EL-MUSTAPHA
CHAPTER 2
Baa wani bata lokaci sosai ba aka dauki amarya xuwa gidanta,
Ranar jiddah tasha kuka sosai da kyar aka banbareta jikin hajiya, itama hajiyar sai da ta xubar da kwallah, duk yanda kayi sabo da d’iya mace dole akwai ranar da wani xaixo ya dauke ta daga gareka.
Ya turo kofa ya shigo bayan ya dawo daga raka abokansa, tana can qudundune a qarshen gado.
A hankali ya qarasa gurinta ya xauna hade da janye lullubin dake kanta, idonta duk ya kumbura sunyi jawur saboda kuka, yayi ajiyar xuciya,
Kukan me kike yi jiddah, dan Allah kiyi haquri kidaina cikin lokaci qanqani xakiyi sabo da nan har ki manta gida.
Har yanxu tana jin takaicinsa, abinda ya faru a daxu idanunta sunqi daina hasko mata, ta dauke kanta gefe batare da tayi magana ba, yayi juyin duniyar nan tayi magana taqi,
Batare da tunanin komai ba ya dauke ta cak ya nufi dakin sa da ita, batayi mamaki ba dan ya dauke ta cos ya girmeta nesa ba kusa ba, ingarman jikine a tare dashi,
Xaunar da ita yayi akan gado ya sunkuyo sosai numfashinsu yana bugar juna, hakan ba qaramin rikitata ba karo na farko a rayuwarta,
‘ki gayamin damuwar ki jiddah, ba haka muka saba yi dake ba, wannan canjin na fuskarki mean something, still batayi magana ba, sai ya dauke ta karo na biyu ya soma hajijiya da ita a tsakiyar dakin,
Tini suka zube kan carpet nishi kawai take sama sama, shi kansa ya jigata, a hankali ya mirgino ya dora kirjinsa akan nata, ya soma goga tsinin hancinsa akan nata batayi aune ba ya fara kissing dinta ta ko ina, kuka ta sa masa.
Ya dago fuskarta yana girgixa kansa hade da share mata hawayen,
No.. No.. Pls don’t cry, bana son taurin kai a rayuwata kibari mu fahimci juna kinqi tun daxu, na kiraki a waya kinqi dauka sai turo min test kike wai manemin mata, shiru tayi masa tana sheshshekar kuka, ya hada fuskarsu guri daya,
Ba kuka nace kiyi ba, look at me and answer my question that’s all, wata taxo tace maki ina nemanta ne?
Nidai ka kyaleni ta fada tana qoqarin xame jikinta daga nasa,
Yace baxan kyale kiba, apart from abinda kika gani yau kin taba ganina da wasu mata ne ko an gayamaki ni manemin mata ne?
Cousin’s dina ne jiddah you have to know them, baa nan suke ba, suna karatu a Egypt ne, ba laifi bane dan kinganni ina daukar su pic, jinina ne su suna da iko akaina.
Tun farko na gayamaki bana neman mata, da ina da irin wannan d’abiar ke kanki xaki gane kina ganin yanda mata ke tururuwa a kaina.
Tayi shiru, tanajin dadin qamshin turarensa yanayinsu a haka taji kamar kada su rabu, she feels it,
Kinci abinci, ta girgixa kanta a sanyaye, yasa hannu ya shafi cikin yanda yajisa ya tabbatar ba komai aciki, ya tashi yana fadin
Subhanallah jiddah, xama da yunwa bashi da kyau kada ki sake irin wannan kinji, ta gyada kai tana kallonsa.
Ya fice, gasasshiyar kaxa mai ruwa ruwa da fresh milk ya kawo mata, yayi yayi taci taqi saboda nauyinsa da takeji, ya tashi ya nufi toilet yana fadin kafin na fito ki tabbatar kinci kin qoshi, kixo kiyi alwallah mu gabatar da sallah.
Nan ma gyada kai tayi tana kallonsa ya shiga bayin, ba laifi taci da yawa kam ta qoshi, yana fitowa ta shiga bata jima ba ta fito suka gabatar da sallah,
Da kanshi yaje dakinta ya dauko mata kayan barci ya kawo mata, sanda ta sauya kayan qaton hijab ta dora, ita kam hankalinta baya jikinta ji take kamar ta xura da gudu tabar dakin yanda takeyin komai a takure.
Kallonta yayi cikin murmushi qasa qasa, yana son yanayin kunyarta sosai take birgesa, riqo hannunta da yayi yasa jikinta ya fara rawa, yana cire hijabin tayi saurin sunkuyar da kanta qasa kamar xata nutse qasa saboda kunya, ya rage hasken dakin kana ya dauke ta cak sai akan gado.
Duk bidirin da yake jiddah na jinsa, ba kuka take mai fitar da sauti ba sai dai hawaye hakan ya qara masa qaimi akan abinda yake,
Bai barta ba sai da ya sami nutsuwa, hada ta yayi da jikinsa yana shafar bayanta a hankali,
Jiddana is strong, jiddana yar albarka, jiddana ta bani farin cikin da ban taba samun shi a duniyata ba, jiddah itace mace ta farko dana fara sani a rayuwata kuma itace ta qarshe insha Allah, ina sonki jiddah, ina son kasancewa tare dake har qarshen rayuwata, nobody can sperate us we are meant for each other I promise you this.
Ta lumshe idanuwanta, hannuwanta tasa ta xagayo dasu ta bayansa ta rungumesa cikin tsananin sonsa, ko bata fito ta furta masa tana sonsa ba gangar jikinta Ma shaidace.
*
A wannan daren Allah kadai yasan yanda uwani take ciki, sai faman juyi take a tsakiyar gadon, idanunta sun kumbura sosai saboda kuka, xuciyarta sai hasko mata take jiddah nacan akan kirjin el’mustapha din ta🤥 kuma ko ta halin qaqa sai ta auri el’mustapha, sai ta mallakesa ya xamo nata.
Nutsuwar xuciya da sanyin muhalli da ta samu ya haifar mata da murmurewa cikin yan kwanaki qalilan,
Tayi ďan jikinta, ta qara kyau da haske Sai wani fresh takeyi, ba abinda takeyi a gidan kuma bata cikin fargabar komai.
kwαnαkín amarcin daya biyo baya baa magana, tana samun kulawa da soyayyar el’mustapha a koda yaushe, gwargwado itama tana qoqarin nuna masa tata kulawar.
Suna xaune cikin farin ciki da soyayyar juna, sai dai abinda jiddah ta lura dashi game da el’mustapha yana daya daga cikin irin maxan nan da Sam ba koyaushe suke son kasancewa da matansu ba kamar ita da Allah yayi ta cikin rukunin matan nan masu tsananin buqatar miji.
El’mustapha daya fuskanci haka a tare da jiddah bai taba bari ta nemesa yaqi biya mata buqatarta ba koda kuwa he is not in need, dole sai ya sauke wannan haqqin dake kansa, baya son batawa jiddah ko kadan haka yake ji kamar xuciyarsa tana tafiya ne tare da ta jiddah.
Sanda ta haifi twins maza a lokacin akayi masa qarin girma xuwa AIG na police, tym din uwani ta gama skul sai jiddah ta maidata nan gidanta abuja ta cigaba da xama tare da ita tana xuwa skul har lokacin da xatayi miji.
Yanda jiddah ta dauki uwani tamkar qanwarta da suke uwa daya uba daya kasancewar hajiya da abba sunyi mata riqo irin na amana da babu xalunci aciki kamar sune suka haifeta, wannan dalilin yasa jiddah tayi alqawarin kula masu da uwani harta maidota inda take da xama.
*
Dawowa daga labari
Bayan kwana biyu uwani ta murmuje ta saki jikinta tana dan fitowa falo ta xauna tare dasu Aryan,
Sai dai har lokacin bata qara sanya el’mustapha a idanunta ba wannan ya qara shigar da ita cikin wani hali.
Daga lokacin sai ta daina fitowa ko falon sannan ba inda take xuwa makaranta Ma ta daina xuwa, jiddah na damuwa da halin da uwani take ciki kuma tayi tambayar duniya tace mata ba komai sai ta xuba mata idanu.
Da dare suna tare da el’mustapha bayan sun gama komai na al’adarsu sun kwanta, matsawa tayi ta shige jikinsa sosai,
Ya matsota xuwa jikinsa yana fadin, jiddana ina jin barci sosai gashi gobe ina da tafiya tunda sassafe.
Murmushi tayi hade da Jan dogon hancinsa tana kallonsa, abinda kake tunani ba shi bane tunda ka maidani banda wani aiki sai akan wannan abin.
Shima murmushin yayi hade da hada hancinsa da nata yana gogawa a hankali, to menene jiddana?
‘Na rasa gane kan uwani kwana kinnan, bata da aiki sai kuka a koda yaushe, sannan bata fitowa tana daki xaune babu walwala a tare da ita, nayi tunanin bansan laifin me nayi mata kuma nasan bana tauyeta akan komai dake gidannan, ina tsoron kada wani abu yaje ya sameta shiyasa na gayama ko xan fadawa su hajiya ne su san halin da take ciki?
Ikon Allah, ya fada bayan ya tashi xaune yana kallonta,
Bata gayamaki meke damunta bane?
Nayi ta tambayarta tace ba komai, yauma ko da naje dakin tana kuka, Banan ta gayamin ta daina cin abinci sosai.
Yayi shiru yana tunanin, kafin yace kuma ke bakiyi mata komai ba, kinsan xaman tare yau da gobe dole anan samun sabani, meyiwuwa ke xaki iya mata wani abin da xai bata mata rai baki sani ba.
Wlhy banyi ba nayi tunani ban gane komai ba, nayi tambayarta ko Yusuf din tane duka tace aa am totally confused, pls help me out.
Gobe kije da ita asibiti, qila akwai abinda ke damunta ne batason fada, idan kuma babu ki sanarda iyayen ta da wuri.
Nima haka nayi tunanin cos abin yabani tsoro sosai.
Ki kwantar da hankalin ki kinsani bana son damuwar ki ko kadan, insha Allah komai xaixo da sauqi.
Allah yasa, ta fada tana qoqarin gyara kwanciyarta a qirjinsa.
‘Washe gari bayan ya fita office, su Aryan sun tafi makaranta, wanka tayi ta shirya tsaf cikin shirin fita asibiti da uwani.
Sai da ta nufi sashen masu aikinta tayi umarnin da abinda xasu dafa a gidan, kana ta nufi dakin uwani.
Photo ne manne a qirjin uwani tana kwance ta lumshe idanuwanta, ko kadan batayi xaton ganin jiddah a wannan lokacin ba illah motsinta da taji, da sauri ta tashi tana qoqarin boye photon hade da share hawayen fuskarta.
Good morning sister, yau fita xakuyi ne haka.
‘eh amma dake, xamuje asibiti ne a duba agani meke damunki.
Uwani ta dabirce, ni.. ni.. ‘Anty ba abinda ke damuna na gayamaki lafia na qalau,
Idan ba abinda ke damunki, menene dalilin canxawarki uwani? Idan ni da nake yar uwarki bansan damuwar kiba to waye kike so yasani, ko hajiya xan kira a waya ne ita ki gayamata.
Aa dan Allah kiyi haquri anty baxan qara ba, ta fada tana qoqarin share wasu hawaye a fuskarta.
Da alama damuwar ki nada nasaba da Yusuf ne, naganki da photo ina da tabbacin nasa ne, ya fasa auren ne kome, meya hada ki dashi.
Bugun xuciyar uwani ya tsananta, ta gyara xamanta tana kame kamen abinda xata fada, lura da yanayinta ya sanya jiddah xarginta tana kallon photon da uwani ta juya bayansa kamar ta sanshi, ta kauda xargin xuciyarta batare da sanin uwani ba ta shammaceta ta kwace pic din da sauri tana dubawa.
Wanda ta gani ya sanyata kallon uwani da tsananin mamaki hankalinta a tashe, yayin da numfashin uwani ya sarqe saboda tsananin tsoro.
Me kike yi da photon el’mustapha a qirjinki, menene alaqarki da wannan hoton uwani?
Tambayar da taji jiddah nayi mata ne ya sanya ta saki fitsari a inda take xaune batare da ta sani ba.
‘Anty kiyi haquri bada son raina bane, nima ban san yanda akayi ba, laifin xuciyata ne.
Laifin xuciyarki da tayi me uwani? Jiddah ta tambaya tana kallonta cikin rudewa, me kike nufi.
Photon dake hannun jiddah ya subulce ya fadi qasan tiles, me take ji a bakin uwani haka, idan mafarki takeyi Allah ya farkar da ita daga wannan mummunan barcin, uwani ke son el’mustapha din ta, mutumin da bata hada shi da kowa da komai ba, mutumin da batason ko wacce mace ta rabe sa, mutumin da take gani ita kadaice a xuciyarsa har qarshin rayuwarta, taya xata iya rayuwa dashi da wata mace, macen ma uwani yar uwarta, impossible, juyawa tayi ta fita jiri na neman kada ta, she can’t say anything for now amma uwani tayi mata baxata kuma ta cuceta idan har da gaske tana son el’mustapha.
Kallonta uwani keyi har lokacin da ta fice, tausayinta da dana sanin furta mata ya sanyata fargama amma ya xatayi tunda ta kamata dumu dumu da hotonsa a hannu meyiwuwa hakan xaisa ta amince mata ga auren mijinta.
Maida kanta tayi jikin pillow tana kuka sosai, bata iyayen ta takeyi ba yanda el’mustapha xai amince da auren ta shine matsalar, babu boka babu malami alqawari ne na daukar wa kaina ko ta halin qaqa sai na auri el’mustapha, sai ya xamo mallakina a gidannan, ta share hawayen fuskarta, ai ba dan mace daya akayi namiji ba, kowacce kissarta ta fiddata amma ina son el’mustapha kuma sai na rabi inuwarsa, ta share hawayen fuskarta hade da shigewa toilet.
Jiddah kuwa tunda ta shiga dakinta kanta ke mata wani irin nauyi, ta kasa gasgasta abinda kunnuwanta suka jiye mata a yau, uwani ke son mijinta, to ko uwani ta manta dangantakar su ne ta manta matsayinta na yayarta har take son kishi da ita.
Nan take ta fara tunanin take taken uwani akan el’mustapha tabbas biri yayi kama da mai, idan hakane uwani ta cuce ta batayi halin iyayenta na amana ba.
Yinin ranar gabaki daya a daki tayi sa ko abinci bata ci ba har lokacin da su Aryan suka dawo, su kansu sunsan mamin tasu tana cikin damuwa a yau duk surutun da suke mata shiru take a yau sai faman tunani, har lokacin da el’mustapha ya dawo.
Tunda ya shigo falonta yake kiran sunanta cikin muryarsa mai sanyi da dadin sauraro, tayi qoqarin sai ta xuciyarta kada ya gano tana cikin damuwa amma kallo daya yayi mata ya gano hakan a idanuwanta,
Da sassarfa ya isa gareta, ya dora hannunsa akan fuskarta yana kallonta sosai,
‘meke damun jiddana, meyasa idanunki sukayi ja haka.
Da kyar ta hadiye kukan ta haqe da qago murmushin da iya karsa lebbanta,
‘tun daxu nake fama da ciwon kai, dana sha maganine na sami barci inajin wannan daliline ya sanya sauyawar idanuna.
Allah ya baki lfy jiddana, gashi yau ina buqatar kulawar ki, ya xakiyi dani.
Dogon hancinsa taja tana dariya, abinda kake so shi xaa yi idan dai inada wannan iko, shima dariya yayi yayi gaba tana biye dashi a baya har dakin su,
Juyowa yayi yana kallonta, kinsan me Ibrahim yayi kuwa?
Ta girgixa kai tana kallonsa yayin da take qoqarin balle masa botiran rigarsa,
‘aure xai qara next week, har ya bada sadaki amma bada sanin matar sa ba hadixa.
Jiddah ta xaro idanu tana kallonsa, yayin da gabanta ya tsananta bugawa,
Story continues below
‘shi ibrahim din, amma meyasa xaiyiwa hadixa haka?
‘dole ne xai qara kin sani, shekara nawa babu haihuwa sai daga baya nan suka gane ba matsalarshi bace ita keda matsala, as his age ya kamata ace yana da yara yanxu kinga kuwa dole xai qara aure banga laifinsa ba.
Jin kalamansa taji kamar shine xai qara auren da uwani kukan da take dannewa batasan sanda ta fashe da kuka ba, kacokan ya juyo yana kallonta da tsananin mamaki,
Kuka jiddana, meyasa, bafa kece xaa yiwa kishiya ba kinsani, ibrahim nace fa,
She can’t control her tears batasan dalili ba sai xafi xuciyarta ke mata ta riqo hannunsa tana kallonsa,
Bana son kishiya el’mustapha ko wace iri ce, dan Allah kada kamin, ni kadai ce matar ka, ina son ka sosai.
Ya rungumeta sosai yana shafar bayanta cikin shigar rarrashi, namiji na qara aure ne bisa wani dalili nashi, bani da wani dalili da xai sanyani qara aure, bani da wata kalma da xan kare kaina a gaban Allah na rashin adalci tsakanin su, jiddah kadai nake so a rayuwata, jiddah kadai ce matata ba kuma wadda xanso bayanta sai ya’yana, ki cire wannan tunanin a xuciyarki kin sani bana son damuwarki kisa a xuciyarki ke kadaice matar el’mustapha kamar yanda UMMY take *Matar sadiq* ita kadai.
Dalilin wannan ya sanya jiddah cire damuwarta ta kula da mijinta sosai harta manta da wata uwani a gida.
Kwana biyu sosai uwani ta fuskanci canji daga jiddah, sakin fuskar da take mata ta daina babu walwala, hakan yasa jikin uwani yayi matuqar sanyi komai a gidan tanayinsa dar dar musamman masu aikin gidan ta daina takura masu ko yi masu fada akan komai.
Inda surry taje neman mafita bata samu ba kuwa illah fada da sukayi sosai domin bata goyon bayanta,
Jiddah kam ko aike ta daina saka uwani, a falo idan suka hadu sama sama take amsa gaisuwar uwani, sanda qawarta yasmeen taxo kai tsaye tace,
Hakane yasmeen, amma ni saboda iyayenta nake riqe da ita, ki duba irin halaccin da suka mini suka riqeni amana da dukiyata babu ha’inci, tun bansan kaina sosai ba nake tare dasu har sanda suka aurad dani ga abinda nake matuqar so a rayuwata, tsakanina da uwani babu banbanci a gurin su, sun bani amanar uwani tayi karatu a hannuna yanxu idan na maida masu ita ya xasuyi da karatunta daga kaduna xuwa abuja, xasu iya tunanin baxan iya riqe masu uwani bane tun suna raye banyi ba inaga basu raye, kinsan halin mutanen mu akwai mis_understanding,
Hakane na fahimce ki jiddah kiyi masu bayanin komai boye masu ba shine mafita ba gwanda susan abinda yar su ke shirin aikatawa, idan kuma baxaki iya ba ki tattarata ki maidata xama a hostel faqat🙅🏻♀
Bayan kwana biyu babu wani canji daga jiddah tsakaninta da uwani hakan ya sanya uwani kiran Banan,
Kije ki sanarda anty kin shigo dakina kin sameni a sume, kije mata a rude yanda xata gasgasta ki, idan kuma kikace qaryane banan kece mace ta farko a gidannan da xan wulaqanta duk ranar da naxamo matar gidannan.
Jin haka ya saka banan fita da sauri sai dai bata fahimci inda mgnr uwani ta dosa ba na xamanta matar gidan, tana shigowa falon jiddah taci karo da qaton foton el’mustapha sai da taji wani faduwar gaba, tsura masa ido tayi tana kallonsa cikin jin sanyi a xuciyarta ta kowace kusurwa.
Tunawa da kalaman uwani ya sanyata fadawa dakin jiddah.
Yanda jiddah taga banan na hawaye cikin rawar jiki tana fada mata halin da uwani take ciki ya sanya hankalin jiddah tashi,
‘Na shiga uku kada yarinyar mutane taxo ta mutu a hannuna, koda suka je uwani na kwance tsakiyar dakin ta sandare kamar da gaske, banan kuwa mamakin ta take da son sanin dalilinta nayin hakan.
Neman gaggawa jiddah taje ta nema ga security gidan, cikin mota aka sanyata suka nufi asibiti da ita,
Xuciyar jiddah a cunkushe tare da tunani da fargaba iri iri, har lokacin da Likitan ya kirata xuwa office dinta, da alama shima uwani ta hada kai dashine.
Patient din da kika kawo akwai damuwa a tare da ita mai tsanani, akwai abinda take so bata samu ba menene shi?
Dam xuciyar jiddah na buga ta dago tana kallon likitan hawaye shar a idanuwanta,
Da kyar tace mijina take so.
Mijinki take so? Ya tambayeta cikin tsananin mamaki alamar baisan da wannan xancen ba, jiddah ta gyada masa kai tana sharar hawaye,
Yace ke ba yayarta bace, nan Ma ta girgixa kanta,
Ok tor, abata abinda take so cos gab take da kamuwa da ciwon xuciya, kuma dalilin wannan xaku iya rasata a kowane hali.
Jikin jiddah ya dauki rawa, ta fashe da wani irin kuka sosai mai tsuma xuciyar mai saurare.