FETTA
CHAPTER 16
Ta jingina da motar, tana kallon harabar wurin, Suraj ya juya mata baya, ta zuba masa ido tana jin son shi na ratsa jinin jikin ta, Driver ta ya bud’e booth yana fitar da kaya, kayan abinci da ghana must go cike da kayan sawa,
Mai kula da gidan marayun ta buk’aci gani, aka mata iso zuwa office d’insa, “Madam duk abunda ya shigo gidan marayun nan, sai Sir Suraj ya duba ya tantance”, ” OK”, Ta fad’a hakan ya mata dad’i, Tayi dama dan ya yaba,
Office na Suraj dake orphanage d’in suka nufa da kayan, Sule(Mai kula da wurin) ya nuna mata kujera ta zauna, Shima ya zauna suna jiran Suraj.
K’amshin turaren sa da ya daki k’ofofin hancin ta yasa ta lumshe ido, Ya shigo cikin takun sa na k’asaita, Taji tamkar ta rungume shi,
Ya zauna fuskar sa ba walwala, Hankalin sa yaji ya kasa kwanciya da ita, “Sir ta kawo ma marayu kaya ne”, Yayi nodding kai tare da cewa ” Bud’e mu gani”, Sule ya shiga bud’e kayan yana gani, “It’s ok, a d’auka a kai musu”, Ya jawo wani file yana dubawa, ba tare da ya sake bi ta kanta ba,
Tasleem ranta taji ya b’aci, ganin bai nuna appreciation ko jin dad’i ba, ya nuna tamkar bai san da zaman ta ba, Ta had’e b’acin ranta tace ” Sir Suraj ni zan koma”, Ya d’aga mata kai ba tare da ya d’ago kai ya kalleta ba,
Rai a jagule ta bar orphanage d’in, “Akwai aiki a gabana”, Ta fad’awa kanta.
“Maigida haka zamu zuba ido, muna ji muna gani Bello ya rasa Feena”, Cewar Gwaggo, “Toh ya zamuyi tunda tak’i sa”, ” Ni Hajiya Tumba tafi bani haushi yadda ta kasa tsawa ta mata”, “Ai munafuka ce, ba son auren take ba, ita ke zuga su”, Gwaggo cike da takaici tace ” Hmm”
Hayaniya ke tashi gidan karuwai na sabon gari, kowa da abunda yake, Masu shan sigari nayi, masu lido nayi, masu shan wiwi nayi, Karima ta fito d’akin ta d’auke da Abdul, zazzab’i yake zata kai shi asibiti,
“Ban tab’a ganin inda zuwa bariki da yaro ba”, cewar wata karuwa, D’ayar tace ” Wallahi ai ko a bariki na same sa na yarda shege a bola”, “Ni bazan bar sa ma yazo duniya ba”
Karima bata tanka su ba ta wuce abun ta, Ta tari mai napep ya kai ta asibiti, Likita ya duba sa, ya mishi allura tare da bashi drugs, Ta fito bakin asibitin tana tare napep, Bello dake cikin mota ya hangota, Ajiyar zuciya ya sauke tare da hamdala, Ya nufa su, Bata lura dashi ba sai ganin sa tayi a gabanta, Zuciyarta ce ta buga,
“Karima ina kika shiga, kin barni cikin tashin hankali, zuciyata ta kasa natsuwa”, ” Baka san Baba ya kore ni ba”, “Na sani meyasa baki neme ni ba?”, ” Banyi tunanin haka ba”, “Ok kina ina ne yanzu?”, Ba tare da shakku ba tace ” Gidan Karuwai dake sabon gari”
Ya zaro ido yace “Gidan karuwai”, ” Eh”, “Meyasa kika zab’i zama can?”, ” Ana so naje can shiyasa aka kore ni, bani da wurin zama da ya wuce can”, Ta fad’a zuciya a raunane, Tausayin ta ya kama shi, Yace “Dan girman Allah ki bar gidan marayu muje na baki masauki”, Ta girgiza kai tace ” A’ah Ya Bello, kada ka jefa kanka cikin gurb’atacciyar rayuwata”, “Kada ki k’ara danganta rayuwar ki da gurb’atacciya, muje”, Ya karb’i Abdul hannun ta, Ya nufi mota, ba musu tabi bayan sa,
Gidan karuwai ya kai ta, ta d’auko kayan ta tare da musu sallama, Gidan sa dake unguwar hausawa zoo road, Ya kai ta, ya siyan musu kayan abinci da komai na buk’ata, Zata mishi godiya ya hanata, Bello Allah ya d’aura mishi k’aunar Karima, yana son gyara mata rayuwar ta.
STORY CONTINUES BELOW
Wunin yau Fetta ta kasa cin komai, Fara take sha’awar ci, Ganin Suraj baya nan, Ta kira Yasmeen tace ” Dan Allah ta kawo mata fara”, Sai da ta gama tsokanar ta tace zata kawo mata idan ta fito school,
“Aunty na iya soya fara”, Cewar Shafah, ” Haba?”, “Allah, ki bayar da kud’i na siyo, na soya miki ki ajiye ba sai kin sha wahalar nema ba”, Fetta tace ” Toh”, Ta mik’e ta shiga d’aki ta d’auko kud’i ta bata, Tace tayi sauri ta dawo.
Farar da Yasmeen ta kawo mata, take ci hankali kwance, tana kallo,
Kamar daga sama taji an fisge bowl na farar, D’agowar da zata yi taga Suraj tsaye, gabanta ya fad’i, bata tsammaci dawowar sa yanzu ba,
Ransa a matuk’ar b’ace cikin d’aga murya yace “Bakya jin magana ko?”, Idonta yayi narai narai, Kunnen ta ya kama ya murd’e, Cike da azaba ta shiga k’ok’arin janye hannun sa, ” Kinci daraja d’aya da wallahi yau kin yabawa aya zak’in ta”, har lokacin bai saki kunnen ba, sai ma k’ara murd’ewa da yake,
“Kiyi hak’uri ba zan k’ara ci ba”, Ta fad’a tana matsar k’walla, Ya saketa ya nufi hanyar d’aki, Shafah tayi sallama ta shigo, Ya juyo idonsa ya kai kan ledar dake hannun ta, ” Ina wuni?”, “Meye a hannun ki?”, ” Aunty ce ta aike ni”, “Kawo”, Ya fad’a yana mik’a hannu, Ta bashi,
Cikin Fetta ya d’uri ruwa, Ya jefa mata wani mugun kallo wanda bata tab’a ganin ya mata irin shi ba, kusan sakin fitsari tayi saboda tsoro,
” Ke dan uwarki kece mai kawo mata”, Shafah a tsorace tace “Kayi hak’uri ranka ya dad’e”, ” Wallahi wani abu ya samu babyna ke zan kama responsible, idan na sake ganin kin kawo mata abu makamacin wannan sai na lahira yafi ki jin dad’i “, Ya jefa mata farar, ta zube a jikinta,
Fetta alama ya mata ta same shi d’aki, Jiki a sanyaye ta mik’e tabi bayan shi,
” Ina son babyna yazo duniya idan ke bakya so, Wallahi ba zan d’auki ganganci da rayuwar sa ba, da ana mayarwa jikin namiji, da na mayar jikina gudun ki salwanta rayuwar shi”, Mamaki ya hana ta magana, Cin fara shine salwanta rayuwar shi, Sam bata ji haushin kalaman sa ba, sai mamakin son da yake ma babyn tun kafin yazo duniya.
Ya tub’e kayansa ya shiga toilet, Ta fita d’akin ta koma falo tana kallo.
Adnan da Su’ad ne cikin mota suna, Yana kissing da romancing d’inta tana mayar masa martani, A kasalance ya d’ago yace “Baby muje hotel”, Ta mak’e kafad’a tace ” A’ah gaskiya”, “Ina buk’atar ki sosai baby”, ” Ni dai a’ah, ka turo asa rana idan ka k’osa”, “Na gaya miki gidana ne ban k’arasa ba”, ” Toh kayi hak’uri ka k’arasa, ina tsoron having sex”, “Nine fah wanda zaki aura, kina so naje na nemi wasu matan ne?”, Ta girgiza kai, ” So please zo muje”, “A’ah”, Ya janye jikinsa daga nata, ya had’e rai,
Ta shiga lallashin sa, Yak’i sauraren ta, Kisses ta shiga yi masa, tuni ya juyo ya shiga romancing d’inta, Hasken mota data dallo su yasa yayi saurin sakinta, ” Ya Suraj ne, bari na shiga gida”, Ta fice da sauri.
“Sir mun yi bincike”, Cewar Sabeer, ” Me kuka gano?”, “Alhaji Hamisu Tandama yayan Alhaji Zakari ne uban su d’aya”, Suraj yace ” Gud, ina so ku samo mun information akan komai nasu”, “OK Ranka ya dad’e”, Yayi hanging up, Tare da jingina jikin kujerar office d’in sa, Ya lumshe ido yana nazari, kusan minti goma, Ya mik’e ya d’auki mukullin mota, ya nufi gida, bayan ya biya ya siyan ma Fetta kayan k’walama.
Aliya tazo duba lafiyar ta tare da kawo mata wasu magunguna na gargajiya suna hira, Tace ” Wai nikam ina Ya Mu’azzam?” Charaf a kunnen Suraj dake shigowa, zuciyar sa ta harba da k’arfi,
Shigowar sa ya hana Aliya bata amsa, Ba tare da yabi ta kansu ba ya wuce d’aki, Aliya tace “Bari na tashi na tafi, naga mijin naki kamar ransa a b’ace”, Fetta murmushi tayi, itama ta lura da yanayin sa ko waya b’ata masa rai oho,
Ta dawo rakiyar Aliya, Ta tarar dashi falo, Fisgota taji yayi ta fad’o kansa, Idonsa da suka komai jajir cikin nata, ” Kina son tsohon saurayin ki?”, Tambayar tazo mata a bazata, Idonta ta janye daga nasa, Tace “Wacce irin tambaya ce wannan?”, ” Kin kasa cire shi a ranki?, you still love him”, Shiru ta masa ta rasa me zata ce mishi, har ga Allah a yanzu bata jin soyayyar Mu’azzam,
“Da aurena a kanki bazan lamunci kina tambayar wani ba”, Ya fad’a zuciyar sa na tafarfasa, Jin furucin sa ta fahimci inda zantukan sa suka nufa, ” Meye laifi a ciki dan na tambay….”, Bata k’arasa ba sakamakon dukan da ya kaiwa bakin ta, “Wallahi kika sake kiran sunan shi sai na zubar miki da hak’ora”
Bakin ta kama cike da azaba had’e da mamakin sa, Ya ture ta gefe sam ya manta da babyn sa, Ya fice zuciyar sa na zugi, Mota ya shiga ya zauna, ya kwantar da seat, ya kwanta tare da lumshe ido,
“Are u ok?, meyasa zaka ji zafi dan ta tambayi tsohon saurayin ta?”, Ya tambayi kansa, ” Saboda tana amsa sunan matar ka”, Zuciyar sa tayi assuring nasa.Ya dad’e a cikin mota kafin ya fito ya nufi sashen Hajiya, Ya tarar da ita tana ma Feena fad’a ta fitar da miji, kasancewar ransa ya b’aci, shi ya hana ya saka baki, har Hajiya ta gama tace “Ta tafi”, Ta fice tana tunzura baki, sam ba aure a tsarin ta yanzu, chilling kawai, +
Ta kai duban ta ga Suraj, ” Meke damun ka, na hango b’acin rai a tare da kai?”, Yayi faking smile yace “Gajiya ce sai ma’aikatan gidan gona da suka b’ata mun rai”, ” Kayi ta hak’uri, Allah ya shige maka gaba, ya maka jagora”, Ya amsa da “Amin”
Fetta mamakin sa take, Meye laifi a ciki dan ta tambayi Mu’azzam, wani lokaci idan yayi abu tamkar mai aljanu, Ta kawar da tunanin ta hanyar d’auko paper addu’o’in da Mallam ya rubuta mata, ta karanta.
Aunty Jummai ta samo harshen damisa ta hanyar Sarkin Dawa, sai da ta bashi kud’i masu yawa, wanda tayi k’arya bata da lafiya zata asibiti, Hajiya ta bata not knowing asiri zata ma dan’ ta da Fetta da take ji tamkar yar’ ta.
Kamar ko da yaushe ita kad’ai ta yanki daji zuwa wurin boka, Ta kai masa, Yayi dariya wacce duka wurin sai da ya d’auka, “Zata rasa natsuwarta, zamu saka mata tsoro da firgici ta yadda cikin zai zube, Suraj zai k’aunaci Bilkisu so mai tsanani zata koma gidan sa”, Aunty Jummai ta washe hak’ori cike da farin ciki, ” Zaki iya tafiya”, Ta mik’e jiki na b’ari, ta tafi.
“Na rasa wacce hanya zan bi mafi sauk’i na shawo kan Suraj”, Cewar Tasleem, ” Samun irin Suraj nada matuk’ar wahala da zaki ji shawarata da kin hak’ura dashi”, Sophy(Cousin d’inta) Ta fad’a, “What na hak’ura fah kika ce, kinfi kowa sanin type d’in mijin da nake so ne, beside ina matuk’ar son sa bazan iya hak’ura ba”, Sophy ta d’age kafad’a tace ” Ok then “, Tasleem wayarta ta jawo ta shiga kallon pics d’in shi, K’aunar sa na ratsa shi.
*2:10 am*
Fetta ta farka a matuk’ar firgice sakamakon mummunan mafarkin da tayi, Wani na bin ta da wuk’a zai farka cikin ta, Jikin Suraj ta fad’a, tana karanta addu’o’i,
Idonsa ya bud’e ya sauke kanta, “What?, me ya faru?”, Bakinta ya shiga rawa ta kasa fad’a mishi, Bedside lamp ya kunna, Ta had’a zufa duk da sanyin AC dake d’akin, Ya fuskanci matsalar, Jikin sa ya sake jawota cike da tausayin ta, Yasa tafin hannun sa ya goge mata zufar, Ya tofa mata addu’o’i, A hankali yaji tana sauke numfashi alamun bacci ya d’auke ta,
” Wallahi na gano wanda ke da sa hannu, na lahira sai yafi sa jin dad’i sai ya gwammace bai zo duniyar ba, ko ciki d’aya muka fito ba zan tausaya masa ba”, Ya fad’awa kansa cikin tsananin b’acin rai da tausayin ta, Dan zalunci a ma mutum sihiri dan a hana shi zaman lafiya.
Kiran sallar asuba ya tashe su, Suraj ya fara farkawa, Ya shiga toilet, Yayi alwala, Fetta ta farka da addu’a a bakin ta, Mafarkin da tayi na dawo mata, ta karanta addu’ar neman tsari, Ya fito yana sharce ruwan alwala, Gadon ya nufa da niyyar ya tashe ta, yaga ta tashi, Ya juya kan Dressing mirror ya fesa turare ya fice masallaci.
Ta mik’e ta shiga toilet tayi brush da alwala, Raka’atanil fajr ta fara gabatarwa kafin sallar asuba, Bayan ta idar ta zauna tana addu’o’in neman tsari da kariyar ubangiji.
Suraj yau ya dad’e a masallaci yana rok’on ubangiji, Bakwai saura minti biyar ya shigo gida.
Bakin k’ofa suka yi karo, Ta fito zata je kitchen had’a mishi breakfast, Ta gaishe sa, bai amsa, ya mata alama da ido ta koma, Ta juya ta zauna kan kujera,
STORY CONTINUES BELOW
Gefen gado ya zauna, tare da kafeta da ido, “Meya firgita ki jiya?”, Ba tare da tunanin komai ba, Ta fad’a masa mafarkin da tayi, ” Ki k’ara dagewa da addu’a” Ta amsa da “Toh”, tana hango tsantsar damuwa a tare dashi, wanda tasan akan babyn sa ne.
Kwanciya yayi da niyyar komawa bacci, but ya kasa, tunani, fargaba da zullumi sun dabaibaye sa, Tunani yake waye yayi wannan aiki, wanda yake da tabbaci saboda shi ne, Allah ya tona asirin ko waye, a ranar sai yaji dama bai zo duniya ba.
Mik’ewa tayi ta nufi kitchen, in less than one hour ta had’a mishi breakfast, Soyayyen dankali da miyar k’oda, sai ruwan shayi mai had’e da kayan had’i, As usual ta jera masa a dining table, Bacci ne sosai a idon ta,
Ta nufi d’aki ta kwanta gefe gado, Cikin sa ke kuka alamun yunwa, Ya mik’e ya fita nema mishi hakk’in sa, Yayi mamakin ganin abinci a jera, dan bai ji fitar ta ba, yayi nisa a tunani, Ya zauna yayi serving kansa, yaci ya k’oshi,
Yana shiga d’aki, wayarsa ta fara ringing, Ya jawota kan bedside drawer yayi receiving, ” Ranka ya dad’e mun had’a dukkan bayanai, amma shigowar ka Lagos nada matuk’ar muhimmanci”, “I can’t make it Sabeer, kuyi dukkan abunda ya dace”, ” Amma Sir….”, Ya katse shi “Bana son jayayya” Ya katse wayar, Ya fusgar da iska, gara ya rasa komai akan ya tafi wani abu ya samu babyn sa.
Kallon ta yayi, tana bacci hankali kwance, Ya d’aga rigarta ya shafa cikin da ya fara tasowa, “Allah ya kare mun kai babyna, ya kawo ka duniya lafiya”, Ya kwanta tare da jawota jikin shi ya rungume, Cikin minti biyar bacci ya d’auke sa.
” Iyayenki zasu yarda muje dake Dubai”, Cewar Hajiya Rabi, tana shafa jikin Bilkisu, dukkansu babu mai kaya, ba kunya ba tsoron Allah, Hajiya Rabi ko kunya bata ji, yar’ cikinta, Ta zaro ido tace “Dubai my love”, ” Yes muje can mu huta abun mu”, “Za’a barni, sai nace musu wurin aiki aka tura mu”, Hajiya Rabi tace ” Gud”, Tare da sumbatar ta, Nan suka shiga bad’alar su(Allah ya shirya).
“Me zai hana kiyi istibra’i a d’aura mana aure”, Bello ya fad’a yana kafe ta da ido, “Kasan Iyayen ka bara su amince ba”, Cewar Karima, ” Limamin unguwar nan zamu samu ya d’aura mana ba tare da sanin su ba”, Ta zaro ido tace “Baka gudun matsala”, ” Ki bar komai hannu na”, Tayi nodding kai, but zuciyar ta bata natsu ba, halaccin sa gare ta yasa ba zata k’i amincewa ba, Yaji dad’in amincewar ta.
Fetta na d’aki tana gyara wardrobe d’in Suraj, ta jiyo sallamar Yasmeen, Ta amsa tare da mik’ewa ta fita, Kallo d’aya ta mata tasan ba lafiya ba, Idonta sunyi luhu luhu alamun tasha kuka, “Subhanallah Yasmeen meya same ki?”, Ta tambaya cike da damuwa,
” Rashin uba masifa ne Fetta, maraici bai yi ba”, Ta kamo hannun ta tace “Sanar dani meya faru?”, “Naje wa Uncle akan ina so a canza mun mota wannan tana bani matsala, wai ba zai iya ba, banda na raina mutane me tayi, ina bak’in ciki ne dan ya canzawa Fadila mota, ita yar’ sa ce ta zaman mishi dole, nace Uncle cikin kud’in gadona, shikenan ya hau zagina”, Ta k’arasa da fashewa da matsanancin kuka,
Tausayin ta ya kama Fetta sosai, itama ta fara hawayen, ” Kiyi hak’uri Yasmeen, duniyar ce haka, kowa nasa ya sani”, “Allah ya isa wanda suka kashe su Daddy, Allah ya wulak’anta su”, Fetta ta amsa da ” Amin”, Tana k’ara jin tsanar su, tare da jin sabon kewar Mahaifin ta, Ta danne nata ta shiga lallashin Yasmeen, da fad’a mata kalamai masu kwantar da hankali.
Fetta ta k’ara tsorata da lamarin duniya, K’anin mahaifin ka uwa d’aya uba d’aya, lallai komai duniyar nan ana yi dan ganin ido ne, Tana tuna lokacin suna yara, da yake zuwa gidan ya kawowa Yasmeen kaya masu yawa, hadda keke ya tab’a siyan mata, Ba abunda zata cewa su Aliya sai Allah ya saka da alkhairi, sun rik’e ta tamkar jinin su, wani dan’ uwanka ba zai mata yadda suka mata ba.
Shafah ta fito shago Fetta ta aike ta ta siyo mata yoghurt, wanda ke fridge bata son irin su, Mota ta tsaya saitin ta, tare da mata horn, tana da tent shi ya hana ta ganin wanda ke ciki, Ta tsaya tare da wani kwarkwasa,
Zuge glass aka yi, Ganin mace ce ta had’e rai, a tunani ta wani guy ne, “Shafah ko?” Tace “Eh”, ” Idan ba damuwa ki shigo”, Ta fad’a tare da bud’e k’ofar gaba, Ba tare da wani tunani ba ta shiga, “Rufe k’ofar”, Ta rufe,
Tasleem ta nisa tace ” Kece mai aikin Fetta matar Suraj right?”, Ta d’aga kai, “Wani aiki nake so ki mun?”, Ta fad’a tare da bud’e bonnet na mota, ta fiddo bandir na 500, Ta ajiye akan cinyar Shafah, ” Idan kin amince, zan baki ninkin wannan”, Shafah ta zaro ido ganin kud’i masu yawa, Tace “Wane aiki?”, “Ki rik’a sanar dani duk abunda ke faruwa gidan Suraj”, ” Mai sauk’i ne wannan”, “Aiki na gaba zan sanar dake”, Ta d’aga kai, ” Kina da waya?”, “A’ah”, K’aramar waya ta ba ta, Tace ” Akwai number ta a ciki nayi saving da My love, kinsan meye hikimar haka?”, Ta girgiza kai, Ta yadda ko na kira ki ko aga mun cika waya, ba wanda zai zargi wani abu”, Shafah ta d’aga kai cike da mamakin hikima irin nata, Sukayi sallama ta fita cike da murnar tayi kud’i, Tana gama aikin zata gudu k’auyen su, kud’i tazo nema kuma ta samu.
“Ina kika tsaya daga siyo yoghurt?”, Fetta ta tambaya, ” Aunty chanji ne babu aka tsaya nema”, Ta karb’a tace “Kije ki share kitchen”, Ta amsa da ” Toh”, A ranta tace “Na kusa daina miki aiki, nima na faso gari”
“Sarkin kwad’ayi”, Suraj ya fad’a wanda shigowar sa kenan, Ta b’ata rai tace ” Waya sani kwad’ayin?”, “Ana kwad’ayi ana mak’alawa babyna”, Ya fad’a yana zama kusa da ita, ” Ai da ba haka nake ba”, “Kinyi kwanto dai, yanzu kika samu abun fakewa dashi”,
Ya tura hannun sa cikin rigarta, yana shafa cikinta zuwa k’asan marar ta, Ta shiga K’ok’arin janye hannun sa, ” Da babyna nake gaisawa”, Ya fad’a tare da d’age mata gira,
Tuni labari ya canza, wani salo yake mata da ya kashe mata dukkan gabb’an jiki, Lamo tayi jikinsa, A kunne ya mata whispering “You are enjoying it right?”, Kunya ta kamata, ta sunne kanta jikin k’irjin shi, Ya d’ago ta tayi saurin rufe ido, bakinsa taji cikin nata, Ya shiga aika mata sak’onni da suka k’ara kashe mata jiki.K’arar da wayar sa tayi yasa ya raba jikin sa da nata, A kasalance yayi receiving, “Hello Sahibina”, Jin muryar mace ya kashe tare da jan tsaki, Fetta jin muryar mace da abunda tace taji ranta ya b’aci, Mik’ewa tayi jiki a sanyaye ta bar falon, Yabi bayanta da kallo tare da sauke ajiyar zuciya.
” Soon zaka shigo hannu na, yadda zuciyata ta kamu da son ka, sai ka zama mallakina ni kad’ai”, Tasleem ta fad’a tana jujjuya wayarta. +
“Bello”, Kawo lamid’o ya kira sunan sa, ” Na’am” Ya amsa cike da ladabi, ” Na kira ka akan aure, dan Feena da Su’ad sun k’i ka bashi zai sa ka zauna haka ba, sa’anin ka daga masu yara uku sai biyu, na baka sati biyu ka samo mata yar’ asali yar’ manyan mutane bana son harkar tsiya”, Gabansa ya fad’i yace “Abba bana k’i ba, amma ina neman aiki Abuja, idan na samu kud’i suka k’ara shigowa sai na nemi mata yar’ manya, yanzu da ba wani arzik’i ne dani ba, ba zasu amince dani ba”
Kawo lamid’o cike da gamsuwa yace “Kayi tunani mai kyau, Allah yasa ka samu”, Ya amsa da ” Amin”, “Tashi ka tafi”, Ya mik’e cike da farin ciki, Dabara yayi, idan sunyi aure da Karima, su bar garin, da sunan ya samo aiki Abuja.
Fetta suna zaune da Shafah suna hira, Shafah tace ” Aunty nikam cikin ki wata nawa ne?”, Tayi murmushi tace “Meyasa kike tambaya?”, ” Ina so nasan yaushe zaki haihu?”, “Wata uku”, Tace ” Ashe har yanzu akwai sauran lokaci”, “Eh ki tamun addu’a na sauka lafiya”, Ta amsa da ” Toh, Allah ya sauke ki lafiya”, “Amin” Laah na manta ban zubar da shara ba”, Ta fad’a tana mik’ewa ta nufi kitchen,
Dustbin ta d’auka tayi waje, Wayar ta data soka gefen skirt ta fiddo, tayi dialing number Tasleem, bugu d’aya ta d’auka, “Cikin watan sa uku”, Tasleem tace ” Good aikin ki na kyau”, Shafah tayi dariya, Tayi hanging up,
“Ba zai yi wahalar zubarwa ba”, Ta furta tare da yin shu’umin murmushi (Nace ohh masu son cikin ya zube nada yawa)
Malam da Aliya ne zaune tsakar gida suna cin abinci shinkafa da miya, yanzu suna cin mai kyau, Fetta na aiko musu kud’i da kayan abinci akai-akai, ” Ina son ganin Fetta, akwai addu’o’in da nake so na bata”, Cewar Malam, “Baka gajiya da bata addu’o’i, kuma ai zaka iya bani na kai mata”, Ya nisa yace ” Mak’iya sun mata yawa, wanda sai an dage da addu’a, akwai tambayoyin da nake son mata ne”, “Sai ka shirya kaje”, ” Haka za’a yi”
“Umma wurin da nake aiki, sun zab’i wasu zasu Dubai, ciki hadda ni”, Aunty Jummai ta zaro ido tace ” Dubai”, Bilkisu tace “Eh”, ” Kaii amma naji dad’i, babu yadda za’ayi a lab’ani”, “Ai Umma masu aiki a wurin ne kawai”, ” Toh idan kinje ki mun tsaraba da yawa”, Bilkisu tace “Toh Umma”, (Bata damu tabi diddik’i ba, sai fad’in a mata tsaraba Allah ya shirya, dama shi Mahaifinta ya janye hannun sa daga al’amuran ta)
Malam yazo gidan, ya tambayi Fetta yadda take ji ta sanar dashi, Ya bata addu’o’i, Ta mishi godiya sosai, Da zai wuce ta raka shi har gate, tare da sha tara ta arzik’i, Shafah na lab’e na jin komai, Ta kira ta fad’awa Tasleem.
Yasmeen jarabawa suke, sam yanzu bata da time, ta kwana biyu bata zo wurin Fetta ba, Tayi kewar ta.
Fitowar ta exam kenan, Kiran Fetta ya shigo, ” Maman unborn”, “Ya kike? Ya exam?”, ” Lafiya lau, yanzu na fito”, “Allah ya bada sa’a”, ” Amin, zan biyo kafin na wuce gida”, “Toh sai kin zo”, Ta kashe, Juyowar da zatayi suka yi ido hud’u da Shafah, ” Ya dai?”, “Uhmm dama”, Duk ta rud’e an kamata tana lab’e, ” Dama me?”, “Cup d’inki na fasa”, ” Shine duk kika tada hankali, ba komai amma ki kiyaye gaba”, Tace “Toh”, Tana shiga kitchen ta d’auka cup d’aya ta fasa, ta jefa dsutbin,
STORY CONTINUES BELOW
” Ashe nima kaina na ja”, Tacewa kanta tare da yin murmushi,
“Exam na jijjiga mana ke, kinga yadda kika yi bak’i”, Cewar Fetta, Yasmeen ta shafi fuska tace ” Komai yi zanyi, am eager mu gama na samu hutu”, “Allah ya baku nasara”, ” Amin”, Ta bud’e jakarta ta zaro wani k’ulli tace “Gashi da madara zaki rik’a sha”, ” Ni fah na gaji da wannan tarkacen naki”, “Su zasu taimaka miki, ki tsaya wasa”, Ta karb’a ta ajiye gefe, ” Zan tafi, na huta, nayi karatun paper gobe”, Ta mata rakiya wurin motar ta.
Shafah taga lokacin da Yasmeen ta bata k’ulli, amma bata ji me tace mata ba, Ta kama baki tare da cewa “Asiri take ma Suraj kenan”,
Bayan gida ta nufa, Ta kira Tasleem, bugu d’aya ta d’auka, ” Yanzu k’awar ta tazo, ta kawo mata magani, wanda daga gani Suraj ake ma asiri”, Tasleem tace “Dama nasan ba banza ta barshi ba, zanyi maganin ta, ki k’ara sa ido sosai”, Shafah ta amsa da ” Toh”, Ta kashe wayar ta soka cikin skirt,
Suraj na zagaye shagunan sa, na electronics, Wayar sa tayi k’ara alamar text message, Bai duba ba, sai da ya gama, Yayi sallama da masu kula da shagunan,
Da sauri driver ya fito, ya bud’e masa gidan baya, ya shiga, wayar ya zaro, ya bud’e message
“_Kayi hankali da matar ka, tana maka asiri_”
Kusan sau biyar yana karantawa, Zuciyar sa ta shiga harbawa da k’arfi, yana nanata asiri a ransa, number yayi dialing a kashe, Ya cije lips cike da takaici, Cikin d’ayan biyu ko da gaske ne ko makirci ake son had’awa, zai yi bincike, Yayi assuring kansa,
“Ranka ya dad’e ina zamu je?”, ” Gida”, Ya umarce sa,
Fetta dake zaune falo, k’amshin turaren sa ya sanar mata dawowar sa, “Sannu da zuwa”, ” Yawwa” Ya amsa ba yabo ba fallasa,
Yau kwata kwata bai sakewa Fetta ba, bata bi ta kansa ba, ta shiga sabgogin ta, Zuciyar sa na k’aryata masa text d’in, yayin da wani b’angare ke son gaskata mishi, duba da yadda baya iya controlling kansa a kanta.
Ya kira number yafi sau ashirin, amsa d’aya ce, a kashe, haka yayi bacci zuciyar sa cike da sak’e sak’e.
Da safe Fetta ta tashi ta had’a mishi breakfast, Tana jerawa a dining table ya fito, “Ina kwana?”, ” Lafiya” Ya amsa a dak’ile, “Ya lafiyar babyna?”, ” Alhamdulillah”
Ba tare da ya sake cewa komai ba, Yayi hanyar fita, “Your breakfast”, Ta tsinci kanta da furtawa, ” I am in hurry, ana jira na”, Ya fice, a ransa yasa ba zai k’ara cin abincin ta ba, sai ya gama bincike,
Bata kawo komai a ranta ba, ta koma d’aki, ta shiga gyarawa.
Shafah eye service, Ta kira Tasleem ta fad’a mata bai ci abinci ba, “Yes my plan is working”, Shafah da ba turanci take ji ba tayi shiru, ” Anjima kisan yadda zaki yi ki fito, akwai abunda zan baki”, “Toh Aunty”, Ta kashe wayar tana waige waige, Suka yi ido hud’u da mai gadi, ” Shafah me kike anan?”, “Waya nayi da masoyina”, Yayi dariya, Ta shige cikin gida.
Fetta a sashen Hajiya ta wuni, Su Feena ko kallo basu ishe ta ba, Sai yan habaice habaice suke, Hajiya ta dabaibayeta da kayan k’walama,
Shafah ganin Fetta bata nan ta samu damar fita, Cikin sauri Tasleem ta bata k’ullin magani, tace ta zuba a abinci zai sa cikin Fetta ya zube, ko Suraj yaci ba zai mishi komai ba, Ta had’a mata da kud’i masu yawa, Cikin da farin ciki ta dawo gida, ita kam abun ta sharr tana samun kud’i daga sama.
Suraj a office tunanin text da aka mishi ya hana shi sukuni, Baya fatan ya zama gaskiya, bai san meyasa sam baya son ya sameta da laifi, Sallamar Rabi’u ta katse mishi tunani,
” Sir kayi bak’o”, “Let him in”, ” OK”
“SS”, ” Man D yaushe ka shigo gari?”, “Jiya, ka gudu nan ka bar mu can”, Yayi dariya yace ” Uzuri ne ya rik’e ni”, “Yayi, ya maganar da muka yi kwanakin baya”, ” Tana nan fah, ban manta ba”, Ya jawo drawer, ya fiddo wani envelope ya mik’a mishi, “Na d’auka ai ka manta”, ” Bana manta abubuwa masu muhimmanci”, “I see”, Ya fad’a tare da nodding kai, ” Zan koma”, “OK”, Suka yi sallama ya wuce.
Fetta da taimakon Shafah ta kammala abincin dare, ta shiga ta watsa ruwa, tayi k’aurin girki.
Ana kiran gab da magrib, Suraj ya nufo gida, bayan ya biya company MTN ya bada number da aka mishi text, akan ayi tracing d’inta,
Shafah ta fito daga kitchen tana waige waige ta nufi dining area, Foodflask ta bud’e a hankali, Ta zuba garin magani, D’agowar da zatayi suka yi ido hud’u da Suraj, 1
Guntun fitsari ta saki tsabar tsoro, Gabanta yayi mummunan fad’uwa, K’arasuwa yayi kusa da ita, Kafin tayi wani motsi, Ya mata lafiyayyan mari wanda sai da ta kai k’asa, Kafin ta d’ago ya k’ara mata wani,
” Uban wa ya saki?”, Ya fad’a a tsawace, wanda zuciyar shi ta gama bashi Fetta ta saka ta, Kasa magana tayi sai jikin ta dake rawa, “Waya saki nace?”, Ta sake yin shiru, tana matsar k’walla, ” Kada ki bari na sake maimaita tambayata “, Murya na rawa tace ” Auntyy ce”, Kansa ne ya masifar sarawa, Yayi k’ok’arin tattaro natsuwar sa ta hanyar cewa “Maganin meye?”, ” Mallakar miji”, “A ina ta samu?”, ” K’awar ta ce ta kawo mata”, Shafah tasan ta tona asiri kashin ta ya bushe, Suraj ba zai barta ta kwana lafiya ba, a yadda yake tsananin son babyn sa, wannan ce hanyar tsirar ta, 1
Suraj jiri yaji na d’ibar sa, yana neman fad’uwa, kujera ya dafa, bai san lokacin da ya kai zaune ba, Zuciyar sa ke tafarfasa, Yana jin wani zafi tamkar ana hura masa wuta.
(Nace Allah ya fidda ki Fetta, kina ganin aya, haters everywhere)