FETTA
CHAPTER 8
Fetta kece dai kamannin ki basu canza ba”, Cewar wani dattijon mutum, ” Fettan mu ta girma, kin tafi kin barmu muna ta cigiyar ki” D’ayar matar ta fad’a, +
Kanta ne ya masifar d’aure mafarki take ko da gaske, wad’annan mutane bata tab’a ganin su ba, ko yan’ uwan ta ne, “Kar dai kice baki gane mu ba”, Mutumin ya fad’a, ” Ban gane ku ba, kuna da masaniya ne akan dangi ne”, “Haba Fetta mu girma mu tashi dake, ki nuna baki san mu ba”, Matar ta fad’a,
Kafin tayi magana, Aunty Jummai tace ” Kada ki raina mana hankali kinji koh”, Da mamaki ta bita da kallo, Hajiya tace “Zauna Fetta”, Sai a lokacin ta samu zama, ” Ki fad’a mun tsakani da Allah, meye tsakaninki da mutane nan”, “Wallahi ban san su ba, ban tab’a ganin su”,
” Laahhh ni Hard’o ne baki sani ba”, Ya fad’a yana tab’a hannu, Hajiya ce ta mishi alama da hannu yayi shiru, Ta juya kan Fetta tace “Kada kiji tsoro, ki fad’a mun gaskiya, sun gaya mun komai a game dake”, Kanta ya fara d’aurewa ta fara shiga rud’u tace ” Me suka ce miki Dan Allah?”,
Hajiya ta gyara murya tace “Iyayenki sun rasu tun kina jaririya, suka barki a hannun k’anin mahaifinki wato Hard’o, a wani kango kuke zama, yana garuwa, Matar sa ke rainonki har kika girma kika yi wayo, Ta fara zuwa dake tasha wurin bara, Mazan tasha da yawa suna sonki saboda kyan ki, da haka suka fara jan hankalin ki da kud’i, tun kina shekara goma kika san maza, ki kwanta dasu su baki kud’i”, ” Ki kwanta dasu su baki kud’i”, Ya sauka a kunnen Suraj, da shigowar sa kenan, Hajiya ta matsa masa ya dawo,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un”, Ta shiga maimaitawa, jin sharrin da aka k’ullu mata da Allah kad’ai zai wanke ta,
” Karuwa kenan, Karuwa zan aura”, Duka suka juyo kallon su gare shi, banda Fetta da taji kalmar Karuwa tamkar saukar aradu, Kuka take son yin ko zata rage nauyin da k’irjin ta ya mata, jin ta take tamkar a wata duniya, jikinta banda kyarma ba abunda yake, Aliya kasa ko da k’wararran motsi tayi, “Meyasa Fetta zata b’oye mata ainahin labarin ta?”, Suraj ya k’arasa shigowa cikin falon, Zuciyar sa na tafarsasa, wane masifar haushi da tsanar Fetta yake ji, tamkar ya rufe ta da duka,
Ta saitin ta yazo wucewa, ya take mata yatsan hannu, sai da yayi k’ara, Tayi saurin janyewa cike da azaba, tana yarfa hannun,
” Ya akayi ta bar wurin ku?”, Aliya ta tambaya, “Wani ta kwanta dashi, yak’i biyan ta kamar yadda yayi alk’awari, ta d’auki kwalba ta buga masa ta gudu”,
Hannu biyu tasa ta toshe kunne, k’wak’walwarta ba zata iya d’aukar labarun k’aryar da ake fad’i akanta ba, ” Munafuka bud’e kunnen ki”, Ya daka mata tsawa, Ko gezau batayi ba, Ya d’aga hannu zai falla mata mari, Hajiya tace “Kul, kar ka fara”,
Hajiya ta taso ta d’aga ta tace ” Taso muje”, Ta mik’e tabi Hajiya ba dan tasan inda take jefa k’afar ta ba, D’aki ta shigar da ita, ta zaunar da ita kan gado, ta saka ma k’ofa key,
“Fetta ina so muyi magana dake kamar yadda uwa zata yi da yar’ ta”, Kai kawai ta iya d’agawa, ” Ki fad’a mun gaskiya tsakani da Allah”,
“Wallahi Hajiya Allah shine shaida ta, bansan su ba, bansan nufin su namun wannan sharri ba, Mahaifiyata ta rasu tun ina shekara biyu, Mahaifina yan fashi suka kashe shi, bansan kowa nawa ba, a gidan Alhaji Adamu na tashi naga Mahaifina na gadi, kisa a miki bincike”, Hajiya taji ta gamsu da zancen ta, tabbas wani tuggun aka shirya dan a lalata auren, Tasan abun yi,
STORY CONTINUES BELOW
” Na yarda dake, ki kwantar da hankalin ki kinji, taso muje”, Suka fito a tare, Nauyin da k’irjin ta ya mata ya rage, ko ba komai Hajiya ta yarda da ita, “Hard’o kuje zan neme ku”, ” Da Fetta zamu tafi?”, Matar ta tambaya, “A’ah zata biyo ku daga baya”, Cike da murna suka ce ” Toh”, Ta basu dubu biyu suyi kud’in mota,
“Meyasa baki barta ta bisu ba, zaman me zata cigaba da yi”, Cewar Suraj, ” Kafin a yanke hukunci ana son gudanar da bincike”, Hajiya ta fad’a, Mik’ewa yayi ya bar falon, dan idan yana kusa da ita, gabansa ke yawaita fad’uwa yana jin haushin ta, Aunty Jummai ana ta b’ata rai ba haka aka so ba.
Hajiya ta kira Aliya gefe ta mata bayani, Ta fahimta taje su koma gida, Aliya ma ta yarda wani tuggu aka shirya ma Fetta, Allah ya tsare ta da sharrin duk mai sharri,
Sai da ta kwanta kan katifar ta, ta samu damar fitar da k’ulloton da ya tsaya mata a mak’oshi ta hanyar kuka.
Hajiya nan take tasa a binciko mata, labarin gidan Marigayi Alhaji Adamu da mai gadin sa, Cikin awanni 3 aka kawo mata komai, tace a nemo mata yaransa guda biyu, da wasu mutane da suka san gidan kafin rasuwar sa.
Ta tattara shaidun ta gaba d’aya, Ta had’a kowa kamar waccen ranar banda Suraj ya fita shagunan sa, Yaransa biyu na ganin Fetta suka ganeta, da yan’uwan sa su biyu, Nan suka bada duka tarihin da suka sani akan Fetta,
Hard’o da Matar sa tuni suka fara had’a zufa, Hajiya tace “Ko kunji?”, Suka d’aga kai sama, ” Zaku fad’i gaskiya ko sai kinji ko a cell”, Tuni Hard’o yace “Bata kai can ba Hajiya zamu fad’a, Wallahi hayar mu akayi, mu bada shaidar k’arya dan aure ya lalacd, a biya mu dubu goma”, ” Waya saka ku?”, “Wani mutumi ne yazo ya fad’a yana yace shima aiko shi akayi”,
Aunty Jummai ta sauke ajiyar zuciya jin basu ambaci sunan ta ba, but ranta a b’ace yake plan d’inta yayi ruining.
” Akan dubu goma kuka zab’i ku zalunci baiwar Allah, bakwa tsoron hakk’i”, “Wallahi talauci yaja, abincin da zamu ci gagarar mu yake”, ” Talauci hauka ne?”,
“Kada kiga laifin su My mum, Talaka zai iya yin komai akan cikar burin sa”, (Da biyu yayi maganar, wanda da Fetta yake)
Kamar daga sama suka ji muryar sa, A ranta tace ” Wai shi kamar aljani sai da ka jiyo muryarsa”, Maganar shi ta shiga nanatawa, Tana fatan watarana ya fuskanci ba kowanne talaka ne haka ba.
“Ku tashi ku fice, munafukai kafin na fara k’wallo daku”, A tsorace suka mik’e sukayi waje, ” Kiyi hak’uri Fetta mun zarge ki”, Cewar Aunty Jummai tayi wani fuskar tausayi, A zuciya kuwa ji take kamar ta shek’e Fetta, “Ba komai”,
Suraj zama yayi kan kujera, Ya kafeta da ido, Kanta na sunkuye k’asa, Tunani daban daban yake akan ta, Yana imagining yadda zasu yi rayuwar aure bayan babu ko d’igon son ta a ranshi.
Hajiya ta k’ara ba Fetta hak’uri, Ta nuna ba komai, Suka koma gida da Aliya,
Da tunanin wane irin dangi zata shiga tun yanzu an fara bin ta da sharri, Allah ya mata kariya da dukkan sharri, Aliya ma ta mata nasiha akan ta dage da addu’a.
*Safiyar Asabar*
A ranar aka d’aura auren FETTA da SURAJ SA’IDU, Dubban mutane sun hallara dan ba k’aramar gayya Hajiya tayi ba, Angon Suraj yasha farar shadda da babbar riga sai d’aukar ido take, Ta matuk’ar yi mishi kyau, Fuskar sa sam ba annuri da angwaye ke yi, Yak’e dole kawai yake, But wannan rana tana d’aya daga cikin ranaku marasa dad’i a rayuwar sa(Hmm).
Fetta tun da taji muryar Malam na fad’in an d’aura aure, Kanta ya wani sara, ta nemi natsuwarta ta rasa, Zazzab’i sosai ya rufeta ta lullub’e cikin bargo, Yan’uwa da abokan arzik’i nata shigowa Allah ya sanya alkhairi,
Rumaisa da sauran k’awayen ta suka shigo suna tambayar ina Amarya, Aliya tace su duba d’akin ta,
“Baccin lafiya kike” Rumaisa ta fad’a tana yaye bargon, hucin zazzab’i taji, “Allah Sarki, duk tunanin first night d’in ne ya kwantar da ke”, Sauran k’awayen suka kwashe da dariya,
” Ina Fetta take ta fito ayi hoto”, Aliya ta shigo tana fad’a, Rumaisa tace “Bata da lafiya”, ” Subhanallah, Sannu Fetta”, Wata leda ta bud’e gefen katifa, Ta jawo magani, ta tashe ta ta bata tasha, “Yanzu zazzab’in zai sauka, ku tabbatar tayi wanka ta fito”, Suka amsa da ” Toh”
Cikin minti 30 ta fara zufa alamun zazzab’in ya sauka, Rumaisa ta had’a mata ruwa, tayi wanka, Mai kad’ai ta shafa, ta saka shadda d’inkin doguwar riga, da tasha stone work, Cikin lefen ta aka sako shaddar, Har yau bata san kayan lefen ta, a tunanin ta ma Aliya ce ta mata na fitar biki (Ina Aliya ina siyan shadda mai tsadar wannan LOL)
“Wai ke ko yar’ powder ba zai Shafa ba kina Amarya”, ” Bar ni a haka”, “Anjima idan zamu kai ki, dole na kira mai kwalliya ta k’ara matso mana kyan ki, yadda ango zai rikice yasan yayi dace”, Fetta shiru tayi bata ce komai na,
Anyi hotona iri-iri, Har Hajiya tayi da tsayuwa, Ta koma d’aki a gajiye.
Wunin ranar bata ci komai ba, sai ruwa da take d’irka ma cikin ta, Rashin natsuwa ba zai barta taci ba.
Saliha ta k’ara zama ranar, Su Rumaisa ke ta surutun su bata saka musu baki ba, Ana idar da sallar magrib, aka fara shirye-shiryen kai Amarya, wani wanka Aliya tasa ta sake ba dan ranta yaso ba, Ta fito da kanta ta mulke ta da wani cream mai k’amshi, Tace ” Su Rumaisa su k’arasa shiryata”
Atamfa super(itama cikin lefen take), Ta saka d’inkin riga da skirt, Mai make-up ta tsantara mata kwalliya, Su Rumaisa fad’in Wow suke da irin kyan da tayi, “Gaskiya Fetta ba k’aramar kyakkyawa bace ke, Wallahi samun irinki da wuya”, Faryda ta fad’a, Kowa ya shiga tofa kyawunta, A ran ta tace ” Tubarkallah”,
Babban gyale da yasha turare aka yafa mata a kai, Fetta da ta kalli kanta a madubi mamaki take itace gaskiya ba abunda baya son gyara, Tana ji ance su fita, Kuzarinta ya tsinke,
Tana ji tana gani aka fitar da ita daga gida, Da addu’a ta fita a bakin ta, K’irjin ta bai fasa bugawa, aka shiga motoci suka kai Amarya, Gani take tamkar a mafarki, Ta auri Suraj mutumin da ko a mafarki bata tab’a tunanin zata zama matar sa ba, igiyoyin sa uku sun hau kanta, Hannun Aliya taji cikin nata, Ta matse shi gam.
Fuskarta a lullub’e har suka shiga b’angaren Hajiya, Ta rik’o ta tana mata nasiha, Hawayenta sun kafe duk yadda taso zubar dasu ta kasa, Yanzu matsayin surukar Hajiya take, Allah mai yadda yaso a lokacin da yaso.
Daga sashen Hajiya, aka nufi sashen Suraj da ita, Nan fah bugun k’irjin ta ya k’aru, tana jin kamar ta fisge ta zunduma da gudu, Tana jin yadda suke yaba kyau da tsaruwar sashen, Suna fad’in ta dace, “Idan kam dan kud’i ake aure ta dace sai dai kash ana yi ne dan so, k’auna da tausayin juna, ta rasa duka a auren ta”
Gado mai masifar taushi da laushi taji an zaunar da ita, Aliya ta shiga yi mata nasiha, “Ki zama mai ladabi da biyayya da hak’uri zaki ci ribar”, Sune kalamanta na k’arshe, Ta k’ara da ” Allah ya bada zaman lafiya”
Bata k’ara shiga tashin hankali ba, sai da kowa ya watse ya bar ta, Tausayin ta kanta da maraici ya dabaibayeta ta shiga raira kuka, Ga marar ta ma murd’a mata kad’an kad’an.
“Amana ce Allah ya baka, Hakk’in ta daga yau ya rataya kan ka, Cin ta, shan ta, suturar ta duka sun rataya a kan ka, ka kula da ita idan baka son b’acin raina, abu na k’arshe ban yarda ku raba d’aki ba, a d’aki d’aya nake so ku zauna”, Wani tashin hankalin yaji, A da yana jin dad’in babu ruwan sa da ita, Mama so take ta kashe shi, Gaba d’aya ma ya raina tsaftar ta, Buzaye dama da k’azanta, 1
Ta katse mishi tunani ” Kaji me nace koh?”, Da k’yar ya iya furta “Toh”, ” Ga Leda can kan dining table d’auka ka tafi Allah ya bada zaman lafiya”,
Mik’ewa yayi yana jin duniyar ta k’ara mishi zafi, Taya zai yi bacci a d’aki d’aya da ita, Tambayar da yake ta nanatawa kansa.Da sallama cikin takun sa na k’asaita ya shigo d’akin, Tana jin sa k’irjinta ya buga, Tayi saurin k’ara jan mayafi ta lullub’e fuskar ta sam bata so ganin shi, +
“Wake son kallon ugly face d’inki, kin taimaka da kika k’ara rufewa”, Shiru tayi tamkar ba da ita yake ba, Tasan daga yau tayi sallama da wulak’anci, bata zama matar shi ba, ya mata balle yanzu,
” Yadda bana son auren ki, haka bana sha’awar kallon fuskar ki, Auren ki yana cikin kundin k’addarata mara kyau”, “Kamar yadda nima auren ka yake cikin nawa”, Wata dariya yayi yace “K’arya kike babu macen da bazata so auren namiji mai kud’i da kyau ba, Mata duk halinku d’aya”
A ranta tace “Zaka san na bambamta da saura”, Ledar dake hannun shi ya ajiye gabanta, Wani k’amshi mai sihirtaccen dad’i ya daki hancin sa, wani shock yaja sa kamar ya fad’a mata, Yayi saurin ja baya, ” Ba turaren asiri ba ko bori zaki hau ba zaki tab’a jan hankalina ba”,
“Turaren asiri”, Ta nanata a ranta, ” Wannan mutumi da rainin hankali yake”, Shi kam har ga Allah ya d’auka na asiri ne saboda yadda shock yaja shi,
“Ga kaza inji Hajiya, tasan kina jin yunwa”, Yana fad’ar haka ya shige toilet,
Ta d’auka fita yayi, Ta sauke ajiyar zuciya, Ta yaye lullub’in ta, Mugun yunwa take ji, Ta sauko kan gadon, Ta zauna k’asan carpet, Ta fara ci, tana kurawa da lemo,
Suraj wanka yayi, Ya fito d’aure da towel iya waist, hankali kwance bai damu da ta gansa haka ba, Kallo d’aya ya mata yaga tayi wani masifar kyau kamar ba ita ba, Yayi saurin kawar da kai, Yana neman tsari daga ita, ” Ko shakka babu wani lak’ani ta karb’u”, Yace wa kansa,
K’arasawa yayi dressing mirror, yana shiri, Juyowar da zatayi da niyyar mik’ewa ta shiga toilet, Taga mutum ba kaya, da sauri ta runtse ido gabanta na fad’uwa, Ko Mahaifinta bata tab’a gani haka ba,
Har ya gama shirin sa idonta a rufe, ba tare da yabi ta kanta ba, Ya hau kan gado, Ya kwanta tsakiya ya babbaje yadda ba zata samu space na kwanciya ba, ba zai tab’a had’a kwanciya da ita ba, sai dai ta kwanta k’asa,
Daina jin motsin sa, Ta bud’e ido, tana sauke ajiyar zuciya, “Me ya dawo yi d’akin nan, a wannan yanayi bayan yasan ina ciki”, ” Iskanci”, Zuciyarta ta fad’a mata, Toilet ta shiga, tsayawa tayi kallon kyau, had’uwa da tsaruwar bayin, Komai tsaf kamar ba bayin namiji ba, Ta wanke hannu, ta watsa ruwa, Towels da ta gani rataye, ta jawo d’aya, Ta fito d’aure da towel,
Idonsa rufe suke tamkar mai bacci but duk wani motsin ta yana ji, Rigar bacci mai shara-shara iya gwiwa ta saka, ba tare da jin fargaba ko kunya ba, Tasan ita kad’ai zata kwana,
Zuciyarta ta mugun bugawa, Ganin mutum kwance kan gado, Da sauri ta shiga k’ok’arin jawo hijab ta saka, “Me yake nufi?, a nan zai kwana?”, Ta jefowa kanta tambayoyi, Ba zata iya kwana d’aki d’aya dashi ba, K’ofar d’akin ta bud’e a hankali, Ta nufi falo, Kan doguwar kujera ta kwanta, Cikin ikon Allah bacci ya d’auke ta.
Suraj bai ji fitar ta ba, dan tuni bacci ya d’auke sa.
Bilkisu tayi tagumi tana zubar hawaye ” Mama wallahi a da bana son Suraj, rabuwar mu na kamu da masifar son sa”, Aunty Jummai tace “Tsinanne malamin can ya cuce mu, kud’inmu kawai ya karb’e ba biyan buk’ata”, ” Mama ki taimakeni na koma gidan Suraj”, “Taya zaki koma bayan yayi aure”, ” Ko a ta biyu ce zanje”, “Na raba ki da kishiya, bata da dad’i, makira ce, zan fara fitar da ita gidan, sai ki koma”, Tace ” Toh Mama”, Tana sharar hawaye.
STORY CONTINUES BELOW
Kiran sallar assalatu a kunnen Fetta, Ta bud’e ido tare da karanta addu’a, Ta mik’e mararta ta masifar murd’awa, dole ta koma ta zauna, tana dafe mara, Sosai take jin azaba, tuni hawaye suka shiga ambaliya kan fuskar ta,
Suraj da ya farka bai ganta d’akin ba, Yace “Allah yasa ta tafi gidansu, da safe ya aika mata takardar ta”.
Brush da alwala yayi, Ya saka jallabiya ya fito zuwa masallaci, A falo ya ganta durk’ushe, Tsaki yayi na rashin jin dad’in ganin ta, Ya wuce ba tare da yabi ta kanta ba.
Fetta ta kasa ko da k’wakk’waran motsi, kewar Aliya taji sosai, itace a duk lokacin da ciwon mara yazo mata, take bata taimako,
Har ya idar da salla ya dawo, tana gurin, Yaso yajii shesshek’ar kukan ta, Ya wuce d’aki abun sa, Ya hau gado ya kwanta, Hankalin sa yaji ya kasa kwanciya, Da lafiya take ba zai je har ya dawo tana wurin ba, ” Hakk’in ta ya rataya a kanka”, Maganar Hajiya ta fad’o masa a rai,
Ya fito ya nufi falo, Ya dad’e tsaye kanta yana tunanin ya zai mata magana, Baya jin zai iya tambayar ta matsalarta, a ganinsa zata raina shi,
“Ke me kike anan?”, Bata amsa shi ba, azabar da take ji ta isheta, ” Maza tashi kafin nayi ball dake”, Yace hakane dan ta fad’i meke damunta, Hannu ta shiga yarfawa alamun azaba, Tsaki yayi zai bar wurin, Ganin tafiyar sa zai yi kuma babu mai taimakon ta tace “Cikina”, Kamar zai ce mata sannu, yaji kalmar ta masa nauyi a baki, D’aki ya koma, Ya d’auki waya ya kira Family doctor su,
” Mugu mara tausayi, dama nasan ba zaka ji tausayina ba”, Ta fad’a hawayenta na k’aruwa, A tunanin ta tafiyar sa yayi,
Cikin minti 15-20 Dr Yusuf ya iso, Ya kira Suraj yace gashi, Ya mishi iso ya shigo, Da hannu ya nuna mishi Fetta, Ya zauna kan kujerar yana latsa waya,
“Sannu Amarya”, Ta d’ago jin muryar wani, Daga shigar sa ya tabbatar mata likita ne, bata tab’a zaton zai kira mata Dr ba, ta d’auka zai bar ta ciwon ya kashe ta,
” Meke damun ki?”, Ta kalli Suraj taga hankalin shi baya kansu, Murya k’asa k’asa tace “Ciwon mara”, ” Idan zaki yi period kike yi?”, Kunyar tambayar taji ta sunkuyar da kai k’asa, “Don’t be shy, ki bani amsa”, Kanta ta d’aga sama, ” Ok “
Rubutu yayi a wata takarda, Ya mik’e yaje gaban Suraj, “Sir ga drugs da za’a siyo mata she will feel better”, Ya mik’a masa cike da ladabi, A girme zai girmi Suraj, but kud’i yasa yana girmama shi, Ya karb’a yana dubawa, Da kai ya masa alama, Yace ” Zan koma”, Ya juya kan Fetta “Amarya Allah ya bada lafiya, Allah ya kawo yan biyu”, Ya kalli Suraj ko zai ga far’a akan fuskar sa, but ya d’aure tamkar bai ji me yace ba.
Taji alamun zuwan bak’on wata, hankalinta ya tashi sanin bata da pad, gashi tana rushing, Mutsu mutsu ta shiga tana tsoron tashi taga ta b’ata wurin, Ga Suraj bashi da niyyar tashi,
Kusan minti 10 suna haka, Yana faman danne-danne a waya, Kiran sa akayi ya tashi ya shiga d’aki, da alama baya so taji wayar.
D’agawa tayi kad’an ta duba, aiko tayi staining, ta zaro ido, jin fitowar sa tayi saurin komawa ta zauna, Ya fice waje, Hamdala tayi, Ta mik’e ta shiga d’aki direct toilet ta nufa, ta tsaftace jikinta, D’ankwalin wata tsohuwar atamfarta ta nannad’a ta saka, Ruwa da omo ta zuba a rubber,
Tana fara zubawa a kujera, Ya shigo idonsa kan kujerar wurin da tayi staining, ” Ke k’azamar ina ce”, Ya fad’a yana yatsina fuska kamar yaga kashi, Kanta ta sunkuyar kunya ta lullub’eta tana jin kamar ta shige cikin k’asa, “Na baki minti goma ki wanke trash d’in nan”,
A sanyaye ta d’ago tana gogewa, Kunya tak’i sakinta duk da ya bar wurin, Tana cikin gogewa taji sallama,
Ta tashi ta bud’e k’ofar, Driver ya mik’o mata leda yace ” Mai gida yace a baki”, Ta karb’a ta koma ciki, Ajiye ledar tayi, sai da ta gama goge wurin tas, Tana so ta shiga d’aki ta d’auko turare ta saka, tana jin kunyar had’uwa dashi, Ledar ta bud’e drugs ne a ciki hadda pad, For the first time ta yaba yayi abun kirki, na siyo mata pad.
Tunanin ta yadda zata shiga tayi wanka ta saka, Wata k’ofa ta gani, Da addu’ar Allah yasa d’aki ne ta murd’a handle, taji a rufe, runtse ido tayi cike da takaici, Mararta ta murd’a dama lafawa tayi, Fridge dake falon ta bud’e, shak’e yake da ruwa na gora, da drinks kala-kala, Ta jawo roba d’aya, Tasha magani.
Kusan awa d’aya bata ji motsin sa ba, bashi da alamar fitowa, Jin ta take a takure tana son tayi wanka, Agogon bango dake manne a falon ta kalla, 7:30am,
“K’ila ma bacci yake”, Zuciyarta ta fad’a mata, Mik’ewa tayi ta lek’a, Ya lullub’e cikin bargo yana baccin sa, K’arasawa tayi cikin d’akin,
Ta shiga toilet, wanka tayi a natse da ruwa masu d’umi, Dan’kwalin ta d’aure a leda, Ta fito dashi ta jefa a dustbin na bayan k’ofar kitchen, Ba k’aramin had’uwa yayi ba, Ta dad’e tana kalle-kalle tana mamakin mallakin ta ne, kafin ta koma d’aki,
A gaggauce ta shirya tana tsoron ya tashi, Doguwar riga d’inkin lace, ta saka ta matukar yi mata kyau, ta feshi jikinta da turaruka, Falo ta fito ta zauna, Tunanin sabuwar rayuwar data tsinci kanta take, Taya zaman su zai kasance da Suraj mutum mai tak’ama, izza da murd’add’en hali.
Sallama taji ana yi, ta tashi ta bud’e k’ofa, Inno ce mai aiki rik’e da basket na abinci, Suka gaisa, ta karb’a ta mata godiya,
A dining table ta jera abincin, Tea kad’ai tasha, idan tana period bata iya cin abinci sosai, dama ya lafiyar giwa,
Shiru har 11 bata ji motsin Suraj ba, ” Wane irin baccin ne yake?” Tacewa kanta,
11:45am
K’amshin turaren sa ta fara jiyo daga d’aki, ” Mayen turare”, Ta fad’a,
Jin kamar tafiyar mutum, Ta d’aga kai charaf idonta cikin nashi, Sanye yake cikin shadda mai d’aukar ido, daga gani sabuwa ce, Kansa babu hula, gashin kansa na k’yalli tamkar mace, Kanta ta sunkuyar k’asa, “Ina kwana?”, Ya d’auki seconds tamkar ba zai amsa ba yace ” Lafiya”, Bata sake cewa komai ba, haka bata d’ago kanta ba.
Dining area ya nufa, Yayi serving kansa abinci ya fara ci, Cikin minti 15 ya kammala, Yasa tissue ya goge bakin sa, Ya mik’e yana kakkab’e jiki,
“Zamu je gaishe da Hajiya”, Ya fad’a a dak’ile, Yace tazo suje shine yake jin asara, Yaci darajar mijin ta ne, da ba zata mik’e ba, sai ya fad’a da ita yake,
Hijab ta zura, Kafin ta fito har yayi waje abun sa, Gab da zai shiga yaja ya tsaya, Gaba tayi abunta dan bata san dalilin sa na tsayuwa ba, Jawota yayi da k’arfi, ya tsayar da ita saitin shi, Ya d’aura fuska kamar bai tab’a dariya ba, Ta gane manufar sa saboda Hajiya,
A jere suka shigo, Hajiya na zaune kamar kullum, Suka durk’usa gabanta suna gaishe ta, Cike da far’a ta amsa, Tana musu ban gajiya, Suka amsa itama suka mata, Nasiha ta musu sosai da addu’ar zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba, Fetta a ranta tace ” Ba amin ba”, Bata fatan ya zama mahaifin yaran ta, Suraj bai damu da addu’ar Hajiya ba, yasan sai an had’a shimfid’a ake samun zuri’a, abunda ba zai tab’a faruwa ba tsakanin su.
“Zan shiga gari” Ya fad’a yana mik’ewa, “Allah ya bada nasara ya tsare ka”, Ya amsa da ” Amin”, Fetta har ya fice bata ce komai ba, “Baki ma mijin ki Allah ya tsare ba, ko kina jin kunya ne”, Yatsun hannun ta ta shiga wasa dasu alamun kunya, Hajiya tayi murmushi tace ” Tashi ki rakasa”,
Kamar ta zunduma ihu, ta mik’e tana tafiya tamkar wacce k’wai ya fashewa a ciki,
Jin kamar ana bin sa a baya, Ya juyo ganinta ya had’e rai “Ke lafiya kike bina”, Ta maze tace ” Ba kai nake bi ba, sashen mu zani”, “Point of correction, Sashena ne ni kad’ai babu komai naki a ciki, aro na baki na d’an lokaci kafin ki koma gidan ku”,
Ya wuce ya bar ta daskare wurin, Kalaman sa sun bak’anta ranta, Ba laifin sa bane dan yace haka, tasan ko cokali ba’a kawota dashi ba, dole ya goran mata, Allah yasa ya sallameta kamar yadda ya fad’a da tafi kowa farin ciki,
Rai a jagule ta shiga sashen, Aliya ta kira ko zata ji sanyi a ranta, ” Amarya”, “Umma ina kwana?”, ” Lafiya lau, ya kika kwana?”, “Lafiya lau”, ” Kin tafi kin barmu da kewa”, “Nima ina matuk’ar kewar ku, yaushe zaki zo?”, ” Sai jibi In shaa Allah, Hajiya ta buk’aci na daina aiki, ta bani jari mai tsoka na fara sana’a” (Ba zai yiyu Fetta na auren a gidan, Aliya na aiki ba), Cike da murna ta shiga yi ma Hajiya addu’a, Sun d’an tab’a hira, ta kashe wayar, Damuwa da b’acin ranta sun rage sosai,
“Ango! Ango!”, Cewar Munir, Ya had’e rai, ” Haba abokina kai da ya kamata ka washe baki kamar gonar auduga”, “Maintain” Ya fad’a a tsawace, Munir yaja bakinsa yayi shiru, yana mamakin wannan k’iyayya da yake wa mata, zai so yaga ranar da Suraj zai fad’a tarkon so.Mu’azzam da yaji labarin auren Fetta yaji ba dad’i, but yana mata Fatan alkhairi, Allah ya mata sauyi da wanda yafi shi, “Suraj yayi dacen mata”, Ya fad’a, +
” Meyasa kika zab’i zama karuwa, abunda Bash ya aikata miki bai isa ya zaman miki darasi ba”, Karima ta nisa tace “Abunda Bash ya aikata mun yasa naji tsanar iskanci da nadama, k’auracewar iyayena da nuna mun halin ko in kula, yasa na fad’a karuwanci dan na samu kud’in taimakon kaina”, ” Iyayen mu na kuskure, idan yarinya ta lalace maimakon a jawo ta a jiki ayi mata nasiha da lurarwa, sai a wofantar da ita daga haka yarinya ta shiga duniya” Cewar Bello (D’an Kawo lamid’o ya dad’e yana son Karima, itace ta k’i sa),
“Karima kiji tsoron Allah, ki tuba kiyi istibra’i ni zan aure ki na baki dukkan kulawa”, Murmushi tayi a duniya babu wanda take so sama da Suraj, tasan ya mata nisan da bara ta tab’a samun shi ba,
” Ya Bello ba nak’i tayin ka bane, amma ina tsoron abunda zai je ya dawo, kasan halin iyayen mu”, “Kada ki damu, ki bar komai hannu na”, Tace ” Allah ya tabbatar mana da alkhairi”, Ya amsa da “Amin”, cike da murna,
Ana kiran magrib Suraj ya dawo gida, Fetta na kwance kan doguwar kujerar falo, tasbaha ce a hannun ta tana lazimi, Da sallama ya shigo, Ta amsa, Ta tashi zaune tace ” Sannu da zuwa”, Ya kalle ta ya kawar da kai, Abunda Bilkisu bata tab’a masa ba, ko sau nawa zai fita ya dawo, bara ta d’aga kai ta kalle shi ba, idan ta mishi magana kud’i take buk’ata, ko tabi ta hanyar Hajiya.
Fetta tana k’ok’arin sauke nauyin da Allah ya d’aura mata ne, Bedroom ya shiga, k’amshin turaren wuta mai dad’i yaji d’akin nayi, gado da komai a gyare tsaf, Ya tab’e baki, ya shiga toilet, Ruwan d’umi ya tara a jacuzzi, ya shiga ya kwanta ciki, a hankali gajiyar da ya kwaso na barin jikin sa.
Knocking k’ofar ake yi kamar zata b’alle, A tsorace ta bud’e, Feena, Su’ad da k’awar su ne, Wani banza kallo suka bita dashi, Suka rab’a gefenta suka shiga ciki, kowaccen su ta zauna tare da d’aura k’afa d’aya kan d’aya, K’awar sai yatsina fuska take tana chewing gum, Fetta d’auke kai tayi, tana latsa waya, banda Suraj na ciki shigewa zata yi ta barsu, bata ciki da rainin wayon su,
“Baki ga mutane ne bane”, Banza tayi tamkar ba da ita ake ba, Su’ad tace ” Fetta dake muke magana”, “Amma Su’ad baki da kunya, ina matsayin matar yayan ki kike fad’in suna na gatsau”, K’awar su tayi shewa tace ” Lallai samun wuri”, “Ke fah yar’ firit daga ina”, A fusace Feena tace ” Ke yar’ matsiyata yar’ cin arzik’i”, Karaf a kunne Suraj,
Basu san yana ciki ba, sai ganin sa suka yi a tsaye, Su’ad tace “Yaya matarka sai rashin…..”, Wata tsawa da ya mata yasa tayi gum,
” Rashin mutuncin ku da iskancin ku har ya kai kan iyalina, ya zama na farko na k’arshe da wata cikin ku zata yi mata ko da kallon banza, yadda kuke daraja ni haka nake so ku daraja MATATA”,
“MATATA” Fetta ta nanata a ranta, tabi sa da kallo, Ya d’auke kai tamkar bashi yayi maganar ba, Ya cigaba “Ku bata hak’uri”, Kowaccen su ta shiga bata hak’uri, ” Ba komai K’anne na”, Da gayya ta fad’a, Rai a k’ufule suka fice,
“Bana son kowa ya fuskanci zaman da muke dake, har yaje kunne Hajiya, ina gudun b’acin ranta, tamkar yadda mutum ke gudu mutuwar sa”, Yana fad’ar haka ya nufi dining area, Ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana jinjina soyayyar da yake wa Mahaifiyar sa,
” Ya Suraj ya kira barorojin can Matar sa”, Su’ad ta fad’a unbelievable, Feena tace “Shima ta bashi a abinci ya cinye”, K’awar su Tasleem tace ” Baki ji yadda zuciyata ta buga ba, da ya kirata matar sa”, “Don’t worry Frnd, asiri na lokaci ne, ke kika dace da Ya Suraj me zai yi da matsiyaciya”, Haka suka cigaba da zagin Fetta.
STORY CONTINUES BELOW
Sha biyu na dare, Fetta na kwance kan kujerar falo, tuni bacci ya fara d’aukarta, Taji kamar motsin mutum, A tsorace ta bud’e ido, tsaye ta ganshi kanta, K’irjinta ya buga, ko mafarki take, idon ta ta murza, still shine sanye da pyjamas,
” Kin iya dafa indomie?”, Ta d’aga kai, “Na baki 20mins ki dafa ki kawo mun d’aki”, Bai jira amsar ta ba, ya koma ciki, Yunwa ta dame shi, babu sauran tuwon dare, yaba masu gadi, Yasha tea amma kamar an k’ara masa yunwa.
Hijabin dake jikinta, ta gyara, Bacci ne sosai a idon ta, Agogo ta kalla 12:05, ” Cikin dare a tashi mutum, a sashi aiki da command, tsabar isa”, Ta shiga kitchen tana gunguni, Tattasai da attarugu ta fara gyarawa ta jajjaga, ta d’aura tukunya, Cikin minti 25 ta kammala, Indomie tasha sardine, kitchen ya game da k’amshi, A plate ta zuba, ta rufe da wani plate, ta saka fork gefe, ta bud’e fridge ta d’auko ruwa masu sanyi da cup, ta jere akan tray,
Sallama tayi bakin k’ofa, zuciyar ta cike da fargaba Allah yasa yayi appreciating, she want to sleep in peace, bata son abunda zai dagula mata lissafi a daren nan,
“Yes, Come in”, Ya fad’a with command, Ta shiga ta ajiye gabansa, Ta juya zata fita, Yace ” Wa zai fitar miki dasu”, Dawowa tayi ta zauna, tana kallon k’asan carpet,
Tuni k’amshin girkin ya dami hancin sa, Ya bud’e ya fara ci, wani shegen dad’i yaji, bai tab’a cin indomie mai dad’in ta ba, but ya shiga yatsina fuska, “Sai dai mutum yaci dan yunwa”, Ya fad’a a fili, Taji sa tayi kamar bata ji ba,
Bacci ya fara fisgarta, a wurin ta b’ingire tana bacci, Tass ya cinye ko k’waya bai rage ba, Ya kalleta tana sharar bacci hankali kwance, kamar zai tashe ta ya k’yaleta, Ya kai kwanukan kitchen, Ya dawo ya kashe wutar d’akin yabi lafiyar gado.
Har ya tashi sallar asuba, bata farka ba, Bai bi ta kanta ba, Yayi alwala ya fice masallaci, Dawowar sa yayi daidai da tashin ta, Da sunan Allah ta tashi a baki, tana mamakin baccin ta a wurin, Ta mik’e zata fita suka kacib’us bakin k’ofa, Tayi saurin ja baya,
” Koma ki gyara d’akin nan, ki goge wurin da ki zubar da yawun bacci”, Mamaki ne ya kamata, a iya saninta bata yawun bacci, da ta tashi bata ga wata alama na tayi ba, “Wulak’anci ne irin nasa”, Zuciyar ta fad’a mata,
Gadon ta gyara a natse, kayan sa da ya cire, ya shiga wanka, ta d’auka ta saka a laundry basket dake corridor d’akin, Tana shara ya fito wanka, Tayi saurin ajiye tsintsiya zata fita, ” Dawo” Ya umarce ta, “Uhmm ka gama shiryawa kar na watsa maka datti”, ” Jikina ko jikin ki”, Bata sake cewa komai ba, ta cigaba da shara, sai da tazo saitin sa, ta watsa mishi datti, Tayi kamar bata sani ba, Yasan da gayya tayi, a ransa yace zanyi maganin ki,
“Kee!”, Ya fad’a a tsawace, Da sauri ta d’ago kai, Ya saki towel yana kakkabe jiki, Gabanta yayi mugun fad’uwa, K’ara ta saki ta jefar da tsintsiya tana rufe ido da hannu biyu, ” Me kike rufewa ido, tunda kika b’ata mun jiki sai kin wanke”, Ya fad’a yana dariyar mugunta,
Idonta ta k’ara damtsewa tace “Dan Allah kayi hak’uri wallahi ban sani ba”, ” Me ye hak’uri, babu shi a dictionary na”, Zubewa tayi k’asa, kamar zata yi kuka, ta shiga rok’on sa, Yace bai san zance ba, ta wuce su shiga toilet ta wanke masa jiki da ta b’ata.
Hawaye ta fara, Shi dariya ma ta bashi yadda duk ta tsore, Sab’anin matan yanzu dake alla-alla su tab’a jikin namiji, Ya kawar da tunanin Yace “Zan hak’ura amma da sharad’i d’aya”, ” Na yarda kome ye zan yi”, “Kullum zaki rik’a wanke mun inners, kuma duk dare kimun tausa har bacci ya d’auke ni”, ” Kayi hak’uri “, ” Toh tashi muje ki wanke jikina”, Tayi saurin cewa “Zanyi wallahi”, ” Oya tashi ki k’arasa shara”
Har ta gama sharar bata bari sun had’a ido ba, Ta fice a kitchen ta zauna tana sharar hawaye, zuciyarta cike da nadamar watsa mishi shara, Gashi ta jawowa kanta, taya zata rik’a mishi tausa kullum, ga wanke inners na k’ato kamar shi.
Yayyen da k’annen Aliya tare da yaran su, Suka zo gidanta, Suka ce ta kaisu suga gidan Amarya, basu zo biki ba, Taji dad’in ganin sun hak’ura, bata san manufar su suje su kwashi banza ba,
Suraj tuni ya fice bayan ya biya ya gaishe da Hajiya, ta tambaye shi lafiyar Fetta, yace tana lafiya,
Fitar sa tayi wanka, tayi shirin ta tsaf, tana k’amshi gidan ta ma ya game da k’amshin turaren wuta mai dad’i, Ta dawo daga sashen Hajiya kenan, bata rufe k’ofa ba, Su Aliya suka shigo, Ta rungumeta cike da murna, Ta karb’i Ali, ta gaishe dasu Yaya Hafsa, Suka zagaya gidan suna yaba kyau da tsaruwar shi, A falo suka baje suna kiran yunwa,
Luba(Yayar Aliya) tace “Kitchen zamu shiga mu girka abunda muke so, dama bamu yi tuwon amarya ba”, Aliya kamar tayi musu magana, gudun ya zama fitina, tayi shiru, Suka shiga kitchen, K’atuwar tukunya suka d’aura jollof, kaji biyar suka soye, hadda k’wai suka soya, Fridge suka bud’e suka kwashi drinks,
A falo suka baje suna ci da yaran su, Aliya ta d’ibarwa Hajar shima dan tasa rigima ne, Fetta na zaune gefe na kallon yadda suke ci hannu baka hannu k’warya, ” Dad’in yar’ka ta auri mai kud’i kenan”, Ya Hafsa ta fad’a tana cika baki da kaza, “Wallahi kuwa”, Cewar Ya Luba,
Aliya sam bata jin dad’in wannan d’abi’a da suke, Fetta tsoronta Suraj ya dawo ya shuka musu rashin mutunci.
Tun daga bakin k’ofa yake jiyo hayaniyar yara, A tunanin sa ko yan’uwan sa ne,
Da kallo yabi falon, Suka shiga gaishe sa, Hannu ya d’aga musu, ya jefawa Fetta wani shegen kallo, Ya shige ciki, hantar cikinta ta kad’a, Ya Luba tace ” Ku tashi mu tafi, masu gida sun dawo”, Abincin suka shiga juyewa a leda, “Ki fad’a masa zamu wuce ko ma samu kud’in mota”, Cewar Ya Hafsa, Aliya tace ” A’ah Ya Hafsat mu tafi kawai, tunda mun gaisa”, “Ke wuce kije ki gaya mishi”, ” Dawo Fetta, tunda mun cika cikinmu ai shikenan”, Suwaiba ta fad’a, Rai bai so ba Ya Hafsa ta fice suka tafi,
Duk abunda suke fad’a yana jin su, yaja tsaki cike da takaicin hali na talaka da kwad’ayi,
Fetta ta musu rakiya bakin gate, Aliya ta jata gefen tana bata hak’uri, Da k’ara mata hud’ubar zama da miji, Ta mata godiya.
A falo taci karo dashi a tsaye, Ya had’e rai kamar hadarin gabas, “Bazan d’auki mayunwatan dangin ki na zuwa gidana, suna b’atawa da nuna tsantsar kwad’ayi, meye ma’anar haka?”, Ya fad’a yana nuna wurin da suka yi kaca kaca da abinci, ” Idan abinci suke buk’ata zan rik’a aika musu ba sai sun zo maula ba”
Fetta ta kasa motsi balle tayi magana tamkar wacce ruwa yaci, Ta tuna Aliya tace ta bashi hak’uri idan ya nuna b’acin ransa, sune da laifi, Ta danne b’acin ran dake taso mata, Tace
“Kayi hak’uri, hakan ba zai k’ara faruwa ba”, Kallo yabi ta dashi, bai tab’a tunanin zata bashi hak’uri ba, ko Su Feena yana da wuya ya musu fad’a suce yayi hak’uri, Dad’in bashi hak’urin yaji har cikin ransa, Bai sake cewa komai ba, Ya koma d’aki.
Fetta ta lura da sanyin da jikinsa yayi, Falon ta shiga gyarawa cike da takaicin halin su Yaya Hafsa.