FETTA CHAPTER 29

FETTA CHAPTER 29

  *Mano Dayak International airport Agadez, Nijar*+ Jirgin su Suraj yayi landing, Zuciyar sa tayi sanyi yana bin airport d’in da kallo, karon farko na zuwan sa k’asar Nijar duk yawace-yawacen sa bai tab’a zuwa ba, babu b’ata lokaci ya d’auki taxi drop zuwa masarautar Agadez, garin yake bi da kallo, tsarin sa ya burge sa, yayin da yake jin nishad’i cikin mintuna kad’an zai had’u da muradin ran sa, Matsayar yan taxi a masarautar driver ya ajiye sa, ya sallame shi ya tafi, Masarautar yake bi da kallo yana ganin tsananin girman ta da tsaruwa, “Fetta sam bata yi kalar gidan sarauta ba, hasalima mahaifinta mai gadi ne, ko shakka babu k’ila bayi ne a cikin masarautar” Zuciyar sa ta fad’a masa, Waige-waige ya shiga ko Allah zai had’a shi da wani ya tambaye sa, “Amma bayi ba kowa ne ya san su ba, kasancewar suna da yawa, ko ya tambayi Fetta ba lallai a ganeta ba” , Wani b’angare na zuciyar sa ya fad’a. Yana tsaye a wurin kusan minti ashirin, ya hango wasu tafe, wanda da dukkan alamu bayi ne, Sallama ya musu, Suka amsa, Yace “Dan Allah ko kunsan Fetta?”, Murmushi d’aya daga cikin su yayi yace “A masarautar nan waye bai san Fetta ba, ba wacce ta dawo kwanaki ba”, Suraj ya d’aga kai yace “Eh ita”, “Ai kowa a masarautar nan yasan Fetta” Cewar d’ayan su, Mamaki Suraj yake tana baiwa kuma kowa ya santa, ko suna nufin a cikin bayi yan’ uwan su, Ya katse tunanin sa da cewa “Ko zaku kaini wurin ta”, A tare suka kama baki suka ce “Rufa mana asiri bama shiga b’angaren amma zamu maka kwatance” Wani mamaki ne ya sake cika sa, “Ummaru ce jeka nuna masa” D’ayan su ya umarci k’aramin cikin su, Yana gaba yana biye dashi a baya, Sunyi tafiya mai nisa kafin su kawo, Suraj k’afafun sa har sun soma masa ciwo, yana jin bai tab’a tafiya mai nisan ta ba, “Ga b’angaren da zaka same ta”, Ya fad’a yana nuna masa sashen Azagas, “Nagode” Ya fad’a yana bin sashen da kallo, kai tsaye ya shiga sai dai ya rasa wacce hanya zai bi da sada zata shi da Fetta wacce yake kyautata zaton baiwa ce a b’angaren. *Diori Hamani International airport Niamey, Nijar.* Jirgin su Fetta yayi landing, Driver da yan’ sanda guda biyu na jiranta a harabar filin jirgin, ba tare da b’ata lokaci ba dan’ sanda ya bud’e mota k’ofa ta shiga ya rufe, Driver yaja mota. Cike da murna Mummy da mutanen gidan suka tarbe ta, Amra na karb’e Mimi hannun ta, masu aiki suka shiga da kayanta d’aki na musamman da aka ware mata na saukar ta a duk lokacin da zata zo, Kan ace me an dabaibayeta da abinci kala kala, taci sosai kasancewar ta d’ebo yunwa, Ruwa taji tana buk’atar watsawa, Ta nufi d’aki, Cikin minti 30 ta watsa ruwa, ta saka doguwar riga mara nauyi wacce ta zauna d’ass a jikinta ta mata kyau sosai, Ta kira Azagas ta sanar da ita isowar nasu, ta dawo falo ta zauna suna hira da jama’ar gidan. “Kai me kake a nan?, waye kai?” Cewar wani dogari da yaren buzaye, Suraj ido ya shiga rabawa kasancewar bai gane me ya fad’a ba, “Baka ji bane ko sai nasa sanda na make ka” Ya d’aga sanda alamun zai buga masa, Suraj yayi saurin cewa “Bak’o ne bana jin yaren ku”, Shima buzun baya jin hausa, dan haka ya cakumo rigar Suraj zai fitar dashi, Sanah ta fito sashen Azagas, “Kai meye haka, waye ka rik’e?” Ta fad’a da yaren buzaye, Cike da girmamawa duk da kasancewar ta yarinya yace “Ban san shi ba daga gani ba buzu bane, na ganshi yana waige waige k’ila b’arawo ne”, “Sake shi” Ta fad’a tana kai dubanta ga Suraj wanda ya ransa ya kai k’ololuwa wurin b’aci, ba’a tab’a wulak’anta sa irin yau ba, “Me kake anan? Ko kayi b’atan hanya ne” Cewar Sanah da hausar ta da bata fita sosai, “A’ah, Ina neman wata ce”, “Ya Sunan ta?”, “Fetta”, Ta jinjina kai tana k’are masa kallo, kamanin sa da Mimi ta hango wanda take kyautata zaton dan’uwan mijin Fetta ne, Ta juya kan dogarin tace “Ka dinga sanin kan aikin ka, ba kawai ka kama mutum ba, ba tare da sanin waye ba”, “Ayi hak’uri ranki ya dad’e”, “Muje ciki” Tacewa Suraj, yabi bayan ta. STORY CONTINUES BELOW Babban falon Azagas tace ya zauna ta shiga ciki, Suraj falon yake bi da kallo duk shige-shigen sa gidan sarauta, bai tab’a zuwa wanda ya kai had’uwa da tsaruwar wannan ba, kayan alatun dake zagaye falon zai tabbatar maka ba k’aramin dukiya suka tara ba, Royal chairs kad’ai dake falon abun kallo ne, ga sanyin Ac had’i da k’amshi ta ko’ina na bugawa, “Wannan falo shi ake kira da aljannar duniya” Ya fad’a yana k’ara bin ko’ina da kallo, Shigowar Azagas tare da Sanah ya katse masa tunani, Daga tufafin jikinta zai tabbatar maka tana da matsayi mai girma a masarautar, zinarin da tayi ado dasu yake bi da kallo, A rayuwar sa bai tab’a ganin zinari mai girma da kyawon sa ba, bai zata anan kusa akwai wanda zai iya ado da zinari haka ba, “Kaine mai neman Fetta” Muryarta ta katse masa tunani, Cikin k’ask’antar da kai yace “Barka da warhaka”, karon farko a rayuwar sa tun bayan da ya mallaki dukiya, yaji wata ta masa kwarjinin da zai iya k’ask’antar da kansa a gabanta, “Barka kadai” Ta amsa da sakin fuska, “Ya gajiyar hanya?”, “Alhamdulillah”, “Kana da alak’a ne da Fetta?” Ta jefo masa tambayar da yake ganin kamar duk duniya a yanzu babu wanda ya kaisa alak’a da ita, “Eh ni mijin ta ne” Da kallon mamaki tabi sa tace “A sanin mu mijin Fetta ya rasu, ko kana nufin k’anin mijin ta”, Kalmar ya rasu ta daki k’irjin sa, hakan na nufin Fetta ce musu tayi ya rasu, a yanzu bashi da wata hujja nacewa shi mijinta ne ko ya fad’a ba lallai su yarda dashi ba, idan ma sun yarda zasu so jin dalilin da yasa ta barsa, Ya numfasa yace “Ina nufin k’anin Mijin ta”, Da murmushi d’auke a fuskar ta tace “ko dai kana so ka maye gurbin dan’ uwan naka”, Shafa k’eyar sa yayi tamkar mai jin kunya, Azagas tace “Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairi”, Ya amsa da “Amin”, “Fetta ta tafi Niamey yau wurin dangin mahaifiyarta biki kuma zata kwana biyu” K’irjinsa yaji ya masifar doka, duk wani kuzarin sa ya katse, Azagas ta lura da yanayin sa tace “Idan ba zaka iya jiran dawowar ta ba sai ka sameta a can”, Sai a lokacin yaji natsuwa ta saukar masa, but yana son sanin alak’ar matar da Fetta, sai dai kuma bai san ya zai tambaye ta ba, ya barwa zuciyar sa baiwa ce dake musu hidima, duba da dukiya irin tasu babu ta yadda Fetta zata zama jinin su. “Fetta ki fito ga mai k’unshi tazo, Mummy tace ke za’a fara yi wa” Cewar Amra, Tayi murmushi tana mik’ewa ta nufi wani sashen a gida, Mummy na zaune tare da yan’ matan kusan su biyar, D’ayar su wacce yar’ kanin Daddy ce tace “Fetta yar’ gata zo ki zauna a miki, ko Mummy ta bari muma a mana”, Mummy tace “Kuyi dai ku gama, sai an mata za’ayi ma ni kaina” Ta juya kan mai k’unshin tace “Ki mata yafi na kowa kyau, ina so ta fito tamkar Amarya” , “Ahh lallai zamu ga yadda zata fi Amarya kyau” Suka fad’a suna dariya, Fetta ma dariya tayi tana zama, aka fara tsantsara mata jan k’unshi. Suraj abinci kala kala aka dabaibaye sa dashi, bai wani ci sosai ba, hankalin sa ya tafi kan son had’uwa da Fetta, a ranar yaso zuwa garin Niamey, Azagas ta buk’aci ya bari washegari idan ya had’u da Amanukal, bai so haka ba, but ba zai iya mata musu ba, yana kuma mamakin yadda a masarautar suke ba bayi muhimmanci da har za’a ce sai a sanar da Sarki. Masauki lafiyayye aka basa wanda zaka rantse na saukar gwamna ne, bai samu damar runtsawa ba, alla alla yake gari ya waye, Karin kumallo mai rai da lafiya aka kawo masa, ruwan shayi kad’ai yasha, Yayi wanka ya shirya, yana jiran kiran Azagas, 8:30 na safe Ta aiko kiran nasa, Cike da ladabi ya gaisheta, ta amsa da sakin fuska, Shigarta ta yau ta sake girgiza shi, zinari da tayi ado dashi ba shine na jiya ba, Haka yayi ta mamaki dukiya irin tasu, Mamakin sa bai k’aru ba sai da ya shiga sashen Amanukal, anan yaga na Azagas ba komai ba ne, Ya samu tarba mai kyau daga wurin Amanukal, ya umarci a kai sa airport na garin, Mota jeep prado da dogarai suka tafi kai sa, a ransa yana yaba karamci irin nasu, hatta da ticket siyan mishi suka yi, bai tab’a ganin mutane irinsu da suka san darajar dan’ adam ba, ko yawan dukiyar tasu ta saka basa jin k’yashin fitar da kud’i, duba da abinci da ya samu zuwa ga masauki, Da tunani birjik a ransa a suka kai airport ne, babu b’ata lokaci jirginsu ya lula sararin samaniya. Fetta tana tsaye gaban madubi tana k’ara gyara kwalliyar ta, shiga tayi cikin shadda mai masifar kyau da tsada, tasha d’inki irin na nijar wanda yayi masifar kyau, daga kunnenta, wuyanta zuwa hannayen ta duka sanyen da zinari mai tsananin kyau, Gashin kanta yaja gyara, jelar gashin da aka kitse ta fito zuwa gadon bayan ta, ta gaba gashin ya kwanta luf, ba k’aramin kyau tayi ba, K’unshin ta ya k’ara haskata zaka rantse da Allah itace Amarya, Turaruka kusan kala biyar ta fesa, ga jikinta dake fitar da sihirtaccen k’amshi na humra wanda ya kama jikin ta, tun zuwanta nijar take amfani dashi, Ta zauna bakin gado tana latsa wayar ta, tana jiram sauran da zasu tafi tare su gama shiryawa. Suraj yana isowa, driver daga gidansu Mummy yazo d’aukar sa, wanda Azagas ce ta kira ta sanar da zuwan sa, Mamaki tsantsa ya cika sa ganin gidan da suka nufa, “Meye kuma had’in Fetta da wannan gida?”, Masaukin bak’i aka kaisa, wanda zaka rantse da Allah a gidan wani hamshak’in mai kud’i kake k’asar waje, masu aiki suka shiga kawo masa abun motsa baki, mamaki ya hana sa shan ko ruwa, babban burin sa ya saka Fetta a ido, Wani matashin saurayi ne ya shigo, wanda yake kyautata zaton yaron gidan ne, ya basa hannu suka gaisa, Ya masa sannu da zuwa, tare da ce masa Fetta na zuwa, ya amsa da “Toh” yana jin fad’uwar gaba, sai a yanzu yake jin fargaba da zullumin wacce tarba zai samu daga gareta, ko zata sauraren sa, Zuciyar sa yaji ta karaya, yayin da rauni ya lullub’e sa.Sallamar Sajida autar Mummy yasa ta d’ago kai ta kalli k’ofa, “Wai kizo kin yi bak’o” Cewar Sajida, “Bak’o kuma” Ta fad’a cike da mamaki, “Eh yana falon bak’i”, Ta amsa da “Toh” tana mik’ewa, cike da mamakin wane bak’o ne ta nufi falon bak’in, a saninta bata yi da kowa zai zo wurin ta ba.+ A hankali ta murd’a k’ofar falon ta shiga, Suraj wanda yayi nisa a tunani da zullumi jin bud’ewar k’ofa, ya d’ago kai ya kalli k’ofar, idonsu suka sark’e cikin na juna, K’irjin Fetta ya duka da tsananin k’arfi, tayi saurin kawar da kanta gefe, yayin da Suraj yake ganin tamkar Nurul ayn ce a gaban sa, tsananin kyau yaga ta k’ara kamar ba Fettan da ya sani ba, zuciyarsa na harbawa tamkar zata fasa k’irjin sa ta fito, wani sabon yanayi yake ji game da ita da ba zai fassarawa ba, shigar ta kad’ai ta tabbatar masa tana cikin daula, haka ko shakka babu tana da alak’a da Masarautar Agadez, “Me ya kawo ka?, waya sanar da kai inda nake? Me kazo yi?” Tambayoyin ta suka sauka a kunnen sa, Duk wani kuzarin sa ya katse, ya rasa da wacce kalma zai fara, Cikin rawar murya yace “F…a…t….”, Ta katse ta tana d’aga hannu “Kaga tashi ka tafi, tuni na dad’e da goge ka cikin tarihin rayuwata, wallahi da nasan kaine bazan zo ba, bana son sake saka a idona”, Suraj wanda hankalin sa ya soma tashi da jin furucin ta yace “A shirye nake na karb’i duk wani hukunci da zaki yanke a kaina, amma Dan Allah ki dawo gareni”, Murmushin takaici tayi tana ganin zancen sa kamar almara tace “Kana tunanin zan koma na cigaba da rayuwa cikin k’azamtacciyar rayuwar ka, kayi kuskure Suraj, duk wata alak’a dake tsakanina da kai na yanke ta daga ranar da na bar gidan ka”, “Baki yanke ba Fetta, wallahi akwai alak’a mai k’arfi tsakanin mu ko kin manta akwai Mimi wacce jinina da naki ke yawo a jikin ta” Ya fad’a tamkar zautacce, “Ina ma zan iya kwashe jininka dake yawo a jikin ta, sam bata dace da Mahaifi irin ka ba”, A raunane yace “Nasan babu yaron da zai yi alfahari da uba irina, nasan rayuwata k’azama ce, ban tab’a zaton haka zata kasance da ban fad’a fashi da makami ba”, “Please ka fita rayuwar mu Suraj, ka tafi kada ka sake dawowa, ka manta ka tab’a sanina a tarihin rayuwar ka, ka manta kana da ya’ mai suna Zainab”, Ta fad’a tana nufar hanyar ficewa, Da sauri yasha gabanta yana fad’in “Bazan iya ba Fatima, wallahi ba zan iya ba, rashin ki a rayuwata daidai yake da rasa raina, zuciyata ta kamu da azabtaccen sonki, duk wani numfashina yana fita ne tare da son ki”, Da kallon mamaki tabi sa tare da yin murmushin takaici tace “Shin ka manta wacece a gaban ka, idan ka manta bari na tuna maka Fetta yar’ mai gadi mara asali, matsiyaciya ko ka manta kalaman ka a gareni lokacin da Hajiya ta had’a auren mu”, Ta sauke ajiyar zuciya tana jin zafi da d’aci a ranta na tuna kalaman sa tace “Bari na tuna maka *AM NOT UR TYPE, SURAJ BA AJIN MACE IRIN KI BANE, BAZAN TAB’A SONKI BA, KO NACE INA SONKI K’ARYA NE*”, Zufa ta shiga tsattsafu masa duk da sanyin Ac dake falon, bai tab’a zaton zai kamu da sonta ba, da bai furta kalaman gareta ba, ina ma zai iya mayar da hannun agogo, nadamar furucin tsantsa a k’wayar idonsa yake kallon ta, cikin sark’ewar murya ya bud’e baki zai yi magana, tayi saurin tare numfashin sa, “A yanzu da kasan Fetta ba yar mai gadi bace, tana da asali kuma ba matsiciya bace kake sona, ko kuwa a yanzu da nasan wanene kai zaka ce kana Sona, har abada bazan yarda da kai ba Suraj”, “Wallahi ina sonki Fetta, pls ki fahimce ni”, “Kalmar sonka tamkar sokar kibiya nake ji a zuciyata, ina rok’on ka da Allah ka fita rayuwata” Ta fad’a tana had’a hannayen ta biyu, “Nasan ni mai laifi ne a wurin ki, ki yafe mun Fatima, ina nadamar kasancewata d’aya daga cikin yan fashin da suka kashe mahaifin ki, ban tab’a kisan kai, ina nadamar daren ranar, ina ji tamkar na goge sa a cikin tarihin rayuwata” STORY CONTINUES BELOW Ya fama mata tabon da yake k’ok’arin b’acewa cikin zuciyar sa, Cikin d’aga murya tace “Ka fita ko wallahi ka tsinci kanka a gidan yari”, “A shirye nake Fatima in dai hakan zai sa ki yafe mun, ki dawo gareni”, “Ya Rabbi” Ta furta tana dafe kanta dake tsananin sara mata, kujerar kusa da ita ta zauna, tana runtse idonta, zuciyarta na dokawa, da tana da k’arfi ba abunda zai hana taja Suraj ta fitar dashi, ganin sa ya tado mata raunukan dake k’ok’arin warkewa a cikin zuciyar ta. Suraj bai k’ara gaskata ya kamu da masifaffan son Fetta ba, sai a yau da yake ganin ta gaban sa, bai san rad’ad’in so ba, sai yau da wacce yake tsananin k’auna bata son ganin sa, kallon ta yake yana jin k’aunarta na yawo cikin jinin jikin sa, yana jin tamkar ya rungumeta ko zai samu sassauci a zuciyar sa, nadamar sakinta ke lullub’e sa, ya rasa wane ganganci ya kaisa ga rubuta mata saki, “Zuciya da sharrin shaid’an” Wani b’angare na zuciyar sa ya fad’a. Su’ad na zaune tsakar gida ta rafsa tagumi, cikinta na kukan yunwa, ba komai na kayan abinci a gidan, tunda ya ajiyeta ya fita bata sake saka shi a ido ba, “Me Adnan yake nufi dani?, me na masa ya tsane ni haka bayan soyayyar da yake nuna mun a baya?” Ta jefowa kanta tambayoyin da bata da amsar su, hawaye masu zafi na wanke fuskar ta, Adnan da wak’e wak’e ya shigo, a wulak’ance ya kalle ta yace “Lafiya kika zubo mun ido”, Su’ad waccs tun shigowar sa take kallon sa tace “Yunwa nake ji”, “Taso kici ni, wacce aurenta bai tsinana mun komai ba”, Da kallon mamaki tabi sa tace “Ban gane ba”, Yace “Ke bari kiji abunda baki sani ba, Ni Adnan ba kowa bane, iyayena talakawa ne dake zaune a k’auyen rimin-gado, yawon neman kud’i ya kawo ni garin Kano, ina da son kud’i da nuna ni wani ne, duk motocin da na rik’a zuwa dasu wurinki na gidansu aboki na ne, bani da komai, kayan auren ki da komai bashi naci, gidan da muka zauna dake haya na d’auka na wata d’aya wanda shima kud’in sa bashi ne, auren jari nayi dake, a zatona zan samu mak’udan kud’i, sai dai tunda na aure ki ko naira ban tab’a samu daga dangin ki ba, ban tab’a sonki ba Su’ad, sha’awar ki da kud’in gidan ku nake so, idan kina son zama dani dole ki samu mun nair miliyan goma wajen Yayanki”, Ya fad’a yana d’aga mata gira, ya fice, Hannu ta d’aura a kai, ta fasa ihu mai had’e da kuka, nadama tsantsa ta lullub’eta, Nadamar auren Adnan, nadamar bayar da kanta garesa tun a waje, nadamar kwad’ayi da buri da ta saka ma rayuwar ta, Ina ma mafarki take ta farka, Kuka take babu mai lallashin ta. Kusan minti talatin falon shiru, Suraj da Fetta kowa da abunda zuciyarsa ke sak’a masa, rurin wayarta ya fargar da ita nisan tunanin da tafi, A kasalance ta d’auki wayar ganin Mummy ce “Fetta kina ina, kizo mu tafi”, Ta amsa da “Toh gani nan Mummy” Tana k’ok’arin saita natsuwar ta, Mik’ewa tayi ba tare da ta dubi Suraj ba, tayi hanyar fita, tamkar wanda aka sawa takunkumi ya kasa ko da k’wakk’waran motsi balle yayi yunk’urin hana ta, yabi ta da kallo azabtaciyyar soyayyar ta na rurawa a zuciyar sa. Bata bari kowa ya fuskanci sauyin yanayi a tare da ita ba, bata koma cikin gida ba, ta shiga mota suka tafi, bata son k’ara ko minti biyar a gidan sanin Suraj yana nan, Mintuna kad’an suka isa wurin event d’in, Fetta k’ok’arin cusa kanta cikin mutane ta rik’a yi duk da hakan ba d’abi’ar ta bace, tayi hakane dan kawar ma kanta tunani da damuwa, Tayi nasarar rashin tunani sai dai sam damuwa bata bar zuciyar ta ba, ganin Suraj ya tado mata damuwar da take k’ok’arin binnewa da shafe ta cikin rayuwar ta. Suraj wanda yayi nisa a duniyar tunani, sam bai ji shigowar cleaners ba, a zaton su bak’on ya tafi, suka zo gyara wuri, D’aya ne yace “Sorry maigida mun d’auka ka gama ne”, Kai ya gyad’a musu alamar ba komai, yana k’ok’arin tattaro natsuwar sa, Yace “Wacece Fetta a gidan nan?”, “Jikar gidan nan ce, mamanta nan ne gidan su”, Mamaki ya cika sa ya sake cewa “Meye had’inta da masarautar Agadez?”, “Kakanta mahaifin Babanta shine sarkin Agadez kafin ya rasu, aka ba yayan babanta”, Da k’yar ya iya jinjina kai tsabar mamakin da ya lullub’e sa, bai iya furta komai ba har cleaners d’in suka fita. “Allah mai iko, dan’ hakin da ka raina…., Meye had’in mahaifinta da gadi, yana kyautata zaton wata k’addarar ta gifta hakan ta kasance” Falon ya k’ara kallo yana shaida Fetta yar’ gata ce, yar’ dangi mai cikar asali ba kamar yadda suke mata kallo a baya ba, duk kud’in sa dangin Fetta sun wuce sanin sa, tayi gadon arzik’i ba haye ba, ta kowane fanni ta gaji arzik’i ga sarauta, banda k’addara Fetta ta wuce ajin auren sa, ko shakka babu dan’ babban gida wanda yayi gadon arzik’i ta dace dashi, Jikin sa ya matuk’ar yi sanyi, karon farko a rayuwar sa da yaji karaya da kasawa, ya raina arzik’in sa yaga inda aka wuce tunanin sa, ko a mafarki bai zata Fetta ta fito daga irin ahalin nan ba, a ko da yaushe maganar sa da tunanin sa kud’in sa take so, sai dai kash bai san tafi k’arfin su ba. Tara na dare aka watse taron bikin, Fetta ta karb’i Mimi hannun Amra, kasancewar gida zasu koma, ita kuma ba can zata ba, gidan k’anin mahaifin Daddy zata je, bata son sake ganin Suraj, Amra tace “Ba zaki bari sai gobe ba”, “A’ah gobe bazan samu natsuwar zuwa ba, kinga kuma idan banje ba, sai kiga har na koma ban samu zuwa ba”, “Toh Shikenan sai goben”, Sukayi sallama, Ta nufi motar yan’ gidan suka tafi, Tasan Mummy zata yi mamakin tafiyar ta gidan ba tare da ta sanar da ita ba, Ta d’auki waya ta kirata, ga mamakin ta Mummy bata nuna wata damuwa ba, hakan ya mata dad’i. Suraj ganin zaman falon ba zai k’ara masa komai ba, dan yayi imani Fetta ba zata sake zuwa ba, Ya mik’e a kasalance ya fita, Ba kowa a harabar gidan sai ma’aikata, bai tsaya neman driver da ya kawo sa ba, ya fita bakin gate, mai taxi ya tara yace ya kai sa hotel na garin, da k’udurin washegari zai dawo ko Allah zai sa Fetta ta sauraren sa, ba zai bar garin Niamey ba, har sai Fetta ta yafe masa ta amincewa komawa gidan sa. Fetta tun isowar su gidan, bata yarda ta zauna ita kad’ai ba ta yadda tunani zai yi arba da zuciyar ta, sai dai bata tsira ba duk iya k’ok’arin ta wurin yakice damuwar ta da tuna duk wani abu da ya danganci Suraj abun ya faskara, Zaune suke falo suna hira tana jefa bakinta jefi jefi, kallo d’aya zaka mata kasan akwai tsantsar damuwa a tare da ita, Ameerah yarinyar gidan wacce zasu yi kusan sa’a da Fetta ta kalleta tace “Fetta akwai abunda ke damun ki ne?” Tayi faking smile tace “Ba komai gajiya ce fah”, “Kije ki kwanta mana”, “Toh” Ta fad’a tana mik’ewa duk da bata son keb’ewa ita kad’ai but ita kad’ai ce hanyar da zata gujewa su fuskanci tana cikin damuwa,+ Kan gadon d’akin ta kwanta, tare da d’aura hannun ta kan zuciyarta tana sauraren sautin dokawar ta, “Ya Rabbi” take furtawa a hankali, ganin Suraj da kalaman sa tun tado mata raunin da yake shirin warkewa a zuciyar ta, “Shin wa ma ya sanar dashi inda take?”, “Yasmeen” Zuciyarta ta bata amsa, Ranta taji ya b’aci, ta fiddo wayarta dake cikin jaka, ta danna kiran Yasmeen, Bugu d’aya Yasmeen ta d’auka, Ba tare da sun gaisa ba tace “Alk’awarin da kika d’auka kenan, meyasa kike son ruguza farin cikina a lokacin da nake k’ok’arin daidaita rayuwata?”, Tasan tabbas Suraj yaje gareta zata yi fushi da ita, but tana fatan nan gaba ta fahimci dalilin yin haka, Ta katse tunanin ta tace “Kiyi hak’uri Fetta shine kad’ai abunda zan iya ce miki”, “Ke da kika aiko sa, ki fad’a masa ya gaggauta tafiya, ya fita rayuwata da na ya’ta”, Ta kashe wayar ba tare da ta jira cewar Yasmeen ba, Mamaki fal zuciyarta na sanar dashi da Yasmeen tayi, despite shine silar kashe iyayenta. Suraj ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai faman zirga zirga yake a d’akin hotel, Ko ruwa ya kasa saka ma cikin sa, duk da yadda yake masa kukan yunwa, Ganin Fetta ya tado masa azabtaciyyar soyayyarta da bai san yana mata irin ta ba sai yau, Zuciyar sa tamkar zata fasa k’irjinsa ta fito tsananin yadda take buga masa, K’wak’walwarsa Fetta take haska masa yayin da zuciyar sa ke rurawa da k’aunar ta, bai tab’a zaton akwai ranar da soyayyarta zata kama sa haka ba, yasha k’aryata so, a yau ya shaida so babbar cuta, Nadamar wulak’anta ta da ya rik’a yi a baya na dabaibaye sa, bai san haka soyayyar ta zata kama shi ba da wallahi ko kallon banza ba zai tab’a mata ba, “Ya Rabbi” ya furta ya kai k’asa, ya zauna dirshan tare da d’aura hannayen sa kan k’irjin sa. Rurin wayarta ya fargar da ita nisan tunanin da tafi, Ganin bak’uwar number tak’i d’auka wanda take kyautata zaton Suraj ne, kira biyar yana shigowa babu wanda ta d’auka, ta jawo wayar zata kashe gaba d’aya, text message ya shigo, “Ki d’auki wayar Sultan ne”, Sultan matsayin second cousin d’in ta yake, “Lafiya Sultan ke kirana ne” bata rufe baki ba wani kiran ya shigo, Ta d’auka ta kanga a kunne, “Assalamu alaikum”, “Wa alaikassalam”, “Ina fatan ban tashe ki daga bacci ba”, “A’ah” Ta bashi amsa tana girgiza kai tamkar tana gabansa, “Toh Mashaa Allah sarauniyar kyawawa”, “Uhmm” tace tana jin ta soma gajiya da wayar, “Ni dai ba zan d’auki lokaci wurin sanar dake sirrin zuciyata ba, tun wancan zuwan da kika yi na kamu da son ki, kuma auren ki nake son yi”, K’irjinta taji ya masifar dokawa sam bata son zancen soyayya, bata tunanin zata tab’a k’ara aure a rayuwar ta, Ta nisa tace “Baka san ni bazawara bace”, “Ni kuwa na sani”, “Toh taya kana saurayi zaka auri bazawara”, “Addinin mu ya haramta ne?”, “Ko d’aya amma ina ganin rashin dacewar hakan”, Dariya yayi yace “Ke dai kice bakya sona kawai, ban miki ba”, “Ko d’aya amma ina so ka bani lokaci nayi shawara”, “Shikenan zan jira duk tsawon lokaci”, “Toh sai da safe”, Ta fad’a tana kashewa ba tare da ta jira cewar sa ba, ta cilar da wayar gefe tare da furta “Ya Allah” ya zama dole ta tattara ta bar garin Niamey dan gujewa Sultan. STORY CONTINUES BELOW Karima rashin mijinta na damun ta sosai, kewar sa a kullum k’aruwa take, Abdul ma bashi da magana sai tashi, yana tambayar ta yaushe zai dawo, wanda a zaton yaron shine mahaifin sa, Yau da zazzab’i da amai ta tashi, wanda take kyautata zaton juna biyu ne, kasancewar wacce tayi ciki ba d’aya ba biyu ba, tasan duk wasu alamomi na masu ciki, wunin ranar tayi ta kwara amai, babu mai taimakon ta. Bello ya fito da shirin sa na zuwa wurin aiki, wanda akan dole yake zuwa ba dan yana son aiki k’ark’ashin Mahaifin Tasleem ba, sai dan tursasawar Kawu Lamid’o, Dining table ya kalla kamar ko da yaushe wayam babu komai na karin kumallo, ya girgiza kai yana ficewa, “Bello! Bello!” Ya tsinkayo muryar Tasleem, cike da takaici ya juyo yana kallon ta, “Wai kai wane irin miji ne Dan Allah, ace zaka fita ba zaka sanar da matar ka ba”, Tsaki yayi ya shige mota, ya barta a gurin tana masifa, yau kam za’a yi ta ta k’are, ya zama dole a d’aukar masa mataki, ta kai mak’ura da halayyar sa. Asuban fari Suraj ya nufi gidansu Fetta, gari bai gama wayewa ba, Fatan sa Allah yasa yau Fetta ta saurare sa, Masu gadin basu hana sa shiga ba, sun rik’e fuskar sa, D’ayan daga cikin ma’aikatan gidan yace ya masa sallama da Fetta, Ya jingina da motar dake fake a harabar gidan, cike da zullumi da addu’ar amincewar ta, Mintuna goma Saurayin ya fito yace “Ance bata nan”, K’irjinsa ya duka, yayin da zuciyar sa ke tabbatar masa tana cikin gidan ganin sa ne bata son yi, Da k’yar ya iya furta “Toh”, Saurayin ya wuce, Kusan minti goma yana tsaye a wurin yana tunanin yadda zai sake tozali da Fetta, ganin bashi da wata mafita, yaja k’afafun sa da yake jin tamkar ba’a jikin sa suke ba, ya nufi hanyar fita daga gidan, zuciyar sa cunkushe da bak’in ciki had’i da damuwa. Fetta sallar asuba da karatun Qur’anin da tayi ya rage mata kaso arba’in na cikin damuwar ta, zaune take bakin gado tana breastfeeding Mimi, tausayin yarinyar fal zuciyarta, sam bata yi dacen mahaifi ba, hawaye dake shirin zubo mata, tayi saurin tarewa, tana matse mimi a jikin ta. Suraj haka ya koma hotel rai ba dad’i, sam babu natsuwa a tare dashi, wayar sa da tun zuwan sa nijar bai bi ta kanta ba, ya d’auka ya kunna karatun Qur’ani, Tunanin kiran Hajiya yazo mishi, yasan tabbas ta neman sa dan jin lafiyar sa, Mik’ewa yayi ya fita, yaci sa’a a bakin hotel d’in akwai wani business centre, Ya siya sim da recharge card ya dawo ciki, Ya saka ya danna kiran mahaifiyar tasa, Hajiya wacce tun a daren da ya tafi take kiran wayar sa, amsar d’aya ce a kashe, hankalinta ya kasa kwanciya, Jin muryar sa yanzu ya kwantar mata hankali, sai dai sam bata damu ta tambaye shi me yaje yi nijar d’in ba, ta barwa zuciyarta harkar kasuwancin sa yaje. “Bello! Bello! Bello! sau nawa na kira ka” Cewar Alhaji Tambari cikin karaji, Bello wanda kansa ke sunkuye k’asa yace “Uku”, “Wallahi hawainiyar ka ta kiyayi rama ta, kana wuce gona da irina, wato duk gargad’i da kashedin da nake wa Uban ka, a banza yake tafiya” Ya juya kan Kawu Lamid’o yace “Kai Lamid’o baka jawa dan’ ka kunne ne, ya’ta ba abar wulak’antawa bace, sanin ku tafi k’arfin sa, banda k’addara irin Tasleem ina auren talaka irin sa, matsalar had’a jini da matsiyata kenan, dama duk yadda kayi da jaki sai yaci kara”, Ran Bello da Kawu Lamid’o ya kai k’ololuwa wurin b’aci, Bello cikin tsananin b’acin rai yace “Ina ga zan sawwak’e mata”, Alhaji Tambari yace “Yar’ tawa zaka mayar bazawara wato dama auren jari kayi da ita, toh bara kaji kana sakinta uban ka zai daina aikina k’ark’ashina”, Kawu Lamid’o hanjin cikin sa suka kad’a duk da ya gaji da cin mutuncin Alhaji Tambari amma yasan muddin ya kore sa wurin aiki, k’aryar sa ta k’are, Cike da fad’a yace “Kai Bello ashe baka da hankali, wallahi idan ka kuskura ka sake ta sai na tsine maka, kuma daga yau kar na sake jin ka mata ba daidai ba”, Cike da takaici na halin mahaifin sa ya mik’e ya bar falon, “Sam baka ba dan’ ka tarbiya ba” Cewar Alhaji Tambari, Kawu Lamid’o hak’uri ya shiga bashi, duk da k’asan zuciyar sa nadamar had’a auren yake, tunda akayi auren kullum da kalar rashin mutunci da wulak’anci da yake fuskanta gurin Alhaji Tambari. Suraj wunin ranar da sak’e sak’en yadda zai had’u da Fetta yake, but bashi da wata hanya, kowane minti yana k’aruwa ne da soyayyarta a zuciyar sa, yayin da idon sa ke azabtuwa da son ganin ta, kwance yake duniyar sam bata masa dad’i. Fetta bikin ranar da suka yi, ya d’auke mata hankali ta yadda bata samu zama ba balle tayi wani dogon tunani, duk da damuwa na nan mak’ale a zuciyar ta, ana tashi bikin ta nufi gidansu Mummy, wanda take kyautata zaton Suraj yabar garin Niamey. Suraj tamkar wanda aka tsikara ya mik’e, zuciyar sa na ingiza sa ya tafi gidansu Fetta ko Allah zai sa ya ganta, Haka ya fito ya shiga taxi zuwa gidan, Harabar gidan ya tsaya yana dube dube tamkar mai neman abu, tsayuwar mota saitin sa yasa ya kai duban sa ga motar, Fetta wacce sam bata lura da Suraj ba, ta fito ciki, Suraj wanda ya zuba mata ido ya kasa ko da k’wakk’waran motsi, k’amshin turaren ta na ziyartar k’ofofin hancin sa suna sake jefa sa a wani yanayi, Idonta ya kai kansa, Saurin ja baya tayi, k’irjinta na tsananin dokawa, ko da wasa bata tsammaci ganin sa ba, Jin muryar Amra tana fad’in “Kinga Mimi har tayi bacci”, Tayi k’ok’arin tattaro natsuwar ta tace “Ai baccin ta ba wuya”, Suraj jin an ambaci Mimi ya kai duban sa ga Amra yace “Pls bani ita” Ya mik’a hannun sa, Fetta tayi saurin fisgewa hannun Amrah, ta wuce, Bayanta suka bi da kallo, kafin Amrah ta dawo da duban ta gare sa, kamannin sa da Mimi ta hango, tana kyautata zaton dan’ uwan Mijin Fetta ne, but meyasa ta mishi haka, ba tare da tace masa komai ba, tabi bayan ta. Suraj wanda hankalin sa ya tashi da yanayin Fetta, hakan ya k’ara tabbatar masa ba zata tab’a sauraren sa ba, ko zai koma Agadez ne ya sanar da Azagas komai, “Are you ok?, Mahaifiyar wanda kayi silar kashewa ce fah”, “Ya ilahi ko Mama zan sanar da komai, watak’ila taji tausayina ta yafe mun, ta rok’i Fetta ta dawo gareni”, “Baka tunanin ta shiga tashin hankali jin ko kai waye?”, Wani b’angare na zuciyar sa ta fad’a, “Ya Allahu ka kawo mun mafita” Ya fad’a yana d’aga hannayen sa sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *