FETTA
CHAPTER 7
Aliya zata shiga d’akin ta, Taga na Fetta a bud’e, “Yau kuma bud’e ta bar d’akin”, Ta shiga ta jawo k’ofa, Ganin ta a sheme tasan ba lafiya ba, Ta tab’a ta taji bata numfashi, Hannu ta d’aura a kai ta fasa ihu, A guje Mallam ya shigo d’akin shima ganin Fetta yayi salati ya sanar da ubangiji, a rud’e ya fita, Ya ciko kofi da ruwan randa ya shek’e mata, +
Tayi firgigit ta tashi “Ya Mu’azzam Dan Allah kace mun wasa kake, kada ka barni”, Aliya ta fahimci meke faruwa cike da tausayin ta, Ta jawo ta jikinta ta rungume, Kuka ta saki mai d’acin rai, duniyar taji ta mata zafi, Ko shakka babu da gaske Ya Mu’azzam ya barta tunda har Umma bata ce wasa yake ba.
Kuka take sosai, Aliya na lallashin ta, Mallam yace ” Kiyi hak’uri Fetta, Allah yayi Mu’azzam ba mijin ki bane, kuma watak’ila auren sa ba alkhairi ba ne, Wani baya auren matar wani, Allah ya kawo miki miji nagari da zai k’aunace ki saboda Allah”,
A ranta ta cire soyayya ba zata k’ara ba, bata sha’awar sake son da’ namiji, bata shirya zuciyarta ta tarwatse ba, A yanzu ma tana daf da.
Alamun bacci tayi, wanda yasa Aliya raba jikinta da nata, Ta kwantar da ita kan katifa, Tasa bargo ta lullub’eta, Suka fita cike da tausayin ta.
Wani sabon babin kuka ta bud’e, K’irjin ta yayi nauyi tamkar an d’aura mata dutse, Da tasan haka soyayya take da bata fara ba, “Ya Allah ka cire mun soyayyar sa, Kada ka k’ara samun son kowanne da’ namiji”,
A daren bata runtsa ba da zazzab’i ta kwana.
Aliya bayan ta idar da sallar asuba, Ganin Fetta bata fito alwala ba, Ta lek’a d’akin, Kwance ta ganta tana rawar sanyi,
” Subhanallah baki da lafiya ne”, Ta fad’a tana tab’a jikinta zafi rau, Ta fita ta sanar da Mallam, “Ohh Kada ta jawo ma kanta wani ciwon”, ” Shiyasa tun farko banso soyayyar su tayi nisa ba”, Ta fad’a cike da damuwa, “Bara naje nan mak’wabta na kira Halima Nurse ta duba ta”,
Nurse ta duba ta tace zazzab’i ne, ta mata allura ta rubuta mata magani, Mallam ya karb’a, ba b’ata lokaci yaje yq siyo, Aliya ta lallab’ata tasha tea da bread, ta bata magani, Sai faman sannu suke jera mata, Ganin sun damu tayi k’ok’arin nuna taji sauk’i, Amma ina zazzab’in bai sake ta ba.
Mallam kad’ai ya tafi wurin sana’a, Aliya zama tayi jinyar Fetta, Da tayi motsi kad’an zatace meke damunta, ina ke mata ciwo, Fetta taga soyayya da kulawa wurin Aliya, Ba abunda zata ce musu sai Allah ya saka musu da alkhairi, Sun zama jininta ta d’auke su tamkar iyayen ta.
Suraj ne ya fito daga sashen Hajiya cikin shigar sa ta kamala, Daga yanayin tafiyar sa zaka san sauri yake,
” You have to drive fast, jirgin mu 10:00am zan tashi, an it’s already 9:45am”, Ya umurci mai tuk’i, Ya figi mota a 360.
“Ya Suraj idan yazo wurin har ya tafi, yana k’amshin sa”, Cewar Feena, ” Mayen turare yake amfani dashi, though wataran zaka ji yana wani k’amshi daban”, Su’ad ta fad’a, ” Yana yi ma mask turare ciniki”,
Hajiya na jin su murmushi kawai tayi, Son turare gadon sa yayi a wurin Mahaifin sa haka yake da son turare, ko nawa zai iya kashewa ya siya.
Bata ga Aliya ba, balle tasa ran ganin Fetta, Ta tambayi masu aikin sun san dalilin rashin zuwan ta, Suka ce a’ah, Bata tab’a haka ba, idan ba zata samu zuwa ba, Tana aikowa, D’aya daga cikin yaran masu aikin ta umarta tace gidan ta taga lafiya.
STORY CONTINUES BELOW
Fetta tunda tasha magani, bacci mai nauyi ya d’auke ta, Aliya na sharar tsakar gida, Lami tayi sallama ta shigo, “Ina wuni?”, ” Lafiya lau Lami”, “Hajiya ce ta aikoni naga lafiya yau baki je aiki ba”, ” Wallahi Fetta ce babu lafiya”, “Allah ya sawwak’e”
Ta koma ta sanar da Hajiya, “Feena tashi ki rakani na duba ta” , “Mama mai aikin zaki je dubawa”, ” Ita ba mutum bace, ni da bani da lafiya ba zama tayi ta kula dani ba, Feena ku cire k’yamar talaka a ran ku, kada ku manta wasu shekaru a baya u’re in the same situation da Fetta”, Ta had’e rai a ran ta tace “Ai da yanzu ba d’aya ba, kuma da Baba nada rai muna cikin rufin asirin mu”,
Haka rai bai so ba, Ta shiga mota ita da Hajiya, Driver yaja su zuwa gidan Aliya, Babu nisa cikin minti 2 suka kawo.
Aliya da matuk’ar farin ciki tarbe su, Ta shimfid’a musu tarbama suka zauna, Feena sai faman yatsina fuska take, Gidan tsaf yayi babu k’azanta, balle tace taga abun k’yank’yami.
Yaro ta samu waje, ta aika ya siyo mata ruwa da lemo, Ta jera a tray ta kai musu, ” Da baki wahalar da kan ki ba Fetta kad’ai muka zo gani”, “Mun gode sosai, amma Dan Allah kusha ruwa”, Hajiya kad’ai tasha,
Suka shiga d’aki suka duba ta, bacci take har suka fito bata sani ba,
” Aliya ina so na tambaye ki akan Fetta, Dan Allah ki fad’a mun gaskiya”, “In shaa Allahu Hajiya zan gaya miki”, ” Su waye iyayen Fetta?”, Tayi dan’ yi jim kad’an tace “Nima ban san iyayen ta ba”, ” Kamar ya?”, Hajiya ta tambaya da mamaki, Feena da taji haka, ta maido hankalin su gare ta, “K’ila ma yar’ tsintuwa ce” Ta fad’a a ran ta,
Aliya tayi gyaran murya ta fayyace ma Hajiya abunda ta sani game da Fetta, hadda rabuwar su da Mu’azzam wanda shine sanadin kwanciyar ta ciwo.
Hajiya jikin ta yayi sanyi, tausayin ta ya kamata tace “Na tausayawa Fetta, Allah zai baku ladar rik’on da kuka yi mata, In Shaa Allah ba da dad’ewa ba Allah zai mata sauyin rayuwa”, ” Allah yasa”, Fad’ar Aliya, “Amin In Shaa Allah, zamu koma”, Ta zaro dubu goma ta ajiye tace ” Ga wannan kuyi lalurar magani”, “A’ah Hajiya da kin bar shi”,
Mik’ewa tayi ta fice, Feena tabi bayanta, Aliya ta musu rakiya tana godiya.
Hajiya da sak’e-sak’e ta koma gida, wanda duk akan Fetta ne, yadda zata taimaka mata wurin samun farin cikin da chanji a rayuwarta, Feena na zuwa gida ta ba Su’ad labari, Sukayi ta tsegumi ashe ma ko asali bata da.
Da ta farka, Aliya ta sanar da ita zuwan Hajiya, Taji dad’i sosai, kuma ta yarda Hajiya mai k’aunar ta ce, Mace mai kud’i kamar ta, tazo duba talaka irin ta, da bata da kowa sai Allah, sai su Aliya.
*Bayan kwana biyu*
Ta bangaren Mu’azzam shima ya kwanta zazzab’i, Mahaifiyar sa har d’aki ta same shi, Taci mishi mutunci, Tace ” Ya kwanta ciwo ne, dan su janye k’udirin su toh babu fashi”
Haka ya lallab’a ya tashi, Ya d’auki dangana da niyyar yi ma iyaye biyayya, yasan In Shaa Allah ba zai tab’e ba.
Fetta na yak’i da zuciyar ta wurin cire Mu’azzam da mantawa dashi amma yana nan mak’ale, though ta rage jin shi kamar da, Number wayar sa da text messages da yake turo mata duka ta goge, banda babu kyau maida hannun kyauta baya, wayar ma mayar masa zata yi, Tana son manta komai and move on with her life kamar da.
Wanke-wanke take tsakar gida, tana sauraren karatun Qur’ani, wanda ke sata jin natsuwa a zuciya da gangar jikinta.
Rumaisa tayi sallama ta shigo, “Nayi fushi sai yau”, ” Dan Allah kiyi hak’uri, tafiya nayi kwana biyu” , “Ba sanarwa”, ” Nima sai a ranar nasan da tafiyar”, “An dawo lafiya”, ” Lafiya lau, Ya jikin ki?”, “Naji sauk’i”, ” Allah ya k’ara lafiya”, “Amin”, Ta jawo kujera ta zauna tana taya ta da d’auraya suna hira, Tana bata labarin soyayyar su da Munir.
” Uhmm ba’a ma soyayya shigar zurfi, tana da dad’i kuma tafi komai wahala, So babbar cuta, So masifa ne”, “Idan haka dace ba kenan”, Cewar Rumaisa, “Ina miki addu’ar kada ki tsinci kan ki a halin da na tsinci kaina, Allah ya bar ki da Munir ya nuna mana auren ku”, ” Amin kema Allah ya nuna mana da wanda yafi Mu’azzam”, (Taji labarin a wurin yan gidan su, “Hmm Rumaisa kenan, Soyayya sai ku”, ” Me kike nufi?”, “Bazan k’ara ba, ban shirya wani heartbreak d’in ba”, ” Kina fad’a ne kawai, sanda zaki fad’a tarkon k’auna waya sani”, Tace “Hmm”, Ita kan iya gaskiyarta kenan.
Bilkisu lafiya ta samu, Raunukan da K’onuwar sun warke sai tabo, Aunty Jummai ta hana ta fita ko’ina, wanda hakan ba k’aramin takura ta yayi ba, A cewar ta ai sai ta fita za’a k’ulla mata wani sharrin, burin ta Bilkisu ta koma gidan Suraj, itama tana son haka dan zaman gidan su sam baya mata dad’i, ta saba cin dad’i.
Shiri tayi tana jiran fitowar Bilkisu, Ta fito sanye da gyale, ” Maza koma ki saka hijabi, a haka zata ji sha’awar ki komawa dan’ta”, Ta koma ta sako k’aton hijabi, “Yawwa ko kefa, idan muka je ki mata ladabi sosai”, Bilkisu tace ” Toh Umma”, “Ungo wannan ki mak’ala a k’ugun ki, zai sa taji tana sonki”, Ta karb’a ta saka,
Ba kunya ta tasa Bilkisu har falon Hajiya, Ta fito tana shirin fita, Har k’asa ta duk’a ta gaisheta, Hajiya ta amsa cike da mamaki, bata tab’a duk’awa ba idan zata gaisheta, ” Barka da rana”, Cewar Aunty Jummai tana washe baki, “Barka kadai Jummai, kune a gidan namu”, ” Eh Bilkisu tace na rako ta, ta gaishe ki, kin kwanta asibiti bata samu zuwa ba”, “Allah sarki, ta kyauta, gashi fita zanyi ana jirana”, ” Ba komai ai mun gaishe ki, tashi mu tafi Bilkisu”, “Sai na aiko”
Daga Bilkisu har Aunty Jummai sunji dad’in furucin ta na k’arshe, A tunanin su aikowa zata yi Bilkisu ta koma, Maganin Mallam yaci kenan.
“Shikenan zaki koma gidan Suraj”, Aunty Jummai ta fad’a cike da murna, ” Na yarda aikin malamin nan tamkar yankan wuk’a”, “Ai na gaya miki, ranar da kika koma su Yelwa zasu ga rashin mutunci”, Mai Napep na jin su ya girgiza kai.
Aliya ta kammala ayyukan ta, Kamar yadda Hajiya ta buk’aci ganinta, ta nufi falon da Hajiya ke sadawa da yan aiki, Dawowar ta kenan, bata shiga d’aki ba, Tazo nan.
Cike da ladabi ta mata sannu da zuwa ta amsa, Tayi gyaran murya tace ” Wata alfarma nake nema a wurin ku, Allah yasa zaku mun”, “Alfarma Hajiya, mu muke dashi da zamu baki”, ” Fetta”, Aliya ta nanata “Fetta”, Hajiya ta d’aga kai ” Ina so ku bani ita na d’aura ma da’ na”,
Ta nisa tace “Kiyi hak’uri Hajiya, amma ina Fetta ina Suraj ai ajinsu ba d’aya ba, kuma ma shi ya ganta yace yana so”, ” Bashi ya gani ba, ni na gani naga ta dace dashi, tun zaman da mukayi da ita asibiti, na fara tunanin had’a su saboda kyawawan halayyar ta, ganin tana da wanda take so na janye k’uduri na, jin labarinta naji tausayin ta ya kamani da k’ara son had’a su”
“Ban k’i ba, amma bamu da hakk’i akan Fetta, ba zan tilasta mata ba, ina tausayin ta a matsayin ta na marainiya, da kinyi hak’uri Hajiya kin janye maganar nan, Fetta ba kalar Suraj bace, sam basu dace ba”, ” Nima bana so a shiga hakk’in ta, da kaina zan mata magana, Zancen basu dace ba babu inda Allah ya haramta aure tsakanin su, da talaka da mai kud’i duk matsayin su d’aya a wurin Allah”
Aliya tace “Toh Allah ya tabbatar da alkhairi”, ” Amin”, “Zaki iya tafiya”,
Ta koma gida cike da wasi wasi, Wani b’angare na zuciyarta na farin ciki dan ba k’aramar d’aukaka Fetta zata samu ba idan ta auri Suraj, iyayen Mu’azzam da suka hana shi auren ta, zasu ga Allah ya bata wanda yafi shi, ta wani b’angare bata farin ciki, ko kad’an bata so a shiga hakk’in Fetta a musguna mata.
Hajiya da kanta ta shirya tazo gidan, Ta sanar da Fetta k’udurin ta na son had’a ta aure da Suraj, Kamar ruwa yaci ta tayi shiru, Zuciyarta na bugawa kamar zata fasa k’irjin ta ta fito, ko rabuwarta da Mu’azzam bata ji tashin hankali kamar wannan ba,
Hajiya ta kama hannun ta tace ” Ki taimaka ki amince, In Shaa Allah auren nan zai kawo sauyi a rayuwar ki”, Tunanin ta ya tsaya cak, k’wak’walarta ta cunkushe, Hajiya mace mai tak’ama da dukiya, matar da take matuk’ar ganin k’ima da girmanta itace a gabanta tana neman alfarma wurin ta, ya zama dole ta amince ko da hakan zai zama silar bankwanan ta da farin ciki, “Na amince Hajiya, Na amince”, Rungumeta tayi jikin ta tace ” Nagode Nagode sosai Fetta, Allah ya haskaka rayuwar ki, yasa auren nan ya zama sanadin alkhairuka a rayuwar ki”, Kasa amsawa tayi har ta fice.
Kukan data ke dannewa ya taho mata, ta shiga rairawa, ta kasa tunanin komai sai kuka.
Jin shigowar Aliya, Tayi saurin share hawaye, Aliya ta zauna gefen katifa kusa da ita, “Fetta tashi muyi magana” +
Ta tashi zaune tana sunkuyar da kanta k’asa dan kar ta fuskanci tayi kuka, “Meyasa kika amince da auren Suraj bayan ba so kike ba?”, Cikin sanyin murya tace ” Ina so, har zuciyata na amince “, ” Meyasa ki kuka?”, “Ina tunanin rabuwa daku ne”, ” Fetta ki gaya mun gaskiya, idan bakya son auren nan, ba wanda zai miki, bana son kiyi auren da babu soyayya a ciki, bashi da dad’i”, Ta had’iye miyau da take jin su tamkar ruwan zafi a mak’oshin ta tace “Na amince Umma, kada ki damu”, Ta sauke ajiyar zuciya tace ” Allah ya tabbatar mana da alkhairi, zanje nan mak’wabta”, “Sai kin dawo”,
Aliya na fita, wasu hawaye masu zafi suka wanke kuncinta, ” Meyasa kika amince da mutumin da bakya so, Mutumin da a ko da yaushe kyara da hantara ce tsakanin ku, Mutumin da baya ganin girma da k’imar talaka, Ya d’auka kud’i sune komai” Zuciyar ta ta fad’a mata,
“Bani da wata mafita, bazan iya k’in amincewa da k’udurin Hajiya Tumba ba”, Ta fad’awa kanta, Mik’ewa tayi, Kanta na sarawa, Ta shiga toilet ta d’auro alwala, Ta fara gabatar da nafilfili tana rok’on Allah ya kawo sanadin da za’a fasa auren, Ta amince da auren shi ne ba dan zuciya, ruhi da gangar jikinta naso ba, Taya zasu yi rayuwa a inuwa d’aya da mutumin da bata so wata alak’a na had’a su.
Hajiya tumba ta koma gida cike da murna, Fetta ta amince da auren, ita kad’ai ce fargabar ta, Suraj baya tsallake maganar ta, Jira take gobe ya dawo ta sanar dashi.
Fetta na danne damuwarta a gaban su Aliya, but deep inside her heart, Bak’in ciki, damuwa da tashin hankali ne cunkushe, Aliya ta lura da sanyin Fetta, but ta d’auka zullumin rabuwa dasu ne kamar yadda ta fad’a, Itama hakan take ji, Fetta ta zama part of them.
Da ta sanarwa Mallam ya kira Fetta Ya tambayi ra’ayin ta, Tace ” Ta amince”, Yayi addu’ar Allah ya tabbatar da alkhairi.
A daren bata runtsa ba, Faman juyi take kan gado, Ta rasa ina zata ranta taji dad’i, Cikin satin nan ta had’u da jarabawa guda biyu, wanda suka jefata a cikin matsananciyar damuwa, Rabuwarta da Mu’azzam tafi mata sauk’i akan auren Suraj, Mu’azzam zata iya manta shi, Suraj fah rayuwa ce ta aure zasu yi, wanda tayi imani ba rayuwa ce mai dad’i ba, watak’ila ma ya saketa idan har ya amince da auren nata, Addu’ar ta Allah yasa kada ya amince.
Yasmeen shiru tana ta jiran kiran Fetta, taji haushin rashin karb’ar number ta, Kayan ta kalla tace “Maybe bata buk’atar su, gobe sai a kai su gidan marayu na gaji da ajiya”
Suraj ya rasa dalilin da yasa wannan karan baya d’okin zuwa Kano kamar ko da yaushe, Yaran sa ja baya suka rik’a yi dashi ganin baya cikin good mood.
Kamar ko da yaushe, bayan yaci abinchi yayi wanka, ya huta, Ya fito da shirin gym, Hajiya ta buk’aci ganin sa.
Ya zauna a gaban ta k’asan carpet, “Suraj”, Ta kira sunan sa in a serious tone, ” Na’am”, “Kayi auren farko wanda bashi da bambamci da baka yi ba”, Ya gyad’a kai, ” Ana auren mace da kyawun halinta da natsuwar ta wanda su na hango maka a tattare da Fetta, ina so ka cika mun burina na auren ta, na tabbatar ba zaka yi da na sani ba”,
Mugun fad’uwa gaban sa yayi, Zufa ta karyo masa, Da k’yar ya iya cewa “Mama please ki bar zancen nan, haka Bilkisu na aure ta, a k’arshe ga muguwar d’abi’ar da take”, ” Halin Bilkisu da Fetta ba d’aya ba”, “Haka kika ce akan Karima da Bilkisu, Mama meyasa kike son had’a ni aure da wanda basu dace dani ba, Bilkisu na aure ta a matsayin ta na yar’uwa ta, Wannan da kike son had’a mu fah, yar’ mai aiki”
STORY CONTINUES BELOW
“Yar’ mai aiki ba mutum bace, Marainiya ce iyayen ta sun rasu, ko dan maraicin ta ka tausaya ka aure ta”, ” Mama marayu nawa ne a duniya sai ita, idan marainiya nake son aura akwai su da yawa a gidan marayuna”, “Ita na zab’ar maka a matsayin abokiyar rayuwa, na yarda da nagarta ta, Fetta will make a good wife, ba zaka tab’a dana sanin auren ta ba i assure you”,
Zufa ke cigaba da tsattsafo masa duk da Ac dake falon, ” Tana da wanda take so kada mu shiga hakk’in ta”, “Sun rabu”, Wata fad’uwar gaban ya sake ji, Yaso hakan ya zama hujja na janye zancen auren su, ” Mama ita ta amince da aurena?”, “Sosai, ita da ban haifa ba, ta amince babu gardama”,
Shiru yayi yana jin haushi da tsanar ta na ratsa shi, Shiyasa ta zauna asibiti dan ta siye Hajiya tace ya aure ta, Yasan maganin ta.
Kafin ya dawo daga tunanin sa, Hajiya ta mik’e ta bar falon, Yasan tayi fushi, ” Ya ilahi”, Ya furta yana dafe kai, “Shi Suraj ya auri yar’aiki abunda ba zai tab’a yiyu wa bane, meyasa Mama bata duba matsayin shi ba, ta rasa dawa zata had’a shi sai wannan yarinyar, bai k’i ya k’are rayuwar sa babu aure ba, a ganin sa babu macen da zata so shi dan Allah, sai dan kud’in shi ko kyau.
Fuskar sa babu annuri ya fito sashen Hajiya, Driver ya umarta yaje yanzu ya taho masa Fetta, Yace Hajiya ke buk’atar ganin ta, a ganin sa yafi k’arfin ya taka yaje gidan su, Ta raina shi ta d’auka he is interested in her, ko wani ya gansa ya raina shi.
Fetta ta k’ara zama shiru shiru, Kullum tana d’aki tana sauraren Qur’ani, Abinci bata iya ci sosai, sai dai ta jagalgala ta ajiye, Damuwa ta ma zuciya da ruhin ta yawa, Sau da yawa ta kan ji kamar ta gudu, Zuciyar ta kece mata ta gudu taje ina, bata san wane hannu zata fad’a ba, Su Aliya zasu shiga tashin hankali na rashin ta, Wannan tunanin ke sa ta fasa aiwatar da haka.
Yaro ya shigo yace ana kiran Fetta a waje, ” Waye?”, Aliya ta tambaya, “Wani ne a cikin mota mai kyau”, ” Allah yasa Suraj ne”, Ta fad’a a ran ta, A fili tace “Je kace tana zuwa”,
Ta lek’a d’akin Fetta ” Ki fito kinyi bak’o”, “Bak’o Umma”, ” Eh kiyi sauri yana jira”,
Tunani take waye, Zuciyar ta sam bata kawo mata Suraj ba, A yadda yake jin kansa tasan bazai tab’a zuwa gidan su ba wurin ta, Hijabi ta zura ta fito, Suka gaisa da driver yace “Hajiya ke buk’atar ganin ta”, Tace ” Bari ta sanar da Umman ta”
Ta koma ciki, ta fad’awa Aliya, tace a dawo lafiya.
Taso ya barta ta tafi a k’asa, Yace Hajiya tace ya taho da ita, Ba dan ranta yaso ba, Ta shiga, Motar kanta ta d’auki k’amshin Suraj, Toshe hancin ta tayi, sam bata son abunda zai rik’a tuna mata dashi, Addu’ar ta Allah yasa kiran da Hajiya ke mata, cewa zata yi ta janye k’udurin ta na son had’a su aure.
Yayi parking motar a cikin harabar gidan, Yace “Tana sashen Sir Suraj”, Kiran sunan shi sai da gaban ta ya fad’i, Ta fito jikinta kamar ba lakka, Tana tafiya tamkar wacce k’wai ya fashewa a ciki, K’irjin ta na bugawa,
Da sallama ta tura k’ofar falon, sanyi had’e da k’amshi ke ya rasa hanci da jikin ta, Idon ta ya sauka kan k’aton hoton sa dake cikin glass, an jingina shi da bango, Ya masifar yi kyau a hoton, Sanye yake cikin riga da wando, turawa ne a bayansa wanda ke nuna ba k’asar yayi hoton ba, Idan baka san shi ba, zaka rantse shima baturen ne.
“Ya miki nisa na har abada, sai hangen nesa, da kin taimakawa kanki kin d’auke idon ki daga kallon sa”, A tsorace ta juyo jin muryar sa tayi daga sama,
Idonta ta sauke cikin nashi, Dukkan su suka ji fad’uwar gaba, Kanta ta sunkuyar k’asa, Ya shiga matso ta, tana ja da baya, zuciyar ta na bugawa kamar zata fasa k’irjinta ta fito saboda tsoro, mai mutumin nan yake shirin aikata mun, Jin k’arar fashewar abu, ta tsaya, Ya cigaba da matsowa, Tayi baya, kwalba ta soki k’afarta, Yatsina fuska tayi alamun azaba, Ya tsaya daf da ita,
” D’ago kai ki kalleni, ki kalli kanki ki fad’a mun idan mun dace da juna “, Kanta k’asa, zugin zafi da k’afarta ke mata ya isheta, ” Am not ur type, Suraj ba ajin mace irin ki ba ne, bazan tab’a sonki ba, ko nace ina sonki k’arya ne” Dama tasan ita ba ajin shi bace, bata san meyasa Hajiya zata had’a su ba, ina ita talaka mara dangi zata auri Suraj,
“Ki fad’a nawa zan biya ki, ki fasa aure na, nasan dukiyata tasa kike son aurena, ko rabin ta kike buk’ata zan mallaka miki, nafi so na rasa komai akan na aure ki”
Maganganun sa jin su take tamkar saukar tafassasun ruwan zafi a gare ta, Hawayen dake shirin zubo mata ta mayar dasu, cikin dakewa tace “Ba komai kud’i ke siyawa ba, Soyayyar gaskiya ba’a siyan ta da kud’i, zaman lafiya da kwanciyar hankali kud’i baya kawo su, Mutunci yafi kud’i, Arzik’i Allah ke ba dashi ga wanda yaso a lokacin da yaso, talaka ba dan Allah baya son shi ba ya hana mishi arzik’i akwai manufar sa na yin haka, Baka da arzik’in da zaka biyani, Zan aure ka ne saboda Mahaifiyar ka amma baka cikin jerin mazan da nake so nayi rayuwar aure dasu, kana tunanin kowacce mace burin ta ta auri mai arzik’i, ka manta nagarta da kyawun hali sune ginshik’in zaman aure”,
Tana fad’ar haka ta rab’a gefan sa ta wuce, tana d’ingisa k’afa, jini na zuba, Tsaye yayi tamkar wanda ruwa yaci sa, Kalaman ta na mishi yawo a kai.
Driver yace tazo ya kaita gida tace bata buk’ata, Da k’yar ta kai kanta gida, k’afarta rad’adin zafi take, but kalaman sa sunfi mata rad’adi akan ciwon ta, Sauk’in da taji a ranta ta mayar masa da magana, wanda ya gare mata wani nauyi a k’irji.
Aliya da sauri ta tarbe ta, tana tambaya meya sameta, Tace ” Kwalba ta taka”, Hijabi ta zura ta rik’eta tace suje chemist, An mata dressing wurin, jinin ya tsaya, Suka dawo gida.
D’aki ta shiga ta kwanta, Kalaman Suraj na mata yawo a k’wak’walwa, “Yadda ba zaka tab’a sona ba, nima bazan tab’a son ka ba, Ina ma ana shiga zuciya da na bashi damar da zai shiga yaga yadda bana k’aunar auren sa” Ta fad’awa kanta,
Daga tsaye bai san lokacin da ya kai zaune ba, Ya rasa tunanin me zai yi, Kalaman ta ke ta yawo a brain d’in shi, Yana son yarda da ita, wani b’angare na zuciyar sa na nuna masa kalaman yaudara ne da dad’in baki.
Hajiya Tumba kud’i ta aikawa Aunty Jummai, bak’in ciki kamar ya kashe su, Ta tasa Bilkisu zuwa gidan Malamin tsibbu, rabin kud’in shi ta bata, Ya tabbatar mata zai yi aiki sosai akan Suraj da Mahaifiyar sa hankalinsu ya karkato kan Bilkisu.
Kiran sa da aka yi ana buk’atar ganin sa gidan Marayun sa yasa ya mik’e, Duk abunda ya shafi gidan Marayun sa baya wasa dashi,
Ya fito yana jin kansa unusual, Tunanin da kalaman yarinyar sun kasa barin zuciya da k’wak’walar sa.
Kaya ne aka kawo gidan Marayun Duk kayan da aka kawo ba’a amfani dasu, sai yazo ya gani ya tantance.
Bud’e kayan yayi, Yaja tsaki yace “Kayan nan babu na kirki a ciki, wani wari suke na bararoji, sun tsufa da yawa”, Kala biyu kad’ai ya cire sauran yace a zubar, A cikin kayan yaga wani d’an k’aramin littafi, Ya bud’e, Bai gane komai da aka rubuta ba, dan ba yaren da yake fahimta bane. 1
Ya saka a aljihu, Ya duba marasa lafiya, Akwai clinic a cikin orphanage d’in, da k’wararrun likitoci.
Garin ya dinga zagayawa, Yayi hakan ne dan ya rage wa kansa damuwa.Hajiya ta kira kawo Sule tace suje nemawa Suraj auren Fetta, Ta bada kud’i masu yawa a siya goro dasu sweets, da sadaki dubu hamsin, Ya sanar da sauran yan’uwan sa, Da yawa sun so yarinyar su zai nema, tunda an watse da Bilkisu. +
Sunzo kamar yadda al’ada ta tanadar, Daga yanayin fuskokin su zaka san sun raina irin gidan da Suraj ya nemi aure, Malam jikinsa yayi sanyi daga yanayin da suke amsa su shi da sauran yan’uwan shi, Basu dad’e ba suka tafi.
Ansa biki nan da sati biyu, Hajiya ta buk’aci haka, bata so a d’auki lokaci.
Malam ya samu Aliya a d’aki, “Ni fah jikina yayi sanyi da wannan al’amari”, Fuska d’auke da damuwa tace ” Meya faru?”, “Baki ga k’allon k’ask’anci da mutanen nan ke mana, ga dukkan alamu sun raina arzik’in mu, ina tsoro Fetta tasha wahala a wurin su”, Aliya ta sauke ajiyar zuciya tace ” In Shaa Allahu alkhairi zai biyo bayan auren nan, kuma ai ba dasu zata zauna ba”, “Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ya bata farin ciki da kwanciyar hankali”, ” Amin”
Fetta na kwance d’aki, sam bata jin dad’in duniyar, Aliya ta shigo da sallama, Ta tashi zaune tare da amsa sallamar, “Masu neman auren ki yanzu suka tafi, sun kawo sadaki da goro an saka biki sati biyu masu zuwa”, Mummunan fad’uwar gaba taji, Ta sunkuyar da kai tamkar mai jin kunya, but zuciyar ta ke bugawa kamar ta fasa ihu, wani k’ulloto ya tsaya mata a mak’oshi, Aliya murmushi tayi tace ” Sarkin kunya”, Ta mik’e ta fice.
Suraj da yaji zancen anje nema masa aure har an saka biki nan da sati biyu, Ya shiga tashin hankali, Mahaifiyar sa ce babu yadda zai yi, da taga mugun b’acin ran sa.
“Mama da gaske Fetta ce Ya Suraj zai aura?” Feena ta tambaya, “Eh”, ” What!”, Su’ad da Feena suka fad’a a tare, “Bararojin da bata da asali”, Feena ta fad’a, ” Mama Ya Suraj ne zai auri Fetta, tabbb”, Su’ad ta fad’a tana jijjiga kai,
“Akwai haramcin aure ne a tsakanin su”, ” Mama ba haramcin ba, amma wallahi ba ajinsa bace, masu aiki ne fah, kuma ba’a san dang…..”, Tsawar da Hajiya ta mata, Yasa taja bakin ta tayi shiru,
“Kada na sake jin bakin ku, marasa hankali da tunani”, Ta shige ta bar su,
” Ah ba banza ba, wallahi asiri tama Mama”, Cewar Su’ad, Feena tace “Ta bata a abinci ta cinye shiyasa ta zauna asibiti, wallahi ta cuce mu”, ” Friends d’in mu ai sai su raina mu, yar’mai aiki fah bararoji”, Kowaccen su ta had’e rai kamar zasu yi kuka.
Su Yelwa da labari yaje musu, Sunyi ta gulma a yar’ mai aiki ya k’are, Karima naji bata ce komai ba, Maza take bi irin manyan Alhazai tana samun kud’i, Iyayen ta basa mata komai ita da yaron ta.
“Kutumar uba, Suraj ne zai yi aure kuma da yar’ mai aiki, wallahi ba zai yiyu ba”, Aunty Jummai ta fad’a cike da masifa, ” Haka naji, jiya ma aka kai kayan sa rana” Bilkisu ta fad’a tana hawaye, “Ke Dalla share hawayen ki, ba za’ayi shi ba, sai na shiga na fita ya lalace” Ta fad’a tana dukan k’irji.
Suraj ya tattara ya koma lagos a cewar sa zai dawo idan ana saura sati d’aya biki but bashi da niyyar dawowa har a gama, sai ta gaji da zaman jiran sa, Ta koma gidan su.
Fetta kewar Mahaifin ta take ji sosai, Tana buk’atar wani abu da ya dangance shi da zai rage mata kewa, Wayarta ta jawo, tayi searching number Yasmeen ta kira, bugu biyu ta d’auka,
Kamar zata fasawa Fetta dodon kunne saboda murna, “Ai na d’auka ba zaki kirani ba”, ” Zan kira mana, abubuwa ne suka mun yawa”, “Allah Sarki, Ya gida da komai?”, ” Lafiya lau”, “Kimun kwatancen gidan zanzo na karb’a”, “Ai da naji ki shiru, na bayar da kayan gidan marayu”, Fetta taji ba dad’i but ko ba komai gidan marayu ne zata samu lada, ” Allah ya kai ladar kabarin sa”, “Amin”, ” Zanyi saving number ki, na rik’a kira muna gaisawa”, “Toh nagode”, Sukayi sallama ta kashe wayar, A fili ta furta ” Allah ya jik’an ku iyayena”
*Bayan sati d’aya*
Aliya nata faman shirye shirye tare da taimakon yan’uwan ta, Yau za’a kawo lefe, Fetta na d’aki sam bata fito ba, balle ta taya aiki, hayaniyar su ma hawa mata kai yake, Da sun san yadda ta tsani auren da basu wahalar da kansu wurin yin hidima ba, a zuciyar ta tana jin ba aure ne mai d’aurewa ba, ta tabbata Suraj ba zai zauna da ita ba, Yanzu ma umarnin Mahaifiyar sa yabi.
Aliya sunyi abinci kala-kala, daidai gwargwado na tarbon bak’i, Bayan sallar la’asar, Suka kawo lefe akwati sha biyu hadda Aunty Jummai da Yelwa cikin yan kawo lefe wanda gulma ce ta kawo su, Dangin Aliya sun yaba irin kayan da aka zuba, wasu a ganin su bata cancanta ba, ita ba yar’ kowa ba mara asali.
Duk abunda ake tana ji daga d’aki, Tana jin kamar ta fita tace musu bata son auren, Pillow ta d’auka ta toshe kunne, Hawaye masu zafi na zarya kan kumatun ta.
Yan kawo lefe sun tafi kowa da abunda yake sak’awa a ran sa, Da yawa sunce bata dace da Suraj ba yafi k’arfin ta, sun manta a ka’idar aure babu mai kud’i ko talaka, Kud’i basu ne rayuwar aure ba.
“Kayan nan sai a raba biyu, ki bata rabi, muma ki bamu, ki d’auki saura”, Cewar Hafsa Yayar Aliya, ” A’ah Ya Hafsa ba za’a yi haka ba, kayan marainiyar Allah bamu da hakk’i akan su”, “Ahh lallai Aliya baki da wayo, hannun wa yarinyar ta tashi bake ba, ta sanadin ki tasan uwar yaron nan”, ” Duk da haka ina tsoron tab’a kayan maraya”,
Taja tsaki ta fice rai a b’ace, Ta koma ta sanar da sauran yan’uwa dama su suka aikota, Suka shiga cewa Aliya bata da wayo, bata kyauta ba, su sha wahalar aiki ta kasa basu komai, Mutum biyu kad’ai suka ce tayi gaskiya marainiya ce, Aka yo kansu, Dole suka yi shiru, Haka suka rabu da Aliya ba arzik’i, sunce sun zare hannun su daga harkar bikin.
Aliya taji bak’in ciki sosai, Mallam ne ya kwantar mata da hankali, Yace “Yan uwan sa zasu maye mata gurbin su”, Duk abunda ke faruwa Fetta bata sani ba.
Ganin har sati d’aya bai dawo ba, Hajiya ta kira sa, Yace wasu ayyuka suka tare sa, Ta jadadda mishi ya tabbatar ya dawo kafin biki, Ya kashe waya cike da takaicin tuna mishi auren bararoji.
Hajiya tasa an sake sabon paint duka gidan, An k’ara gyara sashen Suraj, Tace Aliya kada suyi komai na kayan d’aki ita zata yi, Aliya taso cewa a’ah, Ta hana ta tace a matsayin ya’ ta d’auki Fetta, Ta mata godiya sosai.
Sababbin furnitures aka saka sashen, Kayan kitchen tsadaddu Hajiya ta zuba, Feena da Su’ad kam sun k’ara gaskata Fetta asiri tama mata wannan zumud’i da take akan auren, Addu’ar su Allah yasa asirin ya karye kafin auren dan abun kunya ne ace Ya Suraj zai auri Fetta.
” Ya kamata mu san event nawa za’ayi dan mu san shirye-shiryen da zamu yi”,Cewar Faryda(Islamiyyar su d’aya, Rumaisa ta sanar dasu), Rumaisa tace “Kema kya fad’a kullum ina fama da ita tayi shiru sai murmushi wai ita mai kunya”, “Kuma ita ba fulani ba, mik’o mun wayar ta, mu kira angon muji ta bakin sa”, Wayar ta shiga dubawa babu wani suna da yana nuna number sa, “Kar kice mun baki yi saving number shi”, ” Eh ban yi ba gudun snatchers”, “Idan zaki kira sa fah”, ” Na haddaceta kamar yadda na rik’e suna na”, Suka kwashe da dariya “Ahh soyayya ruwan zuma, Allah ya bamu mu rama”, Cewar Faryda, A ranta tace ” If only kun sani, ko za’a shak’eni ban san ya number sa take ba, me ma zanyi da ita”,
Aliya ta zage wurin siyan kayan gyaran jiki, tana ma Fetta, Tana bin Aliya ne kawai ba dan ranta na so ba, bata ga amfanin su ba, Yau ma dilka ce ta shafe mata jiki dashi, Tana zaune tsakar gida.
” Amarya! Amarya wannan gyara haka”, Rumaisa ta fad’a, Murmushi kawai tayi, “Allah na son ki Fetta, a cikin d’an k’ank’anin lokaci Allah ya baki wanda yafi Mu’azzam”, Murmushi tayi a ran ta tace “Wanda yafi mugayen hali ba”, Haka tayi ta tsokanarta sai dai tayi murmushi.
Minti ashirin yayi a jikinta, Ta shiga wanka, Ta fito tana shafa mai, Aliya ta lek’o tace ta shirya da sauri, zasu je gidan Hajiya, Ta tsinci kanta da fad’uwar gaba, Ta shirya jiki ba k’wari.
Falon Hajiya tsit, sai k’arar TV dake tashi, Zaka d’auka babu kowa ciki, Mutanen ciki kowa ya zauna jigum.
Sababbin fuskokin da ta gani, wanda ko shakka babu daga shigar su da yanayin su zai tabbatar maka da buzaye ne, Da kallo ta bisu, suma sun tsare ta da ido.