FETTA
CHAPTER 3
*Kuyi hak’uri zaku ga na canza sunan Yar’ Kawo Sule daga Aysha zuwa Karima* +
Aunty Jummai kamar an jefo ta ta shigo gidan Kawo Sule, “Ina kike bak’ar munafuka”, Ta fad’a tun daga bakin k’ofa, Yelwa ce ta fito tana yatsina fuska tace ” Lafiya dai?”, “Ba lafiya ta kawoni ba”, ” Toooh Allah ya tsare mu da rashin lafiya”, “Kin je kinyi makirci an had’a Karima da Suraj bayan kinsan yadda Bilkisu ke mutuwar son sa”, Dariya tayi tace ” Haba, ai bani da labari, Suraj shi ya Kawo kansa, ba Karima ta nuna tana so ba”
“Ke Yelwa, da Jummai kike magana ba wata ba, Nasan halin ki tun kina k’aramar ki, kar ki manta ke raino na ce, toh wallahi baki isa ba, In dai ina raye Suraj bilkisu zai aura”, ” Ahayye ai sai mu zuba mu gani, tunda har uwar sa na goyon baya”, “Nasan ba banza ba, wallahi ba banza kika barsu ba, amma nice nan zanyi maganin ki”, Ta fad’a tana dukan k’irji, Ta fice fuuu kamar zata tashi sama.
Hab’a ta rik’e tace ” Ohh kaji ni da mata, idan ke kika raine ni to nafi ki hatsabibanci, ai sai ya auri Bilkisu mu gani”
Suraj jefi-jefi Karima na zuwa tunanin sa, sai yayi tsaki da k’ok’arin kawar da ita, Sam bai san meye soyayya ba, Kuma baya son ya fara ta, Dan yaga yadda take wahalar da mutane, ta jigata su, Yaga yadda abokin sa ya wahala akan so, Hakan ya k’ara sa baya sha’awar ta.
Ya fito da shirin sa na sport, Duk yamma yana fita exercise, a wani recreational centre, Muscles d’inshi kad’ai zaka kalla kasan yana body building, sai da ya fara biyawa sashen Hajiya.
Tana zaune tare da yaranta suna hira, Kowaccen su ta shiga gaishe shi, Yana amsawa, “Mama zan tafi exercise”, ” Toh a dawo lafiya, Ka kula da kan ka”, “In Shaa Allah Mamana”,
Da mota d’aya ya tafi, Amintaccen driver shi na jan shi, ” Ina binciken da nasa kamun akan Alhaji Bello kotangora”, Ya tambayi Driver cike da isa, “Ranka ya d’ade nayi bincike komai, gashi a rubuce”, Ya zaro takarda a aljihu, Ya mik’a masa, Ya karb’a yana dubawa, ” Azzalumin mutum, I will soon break you down”, Ya furta.
Har suka isa wurin yana nazarin bincike da aka masa akan Alhaji Bello.
Fetta na wanke-wanke a tsakar gida, tana yan wak’e-wak’en ta, Aliya ta fito sanye da hijabi, Tace “Zan tafi wurin aiki, Ali na ciki na bacci, idan ya tashi yayi kuka, ki kawo shi”, Ta marairaice fuska tace “Da kin tafi dashi Umma, Allah bana son zuwa gidan nan”, ” Saboda me Fetta, gidan da kowa ke son zuwa, gidan arzik’i cikin ma ana hana mutane shiga”, “Ni dai kawai Umma”, ” Toh ai shikenan”, Ta koma ciki, ta d’auki Ali ta goya, ta fice, Hakan ba k’aramin dad’i yama Fetta ba, bata burin ta sake had’uwa da wannan mutumin mara tausayi, mugu.
Bayan ta gama wanke wanke, Duwatsu ta samu, ta zauna tana carafke, Har Aliya ta dawo ta sameta, Ta tambaye ta taci abinci, Tace a’ah, fad’a ta mata, tare da tasa ta gaba, taci,
Malam ya dawo musu da gasasshen nama suka ci, Yana jan Fetta da hira, da tambayar ta kan makaranta, Tana amsa mishi.
Malam sosai yake tuna mata da Mahaifin ta, Kullum addu’ar sakayya take ma mahaifin ta akan wanda suka kashe shi, da addu’ar samun rahma shi da Mahaifiyar ta.
Yelwa ta zayyane wa Kawo Sule yadda suka yi da Aunty Jummai, “Jummai bata san kunya ba, yanzu ita Yar’ ta tazo tana ma fad’an auren Suraj, saboda tsabar kwad’ayi” (a zuciyata nace kaima ai kwad’ayin yaja ka), “Hmm, kada kayi mamaki, zamanin nan kowa nasa ya sani”, ” Toh wallahi kada ki sake ki d’aga mata k’afa, haukar banza take, Suraj kamar ya auri Karima ya gama, gobe gobe zanje na samu Tumba ayi maganar sa rana”, “Yawwa gara mu hanzarta, kasan halin Jummai kafin tayi wani k’ullin”, ” Barni kawai da ita”, “Toh”, ” Kawo mun abinci”, Ta mik’e ta nufi kitchen, tana jin natsuwa a ranta.
Bilkisu da taji zancen, Ana son had’a Suraj da Karima kuka tasha, Aunty Jummai ta lallashe ta tace ta kwantar da hankalin ta, Dukkansu sun koma gidan Hajiya Tumba, Harara da yan habaice habaice suke wa juna, Su’ad da Safeena kam tsakanin su dasu ido, Suna addu’ar kada ya auri ko d’aya daga cikin su, Sunfi so ya auri Yar’ mai kud’i wacce aka san babanta a k’asar nan, a ganin su bai dace da middle class ba, dan Hajiya Tumba na kwab’ar su da yadda zasu k’yamaci talaka abun ba kad’an ba, Sun manta tsatson da suka fito.
Suraj ya had’a kayan sa a trolley a ranar zai koma Lagos, Jirginsu k’arfe 7 na safe zai tashi, Tafiyar tazo masa a bazata.
Hajiya Tumba bata tashi ba, ya bar mata sak’on wurin masu aiki, a yar’ k’aramar takarda, ya kuma mata text message, Murna sosai suke ya tafi, zasu huta.
Convoy na motocin sa uku suka kai shi airport, 7:15am jirginsu ya lula sama zuwa Lagos.
Hajiya Tumba bata fito ba sai k’arfe 10, da tarar da sak’on sa, Ta kira shi wayar shi kashe, Hakan ya tabbatar mata ya shiga busy, Karin kumallo tayi, Ta koma d’akin ta sama.
Yan’ matan kawai ke ta bidirin su, kasancewar yau lahadi babu lecture, Su’ad tace “Feena kalli yarinyar dake son Ya Suraj”, ” Wow amma ta had’u, she is classy”, “Bari sister, And babanta don ne, Yana da kud’i sosai gata Yar’ gayu, suna da sarauta fah”, ” Gaskiya da ita ya dace, Ya Suraj classy babes ne type d’in shi”,
Karima dake gefe tana jin su wanda da biyu suka yi, Taja tsaki tana mik’ewa, Su’ad tace “Ke dawa kike?” Ta juyo ta watsa mata harara tace “Da wanda ya tsargu”, ” Kinyi kad’an kice zaki zo gidan mu ki raina mana wayo”, “Dad’inta ba zaman ki nake ba”, ” Zaman Ya Suraj kike ya aure ki ko, toh ki sani ba zai tab’a auren ki ba gayyar tsiya”, “Da ba’a san asalin balbela ba sai ace daga misrah take, matsalar mutum yayi hayen arzik’i kenan”,
Saukar mari taji a fuskar ta, Dambe ne ya kacame tsakanin su, Safeena ta taso ta shiga, Suka kama Karima suna duka, Bilkisu ce taje ta sanar da Hajiya, Tsawa ta daka musu, suka daina, Ta shiga tambayar ba’asi, Bilkisu ta fad’a mata, Dukkan su ta had’a tayi wa fad’a sosai,
Karima kamar mayya k’ara nad’e k’afa tayi tak’i barin gidan, Duk da irin gorin dasu Su’ad suka mata, Su kansu sunyi mamakin rashin zuciya irin nata, Bilkisu abun ya mata dad’i, ko ba komai hakan zai sa Suraj ya fasa auren ta, tunda K’annen shi basa son ta, Zasu yi ta zuga. (Nace hmm kema baki tsira ba)
Kawo Sule ya wanko k’afa yazo, Ya buk’aci a mishi sallama da Hajiya Tumba, Bilkisu sama sama ta gaishe shi, Ta mak’e bayan k’ofa taji me zasu tattauna.
Bayan sun gaisa da Hajiya, Ya gyara murya yace “Suraj yaje yaga Karima, kuma na fuskanci sunyi na’am da juna, toh bai kamata mu b’ata lokaci ba, tunda dukan mu a shirye muke, a zauna a saka rana”, Murmushi tayi tana gyaran d’aurin ta da ya soma warwarewa tace ” Yaya Sule sha’ani na aure ba’a masa gaggawa, da an bari sun k’ara fahimtar juna”, “Wane gaggawa abun nan na gida ne fah, kowa yasan halin kowa”, ” Toh idan ya dawo zanji ta bakin sa”, “Au ya koma ne”, ” Eh”, “Da kin kira sa ta waya kinji, kinsan ya kan jima idan ya tafi”, ” Toh” Kawai tace masa, a ranta tana mamakin wannan hanzari da yake.
Bilkisu da sauri ta shiga d’aki, ta kira Aunty jummai ta fad’a mata, Tace ta kwantar da hankalin ta, auren nan da ita za’ayi ba Karima ba, Taji dad’i kuma ta yarda da Mahaifiyar ta, Tasan idan tayi niyyar yin abu to sai ta cimma burinta ko ta wacce hanya.Shigowar sa gida kenan, Ya kalli agogo k’arfe takwas daidai, Kan kujerar falon ya zauna, Yana huce gajiya, Tun isowar sa bai huta ba, Meeting yayi tayi da mutane. +
D’akin sa ya nufa, Yayi wanka tare da alwala, Ya saka jallabiya, ya feshi jikin shi da turare, Sallar isha’i yayi tare da shafa’i da wutri, Ya dad’e a zaune yana addu’o’i, Kafin ya mik’e, Ya hau gado ya kwanta, Ya jawo wayar sa, Yayi dialing number Mahaifiyar sa, Bugu d’aya ta d’auka,
“Mutanen Lagos”, ” Mamana Ina wuni?”, “Lafiya lau, ya gajiyar hanya, da ayyuka?”, “Alhamdulillah Mamana”, ” Ka tafi ka bar mu da kewa”, “Nima ina kewar ku”, ” Allah ya baka nasara a dukkan abunda ka saka gaba”, “Amin”, ” Bari na barka ka huta”, “A gaishe dasu Samee”, ” Zasu ji”,
Yana kashe kiran, wani kira na shigowa ba, Bai san number ba, Dan haka yak’i d’auka, baya d’aukar bak’uwar number, saboda mutane masu kiran sa neman taimako, Yafi so ka kira ta hanyar yaran sa.
Kira uku aka mishi babu wanda ya d’auka, Silent ya mayar da wayar, Jin tayi k’ara alamar text message, Ya duba ya karanta;
“Hy Masoyina, Karima ce, na kira naji ka sauka lafiya”
Yana gamawa karanta yayi tsaki, A fili ya furta “Matan yanzu sam basu da aji, kowacce ji take tamkar ta jawo da’ namiji, Allah ya kyauta”, Ya gyara kwanciya, Baccin wahala ya d’auke sa.
Fetta da tsananin kewar mahaifin ta ta tashi, ba komai ya haddasa haka ba, sai tashi da tayi da son shan Ataye, Kwance take kan k’atuwar katifar dake d’akin, Hawaye na zirya kan kumatun ta, Aliya da taji ta shiru ta d’auka bacci take, Jin shirun yayi yawa, Ta lek’a taga lafiya.
Tana jin shigowar Aliya, tayi saurin share hawaye, tana runtse ido kamar mai bacci, ” Baccin lafiya kike Fetta, nasan bakya dad’ewa kamar haka baki tashi ba”, Ta tab’a jikinta taji ba zafi, “Ina ga jiya dai kin gaji a makaranta”, Ta fice.
Fetta bata tashi ba, haka bata bud’e ido ba har baccin gasken ya d’auke ta.
Karima nata duba waya ko zata ga kiran sa, ko reply na text da ta mishi shiru, Tsaki take tayi ita kad’ai, Jin kira ya shigo, Tayi saurin jawo wayar cikin murna, Ganin mai kiran taja tsaki tana danna reject, Ya sake kira,
Ta d’auka a fusace, ” My baby baby”, “Dalla dakata mallam wacce babyn taka”, ” Karima ni Bashir kike cewa haka”, “An fad’a maka”, ” Nine Bashir fah, ko wani abu aka ce miki nayi”, “Kaga daga yau ka manta ka tab’a sanina, ni yanzu na wuce ajin ka, Mata nake a wurin SS SURAJ SA’IDU nasan kasan shi, na daina harka da k’ananun k’wari”, Bata jira cewar shi ba, Ta kashe tare da jan tsaki, ” Ina tare da SS mai zanyi da kai”
Bashir wayar yabi da kallo cike da mamaki, Ko a mafarki bai d’auka Karima zata mishi haka ba, wata zuciyar tace “Kud’i, ko baka ji wata ce zata aura bane, ina kai ina had’a kanka dashi,, babu komai ga yan’ mata da yawa a gari, zanje na nemi daidai ni”
“A bari auren ya tabbata kafin a fara wulak’anta mutane”, Bilkisu ta fad’a, ” Ke yar hassada da bak’in ciki, tun ba yau ba nasan shirin ku ke da uwarki akan ki auri Suraj, toh wallahi sai hangen nesa ya miki nisa”
Dariya Bilkisu tayi tace “Zaki sha mamaki kuwa, a ranar da zaki ji sanarwar d’aurin aure na da Ya Suraj”, “Na yarda kan ki ya tab’u, kina neman agajin gaggawa”, Karima ta fad’a tana ficewa daga d’akin.
Kiraye kirayen sallar asuba, Ya tashi Suraj, Salati yayi yana mamakin irin bacci da yayi, tunda ya kwanta bai farka ba, Toilet ya shiga, yayi brush tare da alwala, Ya fito ya tafi masallacin dake had’e da compound da yake,
Mak’wabciyar sa Rukayya, yoruba ce, kullum cikin hidimar kawo masa abinci take, In dai yana gari to bata gajiya da kawo masa, Watarana yaci watarana kuma sai dai a koma mata dashi bai ci ba, Tana son sa, ba tare da ya sani ba, Ya d’auki hakan da take mishi mutunci da kyautatawa na mak’wabtaka, Baya gajiya da mata alkhairi, wanda hakan ke sa tana jin dad’i, Da k’ara saka shi a ranta, tare da fatan watarana ya k’aunace ta.
Yau ma breakfast ta aiko masa, Yam balls da gunun gyad’a, Yaci ya k’oshi ya fita wurin harkokin sa.
Karima kullum safiyar Allah sai ta kira Suraj, baya d’aukar wayar ta, duk kiran da zata yi, abun ya fara damun ta, Ta sanar da Mahaifiyar ta(Yelwa), Tace ” Ta kwantar da hankalin ta, ayyuka ne suka mishi yawa, a can da yake ba zaune yake ba”, Taji natsuwa a ranta, but bata fasa kiran shi da mishi text msgs na soyayya ba.
Sau da yawa yana ganin kiran, yake k’in d’auka, Text msgs d’inta kuwa baya bud’ewa, Tana hauka idan tana tunanin zai aure ta, babu aure a tsarin sa, Yana jin har ya koma ga mahalaccin sa ba zai yi aure ba, ko da yayi aure sai da ya ajiye ta, tana amsa sunan matar sa amma babu wata mu’amala ta aure da zata shiga tsakanin su. 1
“Fetta gama wanke-wanke ki kaiwa Hajiya Tumba yajin nan da ta saka nayi mata, bayana ya rik’e kuma tana da buk’atar shi”, ” Toh” ta amsa murya a sanyaye, “Suraj baya nan kwantar da hankalin ki”, Dad’i taji a ranta, zata je ta dawo lafiya ba tare da b’acin rai ba.
Kwano d’aya ya rage dama ta wanke, ta kwashe kwanukan ta kai kitchen, ta d’auraye hannu, ta sako hijabi, Ta karb’i yajin, Yana da yawa sosai tiya biyu ne.
A falon k’asa ta tsaya, Safeena na zaune tana faman latsa waya, Gaishe ta tayi, ta amsa a k’ask’ance, Tana mata kallo kamar taga kashi, ” Maman Ali ce ta aiko ni wurin Hajiya”, “Shine baki tsaya can wurin masu aiki ba, kika shigo har nan”, Kafin tayi magana, Hajiya Tumba ta fito.
” Meye idan tazo nan, ina raba ki da wannan hali, bakya bari ko, kibi duniya a sannu Safeena”, B’ata rai tayi ta mik’e tabar falon, Da far’a ta juya kan Fetta, wacce ta duk’a har k’asa tana gaishe ta, Da far’a ta amsa, “Wai gaji inji Umma, bayan ta ne ke ciwo shiyasa bata zo ba”, ” Subhanallah, Allah ya sawwak’e”, “Amin”,
Pause d’in ta data sauko da ita ta zaro kud’i, Tace ” Gashi ki bata dubu biyu, ke kuma ga dubu d’aya ki siya alawa”, K’in karb’ar dubu d’ayan tayi, a ganin ta sunyi yawa, ita tunda take ko d’ari biyu ba’a tab’a bata ba, balle dubu d’aya, “Ki karb’a mana, baki san baya mayar da hannun kyauta baya ba”, Hannu biyu tasa ta karb’a, tayi godiya, ” Ki gaishe ta”, Hankali da natsuwar yarinya taji ya burgeta, Duk da k’ananun shekarun ta, but tasan abunda ya kamata, iyayenta sun bata tarbiya.
Fetta ta tafi, da mamakin kirki irin na Hajiya Tumba, Yaranta da sun biyo halinta da sun ji dad’i, Yadda suke nuna k’yamata da hantara ga talaka, sam ba haka take ba.
Kud’in duka taba Aliya, ba irin tambayar da bata mata ba akan me take so a siyo mata, Tace bata buk’atar komai, Sau da yawa idan Fetta tayi abu, tana mamakin hankali irin nata wanda ya zarce shekarun ta, Addu’a ta mata da fatan Allah ya inganta rayuwarta, Ta amsa da Amin.Satin Suraj biyu a lagos kafin ya fara tunanin dawowa gida, Ayyuka ne suka masa yawa, bai d’auka zai kai tsawon lokacin kafin ya koma gida ba. +
Kawo Sule yayi ta sintirin zuwa gidan Hajiya Tumba, akan maganar auren Karima da Suraj, Tace mishi tayi magana da Suraj yace a jira ya dawo, tukuna ya shafa mata lafiya, Yacewa Karima yana dawowa ta sanar dashi.
Fetta a kullum safiyar Allah da tunanin su waye dangin ta, meye asalin ta take kwana take tashi, Mahaifin ta ya rasu ba tare da ya sanar da ita komai ba, Ta cire rai da had’uwa da dangin ta.
Shirin sa yayi tsaf, Cikin wando da riga long sleeve, Sun amshi jikin sa, Sun mishi kyau sosai, Bai d’auki kaya ko kala d’aya ba, dan yana da kaya a Kano, Driver sa ya kai shi airport.
Kamar ko da yaushe, Hajiya Tumba ta umarci masu aiki suyi girke-girke, da gyara gida a saka turaren wuta.
Ganin haka Karima da Bilkisu suka san Suraj na tafe, Kowacce tasha ado ta k’ure a daka, harare harare, da habaici suke ta jefan juna.
Karima da Bilkisu da ka gansu zaka san yan uwa ne, suna kama ta jini, Dukkansu bak’ak’e ne(dark in complexion), Karima nada d’an jiki, Bilkisu kuma siririya ce, haka take one babu wani shape.
K’arfe biyu na rana jirgin su Suraj, yayi landing, Ya sauko matattakalar jirgin cikin takun sa na k’asaita, Sosai ya tafi da hankalin matan dake harabar filin jirgi, Babu wacce ta ishe sa kallo, Duk da yadda suke ta kwarkwasa ko zai taya.
Ganin tahowar sa, Da sauri driver motar da yake shiga, Ya fito ya bud’e masa k’ofa, Ya k’araso ya shiga, Yana masa sannu da zuwa.
Gida suka nufa, Karima na jin shigowar motocin sa, Tayi wani juyi tace “My husband is here”, Dogon tsaki Bilkisu taja tace ” Haukar banza”, Kafin ta juyo ta bata amsa ta fice.
Hajiya Tumba tayi murnar ganin Dan’ ta, Tarba sosai ya samu daga gare ta, Yana cin abinci suna hira, Har ya cinye, Samee ta kwashe kwanukan, dan a d’akin Hajiya yaci, ba dining area ba, Sosai yayi kewar mahaifiyar sa.
“Ya kamata kaje ka duba jikin Laurat,(K’anwarta ce) an kwantar da ita asibiti”, ” Subhanallah meke damun ta ne?”, “Hawan jini da diabetes (ciwon suga)”, ” Allah ya bata lafiya”, “Amin”, ” Wane asibiti ne aka kwantar da ita?”, “Asibitin murtala”, ” Ai bai kamata a barta irin asibitocin nan ba, private hospital ya dace”, “Ina kud’in Suraj, jiya ma sai da na kai musu dubu hamsin, baka ga yadda suke a wulak’ance ba, ganin basu da komai”, ” Talaka na ganin rayuwa a k’asar nan, gwamnati ya kamata ta maida hankalin wurin gyaran asibitocin gwamnati, da zaran baka da kud’i to kai fah baka da samun sauk’i, ya kamata ace a irin asibitocin nan magani kyautar ake bayarwa”,
“Hmm Suraj kenan, ina fah zasu yi haka, kowanne son kai ya mishi yawa, burin su su hau mulki, su kwashi dukiyar bayin Allah, basa tsoron hakk’in al’umma da ya rataya a kan su”, ” Allah ya kawo mana sauk’i, anjima idan na huta, zanje sai a canza mata asibiti”, “Allah yayi maka albarka, ya cigaba da baka ikon taimakawa yan’ uwan ka da al’ummar musulmi”, ” Amin Mamana”
Ana idar da Sallar isha’i Kawo Sule yazo gidan, Ya buk’aci a mishi sallama da Hajiya Tumba, “Allah yayi ma wannan bawan Allah naci da takura”, Ta fad’a a ranta, Da sakin fuska suka gaisa, Yace ” Ashe Suraj ya dawo”, “Eh d’azun nan ya iso”, ” Toh Madallah, ko zaki kira shi sai muji ta bakin sa maganar auren su”, “Haba Yaya Sule daga dawowar sa ai a bari ya huta”, ” Wane hutawa kamar wanda yayi tafiyar mota, ai ko tafiyar mota ce yanzu yaci ace ya huta”,
Ganin yana neman mayar da abun rigima, Ta d’auki waya ta kira Suraj, Zaune yake falon sa yana kallon news a NTA, Yaso zuwa asibiti wurin Aunty Laurat bai samu zuwa ba, Gajiya bata bar sa ba, a can lagos kullum cikin aiki yake baya samun wani hutu.
Kiran Mahaifiyar sa ya shigo, Yayi receiving, “Suraj kazo sashena ina son ganin ka”, ” Toh Mamana”, Ya fad’a cike da ladabi, Ta kashe ta dubi Kawo Sule tace “Yana zuwa”, Dariya ya saki yace ” Yawwa ko kefa, ai gara ayi a wuce wurin”, Murmushi kawai tayi a zuciyarta tana addu’ar mafi alkhairi.
Ganin Kawo Sule hakimce kan kujera ya d’aure fuska, Ya zauna kujerar kusa da Mahaifiyar sa, Ya gaishe shi murya ciki-ciki, Yana washe hak’ora ya amsa, yana mishi ya hanya, Ya amsa a dak’ile.
“Mamana dafatan lafiya tasa kike nemana”, Murmushi tayi tace ” Kawon ka ke son magana da kai”, Ya k’ara had’e rai,
Kawo Sule na washe baki yace “Maganar auren ka da Karima, a tsayar da magana a saka rana”, ” Naga sau d’aya muka had’u da ita, a bari mu k’ara fahimtar juna mana”, “Wane fahimtar juna Suraj, abu duk na dangi, Kaga daga kai har Karima duka nine mahaifin ku, zan samu sauran yan uwana a saka rana nan da sati biyu ayi aure”, ” What! Asa…” Ya fad’a a tsawace, Kallon da Hajiya Tumba ta jefa masa, yasa ya had’iye sauran maganar da yayi niyya, “Ya akayi ko bai maka bane, na lura kamar baka son had’in nan”
Hajiya Tumba tayi saurin cewa “Ba baya so bane abun ne yazo masa a bazata”, ” Toh toh, zai bada sadaki dubu hamsin, yanzu zai bayar dan naje musu dashi”, Hajiya Tumba kanta sai da gabanta ya fad’i jin a bada sadaki yanzu, Tayi k’ok’arin b’oye damuwarta tace “Babu kud’i a hannun mu yanzu, gobe za’a aiko”, ” Ina jiran ku, Ni zan koma sai da safe”, Ya mik’e ya fice.
Suraj sai faman had’a hak’ora yake, ransa ya matuk’ar b’aci, Yaso Mahaifiyar sa ta barshi ya fad’awa Kawo Sule bai shirya aure ba, Shine za’a ma aure nan da sati biyu, kuma auren dole ba zai yiyu ba.
Hannun sa ta rik’o tace “Kada ka tada hankalin ka Suraj, addu’a ita zaka rik’e, itace makamin mumini In Shaa Allah komai zai zo da sauk’i”, Kai kawai ya iya d’aga mata, Gaba d’aya ransa a jagule yake, yana jin dama bai dawo ba.
Yan kunni masu kyau kala biyu Aliya ta siyo ma Fetta cikin kud’in da Hajiya Tumba ta bata, Dawowar ta kasuwa kenan ta kira ta ta bata, Da hannun biyu ta karb’a tana murna ta mata godiya, Tace ” Umma ina fatan ba da kud’in da aka bani kika siyo ba”, Aliya tayi murmushi tace “A’ah, nagane yan kunnin kunnen ki duk sun kod’e shine na siyo miki”, ” Allah ya saka da alkhairi Umma”, “Amin”
“Jiya cikin bacci naji kamar ana harbin bindiga”, Cewar Fetta, ” Ashe kema kinji, wallahi yan fashi suka shiga nan mak’wabtaka har sun kashe mutum biyu, so nake na shiga yi musu gaisuwa da jaje”, “Allah ya jik’an su, ya tona asirin su waye”, Ta fad’a zuciya a raunane, Daren da aka kashe mahaifin ta na dawo mata a kai, ” Amin mutanen nan basu da imani, ka kwashe dukiyar mutane, kuma ka d’auki ran sa”
Malam bala dake gefe yana jin su yace “Rashin tausayi ne, da neman kud’i ke saka su, Da yawa talauci ke jawowa idan baka da tawakkali sai ka fad’a wannan mummunan hanya, da gwamnati zata samarwa matasa aiki da Sana’a da an rage sace sace da fashi da makami”, ” Hakane, Allah yasa mu dace”, “Amin”
Fetta tuni ta tashi ta shige d’aki, ta bud’e babin kuka na tuna mahaifin ta, Da rashin sanin makomar ta, Tana da yak’inin a nan zata tabbata tare dasu Aliya har ranar komawarta ga mahaliccin ta, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.
K’arfe 11:30 yayi shirin zuwa asibiti wurin Aunty Laurat, Sai da ya fara biyawa wurin Mahaifiyar sa, Ta masa fatan alkhairi da dawowa lafiya.
Da mota d’aya ya tafi, Bai sha wahalar gane d’akin da take ba, Hajiya ta gaya masa ward da take, da number d’akin,
Ya tausaya ma halin da ya tarar da ita, D’aki ne su kusan goma a ciki, Yayi datti, wari da zarnin fitsari na tashi, Asibiti da ya kamata ace kullum a tsaftace yake, Da k’yar ya iya zama kan kujerar dake d’akin, Allah yayi shi mutum mai k’yank’yami da son tsafta, Hannun sa yasa yana d’an toshe hanci, Ya gaishe ta tare da tambayar ta ya jiki, Cike da farin cikin ganin sa, Ta amsa da sauk’i.
Ba b’ata lokaci ya buk’aci a sallame ta, Aka sallame ta, Ya d’auke ta tare da yaranta su biyu masu jinyar ta, Ya mayar dasu asibitin Standard, D’akin mutum d’aya aka kai ta, Da komai comfortable, Ya biya kud’in komai, Ya tafi da musu alk’awarin zai dawo gobe, Aunty Laurat nata godiya, Ta kira Hajiya Tumba ta mata godiya da addu’ar Allah ya bar zumunci, Yaran Aunty Laurat kuwa kowacce ji take ina ma Suraj ya zama miji gare ta (Hmm SURAJ SAIDU mai farin jini😂)