FETTA CHAPTER 15

FETTA




CHAPTER 15




Bilkisu ta tashi da ciwon mara wanda take kyautata zaton zuwan al’adarta da suke matse yazo dan cikar burin sa, Gwaggo sai faman lek’owa take tana tambaya yazo, +

Fitowar Bilkisu daga toilet kenan, ta tsaftace jikinta da ya soma b’aci, “Yazo ne?” Gwaggo ta jefa mata tambaya, “Eh”, “Mashaa Allah, ina zuwa”

Cikin minti biyu ta dawo d’auke da k’aramar kwalba ta mik’a mata “Karb’a ki zuba ciki”, Ta karb’a tana nufar band’aki.

Fetta ce tsaye jikin madubi, cikin shigar doguwar riga wacce ta kama jikinta ta zauna mata daram, Cool perfume ta d’auka ta fesa, bata son mai hawa kai, amai yake sata.

Hannun taji saman cikinta da ya fara tasowa (yau watan shi biyu da sati biyu), Idonta ta sauka kan hannun wanda ta tabbata Suraj ne, Ta jikin madubi yake kallon ta, Ba k’aramin kyau ta masa ba, Yayin da yake k’ok’arin hana kansa ganin kyan.

Cikin ya cigaba da shafawa cikin wani salo, Saitin kunnen ta ya mata whispering ” Hope babyna na lafiya?”, Kai ta d’aga masa sakamakon kasalar da ya saukar mata, K’ok’arin janye jikinta take, “Ina zaki ban gama gaisawa da babyna ba”,

Ya dawo ta gabanta, ya duk’a ya sumbaci cikin, ” My baby zan fita, sai na dawo”, Ya kamo hannunta ya d’aura saman cikin ya sumbata, Ya mik’e ya fice, Tabi bayansa da kallo, Tare da sauke kasalalliyar ajiyar zuciya.

   Gidan gonar sa ya nufa, Ya fito cikin shigar sa ta kamala da takun sa na k’asaita, “Oga akwai d’aukar wanka”, Cewar wani ma’aikaci, D’ayan yace ” Allah ya bamu danshin su”, “Amin”

    Yazo gaf dasu, suka rissina suka gaishe shi, Ya amsa da sakin fuska, “Ranka ya dad’e gashi akace na baka”, Ya fad’a yana mik’a masa wata k’aramar jaka mai azabar kyau, Ya karb’a ba tare da yace komai ba.

    Shigar sa office, Ya bud’e yaga me ye a ciki, Turare ne designer, sai flower da card mai d’auke da kalaman soyayya a k’asa an rubuta ” From Your Sahiba”, Tsaki yaja ya jillar da kayan gefe, Wayarsa ta d’auki ruri,

   Yayi receiving, “Manyan k’asa” Cewar Jabir(Abokin business d’in sa) “Ai kune manyan”, ” Ku dai da kuka yi wuyar gani”, Suraj yayi dariya yace “Ya harkoki?”, ” Alhamdulillah, An shigo da new model da motoci yaushe zaka shigo ka duba?”, “Ai JB ina ga ka turo mun ta yawa na gani, sauran abubuwa kuma ka duba mun, shigowa ta Lagos ba yanzu ba”, ” Wane uzuri ne haka sai hana ka, kai da nasan baka wasa da neman kud’i”, Ya fashe da dariya yace “Personal issue”, ” Toh Allah ya tabbatar da alkhairi”, “Amin”, Sukayi sallama yayi hanging up,

   ” Ina Karimar take?”, Kawo Sule ya fad’a cike da fad’a, Ya hankad’a k’ofar d’akin ta ya shiga, Yelwa ta biyo bayan sa, Karima dake shirya Abdul ta mishi wanka, Tace “Gani Baba”, ” Ina Mijin da nace ki kawo”, “Baba kayi hak’uri, wallahi kowa baya son aurena”, ” Dallah rufe mun baki, ba zan zauna da k’atuwar budurwa kamar ki cikin gida ba, a gari ana zagina ana cewa na ajiye karuwa, ki tashi ki tattara kayanki ki bar mun gidana, duk ranar da kika kawo miji kizo na miki aure”,

      “Dan girman Allah Baba kayi hak’uri, idan ka kore ni bansan ina zan je ba”, ” Cikin kwartayen ki d’aya ya kama miki gida, kuyi dadiro”, Kuka sosai take tana rok’onsa yak’i sauraren ta, Uwa da ya’ sai Allah, Yelwa tausayin yar’ ta ya kamata , Tace “Kayi hak’uri a k’ara bata lokaci”, A fusace yace ” Ba zanyi hak’urin ba, sau nawa ina bata lokaci”, Zata sake magana ya katse ta, “Kika sake magana wallahi a bakin auren ki, zaki bi ta”, Dole tayi shiru cike da tausayin ta, Ya tasa ta gaba yace ta bar d’akin.

STORY CONTINUES BELOW

    Karima tana kukan bak’in ciki ta shiga had’a kayanta, Abdul shima sai kuka yake, Ta had’a kayanta da na Abdul duka, Tasa yaro ya samo mata mai napep har k’ofar gida, Ta fito taci karo da k’anwar ta Binta ta dawo daga islamiyya, ” Yaya ina zaki da kaya?”, Tana sharar k’walla tace “Baba ya koreni”, ” Innalillahi me kika masa?”, “Ban fitar da miji ba”, ” Baba bai kyauta ba”, Ta fad’a cike da tausayin yar’ uwarta, “Yanzu ina zaki je?”, ” Nima ban sani ba Binta, kicewa Mama ta rik’a mun addu’a kema kina mun”, “In Shaa Allah”, Hawaye fal idonta ta shiga gida, Mai napep yaja Karima, ” Ina zamu je?”, “Sabon gari”, Ta bashi amsa.

   Gidan karuwai dake sabon gari, ya sauketa ta biya shi, Ta shiga, yan gidan sun saba da ita, Tana yawan zuwa, D’aki ta kama, Ta zaunar da Abdul ta fita nema musu abunda zasu ci.

   Ana kiran magrib Suraj ya shigo gida, Ya tsaya masallacin dake had’e da gidan yayi sallah, Ya nufi sashen Hajiya, Samee na kwance kan cinyarta tana mata shagwab’a, ” Tashi mara kunya, k’atuwa dake kina hawa cinya”, Tayi saurin mik’ewa ta shige ciki, “A’ah ka daina hantarar mun Auta, idan bata hau ba wa zai hau?”, ” Babyna mai zuwa”, Hajiya ta kama hab’a tace “Ohh ko kunya”, Ya sosa k’eya yana dariya, tare da zaman k’asan carpet, ya kama yatsun k’afarta yana ja(d’abi’ar sa tun yana yaro)

   ” Dama ina son magana da kai”, Ya tattaro dukkan hankalin sa gareta, “Mai neman auren Su’ad yana son turo iyayen sa”, Suraj ya washe baki, farin ciki ya bayyana kan fuskar sa, Babban burin sa ya aurar dasu, yana da niyyar yi musu maganar su fitar da miji, Hajiya ta lura da farin cikin sa tace ” Amma matsalar Bello yana son ta, Lamid’o yazo nema masa izinin magana da ita, na nuna amincewa ta dan banyi zaton zata k’i sa ba”,

   Suraj yace “Abu ne mai sauk’i, Yarinya ita ta nuna bata so, kuma ba za’a mata auren dole ba, kinsan dai yadda akayi nawa”, Hajiya ta d’an yi shiru kafin ta nisa tace ” Nama Su’ad sha’awar auren Bello mutumin kirki ne”, “Ko kin mata sha’awa Mama, tunda bata so sai a hak’ura”, ” Shikenan zan kira Lamid’o na lurar dashi na bashi hak’uri “, ” Yaushe ne zasu zo?”, “Jibi”, ” Ace musu su zo”, Hajiya tace “Ba damuwa”,

    Fetta nata sharar baccin ta saman kujerar falo, sam bata ji shigowar sa ba, Ya zuba mata ido, a ransa yace ” Ko bacci take kyau take”, Ya kalli cikinta a fili ya furta “Babyna Allah ya nuna mun kazo duniya lafiya”, D’akin ya shiga, a matuk’ar gajiye yake yana buk’atar wanka.

   Kawo Lamid’o jikinsa yayi matuk’ar sanyi, ransa ya b’aci jin zancen Hajiya, Yama kasa cewa komai, ” Hello Hello”, Can yace “Na’am”, ” Kayi shiru”, “Wani d’an tunani yaja ni, umm nace me zai hana a had’a sa da Feena tunda Su’ad tak’i”, ” Ai ba ita yace yana so ba”, Yayi guntuwar dariya yace “Banda abun ki Su’ad da Feena duk d’aya ne, Tunda yaso Su’ad ba zai k’i Feena ba, ni dai ina so a had’a zumuncin nan”, ” Toh ya tuntub’e ta ko zasu daidaita”, “Toh To shikenan”, Ya fad’a yana kashe waya, Hajiya zata so Feena ta amince.

    Aunty Jummai ta had’a dukkan abunda Boka ya buk’ata, Ta faki idon kowa ta yanki daji ba kunya ba tsoron Allah, Ta kai masa, Ya karb’a ya ajiye yace ” Aikin ta bayan kwana biyu za’a yi, ba sai ta dawo ba, zai aika aljani ya b’arar da cikin, sai ya zube zata zo”, Zata yi godiya, Ya katse ta “Ba yanzu ne lokacin godiya ba, sai aika ya cika”, Ta tafi cike da murnar samun nasara.

   Bello na kwance d’akin sa ya rasa meke masa dad’i, Yana ta kiran wayar Karima bata d’auka, daga baya yaji ta kashe, Yaje gidansu Binta ta sanar dashi Baba ya kore ta, Bansan ina zai nemo ta ba,  Kawo Lamid’o ya shigo, Cikin isa da bada umarni yace ” Ka janye zancen auren Su’ad, ka fara neman Feena”, Bai jira amsar sa ba, Ya wuce, Bello ya dafe kansa cike da mamaki, bak’in ciki da takaici na halin iyayen sa.

  Suraj na kwance kan gado, ya maida dukkan hankalin sa kan waya, motocin da Jabir ya turo masa yake dubawa, Fetta na zaune k’asan carpet tana had’a kayan wankin da aka kawo, “Fatima”, Taji ya kira sunan ta wanda shi kad’ai yake fad’ar sa haka, ” Na’am”, Ta amsa, Da hannu ya mata alama tazo, ta tashi taje gabansa, Wayar ya mik’a mata yace “Wacce mota tafi kyau a ciki?”, Ta karb’a tana mamakin dalilin tambayar sa, Ganin kamar tana mamaki, Yace ” Wani ne zai siyan ma matar shi mota wurina, yace na zab’ar mata mai kyau, kece mace zaki fi sanin kalar da ta dace da ita”, Bata tanka sa ba, ta shiga dubawa, Kusan minti uku ya d’auke ta,
      
   “Wannan”, Ta nuna masa, ” Baki iya zab’e ba”, Ya fad’a yana fisge, “Kasan ban iya ba, waya ce kace na zab’a”, Ta fad’a tana murgad’a baki, (Deep cikin zuciyar shi yasan motar tayi kyau, kuma ta dace ta mata, baya son yaba mata ne tafi feeling too important)

   ” Ni kike murgad’awa baki”, Ta sake yi, Zata bar wurin, Ya jawo ta, ta fad’o kansa, “Ouchh cikina”, A rud’e ya d’agota, Yana tab’a cikin “Meya same shi, me kike ji?”, ” Bigeni kayi”, Ta fad’a cike da shagwab’a, “Am sorry my baby”, Ya fad’a yana shafa cikin, Ta gumtse dariyar ta, Ba wani cikin ta da ya bige, tana son ta gujewa hukuncin sa ne.

   *Bayan kwana biyu*

  Iyayen Adnan sunzo da motocin su masu azabar kyau, Daga kansu kaga masu ji da naira, An tarbesu hannun biyu, Sun kawo sweets, goro dasu lemo tamkar za’a bud’e shago, Ranar Su’ad bakinta kasa rufowa yayi, tana ta murna, Ta k’ara gaskata Adnan da gaske yake.

    Yau ce ranar da wa’adin Boka zai cika, Aunty Jummai da Bilkisu na jiran suji labarin zubewar cikin Fetta, Sun san ba Makawa sai ya zube, Dan aikin shi tamkar yankan wuk’a.Fetta bayan ta kammala ayyukan gida da taimakon Shafah, Tayi wanka ta shirya tsaf, Early morning Suraj ya fita ana neman sa gidan marayun sa, Zazzab’in da taji na son rufe ta, Ta d’auki zamzam da Mallam ya aiko mata, tasha tare da shafawa a cikin ta, Ta k’ara da addu’o’i.

      “Assalamu alaikum Ina masu gidan?”, Ta jiyo muryar Yasmeen daga falo, ” Wa’alaikumus salam”, Ta amsa tare da mik’ewa ta fito falo, “Maman Unborn”, ” Babynku na wahalar dani fah”, Ta fad’a tana zama kan kujera, “Mu dai we are eager yazo duniya”, ” Sai kuyi ta addu’a Allah ya kawo shi lafiya”, “Muna yi sai dai mu k’ara”,

   Ta bud’e baki zata yi magana, mararta ta masifar murd’awa, wani zugin azaba ya ziyarce ta, tana jin tamkar marar zata cire, K’asa ta kai tare da furta ” Innalillahi wa inna ilaihir raji’un”, A rud’e Yasmeen tayi kanta tana tambayar lafiya, Kasa bata amsa tayi sai murd’e murd’e take, Tana karanta duk addu’ar da tazo bakin ta,

    Wayar Fetta ta jawo tayi dialing number Suraj, Yayi mamakin ganin kiranta coz bata tab’a kiran shi ba, Yayi receiving yana jin gaban sa na fad’uwa, “Fetta bata da lafiya”, Ta fad’a tana kuka, Hankalin sa a matuk’ar tashe ya kashe wayar, ya d’auki mukullin motar sa ya fita har yana tuntub’e,

    Ya fisgi mota a 360, minti 3 ya kawo sa gida, Shigowar sa yayi daidai da d’aukewar numfashin ta, Yasmeen ta saki k’ara tana fad’in ” Ki tashi Dan Allah Fetta kada ki tafi ki barni”,

    Hankalin sa yayi mummunan tashi ganin ta kwance bata numfashi, Yayi kanta tare da ture Yasmeen gefe bai ma sani ba, Yayi kanta yana jijjigata, “Fatima ki tashi please”, Ko gezau batayi ba, Iskan bakin shi ya shiga hura mata still bata motsa ba, ” D’ebo ruwa”, Ya umarci Yasmeen, Jiki na rawa ta d’ibo, Ya watsa mata still bata motsa ba,

    Wani ihu Yasmeen ta saki tare da fad’in “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un Fetta ta rigamu gidan gaskiya”, ‘Bata mutu ba, wallahi bata mutu ba, zata haifa mun baby, mu rayu tare tana haifa mun wasu”, Ya fad’a hawaye na bin gefen kuncin sa, D’aukarta yayi cak, Ya nufi mota, Yasmeen tabi bayan sa,

    Driver ya kira yaja su, ba zai iya driving ba, ya zauna baya rungume da ita, Yasmeen ta zauna gaba, Suka nufi asibiti.

   Ba b’ata lokaci likitoci suka shiga bata taimakon gaggawa, Kusan awa d’aya suna kan ta but sun kasa gane meke damun ta, Suna da tabbacin bata rasu ba, amma bata numfashi,

    Suraj ya kasa zama sai faman zirga zirga yake a passage na d’akin, Bai tab’a shiga tashin hankali irin na yau ba, Yasmeen kam sai faman kuka take, Hajiya ce ta shigo hankali a tashe, Aliya da Mallam a bayanta, Aliya nata kuka, hijab ma a jirkice ta saka, ” Ya jikin nata?”, Hajiya ta tambaya, Da k’yar ya iya furta “Basu fito ba”, ” Allah ubangiji ya tashi kafad’unta”, Duka suka amsa da “Amin”

  Babban likita ne ya fito, duk ya had’a zufa, Suraj yayi kansa yana tambaya “Ta farka, taji sauk’i?”, Ya dafa kafad’ar sa yace ” Relax, kwantar da hankalin ka”, “Taya hankalina zai kwanta, My wife is unconscious”, Dr yayi shiru cike da tausayin sa, ” Likita Dan Allah ka fad’a mana wane hali take ciki?”, Cewar Mallam, “Baba muma kanmu bamu san meye matsalar ta ba, munyi iyakacin k’ok’arin mu mun kasa ganewa”, Salati da ambaton sunan Allah kowannen su ya shiga yi hankali a tashe, Suraj rik’o Dr yayi yace ” Do your possible best please ta tashi, kada ku bari ta rasa ranta”, “Dr Ameer babban likita ne zai zo yau from India, zuwa dare zai dubata, In Shaa Allah zata tashi”, ” Allah ya yarda”, Cewar Aliya tana sharar k’walla,

    Suraj d’akin ya shiga kai tsaye ba tare da jiran umarnin Dr ba, Gadon da take kwance ya nufa, Ya kamo hannun ta cike da tausayin ta, Addu’o’i ya shiga tofa mata.

   “Zamu iya ganin ta?” Yasmeen ta tambayi Dr, Ya d’aga mata kai,

   Shigowar sa bai sa ya janye hannun sa daga rik’on da ya mata ba, Kallo d’aya Aliya ta mata, ta kawar da kai tana sharar k’walla, cike da tausayin ta.

   “Kada ki b’ata mun lokaci, shiryawa kamar wacce zata gidan gwamna” Aunty Jummai ta fad’a tana gyara hijabin ta, Bilkisu ta fito tasha kwalliya, tana rambad’a k’amshi, “Wannan kwalliyar fah”, ” Umma yau ranar farin ciki ce, ina so idan Ya Suraj ya ganni ya rikice”, Aunty Jummai tayi murmushi tace “Ai auren ki da Suraj kamar an mayar an gama”, Bilkisu tayi dariyar farin ciki.

    Basu tarar da kowa gidan ba sai yan’ aiki, Su’ad da Feena sun tafi bikin k’awar su, Samee na makaranta.

   D’aya daga cikin masu aikin suke sanar dasu Fetta na asibiti bata da lafiya, Farin ciki ya ziyarci zuciyar su, Aunty Jummai ta tambayi wane asibiti, ta sanar dasu, Basu tsaya ba suka fito.

    ” Dama na gaya miki aikin sa tamkar yankan wuk’a”, “Na yarda wallahi Umma”, Ta fad’a tana washe baki,

     A harabar asibitin suka ci karo da Mallam ya siyo ruwa, Suka gaisa, Ya musu jagora zuwa d’akin, Suraj na kusa da Fetta yak’i matsawa ko’ina, Bilkisu wani kishi taji ya tokare mata wuya,

    ” Ya mai jiki?”, Aunty Jummai ta tambaya, “Sai addu’a”, Cewar Hajiya, ” Meke damun ta ne?”, “Muma bamu sani ba, duk bincike likitoci sun kasa ganewa”, “Kuma ba cikin bane”, ” An gaya miki bamu sani ba” Suraj ya fad’a a fusace sam ya manta matsayin ta a wurin shi, Dole taja bakinta tayi shiru, zuciyar ta fal farin ciki sanin aikin su ne,

   Basu jima ba suka tafi, “Umma ni wallahi raina duk ya b’aci ya wani manne mata”, ” Kwantar da hankalin ki, saura k’iris zaman su tare ya k’are”, Ta sauke ajiyar zuciya, haushin da take ji ya rage.

    Throughout Suraj na asibiti bai fita ko’ina ba, Magana ma baya yi sosai, Fatan sa Allah ya tashi kafad’un ta, He is eager dare yayi Dr yazo. 1

    Around 11:00pm Dr Ameer yazo asibitin, Fetta ce patient ta farko da zai fara dubawa, Aka umarci su Hajiya su fito d’akin,

   Har Dr Ameer ya shigo Suraj na d’akin, Ya bashi hannu suka gaisa, “Please Dr do your best ta tashi, tana d’auke da babyna, ina so yazo duniya, mu rayuwa tare”, Dr Ameer yace ” Babyn ka kake so yayi surviving ko Maman baby”, “I need them both”, ” In Shaa Allah zan yi k’ok’ari, Kuyi mana addu’ar samun nasara”, Suraj yayi nodding kai yana jin hankalin sa ya kwanta da Dr Ameer,

    Masallaci ya nufa, Ya shiga nafila da rok’on Allah, Su Aliya basu gaza ba wurin rok’on ubangiji.

    Dr Ameer duk yawon sa na asibitocin fad’in duniya, bai tab’a cin karo da aikin da ya bashi wahala ba kamar na Fetta, Duk iya bincike sa ya kasa gano matsalar ta, Gashi dai bata rasu ba, But sam bata motsi, Hankalin sa ya tashi, lamarin ya bashi tsoro, Tuni ya fad’a gumi, handkerchief dake gefe ya d’auka yana gogewa.

    Kusan awa biyu ya kasa fitowa ya sanar meke faruwa, Yana tausayin Suraj, a yadda na gansa bai san wani hali zai shiga ba,

    Ganin kusan awa biyu Suraj ya fito daga masallaci yana kyautata zaton Dr Ameer ya gama binciken sa, A passage yaci karo dasu Hajiya, “Bai fito ba?”, ” Eh”, Hajiya ta basa amsa,

   D’akin ya lek’a ya hango Dr Ameer zaune yayi tagumi, Ba tare da wani tunani ba, ya bud’e k’ofa ya shigo,

   Dr Ameer ya d’ago kai ya kalle sa, yana jin tausayin sa na shigar shi,

      “Ya jikin nata?”, Suraj ya tambaya, ” Am sorry na kasa gane meye matsalar ta, ban tab’a cin karo da aikin da ya gagare ni kamar wannan “, Suraj bai san lokacin da ya kai k’asa ba, Ya dafe kai, Bai zai iya misalta yanayin da ya tsinci kansa ba, Tunanin sa ya tsaya cak.

    Dr Ameer k’wararre kuma shaharren likita ne da aka san shi a k’asashen daban daban, Duk rashin lafiyar ka, Allah ya bashi baiwar iya treating, Da izinin Allah yayi treating d’in ka sai ka samu sauk’i.Dr Ameer ya taso yazo gaban Suraj, Ya duk’a tare da dafa kafad’ar sa yace “Musulmin k’warai yadda da k’addara aka san shi dashi, kada ka d’aga hankalin ka, ka dage da addu’a”, Kai kawai ya iya d’aga masa, ” Zanje na duba wani patient, na dawo”, Ya d’aga mishi kai, +

    Ganin fitowar shi, Su Aliya suka shiga d’aki, Har lokacin Suraj na zaune a k’asa, “Subhanallah Surajo ya haka, Dan Allah ka tashi, kada ka sawa kanka damuwa”, Mallam ya fad’a yana kama hannun shi, Suraj ya mik’e tamkar wanda aka zarewa jini, Jikin sa ya matuk’ar yi sanyi,

     Aliya da Yasmeen wani sabon babin kuka suka bud’e ganin Fetta bata farfad’o ba, Hajiya ma hankalin ta ya k’ara tashi,

   Mallam ya k’arasa bakin gadon, Ya zuba mata ido yana nazari, Ruwa dake gefen gadon ya d’auka, Ya zuba a cup, ya shiga karanta addu’o’i yana tofawa, kusan minti 20 yana yi,

    Ya zuba a hannu ya shafa mata a fuska, da tafin hannu,  Ya bud’e bakin ta ya zuba wani, Sauran yace Suraj ya shafa mata a mara, Ya karb’a ya shafa mata, Mallam ya cigaba da karanta addu’a yana tofa mata,

    K’ara tayi ta dafe kai, A razane Suraj ya kamo hannun ta, ” Kin tashi?, meke miki ciwo?”, Mallam ya masa alamar yayi shiru, Ya cigaba da mata addu’a, ta shiga fisge fisge, “Zasu kasheni, Marata, Cikina”, Suraj dasu Hajiya lamarin ya basu tsoro, Saitin kunnen ta Mallam ya shiga karanta Bak’ara, A hankali ta daina surutai da fisge fisge, Bacci ya d’auke ta, Tana sauke numfashi a hankali, ” Alhamdulillah” Malam ya furta,

    “Meya sameta, meyasa take haka?” Suraj ya tambaya, wanda kowa a gurin yake son jin amsa, Malam ya nisa yace “Ture aka mata”, Hajiya tace ” Ture, ban gane ba”, “Sihiri ne”, ” What!” Suraj ya fad’a a razane,

   Kowa dake gurin ya girgiza, “Wane azzalumin ne?”, Cewar Aliya, Yasmeen tace ” Allah ya saka mata”, Hajiya ta amsa da “Amin”

    “Da zanga wanda ya mata sihiri, da na kashe shi da hannu wallahil azeem”, Cewar Suraj cike da tsananin b’acin rai,

    ” Godiya ya kamata muyi ubangiji ta samu tashi, dan ga dukkan alamu abun yazo mata sauk’i akan yadda aka so”, Cewar Mallam, Hajiya tace “Toh Alhamdulillah, Allah ya k’ara tsarewa”, Aliya tace ” Amin, Allah ya mata tsari dasu”, “Amin”

    Yasmeen tace “Mutane basu da kyau, basu da imani”, ” Wallahi” Aliya ta fad’a, Haka suka yi ta jimamin lamarin, Suraj yayi shiru yana nazarin waye zai yi wannan aikin.

   Malam da Hajiya sun koma gida, Yasmeen da Aliya a asibitin suka kwana, Suraj ma anan ya kwana, Sam bai runtsa ba, Yana kusa da ita, Sallar asuba kad’ai ta tashe sa,

    Ya dawo masallaci yana shirin zama, Ta bud’e idonta ta zube a kansa, “Fatima”, Ya kira sunan ta, ” Na’am”, Farin ciki ya ziyarci zuciya da gangar jikinsa, “Meke miki ciwo?”, ” Ba komai”, Ta bashi amsa but tana jin marar ta na murd’awa kad’an, “Allah ya k’ara miki lafiya”, Ta amsa da ” Amin” Tana mamakin sa,

   Aliya da Yasmeen cike da farin ciki suka shiga jera mata sannu, tare da yin godiya ga Allah da ya tashi kafad’un ta,

   Ba b’ata lokaci Suraj ya buk’aci sallama tunda abun ba na asibiti bane, Aka sallame su, suka dawo gida, Hajiya tayi matuk’ar farin cikin ganin ta samu lafiya,

   Suraj ya buk’aci kowa yaje gida ya huta shi zai kula da ita, Mallam ya kawo mata zamzam mai d’auke da addu’o’i, ya rubuta mata wasu a paper yace ta rik’a yi,

STORY CONTINUES BELOW

     Fetta is feeling too weak, Bata jin jikinta daidai, da tayi motsi Suraj zai ce meke damun ta, Addu’o’in da Malam ya kawo mata sun taimaka mata ta k’ara jin k’arfin jikin ta.

    “Ina su Feena?” Hajiya ta fito tana tambayar yan’ aiki, Lami tace “Ba’a nan suka kwana ba”, Hajiya ta jinjina kai, duk a zaton ta jiya da ta dawo bata gansu ba, sunyi bacci,

Ta juyo zata koma ciki, taji shigowar su, kallo d’aya zaka musu kasan daga biki suke, Kallon da Hajiya ke jefar musu dashi yasa suka sha jinin jikin su, “A ina kuka kwana?”, Ta tambaye su cike da fad’a, Feena murya na rawa tace ” Gidansu Amarya”, “Akan wane dalili?”, ” Jiya munje Dinner dare yayi, muna tsoron bin hanya shine muka kwana”, “Da izinin wa?”, Sukayi shiru,  ” Tambayar ku nake kunyi shiru “, Ta daka musu tsawa,

    ” Kiyi hak’uri”, Suka had’a baki, “Ya zama na farko na k’arshe da zaku kwana wani wuri ba da izini ba”, Suka amsa da ” Toh”, Suka wuce ciki, jiki a sanyaye.

   Suraj ya saka Rabi’u yayi mishi order jollof rice da chicken, A plate ya zuba tare da spoon, ya nufi d’aki, Fetta dake kwance ya umarta ta tashi, Ta mik’e zaune,

    Abinci ya d’ibo ya tunkari bakin ta dashi, Ta kawar da kai gefe tace “Na k’oshi”, ” Nasan kina jin yunwa ki karb’a kici”, “Bana ji”, ” Baki isa ki bar mun baby da yunwa, Am doing all this for my baby, idan kin haihu kada ki k’ara cin abinci who cares”, Bata ji haushi ba, tasan dama kulawar nan da yadda ya damu da lafiyar ta yana yi ne dan babyn sa,

    “Zaki ci ko sai ranki ya b’aci”, Bata shirya b’acin rai ba, dole ta bud’e baki ya shiga feeding d’in ta, sai da abincin ya k’are, Ya d’auko ruwa a fridge ya bata tasha,

    ” Baki da nasara, tana da k’arfin addu’a da ibada, aiki akan irin su na bani wahala” Cewar Boka cikin karaji, Aunty Jummai cike da tashin hankali tace “Yanzu babu wani abun yi?”, ” Zamu cigaba da aikin muga ko za’a dace”, “Nago…”, ” Ba’a godiya a nan”, Yayi saurin katse ta, “Ki kawo harshen damisa”, Ta zaro ido tace ” Harshen damisa, a ina zan samu?”, “Matsalar ki ce kisan ina zaki samu, tashi ki tafi”, Jiki na rawa ta mik’e, ta fita.

    Rai a jagule ta dawo gida, Daga yanayin ta Bilkisu tasan akwai matsala, ” Umma”, Ta kirata, “Akwai matsala Bilkisu, tana da k’arfin addu’a cikin bai zube ba, aikin akan irin su na bashi wahala”, Take tashin hankali ya bayyana kan fuskar ta, Tace ” Shikenan yanzu bazan koma gidan Suraj ba?”, “Zai cigaba da aiki ko za’a dace, ya buk’aci na kawo harshen damisa”,

    Ta dafe k’irji tace ” Harshen damisa, a ina zamu samo?”, “Shine damuwata”, Bilkisu tayi shiru tana nazari, ta nisa tace ” Mu nemi Sarkin Dawa”, “Kin kawo shawara”,

   Sallamar Zulaihat ya katse su, ” Umma ina wuni?”, Ta duk’a tana gaisheta kamar mutuniyar kirki, Bilkisu ta mik’e suka shiga d’aki,

     “Hajiya Rabi ta dawo fah, tun jiya ta kira ni wai ta kira wayar ki a kashe”, “Haba, jiya bamu kwana da wuta ba”, ” Ayyah ki shirya mu tafi, tana buk’atar ganin ki”, “Wallahi nima ina buk’atar ganin ta, nayi kewar ta sosai”, Ta fad’a tana mik’ewa ta nufi band’aki,

   Anty Yelwa na zaune ta rafsa tagumi, Rashin sanin halin da Karima ke ciki na matuk’ar damun ta, Wayar ta kuma bata shiga,

    ” Har yanzu baki ji labarin Karima ba ko wurin k’awayen ta?”, Binta tace “Wallahi Mama ban ji ba, kullum cikin cigiya nake”, ” Allah ya tsare ta a duk inda take”, “Amin”, ” Mahaifin ku sam bai kyauta ba”,

    “Eh ban kyauta ba d’in ba”, Suka ji muryar Kawo Sule kamar daga sama, Yelwa ta had’e rai, ” Ki fi saniya d’aure fuska, na kore ta d’in, karuwa zan zauna da ita a gidana, kuma wallahi na sake jin kina zancen ta zaki bi bayan ta”, Ya juyo kan Binta “Ke kuma munafuka, ki cigaba da biye mata”, Ya shiga ciki yana zuba ruwan masifa.

    Feena ta nuna bata ra’ayin Bello, wanda hakan ba k’aramin dad’i ya masa ba, Kawo Lamid’o da Gwaggo sun ji haushi sosai, Hajiya ma sun ji haushinta a cewar su ita ya kamata ta tilasta Feena.

   Fetta ta idar da sallar asuba, tana karanta addu’o’in da Malam ya rubuta mata, Suraj ya shigo ya dawo masallaci,

” Ina kwana?”, Ta gaishe shi, “Lafiya lau, ya jikin ki?, hope ba wani pain?”, Tayi nodding kai, ” Mashaa Allah”, Ya furta,

    Toilet ya nufa ya had’a ruwan wanka, Ya tub’e kaya ya shiga cikin bath, “Fatima”, Ya kirata, Ta amsa, ” Zo”, Ta mik’e tayi folding sallayar,

   Ta tsaya bakin k’ofa, tayi knocking, “Come in”, Ba tare da tunanin komai ba ta shiga, ” Zo ki cud’a mun baya”, “Cikina na ciwo, bana iya duk’awa”, Wani kallo ya jefata da shi tare da cewa ” Yaushe ya fara ciwon, I guess yanzu kika cemun lafiya kike?”, “Yanzu ya fara”, Ta fad’a cike da shagwab’a tana turo baki, Shagwab’ar ba k’aramin burge sa tayi ba, Da hannu ya mata alama ta matso,

    Ta matsa kusa dashi, Ya jawota ta fad’o cikin bath d’in, Ta bud’e baki zata yi magana, Ya had’e bakin su wuri d’aya, Tuni ya cire mata kaya, ya wurgar gefe, Ya shiga sarrafa ta yadda yake so, Ta kasa hana shi komai, sai ma martani da ta shiga mayar masa,

    Kusan minti 30 suka d’auka a toilet kafin suka fito, Suka fad’a kan gado tare da lulawa wata duniya,

     Bai barta ba sai da ya samu natsuwa, Idonta ta bud’e cikin nashi, Tayi saurin b’oye kanta cikin k’irjin shi cike da kunya, ” Bana son kilibibi, kunya kika sani”, Wata kunya ta sake lullub’e ta, tamkar ta shige cikin katifar, Ji tayi ya d’auke ta cak ya nufi toilet da ita, A tare suka yi wankan tsarki da wani wanka,

    Suna fitowa, ta koma kan gado tayi kwanciyar ta tare da jan bargo ta rufa,

    Yayi shirin sa cikin shadda getzner coffee color, Ya d’aura wristwatch na kamfanin rador, Ya matuk’ar yi kyau, Ta cikin bargo take kallon sa, a ranta ta yaba kyan da yayi,

    “Zan fita, ki kular mun da babyna”, Ya fad’a yana ficewa.

   Yana fita ta mik’e ta shirya cikin riga da skirt na atamfa sun mata kyau sosai, marar ta ke murd’awa kad’an kad’an tasha zamzam da Malam ya aiko mata, ta shafa.

    Gidan marayun sa yake zagayawa yana ganin yadda abubuwa ke tafiya, Mota k’irar Prado ta shigo, Da sauri driver ya fito ya bud’e k’ofa, Tasleem ta fito cikin shiga ta alfarma, Kallo d’aya Suraj ya mata ya kawar da kai gefe, Yana mamakin wacce? Me tazo yi?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *