FETTA CHAPTER 23
D’aukar ta suka yi, suka jefa bayan mota, Suna kawowa kusa da gidan su, D’aya ya shek’a mata ruwan sanyi masu k’ank’ara, firgigit ta farfad’o tana sauke nauyayyen ajiyar zuciya, k’ofa ya bud’e yasa k’afa ya ture ta, ta fad’i ta gangara gefen titi, Suka je motar tare da bad’a mata k’ura, Goshin ta ya bugu da wani dutse, jini ya shiga tsiyaya, ta dafe goshin cike da azaba tana hawaye, Da k’yar ta mik’e tana ganin jiri, a haka ta kai gida, Mai gadi a rud’e ya bud’e mata k’ofa cike da tsoron ganin yanayin ta, dan a zaton sa, had’ari tayi, gaba d’aya ta canza kama, Alhaji Tambari ya fito da nufin yaje police station yaji ya ake ciki, Gani Tasleem yayo kanta yana fad’in “My daughter Me ya sameki?, accident kika yi?”, Jikin sa ta fad’a ta fashe da kuka, Cike da tashin hankali yace “Ki fad’a mun me ya same ki?”, Ganin idon ma’aikatan gidan a kan su, ya jata cikin gida, Mamanta na zaune falo ganin ta tayi saurin mik’ewa, “Tasleem me ya same ki haka?”, Ta sake fashewa da wani kuka, Alhaji Tambari ya shiga shafa bayanta, ta saki ihun azaba, a rud’e ya d’aga rigarta, Shatin duka rud’u rud’u duk jini da ya gani, Ya matuk’ar d’aga masa hankali ya harzuk’a sa, A fusace yace “Wa ya miki wannan?, wallahi ko waye sai ya gwammace mutuwar sa”, Tayi shiru tana sheshshek’ar kuka, “Ki fad’a mun d’an gidan uban waye”, Ya fad’a a tsawace, karon farkon da ya tab’a mata tsawa, “Suraj ne” Ta fad’a tana jan majina, Jikinsa ya matuk’ar yi sanyi, duk wani kuzari da shirin hukunta ko waye ya katse, yayin da wani bak’in ciki ya tokare wuyan sa, na rashin kasa d’aukar mataki a kan sa, babu yadda zai yi ya tunkari Suraj, yana tsoron ya fallasa sirrin sa, takaici da bak’in ciki suka lullub’e sa, yar’sa tilo d’aya da yafi k’auna a duniya, a aikata mata haka bai d’auki mataki, “Daddy Dan Allah kasa yayi regretting abunda ya aikata mun kuma ya aure ni wallahi ina son sa”, Alhaji Tambari ya kasa ko da k’wakk’waran motsi, sai hak’ora da yake fama had’awa, “Daddy please ka nuna mishi ina da gata”, “Tashi muje asibiti, idan mun dawo zamu yi magana”, Tana sharar hawaye ta mik’e, Ya juya kan Matar sa, “Taso muje”, Ta mik’e tana jimamin al’amarin, ba abun ta tambayi laifin da Tasleem ta masa, yasa yayi mata haka tayi laifi, dan tasan ruwa baya tsami k’asa banza.
Aunty Jummai da wuri ta shirya zuwa k’auyen da bokan ta yake, Minti 35 ya kai ta k’auyen. “Na kai mak’ura da lamarin yarinyar nan, so nake a tura aljanu su kashe ta”, Boka yayi wata k’ara mai firgitarwa, da tasa Aunty Jummai saurin zabura, K’warya mai d’auke da ruwa ta bayyana gaban sa, wani ganye ya zuba a ciki ya karkad’a sau uku, Yayi gyaran murya yace “Tana da k’arfin addu’a kashe ta zai yi matuk’ar wahala, amma auren su zai rabu, zamu saka mata k’iyayyar sa”, Aunty Jummai ta washe baki tace “Ko hakan yayi Zangur, zuwa yaushe hakan zata kasance”, “Nan bada jimawa ba, zan baki aiki na sati biyu dake da yar’ki”, Ta jinjina kai, Ya zaro k’ulli k’ulli, ya mata bayanin kowane amfanin sa, Ta shiga zuba godiya da masa kirari. Fetta allurar da aka mata yasa ta d’an ji k’arfin jikin ta, Yasmeen ta shigo rik’e da Mimi, Tace “Ah jiki ya fara sauk’i tunda har kin samu zama”, Tayi murmushi tace “Alhamdulillah, ciwon kai dai nake ji”, “Allah ya k’ara sauk’i”, “Amin”, “Gata ki bata nono, wunin yau madara take ta sha”, Ta karb’e ta, tana breastfeeding suna hira da Yasmeen, wacce rabin hirar Yasmeen ce me yi, tana sako mata zancen Suraj, bata hana ta ba, ta rasa dalilin da yasa take son hirar tasa. Hajiya na zaune na had’a invitation da sweets, da za’a kaiwa mutanen ta, Suraj yayi sallama ya shigo, Ya durk’usa ya gaisheta, ta amsa, “Mijin Su’ad ya samu aiki a kaduna, a can zasu zo zauna, ya kake gani?”, “Mama kenan, sai kace ni zan zauna mata, ai ita ke damar zab’ar inda take son zama”, Hajiya tayi murmushi tace “Hakane, na gaya maka ne a matsayin ka na babban yaya uba”, Yayi dariya jin dad’in furucin Hajiya, yana matuk’ar son a girmama shi, Yace “Allah dai ya basu zaman lafiya”, “Amin”, “Babu wani abu da ake buk’ata”, “Komai an kammala na kayan d’aki, na hidimar biki ma duk ka bayar”, “Toh Mashaa Allah, bari n duba su Fatima”, Ya nufi d’akin,
“Ina wuni?”, Yasmeen ta gaishe sa tana sunkuyar da kai, “Lafiya lau”, Ya amsa, Ta fice d’akin, Ya kai duban sa ga Fetta, “Ya jikin naki?”, “Da sauk’i”, Ya karb’i Mimi hannun ta, yana tambayar “Kinci abinci?, kinci magani?”, Ta girgiza kai alamar a’ah, Wani banzan kallo ya watsa mata “Meyasa you are so careless lafiyar taki ma baki damu da ita ba”, Ba tace komai ba, ta soma sabawa da halayyar sa, Yaja tsaki yana jawo ledar da ya shigo da ita, Shawarma ce da yoghurt, Ya mik’a mata “Ki cinye yanzu, na baki 10mins”, Ba musu ta karb’a ta fara ci, shawarma ba k’arami dad’i ya mata ba, Taji dad’in nuna damuwar sa a kanta, tas ta cinye, yoghurt d’in ma kad’an ta rage, “Mutum na cin yunwa, ba zai ci abinci ba as if cikin wani zai saka ma”, Ya fad’a yana hararar ta, “D’auko magani ki sha”, Maganin ta d’auko cikin bedside drawer ta sha, a ciki akwai nasa abinci, Cikin minti biyar bacci ya d’auketa, Suraj na gefen nama Mimi wasa, duk da bata fahimtar abunda yake, Juyowar da zai yi yaga tayi bacci, Wani k’yalli yaga tana mishi, ya kasa d’auke idonshi daga kallon ta, A hankali ya kai bakin sa saman nata, Ya shiga sumbata cikin wani irin yanayi, Fetta cikin bacci ta shiga mayar masa martani, ya soma fita hayyacin sa, ya kwantar da Mimi gefe, Ya rungume Fetta tsam jikin sa, yana aika mata sak’onni ta kiss, hannun sa ya kai cikin rigar ta, yana shafa dukiyar fulanin ta, ta shiga bank’aro masa su, tuni ya k’ara rud’ewa, Ya shiga romancing d’in ta, Ta bud’e ido cikin nasa dake lumshe, tayi saurin janye jikin ta tare da ja baya, Ya k’ara jawo ta ta fisge, “Ka bari mana”, Sai a lokacin ya dawo hayyacin sa, but still yana jin matsanancin sha’awa, “Hakk’i na zan karb’a”, Ya fad’a a dake, “Ka manta bana cikin tsarki”, Ta fad’i haka ne dan ta kub’uce masa, ba zata bari a kusancen ta a sashen Hajiya ba, Tsaki yaja ya fice daga d’akin, Yana mamakin me take akan sallaya d’azu, Da k’yar ya kai b’angaren sa, Ya kwanta kan gado ruf da ciki, yana mutsu mutsu a haka bacci ya d’auke sa. Tasleem sun je asibiti anyi treating raunukan da taji, Tun a mota ta fara baccin wahala, Suna dawowa gida, Daddyn ta ya raka ta d’akin ta, ta kwanta sai bacci.
Bai runtsa ba sai faman juyi yake kan gado, bai san yadda zai shawo kan Tasleem ta fahimta ba, baya son yayi failing d’inta for the second time, ya tsani ta nemi abu a wurin sa, ya kasa cika mata, yana ta sak’en sak’en yadda zai b’ullowa al’amarin. Dare ya tsala sosai, Aunty Jummai ta fito tana waige waige, bayan gida ta nufa, ta hak’a rami ta binne laya da akai ma had’i da naman mujiya da harshen kare, Ta zauna kan ramin na minti talatin kamar yadda boka ya umarta, Fetta a firgice ta farka sakamakon mummunan mafarkin da tayi, addu’o’i tayi, ta mik’e ta shiga toilet, ta d’auro alwala ta fara gabatar da nafilfili. Ta dad’e tana addu’o’in neman tsari da dukkan sharrin mai sharri, da neman kariyar ubangiji, har aka fara kiraye kirayen sallar asuba.+ 10:30am Kiran family Dr d’in su ya tashe sa daga bacci, tunda ya dawo masallaci sallar asuba ya koma, Ya d’auka tare da kangawa a kunne, Suka gaisa yace yana bakin gate, Ya mik’e ya saka jallabiya ya fita. Fetta bacci ta koma wuraren k’arfe bakwai, Suraj ya fara shigowa, yayi tapping d’inta a k’afa, Ta bud’e ido tana mitsitsika su, alamun baccin bai sake ta ba, “Za’a miki allura”, Tayi nodding kai tare da cewa “Ina kwana?”, “Lafiya lau, tashi kisa hijab”, Hijab dake gefenta ta jawo ta saka. Yayi ma Dr iso ya shigo, shi ya rik’e mata hannu aka mata allura, baya son hannun Dr na tab’a jikin ta, Dr mamakin kishi irin na Suraj yake, murmushi kawai yayi, “Ina tunanin gobe ba sai an mata ba, jikinta yayi sauk’i sosai, ta dage da shan magani”, Cewar Dr, Hakan ya mishi dad’i, sam baya son Dr na mata allura, dan ba yadda zai yi ne, Ya masa rakiya har motar sa, ya cika masa aljihu da chanji, Dr nata godiya, yana matuk’ar son aiki da Suraj, dan ba k’aramin alkhairi yake masa ba. B’angaren sa ya koma, yau zai tafi lagos, jirginsa sha biyu na rana, yanzu pass 11, Da sauri yayi wanka ya shirya cikin suit da suka matuk’ar yi mishi kyau, briefcase d’in sa kad’ai ya d’auka, A falo ya samu Hajiya tare da Fetta suna breakfast, ta tilasta mata zama suyi tare, “Mama ina kwana”, “Lafiya lau, tafiyar ta tashi”, “Eh”, ” Toh Allah ya tsare, ya bada sa’a da nasara”, “Amin, ina sauri 12 zamu tashi”, Ta juya kan Fetta “Kije kuyi sallama”, Wane sallama zasu yi, banda tana jin nauyin Hajiya bata ga abunda zai sa ta mik’e ba, D’akin ta taga ya nufa, tabi bayan sa, Yana tsaye ya saka hannaye cikin aljihu, “Da Mama bata ce kizo ba, ba zaki zo muyi sallama ba kenan”, Ta sunkuyar da kai k’asa, “Haka ake wa miji, sam baki san kula da miji ba”, Maganganun sa mamaki suka bata, ta kasa furta komai, Ya d’age kafad’a yace “Anyway am travelling, if you need anything you call me”, Ya ajiye mata bandir na 500, Ya juya zai fita, Murya a sanyaye tace “Allah ya tsare ya bada sa’a da nasara”, Ya juyo ya kai dubansa gare ta, Ya amsa da “Amin, you take care”, Ya fice. Mimi ta fara kuka alamun tashi daga bacci, ta d’auketa tana jijjigawa, tare da tofa mata addu’o’i.
Tasleem ta tashi jikinta duk yayi tsami, wanka tayi ta zura doguwar riga, ta fito main falo na gidan, Alhaji Tambari ya fito da shirin sa na zuwa office, Lauratu ta rako sa a baya, “Daddy ina kwana?”, “Lafiya lau, ya jikin naki?”, “Da sauk’i”, “Mummy ina kwana?”, “Lafiya lau”, “Daddy maganar mu ta jiya”, Ya sauke ajiyar zuciya ya kamata hannun ta, ya zaunar da ita kan kujera, shima ya zauna, “Ina so ki saurare ni kuma ki fahimce ni”, Tayi nodding kai, “Suraj da kike gani ba k’aramin mutum bane, hukunta shi zai iya jawo ruining reputation d’ina, ni dan’ siyasa bana son abunda zai tab’a political career d’ina, Am sorry my daughter, kiyi hak’uri”, Ya fad’a yana murza hannun ta, K’ulloton bak’in ciki ya tsaya mata a mak’oshi da k’yar ta iya furta “Ok Daddy na fahimta”, “Yawwa yar’ albarka, idan na dawo i have something special for you”, Ta d’aga kai, “Kiyi murmushi”, Tayi faking smile, “Sai na dawo”, Ya fad’a yana mik’ewa, nauyin dake k’irjinshi ya rage sosai, atleast yayi convincing d’in ta, duk da yana jin takaici na rashin hukunta Suraj. STORY CONTINUES BELOW Bello ya gaji da rashin matar shi a kusa dashi, ga ayyukan da ya baro can, A falo ya samu Kawu Lamid’o tare da Gwaggo suna cin abinci, Ya durk’usa ya gaishe su cike da ladabi, suka amsa, “Abba dama wurin aiki ne suke nema na, nayi ta basu excuses, sunce idan ban koma gobe ba zan rasa aikina”, Kawu Lamid’o sai da ya kai lomar shinkafa baki yace “Kai kuma abun nema ya samu ko, matar dan’ boko ta haifi biro kana neman hanyar guduwa, toh bara kaji wallahi ko birnin sin ka tafi dole kayi auri”, Gwaggo tace “Wai ni ya maganar Tasleem ne”, Cikin sanyin murya yace “Wallahi Gwaggo tak’i ni, ta nuna bata ra’ayi na”, Kawu Lamid’o ya nisa yace “Tashi ka tafi nasan maganin ka”, Bello ya mik’e cike da farin ciki bai hana sa tafiya ba. Yelwa rashin yar’ ta yasa gaba d’aya ta canza, Kawu Sule baya ganin wani far’ar ta, Abinci ma sai taga dama take masa, Yau ma ya shigo gida a gajiye ga yunwa, ya sameta zaune tsakar gida, tana wanki, “Sannu da zuwa” Ta fad’a ba yabo ba fallasa, “Yawwa, zo ki bani abinci yunwa sosai nake ji”, “Ban girka ba, lafiya bata isheni ba”, A fusace yace “Me kike nufi da lafiya bata ishe ki ba, wanki fah kike yi”, Tace “Uhmm”, tare da juya mishi k’eya, “Rashin mutunci ya fara isa ta Yelwa, wallahi zan mummunan sab’a miki”, Bata tanka shi an sai ma wankin ta data cigaba hankali kwance, Ya gama fad’ace fad’acen shi, ya fita a fusace, Tabi bayan sa da harara “Ka gama ganin yadda kake so, tunda ka rabani da ya’ta” Suraj ya tarar da harkokin sa na lagos sunyi k’asa sosai, Kamfanin sa na motoci ya rasa kusan 10 million, Ma’aikatan wurin gaba d’aya ya tara, “Kuna aikin me haka ta fara, bunch of fools and idiots na tara kenan, wallahi wallahi wallahi this should be the last time haka zata faru ko dukkan ku nayi firing d’in ku”, Ya fad’a a tsawace tare da buga teburin dake gaban shi, Jiki na b’ari suka shiga bashi hak’uri, “Ku b’ace mun useless human beings” Ya fad’a cikin karaji, rige rigen fita su shiga yi, Ya dafe kai cike da takaici, ya zama dole ya zauna lagos yayi clearing mess da suka yi, hadda rashin sa na tsawon lokaci yasa haka. Hajiya ta kira ta masa hanya, Fetta sam bata kira ba, wanda hakan ya k’ular dashi, a da bai damu da kiran ta ba, amma yanzu bai san meyasa ya damu da al’amuran ta.
Fetta kiran sa sam bai zo a tunanin ta ba, harkokin ta kawai take. Karima kamar ko da yaushe, ta gyara gidanta, ta saka turaren ta, tayi wanka, tayi shirin ta cikin atamfa riga da skirt, indomie ta dafa musu suka ci ita da Abdul, ta zauna falo tana kallo, kamar daga sama ta jiyo sallamar Bello, tayi saurin kallon k’ofa, shine a tsaye yana mata murmushi, A guje ta rungume sa, Ya matse ta tsam jikin sa, suna jin natsuwa na saukar musu. Fetta saura sati d’aya tayi arba’in, Hajiya tace taje gidansu tayi satin d’ayan, amma ta kira Suraj ta sanar dashi, Taji dad’i sosai tana son kasancewa tare dasu Aliya, ga bikin Su’ad ya gabato dama bata son hayaniya. Waya ce rik’e a hannuj ta, tana tunanin kiran sa bata san me zata fara ce masa ba, kusan minti ashirin tana haka, Ta dake tayi dialing number sa da ta ma saving da Abban Mimi, Suraj na zaune falo yana shan yoghurt yana duba wasu takardu, kiranta ya shigo, Yayi mamakin ganin kiran, lokaci d’aya yaji zuciyar sa tayi sanyi, Yayi picking, “Assalamu Alaikum”, Ta fad’a cikin sanyin murya, “Wa alaikissalam”, “Ina wuni?”, “Lafiya lau”, “Ya aiki?”, “Alhamdulillah, Ya mimi?”, “Lafiya lau”, Ta d’an yi jim kafin tace “Uhmm wai dama Hajiya ce tace na kira na gaya maka zanje gida nayi sati d’aya”, “Shine dalilin da yasa kika kirani?”, “Eh”, Ya kashe wayar tare da jan tsaki ya jefar gefe, Wayar tabi da kallo, tana mamakin saurin kashewar sa, wulak’ancin sa da take gudu shiyasa sam bata son kiran sa, Ta tab’e baki, Ta ajiye wayar, ta shiga had’a kayanta da na Mimi. Da daddare driver ya kai su, Hajiya ta cika su da sha tara na arzik’i ta kaiwa su Mallam, tayi mata godiya sosai. Aliya da Mallam sunyi farin cikin ganin Fetta zata musu sati, Hajar da Aliyu nata tsallen murna, Mallam yace “Yau sai ki bar mana d’aki ni da sabuwar Amarya”, Ya lakaci kumatun Mimi, Aliya tace “Gaka gata ni bana kishi”, Sukayi dariya gaba d’aya, Suna tsakar gida suna hira har sha biyun dare, kowa ya nufi makwanci. Washegari ta kama laraba, ranar za’a fara bikin Su’ad, za’ayi kamu a meena event centre, Amarya Su’ad taci ado ta cakare, Feena ma an k’ure a daka, Fetta tayi shirin ta cikin anko atamfa, d’inkin ya mata kyau, tayi kyau sosai, Hajiya ta aiko driver yazo ya d’auketa ya kai ta, a gida ta bar Mimi wurin Aliya, bata rigima da na bata madara shikenan. K’ofar shiga taci karo da Bilkisu, tasha uban make up, d’inkin ta ya matse ta sosai, ga high hill, tana cin chingum kamar tsohuwar karuwa, Wani banzan kallo ta watsa ma Fetta tare da bangaje ta, Hannu Fetta tasa ta jawo ta, “Bakya gani ne”, “Kutumar ke a suwa da zaki jawoni haka”, Kallon da Fetta ta jefa mata yasa taji ta mata kwarjini, Tsaki taja ta wuce, Fetta ta wuce ciki, Kamun yayi kyau sosai, anyi rawa an chashe anci abinci an k’oshi, mutane na fara watsewa, Fetta ta koma gida. “Umma wai kinsan banzar yarinyar nan dan na bangaje ta, ta jawoni tana gaya mun maganar banza”, Bilkisu ta fad’a a k’ufule, Aunty Jummai tayi k’wafa tace “K’iris ya rage ki zuba ido kiyi kallo”, Fetta ta kawo mata wuya ji take tamkar ta shak’eta sai ta shura lahira, wannan karon tana ji a jikinta aikinsu zai yi tasiri.
Anyi saurin bukukuwa duka Fetta ta hallara, Ranar asabar k’arfe 11 aka d’aura aure wanda mutane da dama suka halarta, Suraj ma ya samu halarta. Fetta na cikin gida, zaune wuri d’aya tana danna wayar ta, mutane nata shige da fice, Aliya tazo yinin biki, Mimi na bayanta ta goya. K’amshin turaren sa da taji, yasa ta d’ago kai ta zube ido a kan sa, Sanye yake cikin sharar shadda da babbar riga da tasha aiki, Ya matuk’ar yi kyau, kai kace shine ango, Fetta kasa d’auke ido tayi daga kallon sa, bata tab’a ganin kyan sa irin yau ba, Rank’wafo da kai yayi saitin fuskarta, har suna jiyo numfashin juna, “Ya dai na miki kyau ne”, Ya fad’a yana d’aga mata gira tare da hura mata iskar bakin sa, Kusan shid’ewa tayi tana jin wani abu ya tsirga tun daga tafin k’afarta zuwa kan ta, Tayi saurin rufe ido. Murmushi yayi yaja da baya, “Ina Mimi?”, Ta bud’e ido tana sunkuyar da kai k’asa tace “Tana wurin Umma”, Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya juya ya fice, Ta sauke ajiyar zuciya tana danna kiran Yasmeen, bugu d’aya ta d’auka, “Hello ban ganki ba tun d’azu”, “School na tsaya but gani nan zuwa yanzu”, “Sai kin zo”, “Ok”, Tayi hanging up.+ Bayan sallar la’asar aka tafi kai Amarya kaduna, Fetta gida ta koma, Yasmeen itama ta wuce. Fetta tun zuwan ta, Aliya ke ta faman bata abubuwan gyaran jiki, Yau ma wani had’i ne ta bata, tace ta kafa kai ta shanye, rai bai so ba ta karb’a tasha. An kai Amarya gidan ta dake unguwar Malali, Yayi kyau matuk’a, Yan ki Amarya sun dawo suna fad’in tsaruwar gidan, Feena ta dawo cike da kewar yar’uwar ta, rana ta farko da suka tab’a rabuwa, aure kenan mai raba ka da iyayen ka da yan uwa, ya kai ka wata sabuwar duniya. Su’ad har d’ayan dare bata ji shigowar Adnan ba, hankalin ta ya fara tashi, tana tunanin ko lafiya, Wayar ta ta lalubo da niyyar kiran sa, taji shigowar sa, Mayafin ta taja ta sake rufe fuskar ta, “Meye na rufe fuska, kamar dai bak’on gani”, Ya fad’a yana dariya, tare da janye mayafin ya cillar gefe, Ta d’ago ido tana kallon sa, “Ina ka tsaya ne tun d’azu”, “Wallahi friend’s house”, Ta b’ata rai “Haba baby yau fah aka kawo maka Amarya, kowane ango d’okin zuwa yake wurin amarya sa amma kai wai gidan aboki”, “Ke ai daban kike da sauran Amare, sune d’okin first night ni kuwa na riga na karb’i nawa”, Maganar sa ba k’aramin b’ata mata rai yayi ba, Ta dake tana kawar da kai gefe, “Bacci nake ji”, Ya fad’a yana tub’e kayansa, ruwa ya watsa, ya saka pyjamas yabi lafiyar gado.
Mamaki, bak’in ciki da takaici ne suka taro suka dababaiyeta lokaci d’aya, ko kazar amare bata samu arzik’in ya shigo mata dashi, tarairayar Amarya da ake babu, kwanciyar sa ma yayi, Shi haka tasa rayuwar yake, Haka ta mik’e rai ba dad’i, tayi wanka ta saka rigar bacci, ta kwanta gefen sa. Suraj ya zama very busy, kullum baya dawowa gida sai 3 na dare, harkokin sa yake son daidaita wa, Ya shigo gida a gajiye lik’is, ruwa ya watsa yabi lafiyar gado, sai dai me bacci ya k’auracewa idon sa, tunanin Fetta ke zuwan masa, Ya rasa meke damun sa kwana biyu, anya lafiyar sa k’alau kuwa, meke shirin faruwa dashi?, Ya jerowa kansa tambayoyin da babu mai bashi amsa ba. Fetta ta farka a tsorace, duk ta had’a gumi, sunan Allah ta shiga ambato, kwanakin nan ta kan yi mummunan mafarkai, Karatun Qur’ani ta kunna a wayar ta, tana saurara tana jin natsuwa, har bacci ya sake d’auke ta. Tasleem Daddynta sabuwar mota dal a bata wacce a k’alla zata yi miliyan biyar, Tayi murna sosai kuma ta nuna masa jin dad’in ta, wanda hakan yasa ya k’ara samun natsuwa, Tasleem bata da wani abu da zata k’ara yi akan Suraj, tana tsoron kashedin da ya mata, mahaifinta ne hope d’in ta shima yace ba zai iya ba, babu yadda ta iya, zuciyarta cunkushe take da tsananin k’aunar sa, tasan da soyayyar sa zata mutu. Zaune yake a office na gidan gonar sa, yana duba takarda mai d’auke da sunaye, Ya kai kan sunan Alhaji Badamasi yaja jan biro, Ya cije lips d’in shi na k’asa, yana jujjuya biro, Turo k’ofar da aka yi, yasa shi kallon k’ofar, sam ya manta ya saka key, “Wa nake gani kamar Munir, dama kana duniyar nan”, “SS manyan gari”, Ya fad’a yana k’arasuwa ciki yaja kujera ya zauna, ya cigaba da cewa “Wallahi baka da kirki, gaba d’aya ka watsar dani, ko sau nawa zan kira ka bara ka d’aga waya ba”, “Abubuwa ne suka yi yawa”, “Hmm so ya harkoki?”, “Alhamdulillah fah, yaushe ka dawo garin?”, “Jiya kasan this week bikina”, “Wow Allah ya sanya alkhairi”, “Amin zamu koma can uganda tare”, “Am happy for you”, Cewar Suraj yana murmushi, Sun tab’a hira kafin ya wuce. STORY CONTINUES BELOW Rumaisa ce zai aura k’awar Fetta, tun lokacin suke zuba soyayya. Fetta ta cika sati d’aya a gida, Bayan sallar isha’i tayi shirin ta tsaf na komawa, Driver na bakin gate na jiran ta, Mallam da Aliya suka sake mata nasiha, tare da addu’o’in zaman lafiya tsakanin ta da Mijin ta, Taji tamkar kar ta tafi, sam bata son rabuwa dasu, sun zame mata wani b’angare na rayuwar ta, Har mota suka mata rakiya, driver yaja cikin minti 5 suka kawo gida, B’angaren Suraj taga an nufa da kayan ta, bata yi magana ba, ta nufi b’angaren Hajiya, A falo ta same ta, Samee na kwance kan cinyar ta tana zuba shagwab’a, Ta durk’usa har k’asa ta gaishe ta, Ta amsa da sakin fuska, “Fetta an dawo”, “Eh”, “Ya kika baro su Aliya?”, “Lafiya lau suna gaishe ku”, “Muna amsawa, sai ki koma b’angaren mijin ki tunda kinyi arba’in”, Hakanan ta tsinci kanta da fad’uwar gaba, Tace “Toh”, Tana mik’ewa, Da sallama ta shiga falon, yana kwance daga shi sai singlet da boxer, Ya amsa sallamar, ya d’ago kai ya kalle ta, Hannu ya mik’a mata alamar ta basa Mimi, ta mik’a masa ita, Ta shiga d’aki, D’ayan d’akin Hajiya ta bud’e an zuba kayan Mimi ciki, Toilet ta shiga ta watsa ruwa, ta saka rigar bacci iya gwiwa, ta fesa turaruka masu sanyin k’amshi, dogon hijab ta saka, ta kwanta kan gado, ta runtse ido tamkar mai bacci,
Jin ta shiru, ya shiga d’akin d’auke da Mimi a kafad’ar sa tana bacci, gefen gado ya shimfid’e ta, Ya zubawa Fetta ido, yana jin wani abu na tsirgar masa, A hankali ya kai hannun sa kan pink lips d’inta ya shafa, taushin su yasa ya kasa d’auke hannun sa, ya shiga zagaye su, Hijabin dake jikinta ya cire, ya saki baki yana kallon kyawawan surar jikin ta, Hannun sa ya kai kan cinyoyin ta masu masifar taushi yana shafawa, daga haka suka lula wata duniya, Fetta ko da farka taga abunda yake mata, bata hana sa ba, sai ma goyon baya da taba sa, Sun raya daren ranar, Fetta taji ta a wata duniya da bata tab’a riskar kanta ba, ji take tamkar yau ya fara kusantar ta, shima hakan yaji ba zai iya misalta yanayin da yaji sa ba. 6:30am Fetta ta fara farkawa, ta kai duban ta gare sa, bacci yake hankali kwance, Ta tsinci kanta ta d’aura hannu saman fuskar sa, ta shafa, Ganin ya motsa tayi saurin janye hannun ta, tana mamakin kanta, “Are u ok?” Ta tambayi kanta, Agogo ta kalla 6:33am, “Ya Allah”, Ta furta tana sauka daga kan gadon, ta shiga toilet, Tayi wankan tsarki, da wankan sabulu, ta d’auro alwala, ta gabatar da sallah, tana jin ba dad’i a ranta na makara, Shiri tayi cikin doguwar riga abaya, tayi light make up, tayi kyau sosai, In less than one hour ta had’a breakfast, noodles da coffee, Ganin kusan 8 bai tashi yayi sallah ba, ta janye bargon da ya rufe a hankali, Ya bud’e ido yana zube su a kanta, wani kyanta yake gani, “Uhmm ka tashi kayi sallah”, “K’arfe nawa?”, Ya tambaya yana mitsittsika ido, “15mins to 8″, Mik’ewa yayi ya shiga toilet, Ta koma falo ta zauna. Kallon da take ya tafi da dukkan tunanin ta har ya shigo falon, bata ji shigowar sa ba, Clapping hannun yayi saitin fuskar ta, ta kallo sa, gira ya d’aga mata, ” Let’s have breakfast”, Ya fad’a yana nufar dining area, ba musu tabi bayan sa, a tare sukayi breakfast, Suna satar kallon juna, da sun had’a ido, Fetta tayi saurin kawar da kai, shi kuwa ko gezau baya yi, Ya riga ta cinyewa, Yace “You make sure ki cinye tas, zan fita”, Ta had’iye abincin dake bakin ta, tace “Allah ya bada sa’a”, Ya amsa da “Amin” Kawu Lamid’o ya shigo gida yana washe baki, kallo d’aya zaka masa kasan yana cikin farin ciki, Gwaggo dake zaune tsakar gida tare da autan ta Khalil, Tace “Wannan far’a mai gadi, kamar an maka albishir da kujerar wanka”, “Ai wannan yafi kujerar makka”, “Meke faruwa?”, “Na samu Alhaji Tambari na nuna masa Bello yaga Tasleem yana so, babu wani ja ya amince, itama ya kira ta a gabana ta nuna amincewar ta”, Gwaggo ta washe baki tace “Kai Alhamdulillah na matuk’ar ji dad’i, dole na taka”, Ta shiga rawa tana juyi. Alhaji Tambari ya amince ne a ganin sa hakan zai sa Tasleem ta manta da Suraj, itama ta amince ne dan ta rage ma kanta danuwar rashin Suraj, tasan bara ta tab’a samun sa ba, ko banza Bello nada kyau, zata lallab’a dashi. *Bayan sati d’aya* Wata shak’uwa mai k’arfi ta sake shiga tsakanin Suraj da Fetta, yadda yake mata wani lokaci ba k’aramin mamakin sa take ba, itama tana mamakin kanta yadda yanzu ta damu da al’amuran sa, Zaune suke falo, ya mik’e k’afa tana masa tausa kamar yadda ya buk’ata, Har lumshe ido yake saboda dad’in tausar, Sallamar Yasmeen ya sata tsayawa, Ta tashi ta bud’e k’ofa, “Amar…..” Bata k’arasa ba ganin Suraj zaune, ta gaishe sa, ta wuce d’akin da kayan Mimi suke, Yarinyar na kwance na bacci abun ta, “Iyayenki sun bar ki, suna can suna shan soyayya abun su”, Ta fad’a tana murmushi, Tabi bayan Yasmeen, Yace “Dawo ki cigaba, ko nace ki tafi”, Zatayi magana ya katse ta, dan dole ta cigaba da mishi tausar, Kuka Mimi ta tsala, Yasmeen sai da ta tsorata da irin kukan, a tsorace ta d’auketa ta nufa falo, Fetta kawaici ya hanata mik’a hannu ta d’auketa, Suraj ne ya mik’a hannu, Yasmeen ta idonta ya kai kan hannun sa, tabon da ta gani yasa gabanta mummunan fad’uwa, har abada ba zata tab’a manta hannun nan ba, Yana karb’ar Mimi, tayi baya da sauri, kanta ke juyawa, jiri na d’ibar ta.