RAI BIYU
CHAPTER 15
Dago kai ya yi da sauri domin ganin wanda ya hana hamnunsa zuwa ga gudan jininsa, ganin Nawwara cikin bachin rai da daure fuska yasa shi mikewa tsaye sai ya kama duka hannayensa biyu yana kuka kamar zai narke a gurin.
“Naw…..” +
Fisge hannayenta ta yi ta ture da dukan karfinta.
“Karka kuskura ka taba min ɗa, hauka ta daina dibanka kana taba jikina ni ba halalinka ba ce” 1
Ta fada cikin wani irin zafin rai. Doc Ismail ya karasa ya rika Jibril yana kallon Nawwara tare da fadin
“Amman ke baki da mutunci ta ya zaki wulakanta babban mutum kamar Jibril a gaban mutane” 1
“Babu ruwanka karka saka min baki a nan”
Jibril ya share hawayen da suka ki tsaya masa ya nufi gurin Noor sai ta tsaya masa tsawa hawaye na zuba a idanuwanta.
“Karka taba min yaro”
Rike shi Doc Ismail ya yi ya ce da Nurses din su wuce da Noor, a gurin Nawwara ta zube kasa saboda jirin da ya dibeta, Doc Ismail ne ya kira wasu Nurse suka kamata suka mayar da kin da ta baro. Hakan ya bawa Jibril damar shiga dakin da aka kai Noor. Ko da ya shiga ya samu Nurses din suna daurashi saman gadon sannan suka saka masa robar jini daya. Fita suka yi daga dakin baya sun gama komai sai Jibril ya karasa inda yake ya durkusa kasan guiwowinsa gurin gadon wasu sabbin hawaye suna zubo masa.
Ko da bachi yake ya farka ya kalli Noor yasan dan sa ne, fuskarsa ce shinfide a fuskar Noor babu inda Noor ya rage shi da komai, hannu ya kai ya rika hannun Noor sai yaji wani irinsa ya shiga hannunsa jini ya hadu da jini Noor din ma da be san inda hankalinsa yake ba sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Kuka Sosai jibril ke yi irin kukan da aka san mata da yinsa, sai kuma yaja hannun Noor ya kai a fuskarsa ya lumshe ido, yana ta goga hannun a fuskarsa, sannan ya yi masa kiss sai kuma ya soma shinshinar hannun kamar zai cinyeshi.
“Am sorry Son, ka yafe min na wulakanta akan haukana, mahaifinka ya tuba ya gane kuskurensa na yi nadama, ban san miya shiga kaina ba ban san miyasa na aikata ba, am really sorry for what i did, please forgive me”
Ya kara fashewa da kuka har numfashinsa na son tsayawa, shigowar Doc Ismail ne yasa shi tsagaita kukan ya dago ya kalleshi.
“Wai miyake faruwa ne? Miye alakar ka da wacan matar ne? Na san dai wannan ba dan ka ba ne ko?”
Tambayar da Doc Ismail ya yi masa kenan.
“Dana ne, ita kuma mata ce”
Daga haka Doc Ismail be kara cewa komai ba, yasan Jibril baya cikin yanayin da zai iya yi masa bayanin komai a yanzu, after that be kama ya saka kanshi akan matsalar iyali ba. Juyawa ya yi ya fice zuciyarsa cike da mamaki bakinsa kuma gumde da tambayoyi.
NAWWARA POV.
Ban san iya awanin da na dauka a sume ma ba, ina farkowa na ji goshina ya cika da nauyi har bana iya gani sosai.
“Sannu”
Muryar Inna ce take gaisheni sai na gyada mata kai dan bana iya magana a wannan lokacin, na dade ina kallon silin sannan idanuwana suka dawo daidai har ya kalleta.
“Ina Noor?”
“Yana can an kaishi wani dakin”
Sai a yanzu na tuno da abunda ya faru, ashe fa wannan suma ta biyu ce na yi.
“Inna miyasa kike bari Jibril ya zo har ya ga Noor”
“Ba zan iya ce miki ga dalilin zuwansa ba, ban kuma san ta ina ya ji ba, nima na tafi neman jini ko da na dawo na tarar ya bada jininsa kuma ya sa an canja miki daki an dawo da ke a nan, shi kuma yasa aka kai shi dakunen nan masu tsada”
STORY CONTINUES BELOW
Na yi sauri sauka saman gado duk da ina jin jikina kamar babu gwari sosai. na fita daga dakin na mike hanya har na isa manyan dakunan, na bude na farko ba shi bane na biyu ma haka na uku hudu biyar haka na bi dakunan sai da na kai daki na bakwai ina turawa sai na hango Noor kwance Jibril kuma zaune saman kujera ya dora kansa gurin jikin Noor hannun Noor kuma a saman kansa dayan hannunsa kuma na sanye cikin na Jibril.
Ban damu da na rufe kofar ba na karasa kusa da gadon cike da tausayin halin da Noor yake ciki, ina tsayawa dai dai kan Jibril sai ya bude idanuwansa da suka kumbura suka ja a hankali ya kalleni, sai kuma ya lumshe.
“Jibril tashi ka fita”
Na fada a tsawace, sai ya bude ido ya yi ma hannun Noor kiss sai ya sake shi, na yi zaton tsaye zai tashi sai kawai na ga ya zube kasan gwuiwowinsa ya fashe da kuka yana hade hannayensa.
“Ki dubi girman Allah Nawwara, ki sassautawa zuciyarki dan Allah ki yafe min, Wallahi na canja dabi’u da halayya duka na canja ki ceci raina kuma ki ceci ran yarona ki taimakeni ki yafe min ba ni da wani buri da ya wuce na ki da na wannan dan nawa, please Nawwara for the sake of our Son ki hakura mu sake sabuwar rayuwa, zuciyata na cike da kuna ina bakincikin abunda na yi muku, kaina a kasa yake ki taimaka min ki bani damar da zan gyara laifina, ba ni buri sai na ki, ki min masauki a gefen zuciyarki dan Allah Nawwara” 9
Hawaye na zuba a idanuwansa yake min wannan rokon da ya soma karyar da zuciyata, nima na fara hawaye.
“Bata lokacinka kawai kake Jibril, ka fitar da ni a ranka ka manta da ni a duniyarka, kai ba tsarata ba ne, na rumtse ido daga kallo duk wani abu da ya shafi rayuwata”
“Ji ceci rai Nawwara, idan yanzu na fadi na mutu ke ce sila, ki taimaka ko dan dan mu”
“Dan mu? Ko da na? Dan da ka ce ba naka ba ne? Ka wulakanta ni saboda cikinsa? Dan da tun da ka turo ni gidanmu ba ka taba saka kafarka ka zo duba shi ba? Dan da baka san cin sa ba baka san shansa ba? Dan da baka san ya rayuwarsa ta ke ciki ba? Dan da ka kasa yankawa ragon suna kasa a ka kirashi da shege? Mahaifina shi ya yanka masa rago ya saka masa suna, yanzu har kana da bakin da zaka kira shi da danka? Kana da idon da zaka zo rana tsaka ka kalleshi kuma ka fada masa kai ne mahaifinsa? Ta wace fuskar zai kalleka? Taya zai kiraka Uba?” 7
Tun da na soma magana ya rumtse ido ya matse hannayensa da ke hade guri daya yana cizo baki, da alama maganar tawa bata masa dadi, sai kuma ya dago fuskarsa da ta yi ja ya kalleni.
“Fada min abunda zan yi wanda zai sa ki yafe min, fada min tafarkin da zan bi Noor ya karbe ni a matsayin ubansa? Taimakeni Nawwara, ki tausayawa rayuwata zan yi komai kike so am ready to die for you”
“Ka wuce sanina Jibril, kaje ka nemi matar da zata so ka ta aureka ta haifa maka yaya, shawara daya zan baka kaje ka yi abunda zai taimaki rayuwarka ina maka fatar samun irin matar da kake so Allah baka sa’a” 1
Mikewa ya yi tsaye ya fice cike da nauyin kafafu, ba tare da ya share hawayen da ke fuskarsa ba. Ni kuma na zauna kusa da dana ina kukan da ban san na minene ba, tausayin da na ko kuma rayuwar da na cinci kaina a ciki.? 2
Bayan sallah isha’i Jidda da mahaifiyarta suka zo duba Noor, daman tun da magariba wasu daga cikin mutanen babban gida suka zo duba shi. Bayan fitarsu sai ga Bilal ya shigo hannayensa da ledoji har gudu hudu har kuma lokacin Noor be farka ba gaba daya hankakina ya tashi duk da likitan ya fada min zai dauki tsawon lokaci yana bachin. Kallo daya na yi ma Bilal na kawar da fuskata, bana ganin komai sai wacan abun da ya faru shekaranjiya wani irin kishi da bakinciki sai suka taro min har na ji kamar na dauki wukar da aka aje ta yanka lemu na daba masa a kirji.
Da Inna ya fara gaisawa sannan ya gaishe da wata abokiyar Inna suka gaisa da Sakina, sai duk suka tashi suka ba mu guri, daya ya zama daga ni sai shi sai kuma Noor da baya cikin hayyacinsa. 1
STORY CONTINUES BELOW
“Nawancy… Wallahi ba abunda kike tunani ba… ”
Hannu na daga masa
“Kai ko Zinatu ko wani abu da ya shafi rayuwarku a yanzu be dame ni ba”
“I know i shouldn’t, ya jikin Noor?”
“Da sauki”
“Allah ya kara sauki”
“Amin”
Bayan wannan bata maganar bata sake shiga tsakanin mu, da ya gaji da zama ne ya mike tsaye ya karasa kusa a Noor cike da nuna kulawa ya duba shi sannan ya kalleni ya ce
“An kama wadanda ya kade sa?”
“Ya gudu, amman mutane sun ce da gangan mutumen ya yi cikinsa da mota ya kadesa, kuma likitan ya ce min Noor ya karye a hannu” 17
Na fada ina fashewa da kuka.
“Sorry a wani waje ne?”
“Sun taso makaranta ne, mutunen ya gudu”
“Amman Mahaifinaa ya sani?”
Wani kallo na watsa masa na sakar masa idanuwana ina ta kallon fuskarsa cike da tsanar furucinsa.
“I mean Jibril”
“Kaima kana cikin mutanen da je ganin laifina akan Jibril ko?”
Yayi saurin komawa ya zauna.
“No ba hakan na ke nufi ba, Jibril ya wulakanta ki Nawancy kuma ya cancanci ko wane irin sakamako daga gareki, Wallahi ko ke ce baki da gaskiya i will support you ballantama kina da gaskiya, kawai bana son abubuwa su miki yawa ne, tunani a yanzu ba na ki ba ne, ki sassautawa zuciyarki, kuma ki rika neman shawara akan abunda ya shige miki duhu”
Na share hawayena na maida idanuwana gurin da na, sai na cinkayo muryarsa yana fadin.
“Ni kaina ban san ranar birthday dina yayi ba, sai a Facebook, su suka turo Zinatu kuma friend dita ce a fb few weeks ago ta turo min friend request na yi accepting ba tare da tunanin komai ba, ta yi min happy birthday tun ana saura kwana daya na yi birthday na, ina tunanin ta nan ta gane xan yi birthday a ranar har ta siyo wannan cake din, ina zaune ta shigo da shi ta kira abokan aikina ban ma san ta kira ki ba sai da na ganki office din” 1
“Mi zai sa ta yi haka? Daman can tana son ka?”
“Gaisuwa bata taba shiga tsakanin da Zinatu ba, idan har kiga na mun hadu sai idan aiki zamu yi, ina tunanin ta yi hakan ne saboda ta shiga tsakaninmu ko kuma…”
Sai ya yi shiru be karasa ba.
“Ko kuma me? Jibril ne ya sata ko? Zai iya saboda mugu ne”
“Ni dai iya abunda na ke son ki sani, ba zan taba cin amanarki ba”
“Amman miyasa ka yi blocking din number ta? Kuma ina ta tura maka sako baka min reply”
“Saboda na baki damar yin tunani da zuciyarki, ina ganin kamar ina kan hanyar da ba zata bulle ba ne, zuwan Jibril a karo na biyu cikin rayuwarki ya karyamin kuzari, bana son na shiga tsakanin farincikinki da kuma tunaninki, bana son na yi abunda zai raba hankalinki gida biyu, na yi hakan ne saboda na daga miki kafa kuma na samawa rayuwata mafita saboda bana so na rasa a take, zuciyata na raya min kamar ba zan aureki ba Nawancy, kin ki bani damar da zan ga magabatanki kuma gashi Jibril zai yi duk abunda zai yi wajen ganin ya mallakeki”
Tausayinsa ya kamani, duk da kasancewar ni ma ina tausayin kaina. 1
“Kokarin mallakata yake Bilal kai kuma tuni ka malleke zuciyata, idan har Nawwara bata auri Bilal ba to ban cancanci auren ko wane irin namiji ba a duniyar nan, na fara rayuwa sau daya sai kuma na mutu, kai ne ka dawo da ni duniyar da mutane suke rayuwa, ka yi nasarar canjani daga mutum mutume zuwa mutum wacce ta san mi ake nufi da rayuwa, na rayu a lokacin da rayuwa take da muhimmanci a gareni, sai Jibril ya kashe min ruhi kuma ya kona shi ya maidashi toka ya shekarda da shi ya bi iska, kai ne mutumen da ka hada tokar ruhina ka tattarata ta sake zama cikakken ruhi na maida shi a cikina, har zuciya ta bude ta kamu da son ka.
Kai ne kadai mutumen da nake so Bilal kai ne mafarkina, burina idan har ka ga ban aureka ba ka tabbatar gawata ce ta ke magana ba ni ba”
Lumshe ido ya yi ya hade yawu sannan ya bude kamar dai be yarda da ni ba, sai ya mike tsaye yana fadin.
“Idan kina bukatar wani abun ki fada min, ko ki kirani, ina son ki san da wannan Nawancy ina sonki sosai ina kaunarki kauna ta hakika” 12
Da kallo na bishi har ya fice, sannan na juyo ina share hawayena na kalli Noor da ke motsi.Bayan fitar Bilal su Inna suka shigo tare da Mama Turai wato Yayar Inna wacce suke uwa daya uba daya. Inna ta zauna saman tabarma ita kuma ta zauna saman kujerar da ke gefen gadon ta Kalli Noor sannan ta kalleni ta ce. +
“Innarki ta labarta min komai, kuma abunda kike ba ki kyautawa, tun da har ya tuba ya dawo ya nemi ganin dansa ai sai ki bashi dama, ke yanzu in ban da Allah ya nufa ko hanya kin isa ki hada da babban mutun kamar wannan balle har ya zo yana rokonki? In wani ne karbe dansa zai yi da karfi ya barki nan, kin samu ya dawo yana neman yafiyarki kina ta masa wasa da kwakwalwa kamar karamin yaro” 6
Na tada kai na kalleta.
“Ke ma laifina kike gani ko Mama Turai?”
“Ai dole na ga laifinki, mutumen arziki irin wannan mai kudi haka, ai sai ki bashi dama ko arzikin nasa ku tatsa ni Wallahi da yana son yata da na aura masa mu ga karshen iskanci” 6
“Amman yanzu har kun manta irin cin mutuncin da cin zarafi da ya yi min?”
“Yanzu ba ya dawo ya tuba ba? Ai Allah ma mukan masa laifi ya yafe mana balle ke da wani be san da zamanki a duniya ba, ke kikan irin laifin da kike yi ma Allah ne?”
Idanuwa sun cika da kwalla saboda na san babu wanda zai fahimce balle ya goya min baya, ni kadai na ke jin abunda na ke ji wata kila saboda ni Jibril ya yi ma abun ba kowa ba. Wannan karon Inna ce ta dora da 6
“Idan har sakamakon Ubangiji kike so tau ko ya kamata ki mika lamurranki gurinsa, ba yin kanki ba ne Allah ne ya jarrabeshi da sonki kuma ya saka masa nadamar abunda ya yi saboda ya jarrabeshi, ki yanzu ba jindadinki ba ne mutumen da ya ce Noor ba dan sa ba ne yanzu har yake risina miki kasa yana neman ki hada shi da dansa? Allah yana son masu yafiya, kuma ba a rama cuta da cuta sai dai a maye cuta da alheri, ina ji miki tsoron kar wannan abun ya dawo kanki, kuma da Noor ya girma ya nemi ubansa ai kara ya girma da Ubansa” 1
Ganin yadda na ke sharar kwalla yasa Inna ta taso ta dafa.
“Na san ya cutar da ke yata amman karki mata shi ma Allah ba zai barshi ba, kuma ba kisan halin da ya shiga ba kamin ya gane cewar ke alheri ce a gareshi, ba dan Jibril yana da arkizi na ke son ki yafe masa ba, sai dan hakan zai wanke ki daga zargin da duniya take miki, kuma Noor zai samu rayuwa mai kyau, ke kuma zaki samu damar gina taki rayuwar a gidan aurenki idan kika auri wanda kike so”
Bani da wani zabin na yafiya ga Jibril saboda yadda Inna take son na yafe masa din, na kan yi kokarin yin abunda duk mahaifiyata take so ko kuwa abun nan baya min dadi, ba dan komai ba sai dan na san ba zata cutar da ni ba, kuma yarda Allah tana tare da yarda iyaye, na yi ma uwar wasu biyayya ma balle tawa uwar wacce ta dauki ciki ta yi nakuda ta haifeni ta raineni na girma, hakika bana da wani farinciki sai na mahaifiyata.
“Zan yafe masa Inna matukar yafe masa din zai faranta ranki, zan yafe masa”
“Na jidadi Allah ya miki albarka kema ya baki yayan da zasu yi miki biyayya”
Ajiyar zuciya na sauke na share hawayen da ke min zuba ina kallon Mama Turai da ke wasar baki.
“Haba ko ke fa, amman ace zuciya kamar ta kafiran farko, Allah ya shiga ya tsakaninku ai mun fi son a shirya” 1
“Dan na yafe masa ba yana nufin zan aureshi ba ne, dan Allah karku tirsasamin yin wani abun daban kuma”
“Babu wanda zai tirsasa miki, wata rana ke da kanki zaki karanta mana sirrin zuciyarki”
Cewar Inna, ni kuma na kalleta na ce
“Zuciyata bata da wani sirrin bayan wanda ke zahiri ke kanki kin san babu wanda na ke so bayan Bilal, be kamata ki zargeni da son wani bayan shi ba”
STORY CONTINUES BELOW
Sai Mama Turai ta taso ta karaso kusa da ni tasa hannunta ta tallafo fuskata yadda zan fuskanceta.
“Tausayin Bilal kike Nawwara amman asalin son yana gurin Baban Noor, ke kanki ba ki san abunda ke damunki ba a yanzu, kina tausayin Bilal amman ba za ki iya aurensa ba, kaddarar da ta hada ku ba zata iya bari ku yi aure ba, saboda ke makwafin RAI BIYU ce a gurin Baban Noor idan babu ke koda ya samu Noor rayuwarsa bata kammaluba, haka ma Noor kina matsayin RAI BIYU a gunsa matsayin uwa kuma uba, babu rabon Bilal a jikinki shiyasa kika kasa bashi dama, Baban Noor kuma be da rabo a jikin kowa ce mace sai ke shiyasa kaddara ta sake hada ku kuma zuciyarsa ta kasa barinsa zama lafiya har sai ya nemo mata yar’uwata, ke ma kuma baren zuciyarki yana gurin Noor da Babansa wannan yasa har gobe ba zaki iya amsa kanki a matsayin cikakiyar mace mai jin kanta a mace ba, kika kasa bawa kowa damar sake aurenki gashi Baban Noor ya dawo. 14
Wani baya auren matar wani Nawwara, da kika auri Faruk baki haihu da shi ba ya mutu ya barki saboda Baban Noor ya samu damar sake aurenki, ko da kin haihu da Faruk sai kin fito saboda kaddara ta yi niyar hadaki da tsohon mijinki Nawwara, kurciya ce take cin ki ke kanki yanzu baki san abunda kike so ba, da yanzu za a daura miki aure da Bilal da ba zaki iya zaman aure da shi ba saboda ba shi zuciyarki ke so ba, kuma kaddara ba zata barku ku yi zaman aure ba, ya kamata ki yi tunani karki aikata abunda zai cutar da ke”
Tana gama fada min haka ta kalli Inna ta ce.
“Ni na tafi Allah ya ba Noor lafiya”
Binta Inna ta yi suka fita tare suka barni a dakin ina faman hawaye, ba zan iya bari kalaman Mama Turai su yaudari zuciyata ba, tabbas ni dai na san Bilal na ke so kuma shi zan aura, ba zan zargi Inna ma domin nasan bata cikin irin mutanen nan da ke son yayanta su auri mai kudi, amman wani lokacin ina ganin kamar saboda Jibril yana da kudi ne yasa take son shi, duk da kasancewar Bilal ba talaka ne talak ba, yana da aikinsa kuma ya yi karatu familynsa ma suna da rufin asiri, amman zuciyar Inna ta fi karkarta gurin Jibril. 6
Motsi Noor ya sake yi a karo na biyu har yana kokarin bude idonsa yana motsi da hannu.
“Momy… ”
Na yi saurin share hawayena na kama hannunsa.
“Na’am Noor sannu ka ji”
“Momy da zafi sun jimun ciwo sosai”
“Kyalesu Allah ya isar maka ya baka lafiya”
Ya kalleni da idanuwansa da suka yi fari sosai, sai kuma ya kalli gefena.
“Momy na yi mafarkin Babana ya zo nan”
Gabana ya fadi.
“Wane Baba kuma?”
“Wanda ya rasu”
Ajiyar zuciya na sauke.
“Wanda ya rasu ai baya dawowa Noor, mafarki kawai ka yi”
Na shafa kansa sannan na mike na fita dan kiran likita.
JIBRIL POV.
Da taimakon Allah ya isa gida, zuciyarsa ta yi masa mugun nauyi, ko parking din kirki be yi ba ya fito ya nufi main house jiri na dibansa, yana shiga falo na fadi a bakin kofa yana tari a wahalce gubar da ya taba ci ta taso masa ta hadu da dattin cocaine dake cikin huhunsa (lung) sai aman jini, har idanuwansa suka canja kala kamar ba zai rayu ba, gashi falon babu kowa sai shi kadai. Tun yana iya gani har ya koma yana gani dishi-dishi sai kuma numfashinsa ya soma nisa hankalinsa ya ba ce 6at.
Ko da ya farka an dora masa kyalle mai sanyi saman kai, yana kwance saman doguwar kujera, Siraj na zaune kusa da shi Zinatu kuma na fuskantarsa fuskarta dauke da tausayinsa. Unkurawa ya yi ya tashi zaune sai ta yi hanzarin miko masa ruwan gora mai sanyi ya karba ya sha.
STORY CONTINUES BELOW
“Yaushe kuka shigo?”
“Tun dazu, gashi har an yi magariba kana sume, Zinatu ce ta gyara gurin kuma da taimakonta muka doraka saman kujerar nan”
Cewar Siraj, sai Jibril ya tada kai ya kalleta ya ce
“Thank you”
“Never Mention Allah ya sauwake ni zanje gida”
“Ba zaki bari na sauke ki ba?”
Ta kalli Siraj da ya yi maganar ta ce
“No zan je da kaina ya kamata ace ina gida by this time, ka kula da abokinka please”
Daga haka ta dauki jakarta ta rayata ta fice, sai Jibril ya unkura zai tashi kirjinsa ya yi masa wani mugun tsuka hakan yasa shi saurin komawa ya zauna yana yar kara.
Siraj ya dafa shi.
“Ka bari ka kara hutawa mana, Jibril kana matsawa kanka da yawa akan yarinyar nan, direban ka ya fada min ka bi bayanta sai kuma na zo nan na sameka cikin jini, ka rika sassautawa kanka dan girman Allah ina tausayin halin da kake ciki”
Jibril ya kalleshi irin kallon nan da shi kadai ya san fassarasa.
“Miyasa ka ce min ba ni da Nawwara? Bayan kuma ina da shi”
Siraj ya hade yawu da karfi.
“Wane irin kana da shi? Ban fahimce ka ba”
“Na ga dana da idanuwa Siraj dan da na haifa da Nawwara dan me zaka boye min?”
“Wace riba zan ci idan na boye maka? Mi zaisa na boye maka? Amman ka tabbatar dan ka ne?”
“Da na ne, jinina da nasa iri daya ne, kamata da tasa iri daya ce, da ace ba a kade shi ba da ba zan samu ganinsa da wuri ba”
“Amman abun nan ya bani mamaki, sai gaskiya akwai wani a abu a kasa, domin wanda nasa na bincika mana ba zai yi karya ba, shi ya fada mana Nawwara bata da da ko daya, sai idan mutumen dan uwanta ita kuma ta nemi ya boye mana din”
“Taya xaka yi bincike kuma ka nemi dan uwanta? Dan ina ne mutumen?”
“Dan unguwarsu ne, amman abun nan ya bani mamaki amman ka bincike Nawwara ta tabbatar maka da danta ne? Shin yana ma raye?” 2
“Yana raye wani ya kade shi da mota, and nayi duk wanda ya taba min yaro ko da Nawwara ce ba zan kyale ba”
Siraj ya karkato ya kalleshi
“Amman idan kaddara ce fa?”
“Ban san kaddara akan da na ba, da ce ni ta mai motar ya kade zan dauka ko amman da na? No never da yanzu na rasashi fa? Kasan halin da Nawwara zata shiga ko kasan halin da ni zan shiga? Who’s ever that person is i will never forgive him”
Wani gumi ne ya soma saukowa Siraj, Jibril kuma ya mike tsaye yana jin zafin da kirjinsa ke yi ya nufi bedroom dinsa, saurin mikewa tsaye Siraj ya yi ya rufa masa bayan. 14
“Yanzu ya zaka karbi danka hannun Nawwara?”
“Shine abunda na ke tunani, zan yi duk yadda take so wajen ganin ta bani da na”
“Ni abunda na ke tunani mai zai hana ka fara fake love da Zinatu, so that ka samu kan Nawwara kuma ka gane idan har yanzu akwai soyayyarta cikin ranka” 1
Jibril ya kalleshi
“Wani lokacin kana yin abu kamar baka san waye ni ba Siraj, am straight forward, if yes yes if no that’s means no for sure”
“Baka fahimta ba ne Jibril ai fake love na ce, kuma da sani Zinatu zaka yi”
“Ba zan yi ba, ka tafi kawai zan samawa kaina mafita”
STORY CONTINUES BELOW
Cikin sanyin jiki Siraj ya juya har zai fita sai kuma ya juyo ya kalli Jibril ya ce.
“Cocaine…” 27
“No please bar ni na ji da abunda ke damuna”
Ya fada yana daga masa hannu, sai Siraj ya juya kunya kunya da shi ya fice. Bathroom Jibril ya shiga ya sakarwa kansa ruwa sosai sannan ya yi wanka gaba daya tare da alwala ya fito, ya saka jallabiya ya rama sallah la’asar ya yi magariba, yana saman carpet din har aka kira isha’i, bayan ya yi ya taso ya dawo parlor ya shiga kitchen ya hadawa kansa ruwan tea. Sai kuma ya dawo falo ya zauna hoton Noor kawai idanuwansa ke nuna masa, sai ga wayarsa na ringing sai a lokacin ya kula da inda wayar take gefen kofa inda ya fadi dazu. Zuwa ya yi ya dauka sai yaga number Abbah. Gaiswa suka fara yi da Abbah kamin ya rufe shi da fada.
“An fada min baka da aiki sai shan cocaine, ka maida kanka wani kalar mutun, idan ba zaka iya ba zan karbe ragamar kamfanin nan na mika a hannun Siraj tun da ya fika kula” 1
“Waya fada maka ina shan cocaine Abbah”
“Kai ka fada min, kai kullum abun ka gaba yake ba baya ba”
“Ka yi hakuri Abbah zan canja”
“Da ya fi maka”
Daga haka Abbah ya kashe wayar. A ranar Jibril be gi bachi ba sai ya tashi ciki dare yana ta sallah nafila abunda be taba yi ba a tsawon rayuwarsa, kuka ya yi sosai ya kaima Allah bukatarsa, shiriyace a cikin abubuwan da ya fi roko sai kuma Nawwara, da asuba ma bayan ya yi sallah asuba ya dora da istigifari yana kankantar da kansa yana neman Allah ya yafe masa.
Washe gari ya kira wani abokinsa ya hada shi da mai tattoo ya zo har gida ya wanke masa tattoos dake wuyansa da kuma na sunan Nawwara da ke hannunsa.
Bayan mutanen ya fita ya shiga kitchen ya soma kansa kwai duk da yana da kuku be nemi ya yi masa ba sai ya hada tea da kansa, a dinning room din kitchen ya zauna yana ci sai ga Siraj ya shigo, bayan sun gaisa ya zauna shima ya zuba ma kansa yana ci, bayan sun gama ya budewa Jibril cocaine. Sai da Jibril ya yi kamar ba zai sha ba sai kuma shaeidan ya zugashi ya dauka ya shaka sosai, sannan ya mike tsaye yana fadin. 2
“Ba zanje office ba, ka yi duk abunda ya dace, Nawwara ma ba zata je ba, saboda dan mu ba lafiya”
Be jira abunda Siraj zai ce ya fito daga kitchen din na nufi bedroom dinsa. Saman gado ya kwanta ya rika bachi kamar wanda ya mutu, be farka ba sai da aka yi sallah azahar. A daren ranar ma sai da Jibril ya raya shi da nafila yana ta rokon Allah ya karkarto masa da hankalin Nawwara kuma ya shiga tsakaninta da duk wani mai son ta bayan shi, abu daya yake ce masa tuwo a kwarya a yanzu ba komai bane face rashin iya karatun kur’anen, haka zai dauko kur’anen ya rike but he can’t read it ko baki be iya hadawa balle har ya tada ya karanta aya, and now he need to know his religion more than everything, yana son yasan abunda Allah ya ce da kuma wanda ya hana, zuciyarsa na raya masa idan har ya shiryu ya zama na kwarai Nawwara zata so shi, a duk lokacin da ya tuna da dansa yana asibiti sai ya ji kamar zai mutu saboda yana son naje ganinsa sai dai yasan Nawwara ba zata bari ba. Haka ya jera kwana uku be sake saka Noor a ido ba a duk lokacin da tunaninsa ya taso masa sai ya dauki cocaine din ya sha sannan ya samu sassauci.
Misalin karfe biyu dare yana zaune saman carpet yana istigifari sai ga Abbah ya kirashi, da fari ya ji tsoro dan yasan Abbah be saba kiranshi a irin wannan lokacin ba, sai kuma daga baya wani tunanin ya zo masa na cewar wata kila Abbah zai masa fada ne akan rashin zuwa aiki da ya yi kwana biyu.
“Hello”
“Jibril kana lafiya?”
“Lafiya kalau Abbah”
“Ka tabbata?”
“Lafiya ta kalau”
“Allah ya tsare ka, kawai na yi wani mafarki ne marar kyau ina fatar babu komai ko? ”
STORY CONTINUES BELOW
“Babu komai Abbah sai damuwa, Nawwara ta ki fahimta ta Abbah kuma akwai da a tsakaninmu”
“Ni ma na samu wannan labarin lokacin da na je zan bawa iyalanta da kuma ita kanta hakuri akan abunda ka yi musu, sai dai ba samu ganin yaron ba”
“Abbah da gaske? Yaushe ka zo?”
“An kwana biyu, kawai dan ban fada maka ba ne”
Abbah ya labarta masa komai daga zuwansa da kuma abubuwan da suka faru, Jibril ya ji dadi hakan ya tabbatar masa da mahaifinsa yana sonsa kuma yana tare da shi.
“Abbah ka taimaka ka min izinin zuwa gidansu Nawwara Dan Allah”
“Ka yi alkawarin ba zaka yi wani abu marar kyau ba?”
“Taya mai neman hanyar gyara zai yi wani abu marar kyau? Wallahi Abbah ina son Nawwara sosai kamar zan hauka ce”
“Amman da muka zaba maka ita ai cewa ka yi baka son ta”
Ya yi shiru be ce komai ba, sai Abbah ya kara da
“Kuma kasan sai dai ka yi hauka dan babu aure a tsakaninku ko? Kasan saki uku ka yi mata fa” 2
Idanuwansa sun cika da kwalla.
“Yanzu Abbah babu wani gyara da za a iya yi? Ba wata mafita?” 2
“Babu zan kwanta sai da safe”
Abbah ya kashe wayarsa, sai Jibril ya fara surutai
“Dole akwai mafita Wallahi, dole a samu mafita No no no”
Wannan tunanin ne ya hana shi bachi har garin Allah ya waye, tun da asuba ya shirya ya fita, kai tsaye asibitin ya nufa. Ya taki sa’a yau Nawwara ce kwana asibitin, ko da ya tura kofar dakin ya shiga zuciyarsa na bugawa dan ya yi tunanin zai samu Inna a ciki ne ko kuma ya tararda Nawwara a farke, sai ya tarar tana kwance bayan Noor saman gadon asibitin suna ta bachinsu a tare, karasawa ya yi kusa da su fuskarsa dauke da murmushi yana kallon iyalinsa. Wayarsa yasa ya dauke su hoto sannan ya cire jacket dinsa ya lulluba musu ya zauna saman kujerar da ke facing dinsu yana ta kallonsu cike da shauki.
“Na bata komai, da yanzu muna nan a iyali daya”
Kadan kadan yake maganar amman hakan be hana Noor farkawa daga guntun bachinsa ba, sosai da sosai yake kallon Jibril ganin wani babban mutum mai kama da shi, sai kuma ya unkura ya tashi zaune zai yi magana Jibril ya dora hannunsa saman bakinsa ya yi masa alama da ya yi shiru.
“Shiiiiiiiiiiii”
Sai ya mika masa hannu alamar ya zo, ba musu Noor ya mika masa nashi hannayen sai ya dauke shi ya zaunar saman jikinsa ya rumgume ya lumshe ido. Hawayen farinciki da bakinciki suka cika masa ido lokaci daya.
“Waye kai kai likita ne?”
Noor ya tambaya da muryarsa yar karama.
Sai Jibril ya girgiza masa kai alamar a a ba tare da ya bude idon ba. Shi kuma sai ya sake tambaya cike da mamaki yana ta kallon fuskarsa.
“Kai ne wanda Inna ta ce min zaka zo ka ganki? Kai ne Uncle din?”
Ya gyada masa kai still be bude idon ba dan baya son Noor ya ga hawayensa, Nawwara kam bachi kawai take abinta bama san ana yi ba.
NAWWARA POV.
karar bude kofar da aka yi ne ya tasheni daga dogon bachin da na ke, sai turaren da na fi tsana a duniya ya yi marhaban sannan na kula da jacket din da aka lulluba min saman jiki. Inna na gani zaune tana jan karbi ba Noor a kusa da ni kamar yadda muka kwanta, saurin zabura na yi.
“Ina Noor?”
“Yana gurin Babansa”
“Dauke sa ya yi? Miyasa kika bari ya shigo?”
“Ke ya kamata na tambaya dan nan na shigo na sameshi”
Na sauka saman gadon hankalina a tashe sai Inna ta rike hannuna.
“Ba gudu zai yi da shi ba, sun fita waje ne su sha iska, ina tunanin ya canja Nawwara a nan ya durkusa yana ta ba ni hakuri, wannan abincin karyawar da kika gani daga kamfani yasa aka kawo”
“Wallahi zai iya gudun min da da mugu ne”
Na fita daga dakin hankalina a tashe, ina fitowa harabar asibitin sai na hango Noor saman motarsa zaune shi kuma na jikina jikin motar ya rumgume Noor. Karasa na yi ina masa fada.
“Waya baka izinin fitar min da da?”
Sai ya dago ya kalleni sai ya sauko da Noor da ko riga babu a jikinsa.
“Ki yi hakuri na fita da shi ne ya sha iska”
Daukar Noor na yi na koma da shi ciki, shi ko sai zuba min tambaya yake akan wannan Uncle din nasa da Inna take fada masa zai zo ya duba shi.
A ranar duk wanda ya kawo mana ziyarar dubiya ya tararda Jibril a asibitin saboda nan ya wuni, duk wani tafiyar numfashin Noor yana kula shi hannun kuma maikaraya yana kula da shi sosai, na yi mamakin da Zinatu ta zo ganin Noor ko da yake ba abun mamaki ba ne duba da Jibril yana cikin asibitin, yau kan Bilal dake zuwa kullum duba Noor ya tarar da Jibril wanda hakan yasa shi kin sakewa sosai daman kwana biyu nan na rasa gane kansa, hakan be min dadi ba dan ban jidadin ganin da Bilal ya yi ma Jibril a asibitin ba, ni kuma na raka shi har gurin gate din asibitin sannan na dawo.
A lokacin Jibril ne kawai cikin dakin Jibril ne kawai sai Noor suna rike da hannun juna, daman Inna waje ta koma da zama bata iya zama a cikin dakin matukar Jibril na ciki.
Kamar jira yake na shigo sai ya mike tsaye ya nuna ni da yatsa fuskarasa a kumbure saboda bacin rai ya ce.
“Kar Bilal ya sake zuwa duba min yaro wannan ya zama na farko kuma na karshe…” 9
Kallonsa na ke sai ma na rasa abunda zan ce masa, daman na san za a rina saboda ya tsargu da yadda na nunawa Bilal kulawa kuma ina ta masa kalamai masu dadi a gaban idonsa, sai dai mai? Ai be isa ya hana Bilal zuwa ganin Noor ba ko dan na bashi dama ya wuni da shi ya bashi damar samun guri har ya fada min wannan maganar? Bana son na yi wata magana a gaban Noor saboda kar ya fahimci wani abu, wannan yasa na kumde maganar da ke bakina har sai ya fita na bishi na fada masa.
Turo kofar da aka yi aka shigo ne yasa dukanmu muka kalli kofar Mustapha ne ya shigo cikin manyan tufafi tare da manyan ledoji Jidda na gafensa.Mustapha ya yi farincikin tararda Jibril da ya yi a dakin ko ba komai yasan Jibril ba zai jidadi ba, a farkon shigowarsa ya shigo da fargaba da kuma tunanin irin kallo da wulakancin da Nawwara zata masa, amman ganin Jibril ya sashi sakewa kamar daman can sun saba da Nawwara.
Murmushin fuskarsa ya fadada ya kunno kai cikin dakin tare da Jidda yana kallon Nawwara. +
“Pretty ashe Babynmu babu lafiya, Wallahi ban sani ba sai jiya ya jikinsa”
Sai da Nawwara ta hadiye yawu sannan ta amsa masa fuskarta ba yabo ba fallasa.
“Da sauki”
Kana ta watsa ma Jidda harara. Kamar be san an hallici mutum a gurin ba haka ya bi ta kusa da Jibril ya karasa kusa da Noor ya dire ledodin da ke hannunsa.
“Cute Boy waya kade min kai”
Noor ya dade yana kallonsa kamin ya amsa masa bakinsa da nauyi.
“Nima ban san shi ba”
“Am sorry dear”
Ya fada yana zama kusa da shi tare da duba hannun sai kuma ya juyo ya kalli Nawwara.
“Pretty amman da sauki sosai ko?”
Nawwara kamar ba zata amsa shi sai dai ganin Jibril yasa ta karaso gurin tana fadin.
“Eh a hannu kawai ya kare”
“Wallahi ban sani ba sai dazun nan Jidda ke fada min”
Nawwara ta kalli Jidda sai Jidda ta dan zaro idon tana daga kafadarta.
“Ya matsa ne sai ya ganki kin san yadda yake damuwa”
“Sorry na zo ban fada miki ba”
“Ba komai”
Cewar Nawwara. Jibril ya rumtse ido ya sauke ajiyar zuciyar da ta mamaye masa kirji, sai ya juyo cikin facin rai ya ce.
“Ya kamata ku tafi yanzu, amman kai yaron nan i warning you karka sake shiga sabgar Nawwara ko ban fada maka ba”
Daga Nawwara har Mustapha da Jidda kallonsa suke.
“Waye wannan daman ka san shi ne?”
Jidda ta tambaya tana kallon Mustapha, sai Jibril ya yi cikinta kamar zai dake ta.
“Babu ruwanki a ciki”
Matsawa baya Jidda ta yi ganin yadda temper dinsa take, sai Mustapha ya taso daga inda yake zaune kusa da Noor yana murmushi ya karaso daf da Jibril ya soma gyara masa kwalar rigarsa.
“Ka kwantar da hankalinka Man, macece fa ba namiji ba kasan namijin da ya amsa sunansa namiji baya taba dukan mace, ko da yake kai ragon namiji ne, shiyasa kake duka kuma kake cin zarafin yarinyar nan marainiyar Allah, anya babu kai a cikin kashe mata mahaifi kuwa? Saboda na ga ka tsawwalla rayuwarsu ne da yawa ka siye gidansu… oops sorry na manta she’s your ex…- “
Ya karashe maganar yana murmushi. Jibril ya daga hannu cike da hasala zai naushi bakinsa sai Mustapha ya rike hannunsa cikin zafin nama ya kai masa na shi naushin a baki har sai da Jibril ya yi baya baya ya rike bakin.
“1-1”
Mustapha ya fada yana murmushin keta. Sai Nawwara ta katsa musu tsawa.
“Miye haka? Ya zaku rika yin abu kamar kananan yara?”
Murmushi Jibril ya yi ya kallon Noor da duk tsoro ya gama mamayeshi ya ce
“Wasa ne fa kawai karki daga hankalinki, amman ki fada masa karya sake zuwa kusa da yaro na”
STORY CONTINUES BELOW
“Ba dan ka na zo nan ba dan Nawwara ne, duk kuma abunda ya shafi Nawwara dole ne ya shafe ni”
Jibril be kara ce masa komai ba, domin yasan wani furuci na fitowa a bakinsa ba mai dadi ba ne, kuma baya son ya yi abunda be kamata ba a gaban dansa, sai kawai ya karasa kusa da Noor ya zauna yana shafashi tare da fiddo wayarsa ya kunna masa game.
“Mu zamu koma, daman na zo ne kawai ganin Noor Allah ya tsare gaba”
“Amin”
Cewar Nawwara, sai Jidda ta daga mata hannu.
“Zamu yi waya”
“Ok thanks”
Suna fita Mustapha ya fara tambayar Jidda labarin Jibril, sai dai bata fada masa komai ba saboda tana tunanin sirrinsu ne ita da Nawwara, but itama tana mamakin yadda aka yi Nawwara ta hakuru har haka ta bari ya zo ganin Noor.
“Amman shi Nawwara take so ko?”
Mustapha ya tambaya yana driving, sai Jidda ta kalleshi.
“Bata son shi, ni dai iya sanina Nawwara Bilal take so”
Kamar zai sake cewa wani abu sai kuma ya yi shiru, sai dai ransa yau yana cike da farinciki saboda abunda ya yi ma Jibril. A bakin kofar gidansu Jidda ya sauketa sannan ya juyo ya dawo gida.
Tun a yanayin shigowarsa ya tabbatarwa da Momynsa yana cikin farinciki, Daddy sa ma ya lura da hakan kasancewar dukansu suna zaune falo ne har su Ikram da Zarah suna kallo harin da aka kai Iraq a channel din Al Jazeera.
“Dad Mom barka da dare”
Sai da suka amsa masa sannan ya zauna saman cushion yana kallon tv kamar yadda suma suke kallo, sai dai ko kadan hakalinsa baya gurin yana can gurin Jibril tunanin halin da Jibril zai kasance kawai yake yana murmushin da be san ya fito masa ba.
“Son lafiya kake wannan far’ar?”
Ya kalleta kamar be san ya yi ba.
“Ba komai, but Mom Dad ya kamata ce kunje ganin yaron Nawwara ya samu accident”
“What…?”
Dadynsa ya fada.
“Mu zaka fadawa muje mu duba yaron Nawwara? Hajiya baki fada masa ya fita harkar yarinyar nan ba? Daman yana nan akan bakansa?”
Momy ta yi saurin dagawa Dadyn hannu.
“Komai da sannu ake binsa kasan halin Mustapha”
“Babu ruwana da wani halinsa, ka var ganin kai kadai na haifa zan iya shafe labarinka a doron kasa matukar ka ce zaka auri yarinyar, ka dauki kanka a matsayin matacce matukar ka tsaya kai da fata akan yarinyar nan”
Mustapha da zuciyarsa ke boiling gumi ya zubo masa ya bude bakinsa da ke rawa ya ce
“Daddy ina son yarinyar nan…”
“Baka san so ba Mustapha, taya zaka so mace da ta auri namiji biyu kuma ta haihu? Kuma in banda haukarka macen da kayi ma kanwarta fyade zaka ce kana sonta kuma da aure? Kana tunanin zata aureka ne? Kana batawa kanka lokacin ne kawai, kuma na fada maka karna sake jin maganar yarinyar nan a cikin gidan nan, ka nemo yar kowa zan aura maka amman ban da ita”
Yana gama fadar hakan ya mike tsaye ya kabe babbar rigarsa cikin bachin rai ya fice, sai Momy ta matso kusa da Mustapha tana kokarin yi masa bayani
“Look son.. “
“No Mom ke kika ce min Dady ya yarda da maganar yarinyar nan, ashe ba da gaske ba ne? Miyasa ba zaku so abunda na ke so ba? Miyasa kuka gagara ganewa?”
Magana yake kamar ba shiba har numfashinshi na hawa wani kan wani, kamin ta kara cewa wani abu ya tashi rai a bace ya bar mata falon.
NAWWARA POV.
Ba jidadin zuwan Mustapha ba domin ban fiye son yana shige min ba, bana son wata alaka tana shiga tsakanin ni da shi, dan ban yarda mutum ya cuceni kuma ya dawo ya ce zai rabe ni ba Jibrrma dan babu yadda zan yi ne.
Bayan fitar Mustapha da mintuna talatin na kalli Jibril fuska a daure na ce.
“Ina son na kwanta dare na yi fa? Kuma ka san Inna tana waje kai take jiran ka fita”
“Ba zan je ko ina ba, a nan zan kwana tare da da na”
Ban yi mamakin furucinsa saboda cocaine yake sha mahaukacin mutum komai zai iya ai, musamman idan ya samu guri in ban da rainin hankali daga kawai na bashi damar ganin Noor sai kuma ya soma yi min katsalandan a lamurrana.
Tashi ya yi ya fita hakan yasa na bishi baya saboda na samu damar fada masa maganganun da ke bakina, ina fita na samshi bakin kofa a ashe ni yake jira.
“Daga Bilal har wannan dan iskan yaron bana son su sake zuwa gurin da na”
“Baka da damar da zaka shardanta min wanda zai so gurin da na da wanda ba zai zo ba, kai yanzu ko kunya baka ji ka kira Noor da danka? Har kana ikirarin kar wani ya zo dubashi?”
“Yes da na ne, alakar da ke tsakaninku daban babu ruwana a ciki”
“Ni na haifi yarona a hannuna ya girma baka da wannan hujjar Jibril, kuma ko zaka wulakanta kowa ban da Bilal saboda ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarta ni da dana, shi Noor ya sani a matsayin Uncle dinsa ba kai ba, da kuma ba naka ba ne nawa ne”
“Ko tau zamu gani”
Na watsa masa harara, ina kokarin juyawa na koma cikin dakin sai ya fisgoni da karfi ya dawo da ni
“Ban yarda ki kwana da shi ba, Inna zata kwana da shi i don’t trust you”
Dariya na farayi saboda abun ya bani dariya sosai. 1
“I’m laughing it’s funny very funny”
“Ba wasa nake miki ba Inna zata kwana da shi ba ke ba, idan ba haka ba, ni zan kwana da shi”
“Ban ga dalilin kwana tare da dan da ka kira da shege ba? Kai baka ma jin kunyar yanzu ka kira shi da danka?”
Hannu ya daga kamar zai dakeni sai kuma ya juya baya ya dafe kansa da hannu daya.
“Na dake ni mana, ai ka saba cin zarafina ko? Ka saba yi min wulakanci a gaban kowa, na yi min cin mutumcin da ya fi ko wanne ai ba ka hada hoto da na wani ba? Ka fadawa iyayena cewar ni karuwa ce..”
“Enough…!”
Ya fada a tsawa ce har sai da hankalin wanda duk wajen dakin ya dawo kanmu, wadanda suke cikin daki kuma suka fito waje, sai dai hakan be sashi fasa fadan abunda zai fada ba.
“Ya isa haka Nawwara ya isa haka, wace irin zuciya ce dake haka? Ke kan wace irin mace ce me ke damunki miya ke cikin kanka? Miyasa kika zabi nanata maganganun nan a ko yaushe ne? Kin san abunda yake raina? Kinsan bakinciki da yake raina? Ban isa na wuce wannan kaddarar ba shiyasa na aikata but abunda kike yi babu tausayi a ciki Nawwara, am lemme tell you abunda kike ba burgewa kike ba kokarin kashe rai kike, kokarin rusa wata rayuwar kike kuma babu abunda zai sa na canja daga manufata”
Yana gama fadar hakan yaja hannun Noor ta da fito waje suka koma cikin dakin, Inna hango Inna take na rufa masa baya rai na a bace. Noor na ganina ya yi saurin sakin Jibril ya dawo guna cike da tsoro, dan Noor ya tsani ganin ana fada.
“Da na ni ya sani ba kai ba, karka sake shiga rayuwarsa”
“Dole na shiga rayuwaraa saboda ni ne asalin ubansa”
“Yes ubansa ne kai na gaji da boyewa”
Na juyar da Noor ina nuna masa Jibril.
“Ka ga wacan? Ba Uncle din ka ba ne shine asalin ubanka Baba Faruk ba babanka ba ne rika ka kawai ya yi, wacan azzalumin ne mahaifinka, shine wanda ya ce kai ba dansa ba ne, da aka haifeka be yanka maka rago ba, kuma be san zafinka ba…”
Ban karasa na naji an dago ni an sauke min kyakyawan mari har biyu a fuska, wanda ya haddasa min daukewar wutar cikin kaina tare da ganin wadansu kanana taurari..