FETTA CHAPTER 30
Suraj ya k’ara kwana biyu garin Niamey but kwanakin nasa basu k’ara masa komai ba sai damuwa da rashin natsuwa na yadda baya samun wani cigaba daga b’angaren Fetta, sam ta daina yarda su had’u, Ganin haka ya shirya tattarawa ya koma Nigeria, ba dan zuciyarsa ta hak’ura da ita ba, sai dan bashi da wata mafita.+ Fetta tana k’ok’arin yak’i da zuciyarta wurin yakice duk wata damuwa da kawar da tunanin Suraj, ta cigaba da harkokin ta, suna shan shagalin biki, sai dai Sultan da ya matsa mata da kira, a rana sai ya kira ta sau biyar, bata k’in d’aga wayar sa, tana matuk’ar jin nauyin sa, amsa d’aya take bashi a ko da yaushe bata gama shawara ba, wanda k’asan zuciyarta bata jin zata tab’a amincewa dashi. K’arfe biyu na ranar laraba Suraj yana cikin garin Kano, bai buk’aci zuwan direbobin sa ba, Taxi ya tara ta kaisa guest house d’in sa, Sallar azahar ya gabatar, ya kwanta kan doguwar kujerar dake falon, kansa na tsananin sara masa, Ruri wayarsa ta soma yaja tsaki yana danna reject ba tare da ya duba mai kiran ba, “Umma kashe mun waya yayi”, Bilkisu ta fad’a cikin tsananin b’acin rai, A fusace Aunty Jummai tace “K’aryar iskanci yake wallahi, bar ni dashi kawai”, Bilkisu ta jinjina kai tana mik’ewa ganin kiran Zulaihat, bata so Aunty Jummai taji wayar da zasu yi. “Sweety kinyi kasuwa fah” Cewar Zulaihat, “Haba dai”, “Wallahi wata Hajiya ce mai dollars taga hoton ki ta rud’e”, Cike da farin ciki Bilkisu tace “Kice na garzayo”, “Yanzu kuwa”, “Gani nan zuwa” Ta kashe wayar, jiki na rawa ta hau shiri. Su’ad tana zaune tsakar gida sai faman hamma take na yunwa, yau kwana biyu bata saka komai a cikinta ba sai ruwa da garin kwaki, Adnan tun ranar da ya sanar da ita shi waye, bata sake ganin shi ba, Hawaye ke zirara kan kumatun ta, Murya a raunane tace “Ya Rabbi ka yafe mun zunubai na, Allah na tuba”, Cikinta yayi k’ugin yunwa, “Ashe haka talakawa suke ji, ashe haka rayuwar talauci take”, Ta fad’a nadamar wulak’anta talaka da ta rik’a yi na dabaibaye ta, Fetta tazo mata a rai, tana tuna irin cin kashin da suka rik’a mata, tana sake nadama. “Fetta ba zaki k’ara mana kwana biyu ba”, Cewar Amra, Fetta dake had’a kayanta a akwati tace “Ai zan dawo, akwai abunda zanyi a Agadez ne”, k’asan zuciyarta bata jin zata dawo nan kusa, tana son gujewa Sultan, “Shikenan idan ma baki dawo ba, mu zamu zo”, Tayi murmushi tace “Toh Shikenan”, Shigowar Mummy ya katse musu hira da murmushi d’auke a fuskar ta tace “Jirgin ku ya kusa tashi, ina fatan kin gama shiryawa”, Ta gyad’a kai sama tace “Eh”, “Ban san me muka miki ba, sam bakya son zama niamey”, Tayi murmushi tace “Ba haka bane Mummy”, “Ba wani nan”, Tayi dariya tana mik’ewa, Masu aiki suka shigo suka fita da kayan ta. Sanah tana jin saukar motar da ta d’auka su Fetta daga airport, ta fito a guje, kai kace ta shekara bata gansu ba, Ta k’ank’ame Fetta tana karb’ar Mimi, “Tumuqqartin nayi kewar ku sosai”, “Muma munyi naki Sanah” Ta fad’a d’auke da murmushi, Suka shiga ciki. “Lale marhaban sannun ku da zuwa” Cewar Azagas fuska d’auke da far’a, “Tanti ina wuni?”, Lafiya lau, ya hanya? Ya mutanen yamai?”, “Alhamdulillah”, “Mik’o min kishiyata na ganta, kwana biyu ban lak’aci hancin ta ba”, Suka yi dariya, Bayan sun natsa, Azagas tace “K’anin mijin ki yazo, ina fatan ya same ki a can”, “Eh mun had’u” Ta fad’a a dak’ile tana mik’ewa, “Zan je nayi sallah” Tayi hanyar fita falon, sam bata son zancen, Azagas tabi bayanta da kallo, cike da mamakin ta, “Ko shakka babu akwai abunda take b’oyewa” Ta fad’a a ranta. Shigar ta d’akin yayi daidai da shigowar kiran Sultan wayar ta, ta d’an ja tsaki kafin ta d’auka, Takurar sa ta soma damun ta, “Gimbiyar mata nayi fushi, kin tafi ba sallama”, Ta nisa tace “Tuba nake, nima tafiyar tazo mun a bazata”, “Shikenan bakya laifi ai”, Tace “Uhmm”, “Ya gajiyar hanya?”, “Alhamdulillah”, “Bara na barki ki huta koh, sai anjima”, “Ok” Ta fad’a tana ajiye wayar tare da sauke numfashi. STORY CONTINUES BELOW *Bayan sati biyu* Suraj ne zaune a office na gidan gonar sa, tun zuwan sa ya kasa aikata komai, tun dawowar sa nijar bai zo ba sai yau, shima Hajiya ce ta lura da rashin fitar sa, ta masa magana, yace baya jin dad’i but yau zai lek’a, tasan rashin Fetta ke damun sa, wanda tana tausaya masa duba da yadda ya canza lokaci d’aya. Sam bai ji knocking k’ofar da ake ba, Ahmad(abokin harkar sa) ya gaji da knocking, ya murd’a k’ofa ya shigo, har ya zauna Suraj bai ankara dashi ba, yayi nisa a tunani, Tebur dake gabansa ya buga, Suraj yayi firgigit ya kai duban sa ga Ahmad, “Yaushe ka shigo?”, “Tunanin me kake SS?, meke damun ka haka gaba d’aya ka canza, kayi rashin lafiya ne?” Ahmad ya jefo masa tambayoyin yana bin sa da kallo ganin yadda ya canza, ya rame yayi bak’i, Suraj ya nisa yace “Bana jin dad’i ne”, “Ayyah Allah ya baka lafiya”, “Amin”, “Amma wacce irin rashin lafiya ce ta tab’a ka haka, nasan baka wasa da neman kud’i, ka tattara komai ka ajiye, operation ka daina zuwa, baka bada umarni kamar yadda ka saba, kamfanonin ka suna ta yin k’asa, ana rasa mak’udan kud’i”, Yayi murmushin gefen baki yace “Na ajiye sana’ar fashi da makami Ahmad”, “What! Kace mun wasa kake SS, na fah sanka da bakin ka ka gaya mun ba zaka tab’a dainawa ba, burin ka ka tara arzik’in mai d’umbin yawa” “Greatest mistake da na tab’a aikawata a rayuwata kenan, am regretting everything Ahmad, ina ji tamkar na maida hannun agogo baya na goge fashi da makami a cikin tarihin rayuwata”, Cike da mamaki Ahmad yace “Me yasa canza ka suddenly?”, “Ahmad kud’i basu ne rayuwa ba, kud’i basa siyan farin ciki da kwanciyar hankali, nayi kuskure da na d’auka kud’i sune rayuwa, a halin yanzu ina da d’umbin dukiya but na rasa farin cikina, na rasa natsuwata, meyasa kud’in basu taimake ni ba? Why?” Ya k’arasa yana had’e hannayen sa, yana cije lips d’in sa, Maganganun Fetta na dawo masa a k’wak’walwa “Ba komai kud’i ke siyawa ba, Soyayyar gaskiya ba’a siyan ta da kud’i, zaman lafiya da kwanciyar hankali kud’i baya kawo su, Mutunci yafi kud’i, Arzik’i Allah ke ba dashi ga wanda yaso a lokacin da yaso, talaka ba dan Allah baya son shi ba ya hana mishi arzik’i akwai manufar sa na yin haka” “Ban fahimci inda maganganun ka suka dosa ba, taya ka rasa farin cikina, sanin kowa ne Hajiya kad’ai zaka rasa, yasa ka rasa farin cikin ka, tana tare da kai, meye damuwar ka?”, “Fetta, itace damuwata, itace farin cikina”, Da kallon mamaki yabi sa yace “Kar kace matar ka baroroji da kake bani labari”, “Ita na kamu da azabtaccen son ta gashi ta bar ni”, Ahmad tsaki yayi yace “Akan mace zaka mayar da kanka haka, macen ma mara aji, talaka, bararoji”, “Kada ka sake danganta ta da sunayen nan” Ya fad’a cikin karaji, “Fetta ta wuce tunani da sanin ka, yar’ asali ce yar’ dangi, kai wallahi ko da ace a matsayin yar’ mai gadi take har yanzu, ina sonta haka, ina k’aunar ta”, Tsaki Ahmad yace “Akan soyayya zaka bar dukiyar ka ta salwance”, “Baka san so ba, baka san cutar so ba, ka rok’i Allah kada ya d’aura maka, Fetta ta fiye mun komai na rayuwar duniya akan ta zan iya sadaukar da komai”, Ahmad ya jinjina kai cike da mamakin abokin sa, tabbas kansa ya tab’u, “Allah ya kawo maka sauk’i, na bar ka lafiya” Ya fad’a yana mik’ewa ya fice. Suraj ya jingina da kujera, yana lumshe ido, soyayyar Fetta na yawo a jinin jikin sa, yana jin komai zai iya rasawa a kanta, sam dukiyar da ya tara bata gaban sa yanzu, ko da zai koma bashi da ko sisi in dai Fetta zata dawo gare sa, baya jin zai tab’a damuwa. “Fetta bata yo waya ba”, Malam ya fad’a, “Wallahi shiru kullum tsammanin kiran nata nake” Cewar Aliya, “Toh Allah yasa lafiya”, “Amin, kullum da ita nake kwana ina tashi a raina, na rasa gane dalilin ta na tafiya”, Malam yace “Ni kaina abun yana d’aure mun kai”, “Hmm”, “Allah ya tsare ta a duk inda take yasa ta dawo garemu ba da jimawa ba”, “Amin, bara na lek’a wurin Malam Habu”, “Sai ka dawo, Allah ya kai lafiya”, Ya amsa da “Amin” yana saka silifas. Fetta rayuwa mai cike da jin dad’i take cikin yan uwan ta, kaso saba’in na cikin damuwar ta ya tafi, matsalar ta d’aya Sultan da ya matsa mata lamba, har Agadez yazo wurin ta, ba k’aramin so yake nuna mata ba, but har yau babu d’igon son sa ko kad’an a zuciyar ta. Kusan awa d’aya da tafiyar Ahmad, Suraj yana zaune a wurin ya kasa aikata komai, “Ina son daidaita rayuwata, na fita daga cikin k’azamtaciyar rayuwar da na d’aura kaina” Ya fad’a zuciyar sa a raunane, Munir yazo masa a rai, shi kad’ai yake tunanin zai bashi shawarar da ta dace, Mukullin motar sa ya d’auka, ya fice zuwa gidan Munir, Yaci sa’a ya tarar dashi a gida, Suna zaune da matar sa suna hira cike da nishad’i, wani abu yaji ya tsigar masa, yana jin ina ma shine da Fetta a irin wannan yanayi, Suka gaisa ta shige ciki, Munir kallo d’aya ya masa ya hango damuwa da rashin natsuwa a tare dashi, “SS kayi rashin lafiya ne?”, “Da ciwon nayi ina tunanin zai fi mun sauk’i akan halin da nake ciki”, “Subhanallahi meke faruwa?”, “Na rasa farin cikina Munir, na rasa natsuwata, ina nadamar rayuwar da na jefa kaina, rashin Fetta a rayuwata ya jefani a matsanancin hali, ina son daidaita rayuwata Munir” Ya k’arasa cikin karyewar zuciya, Tausayin sa ya kama Munir, tsawon shekarun da suka yi bai tab’a ganin sa a yanayi irin na yau ba, Hannun sa ya kamo yace “Hanya d’aya ce ka daina fashi da makami, duk dukiyar da ka tara ta wannan hanyar, kayi sadaka dashi, ka nemi yafiyar mahaifiyar ka, ka cigaba da istigfari neman tuba zuwa ga Allah, In Shaa Allah komai naka zai warware, duk mai sab’on Allah baya tab’a ganin daidai a al’amuran sa, shiyasa abubuwa suka zo maka a haka, but idan ka tuba zuwa ga Allah zaka ga haske a rayuwar ka”, “Ba zan iya tunkarar Mama na sanar da ita, hanyar da na dad’e ina ciyar da ita, bazan iya ba Munir”, “Daurewa zaka yi Suraj, muddin baka nemi yafiyar ta ba, ba zaka ga cigaba ba, domin itama ka cutar da ita, ka yaudare ta, ta d’auka ta tsaftacciyar hanya kake ciyar dasu”, Zufa ta shiga tsattsafo masa, bai san da wane ido zai kalli Mama ya sanar da ita ba, bai san da wane baki zai furta mata sana’ar da ya dad’e yana aikatawa ba, bansan wane hali zata shiga ba idan taji. Hannun Munir yaji saman kafad’ar sa yana fad’in “Be strong Suraj”, Kansa ya d’aga a raunane, “Ka tashi kaje ka sanar da ita, zaka rage wani nauyi a tare da kai”, Ya jinjina kai yace “Nagode Munir, hak’ik’a kai aboki ne nagari, da na bi shawarar ka tun farko ban tsinci kaina a wannan yanayi ba”, Murmushi Munir yace “Ka d’auki haka bisa k’addara”, Yayi nodding kai yana mik’ewa, Ya mishi sallama ya tafi. Zuciyar sa cike da zullumi had’i da fargaba ya tura k’ofar d’akin Hajiya, Ta idar da sallar la’asar kenan tana lazimi, Gefenta ya zauna, zuciyar sa na harbawa da tsananin k’arfi, karon farko a rayuwar sa da yaji Mahaifiyar tasa ta masa kwarjini na musamman, Ta idar da lazimin ta kai dubanta gare sa, “Ina wuni?” Ya furta tamkar mai jin tsoron kalmar, “Lafiya lau, har ka dawo?”, “Eh”, “Toh Madallah”, Bakinsa yaji ya masa nauyi ya kasa k’ara cewa komai, Hajiya ta lura akwai abunda yake son sanar da ita, Ta nisa tace “Akwai wani abu ne?”, “Uhmm d…ama da…ma”, Ya fad’a cikin sark’ewar murya, “Dama me? Ka fad’a mana” Fargabar sa ke k’aruwa, zuciyar sa na tsananta bugawa, K’ok’arin tattaro kuzari da k’arfafa ma kansa gwiwa yayi yace “Tunda na taso naga irin tsangwama da hantara da muke fuskanta daga dangin Abba, dama yadda ake mana kallon k’ask’anci kasancewar bamu dashi, na k’uduri a raina sai nayi kud’i, dan a ganina kud’in sune komai, su kad’ai mutane ke darajawa, su kad’ai zanyi na zama wani abu a duniya a rik’a mana kallon mutane masu daraja, a lokacin da Abba ya rasu, rayuwa ta k’ara tsananta a garemu, naga irin wahalar da kike sha da k’annena, da wulak’ancin da muka k’ara fuskanta wurin dangin Abba, zuciyata ta k’ara hassasa mun neman kud’i ko ta wacce hanya, dan na d’aga darajar ki na miki dukkan gata, na maye ma k’annena gurbin Mahaifi na musu gata, mutane su fara rab’ar ku kamar kowa, furucin Kawu Sule a lokacin da muka je gidansa ya k’ara tunzara ni, “A lokacin da na tafi lagos, tashin farko na had’u da wani Alhaji wanda sana’ar motoci yake, ya jawoni jiki, ya d’auke ni aiki kamfanin sa, sai dai albashin da nake samu dubu hamsin a wata, wanda na raina, ina ganin har yaushe zan tara irin kud’in da nake burin mallaka, na soma tunanin wata hanya da zan samu kud’i cikin k’ank’ani lokaci, sam na manta Allah ke azurta bawa a lokacin da yaso, ban kuma mik’a al’amurana da Allah ba, duba da ba wani ilimin addini ne dani, ana haka Ahmad yazo siyan mota, ni na mishi jagora wajan Alhaji, daga haka muka k’ulla alak’a mai k’arfi, har nake sanar dashi burina na son tara d’umbin dukiya, Yayi murmushi yace Akwai hanya mafi sauk’i da zan zama hamshak’in mai kud’in cikin k’ank’anin lokaci sai dai tana da had’ari, nace wacce hanya ce, Yace fashi da makami, na kid’ima a lokacin, amma da ya nuna mun alfanun da zan samu, a take na amince, daga ranar na tsunduma harkar fashi da makami, wanda da sana’ar na zama abunda na zama yau, ki yafe mun Mama, Dan Allah ki yafe mun, na ciyar daku, na tufatar daku ta hanyar haram” Ya k’arasa yana fashewa da matsananincin kuka Hajiya fuskarta ta jik’e shark’af da hawaye, jikinta na kyarma tamkar wacce ake zubawa k’ank’ara a jiki, yayin da take jin zantukan sa tamkar almara, tana jin ina ma mafarki take ta farka, a tsawon rayuwarta bata tab’a cin karo da tashin hankali irin yau ba, Yaron ta, jininta ya kasance dan’ fashi, Sunan Allah take ambato ko zata samu sassaucin abunda take ji a zuciyata, Jin bata ce komai ba, hankalinsa ya k’ara tashi yace “Mama Dan Allah ki yafe mun ko rayuwata zata daidaita” Cikin shesshek’ar kuka tace “Hadda laifina Suraj, ina da laifi, ban tab’a tuntub’ar ka kan sana’ar ka ba, bana sa ido akan me kake ciki, ban tab’a bin diddik’in sana’ar da kake a lagos ba, ko da kayi kud’i lokaci d’aya ban damu da sanin taya ba, abunda ka gaya mun shi nake yarda, nayi kuskure na rashin saka ido sosai kan al’amur…..”, Ta kasa k’arasawa sakamakon kuka da yaci k’arfin ta. STORY CONTINUES BELOW Suraj shima kukan yake, kusan minti goma babu mai lallashin wani kafin ya nisa yace “Na tuba na daina fashi Mama, zanyi sadaka da dukiyata, na gina tsaftaciyyar rayuwa”, “Na yafe maka Suraj, Allah ya k’ara shiryar da kai, Ya baka ikon daidaita rayuwar ka” Ta fad’a tana tsagaita kukan ta, “Amin Mama, nagode nagode, ki saka baki Fetta ta dawo gareni Dan Allah, tasan ko ni waye shiyasa ta gujeni”, Hajiya tace “A ina zan ganta wacce bamu san inda take ba”, “Tana Agadez, iyayenta sune masu sarautar Agadez, Fetta yar’ dangi ce, danginta na uwa da uba masu arzik’i ne sosai, k’addara ta gifta mahaifinta yazo gadi k’asar nan”, Hajiya ta jinjina kai cike da al’ajabi tace “Shikenan sai mu shirya muje can d’in, zan sanar dasu Aliya”, Ya shiga zuba mata godiya, uwa kenan. Suraj nauyin dake k’irjin sa ya ragu sosai, yana jin wani b’angaren na damuwar sa ya ragu, Part d’in sa ya nufa, duka takardun k’adarorin sa ya kwasa, hadda na gidan da suke ciki, Ya nemi Munir da taimakon sa yayi sadaka da duk dukiyar sa da ya mallaka, bai tsira da komai ba, gidan marayun sa ya mallakawa Munir baya so ya salwanta yana tausayin marayun dake ciki, Munir ya basu k’aramin gidan shi su zauna a ciki, da kud’i dubu d’ari biyar har ya samu sana’ar yi, Haka suka tattara suka koma, Suraj ya fahimci duniya ba’a bakin komai take ba, Duk tarin dukiyar sa yau ya wayi gari bashi da ko naira, har k’asan zuciyarsa yana jin hakan yafi masa kwanciyar hankali, yayin da nake jin ya rabu da najasa, Da yawa mutane sun d’auka k’asar Suraj zai bari, ganin yayi sadaka da gidan sa, ya sallami duka ma’aikatan sa har direbobin sa. “Umma wai kin ji Suraj yayi sadaka da gidan sa, ya sallami duka ma’aikatan sa, ina jin k’asar zai bari” Cewar Bilkisu, “Ya zama dole na tashi tsaye, idan ya bar k’asar nan yaushe zamu k’ara ganin sa”, Cewar Aunty Jummai tana mik’ewa tsaye, “Umma kiyi yadda zakiyi ya tafi dani”, “Baki da damuwa”, Ta jawo mayafinta dake shanye a igiyar tsakar gidan, ta yafa ta fice. Aunty Jummai ta nad’e zaninta tana yankar dajin Allah da babu motsin bil adama, sai da tayi tafiya mai nisa, ta kawo bakin wani k’aton k’ugu, Ta juya baya ta shiga ciki, K’asarmun boka ne zaune da kayan tsibbace tsibbace a gabansa, ta duk’a gabansa tamkar zata kifa, Da hannu ya mata alamar ta tashi, “Meke tafe dake?” Ya fad’a cikin muryar sa mai firgitarwa, “Ya kai mai cika aiki, mai share kukan mu ina so ai mun bak’in aiki da zai juyo da hankalin Suraj gaba d’aya zuwa ga ya’ta, a saka masa mummunar k’iyayyar Fetta kuma ta haukace ta shiga duniya ta yadda ko labarinta ba za’a sake ji ba”, Dariya yayi wacce sai da gurin ya amsa, Yace “Ki dawo gobe ki karb’i aikin ki”, Ta jinjina kai tana masa godiya, Yayi saurin katse ta “Rik’e godiyar ki, ba yanzu ba”, “Toh” Ta fad’a tana mik’ewa, ta fita da baya. Aliya da Mallam zufa ke tsaffafo musu bayan sun gama jin zancen Hajiya, bata b’oye musu komai dangane da halayyar Suraj ba, ta aminta dasu, tasan ba zasu tab’a fallasa sirrin ta ba, Mallam ya nisa yace “Godiya zamu yi Allah tunda har Allah yasa ya shiryu, ya gane gaskiya, sai mu cigaba da masa addu’a Allah ya k’ara shiryar dashi, Fetta kuma Alhamdulillah nayi matuk’ar farin ciki data sadu da danginta, abunda tayi kyauta da bata fallasa sirrin mijin ta ba, sab’anin wasu matan”, Aliya tace “Tabbas Fetta mace ce ta gari, sai dai nasan zai yi wuya ta yarda ta komawa Suraj, duba da tun farkon auren ba auren soyayya suka yi ba, kuma tasha kyara da hantara daga gare sa”, Hajiya tace “Shi Suraj ya wulak’anta ta” Aliya ta gyad’a kai tace “K’warai da gaske, ban sani ba ko daga baya sun daidaita kansu”, Hajiya ta jinjina kai cike da takaicin Suraj, ta kuma k’ara jin k’aunar Fetta duba da bata tab’a kawo k’arar sa ba. Tura k’ofar da k’arfi, yasa Su’ad da ta fara bacci tashi a firgice, Adnan ke bin ta da kallo mai cike da tsana yace “Ya kin samu kud’in ko kuwa?”, “Ban samu ba”, Ta bashi amsa cike da takaici, Saukar mari taji a fuskar ta, “Dan uwarki ni kike ba amsa haka, tsaran wasan ki ne, shegiya mara tarbiya, dama ina zaki yi tarbiya kina bin saurayin hotel, kije na sake ki saki uku”, Hannu ta d’aura a kai tana fashewa da matsanancin kuka, Ya fice abun sa ya barta. “Tumuqqartin meyasa bakya son Sultan, wallahi yana son ki sosai” Cewar Sanah, Fetta dake shan kayan marmari ta gutsira apple tace “Har yanzu ban gama shawara ba”, “Uhmm ko dai soyayyar baban Mimi ta kasa barin ki”, Murmushin takaici tayi tace “Mamacin, ai ni nama soma mantawa dashi”, Sanah tayi dariya ba dan ta yarda ba, Maganar Sanah ta tado mata wani rauni a cikin zuciyarta, kayan marmarin taji sun fita ranta, ta mik’e ta shiga d’aki. Sallamar Hajiya ta fargar da Suraj nisan tunanin da ya tafi, tun d’azu yake jiran dawowar ta, ya mata tuni kan tafiyar su Agadez, “Sannu da zuwa Mama”, Ya fad’a, Ta amsa da “Yawwa” tana zama kan kujera, Ya nisa yace “Kinyi magana dasu Mallam”, Tayi nodding kai, “Uhmm nace sun yarda zasu je Agadez d’in”, “Ai babu maganar zuwa, na fasa, ina ga ka hak’ura da Fetta kawai, naga ba sonta kake ba, yar’ ka kumq za’a karb’u maka nan gaba idan ta k’ara wayo”, A rud’e yace “Wallahi ina son ta Mama, ina k’aunar ta”, “Kana son ta ka dinga wulak’anta ta, k’arya kake duk wanda kake so ba zaka wulak’anta shi ba”, “Nayi dana sani wallahi, am regretting everything, ina masifar k’aunar ta, wallahi zan iya rasa raina a kan ta”, Duk da taji tausayin sa ta dake tace “Babu inda zanje, ka hak’ura da ita kawai” Ta shige d’aki ta saka key, Suraj a wurin ya zube cikin tsananin tashin hankali. Kusan minti talatin yana durk’ushe a wurin ya kasa aiwatar da komai, Hajiya tun shigarta bata sake bi ta kansa ba, a ranta ta k’uduri dole ta k’ara koya masa hankali, ya gane kuskuren sa, yasan kowane dan’ adam nada daraja duk rashin sa.+ Shigowar Samee ya fargar dashi, ya d’aga rinannun idon sa ya kalle ta, Cike da mamakin yanayin sa tace “Ya Suraj ina wuni?”, Da kai ya amsa ta, Ta k’arasa k’ofar d’akin tana knocking, “Waye?” Cewar Hajiya daga ciki tana kyautata zaton Suraj ne, “Mama nice”, “Samee kin dawo”, “Eh”, Ta taso ta bud’e mata k’ofar, Suraj yayi saurin rufa mata baya zuwa cikin d’akin, Ganin haka yasa Samee ficewa, Gwiwoyinsa ya kai k’asa yana had’a hannayen sa guri d’aya yace “Dan girman Allah Mama ki taimake ni Fetta ta dawo gare ni, wallahi na tuba, bazan sake wulak’anta kowa a rayuwa ta ba, nayi alk’awari zan kula da ita, zan yi k’ok’arin wanke laifina na baya, bazan sake makamancin sa ba”, Uwa da da’ sai Allah, tausayin sa taji ya lullub’e ta, Tace “Tashi shikenan zamu je Agadez, na saka baki ta yafe maka, amma ka kiyaye gaba, ko da yake yanzu ai ta wuce sanin ka, tafi k’arfin ka”, Tabbas Hajiya gaskiya ta fad’a yanzu Fetta ba ajin sa bace, tafi k’arfin sa, ya katse tunanin sa ta hanyar yi wa Hajiya godiya. Su’ad da k’yar ta samu kud’in mota dubu biyu na zuwa Kano wurin wata mak’wabciyar ta a gidan da suka zauna farko, Gidansu ta nufa, tayi mamakin ganin babu security bakin gate, ta tura k’ofa da zumar shiga, Mai gadin da bata sani ba ya taso yace “Baiwar Allah wa kike nema?” Da kallon mamaki tabi sa tace “Amma kai bak’on zuwa ne koh?”, Ya gyad’a mata kai yace “Eh amma babu kowa a gidan, mutanen ciki sun tashi”, “Su Hajiya sun tashi ba sanarwa, ko da yake sai muyi sati bamu yi waya ba”, Ta fad’a a ranta, ta juya gare sa tace “Ina suka koma?”, “Rijiyar zaki”, Ta jinjina kai ta masa sallama ta tafi. Da tambaya ta kai gidan dasu Hajiya suka koma, cike da mamakin ganin gidan ta shiga, yayin da zuciyarta ke tabbatar ma ba nan suka dawo ba, Fitowar Samee ya gaskata mata nan d’in ne, “Ya Su’ad oyoyo” Ta fad’a tana rungume ta, “Nan kuka dawo Samee?”, “Eh” Ta fad’a tana gyad’a mata kai, Suka shiga ciki, A falo suka tarar da Hajiya rik’e da charbi a hannu tana lazimi, Ta fad’a jikinta tare da fashewa da kuka, “Lafiya daga shigowa sai kuka, ni dallah d’aga ni”, Cewar Hajiya tana k’ok’arin ture ta daga jikin ta, wanda take kyautata zaton dan taga gidan da suka dawo ne take wannan kukan, Ta sake matse ta tana tsagaita kukan, “Kukan me kike?, ko kukan mun rasa komai”, Mamaki k’arara kan fuskar Su’ad ta d’ago tana kallon Hajiya, sun rasa komai kamar ya, “Mama ban gane inda magangun ki suka dosa ba”, Ba tare da wani tunani ba, ta zayyane mata komai, kukan ta ne ya tsananta, lallai ta yarda duniya ba a bakin komai take ba, kowa yayi d’amara domin ta ya kwance, Kud’i da dukiyar da suke tak’ama dashi ashe duk bata hanyar Allah aka tara ta ba, shiyasa kada ka tab’a son mutum dan dukiyar sa baka san taya ya same ta ba, ka godewa Allah da abunda ya baka, Cikin shesshek’ar kuka tace “Hak’ik’a mun yi kuskure da muka d’auki duniya da zafi, muka d’auka kud’i sune komai, gashi Adnan ya yaudare ni ashe talaka ne bashi da komai, ya sakeni saki uku”, “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un” Hajiya ta shiga jerawa, “Ina nadama sosai a rayuwata Mama, ina ma ana mayar da hannun agogo baya, na gyara rayuwata ta baya, da na sani Ya Bello na aura, mutum mai cikar kamala da kyawawar d’abi’a nak’i sa saboda abun duniya, Mama wallahi yanzu ko mai napep ne zan iya aura in dai zan samu kwanciyar hankali, kud’i basu ne zaman aure ba” Ta k’arasa tana sake zubewa jikin Hajiya tana kuka. Feena fitowar ta daga kitchen kenan ta gama abincin rana, K’anwar Fahad ta shigo tana yatsina fuska tace “Mummy na kira”, Ta amsa da “Toh”, gabanta ya fad’i tasan kiran ta baya tab’a zama alkhairi, tsana k’arara take nuna mata, Mayafinta ta yafa ta nufi b’angaren Mummy, A falo ta tarar da ita zaune sauran yaranta mata uku suna zagaye da ita, suna hira, STORY CONTINUES BELOW Har k’asa ta duk’a ta gaishe ta, ba tare da ta amsa ba, ta jefa mata wani matsiyacin kallo tace “Ki shiga kitchen ki dafa mun naman kai irin wanda kika aiko mun ranar nan”, Ta amsa da “Toh” cike da ladabi, ta mik’e ta shiga kitchen, Dukkan su suna bin ta da harara, yayin da suka jefa mata bak’ak’en maganganu, Duk iya k’ok’arin danne zuciyarta ta kasa, sai da ta tsinci kanta da zubar da hawaye, yayin da take tuna irin cin kashin da suke ma Fetta, ashe haka abun yake, gara ma Fetta Mama na son ta, ita har Mahaifiyar sa ta tsane ta, babu mai sonta a dangin, ko shakka babu alhakin Fetta ke bin ta, Shigowar Khairat ya katse mata tunani, Attagurun data gyara zata yi amfani dashi ta d’auka, “Khairat amfani zan yi dashi”, wani banzan kallo ta watsa mata tace “Ki sake gyara wani”, “Ke dai ki gyara, sanin kan ki Mummy bata son jira”, Tsaki taja tace “Dallah Malama kar ki dameni”, Ranta ya masifar b’aci ta k’yaleta ta shiga gyara wani, sai da ta gama, Khairat ta kai hannu zata d’auka, Feena ta janye tace “Me zaki yi kuma?”, “Amfani zan yi dashi waccan ba zai ishe ni ba”, “Aikuwa baki isa ba wallahi” Cewar Feena rai a k’ufule, Khairat ta shiga k’ok’arin fisgewa, Feena naja, ya b’are ya zubarwa Khairat a ido, ta tsala uban ihu, kan ace me kitchen d’in ya cika da mutanen gidan, suka yi kanta suna tambayar lafiya, Tana tsala ihu tace “Feena ce ta d’ibi attarugu ta watsa mun a ido, dan kawai nace ta sammun nasa a indomie”, Kafin Feena ta kare kanta, Mummy ta fisgota ta falla mata mari biyu, sai da kanta ya sara, sauran yan matan suka yi kanta da duka, sai da suka mata ligis, Khairat nata dariya k’asa k’asa, kad’an ya shigar mata ido, tsabar iya sharri ne, “Wallahi yau sai kin bar gidan nan, muguwar yarinya ba zaki la’anta mun yara ba, idan ruwan idon ta ya tsiyaya fah” Cewar Mummy cike da masifa, Feena kam sai zubar hawaye take, ana haka Fahad ya shigo, Ganin Feena durk’ushe tana kuka yayi kanta cike tashin hankali, tsawar Mummy ta tsayar dashi, “Kada ka kuskura ka nufe ta, wannan azalumar matar taka, dole yau tabar gidan nan, shiyasa naso ka auri yar’ uwar ka, ka k’i gashi ka jajubo mana bare, maza d’auketa ka mayar da ita gidan su” Cikin tsananin tashin hankali ya amsa da “Toh” baya tab’a iya bijirewa umarnin Mahaifiyar sa. Aunty Jummai ta koma wurin boka, ta karb’o mugun sihiri, ya fad’a mata yadda zata yi, ya mata kashedi akan ta kiyaye kada a samu kuskure, ta dawo gida tana jiran lokacin aiwatar yayi. Fahad haka ya d’auki Feena ya nufi gidan su, Mai gadi ya sanar dasu kamar yadda ya sanar da Su’ad, Feena ta shiga tashin hankali da ta riski labarin abunda ya faru, ta kuma fuskanci duniya ba a bakin komai take ba, Ta b’angaren Hajiya addu’a tayi, Allah ya bata ikon cinyen jarabawar nan, ta yarda da k’addara, Allah yana jarabtar bawan sa dan yaga k’arfin imanin sa, yaranta duka kowane da tashi matsala, tana rok’on Allah ya kawo musu maslaha. Suraj wunin ranar a masallaci ya wuni, yana karatun Qur’ani, da addu’o’i had’i da tuba zuwa ga Allah, sai bayan sallar isha’i ya tari napep nufi gidan su Aliya, Yau Suraj mai convoy na motoci shine cikin keke napep, rayuwa kenan, yaje musu kan maganar zuwa Agadez, sun basa tabbacin zasu je, wanda hakan ya masa dad’i, yana da yak’inin ko dan ganin idonsu Fetta zata yafe masa, ta dawo gare sa, da tunanin haka ya koma gida. Su Feena da ya tarar gida, da labarin abunda ya faru gare su, ya tab’a shi sosai, ya tausaya musu, but yafi tausayin Mahaifiyar sa, yana addu’ar Allah ya warware musu matsalolin su. Suraj ya shirya musu tafiya Agadez gaba d’ayan su, Su’ad da Feena suka rok’i suna son zuwa su nemi yafiyar ta, basu da tabbacin zasu yarda ta dawo Nigeria, Safiyar Alhamis suka d’auki shatar mota sharon zuwa jamhuriyar Nijar. Fetta yau sashen Amanukal ta wuni, suna hira da matar sa dasu Abu talib a babban falon sashen, kayan marmari da na malak’ushe a gaban su suna sha, Baiwa daga b’angaren Azagas ta shigo, cike da ladabi ta gurfana gabansu tace “Ana kiran Fetta”, Fetta ranta taji ya b’aci a zaton ta Sultan ne, ya sanar da ita zuwan sa yau, “Kice ina zuwa” Ta fad’a fuska sam ba annuri, Abutalib yana dariya yace “Ko dai Sultan ne yazo, ni na rasa meyasa bakya son sa, bayan bashi da wata makusa”, Harara ta galla masa, tana mik’ewa, sam bata iya wulak’anta dan’ adam ba, da ba abunda zai hana ta k’ara minti talatin kafin taje gare sa. Yawan takalman da taci karo dasu bakin k’ofar shiga babban falon Azagas yasa k’irjin ta tsananin dokawa, kar dai ace Sultan ya gaji da jiran amsar ta ya turo magabatan sa, cike da fargaba ta shiga falon, idonta ya sauka kan na Suraj, wanda tunda aka tafi kiranta, ya zubawa k’ofar ido yana son tozali da ruhin tasa, Saurin kawar da kanta tayi gefe, yayin da zuciyarta ke tsananta bugawa, wani b’angare kuma takaicin sa ne fal, Su Hajiya sun shagala kallon dukiya irin tasu Fetta suna jinjina al’amarin ubangiji yadda Fetta ta kasance cikin ahalin, sam basu ji shigowar ta ba, Dubanta ya kai kan Aliya, sanyi da farin ciki taji ya lullub’e ta lokaci d’aya, a guje ta fad’a jikin ta tana fad’in “Umma na”, Aliya ta k’ank’ame ta tana jin tsantsar k’aunar Fetta, kallo ya koma gare su, Azagas na kallon su tana murmushi, Kusan minti biyar suna rungume da juna kafin ta sake ta, ta juya tana bin kowa da kallo tana gaishe sa, Tayi mamakin ganin su Feena da kuma yanayin fuskokin su yadda suke washe mata baki, Bayan sun natsa, Azagas tace “Fetta meyasa kika b’oye mun mijin ki na raye?”, Fetta ta sunkuyar da kai, tana had’iye wani k’ulloto dake taso mata, Hannun Azagas taji cikin nata, Tace “Ki sanar dani komai Fetta, ina son ji daga bakin ki”, Hakanan taji bata son fallasa sirrin Suraj, Cikin sanyin murya tace “Rabuwar aure ta shiga tsakanin mu, ya sake ni, bana son ku mun kallon wacce ta kashe auren ta, haka kuma bana fatan komawa gidan sa”, Mamakin furucin ta ya kama kowa a wurin duba da yadda ta rufa masa asiri, sab’anin Azagas da bata san komai ba, Hajiya dasu Aliya mamaki biyu ya had’ar musu, na jin ya saketa, Hajiya ta kai duban ta gare sa “Yaushe ka saketa? Wane ganganci ya kai ka ga sakin ta”, “Ita buk’aci haka, wallahi ita ta buk’ata”, Suraj ya fad’a cikin rawar murya, “Tabbas ni na buk’ata dan bana son cigaba da zama dashi” Cewar Fetta babu alamar tsoro ko shakku a tare da ita, Azagas tace “Akan wane dalili?”, “Kiyi hak’uri Tanti bazan iya sanar dake komai ba”, Ta fad’a tana mik’ewa ta bar falon, kowa yabi bayanta da kallo, Suraj zufa ta shiga karyo masa duk da sanyin Ac dake falon, ganin har yanzu babu alamar saukowa a tare da ita. Hajiya ta numfasa tace “Muna neman alfarma a lallasheta ta yarda a mayar da auren ko dan yarinyar dake tsakanin su”, Azagas tace “Ba zamu tilasta mata ba, abunda take so shi muke so, sai dai ko zaku rok’eta idan zata amince”, “Shikenan babu damuwa” Cewar Hajiya, Azagas ta juya kan Aliya da Mallam tana musu godiyar kulawar da suka ma Fetta na tsawon lokaci, Suka nuna babu komai, Allah ne ya had’a jinin su da Fetta. Fetta wacce tayi nisa a tunani, shigowar Aliya ya fargar da ita, Da murmushi d’auke a fuskar ta tace “Umma”, “Na’am Fetta, shine kika gudu kika bar mu ko”, Tayi dariya tace “A’ah Umma”, “Hakane mana” Tayi murmushi ta kawar da zancen ta hanyar cewa “Ina su Ali”, “Suna can k’ok’i na baro su”, “Shine baki zo mun dasu ba”, “Rufa mun asiri, ina zan iya da jigilar su”, “Kai Umma”, “Kema kin san su basa zama wuri d’aya”, “Ni dai da an kawo mun su”, Tace “Uhmm, Fetta meyasa baki sanar dani ba bayan kin gane waye Suraj”, Da kallon mamaki tabi Aliya, “Dukkanmu munsan ko waye Suraj, Mahaifiyar sa ta sanar damu, bayan ya sanar da ita”, Ta numfasa tace “Bana son Hajiya ta shiga tashin hankali duba da halaccin ta gare ni, shiyasa na zab’i nisanta kaina dashi ba tare da na sanar da kowa ba”, Aliya ta jinjina kai tace “Zuciyar ki nada kyau Fetta, samun irin ki nada wuya” “Tabbas Fetta halayyar ki ta bambamta da sauran mutane” Suka ji muryar Hajiya dake shigowa, wacce tun kusan fara zancen su take tsaye bakin k’ofa tana saurare, ta k’araso ciki tana kama hannun Fetta tace “Nagode da halaccin ki gareni Fetta, nagode da baki fallasa sirrin da’na ga duniya ba”, Da murmushi tace “Babu komai Hajiya, nice da godiya, kin mun halacci a rayuwata, baki duba matsayina ba da rashin asalina kika had’i aure da dan’ ki mafi soyuwa a gare ki”, “Duk da haka nagode sosai Fetta”, “Babu komai Hajiya”, Ta nisa tace “Ina rok’on ki alfarma a karo na biyu, duk da nasan ba’a kyauta miki ba, ba’a miki adalchi ba, amma ki dubi girman Allah ki yafewa Suraj, ki dawo gare sa, yayi nadama, yayi sadaka da duka dukiyar sa, ya koma tsaftaciyar rayuwa”, Har cikin zuciyarta taji dad’in jin ya tuba, amma bata jin zata tab’a komawa gare sa, har abada ba zata daina kallon sa a matsayin wanda yayi silar kashe mahaifin ta ba, kuma ma meya sa zai sa a kashe iyayen Yasmeen, Hajiya ta katse mata tunani ta hanyar cewa “Dan Allah ki yafe masa Fetta” Ta numfasa tace “Na yafe masa duniya da lahira, amma bazan iya komawa gare sa ba”, “Saboda me?” Hajiya ta tambaya hankalinta yana soma tashi, sanin farin cikin Suraj a yanzu Fetta, “Ina da wanda nama alk’awarin aure” Ta tsinci kanta da furtawa, “Allah ya tabbatar da alkhairi”, Hajiya ta fad’a a raunane, ba zata ga laifin ta ba, ko ba komai ta yafe masa.