FETTA CHAPTER 22

FETTA CHAPTER 22

Mik’ewa yayi ya d’auki mukullin motar sa, Yan sandan wurin ya umarta su mayar dasu cell, “Ranka ya dad’e yaushe za’a sake mu, Dan Allah a sake mu wallahi mun tuba” cewar Jangwal, Ko kallo bai ishe shi ba balle ya bashi amsa, ya fice daga station d’in, ya nufi gida cike da sak’e sak’en yadda zai yi maganin Tasleem. + Mimi ke ta kuka, Hajiya da Fetta sun rud’e sun rasa me zasu mata ta daina kuka, Fetta ta bata nono tak’i sha, “Ko cikin ta ke ciwo” Cewar Hajiya, Fetta tace “Nima nayi tunanin haka”, “Kira Suraj yazo mu kai ta asibiti” Hajiya ta fad’a tana karb’ar ta, “Kaii yarinyar nan anyi yar’ banza” Su’ad ta fad’a tare da jan tsaki, Feena dake gefe tace “Wallahi duk ta cika mana kunne, kamar naje na shak’e ta”, Su’ad tace “Daga ita har uwar ta na tsane su, sun zo sun zamar mana annoba cikin gida” Shigowar Suraj yasa Fetta tsayawa, Da sauri ya nufi Hajiya yana tambayar “Lafiya?, me ya same ta?”, “Ina tunanin cikin ta ke ciwo, muje a kai ta asibiti”, Ya mik’a hannu zai karb’e ta, Hajiya tace “A’ah kai da zaka yi tuk’i” Cikin minti 30 suka kawo asibiti, Dukkansu a rud’e, Ba b’ata lokaci suka samo ganin likita, Ya duba ta yace “Cikin ta ke ciwo da zazzab’i”, Ya mata allura, ya rubuta musu drugs, a pharmacy na asibitin suka siya suka koma gida. Hajiya ta riga fita da Mimi wacce tayi bacci ana mata allura, Fetta tazo fita yace “Ki kula da ita sosai”, Kai ta mishi nodding ta fice daga motar, Tana mamakin ta haifi ya’ sannan a fad’a mata kula da ita, Yana wa Mimi wani irin so ne, baya son ko kad’an abunda zai tab’a ta ko ya raba shi da ita, zama part d’in su Hajiya ma dan ba yadda zai yi ne, Ya so ya fake da attacking nasu da akayi su dawo part d’in shi, Fetta ta buk’aci komawa,

Falon sa ya zauna yana huce gajiya, Ya lalubo wayar sa, ya shiga text messages, Number da aka mishi message yayi dialing, wanda zuciyar sa ke masa zargin Tasleem, Tasleem na kwance d’akin ta, tana duba hotunan Suraj, wanda shine aikin ta kullum, Taga kiran shi, tayi saurin zabura, gabanta ya fad’i, “Ko dai sun fad’a mishi nice, na shiga uku na”, Har wayar ta tsinke bata d’auka ba, Kira na biyu ya sake shigowa, Cike da zullumi ta danna receive tare da kangawa a kunne, “Tasleem”, Ta jiyo muryar sa, sai da numfashin ta ya d’auke na wucin gadi, Wani sanyi taji na ratsa zuciyarta jin wanda take tsananin k’auna ya kira sunan ta, “Ko ba ita ba ce”, “Ita ce”, Ta fad’a murya na rawa, Ya cije lips d’in shi na k’asa, yana jin tamkar ya shak’aro ta ta cikin wayar, Ya danne abunda yake ji, Yace “I just call to say hi”, Tasleem ji take tamkar a mafarki, farin ciki ya lullub’e ta, tama kasa magana, “Are you there?”, “Eh eh ina ji”, “Ok bye”, Kafin ta sake magana, ya kashe, Wayar tabi da kallo ta kasa yarda, Ta cillar kan gado, Ta buga tsalle cike da murna, “Suraj ya kirani”, Ta mari kanta, “Ko mafarki nake, ba mafarki nake ba, Suraj ne ya kirani, wayyoo dad’i, zuwan da nake gidan marayun sa ashe na shiga ran sa”, Tayi wani juyi cike da farin ciki. Suraj na kashe wayar, yayi murmushin gefen baki sanin plan d’in shi will work, Ya ajiye wayar kan bedside drawer, Ya mik’e ya gabatar da sallar isha’i. “Ka kiyaye ni wallahi idan baka so ganin mummunan b’aci rai, duk yarinyar da kaje wurin ta sai ka samu rashin mutuncin da ka mata tace bata so, toh ka kiyaye ni”, Kawu Lamid’o ya fad’a cike da fad’a, Bello dake durk’ushe gaban shi yace “Kayi hak’uri Abba amma wallahi bana musu wani abu, sune basa ra’ay…”, Gwaggo ta katse shi “Dallah rufewa mutane baki, tunda kai kafi kowa bak’in jini, baka da muguwar kama, kana da abun hannun ka, me zai sa mata har uku su guje ka”, “Abunda na gani kenan, toh wallahi ka maida hankalin ka, ko ka had’u da b’acin rai, ka koma wurin yar’ Alhaji ka bata hak’uri, ka tabbatar ka shawo kan ta” Cewar Kawu Lamid’o,

Wani zufa yaji ta keto masa, dan gaba d’aya baya sonta, tsarin ta da komai nata bai mishi ba, ga uwa uba wulak’anta shi da yayi, Kawu Lamid’o ya katse mishi tunani “Kana ji na ko?”, Ya had’iye b’acin ran da ya taso mishi yace “Eh”, “Tashi ka bani wuri”, Ya mik’e yana jin tamkar ya fasa ihu tsabar bak’in ciki. Tasleem farin ciki kamar ya kashe ta, Suraj ya kira ta, Ta kira Sophy ta sanar da ita, Tace “Ina miki murna, Allah ya bar soyayya”, Ta kashe waya, Tasleem tabi wayar da kallo ganin tayi saurin kashewa kafin tace komai, “Dama nasan bak’in ciki take, bata sona da Suraj, toh sai dai ki mutu wallahi”, Taja tsaki, ta kunna data, taje kan contact d’in shi tayi sending Hy, bai yi delivering ba, Suraj whatsapp bai dame shi ba, is hardly ga kanshi online. *12:30 na rana* Fetta na folding kayan mimi da aka wanke, Suraj yayi sallama ya shigo, k’amshin turaren sa mai dad’i ya ziyarci k’ofofin hancin ta, “Sarkin son turare”, Ta fad’a a ran ta, Ba tare da ta d’ago kanta ba tace “Ina kwana?”, “Lafiya lau”, Ya amsa tare da zuba mata ido, Doguwar riga ce ta atamfa a jikin ta, Ta kamata d’ass a jikin ta, ta mata kyau sosai, Yaji tamkar ya rungume ta, Yayi saurin kwab’ar kan sa, Ya k’arasa bakin gado, Ya d’auki Mimi, “Ya jikin ta?”, Ta amsa da “Da sauk’i bata sake wani kuka ba”, “Kin bata magani?”, “Eh”, “Ok, ki kiyaye bata akan lokaci”, Tayi nodding kai, Ya sumbace ta a goshi, “Get well soon My angel”, Tana so ta tambaye shi, sun fad’i waya turo su, tana fargabar amsar da zai bata, Tana so tasan su wa ke farautar rayuwarta da na yar’ta, Me tana so taji laifin me ta musu?, me ta tare musu? Ya kwantar da Mimi, ya mik’e zai fita, Ta dake tace “Uhmm sun fad’i wanda ya turo su?”, “Idan kinji waye me zaki yi?”, “Ba abunda zanyi amma ina so nasan waye, da kuma dalilin shi”, “Wata ce mai sona”, Ya fad’a tare da kafe ta da ido, kamar mai son gano abu a tare da ita, Kalmar taji ta daki k’irjin ta, ranta yayi mugun b’aci, Bata san sanda ta furta “Mai son ka”, Ya d’aga mata kai, “Meye had’in son da take maka da son kashe mu, tayi ta son ka mana, ka aure ta ma, but plss she should stay away from me and my daughter”, Ta fad’a idonta sun rins sunyi jajir, “Bata son sharing d’ina da kowa shiyasa taks son kawar da ku”, A fusace Fetta ta d’ago kai tace “Then ka sakeni ka aure ta who cares, an gaya mata ina son ka ko na damu da kai”, Zafin furucin ta yasa shi kasa cewa komai, Ya juya ya fice daga d’akin,

Ta fad’a kan gado tare da fashe da kuka, “Who cares, an gaya mata ina son ka ko na damu da kai”, Shi ke mishi yawo a kwak’walwa, Yana jin zafi cikin zuciyar shi, Shi kad’ai ke driving, yana nanata maganganun ta a ranshi, har ya kawo bakin gidan su Tasleem, Wayar sa ya jawo yayi dialing number ta, bugu d’aya ta d’auka, “Ina bakin gate”, Ya kashe bai jira cewar ta ba, Tsalle ta buga ta diro daga gado, “Unbelievable Suraj a gidan mu”, Wadrobe ta bud’e ta fiddo wani dank’areren lace ta saka, ta d’auko sark’a da yan kunni tasa, ta chab’a kwalliya, ta bad’a jikin ta da turare ta fito tana yanga. Ta cikin mota yake hango ta, yana jin tamkar ya fito ya shak’eta sai taji k’amshin lahira, Saitin shi ta tsaya tare da yin knocking glass, Ya sauke glass yana bin ta da kallo, Tasleem tamkar zuciyarta zata fasa k’irjinta ta fito, ba zata iya fassara a yanayin da taji ta ba, Son Suraj ke ratsa ta, Tayi k’arfin halin cewa “Mu shiga daga ciki”, + Ba musu ya bud’e k’ofa ya fito, yabi bayanta, Tana karairaya, Falon bak’i ta nufa dashi, Ya zauna yana k’arewa falon kallon, Masu aiki suka shiga kawo abubuwan motsa baki, Tasleem ta duk’a gaban sa, Ta tsiyaya lemo ta mik’a masa, Ya karb’a yace “Thank you amma bana shan orange juice”, “Ayyah bari a kawo maka wani”, “No Thank you”, Sam bai yarda da ita ba, balle ya sha wani abu daga hannun ta, Ranta bai b’aci ba, zuwan sa gidan yafi mata komai, Ya nisa yace “Ina son mutane irin ki masu nuna tausayin su ga rayuwa” Tayi murmushi tare da yin fari da ido tace “Marayu abun tausayawa ne, sun rasa iyayen su, wasu sun tashi basu san su ba, kaga ya kamata a taimaka musu”, Yayi nodding kai yace “Hakane, shiyasa kika k’ara burgewa”, Tayi murmushi tana jin dad’i na ratsa ta, “But babban abunda yasa kika burgeni naji ina so mu k’alla alak’a tsakanin mu shine yadda kike tsananin so na”, Ta waro ido tace “Dama kansa ina son ka”, Yace “Yes a jiya na sani, kuma na shaida kika tsananin so na, son da ya kai ki ga aika thugs su kashe matata da ya’ta”, Tasleem gabanta yayi mummunan fad’uwa, ta had’iye wani yawu da k’yar, tsoro ya bayyana k’arara kan fuskar ta, “Ya dai?, ya naga kin tsorata, relax!, nasan soyayyata tasa kika aikata haka, naji dad’i da na samu mai k’auna ta haka”, Ya fad’a hankali kwance, yana murmushi dashi kad’ai yasan ma’anar shi, Ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya tace “Ina tsoro na rasa ka Suraj, am deeply in love with you, wallahi na fad’a tarkon k’aunar ka, soyayyarka ta rufe muj ido, bana ji bana gani bana gane komai akan son ka, ka taimake ni ka aure ni”, Ta kai gwiwoyin ta k’asa, Da hannu ya mata alamar ta tashi, Ta tashi ta zauna kan kujera,

“Tunda har na tako k’afa nazo gidan ku, kinsan na shirya miki something special, so taso muje”, Ta mik’e cike da farin ciki tabi bayan sa, Gaban mota ta shiga ta hakimce, Yaja mota yana murmushin gefen baki. Fetta taci kukan ta mai isar ta, Ta tashi zaune tare da fad’in “Kukan me ma nake?, akan me zanyi kuka?”, Taja siririn tsaki tana share hawayen ta, “Allah ya jik’an Addani, ya bi maka hakk’in ka, Mamana Allah ya gafarta miki, Ya Allah ka tsaremu da dukkan masu sharri”, Ta mik’e ta shiga toilet ta watsa ruwa, duk ta had’a gumi kukan da tayi. Aunty Jummai taci ado cikin irin atamfar da ta ba Fetta, Bilkisu dake zaune falo tana kallo tace “Umma wannan kwalliya sai ina?”, “Gidan Hajiya mana, baki ga kayan dake jikina ba”, “Ohh ban gane ba wallahi sai yanzu, amma Umma kan ki naja fah”, Tayi murmushi tace “Mu na wasa ne, tun duniya na kwance muke shu’uman ci”, Bilkisu ta jinjina kai tace “Allah yasa yau naji labari mai dad’i”, Aunty Jummai tace “Kwantar da hankalin ki zaki ji”, Ta fice, Napep ta shiga, ta nufi gidan Hajiya, cike da k’udurin ganin k’arshen Fetta yau. Suraj tunda suka shiga mota, bai sake magana ba, k’ira’ar Sudais da ya kunna yake bi, Tasleem baki ya kasa rufowa, farin ciki fal zuciyar ta tana tare da masoyin ta, har suka kawo wata unguwa mai tsirakun gidaje, layin da suka shiga gaba d’aya gida uku ne, Bakin wani madaidaicin gida yayi horn, Mai gadi ya bud’e gate, Yaja motar ciki, Cike da girmamawa mai gadi ya gaishe sa ya amsa, Tasleem babu tsoro ko fargaba a tare da ita, STORY CONTINUES BELOW “Mu shiga ciki”, Ya fad’a yana yin gaba, tabi bayan sa, Falo taga sun shiga wanda ya tafi da imanin ta, A fili ta furta “Aljannar duniya”, Ba k’aramin had’uwa yayi ba, ba abunda babu na more rayuwa, Tana zauna tana k’arewa falon kallo, K’aramin fridge dake gefen sa, ya bud’e ya d’auko lemo mai sanyi, ya bud’e yayi sip d’aya, “Tasleem”, Ya kira ta da wani yanayi da yasa ta saurin kallon sa, Suraj d’in d’azu ba shine yanzu a gabanta ba, gaba d’aya ya canza, fuskar sa tamkar bai tab’a dariya ba, “Ashe ke sakarya ce wawiya, a cikin dabbobin bansan a wane fanni zan saki ba”, Tasleem da ta fara tsoro tabi sa da kallo cike da mamakin canzawar sa lokaci d’aya, Ya sake yin sip na lemo, Yace “Kina tunanin kiyi yunk’urin kashe iyalina, and i should let you go free”, Yayi wata dariya yace “Shine hauka da wauta irin naki, wacce irin k’wakwalwa ce dake da bata ja, lokaci d’aya kin yarda dani”, Yasa k’afe ya take mata yatsun k’afa, Ta cije baki cike da azaba, “Dan Allah kayi ha…..”, Ya katse da yi mata wata tsawa da tasa falon amsawa “Idan na sake jin bakin ki, sai na zubar miki da hak’ora” Hawayen azaba suka shiga zirya kan kumatun ta, Suraj ya cigaba da matse k’afar cike da mugunta, Wayar sa ya jawo ya danna kira,

Maza ne su biyu masu ji da k’arfi suka shigo, Da hannu ya musu alama su ja Tasleem, D’ayan su ya fisgota da k’arfi, “Wayyo Allah na, Daddy na, Dan Allah kayi hak’uri wallahi bazan k’ara ba, son da nake maka yaja haka”, Ya fice abun sa, ba tare da ya nuna yasan tana yi ba, Haka suka ja ta, tana ihu, wani d’aki mai duhu suka jefata ciki, Suka rufe, Ta shiga ihu da birgima tana kiran “Daddy wayyo Daddyna kazo ka taimake ni, Daddy na” “Baki da kirki wallahi, kwanan ki nawa yau baki zo ba”, Cewar Fetta dake waya da Yasmeen, “Tuba nake uwargidan Surajo wallahi school ce ta saka ni a gaba, amma gobe In Shaa Allah zaki ganni”, “Yar’ ki tayi fushi”, “A’ah ya’ta ba zata yi fushi dani ba”, Shigowar Aunty Jummai yasa tace “Zan kira ki”, Tayi hanging up, “Fetta ana d’aki, ke dai bakya gajiya da zaman d’aki”, Cewar Aunty Jummai tana washe baki, Tayi murmushi tace “Ina wuni?”, “Lafiya lau, yau kinga nasa irin atamfar ki, nace muyi anko koh”, Murya a sanyaye tace “Wallahi Aunty ranar suna aka sace” 1 A razane Aunty Jummai tace “An sace”, “Eh wallahi”, “Garin yaya kika bari aka sace, wane irin sakaci ne wannan, ko dan baki d’auki kayan da muhimmanci ba”, cewar Aunty Jummai cike da fad’a da tsananin b’acin rai, Fetta mamaki ya cikata ganin yadda take fad’a, bai kamata ace ranta ya b’aci haka ba, “Kiyi hak’uri Aunty ba su kad’ai aka d’auke ba, suna da yawa”, “Dallah rufe mun baki, dama talaka irin ki taya zata san darajar kaya, yar’ cin arzik’i”, Yar’ cin arzik’i karaf a kunnen Suraj da shigowar sa kenan ya duba lafiyar babyn sa, Aunty Jummai a zaton ta bai ji ba, Tana washe baki tace “Suraj ne, sannu da zuwa”, Wani matsiyacin kallo da ya jefa mata yasa jikin ta yin sanyi, “Dan Allah daga yau ki fitar sabgar iyalina, Fatima ba yar’ cin arzik’i ba ce, ko kin manta Matata ce mai gadona, gudan jini na daga jikin ta ya fito, so please ki daina jifan ta da bak’ak’en kalamai”, Aunty Jummai ji tayi tamkar k’asa ta bud’e ta shige ciki, kunya, haushi da takaici suka dabaibayeta lokaci d’aya, jiki ba k’wari ta fice daga d’akin, Fetta kukan da ya taho mata, ya koma, Kalaman Suraj yasa taji sanyi a ran ta, Bai bi ta kanta ba, har yanzu yana ji haushin furuncin ta, Mimi ya d’auka ya fice daga d’akin, Tabi bayan sa da kallo, tare da sauke ajiyar zuciya. Aunty Jummai daga d’akin bata zarce ko’ina ba sai gate, ta tari mai napep ya kaita tasha, ta shiga motar da zata kaita k’auyen da bokan ta yake.

Hajiya da Su’ad a gajiye suka dawo gida, sunyi siyayya mai yawa, biki nata k’arasowa, A falo suka baje kayan, Fetta ta fito cike da ladabi tace “Sannu da zuwa”, “Yawwa Fetta, zauna Dan Allah ki tayamu shirya kayan nan”, Ta amsa da “Toh” tana zama, Su’ad tace “Allah ya bar mun ke Mamana da Ya Suraj, wallahi kun fitar dani kunya da gorin dangin miji, a kai mutum ba kayan d’aki ai k’arshen jin kunya kenan”, Habaici take yadawa Fetta, ta gane tayi tamkar bata fahimci me take nufi ba, Hajiya tace “Meye abun jin kunya, kayan d’aki al’ada ce kawai, musulunci bai wajabta, a aure sadaki ne dole”, “Duk da haka dai Mama, gara a maka wallahi ka wuce raini”, “Zaman lafiya shi yafi komai, duk kayan nan da kike gani idan ba zaman lafiya da kwanciyar hankali, duka fita ranki zasu yi, kiga basu da wani amfani”, “Uhmm Mama kenan”, Hajiya ta girgiza kai ganin akwai k’uruciya a tare da ita, Fetta sam maganganun Su’ad basu b’ata mata rai ba, zuwa yanzu yaci ace ta saba da halayyar su. Tasleem taci kuka da birgima babu mai taimakon ta, Ta kira sunan Daddy yafi sau dubu, Cikin ta nata kukan yunwa, duk ta galabaita, K’ofar da aka bud’e yasa ta saurin mik’ewa, Tayi hanyar fita, Ya cafko ta ya mayar da ita, “Dan Allah ka taimaka ka sakeni na tafi, wallahi na maka alk’awarin ko nawa kake so zan baka”, Wani banzan kallo da ya watsa mata, yasa tasha jinin jikin ta, ya tura mata leda gabanta, ya fice tare da rufe k’ofar, Ta saki ihu, ganin ihun ba zai amfane ta ba, ta jawo ledar ta bud’e, Takeaway ne na abinci da ruwa, jiki na rawa ta bud’e, ta fara kaiwa shinkafar loma. Alhaji Tambari ya kasa zaune, ya kasa tsaye, hankalin sa ya tashi ganin har sha biyu na dare, babu yar’sa tilo d’aya ba labarin ta, duka gidajen k’awayen ta, da wurin da aka san tana zuwa anje bata nan, Wayarta a kashe, Ya kira yafi a k’irga, “Ina Tasleem ta shiga?, Idan ma sace ta akayi na rantse da wanda rai na ke hannun sa, ko waye sai nasa ya k’araci rayuwar sa cikin bak’in ciki da nadama”, Matar sa dake gefe tace “Addu’a zamu yi Allah ya bayyana ta”, Wani banzan kallo ya jefa mata, Ya danna kiran commisioner of police, bugu biyu ya d’auka, “Ranka ya dad’e barka da dare”, “Comms ya’ta ta b’ace bansan a wane hannu take ba, ina so ya baza yan’sanda ko’ina nemanta”, “Ok Ranka ya dad’e”, Ya kashe ya kira shugaban yan’ civil defence shima ya sanar dashi, Gidajen radio da Tv duka sai da ya bayar da cigiya. Aunty Jummai bata samu motar zuwa k’auyen ba, Yamma tayi, Ta koma gida rai ba dad’i, Bilkisu bata nan, Ta shige d’aki ta rafsa tagumi, Tsananin tsanar Fetta take ji a ranta, tana ganin ita ta hana mata dukkan jin dad’i, da yanzu Bilkisu na gidan Suraj, Tana cikin daula, taci mai kyau ta sha mai kyau, a daina mata kallon raini, Bak’in fentin da Sahabi ya mata ya goge. + Karima rashin dawowar Mijinta Bello ya soma damun ta, daga kwana biyu yau satin shi d’aya, Kullum ce mata yake yau, gobe, Yau ma tana sa ran dawowar sa kamar yadda yace, Abdul tasa ya d’auko mata wayar ta d’aki, Bello na kwance kan katifar d’akin sa, damuwa da bak’in ciki sun dababaiye sa, kiran Karima ya shigo, Ya d’auka, “My love ina kwana?”, “Lafiya lau, ya kwanan ku?”, “Kewar ka ta hana mu muji dad’in bacci”, Yayi dariya dan kar ta fahimci wani abu yace “Nima ina kewar ku sosai”, “Yau d’in zaka dawo”, “Kiyi hak’uri love wallahi wani aiki ya k’ara tasowa”, Karima ranta taji ba dad’i “Toh” kad’ai ta iya ce masa, Ta kashe wayar tana ji a jikinta ba lafiya ba,

Bello ya ajiye wayar yana dafe kai tare da furta “Ya Allah”. Fetta tunda ta idar da sallar asuba, bata koma bacci ba, Kanta ke ciwo sosai, a kan sallayar ta zauna tare da jingina da gado, ta runtse ido, tana lazimi, A hankali taji ciwon na k’aruwa, zazzab’i ne ya rufe ta, a wurin ta kwanta tana rawar sanyi. Sha d’aya da rabi Suraj ya tashi yayi wanka, Ya shirya cikin shadda fara, ta matuk’ar yi mishi kyau, Ruwan tea kad’ai ya sha ya fito, A falo ya tarar da Hajiya na karin kumallo, Suka gaisa, Ya nufi d’akin Fetta, A rud’e ya k’arasa cikin d’akin ganin tana rawar sanyi, hijabin da ta lullub’e ya janye, Ya tab’a jikinta zafi rau, “Meke damun ki?, tun yaushe baki da lafiya?”, Kasa bashi amsa tayi sai jikinta dake kyarma, D’aukar ta yayi tamkar baby ya d’aura kan gado, Wayar sa ya lalubo ya danna kiran family doctor d’in su, yace yazo urgent, Tunanin taimakon da zai bata yake, kafin zuwan Dr, Kanta ya d’aga daga kan pillow ya d’aura kan cinyar shi, Ya d’aura hannun shi saman kanta yana shafawa a hankali, Ciwon kan taji yana raguwa, Yana ta faman jera mata sannu, Kiran Dr ya tabbatar masa da ya iso, A hankali ya d’aga kanta ya d’aura kan pillow, Ya fito, Hajiya ta tashi daga falon, Dr na tsaye bakin motar sa, Yayi masa iso zuwa jiki, Dr ya dubata yace Malaria ce, cizo sauro ne ya mata kamu, Yace zai mata allura, Suraj yace “A mata a hannu”, “A baya zai fi, wani lokaci allura a hannu na zuwa da matsala”, Suraj ya murtuke fuska yace “Idan har ba zaka mata a hannu ba sai dai a bar allurar”, Dr yayi murmushi ganin kishi k’ara k’ara akan fuskar Suraj, Yace “Alright bari a mata a hannun” Ya mata ya bata drugs, Yace “Za’a mata allura na kwana uku”, Suraj ji yayi tamkar yace a bar allurar, haushin yadda Dr ya rik’e mata hannu yake ji, Ya k’ara da ta rik’a cin abinci sosai, Sukayi sallama ya wuce. Ya kai duban sa gareta, “Ya kike jin jikin naki yanzu?”, “Da sauk’i”, “Allah ya baki lafiya”, Ta amsa da “Amin”

Fita yayi, Part d’insa ya nufa, Ya d’auki plate yayi serving chips da miyar k’oda, yasa wani plate ya rufe, ya dawo sashen Hajiya, Fetta ta d’auka tafiyar sa yayi, har taji haushi na rashin nuna kulawa taci abinci tasha magani, (Nace ina laifi ma ya kira miki Dr), Sallamar sa taji, ta amsa murya k’asa k’asa, “Tashi kici abinci”, Ya fad’a yana zama gefen gado kusa da ita, Ba musu ta zauna, STORY CONTINUES BELOW Abincin ya bud’e, yasa fork ya d’ibo ya nufo bakin ta, Mamaki ne ya kamata, a tunanin ta tunda ta haifi masa babyn sa, ba zai sake feeding d’in ta ba, Ko ya damu da cin abincin ta, “Karb’a mana”, Ta bud’e baki ya saka mata, idonsu ya sark’e cikin na juna, kowanne ba zai iya fassara yanayin da yaji sa ba, Tayi saurin janye idonta, ta sunkuyar da kai k’asa, “Fatima” Ya kira sunan ta cikin wani siga, “Na’am” Ta amsa ba tare da d’ago kai ba, Ya zuba mata ido tamkar mai son cewa wani abu, Sai kuma yayi shiru, ya cigaba da feeding d’in ta, kallon da yake mata, yasa ta kasa sakin jiki taci abincin yadda ya kamata, sai da ta cinye duka, ya bata ruwa ta sha, Ya d’auko drugs ya bata ta sha, “Kiyi bacci ki huta, don’t stress yourself”, Tayi nodding kai, Ya fice, Kwanciya tayi, tana jin dad’i da sanyi a ranta na kulawar da ta samu daga Suraj, ta rasa dalilin da yasa take jin haka. Tasleem sam bata runtsa ba, cizon sauro da cinnaka ya dameta, tana ta faman dukan jikin ta tana hawaye, “Wallahi sai nasa Daddyna yayi maganin ka kuma ka aure ni dole”, Ta fad’a tana sosa wurin da cinnaka ya mata wani mugun cizo, Sallah bata dameta ba, dan haka bata damu tayi yunk’urin yi ba. Police station Suraj ya fara zuwa, Ya buk’aci ganin su Jangwal, suka zube gaban sa suna fad’in “Ranka ya dad’e Dan Allah kasa a sake mu wallahi mun tuba”, Ya nisa yace “Zan sa a sake ku amma da sharad’i d’aya, zaku yi alk’awarin daina aikata ta’addanci, idan aka k’ara kama ku da wani laifi, zaku bak’unci lahira”, “Wallahi mun tuba, dama rashin aikin yi ne da talauci ya saka mu, ko faskare ne zamu koma yi”, “Zan baku jari ku kama sana’a”, Suka shiga zuba godiya, Ya buk’aci a sake su, Yaba kowannen su dubu d’ari, Addu’a ba wacce basu mishi ba, A ransu sun k’uduri aniyar daina ta’addanci. Gidan gonar sa ya wuce, Yana shiga office, Rabi’u ya rufa masa baya, Cike da girmawawa ya gaishe shi, Ya amsa, “Ranka ya dad’e Kamal ya kirani jiya, harkoki a lagos sun fara chab’ewa, ana buk’atar ka can”, “Me kuke nufi?”, “Rashin ka a can na tsawon lokaci yasa ba komai suke iya handling ba”, “Naji”, “Ok Ranka ya dad’e”, Ya juya ya fice. “Ya zama dole naje lagos duk da bana son nisa da babyna”, Ya fad’a yana duba wani file mai d’auke da harkokin sa na lagos. Bello da k’yar ya samu fitowa daga d’aki, ya gaishe da iyayensa, Kawu Lamid’o yace “Sai yanzu ka fito”, “Kaina ne ke ciwo, nasha magani na kwanta”, “Toh Allah ya k’ara sauk’i”, “Amin” “Tasleem yarinyar mai gida, ta b’ace tun jiya ba’a san inda take ba, kana da masaniya a kai?”, Da kallon mamaki yabi mahaifin nasa, “Tambayar ka nake kana da masaniya a kai, ko dan nace dole ka aure ta, yasa kayi sanadiyyar b’acewar ta”, Tsananin b’acin rai da takaici ya lullub’e zuciyar sa yace “Haba Abba kafi kowa sanin halina akan me zaka mun wannan mummunan zargin”, Gwaggo tace “Gaskiya bana tunanin Bello zai aikata haka, ka manta halayyar sa”, Kawu Lamid’o yace “Ahh na sani ko ya canza” A fusace ya mik’e ya fita, idan ya tsaya zai iya fad’awa Mahaifin sa maganar da bata dace ba, “Ya Allah wane irin iyaye ka bani”, Ya fad’a yana dafe zuciyar sa da yake jin tamkar zata fashe. “Wai ke Sis ba zaki hak’ura da dating dating d’in nan ki fitar da miji kiyi aure ba”, Cewar Su’ad, “Uhmm ke ni k’yaleni ban shirya ma stress na aure ba”, “Shikenan, nikam next week kamar yanzu ina gidan masoyina”, Feena ta tab’e baki tana danna waya, “Dan’ halak ana maganar sa yana kira”, Ta fad’a tana danna receive, “Hello baby boo”, “Gani cikin gidanku”, “Really?”, “Yeah ki fito”, D’an k’aramin mayafi ta yafa, ta fesa turare, Cikin mota ta same sa, Tace “Fito mu shiga ciki”, Ba musu ya fito yabi bayan ta zuwa main falo na gidan, “Bari na kawo maka ruwa”, “A’ah yi zaman ki abu kawai nazo na nuna miki”, Takarda ya mik’a mata yace “Duba ki gani”, Ta karb’a ta karanta takardar transfer ce da k’arin girma a wurin aiki, an mishi transfer zuwa kaduna, za’a bashi gida da mota, ga albashi mai tsoka, “Wow babylove Am soo happy naji dad’i wallahi”, Ta manna mishi peck, ta manta a ina suke, Yayi murmushi yace “Kin shirya zama kaduna tare dani, ko anan zaki zauna na rik’a zuwa weekend”, “Tabb ai k’afar ka, k’afata, yanzu zan fad’awa Mama ayi mun jere a can”, Yayi dariya yace “Naji dad’in jin haka, bari naje na sanar dasu mummy ke na fara nunawa”, Farin ciki ya sake lullub’eta jin itace farko, “I love you baby”, “I love you more”, Ta masa rakiya har bakin motar sa, ta dawo cikin gida, Ta sanar da Hajiya, tace ba damuwa sai a mata a can, ai cigaba ne aka samu.

Alhaji Tambari ya rafsa tagumi, daren jiya sam bai runtsa ba, abincin da matar sa ta ajiye masa, ko bud’ewa bai yi balle yasan meye a ciki, “Alhaji Dan Allah ka kwantar da hankalin ka kaci abinci”, A fusace ya d’ago cike da fad’a yace “Na lura sam baki damu da yar’ nan ba, yadda kika san ba ke kika haife ta ba, wato har kinga wurin cin abinci, ba’a san halin da daughter take ciki ba”, Tayi murmushi tana mamakin halayya ta mijin ta, ina ga tafi sa damuwa, kawai tana juriya da takwalli ne, ba kamar shi ba, da baya fawwalawa Allah al’amuran sa. Suraj a gidan gonar sa yayi sallar la’asar tare da ma’aikatan sa, Yana idarwa bai koma office ba, Ya shiga office ya nufi gidan da ya kai Tasleem. Kwance take a galabaice, ga yunwar da ta addabe ta, Jin an bud’e k’ofa tayi saurin mik’ewa, a zaton ta abinci aka kawo mata, Ganin Suraj da yanayin fuskar sa, yasa tayi saurin ja baya, Matsowa ya shiya yi tana ja da baya, har ta kai k’arshen bango, covered shoe d’in shi yasa ya take mata yatsun k’afa, ta saki ihun azaba, da hannu ya mata alamar ta masa shiru, bindiga ya zaro ya d’aura saman goshin ta, “Kafin ki kashe iyalina ni bari na kashe ki”, A matuk’ar tsorace tace “Dan Allah ka taimaka kamun rai, wallahi na tuba, bazan sake bibiyar rayuwar ka da ta iyalin ka ba”, “K’arya kike, gara na aika ki lahira”, Fitsari ta saki tsabar tsoro, Saurin ja da baya yayi yace “You are very stupid, taya kike tunanin mace mara aji irin ki zata burge SURAJ SA’ID”, “Kayi hak’uri Dan girman Allah”, Murmushin gefen baki yayi, “Sassauci d’aya zan miki shine rashin kashe ki, amma dole ki k’arbi hukunci, abu na k’arahe ki wallahi na rantse da Allah da kika sake yunk’urin aiwatar da wani abu, sai na b’atar dake, an shafe tarihin ki a rayuwa”, Tasleem ta matuk’ar tsorata da kalaman sa, 1 Ya fice, gadaran maza ne guda biyu suka shigo, D’aya rik’e da sharb’eb’iyar bulala, Cikin d’aga murya yace “Kwanta”, Ba musu ta kwanta, gabanta na dukan uku, ganin girman bulalar ba k’aramin d’aga mata hankali yayi ba, Bulalar ya shiga zuba mata a baya da k’arfin sa, “Wayyo Allah na na shiga uku, bayana ya karye, zan mutu”, Bai tausaya mata ba, ya cigaba da zuba mata, sai da ya mata guda d’ari, Bata sake wani motsi a gurin ba, numfashin ta ya d’auke.      

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *