FETTA CHAPTER 14

FETTA




CHAPTER 14




_Ina mai baku hak’uri naji na shiru kwana biyu, Masu kirana da masu msg ta WhatsApp nagde da kulawa, Wanda ban samu reply d’insu ba Dafatan zaku mun uzuri_ +

Lasifukan masallatai ke tashi na kiran sallar asuba but sam Fetta bata motsa ba balle tayi alamar tashi, Nauyayyen bacci take, A hankali Suraj ya bud’e idonsa ya sauke akan ta, Bacci take hankali kwance bata da alamun tashi, Yayi mamaki tun zuwanta gidan kiran farko take tashi, “Ciki kenan” Ya fad’awa kansa,

Mik’ewa ya shiga toilet ya d’auro alwala, Ya nufi masallaci ba tare da ya tashe ta ba.

*6:30am*

Ya dawo daga masallaci, Bargon data lullub’e dashi, ya janye a hankali, Tare da hura mata iskar baki a fuska, Lumsassun idonta masu cike da bacci ta zuba a kansa, Ya d’age mata gira da fad’in “A tashi ayi sallah Maman unborn”,

Window ta kalla taga alamun gari ya fara wayewa, Salati tayi ta mik’e da mamakin irin baccin da tayi.

Suraj na shirin komawa bacci, Wayarsa tayi k’ara alamar text message, Tsaki yayi ya jawo wayar ya duba, ” Ina fatan masoyina ya tashi lafiya, I love you soo much”, Bai yi mamaki ba ya saba cin karo da text msgs na mata daban daban, Ajiye wayar yayi tare da jan bargo ya rufa, cikin mintunan da suka gaza uku bacci ya d’auke sa.

Fetta bayan ta idar da sallar asuba, Ta zauna tana lazimi kusan awa d’aya ta d’auka, Ta nufi kitchen had’a kumallo, Toasted bread da ruwan tea mai d’auke da ganyen shayi kala-kala ta had’a masa, shine abu mafi sauk’i da take jin zata iya, Kamar ko da yaushe ta jera a kan dining table.

Gidan ta shiga gyarawa, tana goge su TV da speakers.

Kiran da ya shigo wayarsa ya tashe ta, Yayi tsaki yafi kala uku kafin ya d’auka ba tare da ya duba mai kiran ba, “Ranka ya dad’e” Ya jiyo muryar Rabi’u, “Yes”, Ya fad’a cikin murya mai d’auke da bacci, ” Batun tafiyar ka Lagos yau anyi booking flight “, ” Cancel it”, “Amma ranka ya dad’e zuwan ka nada muhimmanci”, ” Idan na tafi wa kake so ya kula da Matata da abunda ke cikinta”, Ya fad’a a tsawace yana kashe wayar, Rabi’u yabi wayar da kallo yayi dariya tare da fad’in “Oga za’a zama Baba, duk plans d’insa na Lagos ya barsu, gaskiya Babyn d’an gata ne”

   Kasa komawa baccin yayi, Cikinsa ke masa kukan yunwa, Ya mik’e ya fito falo.

    Fetta na rik’e da tsintsiya ta duk’a zata fara shara, Hannun ta taji an rik’e an d’ago da ita,

“Me zaki yi?”, Da mamaki tabi sa da kallo tace ” Shara”, “Daga yau na d’auke miki duka aikin gidan nan”, Ya fad’a cike da isa, “Nifah zan iya, ciki kamar wata mai nakasa”, ” Ban yarda babyna ya wahala ko kad’an ba”, Dariya ma yaso ya bata a zuciyarta tace “Ahh masu Baby”,

   Tsintsiyar ya fisge a hannun ta, Ya nufi kitchen ya ajiye, Zama yayi kan dining table tare da umartar tazo, Ba musu taje, Kujerar kusa dashi ya nuna mata ta zauna,

      A cup d’aya ya had’a tea, Yayi sip d’aya, Ya nufi bakin ta dashi, Kawar da kai tayi gefe tace ” Nayi breakfast”, Murmushin gefen baki yayi yana sake nufo ta da kofin, Ta gumtse baki tana b’ata rai, Kallo ya jefa mata na kinsan saura, Ba shiri ta bud’e bakin, Ya bata tayi sip d’aya, A tare sukaci bread da tea, Yana feeding d’inta.

     Hajiya da kanta ta kira Aliya ta sanar da ita zancen cikin Fetta, Alhamdulillah ta shiga jerawa bakin ta ya kasa rufowa, Mallam dake zaune kusa da ita, Yace “Lafiya?”, ” Fetta ce d’auke da juna biyu”, Baki ya washe cike da murna yace “Alhamdulillah Allah ubangiji ya raba lafiya, ya bada mai albarka”, ” Amin, anjima zanje na duba ta tana fama da laulayi”, “Ai tare zamu”, ” Toh, kai amma naji dad’i haka zai k’ara dank’on k’auna tsakanin su Suraj”, Mallam yace “Sosai, Allah ya barsu tare ya dawwamar dasu cikin farin ciki”, Ta amsa da “Amin”, Suna matuk’ar son farin ciki Fetta, haka suke jin ta tamkar yar’su jinin su.

STORY CONTINUES BELOW


     ” Me zai hana ki tattara zancen Suraj ki watsar, kud’i yasa kike maitar sa kuma kina samu yanzu, idan ma dan sha’awa ne kina da mai kawar miki”, Cewar Zulaihat, Bilkisu ta nisa tace “A da nake son Ya Suraj dan kud’insa amma yanzu so na gaskiya nake masa wallahi, Son sa tamkar zai fasa k’irjina ya fito”, ” Ai sai kiyi ta son wanda ya miki duka da saki uku”, Taja tsaki cike da takaicin ta, “Hmm ba zaki gane ba”, ” Ni dai tashi mu tafi Hajiya Rabi sai kira take”, Mik’ewa tayi ta sake gyara fuska da fesa turare, Suka fice.

    Hajiya ta umarci Su Feena suje su gaishe da Fetta, Ba dan rai yaso ba suka nufi sashen, Tana zaune falo cikin shirinta na gown material, k’amshi na fita a jikinta, Suraj na d’aki yana shiri.

     “Sannu da jiki”, Cewar Su’ad murya tamkar an shak’e kaza, ” Yawwa”, Ta amsa, “Sannu da jiki”, Feena ta fad’a tana yatsina fuska, Ta amsa ba tare da kalle ta ba, Suka mik’e suka wuce.

    Feena tace ” Wai kinga yadda take amsa mutane”, Su’ad tace “Yarinyar nan ta samu wuri da yawa fah”, ” Ni wallahi ji nake kamar na kama shegiya nayi ta duka sai cikin ya b’are”, “Wallahi nima tana wani jin kai”, ” Kinsan talaka idan ya samu wuri”, “Allah yasa cikin ya zube”, ” Amin wallahi”

    Suraj wunin ranar a gida yayi sa, Duk wani motsin ta akan idon sa, Jin ta take a takure, komai tayi sai yace ba haka ba, tamkar cikin ba jikinta yake ba, Yana nuna yafi iko dashi.

     Aikin gidan ya hanata, Mai aiki ya kira sashen Hajiya, tayi komai, Ta kama mata tayi girkin rana.

     Ana sallar la’asar ya fita zasu yi meeting da wasu mutane, Sai da ya jadadda mata ta kula, idan wani abu ya sami babynsa zata  fuskanci hukunci.

      Ya fita ba dad’ewa Aliya da Mallam suka zo, Tayi matuk’ar farin cikin ganin su tun ba Mallam, Ta rasa ina zata saka su, Tuni ta dabaibayesu da abun motsa baki, Mallam yace “Hidimar ta isa haka Fetta”, Tayi dariya tana ajiye bowl na soyayyun kaji, ” Ya jikin ki?”, Cike da kunya ta amsa da “Alhamdulillah”, ” Allah ya k’ara lafiya ya raba lafiya”, Aliya ce ta amsa “Amin”, Kunya ta hanata amsawa.

     Mallam bai jima ba ya tafi bayan ta cika sa da sha tara ta arzik’i, Aliya sai bayan magrib ta tafi, ta bata shawarwari na masu cikin sosai, Ta biya sashen Hajiya sun gaisa.

     Tana dawowa rakiyar ta kiran Yasmeen ya shigo wayarta, Shine kira na uku ta mata tana tambayar lafiyarta, Ita har mamakin take yadda suke zumud’in cikin,

” Mother to be ina fatan kina lafiya?”, “Lafiya lau”, Yasmeen tace ” Ina Father to be?”, Katse wayar tayi ba tare da ta amsa ba, Bata son tsiyar Yasmeen.

   Gajiye lik’iss ya dawo gida, lafiyarta ya fara tambaya, Ruwa kad’ai ya watsa, Ya sata sukaci abinci tare, Yabi lafiyar gado, Duk yadda yake buk’atar tausa haka ya hak’ura dan kar babyn sa ya wahala.

    Kawo Lamid’o ya fito cikin shirin sa, Gwaggo ta kalle sa tace “Allah ya d’aura ka akan ta ta amince”, Yayi murmushi yace ” Hajiya Tumba na ganin girmana nasan ba zata yi turning d’ina down ba”, Gwaggo tayi nodding kai cike da gamsuwa, Ta masa rakiya da addu’ar a dawo lafiya.

    Da far’a Hajiya ta tarbe sa, Bayan sun gaisa, Ya gyara murya yace “Dama Bello ne yaga Su’ad yana so, shine ya fad’a mun nazo na nema masa izini”, ” Haba Lamid’o yanzu dan Bello na son Su’ad sai kazo nema masa izini, ai dukkan su yaran ka ne, kana da iko akan su”, Cike da murna yace “Hakane amma gara a sanar dake”,  Hajiya tayi murmushi, zuciyarta cike da farin ciki tasan Bello yaro ne mai hankali, natsuwa da addini kowacce uwa ta gari zata yi ma yar’ta sha’awar shi, Tace ” Allah ya tabbatar mana da alkhairi”, “Amin Amin”

   Kawo Lamid’o da ya komawa Gwaggo da zancen, hadda rawar farin ciki ta taka, Ya kira Bello ya sake jadada masa ya rik’a zuwa wurin Su’ad su fahimci juna, Rai ba dad’i ya amsa da toh.

     “Ni wallahi bana son Bello ba ajina bane”, Su’ad ta fad’a tana kumbure kumbure kamar zata yi kuka, Hajiya rik’e da hab’a tabi ta da kallo tace ” Bello ne ba ajin ki ba, Yaro mai hankali da natsuwa”, “Mama ni ina da wanda nake so”, ” Kina da wanda kike so koh?”, Ta d’aga kai, “Kice masa nan da sati d’aya ya turo”, Tana fad’ar haka ta mik’e ta fice d’akin.

   Su’ad wani juyi tayi tace “Nasan My guy zai turo ya dad’e yana mun maganar aure, me zanyi da Bello kaya basu wani zauna masa ba.

    Baccin rana yanzu ya zama al’adarta, A sallayar data idar da sallar azahar bacci ya d’auke ta, Vibrating da hsaken wayar dake gefenta, da ita tayi azkar, Ya tasheta, Text message ne aka turo mata, Daga kwance ta jawo wayar ta duba,

*”Ki fara k’irgawa wa’adin barin ki gidan Suraj, Ni kad’ai zan zama matar sa, ni na dace dashi”*

   Sau uku tana karantawa, Ta tsinci kanta da fad’uwar gaba da b’acin rai wanda ta rasa dalili.”Ki k’irga wa’adin barin ki gidan Suraj”, Take ta nanatawa a ranta, Message d’in ya kasa b’ace mata, Kiran sallar la’asar da ta jiyo, Ta mik’e ta shiga toilet ta d’auro alwala, Ta gabatar da sallah tare da addu’o’i, B’acin rai da take ji ya bar zuciyar ta. +

    Falo ta tarar dashi zaune, Yana kallon news, Ya d’ago kai ya zuba mata ido, Sosai yaga ta masa kyau ta k’ara cikowa, Dukiyar fulaninta kamar su fasa rigarta, wani yarr yaji a jikinsa, kwana biyu ya d’aga mata k’afa saboda lafiyar babynsa, Da hannu ya mata alama tazo, Ba musu tazo kusa dashi ta zauna, Hannu yasa ya kwanto ta jikinshi, Tana k’ok’arin mik’ewa ya sake matse ta, Ya d’an d’aga rigarta, yana shafo k’asan mararta, tsigar jikinta ya tashi,  Ta d’an ture hannun sa, ” Lafiyar babynsa nake dubawa”, Ya fad’a yana d’aga mata gira tare da k’ara shafowa har can k’asa cikin wani salo,

   Jikinta ya mutu lik’is, Tuni ya shiga sarrafata cikin wani salo na daban, mai rikita zuciya da gangar jiki, Ta shiga mayar masa martani ba tare da ta sani ba, Basu dawo hayyacinsu ba sai da suka samu natsuwa, sam sun manta a falo suke, Rigarta ta shiga gyarawa tana k’okarin saka zip, Yasa hannu ya tsayar da ita, Kafin tayi magana ya d’agata sama, ya nufi toilet da ita,

Gajeran wandonsa yake k’ok’arin cirewa, Tayi saurin sa hannu tana rufe fuska,

    “Bana son kilibibi yau kika fara gani, naga yanzu kika gama yadda kike so dashi”, Tamkar ta nutse a k’asa tsabar kunya, Ta sake gumtse idonta, ” Ni dalla bud’e ido, na cud’a ki bana son babyna ya wahala”,

   Babu yadda ta iya, cike da jin kunya tayi wankan tsarki, Ya mata wanka, Ya ma kanshi, Shi ya d’aura mata towel ya d’auko ta, Ya fito da ita, ya zaunar kan dressing mirror, Ya shafa mata mai, ya shirya ta tsaf, Kunya ta hanata ce masa komai,

    Ta mik’e zata fita d’akin ta jiyo muryar sa, “Don’t feel too important darajar babyna kike ci”, ” Kai ma darajar babyn naka yasa na bar ka”, Tana fad’ar haka ta fice, Yabi bayanta da kallo, tare da yin murmushin gefen baki.

    Kitchen ta nufa, Ta d’aura girki da taimakon Shafa(Yarinyar da Hajiya ta kawo mata).

     Aunty Jummai ke ta k’urmawa cikin daji, ta tattare zani saboda ciyayi da k’aya, Tafiya take tana waige-waige ita kad’ai kamar mayya, Har ta kawo wani k’ugu,

    “Kada ki shigo da k’afar dama”, Taji an fad’a da razananniyar murya, A tsorace ta mayar da k’afar dama, ta shiga da hagu, Tana ta kutsawa tazo gaban wani k’asurgumin boka, Kallon sa kad’ai ya isa yasa ka firgita, Gabansa ta durk’ushe, ” An sanar dani meke tafe yake”, Jiki na rawa tace “Toh”

    “Zaki kawo jinin hailar yar’ ki, da zuciyar zakara da gashin jab’a”, Ba tare da wani shakku ba ta amsa da ” Toh”, Zuciyarta ta bushe komai zata iya aikatawa dan cimma burinta, “Sai kin kawo za’a yi aiki”, Ya fad’a cikin murya mai karaji, Ta mik’e jiki na rawa, Ta tafi, Jikinta duk k’aya ta isa gida, Bilkisu ta tayata cirewa tana sanar da ita yadda suka yi,

    ” Umma bakya tsoro, nifa ina tsoron mu’amala da irin su”, “Dallah wane tsoro, irinsu ne aikinsu tamkar yankan wuk’a, Malam tsibbun nan da yawa kud’in mutum kawai suke cinyewa”, ” Yaushe zaki yi al’ada nan da sati d’aya”, “Allah ya kaimu”, ” Amin Allah yasa dai a dace”, “Zama a dace”, Bilkisu tayi murmushin farin ciki.

   Su’ad ce kwance jikin Adnan a cikin mota gidan k’awar ta nan suke had’uwa, ” Albishirin ka”, Ta fad’a tana k’ara narkewa jikin sa, “Goro fari  tass”, ” Mama tace na fad’a maka ka turo”, Ya sake rungumota jikin shi Yace “Wooo Am soo happy zaki zama matata”, Farin ciki ya sake lullub’eta ganin yadda yake murna, tasan dama zai yi murna, ” Can’t wait naga mun zama husband and wife”, Tace “Same my love”, Tana manna mishi kiss, Sai da sukayi romancing juna sosai, suka rabu, Ta koma gida cike da murna.

    Suraj ya fito daga gidan gonar sa ya biya wani boutique na kayan manya da jarirai, Kaya sosai ya siya na babies(Nace zumud’i tun yanzu)

    Bakin k’ofar fitowa yaji an buge ledar hannun sa na dama, Kayan suka zube, Da sauri ta duk’a tana kwashewa, Ta d’ago idonta cikin nashi, Yayi saurin kawar da kai gefe saboda fad’uwar gaban da yaji, ” Am sorry”, Ta fad’a , Ya karb’a ba tare da yace mata komai ba, “But kamar na san ka”,  Kafad’a ya d’age mata yace ” Maybe”, Yayi gaba abunsa, Sosai taji ya burgeta,

    “Sai na aure ka Suraj, This is part of my plan”, Cewar Tasleem, Ta juya ta fice daga boutique d’in, ba abu tazo siya ba, shi ta biyo daga gidan gonar sa.

    Yana parking motar sa cikin gida, wayarsa tayi k’ara alamar text message ” I will always love you Sahibina”, Da same number ta ranar, Yayi tsaki, Ya kwashi ledoji ya shiga cikin gida.

    Fetta na zaune k’asan carpet tana cin fara wacce tasa Shafah ta samo mata, Idonsa ne ya kai kan bowl na farar, Ledojin dake hannun sa ya saki, Ya k’arasa gabanta, “Meye wannan kike ci?”, Ya fad’a yana d’aukar bowl, yana sake dubawa, ” Fara”, Ta bashi amsa hankali kwance, “What!”, Ya fad’a a tsawace, ” Are you out of my sense”, Da mamaki tabi sa da kallo, “Fara kike ci, babyna kike ba wannan abun”, Ya fad’a yana nufar dustbin na falon ya jefa hadda bowl d’in,

    Ya dawo saitin ta ” Wannan ya zama na k’arshe, ki bari idan kin haifa mun babyna kici kyankyaso bama fara ba”,

Ya wuce d’aki abun sa, Ta tsinci kanta da jin zafin furucin sa, bata san sai yaushe zai fara nuna damuwar sa a kanta, wata zuciyar tace “Meyasa zaki damu da nuna damuwar sa a kanki”, Taja siririn tsaki, ta d’auki remote, Ta kamo sunna TV, ana wa’azin Malam Aminu Daurawa mutumin, wa’azin ya tafi da dukkan tunanin ta.

     Kusan awa d’aya ya d’auketa tana kallo, ta maida dukkan hankalinta wa’azin na shigar ta,

   Suraj ganin shiru bata shigo ba, Ya mik’e ya lek’a yaga lafiya, Har yazo ya zauna kusa da ita bata sani ba, Saukar numfashin sa yasa ta juyowa, Idonta cikin nasa, ya kashe mata d’aya, Ta kawar da kai ta maida kallonta ga TV.

  Gama wa’azin yasa shi mik’ewa da fad’in “Ki kwashe su ki ajiye in a safe place”, Ya nuna mata ledojin da ya shigo dasu d’azu, Bai jira amsarta ba ya shige d’aki,

    Ledojin ta shiga tattarawa, Kayan babies masu azabar kyau ta gani unisex wanda maza zasu iya sawa mata zasu iya sawa, Mamaki ya kamata tun yanzu ya fara siyan kayan babies, lallai ba k’aramin so yake wa cikin ba, Da tunanin haka ta kwashe, Ta shiga d’aki ta zuba a cikin d’aya daga akwatin ta na lefe.

   ” Na gaji da irin zaman nan da muke”, Karima ta fad’a tana raba jikinta daga Alhaji Mu’azu, “Haba swty yanzu kin gaji dani”, Ya fad’a yana sake jawo ta jikin sa,  ” Ba wai na gaji da kai bane, amma me zai hana muyi aure yadda zamu fi jin dad’in juna”, Sakinta yayi ya b’ata rai “Kinsan me kike fad’awa kuwa, ai ni na rufe aure, kina so yarana suce na jawo musu abun kunya, tsofai tsofai dani zan auri yarinya”, ” Amma baka ji kunyar aikata zina ba, ai gara kayi aure akan su san aika aikar da kake”, “Kar kimun rashin kunya”, ” Dama akwai kunya ne tsakaninmu kana taushe ni, Toh wallahi anyi na k’arshe tsohon banza”, “Nine tsohon banzan”, ” Sosai kuwa”, Taja tsaki ta d’auki bandir na dubu d’aya da ya ajiye mata, Ta jefa jaka ta fice.

   Yabi bayanta da kallo, cike da takaici yar’ cikinsa na gaya mishi magana, Shi yajawa kansa, ya mayar da kansa mutumin banza, Da k’ima da darajarsa amma sun zube a idonta, da idon duk yarinyar da ya kwanta da ita.

  Karima cikin samarinta duk wanda tama maganar aure da dalilin da yake kawo mata, wasu ma k’iri k’iri suke fad’a mata baza su iya auren karuwa ba, Tana cikin matsananciyar damuwa, Ga Kawo Sule ya k’ara jadadda mata idan bata fito da miji ba, nan da kwana 3 zai kore ta daga gidan, taje can ta cigaba da yawon iskancin ta.Fetta ta tashi bata jin dad’in jikinta abun ku da masu ciki yau ciwo gobe lafiya, Aikin gidan ta kasa, Shafah tayi komai, Wanka da taimakon Suraj tayi, Sai faman jera mata sannu yake, motsi kad’an zai ce meke damun ta, Ya kasa natsuwa, ko bakin k’ofa bai fita ba, Ya so suje asibiti tak’i tace ba wani ciwo bane, Ya bata magani tasha bacci ya d’auketa, +

    Kan gadon ya hau, ya d’aga bargon da ta lullub’e ya shiga, tare da jawo ta jikin shi, Hucin zazzabin ta na sauka jikin shi, Tausayin ta sosai ya kama shi yana jin tamkar ya mayar da ciwon a kansa,

    Hajiya jin sa shiru har kusan la’asar bai zo ya gaishe ta ba kuma bata ji fitar sa ba, Zuciyarta ta sak’a mata ba lafiya ba, Su Feena basa nan ta aike su, su duba mata ko lafiya, Gyalen ta ta yafa ta nufi sashen, Tayi ta knocking shiru, Daga d’aki sam basu jiyo ba, Kusan minti 2 tana tsaye babu ko alamar su, Tsoro ya fara kamata, Ta koma sashen ta, Ta d’auki wayar ta, Tayi dialing number sa,

    Wayarsa dake bedside drawer ta d’auki ruri, Ya jawo da sauri ya kashe, baya so sound d’in ya tashe ta, Ganin Hajiya ce mai kiran, Ya danna receive, “Assalamu Alaikum”, Yayi sallama, Sanyayyar ajiyar zuciya tayi jin muryar sa lafiya, ” Wslm Ina ka shiga yau Suraj?”, “Fetta ce bata da lafiya”, ” Subhanallah, dama masu ciki basu cika lafiya ba”, Yace “Wallahi”, ” Allah ya bata lafiya ya raba lafiya”, “Amin”, ” Da hankalina ya tashi naji shiru”, “Ai in kaji shiru lafiya ce”, Tayi dariya tace ” Hakane, kuna tare ne na mata sannu”, “Bacci take”, ” Idan ta tashi kace ina gaisheta, ina mata sannu”, Ya amsa da “Toh”, Ta kashe wayar.

    Bello ya fito da shirin sa zuwa office, yaci karo da Kawo Lamid’o shima ya fito, Ya rissina ya gaishe sa, Ya amsa tare da jefo masa tambaya ” Kana zuwa gurin Su’ad kuwa”, Ya d’an sosa k’eya yace “Kwana biyu ban je ba, ayyuka sunyi yawa”, ” Wane aiki ne zai hana maka zuwa ko da daddare, naga take taken fa wallahi zan mugun sab’a ma”, “Kayi hak’uri zan gyara” , “Kar ma ka gyara” Ya fad’a a fusace ya shige mota.

    Bello rai ba dad’i, zuciya d’auke da damuwa, Yaja motar sa zuwa wurin aiki.

   “Ga wannan addu’a ce nama Fetta ki kai mata” Mallam ya fad’a yana mik’awa Aliya jarka mai d’auke da ruwan zamzam, Ta karb’a da fad’in “Toh, ” Idan ta shanye a fad’a mun na mata wani”, “Toh zan sanar da ita”, ” Ni na tafi”, “A dawo lafiya”, ” Allah yasa”, “Amin”

   Har ya kai bak’in k’ofa ya juyo yace “Ki tabbatar kin kai mata kafin na dawo”, ” Toh In Shaa Allahu”

    Ayyukan gida ta kammala, Dama su Aliyu na koki, Hijabinta ta zura ta nufin gidan, Bugu d’aya, Suraj dake falo yaji, Ya taso ya bud’e, “Ina wuni?”, Ya gaisheta, ” Ina yini ?”, Bai amsa ba ya tsinci kansa da jin nauyi, Ya juyo ya koma ciki, D’aki ya sameta ya sanar da ita zuwan Aliya,

   Jiki ba k’wari ta fito, fuska d’auke da farin cikin zuwan ta, “Fetta babu lafiya”, Ta d’aga kai sama, ” Sannu koh”, “Yawwa”, Ta amsa da k’yar, ” Kamar Mallam ya sani ya miki addu’o’i”, “Na me Umma?”, ” Sauk’i da samun kariyar ubangiji, kasala da yawan laulayi da izinin Allah zaki daina, nima yamun lokacin cikin Haulat da Ali kuma na samu sauk’i sosai”, Farin ciki ne ya ziyarce ta yadda Mallam da Aliya ke nuna kulawa a kanta.

   Zamzam ta d’iba a kofi taba Fetta tasha, sauran ta shafa mata a ciki da jiki, “Allah ya baki lafiya, ya sauke ki lafiya”, ” Amin”, “Ni zan koma”, ” Da sauri Umma”, “Ba zama na zo ba, sak’on nan kad’ai ya kawoni”, Ta marairaice fuska ” Ki cewa Abba, Nagode sosai, Allah ya saka mishi da alkhairi”, “Amin”, Ta taso zata mata rakiya tace ” Koma ke da baki da lafiya”, Ta koma ba dan rai yaso ba.

STORY CONTINUES BELOW


   Aliya na fita, Yasmeen da cousins d’in ta guda biyu suka shigo, “Mai ciki” Yasmeen ta fad’a cikin sigar tsokana, Fetta ta harare ta, Ameerah tace “K’yaleta Sister”, Zee tace ” Ta cika tsokana”, Yasmeen tayi dariya, Ameerah tace “Laces muka zo dubawa”, ” OK bara na d’auko muku”

    D’aki ta shiga, Suraj nata faman operating system, Yaji shigowarta bai d’aga kai ya kalleta, Ta d’auki leda da sauran laces ke ciki ta fita, sun kusa k’arewa,

     Zamzam da tasha tamkar miracle taji k’arfin jikinta sosai, ta nemi zazzab’in ta rasa, Duka suka siye, sun musu kyau sosai, anan take suka mata transfer kud’in, tuni ta bud’e account, Basu jima ba suka tafi, sanin Oga Suraj na nan.

   Bedroom ta koma, Ta d’auki hijab, Tace mishi zata sashen Hajiya, “Ke da baki da lafiya”, ” Naji sauk’i”, “OK jirani mu tafi tare”,

Falo ta dawo tana jiran fitowar sa, kusan minti goma ya d’auka, Ya fito yana zuba k’amshi tamkar wanda za shi wani wuri, Sun fito waje ya kamo hannun ta, yak’i saki har suka isa sashen Hajiya, Tana k’ok’arin janye hannun ta ya sake matse shi gam,

   Feena da Su’ad na zaune falo suka ga shigowar su, yana rik’e da hannun ta, Suka kalli juna suka jinjina kai tare da tab’e baki, Bayan wucewar su,

   Feena tace ” Tirk’ashi”, Su’ad tace “Abun mamaki baya k’arewa”, ” Wannan shegiyar ta gama shanye Ya Suraj”, Su’ad tace “Bararoji fah aka ce”, ” Allah dai ya kub’utar dashi”, “Amin”, Haka suka cigaba da jinjina rik’e hannun ta da yayi har sashen Hajiya, yana ganinsu but ko kunya ya saki.

   Gab da zasu shiga d’akin Hajiya, Ta fisge hannun ta, ta shige da sauri,

   Hajiya na zaune kan gado tana k’irga kud’i, Ta durk’usa ta gaisheta, ” Haba Fetta nace miki ki daina duk’awa, ki duba lafiyar ki, ko a tsaye kika gaishe ni ya wadatar”, Tayi murmushi ta zauna kan carpet,

    “Mamana ta kaina”, Suraj ya fad’a yana shigowa, ” Dan’ albarka”, Yayi murmushi har fararen hak’oran sa masu k’ara mishi kyau suka fito, Fetta da ta tsura mishi ido a ranta tace “Ba dai kyau ba”, Yana juyowa suka had’a ido, Ya d’aga gira alamar ya dai, Kunya taji ya kamata tana kallon sa, Ta kawar da kai gefe.

   ” Yanzu nake shirin aika miki dambun nama, nasan masu ciki ba’a raba su da kwad’ayi”, Cewar Hajiya, Kafin tayi magana Suraj yayi saurin cewa “Aikuwa d’an banzan kwad’ayi ne da ita”, ” Babynka mai kwad’ayin ai”, “A’ah Maman baby dai”, ” Wato abun son kai ne”, Yayi dariya, Hajiya ta juya kan Fetta tace “Share sa, ni nasan baby ne mai kwad’ayi”, Fetta tayi dariya,

   Sun jima sashen Hajiya, Kafin suka koma sashen su da dambun nama mai yawa cike da k’aramin bucket.

    Suraj ya tasa gaba yana ta ci, ” Baban baby ne dai mai kwad’ayi “, ” Salon rowa dan na daina ci, toh sai naci”, Shiru tayi ta kasa cewa komai, wato shi duk ta yadda aka yi, sai ya b’ullo ta wata hanya, Mik’ewa tayi ta bar masa falon.

    Bello bayan ya dawo office, Yaci abinci, ya sake wanka ya shirya, Ya fito yana ta rambad’a k’amshi, Zuciyarsa a jagule, sam baya k’aunar zuwa wurin Su’ad.

    Kai tsaye cikin gida ya shiga, Ya zauna a babban falo k’asa, D’aya daga cikin masu aikin ya aika ta kirata.

    Tana falon sama tana kallo, Lami ta rissina tace “Aunty kinyi bak’o”, (Duk da kasancewar ta girmi Su’ad, but dole tace mata Aunty kuma ta rissina, basa ma masu aiki da wasa) ” Kice masa ina zuwa”, A tunanin ta Adnan ne, sunyi dashi zai zo.

    Kwalliya ta sake yi, ta fito k’amshi na tashi, Fuska d’auke da annuri yau ya fara zuwa gidan su, Turus tayi ganin wanda bata yi expecting ba, Ta b’ata rai, “K’araso ki zauna mana”,

   Ta sake had’e rai ta zauna kujerar nesa dashi, ” Ya Bello wai bana fad’a maka alak’ar mu ba zata yiyu ba”, “Iyayenmu sunce dole mu zama k’ark’ashin inuwa d’aya”, ” Ni wallahi babu wanda zai mun auren dole, akwai wanda nake so”, Tana fad’ar haka ta mik’e ta bar falon, Yabi bayanta da kallo yana sakin murmushin farin ciki, Rashin amincewarta shine hanyar da zata kawo rabuwar su, Yana fatan kada Hajiya ta tursasata kamar yadda iyayen sa suka masa.

   Ya mik’e ya tafi, b’acin ran dake zuciyarsa ya rage sosai.

   Bello bai dad’e da tafiya ba, Adnan yazo, cike da murna ta fito, Sanin gidansu ne wani zai iya fitowa ya hana ta rungume shi, Tuni ta dabaibayeshi da abubuwan motsa baki, Sai da yace ya isa haka, Ta kashe murya tace “Yau ka fara zuwa gidanmu ya kamata a karrama ka”, Yayi smiling, Tayi serving d’insa abinci, kad’an yaci shima dan ta matsa mishi, Yasha lemo da snacks,

    Ta kira Hajiya su gaisa, har k’asa ya duk’a ya gaisheta, Ta yaba da ladabin sa, Tayi addu’ar mafi alkhairi ta koma ciki, Bai jima ba yace zai koma yana jin kunya, Ta masa rakiya, Ya k’ara jaddada mata cikin satin zai turo iyayensa, Zuciyarta fal farin ciki ta dawo cikin gida.

   Fetta ke ta faman ci dan’ sololo wanda ta saka Shafah ta mata, Ta zabga mishi yaji, kasa cinyewa tayi saboda yaji, tasha ruwa tasha sweet but bata daina ji ba, Bakinta ban da zugin yajin ba abunda yake, sai faman yarfa hannu take, Suraj ya shigo,

     A rud’e yayi kanta yana tambayar lafiya, A tunanin sa wani abu ya samu cikin, Bakinta ta shiga nuna masa, Ya kamo bakin yana dubawa bai ga alamar ciwo ba, ” Me ya samu bakin?”, “Yaji”, Da fad’a tana cigaba da yarfa hannu, ” Waya ce kici yaji, salon ki illata mun baby”, Ya fad’a a tsawace, Bata tanka sa, sai ma hawaye da ta shiga yi na zugin da bakin ta ke mata, Bakinta ya kama yasa cikin nashi, Ya shiga tsotsewa, bata hana sa ba, sai ma zugin da take ji yana ragewa, Wani salo ya shiga yi mata, da ya soma rikita, Daga shanye yaji suka lola wata duniya, Ya d’auketa cak ya nufi gida, Ya kwantar kan gado suka shiga duniyar ma’aurata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *