RAI BIYU
CHAPTER 16
Zafin marin ya haddasa min ganin duhu a idanuwana, sai na kyabta idon sau biyar sannan na ga Inna dake tsaye tana hararata, Noor kuma ya fashe da kuka ya rike min kafafu da dayan hannunsa. Hawayene suka soma zuba a idanuwana ina dafe da kuncina, sai na juyo na kalli Jibril da shi ma idanuwansa ke cike da kwalla, juyawa ya yi ya bar dakin ba tare da ya ce komai ba, sai da yaja kofar dakin sannan Inna ta soma fadamin maganganu marar dadi. +
“Ina miki kallon mai hankali ashe baki da hankali, abunda kika aikata a yanzu ya fi abunda Jibril ya yi ma Noor shekarun da suka wuce, miye abun burgewa a cikin fadar irin wannan maganar a gaban idon dansa? Wane irin kallo kike son dan sa ya masa? Kina tunanin burgeshi zaki yi? Ki haddasawa danki tsanar ubansa da kanki? Idan ke baki son shi karki shiga tsakanin uba da da, Wallahi da Noor zai girma a cikin talaucin da ya fi wannan kuma daga baya ya hadu da mahaifinsa dole ne sai ya masa biyayya saboda haka Allah ya ce. 2
Wace irin zuciya ce da ke Nawwara, ke baki ma Allah laifi ya yafe miki ne? Wa kika fi? Idan ma ba zaki yafe masa ba ai ba sai kin shiga tsakaninsa da dansa, Wannan ba halinki ba ne Nawwara kuma ba halina ba ne ba kuma halin Babanki ba ne, ban san inda kika dauko wannan bakar zuciyar ba” 1
Tun da ta soma maganar na lumshe ido hawaye na cigaba da min zuba, sai na ji ta fisge Noor daga rikon da ya yi min ina bude ido ta nuna min hanyar fita.
“Fita ki bar dakin nan”
Na bude baki zan yi magana ta daga min hannu.
“Bana son jin wata magana daga bakinki ki fice kawai kije gida”
Juyawa na yi kafafuna da nauyi zuciyata kuma da rauni na fito daga dakin ina share hawayena. Kowa kallona yake ni kuma na ki na kalli kowa na fito ina wata tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na nufi bakin gate din asibitin.
Miyasa kowa ya kasa fahimtata? Miyasa ni kadai na ke jin abunda na ke ji babu mai ji min zafi? Ni kadai na san irin wulakancin da na fuskanta a gidan Jibril amman yau Inna har ta tana marina saboda shi? Zama da mutane da kalubale shi yake canjawa mutum rayuwa Inna ta kasa fahimtar hakan.
Har na isa gida kuka nake, mai Napep din har tambaya ya yi wai ko an yi min mutuwa ne nidai ban amsa shi ba, da hawayen fuskata na shiga gida Sakina da Jamila suna zaune waje suna shan iskar hadari da ke kadawa, yanayin shogowata yasa Sakina ta taso ta sauri ta tari ne sai ta haska fuskata. 2
“Lafiya Anti Nawwara? Ko Noor ya mutu ne?”
Na girgiza mata kai alamar a’a, ina kallon yanayinta da ya yi min kama da na Habiba, banbancinsu da Habiba ce rumgumeni zata yi ta fashe da kuka ko da kuwa bata san abunda na ke wa kuka ba.
“Anti Nawwara miya faru?”
Ta tambaya tana jijjigani zuciyarta cike da fargabar abunda ya saka ni kuka.
“Na rasa komai Sakina, na rasa karatuna wanda shine gimshiken rayuwata saboda Jibril, na rasa mahaifina mai fahimtar kukana, na rasa yar’uwar da ke goyon bayana, yanzu kuma zan rasa Noor Inna kuma tana goyon bayan Jibril, ni kan miya ragemin a duniyar nan? Kowa baya fahimtata, babu mai jin yarena, ni kadai na ke kukana, damuwata ni kadai ta dama, ni kadai na ke jin zafina, duniya ta juya min baya ta kona min komai na farinciki, duk abunda na taba zafi yake min, mai amfanin kuma ta mayarda shi toka da na taba sai dai ya bi iska, na kasa gane bayana balle na fuskancin gaba, babu ranar tsayuwar hawayena” 2
Ta rika hannuna tana kuka kamar yadda Habiba take min.
“Allah yana tare da ke Anti Nawwara shi zai miki maganin komai”
Na gyada kaina alamar gamsu har na saukarda nauyayyen ajiyar zuciya. Sannan na share hawayena na nufi dakinmu.
“Habiba”
Ina shiga na ambaci sunanta kamar tana jina, sai kuma na kwanta saman katifa ina hawaye, wayar da ke hannuna ta yi kara alamar sako, ina dubawa na ga number Jibril.
STORY CONTINUES BELOW
_I’m so Sorry Nawwara i’m sorry_ 1
Haka ya rubuta a sakon, wai na yi wurgi da wayar na kara fashewa da kuka. A ranar kwana na yi ina kaiwa Allah kukana saboda bachi ya yi kaura daga idona. Na mikawa Allah lamurana, sannan na bar masa zabi akan dukan abunda zai fi zama alheri a rayuwata, a ranar na roka idan ma mutuwa ce ta fi alheri a gareni Allah ya matso min da ita, idan kuma ba iyakar wahalata kenan ba, Allah ya bani zuciyar da zan iya dauka, saboda shi ya tsara min komai. 2
Washe gari Inna bata dawo ba sai tara da rabi, ban ga annuri a fuskarta ba wanda hakan ke nuna har yanxu bata huce ba kenan, ban kuma ji ta ce na shirya na je ba, daman ni na ke kwana da shi sannan ita kuma da rana taje ni sai na dawo na yi wanka na shirya sannan na koma.
A daki na sameta na durkusa kasa na rike kafafunta ina kukan da ni kadai nasan zafin fitar hawayena
“Inna ki dubi girma Allah ki yafe min, Wallahi duk kika yi fushi da ni Allah ma fushi zai yi da ni, ke kadai kika rage min a duniyar nan, ba ni da wani gata sai na Ubangiji da yayi min ta hanyarki, zan iya jure komai amman ban da fushinki da rashinki babu dan da zaiyi albarka matukar uwarshi tana fushi da shi, mai yawan neman yafiyar mahaifiyarsa da mahaliccinsa kuma dan gata ne har a gurin Allah, kuma ba zai taba tabewa ba, yarda Allah tana tare da yardar iyaye, idan suka yarda da kai to Allah ma ya yarda da kai, ki taimaki rayuwa kada na zama daya daga cikin masu tabewa, kar soyyayyar wami yasa ki yi fushi da yarki” 2
Zaunawa ta yi bakin gadon tana kallona fuskarta dauke da damuwa.
“Ba zan taba fushi da ke ba, domin na san illar fushin uwa ga yayanta, na mareki ne kuma na daure miki fuska ne saboda ki gane abunda kika aikata babba ne, na san zuciyarki zata zargeni da cewar ina son Jibril fiye da ke, ba saboda kudin Jibril yasa na yi miki haka ba, da kudinsa na ke kwadayi da na cilasta miki komawa gidansa ko kuma kulla wata alaka da shi, ba wannan na ke dubi ba Nawwara, rayuwar dan ki ta nan gaba nake hangowa da kuma taki rayuwar, wata rana zaki gane gaskiya nake fada miki wata kila a lokacin bana raye, amman za ki gasgatani, ba zan taba cilasta miki gurin auren Jibril daman tun farko bamu cilasta miki ba, amman na san ko da mahaifinki yana raye kwatankwacin abunda na aikata shi zai aikata a gareki, ba zan taba fushi da ke ba”
Na kwantar da kaina saman cinyoyinta wata kalar rahama ta uwa tana shiga cikina. 1
“Na gode Inna, na miki alkawari ba zan sake yin abunda zai sa ki fushi ba, ko da kuwa abun nan baya min dadi”
“Allah ya sauwake miki wannan rayuwa ya baki wanda zuciyarki take muradi wanda zai share miki kukanki kuma wanda za ki more hakurin da kika yi ta hanyarsa” 1
“Amin”
Sakina ta shigo tana tambayar jikin Noor, sai Inna ta amsa mata da
“Ya ji sauki, yanzu wanka zan yi na koma”
“Bari na shirya na je”
Na fada ina kokarin tashi tsaye, sai Inna ta rike min hannu.
“Aa ba sai kin je ba, ki hutar da kanki daga yau zuwa gobe”
“Saboda mai?”
“Saboda ki samu sukuni a zuciyarki, kuma ki shirya amsa tambayoyin da Noor zai miki, domin yana ta min na ce masa ban sani ba ke kadai kika sani, dan haka yana nan yana jiranki, kuma Jibril yasa an canja mana wata asibitin tun jiya da dare an kaimu wata” 1
“Tau Inna”
Na amsa ba dan raina ya so ba, tabbas Jibril na daf da rabani da dan na ni kadai na sha zafin daukar cikinsa na raineshi kuma na haifi abuna saboda kawai shi yana da dukiya. 5
JIBRIL POV.
Shiru ya yi ya rasa abunda zai cewa Abbah, zuwa can ya sauke ajiyar zuciya ya ce
“Abbah sam na manta da ranar ma sai yanzu”
STORY CONTINUES BELOW
“This is rubbish kasan hasarar kwangila irin wannan tana janyo a fara raina mana kamfani? Kowa ya sa rai mu za a bawa kwangilar nan amman saboda sakacinka komai ya lalace”
“Abbah kasan ba guri daya hankalina yake a yanzu ba”
“Fine ka mikawa Siraj ragamar kamfanin nan, a duk lokacin da ka dawo cikin hayyacinka sai ka kamfanin ya dawo hannunka, amman ba zai yiyu muyi ta hasara hakan nan kawai ba”
“Okay Abbah nima hakan zai fi min an gaskiya bana cikin kwanciyar hankali a yanzu” 1
“Ai kai ka jawa kanka komai saboda baka jin magana, da gaskiyar Hajiya (step mother dinsa) da take cewa na rika kyaleka duk da gangan kake komai” 1
Ajiyar zuciya Jibril ya sauke be sake cewa komai ba, yana ta sauraren fadan da Abbah ke masa, kamin daga bisani ya kashe wayar.
“Oh Allahna kai kadaine gatana”
Ya furta yana shafa fuskarsa. Siraj dake gefensa ya dashi
“Ka kwamtar da hankalinka Jibril komai zai wuce, matsalar ka kawai kana sakewa Nawwara ne da yawa, be kamata ace tana maka irin wannan cin mutuncin ba” 1
“Idan bata min wannan cin mutuncin Siraj ba zan taba gane cewar tana so na ba, kuma a duk lokacin da ta yi fushi ta kan fadi kalmar da zata amfaneni, jiya ma ta fadi kalmar wani Faruk wanda na fada maka maybe tsohon mijinta ne” 1
“Ba lallai ya zama tsohon mijinta ba Jibril ina ta nanata maka, maybe wani dan uwanta ne ko makocinsu, ni abunda na ke ganin ya fi kawai ka ka fitar da kudi sai a nemo wani wanda zai aureta ana daura auren sai ya saketa kaga shikenan sai kai kuma ka aureta hankali kwance zuciya zaune, sai a nemo wani talaka mai neman na kansa ko da tsoho ne Nawwara ta aura” 2
“Amman dai kai wawa ne Siraj, taya zan bari Nawwara ta auri wani? Ai itama ba zata taba yarda ta auri wani dan ta fito ta aureni ba, and ba zan iya barin kowa ya kwanta kusa da ita ba saboda har yanzu ita iyalina ce, duk wanda ya kwanta gado daya da matata sai na hora shi, ballantana kaddara ta kaishi ya kusanceta ko waye mutuwa kawai ta dace da shi” 1
“No Man no ba ina nufin ya aureta ba ya kwana da ita ba, ana daura auren zai saketa shikenan fa, idan kuma kana jinnrashin natsuwar hakan sai ka nemi wanda yake kusa da kai wadda ba zai musa maka ba sai ya aureta” 1
“Zan yi tunani akai, amman ina son ka bincika min gaskiya magana akan auren nan, and Abbah ya ce na mika maka ragamar kamfanin nan yanzu”
“What…?”
Ya amsa da karfi zuciyarsa kuma cike da farinciki. 5
“Saboda mai?”
“Ba komai kawai ina ganin kamar akwai wanda yake tsegunta ma Abbah wani abun ne akan kamfanin da kuma rayuwata, saboda kwanaki ma yayi ta min fada akan wai ina shan cocaine yanzu kuma yana fada akan kwangilar gobnatin taraiya da muka rasa ta gina gidaje, wai an fada masa ko takardar kamfaninmu bamu tura ba” 1
“Gaskiya akwai wanda yake labarta masa wani abu akai, amman gaskiya ni ba zan iya daukar ragamar kamfanin nan ba, taya kai za ace ka aje abu ni kuma sai ace na dauka? Gaskiya ba zai yiyu ba” 5
“No no he trust you ne, ai kasan Abbah idan be yarda da mutum ba ba zai saka shi a arkar kasuwancinsa ba, ni ma da be yarda da ni ba ai da ba zai kawo nan a wannan kamfanin ba, so karka bashi kunya kawai ka yi aikin nan nima zaka taimakamin domin zan samu na kula da Nawwara”
“Zan yi tunani a kai”
“Ba wani tunani sai ka karba”
Siraj ya tashi tsaye yana nuna kamar be jidadin abun ba, alhalin kasan zuciyarsa farinciki ne kawai da murna. 2
STORY CONTINUES BELOW
“Zan tafi xan sa ayi bincike akan Nawwara din”
“Thank you so Friend Allah ya bar mu tare” 2
“Amin akwai hoda idan…” 1
“Hodar nan tana daya daga cikin abunda Nawwara ta tsana, ina ta kokarin daina shanta ina son na zama mutumen kirki Siraj, ina da yaro a yanzu kuma ina son Nawwara ta dawo rayuwata dole ne wani halin za a zubar da shi” 2
Tabe baki Siraj ya yi.
“Nawwara dai Nawwara, ga Zinatu tana son ka amman hankalinka yana gurin wacce bata ganin tausayinka” 1
“Ka tafi kawai zai fi maka, bana son kana min maganar kowa ban da Nawwara”
Ya fice yana wani sunsun da kai. Yana fita Jibril ya kira Rabi ta waya yana fada mata abunda yake son ta yi.
“Bincike na ke son ki min akan Nawwara saboda na san Siraj ba zai samu dama ba a yanzu saboda shi ne new ceo din ku yanzu”
“New ceo Sir? Why ka bar garin ne?”
“No Abbah ya bukaci a bashi ni akwai abunda na ke, ki bincika sosai please”
“Okay Sir amman miye alakarka da ita saboda na san irin binciken da zan yi”
“She’s my wife, my ex-wife mother of my only Son”
“Okay Sir zan yi komai inshallah”
Sai ya kashe wayar ya mike tsaye ya shiga bathroom, in 40 minutes ya shirya ya fito ya nufi asibitin zuciyarsa cike da zumudin ganin dansa.
Tunda ya shigo cikin aaibitin ake ta gaishe shi har ya isa sashen da Noor yake be riko masa komai ba, saboda yasa a rika kawo masa abincin da abun tabawa daga wani kasaitaccen restaurant sau uku a rana.
Yana tura kofar dakin ya shiga, sai ya nemi farincikin da ke zuciyarsa da fuskarsa ya rasa, saboda ganin Bilal da ya yi zaune saman hospital bed din rumgume da Noor da ya shige jikinsa sosai ya labe kamar mai bachi.
“What are you doing here?”
Ya tambaya kamar be san inda Bilal ya fito ba. Uffan Bilal be ce masa ba ya yi kokarin sauke Noor daga jikinsa sai Noor ya kara lake masa wanda hakan ya bata ran Jibril.
“Uncle Bilal zan bi ka”
“Aa baka ganin baka da lafiya? Kana bukatar kulawa idan ka ji sauki da kaina xan zo na daukeka na kaina gida sai muje yawo ka ji”
Ya gyada masa kai yana kuka.
“Uncle Bilal zaka dawo anjima ko?”
“Eh zan dawo”
“Tau ka zo min da Momy”
“Zata zo, aiki take yi shiyasa bata zo ba”
Sai da Bilal ya shafa kansa sannan ya fita sai Jibril ya bishi a bakin kofar dakin ya jefa masa wata magana.
“Nawwara bata fada maka karka sake zuwa ganin Noor ba”
“Bata fada min ba”
“To ni na fada maka”
Bilal ya kalleshi ta kyau sannan ya ce.
“Look Jibril duk abunda na ke maka a kamfani ina yi maka ne sabida you’re my boss a gurin kuma ina aikine dole duk abunda ka ce na bi, a waje ma ina respecting dinka so karka zubar da girmanka” 1
“Karka soma fada min wata maganar banza a nan, daga Nawwara har Noor mallakina ne” 1
“Noor ne kawai Mallakinka, amman Nawwara ba mallakinka ba ce, ka bar ganin kana da duka ba komai kudi yake siya ba, rashin arziki kuma ba shi zaisa takala ya wofintar da kanta a raina shi ba, ka taka a hankali” 1
Sai kawai Jibril ya yi dariya ya juya ya koma ciki. A ranar ya sha fama da Noor kamin Inna ta zo saboda Noor na ganin kamar Nawwara ba zata sake zuwa gurin ba, a ranar ya saka cewar kar securities din su sake bawa kowa damar ganin dansa in ban da Inna sai kuma wanda Inna ta fito da kanta ta zo da shigo da shi.
Da dare ya koma gida jikinsa agajewa ba dan kuma ya yi wani aikin ba sai dan tunanin da ke zuciyarsa ne ya saukar masa da gajiya. A lokacin ne Rabi ta kira shi take labarta masa abunda ta samo kamin fa kara bincike.
“Sir Nawwara ta auri miji biyu bayan baban Noor da auri wani Faruk amman ya rasu, sai dai mutane suna zargin cewa aurenta na fari ba aure ta yi ba saboda an boye abun kuma sai ta dawo gida da ciki”
Ya dan yi Jimm kamar ba zai ce komai ba.
“Ina kika ji wannan”
“A wani gidan makotansu ne na ji, saboda na nuna musu yayana yana son ya aureta ita kuma ta boye masa tace budurwa ce” 1
“Thank you, akwai wani abun da ya kamata na sani ne bayan wannan”
“Babu amman nace suna fama da talauci sosai, Babanta ya rasu saboda sukan da police suka masa akan sun kamashi ya yi sata wacce matar da yayanta suke cewa wai ba gaskiya bane, wasu kuma ce gaskiya ne, yar uwarta kuma ta rasu wacce ta fi so a cikin kananeta, zan fadada bincike nan har sai idan na kammala sannan zan labarta maka komai”
“Na gode, na san ba aikinki bane amman na gode, ki turo min account number dinki”
“Okay Sir thank you”
Yana sauke wayar sai duk jikinsa ya yi sanyi, wani irin tausayin Nawwara ya rufe shi. Ranar kwana ya yi da tunaninta da kuma tunanin irin wahalar da ta fuskanta gidansa. Washe gari sun da safe ya shirya ya nufi asibitin dan yana son ya yi breakfast tare da Noor, sai ya samu Nawwara bakin kofar harabar da zata sadata da dakin an hanata shiga, tana ganinshi ta sauke kanta kasa har sai da ya karaso kusa da ita.
“Nawwara da yanzu ban dawo rayuwar Noor ba, haka za ki yi ta masa bitar maratun na ko?”
“Akwai sama ko kasa da abunda ya kamata na karanta masa ne bayan abunda ya faru? Kana da sa’a Jibril komai kake so kana samu, na raini da na rana daya ya zo ya zama naka” 6
Ya cije lebensa na kasa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce
“Kina ganin kamar darin duniya ne abunda kawai nake so? Ba shi ne kadai gata ba Nawwara, matukar babu ke babu Noor ina jin kamar rayuwata bata da amfani a duniyar nan, ni taimake ni Nawwara ki bani damar da zan zama silar farincikinki”
Ta tada kai ta kalleshi da idanuwata dake cike da kwalla.
“Idan na yafe maka zaka daina shiga sabgata?” 5
“Zan daina matukar za ki daina shiga rayuwar da na….!”
Na yi murmushin mamaki ganin irin karfin halin Jibril, lallai maza basa da kunya yanxu har yana da bakin da zai ce min wai sai idan zan rabo da dansa? Ni zai kalli tsabar idanuwana ya ce min haka?
“Ba zaki iya rabuwa da Noor ba, ni kuma ba zan iya rabuwa da ke ba, ba kuma zan daina neman ki yafe min ba”
“Zan iya shiga?”
Na tambaya ina kallon security da ya tare kofar, sai ya kalli security ya ce
“Bata hanya ta wuce matata ce” 1
Da sauri ya janye min ya bude min kofa, ni kuma na shiga ina murmushin jin ya kira ni da matarsa lallai iska na wahalar da mai kayan kara. Ina gaba yana bina ba dan na san inda dakunan suke ba daman can Inna ce ta kwatantamin, har na wuce dakin sai ya kira da sunan da be taba kirana ba har na dauka cewar ba da ni yake ba
“Mrs Makama” 2
Ganin ban waigo ba yasa ya kara da cewar
“A nan dakin yake”
Juyowa na yi na dawo na shiga kofar da ya bude min, a yanayin yadda dakin Noor yake sai ka rantse da Allah ba cikin asibiti ba ne, ya kawata masa dakin da teddys ga wani madaidaicin plasma dake lake gurin freezer din dakin. Noor na ganina ya yi saurin saukowa saman gado ya doso inda na ke sai muka rumgume juna.
“Momy miyasa baki zo ba jiya da wata jiya kamin jiya?”
Dariya na yi na shafa kansa.
“Tan ba ga Daddynka yana kula da kai ba?”
Ta da kai ya yi ya kalli Jibril.
“Momy da gaske shine Babana?”
“Ee mana ba ga kamaninka nan kana ganin a fuskarsa ba?”
“Amman Babana Faruk fa?”
Daukarsa na yi na dora saman hospital bed din sai nima na zauna, Jibril kuma ya zauna a kujerar da ke fuskantarmu, sai na kama hannayen Noor na ce
“Baba Faruk ya rike ka kamar dansa, saboda a lokacin Babanka baya nan ya yi tafiya zuwa gurin karatu wata kasar, kuma baya son ace maka baya nan shiyasa ya fadawa Baba Faruk cewar ya ce shine mahaifinka kamin ya dawo”
“Miyasa Inna ta mareki saboda shi?”
“Saboda na boye maka gaskiya tun farko ban fada maka ba sai yanzu, tana ganin kamar ba zaka fahimta ba”
“Miyasa kika ce Uncle dina ne sai kuma yanzu kika ce shine Babana kuma?”
Yanzu kan ban san mi zan kara ce masa ba kuma, jin na yi shiru ban amsa masa ba yasa ya kara aiko min da wata tambayar. 1
“Ko dai da Baba Faruk ya rasu sai wannan ya dawo?”
“Aa kamin na auri Faruk na fara auren Babanka sai kaddarar aure ta raba mu, ya tafi karatu wata kasar sai Faruk ya aureni kai kuma ya rika ka kamar dansa saboda yana so na kuma ya san kimata, amman ba shine asalin mahaifinka ba, wannan shine mahaifinka na gaskiya shiyasa ake kiranka da Muhammad Jibril ba Muhammad Faruk ba”
Ya yi shiru kamar mai tunani sai kuma ya yi murmushin da ya bayyana hakoransa.
“Momy na gane, yanzu Babana be rasu ba kenan?”
“Gashi a gabanka kana gani, kuma yana son ka sosai kai har ma ya fi ni son ka”
Na fada ina nuna masa Jibril
Murmushi Noor ya yi sosai ga dukan alamun yaji dadin haka, sai na rika shi ya sauka saman gadon ya nufi inda Jibril yake yana ta kallonsa.
“Kuma fuskarmu guda ko Momy?”
STORY CONTINUES BELOW
“To ai shine mahaifinka shiyasa kuka yi kama, kaga ai baku yi kama da Baba Faruk ba ko kun yi kama?”
“A’a”
Sai Jibril ya daukeshi ya dora saman cinyoyinsa ya rumgume yana sauke ajiyar zuciya.
“Thank you so much Dear” 1
Ya fada yana kallona fuskarsa na nuna jindadin da ke cikin ransa. Tun daga ranar na ke ta kokari wajen kawarda duk wani abu da zuciyata take nuna min, hakan ba karamin faranta ran Jibril da Inna ya yi, ni ko farincikina farincikin mahaifita da kuma da na, sati daya da muka a asibiti ya isa ya samarda wani kudi na littafin soyayyar uba da da tsakanin Jibril da Noor, saosai da sosai Noor yake son babansa yana shiga jikinsa wani lokacin haka zai kyaleni ya yi ta sha’aninsa shi da mahaifinsa, Jibril kuma kamar ya cinye shi yake ji cikin kwana biyu ya yayatawa duniya cewar yana da, abun mamaki har Abbah sai da ya zo ganinsa yan uwansa ma wadanda suke uba daya sai da suka zo, abokaninsa na nesa da na kusa suna ta zuwa ganin Noor saboda ya fada musu dansa ya kare a gabana wasu ke cewa daman wai kana da? Mun samu alheri sosai domin duk abunda ka bawa Noor Jibril baya dauka ni yake barwa, sai dai wani abun da yake bani mamaki duk cikin masu nan ban taba ganin Siraj ba duk kuwa da kasancewar ba ko yaushe na ke tare da Noor ba, amman a yadda nake ganin abotarsu ya kamata ace Siraj gana zuwa ko da be zo kullum ba ya zo ko da sau hudu ne a sati. Ranar da Noor ya kwana takwas a asibitin na bukaci a sallamemu amman sai ya ki, ni kuma ba dan komai na ke son komawa gida ba sai dan Bilal saboda kwana biyu nan na rasa gane kansa ya kasa fahimtata yawan zuwa da nake asibiti jinyar Noor yana ganin kamar wata sabuwar soyayyace ke kulluwa tsakanin da Jibril.
A ranar da muka fara zuwa kotu zama na farko na sha kuka a ranar saboda ya tuna min da mahaifina da kuma Habiba, na yabawa Dpo sosai domin ya nuna kulawa akan case din ga kuma police din da alkali ya bada ikon tsarewa har zama na gaba, wani abun da ya bani mamakin matar da ta ce Mahaifinmu ya yi mata sata tana da yanayi da Siraj sosai kuma ita ba ce a tsareta ba saboda tana da kudi ko kuma tana da daurin gindi ko kuma dan tana da kokarin kare kanta cewar ba ita ta saka su ba oho. Ni dai har muka fito daga cikin kotun ban daina harararta ba ita kuma bata daina kallona ba. 2
Tare muka fito da Inna da Sakina, sai Jidda da Bilal da kuma yan uwan Baba da na Inna, kowa da abunda yake fada ni dai ban ce komai ba, har muka shiga Napep muka dawo gida. Muna shigowa gida Jidda take labarta min cewar Mustapha ba shi da lafiya jiya aka kai shi asibitinsu Jibril.
“Miya ke damunsa?”
“Ke kika damunsa Nawwara”
“Kamar ya? Ai na ce na yafe masa”
Ta yi shiru bata sake cewa komai ba.
“Kinje kin duba shi?”
“Ina tsoron mahaifansa”
“Mai tsoro baya zama gwanin Jidda matukar kika saka tsoro a zuciyarki Mustapha ba zai taba fahimtar cewar kina son shi ba”
Ta kalleni da sauri.
“Waya ce ina son sa? Mustapha da yake son ki sai kuma ace ni ina son sa?” 1
“Ba fada min aka yi ba, a idanuwanki na karanta”
“Baki min adalci ba Nawwara baki san komai a kaina ba” 1
Ya mike tsaye a fusace ta fice, ni kuma na bita da kallon mamaki domin ban ga abun daga hankali a cikin wannan maganar ba.
Tashi na yi soma dora girki muna ta firar yadda zaman kotun ya wakana ni da Inna, da dare sai ga Bilal ya kirani a waya wai na fito yana kofar gida.
Na yi mamakin jin hakan saboda kwana biyu ya dauke min kafa daga zuwa fira ko da kuwa ni na bukaci hakan sai dai mu gaisa a waya, na dauri aniyar sakashi farinciki a yau ko da kuwa ba da niyar hakan ya taho ba, dan haka na dauki kayan kwaliyata na dandasa kwaliya mai kyau na feshe jikina da turaren da Jibril ya aiko min cikin kayan da ya siyo min kwanaki, na dauki gown din atamfa da take cikin kayan da Jibril ya aiko min na saka, ni kaina na san na yi kyau a wannan dare, Inna ma kallona kawai ta yi tayi murmushi, nima na fice ina murmushi.
A yanayin yadda na tararda shi yasa ni jin babu dadi, domin kuwa fuskarsa babu annuri jikinsa kamar a sanyaye, bayan na masa sallama sai ya amsa min idonsa akaina kamar zai cinyeni.
STORY CONTINUES BELOW
“Nawancy kin yi kyau”
“Dan kai kadai na yi ta na gode da ka yaba”
Sai dan yi murmushi.
“Aiko ya kamata na bada tukuici ko?”
“Ka adana tukuicinka da daddadan kalamanka har sai na fada maka dalilin wannan kwaliyar tawa”
“Akwai wani daliline bayan wanda na gani?”
“Sosai ma, a wancan gani ka yi, wannan kuma ji zaka yi”
Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi.
“Nawancy kina yaudarar zuciyata da yawa, da fushi na zo nan gurin, amman kin shiga kin yi nikaya kin tarwatsa duk wani damuwa da fada da na zo da su”
“Ai daman haka ya kamata ko wace amarya ta kasance gurin angonta, mai wanke danuwarsa ta shimfida farinciki a zuciyarsa”
“Ina ma da gaske Nawancy amaryar Bilal ce da yafi kowa farinciki a duniyar nan”
“Akwai wanda ya isa ya hana abunda Allah ya zo kasanewarsa tun farkon hallitar Nawwara?”
“Babu”
“Ashe ko Nawwara sai ta fi Bilal kasancewa a cikin farinciki daga ranar da aka daura aurenta da angon da ya fi ko wane ango tsada a duniyar nan”
Ya yi murmushi yana kallona tare da lumshe ido.
“Ina son ki sosai Nawancy”
“Kai so na kawai ka ke ni ko kaunar ka na ke”
Ya sauke ajiyar zuciya.
“Kamin ki kaini duniyar da ba zan iya dawowa ba, fadan min dalilinki na yi wannan kwaliyar”
“Kamin na maka albishir mai tsada ya kamata ace ka fada min abunda ya kawo ka nan”
“Yo tun yaushe kika duniyar kwakwalwa kika mantar da ni wanene ni ma, balle abunda ya kawo ni nan kuma”
“Yanzu dai rumtse idonka sai na fada maka albishir din”
“Ai kunnene yake ji ba idanuwa ba”
“Ina gudun kyawawan idanuwan nan naka su ba ni kunya ne”
Sai ya yi dariya ya lumshe idanuwasa.
“Inna ta ce na fada maka, idan ka shirya ka turo magabatanka suje can Baban gida su gana da nawa magabatan”
Da sauri ya bude idanuwansa ya kallini
“Da gaske Nawancy?”
“Na saba maka irin wannan wasan ne?”
Wani ihu ya yi ya daka tsalle ya dire, ni kuma na yo cikin gida da gudu ina dariya. Da na shigo sai na ce da Inna Bilal ya ce zai turo magabatansa amman be saka rana ba. 4
“Mashallah Allah ina fatar kina sonshi dan karki yi wa kanki zabi irin na baya, kuma ina son ki bawa Allah zabi a cikin lamurranki nima zan taya ki da addua idan aurenki da Bilal alheri Allah yasa ayi, idan kuma ba alheri ba ne Allah ya kawo maslaha”
“Amin Inna, inshallah Alheri ne”
Daga wannan sai fira ta biyo baya Inna na ta nanata min burinta na ganin na yi aure domin shine kwanciyar hankalinta, a daren Bilal ya yi min kira ya fi a kirga ni kuma na ki dagawa, misalin uku da rabi na dare na tashi na yi nafila na Mikawa Allah zabina akan ya zaba min dukan abunda zai fi zama alheri a rayuwata. Washe gari bayan na gama komai na shirya na nufi asibiti zuciyata cike da tunanin yanayin Jidda gabana kuma nata faduwar da ban san daliliba.
Jirbil kawai na tarar a dakin Noor baya nan, na gaisheshi cikin ladabi kamar yadda na saba masa a yanzu. Be amsa min ba sai ya matso kusa da ni yana ta kallona kamin ya risina kasa wanda hakan yasa ni ja da baya.
STORY CONTINUES BELOW
“Nawwara dan Allah ki yafe min abunda na yi miki na san na yi kuskure amman ki dubi girman Allah ki yafe min” 4
“A kwanakin nan da muka dauka be isa yasa ka fahimci cewar na yafe maka ba?”
Ya mike tsaye yana kallona.
“Ki kalli cikin kwayar idanuwana ki ce kin yafe min”
Ya fadi hakan ne saboda ya tabbatar da yafiyar tawa, domin yasan babu abunda zan gani a cikin idanuwansa sai tsanarsa da kiyayyarsa, ras na sauke idanuwa cikina nasa zuciya a natse bakina ya furta cewar.
“Na yafe maka Jibril Allah ma ya shaida na yafe maka”
Lumshe ido ya yi sai ga hawaye sun sauko masa, yaja wani dogon numfashi ya sauke, sannan ya bude idanuwansa ya kalleni
“Yanzu za ki iya aure na kenan?” 1
“Dan na yafe maka ba shi yake nufin zan iya sake zaman aure da kai ba, ni ina da wanda zuciyata take so”
“Wa kike so Nawwara? Wanene wannan wanda ya fini sa’a da dacewa a rayuwa? Wanene wanda be shirya zaman duniya a yanzu ba?”
Na shiru ina kallonsa.
“Mustapha ne ko?”
Kamin na ce wani abu sai wata nurse ta turo kofar dakin ta shigo hannunta rike da na Noor.
“Sir an gama”
“Thank you”
Ya fada yana share hawayensa, sai da ta fice sannan ya nufi Noor ya dauke shi ya rumgume.
“Come here my happiness”
“Momy yanzu kika zo?”
Na daga masa kai sai na karasa gurin gadon na zauna, Jibril kuma ya zauna a kujerar da ke fuskantata yana rumgume da Noor, idanuwansa na ta xika da hawaye tana kallona.
Muna haka aka turo kofar dakin a aka shigo Zinatu ce tare da Rabi sai kuma wani bakon mutun da ban waye fuskarsa ba. Da dan farka ta karaso kusa da mu ta aje ledodin da ke hannunta sannan ya zauna kusa da ni tana kallon Jibril.
“Ashe kana nan”
“Akwai wani gurin da ya kamata na kasancene bayan nan?”
Ya fada yana mikawa mutumen hannunsa su gaisa. Rabi kuma ya zo tana mikawa Noor hannu
“Zo nan dan Daddynsa”
Dariya kawai ya yi mata amman be yarda ya bar jikin Jibril ba, ya labe sosai kamar wani karamin yaro mai shan mama.
“Sir Akwai maganar da ya kamata mu yi”
“Tana da muhimmanci ne sosai?”
“Eh akan abunda kasa ayi ne, kuma Siraj yana waje yana jiranka ya ce a gaishe da Noor”
Zinatu ta mike tsaye ta karbi Noor shi kuma ya tashi ya fice dare da mutumen da kuma Rabi.
“My Son ya jikinka?”
“Na ji sauki Daddy ya ce nan da kwana biyu za a warware hannu”
“Mashallah Allah ya tsare gaba ya kara lafiya”
“Amin”
Ya amsa bakin nan chakoi, sai ta kalleni.
“Kin kusa komawa aiki kenan ko?”
“Inshallah”
Daga haka ban sake cewa wani abu ba, itama bata sake cewa ba, sai ma dauko ledar da ta zo da ita da tayi ta bude ta fiddo chocolate mai shegen tsada ta mikawa Noor. Bayan kamar mintuna talatin sai Rabi ta sake shigowa tana fadin.
“Zinatu Siraj na kiranki wai ki zo zai wuce”
Zinatu ta sauke Noor saman jikinta ta aje shi kasa tare da yi masa kiss.
“Allah ya kara sauki da na”
“Amin na gode”
“Nawwara na wuce”
“Mun gode Zinatu Allah ya bar zumunci”
“Amin”
Bayan ta fice, Rabi ta maida kofar dakin ta rufe ta nufo ni tana fadin.
“Nawwara ina son muyi magana da ke mai muhimmanci”
“Akan me?”
“Akan ke da Noor da Jibril da kuma Siraj abunda ya shafi rayuwarku ne ku duka”
Gabana ya fadi
“Ban gane ba”
“Asirrance na ke son mu yi maganar, amman kamin nan ko kin san cewar Jibril ya kori Bilal a kamfani tun last week? And there’s something behind Noor accident…” 8
Na mike tsaye da sauri.
“When how i don’t understand?”
Kamin ta kara cewa wani abu sai ta ga Jibril ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta yi saurin juyawa tana dariya.
“Kin jiki Nawwara da wata magana, masu kudi ai suna can inda suke, ni dai na tafi Allah kara lafiya”
Kamar na ce wani abu sai kuma na amsa da.
“Amin na gode”
Tana ficewa, Jibril ya kalleni ya ce.
“Kin san an kawo Mustapha a asibitinmu kuma ba shi da lafiya sosai, yana icu room 14”
“Na sani”
“Mi kike son a masa?” 2
Na masa wani kallo kamar ban fahimci abunda yake cewa ba. Sai yasa hannunsa aljihu ya ciro karamin hoton Habiba ya mika min. Na karba hannuna na rawa sam na manta da inda na jefarda hoton ma. Ina karba sai ya juya ya fice ya bar nan tsaye da mamaki, ya aka yi yasan abunda Mustapha ya aikata? Ina ya samu hoton Habiba? Me yake nufi da abunda nake son a yi masa, ga kuma maganganun Rabi da suka tsaya min a rai.
Saurin juyawa na yi na fita harabar asibitin ina tambayar inda icu yake, aka fada min sai na doshi gurin da sauri ina duba number din room din har na kai ga mai 14, ina dosar dakin sai Jibril ya fito tare da wasu Nurses, kallona kawai ya yi ya dauke kai ya fice, ni kuma na saki baki jikina a sanyaye ina kallon dakin, Mustapha nake hangowa da ke kwance kamar gawa, Mutanen da ke cikin dakin suna ta rusar kuka, ban san lokacin da nawa hawayen suka fara zuba ba, na juyo da sauri na biyo bayan Jibril hangosa na yi tsaye yana magana da wani likita na doshi inda yake ina hawayena bakina na rawa kafafuwana kuma kamar zan fadi.
Yana hangoni ya yi saurin sallamar mutumen ya shige dakin, ni kuma ina isa na baki kofar office din na fada.
“Me ka masa Jibril? Me ka masa?”
Ya zauna saman kujera yana kallona
“Duk mutumen da ya kashe rai shima kisa ne ya cancanta da shi, daukar fansar yar uwarki na yi miki” 2
“Be kashe rai ba, fyade kawai ya yi mata miyasa zaka kasheshi mi ya kama?”
“Ba shi kadai zan kashe ba?” 1
“Mutum nawa zaka kashe?”
“Adadin mutanen da zasu furta ko kuma su nuna soyayyarsu a gareki, kamar Bilal” 9
Ya fada yana tabe baki, ni kuma na zaro ido naja baya baya har ina kokarin faduwa, sai kuma na juya a firgice na fice daga office din kamar mahaukaciya.Har na kawo bakin gate din asibitin kuka na ke ina ta tunanin abun yi, wane irin mutum ne da zai kashe rai saboda cin ma wata bukata tasa ta kanshin kansa? Ko ni da na tsani Mustapha ba zan iya kasheshi ba ko na saka a kasheshi ba, bayan shi kuma ya ce Bilal ne next, dole ne na sanar da police wannan maganar ba zan iya kyalewa ba, wayata na dauko na kira Bilal bugu daya ya dauka muryarsa da walwala da alama yana cikin farinciki. +
“Nawancy”
“Kana ina”
“Ina kofar gidanmu”
“Dan Allah ka sameni guiwa station yanzu”
“Lafiya? Kuka kike yi”
“Ka zo yanzu ka ji”
“Okay tau”
Daga haka na kashe wayar na tari achaba na hau domin shi ya fi kusa da station, ko da na isa har ya isa bakin station din yana ta yi min waya, yana ganina ya doso inda na ke yana tambaya dalilin kiransa da na yi.
“Bilal Jibril ya kashe Mustapha kuma ya ce kai ne na biyu”
“What? Nawancy kin san abunda kike fada kuwa”
“Na sani na gani da idona ya kasheshi”
Na fada ina kuka, sai ya matso kusa da ni yana kwantar da hannayensa.
“No listen Jibril is very smart ba zai kashe Mustapha, maybe dai yana miki wasa ne, ko kuma yana son ya yi amfani da wannan damar ne ya cinma wani buri nasa”
“Wallahi da gaske ne, na ga gawar Jibril da kaina”
Na fada ina cigaba da kuka, sai ga wani dan sanda ya zo kusa da mu yana tambayar dalilin zuwanmu gurin.
“Dpo na ke son gani shi yace na same shi nan akan case din mahaifinmu”
“Amman baki da number shi?”
“Ba ni da amman shi yana da tawa number, dan Allah ka fada masa da gaggauwa”
“Okay”
Ya juya ya koma ciki, na yi wannan karyar ne saboda na samu gamin dpo cikin sauki, domin nasan duka wadannan kananan yan sandan ba zasu iya handling case din Jibril ba. Bayan kamar minti biyar sai ga police din ya dawo ya ce mu shiga ciki, sai dai basu bamu damar hakan ba sai da suka binka komai na mu.
Cikin office dinsa muka sameshi yana sanye uniform dinsa na yansanda yana ta rubuce rubuce a takardun da ke gabansa, da hannu ya nuna mana kujerar zama.
“Bismillah”
Na zauna hawaye na ta bin fuskata, sai ya aje rubutun da yake ya fuskance mu.
“Lafiya dai Nawwara?”
“Ba.. Ba.. Ba akan case din Baba na zo ba, na ce haka ne saboda na samu ganinka”
Na fada ina kuka, sai mika hannunsa ya dauko tissue ya bani na share hawayena da majinar da ta zubo min, sai kuma ya mike tsaye ya nufi freezer sa ya bude ya dauko gorar ruwa da kofi ya bulbula min.
Ba musu na dauka na shanye, ya sake zuba min na shanye sai ya karbe kofin ya maida gefe ya zauna yana kallona. 1
“Relax ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ki a nan”
Na gyada masa kai sannan na sauke ajiyar zuciya wanda hakan ya bani damar soma masa bayani.
“Wani ne yake barazana ga rayuwar Bilal ya ce sai ya kasheshi”
Ya kalli Bilal a kaikaice.
“Miye tsakaninki da Bilal din?”
“Shine wanda zan aura”
“Wacan wanda yake barazana ga rayuwarki fa?”
“Tsohon mijina ne”
STORY CONTINUES BELOW
Jinginawa ya yi da kujerar yana kallonmu.
“Fada suka yi da har maganar kisa ta shiga ciki”
“Aa kawai dai baya son shi ne, yanzu ya kashe wani kuma ya ce Bilal ne na biyu”
“Dan taadda ne mijin na ki?”
“Aa likita ne, amman yanzu yayi ma wani allura ya mutu”
Ya kalli Bilal
“Kai namiji ne maybe zaka fi yin bayani mai gamsarwa, ko fada ya taba hada ka da mutumen? Ko kuma wani abu ya shiga tsakaminku”
“Gaskiya babu abunda ya taba shigo tsakaninmu”
“Haka kawai yayi maka barazanar kisa?”
“Aa shi besan an yi ba, ni ya fadawa kawai ina son a shiga tsakaninmu da shine domin duk abunda ya samu Bilal shine”
“Okay amman dole ne zamu yi magana da shi, yanzu zan sa a dauki statement dinku, kin san inda zamu samu wacan din?”
“Ee ina da number wayarsa”
“Tau ki bamu sai mu kira”
Daga haka ya dauki telephone dinsa ya kira wani police yana shigowa ya sare masa shi kuma ya nuna mu.
“Kaje ku dauki statement dinsu, kuma ka karbi number a hannunta ka kira mutumen ka ce ana nemansa”
“Yes Sir”
Tare muka fito da police din suka kawo mu reception suka dauko takardar aka saka sunana da na Bilal sannan na soma yi musus bayanin komai, bayan mun gama na basu number Jibril suka kira shi, ko thirty minutes ba a kara ba sai gashi ya iso gurin fuskara babu annuri. Sai aka sake maida mu gurin dpo tare da statement din da aka dauka. Muna shiga Jibril ya mika masa hannu suka gaisa ya zauna saman kujera ba tare da ya jira an masa izinin zaman ba, Bilal ya zauna a kujerar da ke fuskantar ta Jibril, ni kuma na zauna a kujerar da ke bayan Bilal.
“Dpo kun ce kuna bukatar ganina”
“Yes Nawwara ta kawo kararka akan cewar kana barazana ga rayuwar mijin da zata aura Bilal”
Sai ya juyo ya kalli Bilal kamar daman can be san da shi a gurin ba sai yanzu, sai kuma ya maida dubansa gurin dpo.
“Mi nayi?”
“Ta ce ka ce sai ka kashe Bilal, kuma ka kashe wani kamin shi ka ce shine next”
“Yanzu dpo tsakanin da Allah na maka kama da mai kisa?”
“Ai abun ba daga kama ba ne”
“Idan ina son kashe Bilal ba sai na fadawa Nawwara ba, kuma taya namiji mai iyali kamar ni xai bata lokacinsa gurin wannan wasan kamar wani karamin yaro? Ni ban kawo kararshi ba shi zai kawo karata? Mutumen da kake gani yana barazana ga rayuwata da ta iyalina, my friend has told me Bilal din nan yana da hannu a kokari kashe min yaro, amman ban masa komai ba saboda ban tabbatar da gaskiyar ba na fi son na kama shi red handle, wannan yasa na koreshi daga kamfanina, a kamfanina yake aiki amman babu irin cin fuskar da baya min da matar nan saboda ya san ina sonta”
Ya juyo ya kalli Bilal.
“Saboda na koreka daga aiki shiyasa kake kokarin bata min sunan asibiti ko? Kake kokarin saka Nawwara against me ko? Idan mun gama da wannan case din zan shigar da nawa case din akanka, dan zaka iyayi min komai wajen ganin ka bata min suna ko aikina”
“Kana ganin xaka iya taka kowa saboda kana da kudi ko Jibril? Zuciyarka tana yaudararka akan ka aikata dukan abunda kake so saboda kana da kudi ko? Har yanzu zuciyarka karya take fada maka, ka kasa fahimtar cewar ba komai kudi suke siya ba, kana yaudarar kanka da yawa Jibril”
STORY CONTINUES BELOW
Cewar Bilal cikin fushi. Sai Jibril yasa dariya ya kalli dpo ya ce
“Kaga abunda na ke fada maka ko? Babu komai a zuciyarsa sai tsanata da neman hanyar da zai lalata min suna”
Ni kuma na mike tsaye ina fadin.
“Ba bata maka suna zai yi ba, gaskiya ya fada, kuma ni ka fadawa cewar sai ka kashe Bilal kuma yanzu haka ka kashe Mustapha”
Dpo ya daga mana hannu.
“Ba fada muka kiraku ku mana a nan ba”
“Kamin nan dan Allah dpo ina son ka bani yaranka suje su duba wanda ta ke cewa na kashe”
Mun dade a office din Bilal da Jibril suna ta musayar yawu, sannan saka rubuta yarjejeniyar cewar duk abunda ya samu Bilal Jibril ya saka hannu akan cewar ya yarda aka kira Siraj ya yi sheida Bilal kuma aka kira mahaifinsa. Daga bisani muka dunguma gaba daya muka nufi asibitin. Abun mamaki muna shiga dakin da Mustapha yake sai muka same shi zaune yana cin abinci kamar ba shi na ga a mace ba dazu. Yana ganina ya rika kokarin saukowa saman gadon sai mahaifiyarsa ta katsa min tsara. 5
“Ke kan kin shiga uku Nawwara, ba zaki bar dan mu ya huta ba, wannan wace irin rayuwa ce saboda ke dan mu yake kwance nan yanzu kuma sai ki biyoshi har nan asibiti akan wane dalili”
Juyawa kawai yan sanda suka yi suka koma ni kuma na sulale kasa a gurin ba dan na suma ba sai dan kafafuwana da suka min sanyi, ga hawayen da suka soma nin zuba babu kakkautawa.
“Haba Mom miyasa kike min haka ne? Wallahi da ki yi ma Nawwara fada kara ki yi min”
Tasowa ta yi ta karaso inda na ke.
“Ban san kaddara ba Nawwara, duk na rasa dana saboda ke ki fara kirga irin asarar da zata sameki kema”
“Tir da mace dattijowa irin ki ta tsaya tana fadin bata yarda da kaddaraba, ke an fada miki Nawwara son Mustapha take ne?”
Cewar Bilal yana kokarin defending dina, wata muguwar harara Hajiyar Mustapha ta watsa masa. Sai mahaifin Bilal ya katsa masa tsawa.
“Bilal wuce muje”
Sai da ya kalleni kamar ba zai iya bari a gurin ba, sai kuma ya juya ya fice tare da mahaifinsa, ni kuma na unkura na tashi ina nuna na fito daga gurin na nufi sashen da Noor yake.
Ko da na tura kofar na shiga Noor yana bachi hankalinsa kwance, kusa da shi na zauna hawaye na zuba a idanuwana, na kai hannu na shafa shi. Ina haka sai Jibril ya turo kofar dakin ya shigo yana sanye da labcoat, bayan ya maida kofar ya rufe ya zuba hannayensa cikin aljihu ya doso inda nake. 1
“Na sallami yan sandan”
Ban dago na kalleshi ba balle kuma har na amsa masa.
“I’m sorry Nawwara”
“Na tsane ka Jibril”
“Na sani”
Ya amsa min a takaice.
“Ka sake dawowa saboda ka ruguza sauran farincikin da ya rage min ko?”
“Wallahi ba dan haka na dawo rayuwarki ba, Nawwara ba ki cancanci auren kowa ba sai ni ko dan Noor, yanzu kin fi son ki barwa wata uwar ta yi miki rainon da? Dan kin san ba zan taba bari kije min da shi gidan duk wanda kika aura ba ko?”
“Kowa kallon mahaukaciya yake min, ka kunyata ni a gaban mahaifin Bilal” 1
“Bani da wani zabin ne Nawwara, Wallahi ina son ki sosai, saboda ke nake ta canja rayuwata Nawwara, dis week wani Malami zai fara zuwa yana karantar da ni saboda kawai na samu xama cikakkane namiji da kike so, amman hankalin ya koma kan Bilal, kin kasa fahimtata Nawwara”
Na daga kai na kalleshi.
“Bana son ka Jibril miyasa ka kasa fahimta? Hakika Noor be yi dacen uba”
“Babu wanda zuciyarki take so sai ni Nawwara, Nawwara idan kika aure wani ba ni ba, rayuwata da ta Noor tana cikin hadari”
“Bari idan na auri Bilal din, ku fadi ku mutu” 2
Ina fadar hakan na mike tsaye na share hawayena na fice daga dakin zuciyata na mugun kuna.
Ko da na iso gida numfashina har sama yake kamar zan hadiye zuciya na mutu saboda bacin rai, tun daga yanayin sallama ta ya kwantarda Inna irin damuwar da na taho da ita ga wani uban ja da idanuwa suka yi sun kumbura sosai saboda kukan da nayi. Muryata a dakishe na zauna saman tabarmar da Inna take zaune na fara rusa kuka, sai hankalin Inna ya tashi.
“Lafiya miya same ki?”
“Jibril ne”
“Yi hakuri tsagaita kukan sai ki min bayani, amman kamin nan kina da bakuwa”
“Wacece?”
Na tambaya cikin kuka.
“Muma ba mu santa ba, amman tun dazu take jiranki”
Na share hawayena na mike tsaye na nufi dakin Inna domin ganin wacece, abun mamaki sai na samu Aisha zaune tana kallon kofa da alama ta ji shigowata kuma ta ji lokacin da na doso dakin.