RAI BIYU
CHAPTER 8
Haba Nawwara abunda kike ba shi da kyau Wallahi na san kin tsani masu kuɗi amman wannan mutumen fa taimakonki ya yi ban san abunda bawan Allah nan ya yi miki ba duk kin bi kin tsaneshi, haka sam be dace ba, ni kaina na tuhumesa lokacin da ya zo har gida ya faɗa min na ce miyasa be faɗa ba gidanku ya ce yana gudun zargin ne kuma da na zo nan asibitin na tarar mutun biyu da suka kawo ki tare, Wallahi babu wani abu Nawwara dan Allah ki kwantar da hankalinki” +
Shine abunda Jidda ta faɗa lokacin data ƙaraso kusa da ni. Mustapha kuma na daga can nesa da mu ya sako min ido kamar zai cinye ni. Kallo ɗaya na yi masa na ɗauke kai ba tare da na ce da ita komai ba na cigaba da tafiyata, zuciyarta na mugun bugawa kamar zata faɗo. Tare muka fito da Habiba a har bakin gate ɗin Specialist hospital dake sokoto, motar Mustapha ce ta sha gabanmu be ce komai ba ya miƙa hannu daga inda yake zaune ya buɗe mazaunin baya. Jidda ce ta iya riƙa ganbun motar ni kan ko kallo bata isa ban na kauce mata na cigaba da tafiyata har na tsada mai adaidaita na shige ina faɗa masa inda zai kaini, yana ƙoƙarin tashi sai ga Jidda ta dakatar da shi ta shigo tana min masifa wai abunda na ke bana kyauwa, ni dai ban kulata ba saboda na san bata san zafi da irin ƙiyayyar da raina ta Mustapha ba, tun da ban taɓa faɗa mata cewar shine mutumen da ya yi sanadiyar muturwar ƴar’uwata ba.
A gurin da aka saba saukeni na ce ya ajeni na saka hannu aljihu na ciro kuɗi a bashi sai a lokacin na tuna da hoton Habiba da na baro a wacan baƙin kamfanin da bana fatar ko a mafarki na sake zuwa, gaskiya na ji babu daɗi sosai domin shine kaɗai hoton Habiba da nake da shi a yanzu wanda take da girmanta, ta ɗaukeshi ne lokacin da zata yi canjin makaranta daga Hafsatu zuwa Nana girl’s, abunka da takala ba hotone a gabanmu ba sai idan wani abun ya tashi na dole sannan muke zuwa yin hoto.
“Ina wayata?”
Na tambayi Jidda bayan mai adaidaita ɗin ya bamu canji, hannu tasa cikin jakarta ta ɗauko wayar ta miƙa min.
“Gashi”
Ina karɓa na sa kai gabana muka cigaba da tafiya tare.
“Gaskiya halinki bashi da kyau Nawwara, idan har baki yabawa Mustapha ba to ba zaki zageshi ba”
“Ce miki ya yi na zageshi?”
“Ko baki zageshi ba kin faɗa masa magana marar daɗi domin alamu sun nuna haka, ban san abunda bawan Allah ya yi miki ba, ko dai akwai wani abun ne?”
Na tsaya ina kallonta
“Wai miyasa kika damu ne Jidda?”
“Saboda ya taimakeki, da be kawo ki asibiti ba da Allah kaɗai yasan halin da zaki kasance akan hanya”
“Da barina ya yi akan hanyar mota ta takani ko kuma mutane suka ɗaukeni suka jefar a bola, da ya fi min farinciki sama da ɗauko da ya yi ya kawo asibiti, dan Allah ki tattara duk wani abu da ya danganci maganar nan ki ajeta a gefe”
Na tada kai na cigaba da tafiyata har na isa gida ban waiga na kalli Jidda dake gefena ba. Ita ce ta faɗawa Inna abunda ya faru da kuma irin abunda na yi ma Mustapha har Inna da kanta ta dinga ganin rashin kyautawa da kuma faɗar abunda na yi ba halina ba ne.
Ni dai ban iya cewa Inna komai ba tun da nasan ita ma ban faɗa mata cewar shine mutumen da ya yi ma Habiba aika-aika ba. Tufafin jikina na cire na saka a murhu na ƙone tare da Hijab ɗin duka na haɗa na ƙone saboda mutun biyu Mustapha da kuma Jibril tsakanin su ba zan iya banbance wanda zuciyata ta fi tsana ba. Ina gaban Murhu Inna ta fito daga ɗaki jin ƙauri ta saka salati.
“Lafiya kike ƙone kayan aikin kuma Nawwara mi yake damunki?”
“Inna sun koreni dan haka bana da buƙatar wannan kayan”
“Garin ya wani abun kika yi?”
“Ban yi komai ba, saboda kawai na daɗe ban je ba”
“Ba kince Bilal ya faɗa musu baki da lafiya ba?”
STORY CONTINUES BELOW
“Wai basu yarda ba shugaban Kamfanin ne bashi da mutunci”
“Allah ya kyauta ya baki wani”
Ta faɗa cikin muryar da ke nuna bata jidaɗin haka ba. Ƙarasowa ta yi kusa da ni ta riƙani ta tayar tsaye.
“Tashi gaban hayaƙi, bari na saka miki ruwa ki yi wanka”
“A’a zan iya Inna”
“Babu ƙarfi jikinki Nawwara baki ga yanxu kika dawo daga asibiti ba”
Da kanta ta haɗa min ruwan na shiga banɗaki na yi wanka, bayan na fito na ɗauki buta na yi alwala na shiga ɗakinmu sai na samu Inna zaune tana yanka min albasa a wake da shinkafa, saboda ta san ina son na saka albasa da tumatur idan zan ci wake.
“Gashi nan idan kin gama sallah sai ki ci, bari na kawo miki ruwa”
Ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita ni kuma sai na yi saurin dakatar da ita.
“Haba Inna kina ta min abu sai kace ƙaramar yarinya ni ya kamata ace ina hidima dake ba wai ke ki yi da ni ba”
Tsayawa tayi jikin ƙofa tana murmushi tare da wasa da wuƙa da kuma ragowar albasar dake hannunta ta ce.
“Nawwara ji nake kamar da nayi wani sakaci kaɗan rasaki zanyi, ɗazun da baki dawo a lokacin da kika saba dawowa ba hankalina ya tashi sosai, ba san yadda zanyi ba idan har na rasaki bayan na rasa Habiba, kuma kina a matsayin RAI BIYU a yanzu ni da kuma ɗanki, shi ma ya damu da be ganki ba lokacin da ya dawo daga makaranta, yana ta tambayar ina Momy nace mishi kina gurin aiki amman daker ya yarda ya tafi islamiya, ɗanki yasan zafin rabuwa da mutun yasan idan aka tafi ba a dawowa shiyasa saboda ya rabu da Habiba dan haka ba zamu iya jure rashinki ba”
Tana faɗar hakan tasa kai ta fice idonta cike da ƙwalla, ni kuma na jingina na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya, wani irin tausayinta ne ya rufe ni. Jin wayata tayi ƙara yasa na buɗe ido na nufi inda wayar take, tun kamin na ɗauka gabana na faɗi saboda saƙone daga One-On-One Limitless Company, ji nayi bana da buƙatar sanin abunda saƙon ya ƙumsa, dan haka na danna delete na goge shi ba tare da na karanta ba.
Sai da na gama rama sallah azahar sannan na gabatar da sallah la’asar, sai na zauna na ci abincin sai ba sosai ba saboda bana jindaɗin abinci a yanzu, sai dai shigowar Inna yasa na zage dantse na yi ta auna abinci domin nasan zata damu idan ta ga banci da yawa ba. Na yi ƙoƙarin ganin na danne damuwata amman mahaifiya ta fi gaban wasa ita da kanta ta tsinkayi hakan a cikin idona.
“Nawwara kamar akwai abunda yake damunki, idan dai dan maganar aikin nan ne ki kwantar da hankalinki Allah zai sake baki wani kamar yadda ya baki wannan”
Kai kawai na iya ɗaga mata domin na gansu maganar aikince kamar yadda take hasashe, domin idan har ta tiƙe ni ban san mi zan faɗa mata ba. Tashi tayi ta fita jin wata maƙociyarmu ta shigo, ni kuma na rafka uban tagumi ina kallon ƙasa amman hankalina yana can gurin rayuwata ta baya.
FLASH BACK.
_“Yau za’ayi ina fatar zaka samu zuwa kai da madam, tau ya yi sai kun ƙaraso”_
_Haka na ji ya faɗa a waya, sannan na miƙe tsaye yana min wani gumun kallo ya ce._
_“Wallahi duk kika sake abokaina suka zo gidan nan kuma kika fito sai na halakaki, kinji ni ko?”_
_Da sauri na ɗaga masa kai hawaye na zuba a idona, sai ya kaɗa kai fuska babu annuri ya nufi ɗakinsa yana wani irin jinkansa, ni kuma na zube a gurin ina kuka saboda zafin ruwan zafin da ya watsa min a hannu kuma ya hanani kuka saboda tsabar zalumci. Ina a gurin ina aikin kuka har ya shirya ya fito sai ƙamshin turare yake ya tsaya a kaina ya nuna ni da yatsa_
STORY CONTINUES BELOW
_“Ki shiga cikin ɗaki ki kulli kanki karki yarda ki fito”_
_Na amsa masa da tau jikina na rawa ina ta ƙoƙarin haɗe kukana nasan idan har na yi kuka a gabansa zai iya dukana, kamar yadda ya umarce ni haka na shiga cikin ɗakin na rufe kaina wanda hakan ya bani damar tausayawa kaina da kaina. Can zuwa dare na soma jin hayaniyar abokansa ta hirar da suke na iya gane ashe muƙamine ya samu amman ya gagara faɗa min saboda ƙiyayyar da yake min, haka yake duk lokacin da wani abun ya sameshi sai dai na ji a waje ba dai ya faɗa min ba. Har suka yi abunda zasu yi suka gama ban fito ba, bayan fitarsu da minti ashiri na ji an buga ƙofar ɗakina, yanayin yadda aka banki ƙofar ne ya fahimtar da ni cewar Jibril ne yake buga ƙofar, cikin hanzari naje na buɗe saboda na san baya son jira, sai nayi arba da yatsunsa biyar a kuncina, ma’ana wanke min fuska da mari yana faɗin_
_“Ke kiƙa faɗawa Abbah zanje meeting ba dake ba ko?”_
_Baya-baya na yi ina girgiza masa kai_
_“Na rantse da Allah ban faɗa ba, Wallahu ba ni bace”_
_Na faɗa cikin kuka, sai ya watsa min harara, yace na canja tufafi muje amman duk na masa kuka cikin mutane sai ya ɓanlani, jin wannan yasa hawayena ya yanke tun kamin ma mu fita domin na san haƙinsa ne sarai zai iya ci min mutunci a gaban kowa, sai dai ban daina jin zafin marinba har muka isa gurin da ake tare, gurine dake cike da manyan mutane an ƙawata gurin anyi masa kwalliya gwanin sha’awa. kowa da mazauninsa, an kasa mutane daban-daban wasu na tare da matansu wasu kuma na tare da familysu. Tare muka shigo da shi amman muna shiga harabar gurin sai yayi kamar be sannin ba tare da gargaɗina akan karna yarda na nuna cewar ni matarsa ce. Guri na samu kusa da wasu baƙin na zauna, bayan an gama jawabin da akeyi aka kirashi aka karramashi, sai yaje ya karɓi Award ya yi jawabi godiya, a lokacin Abbah da Hajiya basa nan dan haka babu wacce zai kira bayan su sai ni da nake matarsa, amman abun mamaki sai ya kira sunan budurwarsa Asiya ko kuma ma nace karuwarsa, haka ta miƙe tsaye tana ta karairaya ta haura gurin tana taya shi murna. Ni kuma ina daga nan zaune ina hawaye_
_Wani mutun ne ya miƙo min tissue yana min kalaman da mijina abokin rayuwata be taɓa min ba_
_“Kuka be cancanci kyakkyawar fuskarnan taki ba dan Allah karɓi ki share hawayenki”_
_Kallonsa na yi amman na kasa karɓa saboda idon Jibril na kaina, haka mutumen ya matsa min amman naƙi kula shi har aka tashi taron, a gurin da zamu shiga mota ya tare mutumen ya riƙa bugar masa baki wai ya yi magana da matarsa, babu kalar baƙar maganar da saurayin be faɗa masa ba, sannan aka rabasu ni kuma ya sakoni gaba muka dawo gida, kamar jira yake mu iso ya sakani gaba da duka wai na kula wani namijin har wani huci yake kamar zaki…_
BACK TO STORY
Shigowar Noor ne ya katse min tunani, sai ya yi saurin aje allon dake hannunsa ya nufo yana share min hawayen da ban san sun zubo ba.
“Momy miyasa kike kuka? Shiru shiru shiru kinji Allah ya miki albakar, yi shiru shiru faɗa min waya taɓa ki?”
Shine abunda yake faɗa tare da saka haɓar rigarsa ya goge min fuska, ina kallonsa gabana ya faɗi fuskar Jibril ce shimfiɗe a fuskarsa babu inda ya ragoshi tun daga kan hancinsa har ido da baki da fari komai na ubansa ne, rumgumeshi nayi muka kwanta saman kafitar da nake zaune.
_“Ba cikina ba ne…!”_
Shine abunda ya faɗo min a rai, sai na ƙara ƙanƙame Noor kamar ance za a rabani da shi. Bachine ya kwashemu ni da shi bamu farka ba sai da Sakina ta shigo tana tashina wai anyi magariba.
Bayan Sallah isha’i Bilal ya kirani a waya yace min yana ƙofar gida, nasan daman zaizo tun da yau ban karɓi kuɗin da ya saba bani ba. Sai dai na sha mamaki lokacin da fita muna fira da shi.
“Miyasa kika fita Kamfani ɗazu kina kuka?”
Shine abunda ya fara tambayata, nasan wata ƙila wani ne ya faɗa masa, ni kuma sai na masa ƙarya da cewar saboda sun ƙoreni yasa ni kuka, ya nuna min damuwarsa sosai har ma ya yi alƙawarin zai yi wani abu wajen ganin an maidani aikin, amman na nuna masa bana so. Sai tara da rabi muka rabu ban faɗa masa cewar na suma a titi ba duk na san nan gaba kaɗan zan ji a gurin Jidda domin bata ɓoye masa komai da ya dangance ni.
Ko da na shiga gida wayata na ta ringing ko da na duba sai naga baƙuwar number, kamar kar na dauka sai kuma na ɗauka tare da sallama, sai na ji ba a amsa min ba kuma ba a ce komai ba har na tsawon lokaci, hakan yasa na sake sallamar nan ma shiru har sai da na duba wayar naga mai kiran be kashe ba, na sake karawa nayi sallama a karo na uku ba amsa min ba kuma ba a ce komai ba, hakan yasa na kashe wayar dan da alama mai kiran yana son sauraren muryarta ne kawai duk da ban san ko wanene ba.
WASHE GARI…
Misalin bakwai da rabi saƙon kamfanin ya sake shigowa, nan ma ban karanta ba na goge, na shigaba da haɗa abun karinmu da nakeyi. Sallamar baƙuwar murya yasa na ɗago daga gaban murhun da nake na amsa mata ina mata kallon rashin sanin, sai da ta gaisheni sannan ta matso kusa da ni ta aje min leda biyu dake hannunta ta ce
“Wai gashi inji Ya Mustapha ya ce abawa Nawwara, kuma wai yana mata sannu da jiki”
Har na buɗe baki zance mata ta ɗauki kayan ta koma da su sai ga Inna ta fito daga ɗaki tana amsawa kamar tasan ni ba zan amsa ɗin ba.
“Mashallah ki ce an gode Allah ya saka da alheri, jiki kuma ya yi sauƙi sosai”
Da wannan budurwar ta juya ta koma wacce nake san ran riƙonta ake a gidansu Mustapha domin iyayensa shi kaɗai suka haifa. Tana fita na ɗauki kayan na fice na bar Inna tsaye tana kallon ikon Allah domin nasan idan har na ce yarinyar ta ɗauki kayan ta koma dasu a gabanta ba zata bari ba, amman yanzu bata san mi zanyi ba dole ta saka min ido.
Ina fita na yi karo da shi a ƙofar gidanmu sai ya ɗanyi nisa da gidanmu kaɗan yana sanye da jallabiya, daga inda nake tsaye na jefa masa ledodin na juyo abuna.“Me kika yi kenan?”
Ina shigowa gida ta jefo min wannan tambayar, da fari na tsaya tunanin abunda zan ce mata sai kuma daga baya na yanke shawarar faɗa mata gaskiya.
“Mayar masa da abunsa na yi, bamu da buƙatar taimakoshi”
“Amman Nawwara ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, mutumen da ya tsinceki gefen titi ya taimaka miki ya kaiki asibiti garin Allah ya waye kuma ya aiko ganinki shine zaki mayar masa da kayansa? Wannan wace irin rayuwace Nawwara? Mi yake damunki? Wulaƙanta ɗan’adam? Kuma mutun kamar Mustapha yaron da babu wanda ya isa ya nuna masa ɗan yatsa amman har kike ƙoƙarin ci masa zarafi?”
Yanayin fuskarta da kuma lamanta na fahimci ranta ya ɓace sosai akan abunda na yi, ni kuma na marairaice mata kamar zanyi kuka.
“Inna kin san waye Mustapha ana yaba masa da neman matan banza, dan me zai kawo min abu na karɓa, bayan ban san manufarsa a kaina ba”
Ta ƙaraso kusa da ni
“Shiyasa na ke son ki lallaɓa da shi ku rabu lafiya, da baki watsa masa kayansa ba sai ki amsa ki masa godiya in yaso daga baya sai ki nemi ya rabu da ke”
“Zan kiyaye nan gaba”
Da wannan muka raba na nufi murhu na cigaba da hura wuta, ita kuma ta koma ɗaki tana cewa Sakina ta zo ta siyo mana ƙosai. Har na dama kumun tunani ɗaya ne a raina, na faɗawa Inna gaskiya game da Mustapha ko kuma na barwa cikina, idan ma na faɗawa Inna amfanin me zai mata? Idan kuma na bari ban faɗa ba ni amfanin me haka zai min?
Ina cikin wannan tunanin naji muryar Namiji yana sallama a ƙofar gidanmu, bayan naji tsayawar mota da kamar minti huɗu, dakan uku-uku gabana ya yi duk da ban san ko wanene ma. Ko da na bar gaban murhun Jamila har ta kai waje, sai gata ta dawo da sauri tana kirana.
“Anty wai ki zo ana kira a waje”
“Waye?”
“Wanine”
Mustapha na fara kawowa a raina, amman da shi ne ai Jamila ta sanshi da shine ai ba zata ce wani ba. Miƙewa na yi tsaye na tare da bokitin da na dama kunun na nufi ɗakin Inna na aje mata sannan na ɗauki Hijabinta na saka na nufi ƙofar gida gabana sai faɗuwa yake musamman da na yi arba da mutumen dake sanye da rigar kamfanin da kuma hularsu, tun kamin na masa sallama shi ya fara min tare da faɗin sunana.
“Khadija Musa Kafinta”
“Sunana ne”
“Zaki saka hannu a nan sai na baki saƙon da aka aiko miki”
“Bana da buƙata ka mayarda saƙon, kuma ka faɗawa shugabanku ya dakatar duk wani saƙo da suke aiko min bana da buƙata”
Sakin baki mutumen ya yi yana kallona, kamin ya barshi tsaye a gurin nayi shigewata, zuciyata cike da tunanin abunda ke cikin saƙon a lokacin na riƙa da na sanin ƙin karɓa da na yi domin sosai na so naga abunda aka rubuta, sai dai kuma ta wani babin bana da buƙatar duk wani abu daya dangancin Jibril idan har na saka masa fuska tabbas zai sake nuna wasa da ni kamar yadda ya yi a baya.
Wani mugun murmushi na samu kaina da yi lokacin da na tuna hawayen da na gani a fuskar Jibril, ashe zai iya zubar da ƙwalla saboda ganina har ya riƙa hannuna ya shafa a fuskarsa, mace da ya ce kashe yafi ta daraja a gunsa, lallai akwai babban labari a cikin hawayensa, domin ba kasafai Jibril ya ke nadama akan abunda ya aikata ba.
“Kee… Lafiya kike murmushi ke kaɗai kuma?”
Tambayar da tayi min ta dawo dani daga duniyar tunanin da na tafi har na yi dariya na matsa kusa da ita na rumgumeta.
“Ina sonki sosai Mamana”
“Waye ya zo yanzun kuma?”
“Daga kamfanin da nake aiki ne, suka aiko saƙo amman ban karɓa ba”
STORY CONTINUES BELOW
“Saboda me?”
“Nasan babu komai a ciki sai wulaƙanci”
“Ai da kin karɓa kin duba wata ƙila zai miki amfani”
“Ya riga ya tafi”
“Allah ya kyauta”
Sai duk muka amsa da Amin. Bayan mun gama karyawa, su Sakina suka shirya suka tafi makaranta tare da Noor, sai dai gabana nata faɗuwa saboda ina ganin kamar wani abu zai faru da ɗana. Sai da suka je makarantar suka dawo sannan hankalina ya kwanta.
Can da yamma sai ga Jidda ta shigo gidanmu da manyan ledoji, daman ta saba a duk lokacin da nake rashin lafiya sai ta riƙo min wani abu take zuwa gidanmu dubani, sai dai abunda ya ban mamaki siyayar da ta yi min ta fi ƙarfin Jidda duk da nasan sun fimu rufin asiri. Bayan sun gama gaisawa da Inna ta ƙasaro inda nake zaune ta dire min ledojin tana zolayata kamar yadda ta saba.
“Gawa ta ƙi rame, kin ƙi ki mutu mu ci gado”
“Mutuwata ba yanzu ba yarinya sai ke da danjinku kaf kun ƙare”
Sai duk muka saka dariya har Inna dake ninkar kayan da na wanke ɗazu na su Jamila. Mun sha fira sosai da Jidda daga bisani na tambayeta inda ta samo wannan kayan domin ita kanta tasan na san wannan kayan yafi ƙarfinta, bata ɓoye min komai ba ta faɗa min daman can Jidda bata ɓoye min komai.
“Wallahi Mustapha ne ya kawo ya ce idan zanje na riƙa miki wannan, wai kar nake hannu sake, daman ina ta tunanin abunda zan riƙo miki dan bani da kuɗi kuma bana son zuwa haka nan”
“Daman kuna waya da shi?”
“A’a ɗazu dai ne ya zo yake tambayata jikinki kuma ya bani number wayarsa wai idan zanje dubiyarki na faɗa masa, shine fa ya kwaso min wannan kayan”
Bana son Jidda ta zargi wani abu, hakan yasa ban ƙara masa wata tambayar ba, sai kawai muka ɗauko wata firar. Sai da aka kira sallah magariba sannan na rakata ƙofar gida ta wuce tana mintar rashin adalci na mai kamfanin da nake aiki, domin na labarta masa cewar ya koreni.
Tun daga wannan ranar kullum sai Mustapha ya aiko da saƙon a gidanmu da sunan ganin lafiyar jikina, wasiƙar gurin aiki kam kullum sai tazo gidanmu bayan ta waya da ake aiko min, tun Inna na lallaɓa na koma aikin har ta gaji ta zuba min ido domin ta fahimci ba zan koma ɗin ba, na kan faɗa mata ni bana son aiki a kamfanin ne saboda dokokin kamfanin. Bilal ma ya yi mamaki matuƙa ji da ganin yadda kamfanin yake neman na koma aikin bayan ance an koreni, shi da kansa yake faɗa min ko da harkar kasuwanci kanfanin zai ƙulla da kai da zai ci riba matuƙar suka koreka ba zasu nemeka ba balle kuma ma’aikaci, babu irin tambayar da bai min ba akan ko nasan wanine a kanfanin amman na nuna masa ni bansan kowa ba har ma na yi masa iƙirarin cewar ai na fada cewar ban yafe Haƙƙina ba wata ƙila shiyasa suke son na dawo aikin.
Sam ban taɓa ɗaukar lamarin Mustapha azimun ba ne sai yau da mahaifiyarsa ta zo dubani, ita kanta Inna mamaki ya cikata kuma ta ɗan tsorata da lamarin kamar yadda nima nake ta almarar abun tare da tunanin abunda yake ƙoƙarin aikatawa. Kana ganinta kasan zuwan cilas ne domin ƙyamar gidanmu take sosai, zama na sai ya gagareta sai wani kallon gidan take a hankaɗe a tsaye ta yi min ya jiki ni kuma na bawa banza ajiyarta har sai da Inna ta amsa ta tana ta ƙoƙarin kareni, saboda ta tsarku da yadda na share Hajiyar a tsaye ko gefenta ban kalla ba balle har na iya gaisheta.
“Iska ne da ita abubuwan ne sai a hankali”
Ta taɓe baki tana gyara tsayuwar gilashin idonta.
“Daman Son ne ya faɗa min akwai yarinyar da kai asibiti yana son na zo na dubata, ni zan wuce”
Ko sakon biyar bata ƙara a gidanmu ba ta fice tana wani irin taku na ƙasaita Inna ta bita tana masa godiya, ni kuma na bita da harara, daman ba zan lissafata a cikin mutane mn da suka mana gaisuwar Habiba ko Baba ba duk da bana iya tantance kowa da kowa amman da tazo da dole wasu zasu ganta ko da ba ni ba, gashi tsanar ɗanta ya dasa nin tsanarta musamman yanzu dana fahimcin bana sha’awar mutane irinmu.
Inna na dawowa daga rakiyarta ta cire takalmin ta buga min a kai, kana ta nuna ni da shi tana faɗin
“Allah ya canja miki wannan baƙin halin da ya taso miki, ai ba ita kika kunyata ba ni kika kunyata”
Tana faɗar haka ta nufi ɗaki ranta a ɓace, rabon da Inna ta ɗauki wani abu ta dakeni tun ina junior high school lokacin da na zo wani hutu, amman yau gashi ranta ya ɓace har ta buga min takalme a kai saboda ɓacin rai. Tashi na yi na bita ɗaki na bata haƙuri tare da shaida mata ba zan sake sannan muka shirya da ita har ma tayi min bitar zaman da mutane da kuma taka tsantsan na ka samu ka rabu da kowa lafiya.
Haka muka zauna muna ta fira har su Noor suka dawo daga makarantar allo na tura masa karantunsa ya wanke allon yana ta murna wai malaminsu ya ce ya iya idan yaje gida ya wanke allo gobe yi masa wani rubutun. Bayan sallah magariba Bilal ya sallamomin kamar yadda ya saba sai dai yau sallamar tasa ta musammance domin firar kansa yake min wai mutane nata maganar ya kamata ya yi aure har da ƴan gidansu, ni dai murmushi kawai nake inda kuma ya kamata na yi dariya sai nayi dariya, har muka rabu beji wata kalma da yake zato daga bakina ba, hasalima ban barshi ya daɗe kamar yadda ya saba ba ganin inda akalar labarinsa ya dosa a yau.
Misalin tara da rabi muka kulle gidanmu bayan mun gama fira da Bilal, na bawa Sakina ta kai min wayata maƙota saboda na samu caji, sai na alwalar na shigo ɗakin Inna na yi sallah isha’i, sannan na shiga na gyarawa su Sakina gurin kwanansu, ni kuma na dawo ɗakin Inna domin a yanzu na daina barinta tana kwana ita kaɗai.
Saman gado muka haye ni da Inna Noor na bayana daman duk inda nake kwana a nan yake kwanan, na yi matashin kai da fillon Habiba kamar yadda na saba sannan na yi Noor addu’ah bayan wacce ya karanta ta shiga bachi, ni ma na yi muka kwanta cike da aminci da salama.
Can cikin bachi naji Inna na tashina a hankali, ina buɗe ido hankalina ya tashi sosai, sakamakon jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar gidanmu da muka ji ana yi, ashe nice bachi ya lula da ni sosai ban ji ba har sai da aka tasheni su Sakina da Jamila kan tuni suka ji har sunyo ɗakinku sun ta ɓoya bayan Inna suna kuka, Noor ma yana ƙanƙame da Inna jikinsa sai rawa yake.
“Ku shige ƙarƙashin gado”
Inna ta faɗa kaɗan-kaɗan, ni kan araina na ce wane irin ƙarƙashin gado kuma ƙarƙashin gadon da itace ne muka saka a ƙasa ni da Habiba, saboda a samu yabuɗaɗɗiyar katifar ta tsaya. Kamin mu yi wani unƙuri sai dirowar mutane muka ji cikin ɗakinmu, daman ƙofar ɗakin ta cire ta can farkon shigowa gidace kawai ta rage muke rufe gidan da ita. Fitila mai haske sosai ɗayansu ya dallo min ba shiri na rumtse ido jikina na rawa na rumgume Inna ina saki fitsari abunka da mai mugun tsoro…
TO SU WAYE KUMA WAƊANNAN😨😱
Sakina da Jamila ne suka saka da Noor ne suka ihu ganin bindiga nikan dabam idanuwana a rufe suke addu’a kawai nake karantowa. +
“Ku yi mana shiru..”
Ɗaya daga cikinsu ya faɗa a tsawace cikin wata murya mai kamar doro, sai duk suka yi tsif kamar babu su a gurin.
“Dan Allah dan Annabi karku cutar min da yara ku yi haƙuri”
Shine abunda Inna take ta roƙo muryarta na rawa alamar tsoro yana tare da ita.
“Ki kwantar da hankalinki ba zamu miki komai ba ba zamu taɓa kowa na ki ba, kuɗi muke so ko abun kuɗi”
Jin wannan yasa na sassauta riƙon da nayi wa Inna na buɗe ido tare da ɗagowa na kalli fuskokin waɗannan mutane da suka zo neman kuɗi a gidanmu, ina ɗagowa ɗayan ya dalla min fitila a ido gashi ba shiri na sake rumtse ido.
Ɗan abunda Inna ta san tana da shi na canji taje ta ɗauko ta kawo musu jikinta sai rawa yake tana faɗin
“Shikenan na ke dashi a gidan nan Wallahi ba muda komai mu talakawa ne”
“Kina da ɗan kunnen zinari ko azurfa?” 1
“Wallahi bamu da shi”
Ta bashi amsa ciki kuka mai cike da tsoro. Ban sake jin sun ce komai ba sai kawai na jin nayi suna da bincikar kayan da ke ɗakin wasu kuma suka nufi ɗakinmu wacan dake waje suna bincika, hakan ya bani damar buɗe idona a karo na biyu na kalli mutun huɗu da suke ɗakin suna mana bincike, daga ganinsu manyan ɓarayi ne domin ɗauke suƙe da manyan bindigogi fuskarsu sanye da fuska irin ta manyan ƴan fashin nan dukansu danye suke da baƙar riga da jean banƙi.
Mun ga ikon Allah a wannan ranar domin komai sai da suka bincike, sam basu yarda bamu da komai ba, har tufafinmu sai da suka bincika suka tsince masu kyau, ragowar shinkafar da ta rage mana mana dafawa har da ita suka haɗa, wani abun ɗaure kai har da tukunyar da muke dafa abincin sannan suka ce duk mu rufe idonmu kuma mu kwanta, sannan suka fice suna cewa duk wanda ya ɗago sai sun halbeshi. Ni dai ba buɗe ido ba ko motsi ban sake yi ba har na kusan minti talati saboda kawai tsoro.
A daren babu wanda ya sake runtsawa daga ni har Inna da Sakina, Jamila da Noor ne kawai suka yi bachi, Noor ma sai da na rumgumeshi. Abu ɗaya ne ya tsaya min a rai har garin Allah ya waye, miyasa basu shiga gidan manyan masu kuɗi ba sai gidanmu? Beside waɗanne irin ɓarayi ne ma da zasu ɗauki tsofin sutura da ragowar shinkafa da ƴan canjin da basu kai dubu biyu ba da sunan sata da alama mu fa manyan ɓarayi ne ba ƙananan ba. 3
‘Turosu aka yi’
Shine abunda zuciyata take ta yawan nanata min, sai dai kuma waya turo su?
Washe gari mutane suka yi ta shigowa suna mana jaje tare da fatar allah ya tsare gaba ciki har da ƴan babban gida, sai dai wannan besa ɗayansu ya yi tunanin cewa mu koma can ba, duk kuwa da kasancewar rayuwarmu tana cikin hatsari saboda suna ganin idan muka koma zama tare da su lalurar mu ce zata hau kansu, kai tirrr da wasu ƴan’uwa!
Da yamma Jidda ta zo ita da mamanta suna jajanta mana take labarta min abunda ake faɗi a unguwa, wai gurin dai suka zo har wasu na cewa ba zasu rasa min fyaɗe ba sai dai ba zan faɗa ba, maganar ta ɓata min rai daman nasan dole mutane su zargi haka ganin bamu da Komai kuma ace sun zo gidanmu.
Baba Sulaiman ne ya kira mai gyara ya gyara mana tsohon ganbun na ƙofar gida da mutane suƙa ɓalle suka shigo. Tun da yamma muka bar gidan saboda ƴan’uwan Inna da suka sha kai akan sai dai mu dawo can da zama, ranar a tudun wada muka kwana gangaren tallatu sayin salamatu mai tuwo. Sun nuna mana mana kulawa sosai aka wuni ana firar ta nan na fahimcin Inna ma ta gano turosu aka yi, sai dai ita ta allaƙa abun ne ga Mustapha har take min faɗan wai na lallaɓa mu rabu lafiya da shi.
Bayan sallah isha’i Bilal ya kirani na kwatanta masa inda nake, ko minti arba’in ba a ƙara ba sai gashi ya iso tudun wada, na fito titi na shigo da shi cikin lungun na mu. Gaisawace first abunda muka fara yi sai yasa na kira masa Inna ya gaisheta tare da yi mata jaje sannan ya ce an gidansu suna gaisheta. Bayan Inna ta shige ya dawo kaina sai bugun cikina yake yana ta son ya ji idan sun min wani na san wannan ba zai rasa nasaba da maganganun mutane da yake ji ba.
“Kaima ka yarda da abunda mutane duke faɗa kenan”
Ajiyar zuciya ya sauke ya gyara tsayuwarsa ya ce.
“Yarda ta da rashin yardata duka suna gurinki, Wallahi komai kika faɗa min zan yarda da shi Nawancy”
“Idan har ka yarda da ni toh ka yarda da duk abunda zan faɗa maka, Wallahi basu min komai ba ko hannuna basu riƙa ba, babu wanda suka taɓa a gidanmu”
Sanyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jinginawa jikin iccen tarbejiya dake ƙofar gidan yana hamdala.
“Allah na gode maka, Wallahi Nawancy da sun taɓa ki ban san yadda zan yi ba ban san iya halin da zan shigaba”
“Da ba zaka iya aurena ba ko?”
Hakan yasa shi ɗagowa daga jinginen da yake da sauri yana kallona fuskarsa da ɗauke da murmushi.
“Nawancyta da gaske kike maganar nan da kika yi?”
Ya tambaya yana matsowa kusa da ni kamar zai haɗa numfashinsa da nawa, hanzarin matsawa baya nake sai ya yi caraf ya cafke min hannun yana cigaba da matsosa kusa da ni.
“Kin san waye ni babu abunda zan miki, kawai ina son na tabbatar ne, Wallahi Nawancy i’m ever ready to marry you dan Allah ki taimaka min”
“Mutane fa zasu gani”
Na faɗa a tsawalle ina kawar da fuskata, sai na yi sa’a ya sake ni, ina ganin hakan na juya da gudu na shige gida.
Babu irin kiran da be min ba ta waya amman na ƙi ɗagawa har ya gaji ya tafiyarsa.
Kwanan mu biyu a can muka dawo gida saboda tsallawa da muka yi saboda gidan gidan taro ne babu sakewa sosai, ga yaran gidan basa da ragowa a gaban idona suke buge Noor ba damar nayi magana ace na yi rashin ta ido su kuma ba zasu iya yi ma yaransu magana ba.
Ranar da muka dawo ma mutane sun ta zuwa yi mana jaje mutanen da basu samu zuwa mana washe garin da abun ya faru ba, saƙon kamfani kan kamar ƙa’ida ko da muka dawo mun tarar da wasiƙa biyu wacce aka kawo yau ita ce ta uku ban da ta waya da nake ta karɓa ko wace safiya da kuma yammaci.
Bayan na gama gyare-gyaren gida na shinfida tabarma na zauna tsakar gida ina ta nazarin abubuwan rayuwa ciki har da wannan abun da ya same mu, da kuma maganar ƴan sanda da suka yi mana izgilanci amman shiru har yau babu dpo babu labarinsa, ga kuma Jibril da ya sakoni a gaba yanzu.
Wai shi Jibril me yake nufi ne ya yi nadama ko kuma so yake na koma aiki ƙarƙashinsa ta yadda zai sake gallazamin ya ɗauka kamar da ne?
“Kut”
A fili na yi ƙwafa, kana na ɗaga kaina dake ƙasa na kalli Inna wacce ta fito daga ɗaki tana maganar aikina.
“Ni fa wannan lamarin har tsoro yake bani Nawwara, ban taɓa ganin wanda aka matsawa ya koma aiki kamar ki ba, anya babu wani abu?”
Na yi dariyar da ni ƙaɗai nasan abunda yake nan.
“Babu komai Wallahi kawai dai kin san abu idan aka ce maka da turawa ne, shiyasa”
“Amman ke miyasa kika tsaya kai da fata akan ba zaki koma ba, nifa ina jin da kamar akwai wani abu”
“Babu komai kawai ina musu jan ajine saboda susan ba ko wanne mai neman aiki ba ne wulaƙantacce, zan koma aiki Inna ai dole ma ne na koma aikin ko dan na bawa marar ɗa kunya! Kuma ni kaina ina da buƙatar aikin saboda zai taimaka mana mi tallafawa kan mu da kan mu” 4
Na faɗa ina sauke ajiyar zuciya Inna kuma tana amsa sallamar Malam Haruna mai gidan da muke haya…!