FETTA CHAPTER 21

FETTA CHAPTER 21

Su’ad da Feena sun dawo ba tare da kowa ya gansu ba, Suka shige d’akunan su, Sunyi nasarar shawon kan samarin nasu sun hak’ura, Su’ad sai da suka darje da Adnan, Feena duk chilling d’inta ko romance bata tab’a yi ba, tana tsoron zina(Nace da tsoron Allah a ranki). + Bayan sallar isha’i, kowa ya watse, Suraj ya shigo cikin gida, A d’aki ya samu Fetta tana k’ok’arin cire kaya ta shiga wanka, “Ki shirya zamu yi pics”, Yana fad’ar haka bai jira cewar ta ba, Ya fice, Tabi bayan sa da kallo, ta sauke ajiyar zuciya, har ga Allah a gajiye take amma ya ta iya, Ta sake shiri, a babban falon gidan ta same shi, Yana d’auke da Mimi, Sukayi hotuna different styles, Ta juya zata koma ciki, Ya rik’o hannun ta, Ta juyo tana kallon sa, Ya saki hannun tare da cewa “Biyo ni”, Ba musu tabi bayan sa, A harabar gidan ya tsaya kusa da wata dalalleliyar mota, hannun ta ya jawo ya d’aura mata key, “Tukwicin haifa mun little angel” Ya fad’a yana kallon Mimi, Ta kalli motar itace wacce ya tab’a cewa ta taya shi zab’e, abokin shi zai siyan ma matar shi,

Mamaki ya cika ta, a ganin ta wannan mota tafi k’arfin ta, Murya a sanyaye tace “Nagode amma ba sai ka bani tukwicin komai ba, yayi yawwa besides ban iya tu….”, Kallon da ya jefa mata yasa ta kasa k’arasa maganar, Fuskar ya d’aure wanda ta dad’e bata ga yanayin da haka ba, Ya wuce part d’in sa, Ganin yanayin sa taji duk ba dad’i ba, tana ganin bata kyauta ba, Rai ba dad’i ta koma sashen Hajiya, Bakin gado ta zauna shiru, Ta jawo wayar ta, tayi mishi text ta tura, Suraj na rungume da Mimi, system na gefen sa yana operating, wayar sa tayi k’ara, kamar zai share, ya jawo ya duba “Kayi hak’uri ba nak’i kyautar da kamun ba ne, sai dai ina ganin kamar yayi girma, hidimar da kamun kad’ai ta wadatar, Nagode Allah ya saka da alkhairi” Yana gamawa karantawa yaji wani sanyi a ranshi da ya rasa dalili, Murmushi yayi ya ajiye wayar ya cigaba da operating system. Fetta nata jiran taga reply d’in sa shiru, ko har yanzu fushi yake, ranta taji duk ba dad’i, “Meyasa zaki damu?”, Ta tambayi kanta, Siririn taki taja, Ta gyara kwanciyar ta, a haka bacci ya d’auke ta, Feena taje sashen kai mishi abincin dare, Ya bata Mimi ta kai ma Fetta,

Cikin bacci taji k’arar k’ofa, Ta bud’e ido taga Feena ce rik’e da Mimi, “Gata inji Ya Suraj”, Ta mik’a mata, ta fice Tabbas fushi yake dani tunda har yak’i maido Mimi da kansa kamar yadda ya saba, Rai ba dad’i ta shimfid’e ta, ta koma bacci. 2:00am na dare Jirgin su Tasleem yayi landing, Tana sauke k’afarta matattakar jirgi na k’arshe, Tayi wani shu’umin murmushi, Zuciyarta ta bushe, soyayyar Suraj yasa ta makance, komai zata iya aikata, ta dawo 9ja da k’udurin kawar da Fetta da yar’ta a doron k’asa. Driver gidan su yazo d’aukar ta, Daddyn ta na falo na jiran isowar shalelen sa, Tana shiga falon ta fad’a jikin sa, “Oyoyo My daughter”, “Daddyna i miss you”, “Ya gajiyar hanya?”, “Alhamdulillah”, “Ki shiga kiyi wanka, kizo kici abinci sai ki kwanta”, “Toh Daddy”, Ta fad’a tana mik’ewa ta nufi d’aki, Wayarta ta zaro daga cikin handbag, ta bud’e wadrobe na d’akin ta, sim ne a ciki zasu kai guda biyar, ta d’auki d’aya tasa a wayar, Kan number Suraj taje, Ta tura mishi text STORY CONTINUES BELOW

“Habibina can’t wait to be with you”, Suraj yaji k’arar shigowar text, a zaton sa Fetta ce, yana dubawa yaga number ce, yaja tsaki ya cigaba da baccin sa. Tasleem abinci kad’an taci, sam bata da natsuwar ci, bacci ma ya gagare ta, fatan ta burin ta ya cika. 10:30am Suraj ya fito cikin shirin sa na shadda coffee color, ta matuk’ar yi masa kyau, hular kansa ta zauna daram, yana ta rambad’a k’amshi, Hajiya na zaune kan dining table tana breakfast tare dasu Feena, Yayi sallama ya shigo, Su Su’ad suka shiga gaishe sa, Ya amsa, Ya kai duban sa ga Hajiya, “Mama ina kwana?”, Ya fad’a tare da duk’awa, “Lafiya lau”, “Ya gajiyar hidima?”, “Alhamdulillah, zaka fita ne?”, “Eh zan je gidan marayu”, “Toh Allah ya kai ka lafiya ya bada sa’a”, Ya amsa da “Amin” “Saura sati nawa bikin naki?”, Ya tambayi Su’ad, “Sati uku”, “Mama nace maganar kayan d’akin ta, nayi order gadaje guda uku da set na kujeru biyu daga china, zuwa jibi zasu iso, sauran kaya kuma zan bada kud’i sai ku k’arasa”, “Kaii Mashaa Allah, Allah dai ya saka maka da alkhairi”, Ya kasa amsawa dan a ganin sa Shine Uban su hakk’in sa ne ya musu, Su’ad wacce bakin ta ya kasa rufewa tsabar farin ciki tace “Nagode Nagode sosai Yaya”, Kai kawai yayi nodding, “Su ko addu’a basu iya ba unlike Fetta” Ya fad’a a ran sa. Dak’in Fetta ya shiga, tana sharar baccin wahala, Mimi itama bacci take, ya sumbaceta, Ya kai duban sa ga Fetta, hannun ta ya sauka kan gadon, yana lilo, Ya d’ago hannun, lallen ta ya masifar burge shi, ya tsinci kansa da sumbatar hannun, ya d’aura kan gado, sannan ya fice. Shigowar motar sa, Yayi daidai da fitowar Tasleem daga motar ta, Driver ta ta umarta ya fito da kayan abincin da tazo dasu, Suraj ya fito motar sa, ba tare da ya kai duban sa gare ta ba ya shige office d’in sa, hakan ya k’ular da ita, duk gayun da taci saboda shi, “Soon zaka zama mallakina”, Tayi assuring kanta,

Taso ta same shi office d’in shi, Yace “Baya buk’atar ganin kowa”, Files ne jibge ya tarar dasu, wanda duk sai yayi going through yaga abubuwan da suka guduna tafiyar da yayi. Tasleem haka ta koma gida rai a b’ace, ta cillar da gyalen ta, da jaka kan gado, “Yau zan kawo k’arshen komai”, Ta fad’a tana damtse hannayen ta, idon ta sunyi jajir. “Mutanen Abuja, sai yau ake ganin ku”, Cewar Gwaggo, Bello ya shafi kan shi yace “Ayi hak’uri Gwaggo yanayin aikin namu ne”, “Uhmm Ya gajiyar hanya?”, “Alhamdulillah”, Ta ajiye tray gaban shi tace “Ga abinci, nasan ka kwaso yunwa”, Yayi dariya yace “Wallahi kuwa” Yana cin abincin, Kawu Lamid’o ya shigo, “Ah har ka iso, tafiyar safe kayi kenan”, “Eh Abba, ina wuni?”, “Lafiya lau”, “Ya gajiyar hanya?”, “Alhamdulillah” Nan ya zauna suka ci abincin tare, suna hira, Kiran sallar azahar yasa suka mik’e suka nufi masallaci, Bayan sun dawo sallah, Kawu Lamid’o yace “Ina so ka saurareni da kyau, yanzu aiki ya kankama, sai maganar aure, naga kasa shiririta, ka sani ba zaka bar garin nan ba, sai ka fitar da mata”, A razane ya d’ago ya kalli Kawu Lamid’o, “Ka kalleni da kyau, na lura kana so ka maida ni mutumin banza, dan haka dole ka fitar da mata a tsayar da magana kafin ka koma”, Gwaggo dake gefe tace “Hakan shine daidai, yaro ya kai munzilin ajiye iyali amma kamar wanda aka tsaface, idan ma Yelwa tayi wani abu dan munk’i yarda ka auri yar’ ta, wallahi sai ya warware”, Kawu lamid’o yace “Kai bama zai bar garin nan ba sai an d’aura aure”,

Gabansa yayi mummunan fad’uwa, hankalin sa ya tashi, “Kaji abunda na gaya maka”, Da k’yar ya iya furta “Toh”, Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Sha biyu saura Fetta ta farka, tayi mamakin baccin da tayi, tuni Aliya tazo ta d’auki Mimi, ta mata wanka, da tayi kuka ta bata madara, ta goya ta. Toilet ta shiga, tayi brush, tayi wanka, ta shirya cikin wani material red da akai ma ado da duwatsu, ya matuk’ar yi mata kyau, Tana fesa turare, Yasmeen tayi sallama ta shigo, “Amarya kuma uwargidan Surajo”, “Kin zo kenan ki fara damuna”, Yasmeen tayi dariya tace “Ni ya’ta nazo gani ba ke ba”, “Ai sai ki ganta ki koma”, “Shigowa ta naji su Feena na tsegumi Suraj ya siyan miki mota”, Fetta tayi murmushi tace “Eh jiya ya bani”, Wani tsalle Yasmeen tayi tace “Woo wallahi Suraj ya fola, ya fad’a tsundum, kyautar mota fah”, Fetta mamakin murnar da Yasmeen ke yi, ta tsaya tana yi, “Uhmm ni dai kin isheni da ihu”, Yasmeen tace “Wallahi Suraj ya kamo da sonki”, “Naji ni dai zo ki tayani shirya kayan nan, jiya ban samu natsuwa ba” Kayan barka suka shiga shiryawa cikin akwati, Mamaki ne ya kama Fetta ganin babu kusan kala goma da atamfa biyar, ciki hadda kayan barkan Aunty Jummai, “Yasmeen kinsan an saci kayan nan”, Ta zaro ido tace “Haba dai?”, “Allah”, “Kai mutane basa tsoron Allah, wasu dama sata ke kawo su”, Fetta tace “Ko waye yama kan shi”, Yasmeen ta cigaba da mita, Fetta bata damu ba, kaya kam har sun ma Mimi yawa.”Wai anya Fetta ta d’aura zanin da kika bata, kuma ta sawa yar’ta kayan”, Aunty Jummai fuska d’auke da damuwa tace “Ina fah ta saka, da ta saka ai da tuni ta shiga daji, yar’ ta bak’unci lahira”, Bilkisu tace “Meye abun yi?”, “Hmm ai ni wannan al’amari na d’aure mun kai, yarinya duk ta yadda aka biyo mata sai ta tsira”, “Wallahi nima Umma shine abunda ke matuk’ar bani mamaki”, “Gobe zanje gidan na tabbatar an sawa jaririyar kayan, ita kuma ta d’aura zanin”, “Kiyi k’ok’ari please Umma”, “Kada ki damu” +

Suraj bai dawo gida ba sai 11 na dare, Sashen Hajiya ya nufa dan duba lafiyar babyn sa, Fetta na kwance idon ta a rufe but ba bacci take ba, tunanin rayuwarta take, babban burinta ta sadu da dangin ta, Rayuwar da suka yi da mahaifin ta, take tunawa, Hawaye masu zafi na bin gefen kuncin ta, Suraj shigowar sa kenan idon sa ya kai kanta, “Ya ilahi kullum kuka, bata gajiya” Hannun sa ya kai kan fuskar ta, yana share mata, Jin hannun mutum a fuskarta, yasa tayi saurin bud’e ido cikin nasa, Ya kafeta da ido, tayi saurin mayar dasu ta rufe, “Ke bakya gajiya da kuka, sai kin k’arar da hawayen ki” “Kukan shi kad’ai nake na samu sauk’i a zuciyata”, “Addu’a itace makamin mumini, kuka ba zai amfane ki da komai ba”, Ya fad’a ya juya kan Mimi, ya d’auketa “My little angel kina ta bacci abin ki, kar ki biyo momman ki da kuka kinji, Allah ya dawwamar dake cikin natsuwa da kwanciyar hankali”, Fetta ta amsa da “Amin, nima Allah ya yaye mun”, Ta fad’a cike da takaicin sa, gani take kamar da gayya yayi addu’ar, Kallon ta yayi ya girgiza kai, ya fahimci taji haushi, toh meye abun jin haushi addu’a ce yayi ma yar’sa, bai sake ce mata komai ba, Ya fice daga d’akin, Fetta hakan ya k’ara k’ular da ita, “Wato yar’ sa ce damuwar sa, ita kad’ai yake wa fatan samun natsuwa da kwanciyar hankali, ni ko a jikin sa”, Wata zuciyar tace “Meyasa zaki damu da rashin damuwar sa, kin manta dama bashi da tausayi”, Taja tsaki tare da gyara kwanciya, sam bacci yak’i d’aukar ta, sai faman juyi take. Suraj wanka kad’ai yayi ko kan abincin da aka ajiye masa bai yi ba, ba wani dad’in sa yake ji ba, A hanya ya siya yoghurt da nama yaci, yabi lafiyar gado, a matuk’ar gajiye yake, Cikin minti goma, bacci ya d’auke sa. 3:00am na dare Dare ya tsala sosai, baka jin motsin komai sai haushin karnuka, garadan maza fuskar su rufe da mask, suka dirko fence na gidan Suraj, ta bayan gidan suka shigo, sanin gaban gidan akwai security sosai, Waige waige suka shiga yi, D’aya daga cikin su yace “Ina zamu ganta?”, “Ance tana main part na gidan”, Biyu suka nufi sashen Hajiya, biyu suka tsaya waje suna musu gadi, Su’ad na kwance d’akin ta tana waya da Adnan, wanda kullum suke raba dare suna yi, sai asuba suke bacci, ko suyi video call suna kallon tsaraicin juna. Bugun k’ofar da taji ana yi alamun b’allawa, Yasa ta tsorata, “Baby kamar k’ofa nake jin ana k’ok’arin b’allawa”, “Haba dai”, “Wallahi bara ka ji”, Sukayi shiru yana saurare, “Tabbas bugun k’ofa ne, toh waye”, Wayar tayi saurin kashewa jin bugun ya k’aru, A hankali ta bud’e d’akin ta, ta nufi na Hajiya, tana shiga suna b’alla k’ofar, Suka shigo falo, waige waige suke, “D’akin k’asa aka ce take” “Mama tashi! tashi!, ina tunanin yan fashi a gidan”, Hajiya ta farka firgigit “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, yan fashi”, Ta d’aga kai cike da tsoro, Hajiya wayarta ta lalubo ta danna kiran Suraj, STORY CONTINUES BELOW

Cikin bacci yaji wayar sa na k’ara, sam ya manta ya kashe ko ya saka silent, “Yan fashi a gidan nan”, Yaji muryar Hajiya cikin tashin hankali, Saurin mik’ewa yayi yace “Yan fashi”, “Eh suna sashen nan” Ya kashe wayar, gado ya hankad’a ya jawo bindiga, ya fito yana sand’a, baya son sanar da security suyi harbi, suyi saurin guduwa, Yafi so a kama su. Bugun k’ofar da ake, ya tashi Fetta wanda tasan bana lafiya bane, Mimi ta d’auka, Ta shiga dube dube ina zasu b’oye, Wadrobe ta bud’e ta shige, Suka b’alla k’ofar d’akin, “Ina take?”, D’ayan yace “Duba cikin toilet nayi searching d’akin”, Fetta dake cikin wadrobe tana jin su, k’irjinta na duka, tsananin tsoro da tashin hankali sun dabaibayeta, duk addu’ar da tazo bakin ta, tana karantawa. Suraj cikin sand’a ya shigo sashen Hajiya, ba tare da wanda suke baya sun gan shi ba, Motsin da yaji a d’akin Fetta yasa ya nufi can, Wadrobe ya jawo ya bud’e, Wata muguwar dariya ya fashe da ita yace “Nan kika b’oye, Jangwal fito gata nan”, Wanda aka kira da Jangwal ya fito daga toilet, Fetta jikinta banda kyarma ba abunda yake, tsabar tsoro tamkar zuciyarta zata fasa k’irjin ta, ta fito, “Yau k’arshen ki yazo, zaki bak’unci lahira ke da yar’ ki”, “Dan Allah ku kasheni amma kar ku tab’a ya’ta”, Ta fad’a murya na rawa, Wata dariya suka shek’e da ita, Jangwal ya saita bindiga, Fetta ta damtse ido tare da matse yar’ta k’irjin ta, K’arar harbin bindiga ya farkar da sauran jama’an gidan, Su’ad ta buga tsalle ta fad’a kan Hajiya, “Mun shiga uku wa suka harba”, Hajiya ta fad’a cike da tsananin tashin hankali, Securities suna jin harbi, kowanne ya mik’e ya d’auki bindiga, Suka zagaya gidan, Biyun dake waje sun hango su, Da sauri suka haura katanga suka arce. Jangwal ne yashe a k’asa rik’e da k’afar sa dake tsiyayar jini, Suraj ya harbe sa, D’ayan ya matse mishi wuya, yana kakarin amai, sai faman fito da harshe yake, idonsa sun firfito, Fetta in banda kuka ba abunda take, jikinta har lokacin bai bar kyarma ba. Securities cikin gida suka shiga, su tabbata akwai wasu a ciki, Shigowar su d’akin yasa Suraj ya sake shi, “Ku fitar dasu, ku wuce dasu station”, “Ok Sir” Suka ja su, tare da saka musu hand-cuff suka fice dasu, Fetta dake durk’ushe k’asa, ya d’ago ya karb’i Mimi, Ya rungumota jikin sa, Lafewa tayi jikin sa, tana mayar da numfashi da k’yar, bayanta ya shiga bugawa a hankali, Ranar da aka kashe Mahaifinta ya dawo mata, tana ganin tamkar yau ne, “Meyasa ake farautar rayuwar su?” Kuka ta shiga rairawa, Suraj har cikin ransa yake jin kukan ta, bai yi yunk’urin hana ta ba, ya barta ta fitar da abunda take ji ta hanyar kuka, Hajiya da Su’ad sun kasa fitowa daga d’aki, Feena ma ta k’udundune cikin bargo, tsoro ya dabaibayeta, “Waya turo su?, Meyasa suke son kashe Matata da ya’ta?, wani abu ta samu ko saboda nine?, i have to find out, ko waye i will make sure he or she pay for this”, Suraj ya fad’a yana cije lips na k’asa, Fetta ta tsagaita da kukan, sai ajiyar zuciya da take, Ya mik’ar da ita, Ya rik’o hannun ta, Suka fito daga d’akin, Sama suka nufa d’akin Hajiya, “My Son ina suke?, Sun tafi?, basu tab’a kowa ba?”, “Eh Mama an kama mutum biyu, an wuce dasu station”, Ajiyar zuciya ta sauke tace “Alhamdulillah, Allah ya k’ara mana tsari da mugayen mutane”, Ya amsa da “Amin”, Ganin yanayin Fetta tasan a firgice take, Tace “Fetta sannu koh”, Murya a dasashe tace “Yawwa” “Fetta suke son kashewa da Mimi, i wonder wanda ya turo su”, Hajiya a kid’ime tace “Kisa, su kashe su”, Ya d’aga kai, “Hasbunallahu wa’ ni’imal wakeel, ya zama dole a d’auki mataki, a san waya turo su”, Suraj yace “Zanyi iyakar k’ok’arin wurin gano wanda ya turo su”, “Allah ya tona asirin ko waye”, “Amin”

“Zamu je da ita part d’ina, har ta samu natsuwa”, Hajiya tace “Toh”, Cike da gamsuwa. Tasleem nata zirga zirga d’akinta tana jira taji sun kirata sunce sun aiwatar, K’arar wayar ta, tayi picking da sauri, “Hello ina fatan kun aika su lahira”, “Hajiya an samu matsala”, “What!” Ta fad’a a tsawace, “Su Jangwal suka shiga cikin gida, an kama su” Wani uban ihu tayi, ta saki wayar ta fad’i, Ta shiga bubbuga k’afarta cike da tsananin bak’in ciki, b’acin rai da takaici. Mallam ne ya farka firgigit duk ya had’a gumi, Ya tada Aliya, “Mallam lafiya?”, “Tabbas akwai abunda ya faru da Fetta, kira muji tana lafiya”, “Mallam yanzu fah hudu na dare, In Shaa Allah ba abunda ya sameta mafarki ne”, “Ni nasan akwai matsala, bana mafarki irin haka, ba tare da wani abu ba”, “Mu tashi muyi mata addu’a, gobe da safe sai muje gidan” Suka mik’e suka d’auro alwala, suka fara gabatar da nafilfili.Hannun sa rik’e da nata har zuwa part d’in shi, Bakin gado ya zaunar da ita, Ya shimfid’e Mimi wacce tuni tayi bacci a hannun sa, + K’aramin fridge dake d’akin ya bud’e ya d’auko bottle na ruwa masu sanyi, Ya bud’e ya mik’a mata, ba musu ta karb’a, Kusan rabin robar ta sha, ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya, ruwan sun saka ta jin wani sanyi a ranta, “Oya sleep bana son na k’ara ganin hawayen ki”, Ya fad’a yana nuna mata pillow, Kai ta mishi nodding ta kwanta, shima ya kwanta tare da kashe wutar d’akin. Fetta ta nemi bacci ta rasa, ta kawai rufe ido ne tamkar mai bacci dan kar Suraj ya fuskanta, tunani ne birjik a k’wak’walwar ta, Cikin mintuna kad’an bacci ya d’auke sa, saukar numfashin sa kad’ai take ji, Hakan yasa ta bud’e ido ta zuba a kansa, Ba zata iya fassara me take ji a kan sa ba, Tabbas yau taji yana da matsayi a rayuwar ta, yayi rescueing life d’in ta, “Ashe yana da tausayi?” Ta tambayi kanta, Wata zuciyar tace “Yayi ne dan yar’ sa”, Siririn tsaki taja tare da kawar da kanta daga kallon sa, “Ba zan tab’a bari asiri na ya tonu ba, sai an samu Suraj ta kowane halin, son da nake masa ba zai tafi a banza ba wallahi”, Tasleem ta fad’a, ta kasa bacci sai faman juyi take kan gado. *5:40am* Kiran sallar asuba ya tashi Suraj, ya mik’e da sunan Allah a baki, Fetta har lokacin bata yi bacci ba, ta hau mitsittsika ido alamun daga bacci ta tashi, “Zan koma sashen Hajiya”, Ran sa ne yaji ya b’aci, wato har ta gaji dashi tunda asuba tana buk’atar komawa, “K’ofa a bud’e take ai, ko na rik’e ki”, Ya fad’a yana shigewa toilet, Cike da haushin kalaman sa, ta d’auki Mimi ta fice daga sashen, “Wato shi ba zai tab’a canzawa ba”, Wani b’angare na zuciyar ta yace “Hali zanen dutse” Toilet ta shiga, tayi wanka, pad take son canzawa, shiyasa ta buk’aci dawowa, doguwar riga ta saka, ta fesa turare ba tayi kwalliya ba, Ta kwanta kan gado, cikin ikon Allah bacci ya d’auke ta, Suraj ya fito toilet bai ganta ba, ita da Mimi, Prayer mat ya shimfid’a ya kabbara sallah. Bello sun dawo sallar asuba tare da Kawu Lamid’o, Zai wuce d’akin sa, Kawu Lamid’o yace “Nayi wata yar’ shawara ka duba yarinyar mai gidana watak’ila taku tazo d’aya”, Bello yace “Toh”, Yana jin wani k’ulloton bak’in ciki ya tsaya masa mak’oshi, Ya wuce d’akin sa, yana tunanin hali irin na iyayen shi, burin su ya auri yar’ mai hannu da shuni basu damu da tarbiyar ta ba, ya tabbata saboda kud’in mai gidanshi yace ya nemi yar’ sa, sanin kowa ne bata da natsuwa, Ya kwanta kan gado yana had’iyar bak’in ciki. Masu aikin gidan da hirar abunda ya faru jiya suka tashi, kowa yana tofa albarkacin bakin sa.

Suraj ruwan tea kad’ai ya sha, Ya fito burin sa ya isa station, yaji wanda ya turo su, A lek’a sashen Hajiya tana bacci, bai bi ta kan Fetta ba ya fice. Tunda aka kai su Jangwal cell aka rufe, ba’a musu komai ba, suna jiran su ji daga Suraj, an dai cirewa Jangwal bullet aka d’aure k’afar, Yan’ sandan wurin na matuk’ar girmama shi, cikin ladabi suka gaishe shi, Ya amsa, Ya buk’aci ganin su Jangwal, aka fito dasu, ganin shi kad’ai sai da gabansu ya fad’i, suka dake, suna son su nuna su yan iska ne, STORY CONTINUES BELOW “Bana son b’ata lokaci, kuma bana son k’arya ku fad’a mun waya aiko ku”, A tare suka ce “Babu”, “Kuna nufin ko kuka saka kanku”, “Eh” Ba dan ya gamsu ba yace “Akan wane dalili?, ta muku laifi ne?”, Suka yi shiru, “Tambayar ku nake”, Ya fad’a a tsawace, Jangwal yace “Kawai kawai dai ka gane dai”, Wani wawan mari ya falla mishi, “Zaka gaya mun wanda ya aiko ku, ko sai na murd’e wuyan ka”, Ya bud’e baki zai yi magana ya tuna warning d’in Tasleem, “Idana aka kama ku ka kuskura ka kira sunana, wallahi sai na kashe mahaifiyar ka da k’annen ka”, Yayi shiru zufa na tsattsafo mishi, “Kai ma zaka yi magana ko sai na tarwatsa kan ka da bindiga”, Shima warning d’in Tasleem ya tuna, “Sai na kashe gurgun mahaifin ka, na makantar da Mahaifiyar ka, nasa k’atti biyar suma k’anwar ka fyad’e”, Duka su hud’un su sai da ta basu warning, babu wanda bata san komai akan shi ba, sai da tayi bincike a kansu kafin ta sa su aiki. Wayar Suraj ta hau ruri, Yayi picking, “Sir Alhaji Sule Kotangora ya shigo gari”, “Ok on my way”, Ya fad’a tare da hanging up, “Ku tabbatar kafin na dawo kun shirya gaya mun gaskiya ko wallahi ku bak’unci lahira”, Ya fad’a, yana fita daga station d’in, aka ja su aka mayar dasu cell. Mallam da Aliya a tare suka zo, Mallam ta tsaya daga bakin gate wurin securities, Aliya ta shiga ciki, Fetta baccin da tayi ya saka mata natsuwa, tana zaune cin abinci, Mimi na wurin Hajiya, Aliya ta shigo, “Umma ina wuni?”, “Lafiya lau Fetta, ina jikalle?”, “Tana wurin Hajiya”, “Toh madallah, tare muke da Mallam yana waje”, “Kice ya shigo Umma”, “A’ah sauri yake muje dai ku gaisa”, Hijab ta zura suka fito waje, har k’asa ta duk’a ta gaishe shi ya amsa, yana tambayar komai lafiya, tace lafiya lau, bata son sanar dasu abunda ya faru jiya hankalin su ya tashi, Wata yar’ takardar ya fiddo daga aljihu ya mik’a mata, “Addu’o’i ne kullum da safe ki rik’a karantawa”, “In Shaa Allah, Nagode”, “Zamu koma ki gaida mai gidan naki”, Aliya tace “Ki gaishe da Hajiya, kice mata ina sauri, na bar ayyuka gida”, Tace “Toh”, Suka wuce, Ta koma cikin gida. Bilkisu ta shigo rik’e da ledoji cike da kaya, Wata k’awarta da suka yi mad’igo yau, ta mata siyayya, Aunty Jummai dake tsakar gida ta washe baki tace “Yar’ albarka meye aka siyo mana”, Bilkisu ta d’an tab’e baki tace “Kayan shafa ne da k’walama”, “Ni ba ruwana da kayan shafa, banj dai na k’walamar”, Ta mik’a mata leda d’aya mai d’auke da Shawarma, yoghurt da kaza, Aunty Jummai ta washe baki ta fara fisgar kaza tana kaiwa baki, sam bata damu tasan wane aiki yar’ ta ke yi ba, ita dai a bata kud’i ta kashe, a kawo mata dad’i ta lamshe, “Yau naga Abba a shagon da naje siyayya yayi tamkar bai sanni ba, nima na d’auke kai”, Aunty Jummai ta fisgi cinyar kaza tace “Gara da kika mishi haka, ni tun korar mu da yayi ya sire mun wallahi”, “Nima wallahi Umma”, “Sai yayi nadama”, “Uhmm bari na shiga na watsa ruwa”, Kawu Lamid’o ya umarci Bello yaje yaga yarinyar mai gidan sa Alhaji Tambari, Bello rai ba dad’i yaja motar sa ya nufi gidan. Tsayawa yayi yana kallon girman gidan, Mansion house ne, banda abun Mahaifin shi ina shi ina yar’ gidan nan, Yayi horn, Security ya fito ya tambaye shi “Wurin wa za shi”, Ya rasa wa zai ce dan shi bai san sunan ta ba, Ya nisa yace “Yarinyar gida”, A zaton security saurayin ta ne, dan maza da dama na zuwa wurin ta, Ya bud’e mishi gate, Ya shiga. Bello jikin shi ya k’ara yin sanyi ganin cikin gidan, wajen gate ba komai ba ne, Kusan minti goma yana zaune cikin mota, bai san me zai fara ce mata ba, Can ya hango wata ta fito daga cikin gidan, ga dukkan alamu yar’ aiki ce. Ya fito daga motar ya tunkare ta, Ya mata sallama ta amsa, “Dan Allah yarinyar gidan nan zaki kira mun”, “Aunty Tasleem”, Yace “Eh”, Tace “Tohm”, Ya jingina da mota yana jiran fitowar ta, Tasleem wunin ranar tana d’aki tana sak’e sak’en yadda asirinta ba zai tonu ba, zuciyarta na mata wasi wasi zasu iya tona asirin ta, yayin da wani b’angare ke ce mata ba zasu yi ba, duba da warning d’in ta. Larai tayi sallama ta shigo, Tace “Ana kiran ta waje”, Cike da gadara tace “Waye?”, “Bai fad’a mun sunan shi ba”, Ko sun fad’i nice na turo su, Suraj ya biyoni, “Je ki ina zuwa”, Dan’ k’aramin mayafinta ta yafa ta fito, Ganin Bello yasa ta bishi da matsiyacin kallo, “Mallam lafiya dai?”, Ba abunda Bello ya tsana irin wulak’anci da raini, Kasa ce mata komai yayi, Ya shiga motar sa yaja, Tsaki tayi tace “Sakaran banza, baka da courage na mun magana kazo wurina”, Ta koma ciki tana mita. Bello ransa ya b’aci matuk’a, ya k’uduri ba zai k’ara tako k’afar sa gidan ba. Suraj sai bayan sallar magrib ya gama harkokin sa, ya koma station, Ba b’ata lokaci aka fito dasu Jangwal, Bindiga ya karb’a hannun d’aya daga cikin yan’ sandan, Fuskar sa ba alamar wasa yace “Bana son b’ata lokaci, ku fad’a mun wanda ya kai ku, ku wallahi na tarwatsa kanku da bindigar nan”, Ganin yadda ya harbi Jangwal yasa suka tsorata, Jangwal yace “Zan fad’i gaskiya amma Dan Allah kar ka bari a cutar da iyayen mu”, D’ayan yace “Ka taimake mu ranka ya dad’e” “I promise ba abunda zai samu iyayen ku”, Jangwal yace “Tasleem ce itace ta saka mu”, “Wacece Tasleem?”, “Yarinyar Alhaji Tambari” Suraj mamaki ya cika sa, bai tab’a kawo ma ransa itace ba, “Tasleem yar’ Alhaji Tambari” Ya furta, idon sa suka kad’a sukayi jajir, ya cije lips d’in shi na k’asa, “TASLEEM TASLEEM i will make sure you pay for this, idan ma ubanki ya tsaya miki…….”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *