KE NAKESO
CHAPTER 1
YANAYIN MAIJIDDA… +
Ta dade a tsaye a wurin tana tunanin yanda har rayuwarta ta kawo wannan gaba, na farko dai ita ba kowan kowa ba, ita ‘yar talaka ce, ita ba kyaun dauke hankali gareta ba, ba kuma ilimi na fada a kara ba amma gashi a dalilinta ta hada sarkakiyar da ta rasa yanda zata yi ta warware shi. 1
Asali ma rayuwa tayi mata kunci tayi mata zafi, a wurin aiki ta rasa abun da yake mata dadi kowa ya juya mata baya, a gida iyayenta basu ko kula juna duk a dalilinta, sannan yanzu ga wannan!
Ita Maijidda yaya zatayi da rayuwarta ne?
Shekaru biyar da suka wuce idan akace zata tsinci kanta a halin da take ciki zata musa ko ma ta karyata, sai gashi hukunci daya da ta yanke a rayuwarta zabi guda da tayi ya dawo yana damunta, ko kadan bata danasani da zabin da tayi a wancan lokaci ko da za a MAIMAITA TARIHI hakan ne zai kasance zabinta yau ma domin kaf rayuwarta idan ta duba babu lokutan da tafi farin ciki irin shekarun nan da suka shude, haka kuma kawowan karshen su ne yasa ta rasa dukkan farin cikin ta gaba daya, duniyar ta mata zafi ta mata duhu bata da madogara.
Wani zazzafan hawaye ne ya kubce mata, nan tsakar falon Baba gwiwowinta suka sage ta zube a kasa.
Umma dake shanya a tsakar gida tana hangota ta kofar falon jikinta duk ya mace, tunani guda ne a ranta “Ya Allah ko yaushe Maijidda zata samu farin cikinta ya dawo gareta?” 2
FARKON LABARIN
16 SEPTEMBER 2006
Yana kallon wayar tana kara amma ya gagara dagawa, tunanin abun da zai fadawa danuwansa yakeyi, don ya san yanda sukayi dashi karo na karshe, amma ganin adadin missed calls din yasa ya daga gudun kar ya zarge shi.
“Assalamu alaikum” Abdul Ali ya fada a sanyaye. 6
“wa alaikumussalam warahmatullah, dole ka amsa kasa-kasa yanzu abun da kakeyi ya dace kenan?”
“Don Allah kayi hakuri bana kusa ne.”
“Good, yanzu kuma abun ya kaiga ka kira sunan Allah a jumla daya da karya ko?”
Abdul Ali ya runtse idanunsa yana tunanin abun fadi duk da ya kwana da sanin cewa babu abun fadi domin karyarsa ta kare, kuma ma wa zaiyi wa karyar?
Na farko dai duk duniya bayi da kaman Dr. Rayyan hatta Hajiyarsu da ya fi kusanci da ita bta sana abubuwa game da rayuwarsa ba kaman yanda Dr. Rayyan ya sani shine abokinsa kuma danuwansa mafi kusanci wanda yafi so duk duniya, duk da kasancewar shi ya biyoshi a haife basu ko fada irin ta yaya da kanin nan, saboda irin girman da Abdul Alin yake bashi a dalilin matsayin da Rayyan yake dashi a rayuwarsa.
Kaunace tsagwaronta ta dan uwantaka a tsakaninsu, wanda ya samu asali daga dattako irin na Rayyan da kuma HALIN GIRMA da ya mallaka. 2
“Kayi shiru kana jina”
“OKay, yi hakuri na amince I’ve been avoiding you”
“Dalili?”
“Kar ka min haka Dakta ka san dalili, amma in sha ALlah ending this month ina nan tafe, amma sai ka min alkawarin kaima idan nazo bazan koma ba sai ka samu mata kayi settling” 1
“Sai kazo ka sama min ai.” 1
“Ko baka fada ba, ina nan zuwa, nayi maganar ma da su Baba da Hajiya.”
“Muna sa idanu don naga alama kai kam idan mukayi kuskure kayi aure ta can to sai mun biya kudi mu ganka, mutum daga zuwa karatu sai ka kama ka share wuri kayi zamanka?”
“NIma kaina bana jin dadin zaman zan taho in sha ALlah.”
Nan dai ‘yan uwan junan suka sallame, Abdul Ali na kashe waya ya sauke ajiyar zuciya. Dole ya tsaida shawara guda, batun aikinsa, shin yana shirye da ya koma gida yanzu ko kuwa?
STORY CONTINUES BELOW
******** ********* ********
Hauwa Kabir (Mai-jidda), kamar yaddamutane suka fi saninta, haifaffiyar garin Hadeja ce, ita-ce ‘ya ta hudu a wurin iyayenta. 2
Malam Kabir da Umma Laraba. Sana’a ta kawo mahaifinta Dutse, wannan ya sa duk suka tashi anan cikin unguwar Limawa. Yayanta Hamza ma anan yake da matarsa Fauziyya.
Yarsu Maryam kuma Kano take aure, sai mai bi mata Abbakar, sai Mai-jidda da kuma kaninta Abdul Majid. Malam Kabir Dan kasuwa ne.
Kuma daidai gwargwado yana da rufin asirin sa, mutum ne mai gudun zuciya, hakanan ya kafu kan ganin yaran sa sun samu ingattacciyar tarbiyya daidai gwargwado.
Matansa biyu ne. Amma Allah ya yi wa amaryarsa rasuwa wurin haihuwa, ita da abin da ke cikin ta. Tun kuma lokacin bai sake karin aure ba, yana zaune da shi da Umma Laraba sai yaransa.
Ba abin da yake daga masa hankali, irin yaddamutune suka canza da shudewar ko wace zamani, hakan ya sa yake sa ido sosai kan yaran sa.
Yake kuma yawaita yi masu nasiha kan lamarin rayuwa. Wannan dalilin ne ya sa hankalinsa ya tashi da Mai-jidda ta zo masa da bukatar tafiya Kano, domin karo karatu, damuwarsa daya.
Ba aure ne da ita ba, ba kuma mai tsawata mata, don haka ya-ce. “Hauwa’u ba na ki karatunki bane, amma a ganina me zai hana ki shiga daya daga cikin makarantun garin nan, amma har sai kin tafi cikin Kano?”
Mai-jidda ta tsorata, ita damar ba fitowar sakamakon jarrabawarta bane abin tsoron yardar Baba kan tafiyar ta makarantar, shi ta fi ji. Ta rage murya ta-ce. “Baba don Allah ka yi hakuri, ko gidan Yaya Maryam sai na zauna, tunda suna kusa da makarantar.”
Baba ya kalleta ya-ce. “Maryam din zaman kanta take yi, za ki tattara ki jibgu masu a gida, idan ki ka takura su fa, ko ki ka dora masu wata dawainiya?”
Da haka dai ta yi shiru da wannan maganar, har sai da Yaya Maryam suka zo bikin sallah. Suna hira a dakin Umma ne. Maryam ta-ce.
“Oh ni Umma, haka za ki yi ta sa Mai-jidda a gaba ki na kallonta, sai habbaka take yi a dakinki”. 2
Mai-jidda ta tsume tana kunkuni. Yaya Abbakar ya-ce. “Karya aka yi, haka za ki yi ta zama, mates dinki wasu sun yi aure, wasu kuwa har sun fara karatu, amma ke ko nema ba kya yi.”
Mai-jidda ta narkar fuska ta-ce, “Ina so na nema, to amma Baba ya-ce wai ba zan tafi Kano ni kadai ba, tunda ban yi aure ba, na fada masa ga Yaya Maryam, wai shi ne ya-ce, ai ba zaman kanki ki ke yi ba.”
“To shi ne ba za ki yi waya ki fada min ba, ai sai na yiwa Baban su A’isha magana, ki zo ki yi zaman ki, don zuwa makaranta kuma abin da wataran zai kare.”
Nan take dadi ya cika zuciyar Mai-jidda fal! Hakan kuwa aka yi, sai da mijin Yaya Maryam ya sa baki a maganar, sannan Baba ya amince tare da jaddada masu cewa to amanar Hauwa’u ya ba su.
Su kula masa da ita. Tuni ta bada takardunta, domin a sake sa ta a cikin jerin masu neman gurbi a jami’ar ta Bayero, sai dai kuma sanda ta sake zana JAMB.
“Oh ni wannan zumudi haka, sai ka ce kanki a ka fara zuwa jami’a. Allah dai ya sa ayi wo abin kirki a can”.
“Hmm Umma, ai ba sai kin fada ba, ke dai ci-gaba da mika addu’arki daganan cikin ikon Allah, za ki ga mun gama da nasara”.
Umma ta yi murmushi tana kwashe shanyar dake kan igiya a tsakar gida, yayin da Mai-jidda ke ta faman hada jakarta.
Cikin karshen sati ta wuce Kano, bayan ta samu sunanta ya fito a cikin wadanda suka samu gurbi a shekarar bana.
Tana isa kai tsaye gidan Yaya Maryam ta wuce a Dorayi, sun yi farin cikin ganin juna, daki guda aka ware mata, inda za ta zauna ta yi karatunta a tsanake. Da dare ne ta fitar da tsarabar Umma, ta ba ta.
STORY CONTINUES BELOW
“Oh Umma dai ba ta gajiya, kwanan nan fa da Yaya Hamza zai zo, sai da ta ba shi sako wai a kawo mana.”
“In dai Umma ce, sai a hankali, zan taho sai kin ga soye-soyen cincin da su dakan yaji, nace mata Umma fa a gidan Yaya Maryam zan zauna, sai ta-ce, ai na kawo mu yi amfani da shi anan.”
Suka yi dariya cikin nishadi, nan A’isha ta shigo dakin ta-ce. “Anty Mai-jidda zan zo ki min kitso, kin fi Mamana iyawa”.
“Ki bar ta ta huta mana, ba ki ga yanzu ta zo bane? Kuma ki ka ce ta fi ni iyawa ko? Shi kenan, wataran za ki ce nai miki ai, za ki gani”.
“A’a Mama, ke ma ki yi hakuri, kin iya fa, na Anty Mai-jidda kawai baida zafi ne.” Yarinyar ta ba su dariya sosai.
Cikin wannan satin ta fara zuwa makaranta, bayan kwakwar da ta sha wurin yin (Register), idan ta dawo gida, sai bugewa da barcin gajiya, a hankali har ta saba da sintirin makarantar. 5
Har ta fara sabawa da abokan karatunta, kasancewarta mai faram-faram! Da jama’a, sannan ba ta boye abin da ke cikin ta, hakan ya sa jama’a da dama sun santa. 3
Sai dai duk faram-faram! Dinta, ba ta cika sakewa mutane har ta yi kawance mai zurfi da su ba, don haka ta sa kai a karatu sosai, tana fahimtar abin da ake masu a aji, sannan tana kara fahimtar abokan karatunta, tuni ta zabi abokananta, ta kuma san na watsarwa.
Duk sanda ta gama (Lectures), ba abinda yake zaunar da ita, da wuri take komawa gida, ta taya Yaya Maryam ayyukan gida da dare kuma ta zauna a daki, ta yi bi-tar karatunta.
A haka har ta kammala zangonta (Semester) na farko cikin nasara, suna yin hutu, ta tattara ta koma gida wajen Umman ta, a can ta cinye hutunta gaba daya.
Sai da aka koma makaranta ta dawo Kano, har Yaya Maryam tana mata tsiya. “Da har ki na Allah-Allah ki wuce, ga shi dai kin dawo, mun zama daya.”
“Yaya Maryam ba za ki gane bane, ba abin da ya kai gida dadi”. 2
“Eh, duk magana ki ke yi, ki yi aure dai ki gani, don ba ki da aure ne, ya sa ki ke wannan maganar, musamman idan ki ka auri wanda ba Dan garin ku ba”.
“Wai me ya yi zafi? Ni kam ai sai wanda zai ajiye ni kusa da Umma ta, zan aura”.
Yaya Maryam ta ce, “Tukun mu fara ganin saurayin ma mana, sannan a soma maganar aure. Mutane biyu suna biyowa ta wurina, amma kin ki bada kofa har kunya na ke ji, idan sun min tuni.”
“Yaya Maryam, duk ki rabu da su, ni yanzu karatuna na sa a gaba, idan lokacin da ya dace ya zo, ai zan kawo maku, sai dai ba yanzu bane wannan lokacin.”
Yaya Maryam ta kan yi dariya, ta rabu da ita, duk sanda suka yi wannan maganar, ita ta rasa menene alkiblar Mai-jidda? Mace kam ai duk inda ta kai, aure shi ne darajarta, amma sam Mai-jidda ba ta so ana mata wannan maganar.
Wataran Umma ta kan damu da tunanin wai ko aljani ya aure ta ne, tunda ba wanda ya taba ganinta da saurayi. 3
********
Kamar kullum yana fitowa daga gida zai wuce wurin aiki, yau ma ya ganta a tsaye tana jiran abin hawa, sai dai sabanin da, da yake wucewa idan ya ganta, yau fakawa ya yi a gefen titi, ya tsaya ya kare mata kallo tsab!
Tana da fuska mai tsawo da cikakken girar da ya kwanta sosai a saman matsakaita idanunta, abu guda da ya kan karawa fuskarta armashi, shi ne murmushinta a koda yaushe bai taba ganinta a tsume ba.
Tana da matsakaicin tsawo, sannan ba ta faye haske ba, amma akwai wani abu a tare da ita da ya kansa, idan ya kalleta baya jin ya dauke idanunsa, yawanci da hijabi ya fi ganinta, wasu lokutan kuma da abaya.
Yana cikin karewa wannan kyakkyawar halittar kallo ne, sai ga a daidaita sahu ya zo ya tsaya a gabanta, wucewar da zai yi kuwa, ya ga ba tanan, hakan ya sa ya tada motarsa cikin ajiyar zuciya, ya wuce wurin aiki.
“Mai-jidda don Allah ki daina yi wa bawan Allan nan haka, kullum sai ya nemi ki ba shi lokaci, amma ke sam baya gaban ki”.
Mai-jidda ta yi murmushi ta-ce. “Ki rabu da shi Mabruka, zai yi, ya gaji, na fada masa idan da gaske yake yi, to ya jira zuwa lokacin da na dibarwa kaina, amma idan sauri yake yi kuwa, ‘yan mata nawa ne a garin nan? Idan har zan fara kula mutum, to sai na kai aji uku Insha-Allahu, kafin nan na san na yi nisa a karatu, amma yanzu ban ko san tudun dafawa na ba, ina zan hada taura biyu a baki?”
Mabruka ta rufe (Handout) din da take dubawa ta-ce. “Ni dai ban san wani irin ra’ayi ki ke da shi ba haka, ina rokon Allah ya hadaki da wani Sarkin naci, wanda zai sace zuciyarki, tuni za ki manta wannan kalaman naki”.
“Hmm! Ban ga wannan ba, kin san yadda aka yi na samu Baba ya bari na taho karatun nan kuwa? Ai ba zan yarda wani abu ya katse min shi ba. Insha-Allahu.”
“Wasa ki ke yi, ba ki san meye so ba, duk za ki mance da wannan bayanin.”
Mai-jidda ta yi murmushi, ta kada kanta. “Ke dai mu bar maganar kawai, tashi mu shiga aji, ina ga (Next Lecturer) yanzu zai shigo.” Ta fada tare da duba agogon hannunta.
Mai-jidda ta dade ba ta ji Lecture din da yai mata dadi ba, ta fahimta irin na wannan ranar, saboda Malamin nan yana da ilimi, ya kuma san yadda zai bi da dalibansa, su so su ji me yake son fada masu, sannan su fahimci abin da ya fada din.
Dadin karawa, sai ya tabbatar da hankalin kowa na ajin, domin kuwa yanayi yana tambayar kowa game da darasin, koma ya ce ka yi bayanin wani abu kafin ya ci-gaba da koyarwar. Suna fitowa, kawarta Mabruka ta-ce “Kai gaskiya, Lecture din yau na daban ne.
Shi ne Lecturer din da aka ce zai fara mana, wanda duk jami’ar da ya je ya koyar na awa guda. Makudan kudi ake biyansa, sannan kuma ya fi zama a kasar waje. 2
Yanzu ne zai karbi koyarwa mai tsawo a jami’ar nan. Gaskiya ya hadu, kwata-kwata ance bai wuci shekaru talatin ba, zuwa da hudu ba, amma ki ga irin matsayin da ya kai, yanzu haka ma fa Doctor ne”.
Mai-jidda tana ta ji Mabruka, sai kwararo bayani take yi. “Ke kuma a ina ki ka samu tarihin rayuwarsa?”
“Cab! Ai don ba kya hira da su Auwal ne, su suke fada, ranar na ji, sai dai sai yau na gan shi ni ma.”
Mai-jidda ta yi murmushi, tabbas ta yarda da maganar kawarta, mutumin ya san me yake yi. Duk lokacin da ya shigo ajin, yana lura da ita, ba ta taba ba shi amsa ba ko kuwa ta yi tambaya a ajin, sai dai duk abin da ya fada, idan ta gama saurare sai ta rubuta. Gaba ki daya ‘yan matan ajin kowa ribibi take yi ya san da ita, amma banda wannan. Hakan ya sa ranar ya ba su (Assignment), ya kuma raba su gida-gida, kowane (Group) za su yi (Presenting) na su. Don haka da (Group) din su Mai-jidda suka zo yi. +
Ya duba ya ga su biyu ne mata a (Group) din, don haka ya nuna ta ya-ce ita za ta yi (Presenting) nasu aikin. Abin ya bawa Mai-jidda mamaki, ganin ita ba ta wani yin shisshigi a ajin. Yaya aka yi ma ya san sunan ta? 5
Da yake ta saba da duka ‘yan ajin, ba ta ji wani dardar! Ba, ta hau bayanin nasu aikin cikin murya mai taushi da gamsarwa a cikin turanci wadatacciya.
Tabbas! Ta burge kowa, yadda ta bada gamsasshen bayani, amma ba wanda ta fi burgewa irin Malamin na su, don haka sun samu maki cikkake.
Dr. Rayyan Sani, ya samu kansa a yanayin da bai taba samun kansa ba na damuwa da al’amarin dalibarsa guda, muddin ya koyar yaga ba ta yi tambaya ba, sai ya ji ko dai ba ta fahimci darasin bane, amma a hankali ya nemi share fagen Hauwa Kabir daga zuciyarsa da tunaninsa, saboda a ka’idar sa, babu hada sha’anin koyarwa da wani AL’AMARI na ZUCCI. 10
Bayan sun fito daga wani gwaji ne. Mai-jidda ta wuce wurin cin abinci da kawarta Mabruka, suna tafe suna hira kan gwajin da suka gama yi yanzu.
Suna shiga, suka fadi abin da suke so, wurin bai cika da jama’a sosai ba, sai dai teburin gefensu akwai mutum daya da yake zaune, ya ba su baya. Ba su ma kula da shi ba, sun fara cin abinci ne. Mabruka ta-ce.
“Don Allah ki bawa Hafiz lokacin ki, ni fa kun sani a tsakiya, wannan ya gwarani ta can, wancan ya matsa min tanan. Yanzu kam dai koma menene, ai kin san ba za ki yi wasa da karatunki ba, shi fa da gaske yake yi”.
Mai-jidda ta yi murmushi ta-ce. “Ni fa ki na ba ni dariya, ban san sau nawa zan fada miki ba, ba Hafiz ba, ko ma waye ne, ba ni da lokacinsa yanzu, saboda ina da kayadajjen lokaci. So, idan zai iya jira, ya jira”.
“Ni kam Allah ya sa Baba ya-ce ki fidda miji, muna komawa gida, na ga ta wannan ka’idar ta ki. Gaskiyar Umma ce da ta-ce ko sai an hada da rukiyya ne. Ki ga yadda Hafiz ya hadu, ga kudi ga kyau, ‘yan mata Rushing suke a kansa, amma ya dage sai ke, ke kuma baya ma gaban ki sam”.
“Hmm Mabruka, na ba ki shi kyauta”. 1
Saura kadan ya yi dariya da ya ji ta fadi haka, ya kurbi abin shan shi ba tare da ya tanka ba.
Mabruka ta-ce. “Ai ke ma don kin san ke ya-ce yake so, idan ba haka ba, ba wani bata lokaci. Ke akwai ma wanda yake burge ki kuwa ma a duniya. Kin ga Dr. kowa na rubibin sa, wasu har ba su rasa Lakcan sa don kawai su ganshi, ke kuwa ko a jikin ki, ban taba ji ko hirar sa ma ki na yi ba”. 4
“Akan me ya sa zan yi hirarsa, tsakani na da shi koyarwa, ya koyar da ni, na dau darasi, shi kenan. Kun tsaya ku na batawa kanku lokaci, ni ban ga meye abin rawar jiki ba anan. Yes, yana da kyau, yana da ilimi, and so what?” 3
Murmushi ya yi da ya ji wannan gaba ta hirar ta su. Mai-jidda ta ci-gaba da cewa. “Hala ma yana da matar da yake matukar so, take son shi, kun tsaya ku na kalle mata miji, ku na kus-kus! A kansa. Idan zai dauka a cikin duk masu son sa, wa zai dauka, wa zai bari? So bata lokacinku ku ke yi…”
STORY CONTINUES BELOW
Mabruka ta yi saurin taba Mai-jidda, amma sai da ta ci-gaba. “Sannan ki na ganin yadda yake wani shan kamshi, yana magana da kyar, kamar a turai aka haife shi, ni ban ga abin burgewan…” 10
Ganin sa ta yi a gabanta kawai ya zura hannaye cikin aljifayen wandon sa, kafafun sa sake da Loafers masu laushi. 16
Ta hadiye wani abu makut a wuyanta, hankalinta ya tashi, nan take kwakwalwarta ta faro tariyo abin da ta fada akan sa, ta ji ko ta kwafsa, amma ina kwakwalwarta ta daina tunani. Murmushi ya yi, maimakon ya hau ta da fada, ya ja kujerar gefenta, ya zauna. 3
“Hauwa’u right?”
“Malam, ka yi hakuri, ban yi niyyar… I’am so sorry!” Ta mike ta dau jakarta za ta bar tebur din, amma kallo ya bi-ta da shi ya-ce, “Zauna, mu yi magana”. 1
Yau ta shiga uku, shi kenan zai sa a koreta a makarantar, tunda da kunnensa ya ji tana kushe shi. A sanyaye ta zauna. “Ina saurarenki?”
“Malam…”
“Ga ki, gani. Just tell me, fada min duka aibuna, kin san Dan-Adam ajizi ne, amma ina son mutum mai fadin gaskiya komai rintsi, so, fada min menene abinda ba kya so a tare da ni?” Mai-jidda ta dubi Mabruka, ta saukar da kanta kasa, sannan ta-ce.
“Ni ba abinda ya shafe ni da rayuwarka, duk abin da ka ke so, za ka iya yi rayuwarka ce, don haka, kayi min afuwa, idan na bata maka rai da wani furuci na”.
Ta mike ta bar tebur din. Mabruka ta bi bayanta da sauri. “Yau mun shiga uku, kin ga abin da ki ka jawo mana ko? Me ya kai ki cewa baya burgeki, ya faye jiji da kai? Yanzu yaya za mu yi? Ga shi ya san sunan ki.” 4
“Ba abin da zai yi, ki rabu da shi.”
Mabruka tayi mata kallon ba ta ma san me take yi ba.
Suna fita, ya bi-ta da kallo. He liked the girl, tana matukar burge shi. Ranar dai duk yadda ya so ya hana zuciyarsa, tare da tunanin Hauwa Kabir ya kwana a ransa. 3
Daga ranar Mai-jidda ta kara shiga taitayinta, ba ta yarda ta yi maganar wani Malami a ko ina, sannan idan Dr. Rayyan ya shigo aji, ta daina ko dago kanta ne, saboda sai ya yi ta mata wani kallo na tuhuma, tamkar tayi masa wani gagarumin laifi. 4
********
Yau kam ya rigata fitowa, a wurinsa na kullum ya tsaya, har ya ga fitowarta, yau kamar da damuwa a fuskarta, ko don saboda ta yi latti ko kuwa saboda jarrabawar da suka fara, ji ya yi tamkar ya je ya cire mata damuwar ya dawo mata da murmushinta na kullum. 3
Nan ya ji wani abu ya kulle a zuciyarsa. Ji yake yi tamkar ya fasa tafiyar nan, amma kuma ya zama dole, tunda zai yi (Reporting) a sabon wurin aikinsa, ya so kwarai yayi mata magana game da abin da yake ji game da ita, amma ba ya so yayi mata katsalandan a karatunta. 13
Don haka yau ma ba tare da ya-ce komai ba, yana gani ta shiga abin hawa ta tafi, ba tare da ya san sunanta ba, haka ba tare da ya san gidan su ba.
Tana kallon mai motar nan ya tayar ya tafi, ta yi ajiyar zuciya, don wannan karo na hudu kenan da ta kula da shi, da farko ta zaci kawai hanya ce ke hada su, amma sai ta kula kullum sai ta hango shi a zaune a motar. 5
Da zarar ta shiga abin hawa sai ta ga ya tafi. Amma tunda bai taba mata magana ba, ba ta damu ba, sannan ko fuskar shi ba ta taba gani ba, ita dai ta san anan kullum take samun motar sa.
Wataran kuma sai ta fito yake fitowa. Wataran ta kan ji kamar ta same shi ta tambaye shi me ya sa yake bin ta? Amma kuma ta ga rashin dacewar hakan, idan ya zamanto wani abu ne daban, ba ita yake bi ba.
Suna duba wani darasi ne. Auwal ya-ce. “Mai-jidda ni ban tambayeki ba, ko kin samu waya?.”
Ta dube shi a cikin rashin fahimta “Waya kuma Auwal?”
STORY CONTINUES BELOW
“Eh, ranar wani mutumi ya zo nan nemanki, ya samu za mu shiga aji, ke ya nuna. Ni kuma ganin sa a tsanake, ya sa na fada masa sunanki, na kuma ba shi lambar wayarki ma”.
“Mabruka, idan nace miki me ya sa ki ke kula su Auwal, sai ki ce yana da hankali da son karatu, yanzu idan banda kai Auwal. Yaya za ka bawa kowa lambar wayata, bayan ya nuna maka ban san shi ba, asali ma kai ka fada masa sunana?”
“To yanzu dai ki kwantar da hankalinki, tunda bai kiraki ba.”
“Gaskiya kar ka sake min haka Auwal, ba na so.”
Mabruka tana kunshe da dariya, suka yi ido da Auwal. Sannan suka shiga aji.
***********
Suna zaune a gindin bishiya, tana bitar takardarta na jarrabawar da za su shiga zanawa, wanda kuma shi ne na karshe a wannan zango, daga shi sai kuma aji biyu, sai ga Auwal ya nufi inda suke zaune, ita da Mabruka da wasu (Course mates) din su. Ita ya nufa ya-ce.
“Hauwa idan kin fito wannan jarrabawar. Dr. Rayyan na nemanki a ofis dinsa”. Sai da ta ji wani ras! Yau ita kuma me ya hada ta da shi, da zai aika ta je? To ko dai ta yi wani shirme ne a jarrabawarta? Kai me ya sa zai fada mata, idan ma ta yi shirmen?
Ita kadai dai sakawa take yi tana kwancewa, da kyar ta natsu, ta zana wannan jarrabawar. Mabruka ta roka suka je tare. Hannunta na rawa, ta bude ofis din ta shiga. Kansa na kasa yana nazarin wani abu, ta shigo ta gaishe shi, ya nuna masu wurin zama ya-ce, su zauna.
“Yaya jarrabawar dai?” Ya tambaya yana duban Mai-jidda.
“Alhamdulillahi! Mun gama yau.”
“To ya yi kyau, tunda kun gama yau, ba shigowa makaranta kenan?”
Mai-jidda ta fara jin haushin tambayoyinsa, me zai kawo su to tunda ba a komai.
“Sai dai idan ka na so ka ci-gaba da Lectures, za mu iya shigowa.”
Ya yi murmushi ya-ce. “Wata alfarma na ke nema, tunda ba kya makaranta da fatan za a ba ni?”
Mabruka ta dubeta hade da zare idanu, ta dan taba kawarta, alamar ta amince su ji meye ne. “Allah ya sa zan iya.”
“Lambar wayarki na ke so, sannan kuma da sunan unguwarku, ina da magana da mahaifinki”.
Da sauri ta dago idanu tana dubansa cikin tsoro ta-ce. Shi kenan ta fadi jarrabawarta. To amma fa ta dage. Yaya aka yi haka? “Malam ai ba a garin nan yake ba.”
“A ina yake?”
“Yana Dutse, amma don Allah duk abin da ka ke da niyyar fada masa, ka yi hakuri kar ka fada. Idan ni ce da kuskure, zan gyara, kar ka bari ya sani”. Ta fada a sanyaye.
“Kar ki damu, rubuta min address din anan da kuma lambar, idan har kin amince, ba laifinki zan fada masa ba.” Da sauri ta rubuta masa, tun kan ya canza ra’ayinsa, ya fadi aibunta gun Baba. 2
“Shi kenan?”
“Idan ban gane ba, zan kiraki a waya ki fada min.”
Kai kawai ta daga masa ta-ce. “Sai anjima.”
Ta tashi suka fita, suna fita. Mabruka ta maketa a kafada, tana wani murna kamar an mata albishir da kujerar Hajji. “Me ye haka? Ke dadi ma ki ke ji wannan mutumin zai kai karana gida, ki na wani murna ko? baki san yanda zan kare ba a hannun Baba.” 4
“Oh, Allah! Wataran kamar na ba ki aron kwakwalwata na ke ji, ke yanzu ba ki gane komai ba?” 10
“Me kuma zan gane, bayan ke muguwa ce, ki na farin ciki da damuwata”. Mabruka ta-ce. “Kawata Dr. Rayyan ba karar ki zai kai ba, zai je gidan ku ne, saboda ke, saboda yana son ki”.
STORY CONTINUES BELOW
Anan Mai-jidda ta tsaya cak! Sai kuma ta yi wani tunanin, ta-ce. “Kawai don mutum ya karbi lambar waya, ba shi bane yake nufin yana so-na, kuma ni na fada miki ba zan kula kowa ba, sai nan da shekara biyu Insha-Allahu”.
Murmushi Mabruka ta yi cikin jin dadi ta-ce. “Mai-jidda and Dakta, wai I can’t wait. Tsaya ma tukun, wai me ya sa duk hadaddun mazan nan ke kadai suke so, zan raba gari dake, ko ni ma wani zai ganni ya taya”. 4
Mai-jidda ta san halin Mabruka kwarai da zolaya ta-ce. “Kya ji da shi ai, idan dai maza ne.”
Ba ta sake tunanin Dr Rayyan ba, ta wuce gidan Yaya Maryam, ranar murna ba ya ita, ta ji wani sayau a ranta, kasancewar ta gama jarabawarta.
Damuwarta daya a wannan safiyar, da ma wanda ta shude, ba ta ga motar nan da take yawan gani ba, idan ta zo tafiya makaranta. Don haka ta yi fatan komai lafiya. 5
Bayan kwana biyu ta wuce Dutse, tana Allah-Allah ta ga Ummanta, don wannan (Semester) din sau uku kawai ta zo gida. Ba ta wani tsaya hutawa ba, ta bazama gaisuwar ‘yan-uwa, ta dawo gida.
*********
Wata ranar Juma’a da yamma ne ta same shi a kofar gidan su. Tsayawa ta yi cak! Kamar ta ruga da gudu ta koma inda ta fito, to amma me zai sa ta gudu?
Tunda wajen Baba ya zo, iyaka ta gaishe shi, ta wuce cikin gida, ya yi abin da ya kawo shi, ya tafi shi kuma. A tsanake cikin kula ta karasa inda yake.
“Sannu da zuwa.” Ta fada a sanyaye, don zuciyarta na ta mata tsalle. “Yaya aka yi ka gane, ba ka kira wayata ba?”
“Ba wuyar ganewa. Yaya hutu?”
“Lafiya kalau, ka shigo ciki mana, ko ba ka yi sallama bane?”
“Ban samu kowa bane, shi ya sa.” Hala ya dade a tsaye anan, sai ta ji wani iri gaba daya. Ta shigar da shi falon Baba, ta wuce cikin gida ta samo masa abinci da ruwa mai sanyi, kafin ta aika yaro ya sayo mata drinks a shagon kofar gidan su.
Ta kawo masa komai, sannan ta yiwa Umma magana ta-ce. “Umma Malamin makarantar mu ne ya zo ganin Baba, kuma bai dawo ba tukun, ko za ku gaisa?”
“To, ayya ina ga bai san yana tafe ba ko? Amma kuwa ya kusa dawowa, ya dai jira shi”.
Mai-jidda ta koma falon ta same shi. “Ka yi hakuri fa, Baban ya kusa dawowa yanzu, sai ka same shi.”
Ta dan yi shiru tana tunanin abin da ke ranta kafin ta-ce. “Amma dai ka tuna maganar da muka yi da kai a makaranta ko?”
“Hauwa kenan, na tuna, ki kwantar da hanakalinki, wani abu daban zan tattauna da Baba, ina fatan ba za ki damu ba?”
Ta yi wani ajiyar zuciya, sannan ta-ce. “Ba komai, bari na gwada wayarsa na ji.”
Tana kokarin danna wayar ne, sai ga sallamar Baba a falon. Tayi masa sannu da zuwa, sannan ta kawo masa ruwa, ta samu suna gaisawa da Dr. Rayyan.
Bayan sun gama ta-ce. “Baba wannan Dr. Rayyan ne. Malamin mu a makaranta, ya-ce ya zo wurin ka ne, yanzu ma da zan kira ka a waya.”
“Ayya, sannu da zuwa. Yaya hidima da fama da Dalibai?”
“Alhamdulillahi! Yallabai, sai godiya”.
Mai-jidda ta mike ta koma cikin gida, kamar ta labe ta ji me Dokta zai hada shi da Babanta. Amma ta yi tunanin rashin dacewar hakan, don haka ta yi wucewarta daki.
Can Abdulmajid ya kirata, wai ta je falo bakon zai tafi, ta samu Baba ya fita a falon, don haka ta-ce. “Har kun gama maganar?”
Murmushi ya yi ya-ce. “Eh, kuma Alhamdulillahi na samu abin da ya kawoni”. 1
STORY CONTINUES BELOW
Ta dube shi a tsarge cikin rashin fahimta. “Baba ya yi min izinin na nemi aurenki, da fatan zan samu kofa a wajenki?” 14
Mai-jidda sai da ta ji kamar an naushi cikinta, yayin da take koshe dam! Saura kiris! Ta saki fitsari don razana. 1
“Malam, aure kuma… Ni?” Ta rasa me daya take ji, bacin rai ne ko razana ko kuma haushi?
“Kwarai kuwa, akwai wata matsala ce?”
Matsala yake tambayarta? Kwarai kuwa akwai babbar matsala.
“Kawai dai na ga, kai Malamina ne, kuma ina karatu, yanzu kuma …”
“Wannan ba hujja bace, na gan ki, kuma na yaba da halin ki, da na tambayi Baba izinin neman aurenki kuma bai sanar da ni cewa ba yanzu zai miki aure ba, saboda haka idan ki na da wata hujja, ina saurare?” 9
Ranta bai mata dadi ba, akan me zai zo kai tsaye wurin Baba? Wato daureta yaso yayi don kar ta masa gardama.
“Tunanin me kikeyi? A tunani na haka addini ya koyar mana ko kuma kin fi so na fara zuwa ta gunki tukun?” 5
Taji mamakin yanda ya karato damuwarta amma yafi ta gaskiya don haka murmushi Mai-jidda ta yi ta rufe idanu, cikin jin kunya, daganan Dr. Rayyan Sani ya san shi zai yi nasarar saye zuciyar Mai-jidda. Sun yi sallama da cewar sai ta ji daga gare shi.
*******
A daidai wannan lokacin ta fara samun wayar. Mai-jidda ta manta fedes da batun Auwal, tana gidan Yaya Hamza aka bugo, bakuwar lamba ta gani. Ba ta cika son daukar lambar da ba ta da ita ba, amma gudun kar abin kila yana da muhimmanci yasa ta daga. “Hello.”
“Assalamu-alaikum”.
“Wa’alaikumus-Salam.” Rashin dago muryar ya sa ta-ce. “Wa ke magana don Allah?”
shiru
“Da Hauwa na ke magana?”
“Eh ita-ce. Sai dai kai ban gane waye bane?”
shiru
“Wani bawan Allah ne, na samu lambarki a cikin makaranta wurin abokan karatunki, da fatan ba za ki damu ba?” 1
Nan da nan Maijidda ta zabura ta zauna, wato wannan ne mutumin ko? Nan da nan taji fushi ya taso mata. “Gaskiya ban ji dadin yadda ka bi abokan karatuna, ka amshi lamba ta ba.”
Shiru taji kamar mai shi bazai amsata ba. Kafin taji muryarsa “Ayi mun afuwa, amma na ga ya dace mu yi magana ne, ni kuma ba na son samunki a bakin titi, wannan ya sa na karbi lambarki, don ki ban address, sai na zo gida mu tattauna”.
“Ni ba a zuwa gidan mu.”
Murmushi ya yi mai sauti ya-ce. “Saboda me ba a zuwa gidanku?”
“Don Allah, ka yi hakuri, ba na son mu batawa kanmu lokaci, domin akwai wanda na ke gani yanzu.”
Ransa yayi masa nauyi da jin batun ta, amma ya-ce. “It’s not fair, ko dama fa ba ki ba ni ba, za ki sallameni”.
“Tukun ma a ina ka sanni? Yaya zan ba ka dama, bayan ban san ko kai waye ba?”
Murmushi ya sake yi “Yaya za ki san ni waye, bayan ba ki ba ni dama ba?”
Maijidda ta juya idanunta wannan ya faye bakin naci. “To shi kenan, na ji. Ni ba a Kano na ke da zama ba”.
“A ina ki ke, ni zan zo duk inda ki ke a fadin duniyar nan.”
Ya ba ta dariya, wannan mutumin wani majnuni ne kawai. “Sai anjima”. Ta fada hade da kashe wayarta.
Anty Fauziyya ta-ce “Mai-jidda ke da waye haka?”
Tana datse wayarne tace “Ke dai rabu da shi, wani ne kawai ya bi-ni makaranta ya amshi wayata a hannun abokan karatuna, tun lokacin bai kira ba, sai yanzu kawai wai shi a dole yana so ya zo na san shi, zan ba shi dama.”
Anty Fauziyya ta yi dariya. “To ki ba shi damar mana?”
“A’a ni da na fara kula Dakta, kuma wane dama zan ba shi, ni ba na son tara samari Wallahi”. 17
“To sai ki fada masa ya hakura ai ko”. Daukan kaskon turaren wuta tayi da zimman kunnawa.
“Na fada masa ina tare da wani. Ki rabu da shi kawai”.
Nan suka shiga wata hirar, ta manta fedes da batun mai waya. 9
*********
A wannan hutun sau uku Dr. Rayyan yana zuwa, kafin a koma makaranta kuwa Mai-jidda ta yi nisa, ba ta da zance sai na Dokta, har dai Yaya Maryam ta-ce “Barka kanwata da lafiyarki, dama Dakta kawai ki ke jira.”
“Yaya Maryam, ni dai ina sauraron sa ne zuwa mu ga abin da hali zai yi.”
“Ahaf, tunda ki ka sa kai, ai shi kenan, anyi an gama, in-ji mai kashi a gado.”
Ba wanda ta fadawa a cikin kawayenta yadda suka yi da Dakta. Sai Mabruka, nan ma ta isheta da bin diddigin abin da ya faru da ya je ganin Baba ne.
Idan ya shiga aji kamar bai santa ba, haka zai koyar ya fita, ita ma idan ta tashi kamar ba ta san shi ba, ba ta zuwa ko ofis dinsa, sai dai ana komawa gida, za ka same su makale da juna. 3
*******
Tana dakin Umma aka sake mata waya. “Hauwa kenan, kuma shi kenan sai ki ka manta da ni, bayan ina jira ki waiwaiyeni.”
Ta gane muryar sarai, don ba irin muryar da za ka manta bane, murmushi ta yi ta-ce “Hmm! Na dauka mun gama wannan maganar da kai ai?”
“To, yaya mutanen gida?”
“Lafiya kalau.”
“Ni fa da gaske na ke miki, son ki na ke yi, kuma ina matukar bukatar ganinki, domin mu yi magana ta gaske, ke kuma ko gidanku, kin ki ki min kwatance.”
“Don Allah bawan Allah ka yi min afuwa, amma a ina ka sanni?”
“Kullum da safe, idan za ki wuce makaranta, na kan gan ki a bakin titi za ki hau abin hawa, tun daga lokacin na ji zuciyata tayi min na’am da ke, wannan ya sa na kasa hakuri har sai da na biki cikin School ranar”. 4
Gaban Mai-jidda ya fadi, yau ta hadu da gamonta, wato shi ne dai mutumin nan, mai mota da take gani. Ita yake bi wato?
“Bi-na ka ke yi?”
“Raina ya gan ki, kuma KE NA KE SO, ba zan iya hakura ba, hakan ya sa na dau wannan matakin, ki yi wa zuciyata adalci, ta samu ganinki, ko za ta huta da dawainiyar da ki ke yi da ita”. 8
Wannan mutumin ya yi kwas, ko sunansa ba ta sani ba, amma ya fara sawa tana ji tamkar ta san shi.
“Ka yi hakuri Malam, abu ne da ba zai yiwu ba.”
“Ni ban taba ganin mai saurin karaya ba irin ki.”
“Ni ce na karaya? Ni ban karaya ba, kawai dai tsoro ka ke ba ni.” Ta fada masa abin da ke cikin ranta.
Murmushi ya yi ya-ce. “Ki daina tsorona, ni Dan cikin Kano ne, ko yau ki ke so, ki aika ayi miki bincike a kaina.” Maganar babba ce kenan. Mai-jidda ta fada a ranta.
“Sai anjima”. Ta fada hade da kashe wayar.
Amma wannan bai sa Dan Kano ya bar kiranta ba, a haka har ta fahimci cewa bai da mata sannan, ta fahimci shi mutum ne da ya lakanci asalin soyayya. Don idan yana mata magana hatta tsigar jikinta tashi yake yi, hakan ya sa ta san cewa shi ba abokin yinta bane. 2
Saboda a bangare guda, ta san Dakta tana son shi, yana da addini, ta yarda da aqidarsa, sannan kuma ta san komai game da shi. Don dai Dan Kano, ba abin da ta sani game da shi, sai garin da ya fito da kuma cewa baida mata, sai kuma iya soyayyarsa, don dai ko sunan sa ya ki ya fada mata, wai sai ta yarda ya zo Dutse. Ita kuma ta-ce babu wannan ranar.
Yau dai ya kamata na ga Hauwa, da fatan dai ba ta kasa yadda ake ta fada ba”. Abdul-Aali ya fada yayin da ya zauna a kujerar falon Dan-uwansa Rayyan. 3
“You won’t be disappointed, wai me ya sa ka damu ka ganta ne?”
“Saboda ina son na ga macen da ta narka zuciyar Dan-uwana. She melted the ice. Wa yake zaton Dr. Rayyan zai so wani abu, bayan littafansa?”
“Abdul-Aali ba ka da kyau, kai sai yaushe za ka kai ni?”
Abdul-Aali yayi shiru, yana murmushi ya-ce. “Tun zuwana, ba mu hadu ba, amma ina tunanin zuwa, kar ka damu zan neme ka”. 1
Dariya Rayyan ya yi, “Kaman da gaske, ni inaga da wa kai su Hajiya suka matsawa lambar ma.”
“A dai faro daga saman zai fi”
***********
Watannin su uku da soma wannan tafiyar. Rayyan ya aika aka yi masa tambayar auren Mai-jidda. Wanda ba su san da neman ba, sai da abin ya ba su mamaki, wai Mai-jidda ce za ta yi aure.
Wannan ya sa Mai-jidda ta kira Dan Kano. “Maganar gaskiya na ke fada maka, ka daina kirata a waya. Allah aure zan yi.” 1
“Me ya sa ki ke min haka Hauwa, ko ganinki kin haramta min, yanzu ina fama da wannan, za ki dauko magana mai daci irin haka ki fada min?”
“Da gaske nake, ka yi hakuri, na yi ta kokarin fada maka hakan, kai ne ka ki fahimta. Amma Insha-Allahu Allah zai hada ka da rabonka, wacce za ta so ka kamar yadda ka ke so-na, domin ni kam na samu wanda na ke so.”
“It hurts Hauwa, ki daina fada. Allah ya ba ki sa’a a rayuwa, amma ni ba zan daina sonki ba, har karshen rayuwata.” 5
Sai da ta ji tausayinsa ya kamata.
“Yau ma ba za ka fada min sunanka ba?” 2
“Mai sonki.” Ya fada, sannan ya kashe wayar, ta duba tana girgiza kanta. 3
Washegari Rayyan da Abdul-Aali suka nufi Dutse ganin matar da Dan-uwansa, kuma abokinsa zai aura. “Gidan Yayanta za mu sameta, iyayenta suna Limawa”.
“Yaushe ku ke shirin sa ranar bikin na ku? Saboda na san shirye-shiryen da zan yi, ka san wurin aikin namu sai a hankali.” Abdul-Aali ya tambaya.
“Kar ka damu, na isa na yi aure, ba Dan-uwana? Idan ka na so ma ka zabi Date shi kenan?”
Abdul-Aali ya-ce. “To ba damuwa, mu je dai na ga ko ta dace da Dan-uwana tukuna.” 3
*****
Mai-jidda na kammala aji biyu aka daura aurenta da Dr Rayyan’u Sani, ba wata hidima aka yi sosai ba baya ga Fatiha da aka shafa. Dokta ya hada liyafa wa abokansa, yayin da Umma da Baba suka yi iyaka kokarin su wajen yi wa ‘yarsu gatan da ya dace. 2
Mabruka ta-ce. “Ikon Allah, yau dai Allah ya nuna mana, idan anyi magana ni sai na yi aji uku na yi aure, ni ba zan bawa kowa kofa ba, ni na so Dokta?
STORY CONTINUES BELOW
Ke ma kin san baya gaba na. Ga shi dai karshen tikatiki tik! Allah ya nuna mana. Allah ya ba ku zaman lafiya da zuri’a dayyaba.”
“Ameen, Allah ya kawo mana na ku mu gani”.
“Bayan duk kin kwace kyawawan.” Mabruka ta fada cikin zolaya.
“Ai na bar miki Hafiz”. Suka yi dariya, can da yamma Yaya Maryam ta sa aka kara sharewa Mai-jidda gidanta aka goge tsab! Sannan ta ta sa keyarsu, duk suka tafi suka bar amarya a gidanta.
Ranar ba wanda ya kai Rayyan farin ciki, saboda ya cimma burinsa na ganin Mai-jidda a gidansa a matsayin matarsa. Ango dai ya shigo gidan shi cike da son matarsa, don haka bai jira komai ba, ya angwance. 7
Rayuwarsu gwanin sha’awa, ba abin da Mai-jidda take muradi irin ta ganta a gefen Rayyan dinta, wasu lokutan ya kan yi tafiya, domin koyarwa a wasu makarantun a matsayin (Visiting Lecturer).
Haka take wuni ta kwana sukuku! Idan shirun yai mata yawa, ta kira shi su yi hirarsu. Wasu lokutan kuma idan karatu ya sha kanta ma ba ta da lokacin yin hirar.
Wasu lokutan yana tafiya take komawa gidansu, ta yi zamanta, haka Mama (Hajiya Zainab) za ta yi ta zuba mata gata iri iri, ba dama ta tashi za ta yi wani gyara a dakin Mama.
Sai ta-ce a’a ta huta, ita da take da karatu sosai. Yaran gidan su Rayyan duk suna boko sosai, duk da dai mahaifinsu bai yi wani zurfi ba a bokon, amma bai hana ya ga ya tsaya yaransa sun yi karatu ba. 2
Rayyan shi ne babba a gidan, kowa Yaya Rayyan yake ce masa, sai Abdul-Aali, Mukhtar ke bin bayan Abdul-Aali, sai dai akwai tazara tsakanin su, ba kamar tsakanin sa da Rayyan ba. Shi Mukhtaar Likita ne.
Sai kanwarsu Suwaiba ita kuma English ta karanta tana aure a Kaduna. Kannen su biyu kuma Sulaiman da Kasim suna babban aji a Sakandire.
Dan zuwan da take yi gidan idan Rayyan ya yi tafiya ne, ya sa ta dada shakuwa da su duka, kowa yana ji da ita a gidan, musamman da ya kasance ita aka fara aurowa, haka idan (Weekend) ya yi gidanta ake zuwa a ci abinci. Kasancewarta faram-faram, ya sa nan da nan kowa ya saba da ita.
Gashi ba ta boye yadda take ji da Rayyan dinta, duk abinda suka zo, suka samu a gidan, idan ta ba su, sai ta-ce su tsaya sai Rayyan dinta ya fara tukun. Har suka fara mata tsiya ta-ce. “Ku dai fadi koma meye ne, ina da kamar shi ne?” 1
Mukhtaar ya-ce. “Babu, haka shi ma bayi da kamar ki.”
Rayyan yayi murmushi, ya-ce. “Su daina dora miki, ina da wanda ya fi-ki ni kam”.
Mai-jidda ta tsume ta-ce. “Dakta Yaya za ka fada min haka a gaban su?”
“Na fi son kowa ya sani ai, don ba da jimawa ba za ta haifo min wanda ya fi ta.” Mai-jidda ta yi saurin barin falon, ai kuwa ba a dade ba.
Maganar Dokta ta zama gaskiya, ta fahimci cewa tana da juna biyu. Haka ta yi ta faman renon ciki da karatu, idan ta dawo gida Dokta ya takarkare yana kula da ita, haka za ta mike kafafu ya yi ta matsawa yana mata sannu, da ta gane kanta shagwaba iri-iri, ba wacce ba ta masa. Wani lokacin ofishinsa take zuwa ta rakashe, sai tana da Lectures ta tafi aji.
“Ki yi lokacin ki ne, ba ki san kwakwar abin cikin ke sawa ake miki haka ba ko?” Ya fada yana murmushi.
“Ni wataran na kan rasa me ya sa ka auro ni? Shin don na tara maka ‘ya’ya ne ko kuwa don ka na so na.” Ta hada rai tana neman rigima, haka zai biye mata su yi ta yi.
Cikinta na da wata takwas da dan dauri ne, bikin Abdul-Aali ya tashi, ba haka ta so ba, amma ba yadda ta iya haka ta shiga hidima, randa aka daura auren Abdul-Aali ta yi likis! Don haka tana dakin Mama.
“Hauwa’u anya ba za ki koma gida haka ba, na ga yau din nan fa kamar cikin ya kara sauka.”
Mai-jidda tana shiru kawai, amma tun da rana take jin ta ba daidai ba, ciwon baya ya kan dan taba ta, amma yanzu zamanta sai ta ji ya tashi gadan-gadan tun tana matsewa har ta fara wash! “Lafiya kuwa Hauwa’u? Ina wayar ta ki a nemi Rayyan din ku tafi asibiti”.
STORY CONTINUES BELOW
Mai-jidda ta lalubo wayarta da kyar ta nemi wayar Rayyan, amma (Network) ba kyau bai shiga ba, ana cikin haka, sai ga Abdul-Aali ya shigo gidan ya samu halin da ake ciki. “Abdul-Aali, su Sulaiman ba su waje ne su zo su kai Hauwa asibiti tun dazu take cikin wani irin hali, mijinta ba a samun wayarsa.”
Ya dubi gefen da Mai-jidda take ta kasa zaune bare tsaye, a tsume ya-ce. “Mama idan kun shirya, sai na ajiye ku a asibitin kafin nan a samu mijin nata.” 3
Mama ba ta yi wata wata ba, ta zari mayafi, Suwaiba ta taimakawa Mai-jidda zuwa mota, sai da suka shiga motar. Mama ta koma gida. Zuwa lokacin an fadawa Rayyan halin da ake ciki, don haka gida ya yi ya dauko jakar haihuwarta, domin ya same su a asibiti.
Abdul Ali sai duba agogo yakeyi ya gama kosawa ta haihu ko mijinta ya zo ya samu ya tafi, ya tsani asibiti. Ga abokansa sun matsa masa da kira ya ma rasa wani irin naci ne dasu. 2
Suwaiba ko ganin ya gagara tsaye bare zaune ta zaci damuwar Maijidda yake ciki.
“Yaya Abdul ka kwantar da hankalin ka, za su fito ai, wani lokacin yana daukar lokaci, idan an ci sa’a kuma ta haihu da wuri.”
“Yanzu duk lokacinnan da ta dauka bai isa ba, za ta kara wani lokaci ba ta haihu ba?”
Suwaiba ta-ce. “Sosai, wasu fa kwana suke su wuni wasu har kwanaki” Yana fita suka hadu da Rayyan a hanya, ya nuna masa inda suke. 1
“Abdul-Aali, thank you. Kawai ina ga ka je gida, kar ka tsaya anan, ga shi za a kai amarya.”
Sai bayan zuwansu da awa uku Mai-jidda ta haiho Danta, ana fito da yaron Abdul-Aali ya gan shi, ya karbe shi bayan Rayyan ya masa addu’a. Ba tare da bata lokaci ba, ya bar asibitin.
*****
Tana gama hutawa, aka turata dakin gefe, inda aka ba ta Danta a hannunta, ta dubi Dokta ta-ce “Kamar wasa fa abu ya taso, wayarka ba ta shiga, sai Abdul-Aali ne ya kawo mu asibiti.”
Rayyan ya kalleta cike da tausayawa. “Weldon dear, kin yi kokari. Allah ya raya mana”.
“Ameen, ban ga Anty Suwaiba ba?”
“Ta je gida dauko kayan Tea, za su taho da su Mama. Abdul-Aali kuma ya wuce gida, kin san yau shi ango ne.”
Mai-jidda ta yi kwafa a ranta, lallai ba ta san tsanar da Abdul-Aali yayi mata ya kai haka ba, a halin da taken nan har ace masa ta haihu, amma ko sannu bai ce mata ba, ya tafi shi ta amaryarsa yake. 7
Ta dubi jinjirinta a hannunta ta ji wani dadi yana ratsa ta, kwanansu daya a asibiti aka sallame su, gidansu Rayyan ta koma inda Mama take ba su kulawa sosai.
Tamkar yadda Ummanta ke ji da ita, haka Mama take ji da ita. Yaya Maryam nan take zuwa duba su kullum.
Ana saura kwana biyu suna ne. Umma ta zo ta duba su, sannan ta koma. Yaro ya ci suna Muhammad. Rayyan kullum yana kusa da iyalinsa, sai dare ya yi yake komawa gida. Abin mamaki har aka yi suna, ba labarin Abdul-Aali bare matarsa a gidan. 6
Ba ta yi magana ba, ganin ranar ma Mama ta yi maganar rashin kawo masu amaryar ta sa. Sai ana gobe za su koma Portharcourt din su ne ya kawota.
“Anty Hauwa, ki yi hakuri fa, ba ki ganmu a suna ba, sweety ne ya-ce na hakura da zuwa, sai bayan suna saboda ribibi ga shi ban gama huce gajiyar biki ba.” 5
“A’a ba komai Hamama, ke da ki ke amarci, me ya kai ki fita suna, kuma na san lokacin ko kin zo ma ba za ki sake ba, saboda jama’a da dama ba ki sansu ba, amma a hankali dai idan ya kai ki ko ina, za ki saba da kowa ki sansu su san ki”. 1
Nan Hamamatu ta ji dadin kalaman Mai-jidda, haka suka sha hirarsu. Da ta tashi tafiya ta ajiye wata jibgegiyar leda ta-ce. “Wannan na yaro ne da naki Sweety ya-ce a kawo maku”. Mai-jidda ta yi mata godiya, sai bayan ta tafi ne, ta kalli ledar, ta ja tsaki. 7
STORY CONTINUES BELOW
“Ina ruwana da wani kayanka.” Ta dauka ta je ta nunawa Mama kayan ta yi godiya sannan ta koma dakinta. Bayan sati uku ta koma gidanta. Kasancewar ta samu mai aiki karatunta zai zo, da dan sauki ga shi ya zo karshe.
********
Tana (Semester) dinta na karshe ne, ta fara kula da canji daga Rayyan, musamman yadda bai cika janta da hira ba kamar da, sannan lokuta da dama ta kan same shi a falonsa yana waya, daga ta shigo, sai ta ga ya kashe, yana cewa babu (Network). Hakan ya sa ta tsargu, amma ba ta bari ta zarge shi ba, ta same shi da maganar. 4
“Ya yi barci ne?” Ya fada tare da shafa kan Muhammad dake hannun Mai-jidda.
“Eh, ya sha wankan ruwan dumi ai, sai gobe kuma idan Allah ya kai mu.”
“Ina ruwan Sarkin daru.” Za ta kwantar da shi ne, ya-ce ta miko masa, ya kwantar da yaron a jikin sa yana duban T.V, a gefen sa, ta zauna, sannan ta-ce. “Dakta, ni kam dai magana ce a baki na”.
Sai da ta samu hankalinsa ta ci-gaba. “Na kula kamar kwanan nan akwai wani canji a tare da kai, kuma ka kasa sanar da ni ko meye, gudun kar na sa abin da ba shi bane a raina. ya sa nace zan maka magana, shin wata matsala ce a tare da kai ko kuwa wani abin ka ke boye min ko na yi maka?”
Cike da fargaba take sauraren amsar da zai ba ta, domin ta kula da yadda idanunsa suka koma, bayan tai masa wannan tambayar. Ya juya ya kwantar da Muhammad a kujerar falon, sannan ya-ce mata. “Ki kwantar da hankalin ki, babu komai daya ciki.”
Kallon da take masa ne, ya sa ya fahimci ba ta gamsu da wannan amsar ba. Murmushi ya yi ya-ce. “Ki kwantar da hanaklinki, ba aure zan yi ba. Na ga kallon tuhumar da ake min kenan”. 13
“Ni ce maka na yi tunani na kenan? Idan ka ga dama ka yi mana”. Ta fada tare da daga kanta cikin rashin kulawa, jawota ya yi jikinsa ya sumbaci saman kanta ya-ce. “Uhmm! Kamar da gaske, bayan na san me ya sa ake zuwa ofis dina wuni.” 2
Ta dago da sauri ta-ce. “Ni ba abinda yake kai ni, sai don na tayaka hira, idan kuma hakan yana takuraka.
Shi kenan sai na daina, daman ai da na je da ban je ba, na san ka na waya da wasu, tunda tun kan bikin mu ma, na san yadda ‘yan mata suke maka caa!
“To ba ga shi ba, idan ance kishi, ki ce ba haka ba.” 2
“Ba dole na yi ba, abinda ka ke so, ai shi ka ke yiwa kishi.” 2
Da haka Rayyan ya kawar da tambayarta, ba tare da ya amsa ba. Mai-jidda ba ta sake dago maganar ba, ganin tunda tayi masa magana, ya koma kusan kamar da, sai dai ya-ce mata ayyuka sun masa yawa a wannan lokacin, don haka ta maida hankalinta wurin jarabawarta ta karshe.
********
Shirye-Shiryen auren Mabruka ne ya taso gadan-gadan, saboda satin da za su gama jarabawa za a daura auren, kasancewar bikin ya zo bagatatan!
Sun dage kwarai wajen karatu, don ganin sun gama cikin nasara, ga Muhammad ya dada wayo sosai. Duk inda suka shiga kuwa, kowa son yaron yake yi.
Mai-jidda tana gidan wunin Mabruka ne, wayarta ta yi kara, ta duba ba ta gane lambar ba, don haka ta dauka a tsanake. “Assalamu-alaikum”.
“Wa’alaikumus-salam!” Mamaki ta ji da jin muryar, don haka ta cire wayar a kunnenta, ta duba, sannan ta ci-gaba da magana.
“Ina wuni.”
Ba tare da ya amsa gaisuwarta ba, ya-ce. “Me ya samu wayar Yaya Rayyan ba na samunsa tun jiya?” 1
“Ina tsammanin (Network) ne”.
“Idan yana kusa, ki ba shi wayar”.
“Ina gidan biki ne…”
“Idan kin koma, ki ce ya kira ni.”
STORY CONTINUES BELOW
Ita ta rasa meye matsalar wannan mutumin, kullum abin shi karuwa yake yi. Ta dade da sa shi a gefe, ya kira wayarta ma ko gaisuwa ba ta cancanta ba, ta tabbata abin na da matukar muhimmanci, idan ba haka ba, ta san ko duniya za ta nade ne, ba zai taba kiran wayarta ba. 2
Tana zuwa gida ta samu Dakta ma shigowarsa kenan, don haka bayan sun natsu ta-ce. “Kanin ka ya kira yana neman wayarka baya samu, wai ka kira shi da alama kiran na da muhimmanci”.
“Me ya sa ki ka ga kamar hakan?”
“Saboda na san ko sama da kasa za su hade. Abdul-Aali ba zai taba kirana ba, ban san ma yadda aka yi yake da lamba ta ba.”
Dariya Rayyan ya yi ya-ce. “Hauwa, ni dai ban san meye Abdul-Aali yai miki ba, haka ki ke fushi.”
“Tab! Ni na ke fushi ko shi yake fushi, haihuwa na yi fa, ko barka bai min ba, yana jibgani a asibiti, ya juya ya tafi, ko sannu bai min ba fa.”
“Oh, don Allah kar ki sani dariya, yanzu yadda na gajin nan. Yaya zan yi idan mutane biyu da na fi so duk duniya suna fada da juna? Kin ga ai ni za ku kayar.
Don haka ki yi hakuri ki masa uzuri, kar ki manta ranar fa shi ango ne, ashe ya yi kokari ma da ya jibge min ke a asibiti kafin na zo.” Ya fada tare da shafo fuskarta. “Miko min wayar tawa, sai ki sama min abinci kafin nan.”
Ta yi yadda ya-ce. Muhammad yana kan kafafunsa yana wasa, ta ajiye abincin ta koma taho da ruwa ne, ta ji maganar sa a waya da Abdul-Aali, duk da karshen maganar ta tsinkaya a dalilin rotsa kofin da tayi a kasa.
Ba ta damu da kwashe fasasshen glass din ba, da gudu ta iso falon ta fada jikin Dakta, yayin da yake dubanta cikin mamakin me ya jawo fashewar abu.
Amma tana shiga jikinsa ya gane ta san komai. Kuka take yi tsakaninta da Allah, da kyar Rayyan ya sa ta yi shiru. “Meye haka Hauwa? Ki daina kuka mana, ko an fada miki shi kenan, komai ya kare?”
“Yanzu Dakta, tuntuni ashe abin da yake damunka kenan, ka ki ka fada min? Ashe ban cancanci na sani ba, nayi maka addu’a.
Na kula da kai, meye amfanin lokaci na da na dauka na ke zubawa a wani karatu, idan ban san halin da mijina yake ciki ba, na taimaka masa, ka yi mana adalci da ka rufeni da wannan batu?”
“Ki kwantar da hanakalinki, me ki ka ji nace?”
“Is it worse?” Ta tambaya tare da goge hawayen da suke ta tunkudar juna a fuskarta.
“For now, dai an samu Dan tsiro ne (Growth), amma karshen wannan watan zan tafi U.S ayi bincike sosai”. 9
Mai-jidda tana hawaye ta-ce. “Daga yau idan ka sake boye min wani abu. Ban yafe maka ba, komai rintsi kar ka sake boye min komai game da rayuwarka.
Lafiyarka lafiyata ce. Yaya ka ke son na yi, idan na tsinci kaina a tsakiyar wannan abu ba tare da warning ba? Shin ka na ganin zan iya rayuwa?”
“Ki daina wannan maganar, addu’a ita-ce gaba, ba ga shi nan ba na yi wata shida da samun labarin tsiron kuma kin taba ganin na kwanta ciwo? Don haka ki kwantar da hankalinki, kawai addu’a za mu yi Allah na tare da mu”.
“Na ji, Insha-Allahu za ka samu lafiya, su Mama da Abba sun sani?”
“Abdul-Aali ne kawai ya sani, kin san tsakani na da shi, sai Allah, saboda haka ki daina fada da shi, yana min ciwo a nan”. Ya fada tare da nuna kirjinsa gurbin zuciyarsa.
“Zan yi kokari na, sai dai ba laifina bane, don ya tsane ni.”
Dariya ya yi, ya sumbaci, saman idanunta da ta lumshe su. Kukan Muhammad suka ji da sauri ta mike, ta manta kwata-kwata da glass din da ta fasa yaron ya yanke.
STORY CONTINUES BELOW
Allah ya sa ma ba mai zurfi bane yankan, da sauri ta sa abin kwashe shara ta kwashe. Yayin da Rayyan ke gyara ciwon yaron. Tana gamawa ta karbe shi a hannun Rayyan. Tana jijjigawa, sannan ta sa masa nono a baki.
Ya tsaya yana kallonsu, yayin da ya share kwalla a gefen idanunsa ba tare da ya bari ta gani ba. 6
An fara azumi, wannan ya bawa Mai-jidda damar dagewa da addu’a kan lafiyar mijinta, domin watan da ya gabata ya je asibiti an sake yi masa gwaje-gwaje.
Ganin duka alamomin cutar ba su gama bayyana ba, suke tunanin idan an ci sa’a za a iya aiki a ciro tsiron da ke cikin kwakwalwar sa, sai dai ba anan damuwar take ba, domin jejin daga kodarsa ta watsu zuwa kwakwalwarsa, don haka aikin babba ne. 9
Da yamma shigowarsa ya sameta, tana aikin buda baki a kicin. “Yaya dai Madam, sannu da aiki.” Ya matso kusa yana leka tukwanen da ke kan murhu. “Me ake shirya mana ne haka, gida sai kamshi yake yi”.
“Za ka gani ai, har an gama karatun ne?”
“Eh, su Mukhtaar ma sun min waya suna isowa.”
“To ba damuwa, ni ma na kusa kammalawa Insha-Allahu.”
“Bari na watsa ruwa kafin nan. Muhammad ya yi barci ne?”
“A’a Yaya Maryam ta yi aika dazu ya bi A’isha suka tafi.” Dokta ya yi dariya, sannan ya wuce ciki. Tana gamawa, ta kimtsa komai a falo, saboda yau duk anan suke da shirin shan ruwa.
Shakuwar su Dakta da ‘yan-uwansa yana ba ta sha’awa sosai, musamman idan ka gansu da iyayensu, za ka dauka ba su da wata damuwa a duniya, hakan ya sa gaba ki dayansu sun girgiza da jin labarin cutar da take tare da Dan-uwansu.
*******
“Anty Hauwa wai ina Muhammad ne, gidan ya yi shiru da yawa.”
Mai-jidda ta yi murmushi ta-ce. “Yau kam gidan Yaya Maryam zai kwana sun tafi da A’isha dazu.”
Shigowar shi ne ya sa ta yi shiru, yayin da kannensa suka fara gaishe shi, kamar ta yi shiru, amma ta gaishe shi, tunda ko idon Yayan nasa bai ji nauyi ya gaishe ta ba. Sama-sama ya amsa mata, ta tabbata da su biyu ne, ko kallon inda take, ba zai yi ba, yanzu kuwa har da cewa. “Ina Muhammad?”
Sulaiman ne ya ba shi amsa. Mai-jidda kuwa ta koma ciki ta bar su, domin ana kokarin kiran Sallah. Tana kammala asham, ta fito ta tattara falon a kwance ta sami Rayyan yana kallon labaru.
Da sauri ta taho gefen shi. “Dakta lafiya dai ko?” Ta fada tana shafa kansa, don ta ji ko lafiya.
Hannayenta ya rike ya-ce. “Lafiya kalau, haka za ki rinka kidimewa, daga kin ganni a kwance? Gajiya-ce kawai”. 3
“Ina su Mukhtar. Yaya su ba su shigo ba?”
“Sun wuce daga masallaci, yau kam ina ga zan shiga da wuri, saboda na samu isasshen hutu.”
“Za ka iya azumin kuwa gobe, na ga idanunka sun yi ja, ba dai kan bane yake ciwo ko?”
“Zan iya, kar ki damu. Na kammala da cikin jami’a ma, kin san dama shekaru hudu ne kuma sun cika, don haka ina da isasshen lokacin samun hutu.”
“To bari na tara maka ruwa, sai ka sa a jikin ka, ko za ka ji dama-dama”.
“Kar ki damu.” Mai-jidda ta bi shi da kallo, ta san daurewa yake yi, yadda ya runtse idanun sa, da ya zo tashi.
Hannunsa ta riko ta-ce. “Yaushe ne komawarka asibiti?”
Ba ta yi aune ba, ta ji ya tafi luuu! Da sauri ta tare shi, amma ya fi karfinta, ga wani kakkarwa da yake yi. Mai-jidda ta kidime, banda kuka ba abinda take yi, can jikin ya mace ya daina kakkarwan, ta gyara shi a kidime take kiran sunan sa “Rayyaan, me ya faru ka bude idanunka…. 6
“Inna-Lillahi’wa-Inna-Ilaihir-Raji’un!” Da sauri ta nemi wayarta, kanta ya kulle ta rasa wanda za ta kira. Da sauri ta danna lambar Mukhtar. “Mukhtar, ku yi sauri ku dawo Dakta ya fadi, ku yi sauri don Allah”.
Da gudu ta tafi kicin, ta debo ruwa ta sa masa, ta dan bubbugi fuskarsa, ko zai farfado. A hankali ya soma tari, ta yi wata ajiyar zuciya tana hamdala, ta gyara masa kwanciya.
Bayan kusan minti sha biyar, wanda suka fi ko wane lokaci tsawo a wurin Mai-jidda, sai ga su Mukhtaar, nan da nan aka wuce da shi asibiti, a hanya ne Mukhatar ya kira Abba yake fada masa abin da ake ciki.
Mai-jidda kam kan a shiga asibiti ta canza kamanni, tamkar ita-ce marar lafiyar. Likitan dai ba abinda yake kokarin yi, illa ya daidaita hayyacin Rayyan saboda ya daina suman, don yayi kusan biyu daga gida zuwa yanzu. 2
Bayan Abba ya fito daga ofishin Likitan ne ya dawo dakin da Dakta yake, Mai-jidda ta gaishe shi, ya amsa, sannan ya dubi Mukhtar ya-ce. “Kai, mayar da Hauwa gida ta huta. Sulaiman zai zauna.”
Mai-jidda ta dubi gefen da Rayyan yake kwance, idanun sa a rufe tamkar mai barci, amma kuma ya samu hakan ne, da taimakon drip dake manne a hannunsa.
Wanda Likitan ya dura maganin barci a ciki. Ba tare da ta musa ba, ta bi Mukhtar, sai dai suna fita ta-ce. “Don Allah mu bi gidan Yaya Maryam na dauki Muhammad”.
“Na zaci a can zai kwana, ko ke ma za ki zauna a can, idan ya so sai mu je ki dauki abin da ki ke bukata ko?”
“Ba komai, zan koma gidana, tunda za a iya neman wani abin a gida. Mukhtar kai Likita ne, shin ba abinda za ayi wa Dakta ya warke?”
Mukhtar ya yi shiru cikin tunani kafin ya-ce. “Kar ki damu sauki yana wurin Allah, kuma za mu yi iya ka kokarin mu, domin Yaya Rayyan ya samu lafiya, ina ga daman yana shirin komawa UCLA a America.
Saboda Treatment, to kin ga ba za mu bata wani lokaci ba. Zan yi magana da Yaya Abdul, sai a san yadda za ayi a matso da tafiyar, tunda ya fara samun Attacks.”
Mai-jidda ta runtse idanunta, wasu hawaye masu zafi suka biyo fuskarta, ta samu Muhammad ya yi barci, don haka Yaya Maryam ta-ce ta bar shi.
Nan ta yi ta ba ta baki akan ta daina kuka. Mukhtar ya maida ita gida, sannan ya koma asibiti. Ranar dai Mai-jidda ba ta runtsa ba, addu’a ta kwana yi, sai da ta yi sallar asuba barci mai nauyi ya kwasheta.
A firgice ta farka, karfe takwas, ta wanke kwanukan jiya, sannan ta shirya ta fita, kai tsaye asibitin ta wuce.
Ta samu ya tashi a barcin, Likitan dai ya-ce zai kara rike shi, sai ya dan samu karfin jiki, kafin ya sallame shi.
A ranar aka kammala magana akan shirye-shiryen tafiya asibiti. An nemawa Mai-jidda Visa za su tafi tare da Mukhtaar kasancewar Abdul-Aali ba zai yiwu ya tafi ba saboda aiki.
A hannun Yaya Maryam ta bar Muhammad, ta je Dutse tayi masu sallama, sannan satin da ya zagayo suka daga zuwa Los Angeles, domin duba lafiyar Dakta.
Da yake Rayyan yana koyarwa a cikin LA ya san garin sosai, sun yi masauki sannan aka yi waya domin jin lokacin da za su shiga asibitin washegari.
Suna zaune a daki ne Dakta ya-ce mata “Ba na so ki daga hankalinki, ba komai Insha-Allahu. Ina so ki daure zuciyarki, wannan satin za a fara gwaje-gwaje ne kafin su san me za a yi”.
“Ba komai, Allah ya sa a dace. Allah ya ba ka lafiya, wannan ita-ce babbar addu’armu.”