FETTA CHAPTER 6

FETTA





CHAPTER 6




Sallama tama Hajiya Tumba da alk’awarin gobe zata dawo. +

Da haushin magangunan Suraj ta dawo gida, A tsakar gida ta tarar da Aliya tana yanka alayyahu, “Sannu da aiki Umma”, ” Yawwa Fetta, kin dawo?”, “Eh”, Ta fad’a tana zama kan kujerar tsugunno, ” Ya kika baro Hajiyar?”, “Da sauk’i, ta buk’aci na zauna da ita har zuwa lokacin da za’a sallame ta”, ” Toh ya kika gani zaki iya?”, Ta d’aga kanta sama, “Kinsan fah kina jarabawa?”, ” Zan iya Umma, ai muna samun interval, Hajiya Tumba nada kirki ina so na samu ladar jinya”, “Toh Shikenan, idan Mallam ya dawo zan sanar dashi”,

“Kawo na yanka miki”, ” A’ah bar shi ai na kusa”, Mik’ewa tayi ta shiga d’aki.

Baban Bilkisu ya kira Suraj ya tambaye shi ba’asin sakin, Ya fad’a masa bai b’oye mishi komai ba, Ya matuk’ar girgiza da jin abunda ta aikata,

Sun ga ruwan bala’i da tijara, Daga Bilkisu har Aunty Jummai ya had’a yayi wa tass, Yace kuma wallahi ba zai ciyar da ita ko k’wayar shinkafar sa ba, Lamuni d’aya zai mata na zaman gidan, Aunty Jummai kam cewa tayi sharri ake wa yar’ta, taji zata kula da cin ta da shan ta.

Labari ya kaiwa su Kawo Sule, “Zan so naga idon Jummai ta gama yi mana dariya da tijara, ga ranar da ake gudu, Bilkisu da aikata mad’igo har an sako ta”, Ta fashe da dariya, Karima tace ” Allah ya sawwak’a”, Taja hannun dan’ ta suka fita, Gaba d’aya tayi sanyi tun abunda Bash ya aikata mata,

Aunty Yelwa murna take sosai da faruwar haka, Kawo Sule ma yayi Allah ya k’ara, Da yawa yan’ uwa Allah ya k’ara suke yi, Jummai ba irin wulak’ancin da bata musu ba, Tana ganin tafi k’arfin su yar’ ta na auren Young billionaire.

Sallama Yelwa ke tayi tun daga bakin k’ofa, Bilkisu dake kwance tsakar gida da d’aurin gaba(Haka take wuni saboda k’onuwar dake bayanta, ga shatin duka duk sunyi rud’u rud’u)
Ta amsa sallamar,

  Jummai ta fito, Ganin Yelwa ta bi ta da harara, Tasan ba zuwan arzik’i tayi ba,

   “Ya da harara Jummai, ni fah jaje nazo yi muku”, ” Baki zo sanya alkhairi ba lokacin biki sai yanzu da aure ya mutu”, “Kinsan fah lokacin muna cikin jimamin na Karima”, Aunty Jummai tace ” Uhmm, ga tabarma ki zauna toh”,

   Ta zauna tana fad’in “Haka Suraj ya mata, Gaskiya ya d’auka da zafi wai, amma dole zai yi haka ka kama matar ka na aikata mad’igo”, ” Ni fah bana son k’ananun maganganu da k’ala sharri, ya’ta bata ga mad’igo ba”, “Ohh jama’a da k’in gaskiya suke, kowa dai yasan abunda yar’ki ta aikata kenan aka sako ta”, ” Kina da Shaida na ta aikata, ke kuwa yar’ki da yake karya ce akan bin maza, ai hadda guzuri tayi”

   Nan suka shiga yi wa juna gori, mak’ota ne suka jiyo su, Suka shigo suka raba su, aka fitar da Yelwa tana ta zage zage, haka aka rabu dai ba arzik’i.

    Zulaihat da labari yaje wa iyayen ta, korar ta Mahaifin ta yayi sai gidan kakannin ta na gefen uwa ta koma, A can take jinya.

    A daren aka shiga yi wa Hajiya tiyata, Su’ad, Feena da Ya Suraj suna asibitin hankalin su ya kasa kwanciya, addu’ar nasara a operation d’in suke, Suraj ya yanke shawarar idan bai yi ba, Zai fitar da ita k’asar, Bai sanar da kowa ba a yan’uwa ya kuma hana su Feena fad’a, Baya so a zo a cika asibitin a isheta da hayaniya, Idan operation d’in is successful zai fad’a musu su zo dubiya, shima dan kar Hajiya tayi fad’a, Tayi ciwo bai sanar da yan’ uwa ba.

STORY CONTINUES BELOW


     K’arfe uku na dare likitocin da suka shiga tiyatan suka fito, A rud’e Suraj yayi wurin babban Likitan, “Ya idon nata?, kun samu nasara?”, Murmushi yayi Yace ”  The operation was successful, idonta zata dawo aiki In shaa Allah after 24hours”, Hannun sa ya d’aga sama ya furta “Alhamdulillah”, Ya kama hannun Dr Yace ” Thank you soo much Dr”, “It’s our duty”,

    Zama yayi akan kujerun dake passage yana hamdala.

    Dressing d’in ta suka k’ara yi, Suka fito da ita daga theatre room zuwa d’akin da take, Suraj ya shiga da saurin sa, An saka bandage an zagaye idon ta,  tana bacci, Hannun ta ya kama ya sumbata ” Sorry Mum, Allah ya baki lafiya”, Feena da Su’ad suka amsa da “Amin”,

    Fetta tun da tashi sallar asuba bata koma ba, Karatun Qur’ani take har gari ya waye, Ta shiga kitchen ta d’aura ruwan zafin kunu.

    Bakwai na safe ta kammala komai tayi shirin ta, Da wuri take son zuwa tasan Hajiya na buk’atar taimakon ta.

    Kaya kala biyu ta d’auka sai brush, Maclean da soson wanka ta saka a yar’ k’aramar jaka.

     Da ta fad’awa Mu’azzam zancen zuwan ta yaso hana ta, Ta nuna mishi aikin lada ne, Ya amince tare da mata fatan alkhairi.

    Rana ta fara b’ullowa, bayan sunyi karin kumallo na kunu da k’osai, Tace ” Zata tafi”, Malam yace “Ki kula da kan ki Fetta, duk da bani da shamaki akan halayyar ki, ki k’ara lura kinsan mu’amala da masu kud’i”, Tace ” In Shaa Allahu Malam”, Ya zaro d’ari biyu ya bata yace tayi kud’in mota, Tasa hannu biyu ta karb’a ta mishi godiya, Aliya ta mata rakiya har k’ofar gida, Tana ji zata yi kewar ta, wannan shine karo na farko tun zuwan ta gidan da zata kwana wani wuri.

      A bakin gate na asibitin Standard mai napep ya ajiye ta, Ta sallame shi ya wuce, Ji tayi an rugume ta, Ta juyo taga Yasmeen, Mamaki ne ya cika ta, “Fetta dama kina nan, ina kika tafi, munyi ta neman ki, har muka fara zargin ko yan fashin suka tafi dake”, ” Hmm dogon labari ne, Ashe basu kashe ki ba”, “Eh Mummy da Daddy sai Ya Sadeeq kad’ai suka harba”, Ta k’arasa da hawaye.

    Itama Fetta hawayen taji sunzo mata tuna mahaifin ta, ” Mutanen nan sun zalunce mu, wata shari’a sai a lahira”, Cewar Yasmeen, “Allah ya saka mana akan su”, Fetta ta fad’a tana sharar k’walla, “Amin”, ” Kayan ki da na Mahaifin ki suna nan a ajiye, kullum fatana na ganki na baki su”, Fetta tayi murmushi tace “Allah sarki, ai yanzu duk sun mun kad’an, kuma duk tsummokara ne, sai dai na Addani na ajiye dan tahiri”, ” Ga number wayata na baki sai kizo gida ki karb’a”, Ta bata wayar ta, ta saka mata suka yi sallama, Kowacce na mamakin girman da d’aya tayi.

   Ta shiga asibitin rai a jagule, Ganin Yasmeen ya tuna mata da mahaifin ta, Ba zata tab’a gafartawa wanda ya kashe shi ba.

    Da sallama ta shiga, Feena kad’ai ta tarar a d’akin, Taji dad’in rashin ganin sa, Duban ta takai kan Hajiya, Cike da tausayawa tace “Aiki aka mata?”, ” Eh” Feena ta bata amsa a dak’ile, “Allah ya bata lafiya”, ” Amin” Ta amsa can ciki.

    Zama tayi k’asan carpet shiru, wayarta ta fitar daga cikin jaka, Ta shiga game.

  Feena tuni bacci ya d’auke ta a wurin, dan jiya basu yi bacci ba.

     Motsi Hajiya tayi, Tana k’ok’arin bud’e ido taji a rufe, Salati tayi ta sanar da ubangiji, Jin muryar ta Fetta ta d’ago tace “Sannu Hajiya, kina buk’atar wani abu?”, ” Meye aka saka mun a ido?”, “Bandage nasan zuwa anjima zasu zo su cire, ki cigaba da gani kamar da”, ” Allah ya yarda Fetta”, “Amin, ko zaki shiga band’aki”, Ta d’aga kanta sama,

Ajiye wayar tayi, Ta k’arasa bakin gado ta kama ta zuwa band’aki, Ta juya baya tare da d’an karu k’ofa tana jira ta gama, Tace ta gama, Ta rik’ota, Daidai k’ofar santsi yaja su, Fetta sai jin tayi a k’asa, Hajiya Suraj ne yayi saurin tare ta,

     Bata dawo daga rad’adin fad’uwar ba, Taji tsawar sa har cikin k’wak’walar ta ” Ke Mahaukaciyar ina ce da bakya kallon gaban ki, da wani abu ya sami Mahaifiyata sai kinyi dana sanin zuwan ki duniya”

    Kalmar Mahaukaciya ke mata yawa a kai, ba’a tab’a fad’a mata kalmar da ta mata zafi irin wannan ba, Runtse ido  tayi cikin jin zafi, Zuciyarta banda tafarfasa ba abunda take, bai duba fad’uwar da tayi ba, sai kiran ta Mahaukaciya, taya da sanin ta zata illata kanta da Mahaifiyar sa, Ji tayi ba zata iya cigaba da kula da ita ba.

    “Haba Suraj, ka duba itama fah ta fad’i, ba da sanin ta ba”, ” Ganganci ne, ya kama ta tasan aikin ta, ba zan lamunci ganganci a aikina ba”,

   A fusace ta mik’e “Kada ka k’ara danganta kula da Hajiya da nake, da aikin ka, ba dan kai nake yi ba kuma ba zan tab’a yi dan kai ba”, Tana fad’ar haka tayi hanyar fita,

   Mamaki ne ya cika sa yadda take gaya mishi magana ” Who the hell did she think she is, Shi Suraj take fad’awa magana, ya zama dole ya banbance mata tsakanin tsakuwa da aya”,

    Can bayan d’akunan asibitin taje, wurin da ba kowa ta kifa kanta akan cinya, Tana kuka, Maraici da kewar Mahaifin ta da rashin sanin asalin ta, Ya taru ya dabaibaye ta.

     Hajiya taji fitar ta duk da ba gani take ba, “Baka kyauta ba Suraj, Allah yasa ba tafiya tayi ba, Feena tashi kije ki dubo mun ita”, Feena wacce tashin ta daga bacci kenan, Ta mik’e ta fita tana tunzura baki.

   Suraj faman huci yake kamar bajimin zaki.

   Feena ta dudduba bata ganta ba, Ta dawo tace bata ganta ba, Hajiya cike da b’acin rai tace ” Maza tashi kaje ka nemota, kai ka korar mun ita dan haka kai zaka nemo ta”, Ya fusgar da iska cike da b’acin rai yace “Mama ni na nemota”, ” Eh idan har kana son farin cikina, ba zan iya zama da kowa asibitin nan ba sai ita”, “Idan akan kula dake ne zan rik’a kula dake”, ” Kai ba macen bane da zaka mun all my needs, so ka tashi ka nemo ta”

    Mahaifiyar sa kad’ai ta isa, ita kad’ai ke da iko akan shi, banda ita babu mahalukin da ya isa yasa ya nemo wata, Mik’ewa yayi yana jin kamar ya had’iye zuciya ya mutu, Mama ta gama downgrading d’in shi da ta saka shi nemo cheap and classless girl, but bashi da wani option da ya wuce nemo ta dan farin cikin ta.

     Dube-dube ya shiga yi,  zuciyar sa ta bashi tana asibitin, Yadda yasan talaka da son kud’i ba zata yarda ta tafi ba, Ta bayan d’akunan ya hango ta, durk’ushe tana kuka.

    Jin mutum tsaye a kanta ta d’ago suka had’a ido, Wani haushi da tsanar sa taji ta dirar mata a zuciya, Ta kawar da kai,

     “Ke!”, Ko gezau bata yi balle ta juyo, Hannu yasa da k’arfi ya juyo da kanta, Ta runtse ido tana saukar da kai k’asa, ” Ya zama na farko na k’arshe da zan fad’i magana ki mayar mun, Daraja d’aya kika ci na Mahaifiyata da wallahi…..”, Yayi shiru yana cije lips,

    Fetta wani tsoron sa taji a ranta kada ya mammake ta a wurin ba mai ceton ta a ranta tace “Kai ma darajar Hajiya kake ci”,

    ” Kije tana neman ki, ki kula da lafiyar ta fiye da yadda zaki kula da taki”, Ji tafi kamar tace ba zata yi ba, tausayi da kirkin Hajiya yasa tayi shiru, Ya juya ya wuce.

   Ta mik’e, idonta sunyi luhu-luhu saboda kuka, Hajiya bata fuskanci tayi kuka ba tunda ba gani take ba, Hak’uri ta bata, Fetta tace ba komai, Feena dake gefe ta tab’e baki, a ranta tace wannan abar ake ba hak’uri.

   Har dare bai k’ara shigowa d’akin ba, Around 3 lokacin tuni Fetta tayi bacci, Dr ya shigo ya cirewa Hajiya bandage, Aiko idon ta ya bud’e tana ganin mutane, ba kamar farkon kawo ta asibitin ba, shima Dr yace idan ta k’ara kwana biyu zata dawo gani kamar da, sai su sallame ta, Godiya tama Allah.

    A lokacin ne Suraj yazo asibitin a gajiye, daga ganin shi wani aikin yayi ya gaji, Kallo d’aya yama Fetta tana ta sharar bacci ya kawar da kai, Yayi murna sosai na ganin idon ta sun bud’e.Kiran sallar asuba da ya zama jikin Fetta, Duk kiran asuba a kunnen ta, Yau ma hakan ce ta kasance, Kiran farko ta tashi da sunan Allah a baki, Mik’a tayi ta tashi, Ta shiga toilet tayi alwala, Ta fito ta gabatar da raka’atanil fajr, ta sallame tayi sallah. +

     Zama tayi tana karanta surorin da ta haddace, Cikin kira’ar ta mai dad’i, Bata d’aga murya ba gudun kada ta tashi Hajiya tana buk’atar hutu.

    Kamar a mafarki Hajiya taji karatun Qur’ani mai dad’i, Bud’e ido tayi ta sauke su kan Fetta, idon ta a lumshe yake, tana zuba karatu, Hajiya a ranta tace “Allah ya bata baiwa, ina ma su Su’ad ne ke karatu haka, sun k’i maida hankali ba yadda bata yi dasu ba, har yanzu basu yi sauka ba”

    Tarin da ya taso mata, Ta dakata da karatun tare da bud’e ido, “Sannu”, Hajiya ta fad’a, Ta kai dubanta gare ta, ” Laah an bud’e miki idon, yanzu kina gani”, Ta fad’a with full excitement, Hajiya tabi ta da kallo tana murmushi yadda take murna ko su Su’ad basu nuna farin cikin su haka ba,

   “Allah ya k’ara miki lafiya”, ” Amin Amin”, Ta mik’e ta shiga toilet.

    Wayarta ta d’auki ruri, Murmushi tayi ganin masoyin ta ne mai kiran, “Amincin Allah ya tabbata a gare ka”, ” Tare da ke, kin tashi lafiya?”, “Lafiya lau, ya gida da ayyuka?”, ” Alhamdulillah, sai dai kewar ki da ta dame ni”, “Nima haka”, ” Anjima zan zo na ganki, dan gaskiya ba zan iya jure har ki dawo ba”, Tana murmushi tace “Sai kazo”, ” Zuwa la’asar idan nazo zan kira ki”, Tace “Toh”, ” I love you “, ” Same”, Ya mata blowing kiss, Tayi saurin kashe wayar tana sunne kai a pillow tamkar yana gabanta.

    “Ina jin Fetta tamkar jini na, kwana biyu da bata gidan nan, sai ina jin duk ba dad’i”, Aliya ta fad’a tana shanya kayan da ta wanke a igiya, Malam yace ” Wallahi nima haka, Yarinya ce mai tsantar hankali da tarbiya”, “Yau zan je na ganta, naga lafiyar ta”, ” Allah ya kaimu, ni zan wuce kasuwa”, Ya fad’a yana saka takalmi, “A dawo lafiya”, ” Allah yasa”

      Gari ya waye, hasken rana ya b’ullo, Su Feena suka zo asibitin da karin kumallo, Ko kallo Fetta bata ishe su ba, Itama ta d’auke kai kamar bata gan su ba,

    “Wai nikam yarinyar nan bata iya gaisuwa bane”, Cewar Feena (Zata ba Fetta shekara 3-4), Su’ad tace ” Kema kya tambaya”, “Sai mutum ya shigo wuri ta d’auke kai, kamar wata shegiya”, ” Sister kinsan wanda ba kowa ba yafi komai jin kan sa”

    Fetta yi tayi tamkar bata san da ita suke ba, Tana game a wayarta hankali kwance, Wanda hakan ba k’aramin k’ular dasu yayi ba, Feena a fusace tace “Ke!”, Ko gezau bata yi ba balle ta nuna wata alama na tasan da ita take, Ta tsani ace mata Ke, bata amsa kalmar ke,

      ” Fetta kike ko uban wa dake nake magana”, Ta d’ago “Au wai dani kike ai KE naji kince”, Tayi maganar hankali kwance, Rai a b’ace zata yi magana Hajiya ta fito daga toilet, Tayi shiru.

   Yau Hajiya da kanta taci abinci lafiya ta samu, Su’ad ko Feena da sun had’a ido da Fetta suke watsa mata harara, Ta d’auke kai daga sabgar su tana nata,

     Ana azahar suka ce zasu je gidan k’awar su anyi kidnapping baban ta,

    ” Al’amarin kidnapping d’in nan sai addu’a, Gwamnati ya kamata ta d’auki mataki, Allah ya k’ara tsaremu shi kuma Allah ya bayyana shi”, Suka amsa da “Amin”, Suka fice.

     ” Yau Suraj bai zo ba, na kira wayoyin sa a kashe, Allah yasa lafiya”, “Maybe wani ayyukan ya tare sa, anjima zaki gan shi”, ” Allah yasa”, A zuciyar ta tace “Ba ameen ba, Allah yasa ma kada yazo asibitin kwata kwata”,

STORY CONTINUES BELOW


    Sallamar sa ta jiyo, Gabanta ya fad’i, Ran ta ya b’aci, Sanye yake cikin shadda sabuwal dal wagambari sai d’aukar ido take, hular dake kansa ta zauna daram, Hannun sa d’aure da agogo wanda ko ba’a fad’a maka ba, daga kallo kasan tsadadde ne, K’afar sa sanye da covered shoe, D’akin ya game da k’amshin turaren sa, Fetta k’amshin ba k’aramin dad’i ya mata ba, Kallo d’aya ta masa ta wankar da kai, A ranta tace ” Akwai d’aukar wanka, sai tak’ama da izza fal a rai”

     Durk’usawa yayi gaban Mahaifiyar sa, Yace ” Mama ina kwana, Ya k’arfin jiki?”, “Alhamdulillah, Ina ka shiga ne yau, ina ta kiran wayoyin ka kashe”, ” D’aurin auren abokina muka je, daga can muka wuce reception, wayoyin kuma na manta su gida”, Ta sauke ajiyar zuciya tace “Allah ya tsare mun kai a duk inda kake”, Ya amsa da ” Amin Mamana”

    Fetta taji sun burgeta, Tana ji ana cewa babu soyayyar da ta kai ta uwa, Ita kam bata rayu da Mahaifiyar ta balle tasan wannan, Ranta taji ba dad’i.

    “Fetta kun gaisa da Suraj kuwa”, Hajiya ta fad’a, Kunya taji ta kamata Hajiya ta lura kenan bata gaishe shi, Murya a sanyaye tace ” Naga ne kuna magana “, ” OK”

    “Ina kwana?”, Kamar ba zai amsa ba yace ” Lafiya, Ina fatan kina kula da ita yadda ya kamata”, “Eh”, Ta bashi amsa, Ganin Hajiya a wurin yasa ta amsa.

    Toilet ta shiga, ta hau wankewa sam bata son zaman su a wuri d’aya takura take, Murmushi yayi Yace ” Kina so naga kina aikin ki kenan, kar ki damu zan biya ki da tsoka”

   Daga ciki ta jiyo sa, Wani k’ulloton bak’in cikin ne ya tsaya mata a wuya, “Wane irin mutum ne shi, ba dama mutum yayi abu sai yace akan kud’i, kud’i kud’i kamar a kanshi aka fara kud’i”, Taja tsaki,

   Ya jiyo tsakin banda Hajiya tana d’akin ba abunda zai hana ya shiga, ya mammake bakin.

   Muryar Aliya da taji, ta fito da gudu tazo ta rungume ta, Itama ta k’ank’ame ta kace sun shekara basu ga juna ba, Suka shiga gaishe gaishe, Surutun da suke ya fara hawa kansa Ya tashi ya fice.

   Ranar Fetta ta saki jiki sunyi hira da Hajiya shima ganin Aliya ne kwana biyu basa tare.

   Ana la’asar Aliya ta wuce, Fetta taji kamar kar ta tafi ko ta bita, Ta mata rakiyar har gate na asibitin.

     Tana toilet ta shiga fitsari, Wayarta ta d’auki ruri, Suraj da shigowar sa kenan ya kai duban sa ga wayar, FUTURE ZAWJ ya gani akan screen na wayar, Tsaki yayi yace ” Yar’ k’arama da ita har tasan soyayya”

    Fetta da ta fito wayar ta tsinke, Wayar na daf da Suraj, Ta kalleshi yana ta faman danna waya tana so tace zata d’auki waya, Taga fuskar nan tasa a tamke, tana tsoro ta mishi magana ya yab’a mata bak’a,

    Kiran Mu’azzam ne ya k’ara shigowa, Dole ta matsa daf dashi ta jawo wayar, K’amshin turaren ta ya daki hancin shi, Bai tab’a jin k’amshi mai dad’i da sanyi irin wannan ba, Saurin toshe hanci yayi saboda yadda yaji sa wani iri, Fetta kam da kallo ta bishi mai yake nufi wari take ko me, Ranta taji ya b’aci, Taja siririn tsaki, Charaf a kunnen sa “Wai ita yarinyar bata da aiki sai tsaki, bata san yadda ya tsani tsaki bane, zai yi maganin ta bari su keb’e”

    Receiving kiran tayi da ya kusa tsinkewa, Ya sanar da ita yazo, Tace “Tana zuwa”, Cike da jin kunyar yadda zata sanar da Hajiya fitar ta, dabara tazo mata, Murya na rawa ” Uhmm Hajiya dama bak’o ne zai zo ya gaishe ki”, “Toh ki shigo dashi”

“Ai ban gane ki ba, kinga yadda kika k’ara fresh kuwa”, ” Ya Mu’azzam baka gajiya da zolaya”, “Allah kuwa”(Dole zata k’ara fresh tunda bata fita ko’ina, 24/7 suna cikin AC)

    ” Muje ciki ka gaida Hajiya”, “Kash gashi ban zo da abun dubiya ba”, ” Babu komai gaisuwar ma ta wadatar”

    Tana gaba yana biye da ita a baya, A zuciyar sa yana addu’ar Allah ya nuna masa ranar da zata zama mallakin shi,

    Hannu yaba Suraj suka gaisa, wanda ya amsa mishi sama sama, Ya gaishe da Hajiya da mata ya jiki, Ta amsa ba yabo ba fallasa,

   Da suka fito yake cewa Fetta “Dama Sir Suraj ne yaron Hajiya”, Tace ” Eh ina ka san shi?”, Dariya yayi yace “Garin nan waye bai san Suraj Sa’idu SS ba, idan ana lissafa masu kud’in nan garin nan yana ciki, babu matashi mai shekarun shi dake da k’udin shi, akwai shi da tausayi da taimakon talaka”, Fetta tace ” Tabb a idon mutane ba, a zahirin gaskiya babu wanda ya kai shi wulak’anta talaka”, “Kamar ya?”, ” Mu bar maganar”,

   Su d’an tab’a hira, Tace “Zata koma ciki kada Hajiya taji ta shiru”, Ta raka shi har mota ya wuce,

     Tana tafiya taji an sha gabanta, Suraj ne tsaye gabanta yayi folding hannu kan k’irji, ” Kada ki k’ara kawo kowanne k’ato asibitin nan, idan kin koma gida sai ki cigaba da ganin samarin ki”

    B’acin rai da wani courage taji yazo mata tace “Ka gyara kalaman ka bana cikin jerin mata masu tara samari, Mu’azzam kad’ai nake ma kallon da’ namiji”, Tana fad’ar haka ta rab’a ta gefen sa ta wuce.

     Kalmar “Mu’azzam kad’ai nake wa kallon da’ namiji” Ke mishi yawo a kai, Me take nufi hadda shi bata ma kallon Namiji, lallai yarinyar nan akwai rainin hankali, Bin jikinsa yayi da kallo yaga ta ina Mu’azzam yafi sa da har take musu kallon ba da’ namiji ba,

   Zuciyar sa tace “Are u OK?, Kake had’a kanka da wancan mara aji irin ta, Daidai ruwa daidai tsaki, Shine type d’in ta, shiyasa take ganin haka”, Ya kawar da tunani, amma duk k’ok’arin ya cire kalmar a ransa ya kasa, it keeps hurting him.

    Yan uwa nata zuwa duba Hajiya, bata ga Bilkisu ba, tayi mamakin rashin ganin ta, Tana jiran Suraj yazo ta tambaye shi.

     10:00 na dare ya shigo, Fetta na shirin bacci, Ganin sa ta fasa kwanciya, Ta rakub’e gefe tana latsa waya tana gyangyad’i,

   ” Nikam ina Bilkisu ne, kowa yazo duba ni banda ita”, Ganin Hajiya ta samu lafiya sosai, Ya fayyace mata komai, Ba Hajiya kad’ai ba hatta Fetta ta girgiza da jin lamarin.

    “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un wannan musiba har ina”, Hajiya ta fad’a zufa na keto mata, ” Kar ki damu Mama, kanta ta cuta”, “Hakane Allah ya shirya mana zuri’a, kai kuma Allah ya maka zab’in alkhairi ya had’a ka da mace ta gari”, Ya kawai amsa da Amin ne, amma a ransa baya jin zai k’ara aure.9:00am +

  Bayan sunyi breakfast, Fetta ta fito wanka tana shiri, Taji ana knocking, Dama idan zata shirya key take sawa, Doguwar riga ta zura, Ta nufi k’ofa ta bud’e, Suraj ne tsaye cikin English wears da suka matuk’ar yi mishi kyau, “Komai ya saka kyau yake mishi”, Ta fad’a a ranta, Kanta ta sunkuyar k’asa tace ” Ina kwana?”, Bata jira amsar shi ba, Ta koma ciki,

    Bai amsa ba ya shiga, Ya gaishe da Hajiya kamar kullum, “Takardar sallamar ki ce Dr ya bani yanzu”, Fetta ajiyar zuciya ta saki mai d’auke da farin ciki, zata koma gida ta huta da wulak’ancin Suraj da k’annensa bata fatan wani abu ya sake had’a su.

   Hajiya cike da murna tace ” Mashaa Allah”, Ita kanta ta k’osa ta bar asibitin ta koma gida, dama zaman asibiti sai dole.

    Yace “Suyi packing zai je ya dawo su wuce”, Hajiya tace ” Kar ya dad’e”

    Cike da murna da zumud’in komawa gida Fetta ta shiga had’a kaya, Hajiya ta kalle ta tace “Fetta sai murna kike zaki tafi ki barni koh”, Kunya taji ta kamata tace ” A’ah Hajiya zaman asibitin ne ba dad’i amma ina jin dad’in zama dake”, “Toh idan hakane mai zai hana ki dawo gidana da zama”,

   Wata fad’uwar gaba taji, Ta had’iye miyau da k’yar, Ta lura da yanayin ta tace ” Ba zan tilasta miki ba, ko ba zaki dawo gidana ba, Dan Allah ki rik’a zuwa kina tayani da wasu ayyuka”, Tace “Toh In shaa Allah”, Hankalinta ya d’an kwanta ko ba komai, zuwa zata rik’a yi tana dawowa ba zama dindin ba.

     Suraj ya dawo, da envelope d’auke da kud’i 100k, Ajiye su yayi gaban Fetta yace ” Ga kud’in ki kamar yadda na fad’a zan biya ki”, Harara ta watsa wa kud’in ta mik’e tana d’aukar jakar kayanta, Hajiya tace “Fetta da kin d’auka, zasu rage muku wasu lalurori”, “A’ah Hajiya Dan Allah nayi bana buk’atar biyan kowa sai na Allah”, ” Allah ya biya ki da mafificin alkhairi”, Ta amsa da “Amin”

    Suraj yace wa kansa “Yarinyar nan akwai fad’in rai, da yar’ mai kud’i ce da anga isa da tinkaho”,

     Hajiya ce tace ya d’auki kud’in niyyar sa ya barsu a wurin, wanda zuciyar sa ke ce masa zata dawo da d’auka, Ya d’auka ya saka a aljihu.

   Motoci biyu yazo dasu, Hajiya ta shiga d’aya shima ya shiga, D’ayar ya umarci driver ya kai Fetta, Ta shiga tana ta rab’a ido, bata tab’a shiga mota mai kyau da tsaruwar wannan ba,

    A bakin k’ofar gidan su yayi parking, Tana k’ok’arin fita yace ” Baiwar Allah ga sak’o inji mai gida”, Ta kalli envelope da ya mik’o mata tace “Ka mayar mishi kace bana buk’ata”, Ta fice abun ta, Driver yabi bayanta da kallo cike da mamakin k’in karb’ar ta,

    
    Aliya tayi murnar ganin Fetta, nan suka shiga hira, ta sanar da ita buk’atar Hajiya na zuwa ta rik’a taya ta aiki, ” Ke dai jinin ku ya had’u da Hajiya”, Fetta tayi murmushi.

    Ma’aikatan gidan kowa murna yake da dawowar Hajiya, Wanda basu samu zuwa asibitin ba, Suna ta zuwa.

    Suraj na garden na gidan, Yana shan iska, wanda most of the time nan ne wurin zaman sa, Driver ya rissina gaban sa cike da girmamawa, Yace “Ranka ya dad’e bata karb’a ba tace bata buk’ata”, ” Ajiye ka tafi”, Ya umarci driver,

     “Wacce irin yarinyar ce wannan mai fad’in rai da d’aukar kanta wani abu, idan tayi hakane dan ta burge sa toh bata burge shi ba”, Yacewa kansa

    
       Yau suka zana jarabawar k’arshe, Rigar ta duk an zane ta da signing, Ana ta bankwana, da exchanging phone numbers, Masu hotona nayi, Duk wanda da akwai maza a ciki bata shiga, Suma mazan sun san halinta babu wanda yayi attempting zuwa yace suyi hoto, Yau da ta kasance rana ce ta farin ciki, sab’anin haka Fetta take ji a ranta, Ta rasa dalilin da yasa bata jin dad’in ranta, ga gabanta da yake yawan fad’uwa, Ta bar hakan a bisa yanayi ne na rayuwa, Dama watarana kaji ka cikin farin ciki, ko sab’anin haka.

     Haka ta dawo gida sukuku, Bata tarar da kowa ba, Ta shiga d’aki ta kwanta tana tunanin rayuwa.

   Mu’azzam ne durk’ushe gaban iyayen sa, Mahaifin sa yayi gyaran murya yace ” Mun kira ne, mu baka umarni ba shawara ba”, Cike da ladabi yace “Toh”, ” Zancen auren yarinyar nan ka janye”, Ya razane ya d’ago ya kalli Mahaifin sa, Ya d’aga kai alamun Yes ya cigaba da cewa ” Mun yanke shawarar had’a ka aure da yar’ wajen yayan mahaifiyar ka”, “Abba auren dole fah zaku mun, Dan Allah Ku barni na auri…..”

  Mahaifiyar sa ta katse sa “Nuna mana bamu isa da kai ba, banda baka san ciwon kan ka ba, Yarinyar da bata da asali zaka aura, Toh auren ka da Binta kamar anyi an gama”, ” Tashi ka ba mutane wuri”, Mahaifin sa ya fad’a a tsawace,

    Mu’azzam ya mik’e yana jin jiri na d’ibar sa, bai tab’a kawowa kansa rabuwa da Fetta ba, a yadda soyayyar ta ta kama shi baya jin zai iya cigaba da rayuwa, Da k’yar ya kai kanshi d’aki, Ya fad’a kan gado yana jin duniyar ta mishi zafi.

    Fetta shiru bata ji Mu’azzam ya kira ta, Ta kira shi yafi sau biyar bai d’auka ba, Ganin har dare, Abun ya fara damun ta, Abinci loma uku tayi ta ajiye, Aliya na lura da ita, Tace “Meke damun ki ne Fetta?”, ” Ba komai, gajiya ce ta makaranta”, “Kije ki kwanta ki huta”, Tace ” Toh”,

   Aliya tasan akwai abunda ke damunta, ba zata fad’a bane, Tana addu’ar Allah yaye mata.

    Wayarta ta jawo ta sake kiran Mu’azzam a karo na ba adadi, Mu’azzam dake kwance yana ganin kiran, Ba zai iya d’auka ba, bai san me zai ce ba, bai san wani hali zata shiga ba, Har kiran ya tsinke.

     “Ya zama dole ka sanar da ita da kan ka, idan taji a wani wuri zata d’auke ka mayaudari” Zuciyar sa ta fad’a mishi,

    Wayar ya d’auka ya shiga rubuta mata message kamar haka ” _Mu d’auki k’addara mai kyau ko mara kyau a duk halin da tazo mana, Allah ya k’addara haka zata kasance a tsakanin mu ba zama rayu da juna ba, iyayena sun zab’ar mun matar da zan aure, kiyi hak’uri Fetta, Ni mai k’aunar ki ne kuma har abada da sonki zan mutu, Allah ya sada mu da alkhairi_

   K’arar text da taji, Ta jawo wayar, Ganin Mu’azzam ne, Cike da murna ta bud’e,

     Tana gama karantawa, Ta saki wayar ta fad’i, Kanta taji na juya mata, tana gani dishi dishi, Duhu ne ya mamaye idon ta, ta fad’i.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *