rink’a jin fad’uwar gaba,
da tsoro tun lokacin da call off letter na ta fito,
ido ya runtse da k’arfi yana tuno Mamy, Daddy, Naufal, Suhaila, Suhaira, Suhaima, Nauman,
ya rink’a ganin fuskar Najwah tana yi mishi murmushi da dariya,
hawaye na gangaro mishi, shi kanshi shugaban k’auyen ba k’aramin tausayi Neehal yabashi ba,
dan dai bashi da yadda zayyi ne kakanshi ma haka ya taso yaga wannan dokar,
cikin sanyin murya shugaban k’auyen ya kuma tambayar mutanen,
danshi gaba d’aya yaranshi sunyi aure,
amma suka ce babu wanda zai bashi,
inmurai dai sai ihuuu suke suna kuka had’i da kiran Jesus,
ganin haka yasa aka kuma kama Neehal aka bank’areshi,
yana ihuuuun kuka kamar ranshi zai fita while yana cigaba da rok’onsu,
sun d’aga mashi zasu tsire shi Malam Liman yayi saurin cewa ” ni zan bashi auren ‘yata *NEELAH…!*,
cak suka tsayar da mashi a dai-dai k’irjinshi, Neehal ya bud’e idanshi daya runtse lokacin da yaga an d’aga mashi za’a tsire shi,
ido ya zubawa Malam Liman yana kallanshi, cikin kwayar idanshi Neehal ya hango tsantsar tausayawa da son da yake mishi,
kwat…! Neehal ya had’iyi wayu cike da fargaba,
shugaban k’auyen ya kalli Malam Liman yace ” ka tabbata zaka bashi auren NEELAH……!?
“Eh…! zan bashi cewar Malam Liman, gaba d’ayan mutanan k’auyen suka cika da tsanin mamaki,
dan kowa yasan irin mugun so da k’aunar da Malam Liman ke yiwa tilon ‘yar tashi NEELAH,
wacce yake jinta tamkar ranshi da rayuwarshi,
shugaban k’auyen ya kalli Neehal yace ” Allah ya taimake ka kana da sauran rayuwa da shan ruwa a gaba,
Malam Liman ya fanshe ka,
ido kawai Neehal ya zubawa Malam Liman ya kasa furta koda kalma d’aya,
shugaban k’auyen yace ” a yau za’a d’aura auren su dan bazai k’ara kwanar mana a gari babu aure ba,
Malam Liman yace ” bakomai na yarda, muje yanzu a d’aura auren,
ba musu gaba d’ayansu suka d’unguma suka koma wajen bukkokinsu,
dan sunyi nesa dasu har suka isa idon Neehal yana kan Malam Liman,
gindin bishiyar da suke zama bisa kaba wanda yake kamar nanne majalisar manyan garin,
nan shi kanshi shugaban k’auyen yake zama, kowa da kowa ya zauna har Neehal da har lokacin jikinshi bai bar tsuma ba,
bayan ya zauna an nutsu Malam Liman ya kalli Neehal yace ” kana da sadakin da zaka bayar….!?
Da sauri jiki na rawa da kerrrrrma Neehal yace ” eh…!,
“bayar, Malam Liman yace, jikinshi na tsuma ya bud’e jakarshi ya zaro bandir d’in 500 na 50k ya mik’a,
gaba d’ayan mutanan k’auyen suka soma magana k’asa-k’asa saboda ganin kud’in da sukayi,
bakin Malam Liman bud’e yace ” yaro wannan kud’in ai yayi yawa,
Neehal yace ” a’a bayyi yawa ba dubu hamsin ne ba yawa,
” dubu hamsin….!?
Shugaban k’auyen da kusan gaba d’ayan jama’ar dake wajen suka maimaita,
dakyar Malam Liman ya yarda ya karb’i 50k d’innan,
Malam Liman ya amsa kana ya kalli shugaban k’auyen yace ” kayi wa NEELAH waliyyanci ni zanyi mishi, fuskar shugaban k’auyen d’aure da murmushi yace ” to…! to…! madallah,
Malam Liman ya kalli Neehal yace ” ya sunanka….!?
Da sauri yace ” Muhammad,
nan take gaba d’ayan mutanan k’auyen suka shaida D’AURIN AUREN NEEHAL BILAL LAGOSA DA NEELAH MUS’AB AKAN SADAKI DUBU HAMSIN……!
dai-dai lokacin da aka shafa fatihar D’AURIN AUREN Najwah ta farka a firgice daga bacci had’i da kurma uban ihuuuun…….!?