FETTA CHAPTER 13

FETTA




CHAPTER 13



K’wak’walarsa ta d’auke, tunanin sa ya tsaya cak, Ya rasa ta ina zai fara, Tafin hannun sa ya d’aura saman goshi ya buga, “Ya Allah”, Ya furta,

Mik’ewa yayi ya shiga toilet, Ya sakar ma kansa shower, Minti 5 ya d’auka ya fito.

A hankali yake jin tunaninsa na dawowa, ” Alhaji Tambari I will eat you raw”, Ya fad’a yana squeezing hannun sa, Mukullin mota ya d’auka, Ya fito, Har ya fice Fetta bata sani ba, tayi nisa a bacci.

Da duhu-duhun gari ya isa gidan gonar sa, Masu gadin da ma’aikata sunyi mamakin ganinsa wannan lokaci, Suka shiga gaishe sa, ya amsa da hannu.

Office d’insa ya bud’e ya shiga, Ya zauna kan kujera, Ya bud’e drawers ya jawo wani file, ya shiga duba takardun ciki, sai da yazo kan wata takarda mai d’auke da sunayen mutane, a k’asa ya rubuta Alhaji Suleiman Tambari.

*8:30am*
Yayi dialing number Alhaji Tambari, bugu d’aya ya d’auka, “Haba Suraj ina ta kiran ka baka d’aukar waya”, ” Ayi mun afuwa my wife is sick”, “Ayyah Allah ya bata lafiya”, ” Amin”, Ya amsa yana jin tamkar ya shak’aro sa ta cikin waya, “Idan ba damuwa ina so mu had’u gidan gona ta, muyi estimate na kud’in da za’a kashe tare”, ” Ai ina ganin ba sai nazo ba kayi kawai”, “Your presence is needed”, ” OK zuwa k’arfe tara zan zo”, “Sai kazo”, Yayi hanging up, Yana cizon lips.

Alhaji Tambari ya fito cikin shirin sa, Fuskar sa d’auke da annurin samun nasara, Tasleem ya tarar a falonsa, ” Daddy ina kwana?”, “Lafiya lau Daughter, kin tashi lafiya?”, ” Lafiya Daddy”, “Allah ya k’ara miki lafiya”, ” Amin”

 “Daddy kud’ina sun k’are”, ” Ba nace ki daina bari sai sun k’are kafin ki sanar dani ba”, “Sorry” Ta fad’a tana turo baki, “Daga yau idan sun kusa k’arewa ki sanar dani”, Tayi nodding kai, ” Uhmm Daddy ya maga….”, Ya katse ta “Kwantar da hankalin ki, saura k’iriss ki zama matar SS”, Ta washe baki cike da murna, ” Waya ga daughter na Amarya”, Tasa hannu ta rufe fuska, ta fice da gudu, Yabi bayanta da kallo cike da tsantsar so, Burinsa a ko da yaushe ya ganta cikin farin ciki.

   Zafi ya tashe ta, Ta mik’e da addu’ar tashi daga bacci, Zufa duk ya dabaibayeta alamun zazzab’in ya sauka, Ciwon kan ta nema ta rasa, “Alhamdulillah”, Ta furta, bargo ta nad’e, ta nufi d’aki,

     Ganin baya d’akin ta d’auka yana toilet, Ta shiga gyaran d’akin, ganin har ta kammala ta saka turaren wuta, bai fito ba, Ya tabbatar mata ya fita.

     Gidan tass ta gyara, Batayi abincin breakfast ba, Tea kad’ai tasha, Tayi wanka ta shirya tsaf, jikinta na fitar da k’amshi mai dad’i.

    Alhaji Tambari shi kad’ai ya nufi wurin Suraj.

     ” Sir ya iso”, Cewar Rabi’u, Ya dad’s a tsaye bakin window, Yana jiran shigowar sa, ya sanar da Suraj kamar yadda ya umarce shi, “Ina abunda nace ka karb’o mun wurin security”, Yasa hannu a aljihu ya mik’a masa yana rissinawa, Ya karb’a ya d’aura soka aljihun wandon sa, ” Zaka iya tafiya, and make sure komai ya tafi daidai”, “OK Sir”

     “Saurayi mai tashen naira”, Alhaji Tambari ya fad’a yana jan kujera ya zauna, Suraj yayi murmushi wanda shi kad’ai yasan manufar sa Yace ” Barka da Zuwa”, Yana mik’a masa hannu, “Barka kadai” Suka yi sallama,

     Mik’ewa yayi, Ya nufi k’ofa ya saka mata key, Ya cire mukullin ya jefa cikin aljihu, “Ya ka rufe k’ofa?”, Alhaji ya tambaya, ” Saboda tsaro”, Yayi dariya yace “Hakan nada kyau”

STORY CONTINUES BELOW


   Ya zauna ya d’aura k’afarsa saman table dake gabansa, ya d’aura d’aya a saman d’aya,

     “Muyi sauri, ina da meeting da governor akan kwangilar yaji shiru ba’a fara ba”

    Wata dariya Suraj ya fashe da ita yace “Ohh Really”, Da mamaki Alhaji ya bisa da kallo, ” Alhaji Suleiman Tambari kayi kuskuren shigowa rayuwar Suraj Sa’id”, “B..an.ga..ne ba”, Ya fad’a murya na rawa.

    ” Zaka gane”, Ya mik’e tsaye, Ya shiga zagaya office d’in, “Meye manufar ka a kaina?, Me kake da shiri a kaina?”,

    Alhaji Tambari ya girgiza, ya dake yace ” Wacce manufa kuwa, banda alak’a ta kwangila da nake so mu amafana da juna”,

    Ya rank’wafo da kansa saitin sa, Yana kallon k’wayar idonsa Yace “Duk tsohon da bai ji kunyar hawa jaki ba, jakin ba zai ji kunyar yadda shi ba”

      Alhaji da ya fara tsorata da yanayin Suraj yace “Nifah ban gane ina maganganun ka suka dosa ba”, Bindiga ya zaro daga aljihun sa, Ya saita kansa, ” Wallahi ko ka fad’a mun manufar ka a kaina, ko na fasa kanka”

    “Kai ni zaka kashe, bayan kasan waye ni a k’asar nan, kana so ka k’are rayuwar ka a gidan yari”, Dariya Suraj yayi yace ” Idan na kashe ka a cikin gidan nan zan binne ka, babu wanda zai san da gawar ka”,

      Alhaji ya had’iye miyau tsoro, “Idan kuma taurin kai zaka yi, ka fara k’irga mintuna da suka rage maka”, Ya k’ara saita bindigar da kyau,

    ” Uhmm kaga Suraj, mu bar kwangilar nan, na hak’ura, bud’e mun k’ofa na tafi”, “Ba zaka bar gidan nan ba, sai ka fad’a mun dalilin ka na shigowa rayuwata”,

   Alhaji ganin bashi da wata mafita, kuma a yadda yaga yanayin Suraj zai iya kashe sa, Yace ” Ka gafarceni idan na sanar da kai, kada kamun komai”, Ya girgiza kai alamar ba zai masa ba,

    Ya nisa yace “Ya’ta d’aya tilo wacce k’awar k’annen ka ce, Allah ya jarabceta da son ka, ta fad’a mun zata iya rasa ranta idan bata same ka ba, hakan yasa nayi niyyar yaudarar ka da kwangilar k’arya, idan ka saka kud’in ka kayi ayyuka, na sanar da kai gwamnati bata samu biya ba, a lokacin zaka buk’aci kud’i sosai, Ni kuma nace zan baka da sharad’in zaka auri ya’ta, Ka gafarceni nayi ne dan farin cikin ya’ta”

    Jikinsa yayi matuk’ar sanyi, Fetta ta fad’o masa rai, “Fatima taimako na take shirin yi”, Ya fad’awa kansa, bai san lokacin da ya kai zaune ba,

    ” Kayi hak’uri”, Alhaji ya katse masa tunani, “Zan barka ka tafi, but da sharad’i, idan ka sake ka kayi yunk’urin aiwatar da wani abu a kaina, zan yad’a ka duniya, which zai iya affecting political career and reputation d’in ka”, ” Wallahi ba abunda zan yi, idan na samu na fita a nan, bazan k’ara bibiyar rayuwar ka”, Mukullin ya jefa masa, Ya d’auka jiki na rawa, ya bud’e k’ofa ya fice har yana tuntub’e,

     Suraj kwantar da kansa yayi jikin kujera, Zuciyar sa na harbawa da matuk’ar sauri, jikinsa tamkar an zare masa lakka saboda yadda yayi sanyi, Tuno irin rashin mutunci da yama Fetta akan kud’in, da yadda ya k’aryata ta, Ya buga hannun sa kan tebur, “Ya ILahi”, Ya furta, Yana had’e hannayen sa wuri d’aya, Maganganun Hajiya ke dawo masa a kai,

     ” Fatima kin taimaki rayuwata, kin kub’utar dani daga sharrin Alhaji Tambari”, Zuciyarsa ta tabbatar masa kud’i basa gabanta, ba dan su ta aure shi ba.

    Da k’yar ya mik’e, Ya fito, ba tare da yabi ta kan ma’aikatan ba, Ya shiga mota, Yaja zuwa gida, Cike da tunanin da wane ido zai kalli Fetta.

      Sashen Hajiya ya nufa, Ita dasu Feena ya same ta a falo, Suka shiga gaishe sa, Ya amsa da hannu.

    K’asan carpet ya zauna saitin Hajiya, Ta kallesa tace “Meke damun ka, na hango damuwa a tare da kai”, Yayi shiru ya rasa ta ina zai fara sanar da Hajiya, ” Ka fad’a mun damuwar ka”

STORY CONTINUES BELOW


    Ya nisa ya zayyane mata komai, Murmushi mai cike da farin ciki tayi tace “Alhamdulillah! Allah nagode maka da zuwan Fetta cikin rayuwar mu, hak’ik’a Suraj kayi dacen mace ta gari, cikin suffofin mace ta gari wacce zata kare ma dukiyar ka, Fetta have a golden heart, ka rik’e ta hannu biyu”, Yayi shiru bai ce komai ba tamkar wanda ruwa yaci sa.

    Su’ad da Feena jikinsu yayi sanyi, zuciyarsu cike da haushin Tasleem da Mahaifinta, kowaccen su ta kud’uri shuka ma Tasleem rashin mutunci, karon farko da suka yaba da k’ok’arin Fetta.

    Hajiya ta umarci Samee ta kirata, Tana zaune tana kallo, Samee ta shigo da sallama, Ta gaisheta ta amsa, ” Mama na kiran ki”, “Toh”

   Hijab ta d’auko ta saka, Tabi bayan Samee.

    A falo duka ta gansu, Jiki a sanyaye ta shiga tsoron ta kar dai Suraj ya sanar dasu ita ta d’auki kud’in, bata so Hajiya ta zarge ta, Tayi sallama, Murya Hajiya taji ta amsa,

    “Zo ya’ta ki zauna kusa dani”, Jin haka ta sauke ajiyar zuciya, K’amshin turaren ta da ya daki hancin sa, yasa ya d’ago kai ya kalleta, tun shigowarta kansa na sunkuye k’asa, Wani nauyi da kunyarta yake ji, Karon farko a rayuwarsa yayi feeling guilty dan yama wani abun rashin kyautawa.

       Kusa da Hajiya ta zauna, Ta rik’o hannun ta tace ” Mun gode sosai Fetta,  kin taimaki Family nan, kin taimakawa mijin ki daga fad’awa halaka, ke alheri ce a rayuwar mu”, Wani sanyi taji na ratsa ta, farin ciki ya lullub’e ta jin gaskiya ta bayyana, “Allah ya sada ki da alkhairin sa”, Murya a sanyaye tace ” Amin”, “Ina zuwa”, Ta fad’a tana mik’ewa,

    Suraj na ganin Hajiya ta shiga ciki, Ya mik’e ya fice,

     ” Ina Suraj d’in?”, Hajiya ta tambaya, Feena tace “Ya fita”

    Zama tayi ta kamo hannun Fetta, Tana k’ok’arin saka mata bangles masu azabar kyau, “Ga tukwicin ki” Ta d’an janye hannun ta tace “Ki barshi Hajiya, nagode”, Kallon da ta jefa mata yasa, ta tsayar da hannun ta saka mata.

    Feena ta kalli Su’ad suka kalli juna, Ransu a matuk’ar b’ace, Sun dad’e suna naci Hajiya ta basu, kowannen su ya d’auki biyu ta hana, Zuwanta London ta siyo su na diamond ne.

   Murya k’asa k’asa Feena tace ” Tashin sense”, Su’ad tace “Hmm lallai”, Bak’in ciki da hassada fal a ransu.

   Kiran wayar Hajiya da akayi, Yasa ta mik’e ta nufi sashen su.

    A falo ta tarar dashi zaune, Yana danna waya, bata bi ta kansa ba, Ta nufi kitchen.

   Bilkisu ta zuba ado mai d’aukar hankali kai kace gidan biki zata, k’amshin turare na tashi daga jikinta, Aunty Jummai ta kalleta tace ” Ina zuwa?”, “Bikin wata k’awar mu, da mukayi makaranta tare”, ” Toh ki sauri ki dawo, zamuje gidan Hajiya Tumba”, Ta amsa da “Toh”, Tana ficewa.

    A bakin k’ofa ta tarar da Zulaihat na jiran ta ” Wannan kwalliya haka, gaskiya naji kishi”, “Ai ke nama”, ” Ba wani”, “Yau rigima kike ji, ni dai mu tafi”

     Wani had’add’en gida Bilkisu taga sun shiga, babu abunda babu na more rayuwa, Tana ta raba ido tana kallon dukiyar da aka narka a gidan, Kallo d’aya Hajiya Rabi tama Bilkisu, taji ta tafi da tunanin ta, Ba b’ata lokaci suka shiga d’aki, suka yi bad’alar su, ta cika mata jaka da kud’i, ta dawo gida ana magrib, Aunty Jummai ta mata fad’an rashin dawowa da wuri, Zuwa gidan Hajiya Tumba sai kuma gobe.

    Alhaji Tambari da ya koma gida ya buk’aci ganin Tasleem, Ya kwanto ta jikin shi,

     “Am sorry my daughter this time around i fail”, Ta d’ago tace ” Daddy don’t tell me Suraj ba zai aure ni ba”, “Kinsan baki tab’a neman abu a wurina kin rasa ba”, Ta d’aga kai, ” Ina rok’on ki, ki hak’ura da Suraj, idan bakya so na rasa aikina da mutunci na”, “But Daddy why?”, ” Tasleem don’t insist on knowing “, Jiki a sanyaye ta mik’e ta bar falon, Yabi bayanta da kallo yana jin ransa baya masa dad’i,

    Kan gadon d’akinta ta fad’a ta fashe da kuka, sai da tayi mai isarta ta share hawaye ” Idan kai ka kasa, I will fight for myself, sai na auri Suraj”, Tayi assuring kanta.

    Wunin ranar Suraj a gida yayi sa, Fetta bata bi ta kansa ba, balle ta nuna tasan da zaman sa gidan, abunda ya mata is hurting her badly, Ta k’udurta ma kanta nesanta kanta dashi.

     Kwanciyar k’asan yau taji bata ra’ayi, K’arshen gado ta kwanta, Tana jin sa ya hau ya kwanta,

     Godiya yake son mata, Yana jin nauyi, cikin dakewa yace “Thank you for helping me”, ” Don’t thank me, banyi dan kai ba”, Ta ka’ra gyara kwanciyarta taja bargo ta lullub’e,

Yaji zafin furucin ta, so ba dan shi tayi ba, Wata zuciyar tace “Meyasa zaka jin haushi dan bata yi dan kai ba, tayi ne dan Mahaifiyar ka”, But still ya kasa daina jin zafin furucin.”Kar kiga mun sa miki ido, ki d’auka tsoron ki muke, na gaji da shashancin ki, labarai na zuwa kunne na akan iskancin da kike a gari”, Kawo Sule ya fad’a cike da fad’a, Karima dake durk’ushe gabanshi tana jin dama bashi ne mahaifin ta ba, Sam bai san ya bata tarbiya ba, wanda lalacewar ta yana da kaso 90 na bada gudunmuwa. +

    Ya k’ara da ” Na baki sati biyu cikin samarin ki, ki fitar da miji, ko wallahi na had’a ki da duk wanda naga dama, kinji na rantse, bazan zauna da k’atuwar budurwa tana jawo mun abun kunya ba”, Yana fad’ar haka ya bula rigar shi ya tashi, Yelwa tace “Kin dai ji, yarinya kin zama karya, kibi wannan kibi wancan”

     Karima tashin hankali ya dabaibayeta jin zancen aure, bata san wa zata tsayar ba, Duka samarin ta babu na aure, Ya Bello mahaifiyarsa ta hana, tasan duk mutumin arzik’i ba zai aure ta ba, wasu hawaye masu zafi suka zubo kan kumatun ta, Ta mik’e zata bar falon, Yelwa ta bita da kallo “Ko zaki zubar da duka hawayen ki sai an miki aure, mara kunyar yarinya, anya ma ba’a mun musayar ki wurin haihuwa ba”

     Karima a ranta taji dama hakan ta kasance, sam bata yi dacen iyaye ba.

    Kiran farko a kunne Fetta, ta mik’e da sunan Allah, ta shiga toilet tayi alwala, Ta fito, ta fara gabatar da nafilfili.

      Kiran assalatu ya tashi Suraj, ya sauke idon shi akanta, Ya kawar da kansa gefe, Ya mik’e ya shiga toilet, Yayi alwala, Ya fesa turare ya fice masallaci.

     Turaren nashi taji na hawa mata kai, Tana idar da sallah, ta d’auki Al Qur’ani ta koma falo, Tana muraja’a.

    A falo ya tarar da ita, Yayi mamakin ganinta, sanin sa a d’aki take, “Ina kwana?”, Ta fad’a ba tare da ta d’ago kanta ba, ” Lafiya lau”, Ya amsa yana shiga d’aki.

     *6:30am*
  Ta rufe Qur’anin ta ajiye, Ta shiga kitchen had’a breakfast, Cikin awa d’aya ta had’a kunun gyad’a da yam and egg, Ta jera a dining table.

     Kwance ta same sa kan gado yana bacci hankali kwance, Ta kalli fuskar sa, fara tass da ita wacce hutu ya zauna mata, “Handsome”, Ta fad’a, Ta kawar da kai, ta nufi band’aki, Wanka tayi, ta tsantsara kwalliya cikin lace d’inkin riga da skirt, ya matuk’ar yi mata kyau, Tabi jikinta da turaruka masu dad’i.

    Falo ta fita ta kunna kallo, wanda ya tafi da dukkan tunanin ta.

     ” Zo ki had’a mun ruwan wanka”, Taji yo muryarsa daga d’aki, Ba musu ta mik’e, Ta shiga d’akin yabi ta da kallo, Ta masifar yi mishi kyau, yayin da k’amshin ta ya jefa sa a wani yanayi, yana jin tamkar ya rungume ta.

     Ta had’a mishi ruwan wanka, Ta fito, a tsaye ta gansa d’aure da towel, Tayi saurin kawar da kanta, ta fice d’akin, Yabi bayanta da kallo yana sauke ajiyar zuciya.

    Ya dad’e cikin jacuzzi yana wanka, ko zai samu sassaucin abunda yake ji, but nothing change, Haka ya fito d’aure da bathrobe.

     “Fatima!”, Ya kira ta, ” Na’am”, Ta amsa tana mik’ewa ta nufi d’akin, Da hannu ya mata alama ta shafa mishi cream a baya, Da kallon mamaki tabi sa, Ya juyo da kallon sa gareta, ya zuba mata mayun idonsa, suka had’a ido ya d’age mata gira, Sunkuyar da kanta tayi k’asa, dan kunya ya bata.

STORY CONTINUES BELOW


    Cream d’in ya d’auka ya lakata, ya jawo hannun ta, ya shafa mata a tafin hannu, Ya juya baya yana fad’in “Oya shafa mun”, Tamkar ba zata yi ba, but bata son su tsaya jayayya, Tayi rubbing ta shafa masa, Hannun ta mai laushi, ya sake jefa sa a wani yanayi, Ya lumshe ido,

   Ji tayi ya jawo ta, Ta fad’o jikinsa, Tana k’ok’arin mik’ewa ya had’e jikinsu, Yana sauke ajiyar zuciya, ” You scent nice”, Ya fad’a da kasalalliyar murya , Labari ne ya fara canzawa, yana mata wani irin salo, Kasa hana sa tayi, sai ma wuya da ta mik’a masa, wanda hakan ya masa matuk’ar dad’i.

     Kan gado duka suka tsinci kansu, Suraj sai da ya tabbatar ya samu natsuwa, Ya mirgina gefe zuciyar sa wasai, yana jin wani farin ciki na ratsa shi.

     Fetta haushin kanta ne ya dabaibayeta, bata san ya akai ta sakar masa ragama ba, Tana jin sa ya mik’e, ya tsaftace jikinsa, Ya shirya, yana fesa turare, tayi saurin toshe hancin ta, Sam yanzu baya mata d’adi.

     Ya fice ba tare da yace mata komai ba, Ya lura da yanayin ta yan’ tsiyar ne  a kanta, ban shirya ma tsiyarta ba.

    Toilet ta shiga ta tsaftace jikinta, Tana fitowa kiran Yasmeen ya shiga wayarta, Tayi receiving,

     “Ina taso na kira ki ban samu natsuwa ba”, Cewar Fetta, ” Hankalina ya kasa kwanciya, ina ta zullumi, nayi ta kiran wayar ki bata shiga”, “Ina ga laifin network”, ” Toh ina Suraj d’in an gane gaskiya”, Ta fad’a mata yadda akayi, Cike da murna tace “Alhamdulillah, na matuk’ar ji dad’i yanzu zai k’ara ganin k’imar ki”, Fetta murmushi tayi tace ” Ina shiryawa, zan k’ara kiran ki”, “Toh ayi kwalliya mai d’aukar hankali”, ” Ke koh”, Ta fad’a tana kashe wayar.

     A gaggauce ta shirya sakamakon kanta da taji yana masifar ciwo, Panadol da Suraj ya bata ta d’auka tasha, ta kwanta, Kan ace haka zazzab’i ya rufe ta.

     “Ashe baku da mutunci, baku gaji arzik’i ba, mun d’auke ki da zuciya d’aya but ke so kike ki duk’ufar damu”, Cewar Su’ad ta rik’e k’ugu cike da masifa, Feena tace ” Mun gode Allah da akayi walk’iya halin ku ya fito tun kafin ki aure shi”, Tasleem da mamaki tabi su da kallo tace “Nifah ban gane ina maganar ku ta dosa ba”, Su’ad tace ” Rainawa kanki hankali, toh bari kiji daga yau ki cire zancen auren Ya Suraj a ranki, yafi k’arfin ki”

    Guntuwar dariya Tasleem tayi tace “Zancen banza kenan, Ya Suraj kamar na aure sa na gama”, Feena tace ” Sai ki aure sa mu gani”, “We shall see”, Tasleem ta fad’a tayi gaba, ta barsu suna surfa mata zagi, bata waiwayo ba ballatana ta nuna tasan da ta suke.

    Aliya ta fito da shirinta, ” Umma zan biki” Cewar Ali, “A’ah islamiyya zaka, ka bari ranar alhamis na kai ka, ka wuni”, Ya tunzura baki ya koma cikin gida, ” Ga wannan ki kai mata”, Mallam ya fad’a yana mik’a mata bak’ar leda, gasasshen nama ne mai yawa, Aliya ta karb’a tana fad’in “Sai na dawo”, ” A dawo lafiya”

     
       Daga d’aki ta jiyo sallamar Aliya, A daddafe ta fito, jiri ke d’ibar ta, Kallo d’aya Aliya ta mata tasan bata da lafiya, “Umma ina wuni?”, ” Baki da lafiya ne?”, “Ciwon kai da zazzab’i”, Ta fad’a tana zama,

     ” Subhanallah kinsha magani?”, “Eh nasha panadol”, ” Ai panadol ba zai miki magani ba, kuje asibiti”, Ta gyad’a kanta, “Kinci abinci”, ” A’ah”, “Meyasa?”, ” Bazan iya dafawa ba”, “Bara na shiga na dafa miki”, Ta fad’a tana cire mayafi.

     Bata d’auki lokaci ba, kasancewar akwai komai a kitchen d’in, Ta dafa jollof, Fetta ta kira ta bata foodflask ta sakawa Suraj, ta ajiye masa a dining table kamar ko da yaushe.

   Aliya ta tilasta mata cin abinci, Tana yin spoon uku sai amai, A rud’e tayi kanta tana mata sannu, Ta zaunar da ita, ta gyara wurin, Ta bata naman da Malam ya aiko mata, Shi taci sosai.

   Sai kusan magrib ta tafi, A bakin gate taci karo da Aunty Jummai da Bilkisu, Ta musu sannu, Aunty Jummai ta bita da shegen kallo, ” Ya’ta auri mai kud’i, kullum ana hanyar gidanta cin arzik’i “, Aliya tayi gaba abunta ba tare data nuna tasan da ita take ba.

STORY CONTINUES BELOW


    Sashen Hajiya suka yada zango, ba kowa a falon, Sai sanyin Ac da k’arar TV dake tashi, Aunty Jummai ta zauna kan kujera tana fad’in ” Wash”, Bilkisu tace “Nayi missing wannan ni’ima, Allah ya nuna mun na dawo”, Aunty Jummai ta amsa da ” Amin”

   Kusan minti 15 suna zaune, sun saki baki suna kallo da shan AC.

    Hajiya ta fito, “Jummai yaushe kuka zo?”, ” Munyi kusan minti 20″, “Shine baku aika an kirani ba, ko ku shiga ciki”, ” Kallo ne ya d’auke mana hankali”, Tayi dariya, “Ina wuni?” Bilkisu ta gaisheta tana duk’awa har k’asa, “Lafiya lau”, Ta amsa da sakin fuska

    Aunty Jummai ta shiga jan ta hira da son jin ko Suraj sun rabu da Fetta.

     Suraj a gidan marayun sa ya wuni, Ya tattauna da yaran kan matsalolin su, da gyare-gyaren da za’a yi.

   Yana idar da sallar magrib ya nufo gida, Ya kwaso yunwa sosai, tun breakfast na safe ne a cikin sa, Direct dining area ya nufa, Yayi serving kansa,  Spoon d’aya yayi ya tabbatar masa ba ita ta girka ba,

     ” Yau kuma wani sabon salo tazo dashi naba wani yayi girki”, Ya fad’a yana mik’ewa ya nufi d’akin dan jin dalilin ta,

     A kwance ya tarar da ita, ta lullub’e tana rawar sanyi, “Are u ok?”, Ta jiyo muryarsa, Jikinta yayi tsanani, bata jin zata yi tashi, Ganin ta mishi shiru, ya k’arasa bakin gadon, Ya janye bargon, hucin zafin jikinta yaji,

    Hannun sa ya d’aura kan wuyanta yaji zafi sosai, Yana k’ok’arin d’agota k’amshin turaren sa ya daki hancin ta, Ta shek’o masa amai a jiki, A rud’e yake jera mata ” Sannu”, Ya cire rigarsa, Ya tsaftace wurin, Hijab ya d’auka ya saka mata, Ya kamata,

   Fetta tayi lamo a jikinsa, ba k’aramin jin jiki take ba, Yana jin zafin jikinta a jikin sa, Ya nufi mota da ita, Ya kwantar da ita seat d’in baya, Yaja motar zuwa asibiti.

   Mintuna kad’an ya kawo su asibitin , ba k’aramin gudu yayi ba.

   Ba b’ata lokaci suka samu ganin Dr, bayan ya mata gwaje-gwaje, Ya kallesu da murmushi d’auke a fuskar sa yace “Congratulations matar ka na d’auke da ciki na wata d’aya da sati biyu”, Suraj a zabure yace ” Kana nufin am going to be Father “, Dr yayi nodding kansa, ” Alhamdulillah “, Ya furta yana jin farin cikin da bai tab’a ji ba na ratsa shi, bai san yana son yara ba sai yau, bai san yana son ganin jinin sa ba sai yau,

    Fetta runtse ido tayi cike da tashin hankali, ” Ciki”, Ta nanata a ranta, “Wanda baya sonta, baya k’aunarta, tasan watarana zai rabu da ita, zata haihu tare da shi, banda zubar da ciki haramun ne, wallahi da ta b’arar da shi, yanzu ya zata yi”,

     Shawarwarin da Dr ke basu ya katse mata tunani, Har lokacin idonta a lumshe, tana jin kanta na sara mata, Drugs ya rubuta musu tare da addu’ar sauka lafiya,

    ” Tashi mu tafi”, Ya fad’a yana rik’ota, Jirin da take ji yasa ta yarda, Ya rik’eta har zuwa mota,

   Pharmacy ya tsaya ya siya drugs, A kusa dasu ya siya kaza, Ya nufi gida zuciyar sa tamkar an zuba masa k’ank’ara tsabar farin ciki.

    Shi ya rik’ata har zuwa cikin gida, Ya zaunar da ita kan gado, Ya d’auko plate a kitchen, ya saka kazar,

    Ya zauna kusa da ita ya d’iba fata, “Bud’e baki”, ” Na k’oshi”, “Baki isa ba, ba zaki bar mun baby da yunwa ba”, ” Toh fah sabon salo”, Ta fad’a a ranta,

   Kallon da ya rik’a jefar ta dashi, Yasa dole ta bud’e baki, Kallo ne mai kashe gabb’an jiki da jefa ka a wani yanayi, Suraj ba baya ba, Ya nak’allaci salon kallo.

    Ya shiga feeding d’inta, sai da yaga tana kakarin amai, ya daina, Ya bata magani tasha, Ya umarceta ta kwanta, Rigarta ya d’aga ya sumbaci cikin ta, “Sleep well my baby”,  Yaja bargo ya lullub’e, Ya fice d’akin, ” Oh ni”, Tana sauke ajiyar zuciya.

   Sashen Hajiya ya nufa, har lokacin Su Aunty Jummai na nan, Suka shiga gaishe sa, Ya amsa da sakin fuska, Farin ciki ya lullub’e su a tunanin su asirin su ya fara tasiri.

    Kusa da Hajiya ya zauna, Yana fad’in “Albishirin ki Mama”, ” Goro fari tass”, Aunty Jummai da Bilkisu suka kasa kunnen jin me zai ce,

   “Kin Kusa samun jika”, ” Da gaske”, Ta fad’a da matuk’ar farin ciki, Ya d’aga mata kai, yana mik’a mata result da Dr ya basu,

     “Alhamdulillah!”, Ta shiga nanatawa ba zata iya misalta farin cikin da take ciki ba.

    Aunty Jummai k’irjinta yayi mummunar bugawa, hankalinta ya tashi, Yayin da Bilkisu taji tamkar ta d’aura hannu a kai ta kurma ihu.

   Aunty Jummai tayi k’ok’arin b’oye yanayinta ta hanyar fad’in ” Allah ya raba lafiya”, Bilkisu da k’yar ta iya cewa “Nayi murna”

   Suka mik’e suka ce zasu wuce, Dan idan suka zauna, bak’in cikin su ba zaa b’oyo ba sai an gano su.

   Suraj ya zaro kud’i a aljihun sa da bai san adadin su ba, ya mik’a musu, Bilkisu tayi k’arfin halin karb’a, kud’in sam basa d’okin su a halin yanzu.Tamkar wad’anda akaiwa mutuwa haka Aunty Jummai da Bilkisu suka isa gida, Fuskar su sam babu walwala. +

    Kujerar dake tsakar gida Aunty Jummai ta zauna tana fad’in “Fetta da ciki tirk’ashi”, Bilkisu tace ” Umma idan ta haihu na shiga uku”, “Ke dallah daina kiran ta haihu, ke har fata kike ta haihu”, Bilkisu ta girgiza kai, ” Bamu ga ta zama ba, kawar da cikin shine mafita”, Bilkisu tace “Ban tab’a jin tashin hankali irin na yau ba”, Aunty Jummai tace ” Nifah yarinyar nan gani nake tamkar tana tsafi, kome muka mata baya kamata” (K’arfin addu’a kenan”, “Ba zata rasa tsafi ba, duk asirin mu baya cin ta”, ” Ba tsafi take ba, ko itace bokan sai na b’arar da cikin”, Tayi assuring kanta.

    Fetta kusan awa biyu ta d’auka tana bacci, A hankali ta bud’e idonta tana jin ta wasai, Zazzab’in ya sauka, ciwon kan ma ya rage sosai, Suraj dake zaune kan kujera yana operating system, Ya d’ago kai ya kalleta, Idonsa cikin nata, Gira ga d’aga mata alamar “Ya dai” Kawar da kanta tayi gefe,

      “Ya lafiyar babyna?”,  Ba ma lafiyar ta yake ba, ta babyn sa, Haushi taji ya bata, da jin dama cikin ya b’are, Banza ta masa tana nufar hanyar toilet, Ji tayi ya juyo da ita, suna fuskantar juna, Hannun sa ya d’aura saman wuyanta, Yaji babu zafi, Ya shafa cikinta yace ” Allah ya k’ara ma babyna lafiya”, Da kallo tabi sa, Ya kashe mata ido d’aya, Yana ficewa d’akin,

    “Huu”, Ta fad’a tana sauke ajiyar zuciya, Ta shiga toilet, Ruwa masu d’umi tayi wanka dasu, Ta k’ara jin k’arfin jikin ta.

    
   Fitowar ta falo yayi daidai da shigowar sa tare da Hajiya, da wata Yar’ budurwa a baya d’auke da basket na abinci.

    ” Ina wuni?”, Ta gaishe da Hajiya tana rissinawa, Hajiya tayi saurin d’agata “A’ah tashi, ki daina duk’awa kinsan bake kad’ai kike ba”, Kunya taji ta zauna k’asan carpet tana sunkuyar da kai, Fetta bata tab’a zama kan kujera, Hajiya na zaune, wanda hakan ke k’ara sa Hajiya ganin tarbiyar ta.

   ” Ajiye abincin kan dining”, Hajiya ta umarci yarinyar, “Tuwo ne nayi miki da kaina, kici zaki k’ara jin k’arfin jikin ki”, ” Mama ki mata fad’a, sam bata son cin abinci”, Cewar Suraj yana tsare ta da ido, “Fetta ki rik’a cin abinci kinji, kinga yanzu bake kad’ai kike ba”, Tayi nodding kai, ” Ga yarinya na samo miki, zata rik’a zuwa tana taya ki aiki”, Ta amsa da “Toh”, tana godiya, Dan kar Hajiya taga ta mata gwaninta, ta nuna bata so, yasa ta amince da zaman mai aikin, sam bata son mai aiki, ” Zan koma, tana sashena idan kina buk’atar aiki, ki aiko a kirata”, “Toh” ta amsa.

    Ta mik’e ta fita, Yarinyar tabi bayanta.

   Suraj mik’ewa yayi ya shiga kitchen, Ya d’auko plate, Yayi serving tuwo,

    Kusa da ita ya zauna, Ya ajiye plate d’in a k’asa, “Babyna zanyi feeding”, “Ya k’oshi”, Ta fad’a tana k’ok’arin mik’ewa, Ya jawota ta fad’a kan laps d’inta, Saurin sauka tayi, ” Wallahi zan miki d’ure”, Da kallo mai cike da takaici tabi sa, Ya d’aure fuska “Ba za’a haifar mun baby ramamme ba”,

    Tuwon ya d’iba ya nufi bakinta dashi, Ta kawar da kai, Yasa d’ayan hannun ya juyo da kanta, ” Kina so na baki na bakina”, Ya fad’a fuska ba alamar wasa, bata tanka sa ba, har ga Allah bata jin tuwo, Ganin yana k’ok’arin sa tuwon bakinsa, Tayi saurin bud’e baki,

     Ya saka a bakin sa, Ya kamo bakinta ya matse ya juye mata tare da had’e bakinsu wuri d’aya, ba shiri ta had’e, “Zaki bud’e baki, ko na cigaba da miki haka”, Bakin ta bud’e ya shiga bata, Zuciyarta fal da takaicin sa.

STORY CONTINUES BELOW


    Kusan rabin tuwon ta cinye, Ya d’auke plate, Ya bata drugs tasha.

     “Gwaggo Dan Allah kiyi hak’uri ki bari na auri Karima, tunda Su’ad tak’i ni”, Harara ta watsa mishi tace ” Idan ka sake mun maganar Karima wallahi ranka sai yayi mummunan b’aci kaji na rantse”, Yayi shiru zuciyar sa cike da takaici, “Su’ad ko Safeena zaka aura, mahaifin ka zai je nema maka auren su, Nasan Hajiya ba zata watsa mana k’asa a ido ba”, ” Gwaggo auren dole fah kenan za’a musu”, Dak’uwa ta masa tace “Kaci uban ka, lokacin da na auri ubanka ban tab’a ganinsa ba sai ranar da aka kawoni, Ku ai kun tab’a ganin juna kuma jini d’aya kuke, yaro tamkar wanda aka shanye baka da zance sai Karima”

    “Ka gaggauta cire zancen auren Karima a ranka, in dai nine mahaifin ka bazan aura maka ita ba”, Kawo lamid’o ya fad’a yana fitowa daga d’aki, ” Yawwa gara yaji daga bakin ka, sai yafi maida hankali”, “Banda baka san ciwon kan ka, Karuwa zaka auro yarinyar da Suraj ya fasa aure akan tayi cikin banza, ta gagari iyayenta balle kai, Toh ahir d’inka, Su’ad ko Safeena zan nema maka aure, tashi ka bani wuri”

    Ya mik’e ya fita, yana jin zuciyarsa tamkar ana hura masa wuta.

     “Assalamu alaikum ina masu gidan?”, Yasmeen ta fad’a tana shigowa, sanin Suraj baya nan, bata ga motocin sa ba.

    Fetta dake kwance ta amsa sallamar, ” Lafiya kika wani kwanta ko dai kin harbu, naga kin k’ara cikowa”, Yasmeen ta fad’a cike da tsokana, Tashi tayi ta zauna tace “Hmm ina cikin damuwa”, A rud’e Yasmeen tace ” Meke damun ki, ina fatan ba wani misunderstanding kuka sake samu dashi ba”, “Idan wannan ne da sauk’i”, ” Toh meya faru?”, “Ciki ne dani”, Ta k’arashe da hawaye,

    Dariya Yasmeen ta kwashe da ita, Tace ” Ban tab’a jin zancen mai dad’in wannan ba, Alhamdulillah, na kusa zama mother”, Wani banzan kallo ta watsa mata tace “Bansan bakya sona ba sai yau”, Hawaye na cigaba da ambaliya saman kumatun ta,

     ” A masoyanki idan ban zo ta d’aya zan zo ta biyu”, “K’arya kike tunda kina murna zan haihu da wanda baya k’aunata, baya ganin daraja ta”,

   Yasmeen ta kamo hannun ta, Cikin sigar lallashi da kwantar da hankali tace ” Suraj yana sonki, ta hanyar cikin nan, soyayyarki zata k’ara kama zuciyar sa”, Fetta ta girgiza kai tace “Baya sona, Cikinsa yake so”, ” Kin tab’a ganin inda aka so da’ aka k’i uwar sa, tunda har yake son cikin dake jikin ki, tabbas yana sonki, da sannu zai yi realising “, ” Bana so na haifi yaro ya tashi cikin maraici kamar yadda na tsinci kaina”, “Ba zai tashi ba In shaa Allah, ki kwantar da hankalin ki, kina addu’a”, Tayi shiru zuciyarta na mata sak’e sake, A yadda taga yana son cikin, zai iya karb’e yaron, ya rabu da ita, bata san tarbiyar yaronta a hannun wa zata koma ba, Rashin uwa maraici ne babba, tayi going through, bata so yaronta ya tsinci kansa.

    Yasmeen ta cigaba da bata shawarwari da k’ok’arin kwantar mata da hankali, Sosai ta rage mata damuwa tare da jin natsuwa.

      Feena ta shigo d’aki tamkar an jefo ta, ” Lafiya Sis?”, Su’ad ta tambaya, “Mama naji tana waya wai Fetta nada ciki”, Su’ad ta zaro ido tace ” Ciki”, “Wallahi k’warai”, ” Tabb zamanta ya tabbata a gidan nan, data fara haifar yara shikenan”, “Wallahi banso tsatson Ya Suraj ya fito daga matsiyaci ba”, Su’ad tace ” Ke ko ni, har na fara masa sha’awar Su’ad yar’ gidan Matawallen kano, ga kud’i ga sarauta”, Haka suka cigaba da jimamin cikin Fetta, ransu sam ba dad’i.

     Fetta ta samu k’arfin jikin dafa masa jollof na taliya da ta sha sardine, Bayan ta kammala, ta sake wanka, A falo tana kallo bacci ya d’auke ta, Cikin na sata bacci sosai.

    Suraj cike da leda na kayan k’walama ya dawo gida, Kallon sa ya kai gareta, fuskarta tayi fayau ta k’ara fresh da kyau, Ga dukkan alamu a takure take baccin, Ledar ya ajiye, Ya d’auke ta tamkar baby, Ya nufi d’aki, Ya kwantar da ita, Yana k’ok’arin rufe ta da bargo, Ta bud’e ido cikin nasa, Ya d’age mata gira, Tayi saurin mayar da idonta ta rufe, da mamakin sabuwar d’abi’ar da ya dauka ta kashe ido d’aya da d’aga gira,

    “Dama lamo kika yi, dan na d’auke ki”, ” Idan ma lamo nayi na saka ka d’aukeni”, Ta fad’a har lokacin idonta a rufe, “Kinci daraja d’aya da na baki hukuncin mayar mun da magana”, Yana fad’ar haka ya fice falon,

    Foodflask dake dining table ya bud’e, k’amshin girkin kad’ai yaji yasan ita ta girka, Ya zauna yaba ciki hakk’in sa, Ya d’auki ledar da ya shigo da ita ya nufi d’aki.

     Sai da ya tabbatar taci shawarma da yoghurt, tasha magani, Suka kwanta bacci.

   ” Mallam na kasa ganewa, ina cikin tashin hankali, ana aiki tamkar ba’a yi”, Cewar Aunty Jummai, Malam ya nisa yace “Wato abunda ke faruwa, Yarinyar tsafi take da bak’in aljanu”, Aunty Jummai tace ” Dama nasan za’a rina”, “Yanzu zaki bada dubu talatin a karya asirin ta”, Tace ” Toh gobe zan dawo na kawo”, “Sai kin zo”, Ya fad’a,

    Aunty Jummai a ranta tace ” Na gama aiki dakai, tana aiki da bak’in aljanu, k’asungurmin boka zan nema yamun maganin ta”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *